Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaseen da Amir suna ta sallama, ai da gudu ta taso ta bud'e k'ofar ta fito, tana ganinsu da farin ciki ta k'araso tana fad'in "Yaseen, Amir, Ku ne dama?"

Rumgume Amir tayi ta zauna k'asa tana kallonsu suna ta washe mata baki suna k'ara daga kai suna kallon gidan, gaisawa sukayi sosai kafin su fad'a mata wanda ya kawosu da wanda yasa a kawosu, murmushi kawai tayi tace "Abdul kenan, ni ce ba zai bari na fita ba."

Da mamaki Yaseen ya kalleta yace "Abdul fa kika ce? Mimi sheikh d'in?"

D'an kyaci tayi alamar kai share dallah tare da mik'ewa tace "Me kuke so na dafa muku?"

Da sauri Amir yace "Miyar nama da shinkafa."

Tintsirewa tayi da dariya ta dunguri kan shi tace "Amir kwadayi ko?"

Dariya suma sukayi suna kallo ta wuce madafar, aiki ta shiga gadan gadan na gaba daya gidan, cikin nutsuwa da hankali ta kammala girkinta mai rai da lafiya, saida ta kwashe kamar yanda take yi kwana biyun nan sannan ta zubawa su Yaseen ta kawo musu, tare da ita suka ci a kwano daya a lokacin 12:00 tayi, mik'ewa tayi ta gyara falon sannan tace su wuce falonta, su Aisha na dawowa daga makaranta basu samu Hafsat ba, saida sukayi wanka sukayi sallah sannan suka ci abinci, ban da Munzeer babu wanda ya je inda take, ita ma tana falonta tare da kannanta suna ta kwasar hirarsu.


04:07 Kabiru ya dawo d'aukarsu dan dama Mama ta ce su dawo dan su tafi islamiyya, tare suka fito tana rik'e da ledar kayan makulashen data siyo ranar zata basu, suna fita farfajiyar su Aisha na tsaye jiran drebansu su ma zasu tafi islamiyya, da wani kallon raini ta shiga bin su Yaseen Wanda tsaf a idon Mimi hakan kuma ya mata ciwo. Da mutumtawa su Heezam da Aswan suka gaisa dasu Yaseen har Aswan na d'an tsokanar Yaseen ma dan suna had'uwa da shi a babban masallacin Kaddafi wajen karatun sheikh.

Wucewa sukayi ta bude musu k'ofar motar zasu shiga, taimakawa Yaseen tayi ya shiga ya zauna dan tsayinshi bai kai ma, zata d'auki Amir ta saka kawai Aisha tayi yar dariya tare da fad'in "Sunan wata waina wai ita 'yar k'unbu."

Sake fashewa tayi da dariya, da k'arfin bala'i Mimi tayi kan ta bata ankara ba ta kasheta da mari tare da shak'ar wuyan hijabinta ta had'ata da bango. A kid'ime kuma a tsorace duk suka kalleta suna zaro ido, kallonsu suka tsaya yi cirko cirko kowa cikinshi ya d'uri ruwa, cikin b'acin rai da fitar hayyaci tace "...




*Alhamdulillah*
7/26/21, 7:58 AM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*49*




Cikin b'acin rai da fitar hayyaci tace "Ke Aisha wacece ke da zaki raina min yan uwa? Akan wane dalili ne zaki shammaci halittarsu? Saboda ina auren ubanki ne?"

Turata tayi da k'arfi har saida kanta ya bugi bango ta d'ora da fad'in "Zaki takani yanda kike so a gidan nan na k'yaleki, amma idan kika ce zaki tab'a iyayena ko yan uwana wallahi kutumar ubanki zan ci a gidan nan saidai uban ki ya sakeni."

Juyawa tayi har zata nufi wajensu Yaseen sai kuma ta juyo ta kalleta tace "Ba kiyi kama da yar Abdul ba, sam halayenki basu dace dana wacce ta fito a tsatson Abdul da Hafsat ba, kaiconki wallahi, kuma fa duk wannan abun da kike yi kina yi ne saboda na auri Abdul ko?"

Yatsina fuska tayi tace "Mun riga da mun zama d'aya Aisha, zan fad'a miki wani abu kuma wanda na tabbatar cikin biyu za'ayi d'aya tunda ke ma aure zakiyi, ko dai mu haihu tare da ke, ko kuma na rigaki haihuwa dan tsohonki ya jima da tura sak'onshi kuma na karb'e da hannu bibbiyu, mu zuba ni da ke a gidan nan tunda kin kasa fahimtar a yanzu ni ma d'in uwarki ce tunda na gauraya da ubanki ."

