Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Nayi sorry yan matana, amma kar a sake daga yau."

Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah."

Da hirarsu ta farin ciki suka isa gidan, ta falon Hafsat suka sake shiga kuma sunyi sa'ar samunta zaune tare da Aisha suna karatu, abun haushi shi ne kallon da Aisha ke musu shi da Mimi, gashi bai ji ta gaishe da ita ba sai ma Mimi ce tayi k'ok'arin fad'in "Aisha karatu ake?"

Amma sai ya ga ta mik'e ranta a b'ace tana fad'in "Amie saida safe."

Da kallo ya bi Aishar har ta shige, Mimi ma d'akinta ta nufa tana fad'in "Saida safenku."

Shigewa tayi ta barshi tare da Hafsat, shi ma yau babu fara'ar nan ya kalleta yace "Zan shiga ciki nayi wanka, kafin na fito ina buk'atar ganin duka yaran nan a falona."

Da fara'a ta amsa mishi da "Angama sheikh nawa."

Shigewa yayi ta bishi da kallo sai kuma tayi saurin mik'ewa ta je had'o mishi kan yaran da tunanin ko lafiya? Bai d'auki lokaci ba ya fito daga wanka ya shirya cikin jallabiya fara tas da ita, yana fitowa falon kam ya samesu dukansu har da Munzeer, mutmushi yayi na jin dad'in girmama maganarshi da Hafsat tayi, duk da abinda zai fad'a yanzun bai shafi Munzeer ba, amma da yace yaran duka saita tasoshi daga bacci shi ma, dan gashi nan kanshi a cinyarta tana daddab'ashi ya tashi saboda ganin sheikh ya fito.

Zaune yayi akan sofar yana kallonsu dukansu, had'e fuska yayi sosai cikin fad'a da muryar tashin hankali yace "Auren da nayi ne yasa nake gani raini k'arara a idonku ko kuma dama can akwai rainin tsakaninmu yanzu ne ya fito? Shin haramun ne na aikata da girmansa ya gawurta har zai iya janyo min rainin 'ya'yan cikina dana haifa? Me na yi? Akan me?"

Ya k'arashe yana kallonsu musamman ma Aisha da Heezam, duk sanda kawunansu sukayi hakan yasa shi d'orawa da fad'in "Auren da nayi? Ko kuma yarinyar ce bata muku ba? Bana son tashin hankali kun sani, amma daga auren yarinya har zaku fara min kallon hadarin kaji har wasunku ma zasu iya bud'a baki su min tambayar da duk ta zo bakinsu bayan na tabbata kuna da hankalin tauna magana kafin ku furtata, to akan me?"

Jinjina kai yayi tare da k'wafa yace "Da ba'a aure ai da ban haifeku ta hanyar aure ba, k'addarata ce ta kawo Mimi a Wanda k'arfina ya fara k'arewa, idan zamuyi adalci yarinyar ce abar dubawa anan, amma ku mahaifiyarku kawai kuka sani, ita kuke taya wa kishi kenan? Shin ita kunga tayi makamancin abinda kuka min ne a yau d'in nan? Haka kawai na tsaya gabanku kuna k'are min kallo cike da raini da son tantance me na aikata da matata a d'akinta."

Kallon Hafsat yayi a sanyaye yace "Qawwama bana da matsala da ke, na tabbata kina iya k'ok'arinki akan tarbiyar yaran nan, amma ki sani zanyi wani abu da ban san ko zai miki dad'i ba, kasancewata uba namiji dole na d'auki matakin gyara kan iyali tun yanzu, dan a yanda na fahimta idan lamarin nan ya gawurta wata rana zan iya shigowa gidan nan na samu d'aya a cikin yaran nan suna dakuwa da Mimi, musamman ma da suke ganin shekarunsu d'aya kumaa tsayinsu d'aya da ita."

Kallon Aisha yayi yace "Ki shirya ma aurenki ranar juma'a mai zuwa insha'Allah."

Kallon Heezam yayi yace "Zan gama kammala maka shirin tafiyarka Madina a satin nan, da zaran kaga d'aurin auren yar uwarka zaka bar k'asar nan."

Kallon Aswan yayi yace "Daga sallah magriba zuwa isha'i zaka fara darasi tare damu a majalisin su Anas, daga isha'i zuwa lokacin da zaka kwanta bacci zaka kasance a d'akin karatu na kana bitar karatunka."

Duka yaran kallonshi suke kowa kamar zaiyi kuka musamman Aisha data fara hawaye, amma sai suka sadda kawunansu k'asa Heezam na fad'in "Ka gafarcemu Abie, mun tuba ba zamu k'ara ba insha'Allah."

Aisha ma da sauri tace "E Abie, ka yafe mana dan Allah, ba zamu sake ba wallahi, zamu d'auki aunty Mimi kamar mahaifiyarmu."

Da mamaki ya kallesu yace "A ganinku saboda ita ne na yanke hukuncin nan? Kar ku min gurguwar fahimta mana, hak'ik'a Aisha sai bayan aurena ne da naji wasu kalaman a bakinki na yanke hukuncin aurenki, amma sauran ai dama na jima da fad'a muku ina da wannan tsarin, yanzu ne lokacin zartarwa yayi."

Cikin shahsek'ar kuka Aisha tace "Abie ka yafe min ba zan k'ara ba, ina so na kammala karatu Abie ba yanzu na ke son aure ba."

Harara ya dalla mata yace "A lokacin da kike buk'atarshi kuma saiki kirashi ya zo?"

Kallon Hafsat yayi da ita dai tayi shiru take kallon yaran, amma fa a zuciyarta kamar zata kama da wuta haka take ji, a gaskiya hukuncin yanzu bai mata ba, dan ita ma kawai ta ta'allak'a haka da aurenshi da Mimi ne, akan me zai yanke ma yaranta wannan hukuncin? Saboda sun kalleshi kawai? Ajiyar zuciya ta sauke sanda yace "Hafsat me kika ce akan haka?"

Girgiza kai tayi a sanyaye tace "Ba komai sheikh, Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, Allah ya mana jagora a lamuranmu."

Wani tattausan murmushi ya saki yana kallonta, a gaskiya da zai bud'a zuciyarshi ya nuna mata irin girma da k'aunar da yake mata musamman halayen nan nata na karamci, tabbas da sai ta ji babu mace mai sa'a a duk duniya kamar ta, da zatayi rawa tayi tsalle ta buga k'irjinta a gaban dubbanin mata kan cewa babu kamarta. Kallon yaran yayi yace "Ku tashi ku je ku kwanta."

Mik'ewa sukayi jiki duk a sanyaye sai Munzeer daya shiga baccinshi a k'afar Hafsat, saida suka fita dukansu ya taso ya d'auki Munzeer d'in sannan ya kama hannunta ta mik'e, a hankali suka fita har suka k'arasa d'aki ya shinfid'eshi ya tofa mishi addu'a, d'aki ya rakata ita ma ta kwanta kafin ya mata saida safe ya fito.



*Alhamdulillah*
7/22/21, 10:14 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*45*



Yana shiga d'akin ya samu Mimi bacci ya d'auketa, saidai da alama baiyi nisa ba dan hannunta har yanzu rik'e da robar ice cream d'inta, karb'a yayi ya aje gefe ya tattare kayan ya aje sannan ya gyara mata rufarta dan tayi wanka ta saka kayan bacci.


*07:30*

A sanyaye take amsa wayar Hajia tana fad'a mata auren Aisha kamar yanda sheikh ya fad'a, cikin son kwantar mata da hankali na iya abinda zata iya kawai Hajia tace "Hafsat karki damu kinji, dama ai sheikh ya sha fad'a idan har ya tashi aurar da ita babu abinda zaiyi na bidi'a, kar ki bari shed'an ya raya miki cewa ya yanke hukuncin nan ne saboda auren da yayi, ki mata addu'a matsayinki na Uwa Allah yasa haka shi yafi alkairi kinji."

A hankali tace "Shikenan Hajia insha'Allah, yanzu ya maganar shirye shirye ko wani gyara?"

Murmushi Hajia tayi tace "Hafsat ai ke ce uwarta kuma kinfi sanin me ya dace da ita, kawai kiyi tunani sai ki tuntub'i Karima kuyi magana, na tabbata dai sheikh ba zai mata kayan d'aki ba dan shi baya cikin wannan tsarin."

A sanyaye tace "Haka yake fad'a Hajia, ba zaiyi kayan d'aki ba kuma ya baka 'ya sannan ya baka abincin da zaka ci, saidai yace a matsayin Anas naa d'alibin da yake ji da shi zai iya mishi kyauta tsakaninshi ne da shi wannan."

Hajia ce tace "To kin gani, kawai ki mata addu'a tunda yaran ke kanki kin tabbatar da yaron kirki ne."

A ladabce tace "Gaskiya ne Hajia, Allah ya tabbatar mana da alkairi."

"Ameen." Hajia ta fad'a kafin suyi sallama ta aje wayar ta fito dan shiga madafa ta taimakawa mai aikin da ke tayata aiki idan ta haihu.

Tun asuba daya tasheta ya tafi masallaci bata sake ganinshi ba, tana idar da sallah ta shiga gyaran d'akinta a nutse, duk da ba wani datti ko wani abun gyaran ke akwai ba, amma saida ta kimtsa komai tayi turaren ruwa dana wuta da kaskon na'ura, tana gamawa ta shiga wanka dan Alhamdulillah yanzu jikinta da sauk'i sosai, tana fitowa a wanka ta zauna ta d'auki ado kamar zata je gasar sarauniyar kyau, cikin wani leshi ta shige ta kashe d'aurin d'an kwali mai hawa-hawa.

Yanda tayi wani masifaffen kyau yasa ta kallon kanta a madubi har ta d'auki selfie, saida ta gama ta aje wayar ta tunkari k'ofar fita, yanda falonta ke ta tashin k'amshin turaren wutar data saka yasa ta fita a falon ta rufo k'ofar.

Falon Hafsat ta shiga da sallama a bakinta, Munzeer da Aswan ne suka amsa a tare suna kallonta, murmushi ta sakar musu tana k'arasawa da fad'in "Sannanku?"

Da ladabi da girmamawa Aswan yace "Ina kwana aunty."

Da fara'a tace "Lafiya lau Aswan, har an shirya tafiya makaranta?"

Da ladabi yace "E aunty."

Munzeer ta tarawa hannu tace "D'an Abbansa yaya? An shirya ne?"

Tasowa yayi da dariyarshi ya mik'a mata hannun, sunkuyawa tayi tana shafa kanshi tana murmushi tace "Ina mamanka?"

Madafa ya nuna mata yace "Tana ciki."

Murmushi tayi tace "Kunyi karin kumallo ne?"

Girgiza kai yayi yace "Shi muke jira."

Mik'ewa tayi daga sunkuyawar tace "Bari na shiga ciki to na kawo maka naka na musamman ko?"

Jinjina kai yayi yana dariya yace "To aunty."

Hanyar madafar ta nufa sai kuma Aisha ta fito tana gyara jakar makarantarta a bayanta da alama sauri take, ba tare da tunanin komai ba Mimi ta sauko da kanta tana fara'a tace "Ina kwana Humaira."

Kallonta tayi tana gimtse fuska, wani wawan tsaki taja ta ci gaba da takawa, ta gabanta ta wuce ta shiga madafar tana fad'in "Amie mun kusa makara fa, har yanzu baku gama ba?"

Girgiza kai Mimi tayi ta shiga madafar ita ma tana tab'e baki a ranta tana fad'in "Kinyi da yar halak yarinya, akan tsohon ubanki zaki min tsaki?"

Tana shigowa suka had'a ido da Hafsat dake aiki tuburan, dukansu murmushi suka ma juna inda Mimi tayi saurin fad'in "Ina kwana aunty?"

Da fara'a sosai ta amsa da "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?"

Jinjina kai tayi tace "Lafiya lau, aiki ake?"

Cikin sakin fuska tace "Wallahi, kinga yau kamar an d'auremu na rasa me ya tsayar damu."

Murmushi tayi tace "Allah sarki, yau da gobe kenan, bari na taimaka muku."

Kamar daga sama Aisha tace "Amie indai wannan matar zata saka hannu a abincin da zamu ci yanzu wallahi saidai na hak'ura da shi."

Da sauri Hafsat ta kalleta hankali tashe tace "Aisha kina lafiya? Me yake damunii ne? Wannan wane irin iskanci ne?"

Turo baki tayi haar da bubbuga k'afafu tace "Lafiya ta k'alau Amie, akan ta ne fa Abie ya daina son mΓ» har zai min auren wuri."

Zaburowa Hafsat tayi zata kwad'a mata mari sai kuwa tayi hanyar fita, Mimi dake k'ofar tsaye tana kallon Aisha da mamaki bata ankara ba ta bangajeta tana fad'in "Dallah malama matsa min ni."

Yanda ta had'a kanta da bango yasa Mimi sakin siriryar k'ara tana dafe k'eyarta dan ta ji zafi sosai, da sauri Hafsat tayi kan Mimi tana tambayar "Subahanallah! Mimi kinji ciwo ne?"

Daurewa tayi ta mayar da hawayenta ta k'ak'aro murmushi ta girgiza kai tace "Ba komai aunty, ki k'yaleta dan Allah."

A tsawace tace "Na k'yaleta fa kika ce? Aisha yarinya ce da har zata min d'anyan kai a gidan nan?"

Fita tayi a madafar a hassale, a sanyaye Mimi ta k'arasa kusa da mai aikin da take gaisheta ta amsa sannan suka ci gaba da aikin.

Hafsat na fitowa a fusace Aisha na daf da k'ofar fita tana ta kumburo baki, nunata tayi da yatsa tana fad'in "Abinda zaki min kenan Aisha? Wannan ita ce koyarwar dana miki? So kike ki nunawa duniya ni malalaciya ce kenan? Kina so ki fad'a da babban murya cewa ban isa dake ba?"

Cikin turo baki tace "Kiyi hak'uri Amie, amma faa ke ma kinsan gaskiya na fad'a, duk saboda ita ne komai yake faruwa."

A zafafe tayi kanta sai kuma Heezam ya fito daga d'akinshi shi ma a shirye, da sauri Hafsat ta kalleshi tace "Heezam kamo min hannun yarinyar can?"

Aisha na jin haka ta fita a guje hakan yasa Heezam kallonta sai kuma ya kalli Hafsat yace "Amie lafiya? Me ta miki yanzu da safe? Ban tab'a ganin b'acin ranki irin haka ba?"

Kamar zatayi kuka tace "Dole ne Heezam, yanzu duk abinda mahaifinku ya fad'a muku jiya ace bai shiga kan Aiaha ba, har ta tsaya tana wa Mimi rashin kunya kuma a gabana."

Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad'i yace "Kiyi hak'uri, ina ga fa dalilin da yasa Abie yace zai mata aure kenan, kinsan matsalar Aisha kafuwa."

D'aga kafad'a yayi yana feso iska yace "Ni dama a shirye nake da tafiyata Madina, dan gari ne da nake mafarkinshi kullum tun ranar da Abie ya labarta min zai turani can karatu, dan haka ban d'auki hukuncin nan da zafi ba, ya min dad'i ni kam."

Wata yar k'wallar tausayinshi Hafsat ta matso tace "Allah ya maka albarka, Allah ya taimakeka ya haskaka maka neman iliminka."

Murmushi yayi yace "Nagode Amie."

Takawa ya shiga yi yana kallonsu Aswan yace "Ku tashi mu wuce kunsan Abie baya so mu tsayar da dreba yayi ta jiranmu ko."

Mik'ewa sukayi inda Hafsat ke fad'in "To abun karin fa?"

Kallonta yayi yace "Amie lokaci ya k'ure, kawai idan munje zamu samu abinda zamu sa a cikinmu."

Jinjina kai tayi tace "To shikenan, Allah ya tsare."

Shafa kan Munzeer tayi tana masa murmushi tace "A dawo lafiya ko yarona."

Bye bye ya mata suna daf da fita Mimi ta fito da sauri tana fad'in "Ku tsaya ku tsaya."

Tsayawa duk sukayi suna kallonta, bred ne ta saka musu soyayyen dankalin turawa a ciki da k'wai da tomate fresh, ninkeshi duka tayi a tissus tana mik'awa kowannensu tana fad'in "Ai ba zaku tafi da yunwa ba, taya za'a fahimci karatu?"

A kunya ce Heezam ya kalleta dan gaskiya kwalliyar data cab'a sai ya gan ta wani wal-wal-wal, d'auke kanshi yayi yana fad'in "Ina kwana aunty."

"Lafiya lau." Ta fad'a sanda take mik'a mishi ta d'ora da "Antashi lafiya?"

"Lafiya lau." Ya fad'a yana karb'a da fad'in "Nagode."

Dukansu godiya suka mata kafin ta mik'awa Aswan tace "Ka mik'awa Aisha wannan."

Hafsat dake murmushi tana kallonsu ne tace "Ai da kin barta ja'ira ta je da yunwar."

Murmushi tayi tace "A'a aunty ayi hak'uri."

Ganin sun fita suna fad'in "Sai mun dawo Amie, sai mun dawo Aunty." Yasa su dukansu suka bisu da "A dawo lafiya, Allah ya tsare."

Suna ficewa Hafsat ta kalli Mimi tace "To me kika girkawa mai gidan? Iya fa yaran kawai muka d'orawa su da zasu tafi."

Murmushi tayi cike da kunya tace "Aunty ai duk abinda kika fad'a shi za ayi."

Girgiza kai tayi tace "A'a fa uwata, karki manta girkinki ne yau da gobe da jibi ke har nan da kwana biyar, dan haka wannan alhakin yana wuyanki, muje dai na taimaka miki da wani abun."

Cike da kunya ta sinne kai ta bi bayan Hafsat d'in, suna shiga ta tsare da tambayar me zata dafa mishi, dan haka kawai tace bari tayi sauce na k'wai da doya.

*Duk* abinda ya faru daga sanda Hafsat ke fad'awa Heezam abonda ya faru har k'arshe duk a idon sheikh daya shigo falon ta k'ofar dake fitowa daga falonshi, jin abinda ya faru yasa shi jin ba dad'i sosai, sai kawai ya share ya koma falonshi ya zauna.

Saida ta kamalla aikin nan tsaf Hafsat ta kalleta tace "Ki je b'angarensa ki ga ko ya dawo daga masallaci, ya kan jima dama bai shigo ba wani lokacin."

Jinjina kai tayi da ladabi ta nufi hanyar, a tsoro tsoro ta k'arasa ta k'wank'wasa tare da bud'ewa a hankali ta tura tana kuma fad'in "Salam."

Dake babu hasken fitila sai ta shiga waige waige, yana zaune kan kujera mai zaman mutum d'aya yana kallonta, saida ta sakΓ© furta "Salam."

Mik'ewa yayi a hankali yalallab'a yayi ramda k'ugunta, hakan ya haddasa mata sakin k'ara a tsorace, da sauri ya rufe mata baki da hannunshi yana fad'in "Shiiii! Ni ne."

Ajiyar zuciya ta saukea hankali ta kalleshi, had'a goshinsu yayi wuri d'aya ba tare daya d'auke hannunshi a bakinta ba yace "Banda abun *Marya* a duk duniyar nan waye yake da lasisin tab'a jikinki bayan ni?"

Lumshe ido tayi a hankali ta bud'e ta kalleshi, hannunta tasa ta d'auke hannunshi a bakinta tace "Ni ma kuma waye yake da hurumin tsoratani a garin nan idan bΓ’ tsohona ba."

Dariya yayi ya shiga neman bakinta saida ya kamoshi ya had'a da nashi ya shiga tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi ita dai saida tana yana neman zage mata zip d'in riga tayi saurin ja baya tana fad'in "Abdallah abinci na zo yi maka tayi fa."

Rik'o hannunta yayi yana sumbatar kuncinta yace "To ai sai na yi wanka ko?"

Jinjina kai tayi tace "To kayi wanka saika fito."

K'ugunta ya sake rik'ewa yace "To muje a tayani wankan ko?"

Zaro ido tayi baki bud'e tace "Lahhh! Ni d'in? Gaskiya kunya nake ji."

Murmushi yayi y'a lak'aci hancinta yana fad'in "Kunyar me? Shin ni ba naki bane? Ko kin manta mun zama d'aya ne."

Mak'ale kafad'a tayi tace "Gaskiya ni dai kunya nake ji."

Cak ya d'auketa ya nufi uwar d'akin da ita yana fad'in "Ba wani nan, idan baki taimaka min ba to zan fasa wankan ma."

Wutsil wutsil ta shiga yi da k'afafu tana fad'in "Abdul ka saukeni k'asa dan Allah kar na fad'o fa."

Murmushi ya saki yana fad'in "Ryam zan iya zagaye garin nan dake a haka babu abinda zai sameki."

Kallon fuskarshi tayi ta sagala hannayenta a wuyanshi tace "Da gaske?"

Girgiza kai yayi yana murmushi, dan sosai take bashi mamaki idan yayi magana tace wai da gaske? Sai yaji wani daban a zuciyarshi yana jin wani nishad'i, tunda har shi ma zai iya yin magana ayi tamtama gaskiya ya fad'a ko akasin haka. Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi tace "Shikenan, ni kuma yau sai ka goyani ma nayi bacci a bayanka."

Suna shiga d'akin ya sauketa yana fad'in "Ko zamu jaraba ne ki gani."

Tattare siket d'inta tayi ta taka gadon sannan tace "To juyo bayanka."

Da dariya ya tsaya kusanta ita kuma ta haye bayanshi, takawa ya fara yi da ita a tsakar d'akin yana fad'in "Kinga a haka sai na zaagaye k'asa d'ari ba d'aya dake."

Dariya tayi ta d'ora hab'arta a kafad'arshi tace "Kenan gari na d'ari d'in ba zaka iya ba?"

Dariya yayi ya duk'a da ita kamar zata fad'a ta gaba yana fad'in "Ke ko? To me zai gagareni indai a kan ki ne?"

D'an bubbuga bayanshi tayi tace "Wai baka jin ciwo a bayanka?"

D'an d'ago kanshi yayi ya kalleta yace "Me yasa kika tambaya?"

Sunkuyar da kai tayi tace "To ai naga irinku..." Dariya tayi ta kwanta a bayanshi sosai kamar zatayi bacci tace "Shikenan dai."

Girgiza kai yayi yana dariya yace "Tsofaffi iri na kike nufi ko? Ryam ban tsufa ba yanda kike tunani, amma sannu kad'an zan tabbatar miki da haka."

Duk'o kanta tayi ta kafad'arshi tace "Ta ya ya akaramakallah?"

Kamar daga sama ta ji ya juyo da ita gabanshi da k'arfi kuma ya rik'eta gam tare da yin k'asa da ita kamar zata fad'i k'asa, rintse ido tayi ta k'amk'ameshi sosaai, cikin kunne ya rad'a "Kin amince na nuna miki?"

Girgiza kai tayi ta bud'e ido tace "Na yafe, na tuba Abdul."

D'agata yayi ya direta k'asa ya jata zuwa ban d'akin yace "To muje a min wanka Innar Issa."

Binshi tayi suka shiga ban d'akin, yanda ya tilasta mata yasa ta b'alle mishi botiran jallabiyarsa shi kuma ya cire, rintse ido tayi sosai tace "Abdallah fita zanyi waje kafin na suma a nan."

Rik'eta yayi yace "Babu inda zaki je, ki suma a nan na gani."

Da k'yar ta samu ta kubto ta baro ban d'akin, a haka ma cewa yayi ta fito mishi da kayanshi da zai saka, wurin kayan ta bud'a saai ta rikice ta rasa wanda zata d'aukar masa, da k'yar ta ciro wata shadda bleu ta d'auko hula da hiramin da takalma duk sa suka dace da kayan ta aje, feshesu tayi da turare ta zauna bakin gadon jiranshi.



*Watak'ila mun shiga hutun sallah insha'Allah*



*Alhamdulillah*
7/23/21, 7:38 AM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*46*




Fitowarshi tasa ta yin zunbur ta mik'e tsaye tana kawar da kanta daga kallonshi dan d'aure yake da towel, kallonta yayi ya kalli kayan data fito mishi da su yana goge ruwan jikinshi yace "Inna Issa ya akayi kika san kayan da zan saka?"

Kallon kayan tayi tana murmushi amma ba tace komai ba, matsowa yayi kusanta yace "Na gane, wato ke ma kina so na ko? Hakan na nufin zuciya da tunaninmu d'aya ne."

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a ba haka bane."

Wani kallo ya bita da shi yace "To ya ya ne?"

Sunkuyar da kai tayi a sanyaye tace "Ba komai."

Daf da ita ya tsaya kamar zai had'eta yace "Baki so na Ryam?"

Cikin turo baki da rashin bawa abun mahimmanci tace "To ai ni ban ma san ya so d'in yake ba."

Kallon tuhuma ya mata yace "Amma kuma a baya kika fad'a min kina son Asas?"

Da saurita kalleshi saikuma ta sunkuyar da kai, jawo k'ugunta yayi ya had'a da nashi yace "Hakan na nufin k'arya kika min?

Da sauri ta girgiza kai cikin sanyin murya tace " Ba k'arya bace sheikh, kayi hak'uri kaji, muje ka ci abinci."

K'arasawa yayi gaban kujera ya zauna ya d'auki mai ya fara murzawa a nutse, tana kallonshi har ya gama ya d'auki kayan ya saka, duk da turaren data fesa musu tana kallo ya d'auki wata k'aramar kwalba ya kuma shafawa a bayan kunnenshi sannan ya d'an murza a tafukan hannayenshi ya murza sosai sannan ya d'auki hula ya mik'a mata yace "Oya Hajia d'ora min."

Karb'a tayi tana dariya tace "Ai naga yanda Abba yake d'orawa na yi."

Murmushi yayi tare da sunkuyowa sosai tsayinsu ya daidaita sannan ta d'ora mishi hular, kallonshi tayi ta saki murmushi tace "Umm! Kayi kyau."

D'aga mata gira yayi yace "Da gaske?"

Jinjina kai tayi alamar eh, nuna mata k'ofa yayi yace "Muje to."

Wucewa tayi gaba ya bi bayanta yana fad'in "Ryam wannan kwalliyar wa ya miki?"

Dariya tayi ta juyo ta kalleshi tace "Ni na yi."

Rik'e hannunta yayi yace "In kuwa hakane zan bayar da kud'in siyan wasu kayan kwalliyar dan a ci gaba da canccara min ita ina kallo."

Dariya tayi cike da jin kunya har suka fita falon, Hafsat na zaune tare da mai aikin, gaisheshi sukayi a ladabce ya amsa a mutumce shi ma, k'arasa yayi wajen cin abincin ya zauna, Hafsat da Mimi ma k'arasawa sukayi sai mai aikin data koma madafa ta zauna, Mimi ce ta zuba musu abincin ta aje ma kowa sannan ta zauna ita ma da na ta a gabanta.

Cikin raha da farin ciki suka gama cin abincin, Mimi na kallonsu suna buga mata soyayyar manya, duk da Hafsat d'in na nuna kunya amma sheikh k'arara yake fad'a mata maganar soyayya ko ya rik'e hannunta, kallonsu ita dai take tana mamakin sheikh d'in. Ya rigasu gamawa ya mik'e, saida ya tsaya gaban kowace ya sumbaci goshinsu ya d'ora da fad'in "Allah ya muku albarka, Allah

Please Login or Register in order to submit comment