Sama da k'asa ta bi ta da harara ta wuce zuwa wajen su Yaseen da sukayi tsuru suna kallonta, saida suka fita a gidan ta juya ta koma ciki ko kallonsu ba tayi ba, Aisha kam ta cika kamar zata fashe ta kawo wuya, Heezam kam girgiza kai yayi yace "Kin ga irinta ai, gobe ma ki k'ara."

Aswan ma murmushi yayi yace "Gaskiya ta fad'a miki, sam bakiyi kama da yar gidan nan ba."

Odar da sukaji tasa su fita da sauri amma ban da Aisha da take tafiya kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki, kalaman Mimi sun tsaya mata sosai a zuciya, musamman yanda take kiran sunan mahaifinta ba girmamawa Abdul gatsau, saida suka shiga mota sai kawai ta fashe da kuka kamar wacce aka k'wak'ulewa ido. Har suka isa islamiya tana kuka bata daina ba, a aji ma ba abinda take sai shashek'a, shiyasa ma ana tashi daga islamiyar ko da dreba ya d'aukesu bai tsaya ko ina ba gida ya diresu.


*Tun* fitarsu dama sunyi waya ita da sheikh suka sha hirarsu ta soyayya, Hafsat ma a can ta wuni sai yamma lik'is ta dawo daf da lokacin tashinsu, tunda sheikh ya dawo da ita kuma bai fita ba yana gida, hakan yasa suna shigowa falon da sallama sun samesu dukansu a falon.

Sheikh na tsaye zai shuge b'angarenshi ya dakata saboda jin shigowarsu, Mimi ta fito daga madafa rik'e da kofi a hannunta ta kawowa Hafsat shayin da tayi na goruba, Hafsat d'in kuma na zaune kan kujera.

Kusan a tare suka amsa sallamar yaran duk suna kallonsu, da sauri Hafsat ta mik'e gabanta na fad'uwa saboda ganin fuskar Aisha, idonta sun k'ank'ance sun kumbura abu ga jar fata, fuskarta ma duk tayi wata kala tsabar kuka sai shatin yatsun daya zauna a kuncinta, dan marin da Mimi ta mata a bazata ne ya zo kuma da mugun k'arfi, da hanzari ta tarbeta tana fad'in "Aisha lafiya? Me ya sameki?"

Sake sinne kai tayi tana ci gaba da shashek'ar kuka, hankali tashe ta kalli su Heezam tace "Kai me ya sameta? Fad'a tayi ne? Ko wani laifin tayi da aka daketa a makaranta?"

Aswan ne ya turo baki ya girgiza kai alamar a'a, sai Heezam daya d'aga kafad'a shi ma alamar uhum! Muryar sheikh ce ta dakesu a bayansu yace "Munzeer yaro na."

Cikin d'aga sauti Munzeer yace "Na'am Abie." Ya fad'a yana nufa inda yake tsaye, kusanshi ya tsaya ya shafa kanshi yace "Shi ne bayan bana nan tayi fad'a ko?"

Da sauri Munzeer yace "A'a Abie, aunty Aisha ce ta yi wa aunty Mimi rashin kunya, shi ne ta mareta a fuska kuma ta zageta."

Tsuru tsuru duk suka zubawa Mimi ido da ita ma ta kafe Munzeer da ido, amma data ga kallon da suke mata sai kawai ta d'auke kan ta tare da aje kofin shayin hannunta akan k'aramin table d'in ta dafe k'ugu alamar tana jiran a yi duk wacce za'ayi.

Hafsat ma d'auke kanta tayi daga Mimi ta kama hannun Aisha da k'arfi suka nufi d'akinta cikin hushi, ganin haka sai sheikh ma ya bi bayanta dan gaskiya baya son b'acin ran Hafsat musamman ma da ita d'in macece da bata cika saurin nuna b'acin ranta ba, Mimi na kallo suka shige d'akin tana tsaye zuciyarta na tafasa tana jin kamar bak'uwa ce ita a gidan nan, kamar bata da wani galihu ko mutumci.

Had'e hawayenta tayi tare da wani abu daya tsaya mata a wuya ita ma t shige d'akinta, saidai zaune tayi a kujerar falo zama irin na jiranka kawai na ke ka zo a yi ta ta k'are, ka zo ayi duk wacce za'ayi amma ba zan d'auka ba.


*A* d'aki kuma yana shiga Aisha na zaune bakin gado Hafsat na tsaye a kan ta tana d'an tab'a fuskar ta ta, da sauri ta juya ta kalleshi cikin hushi da b'acin rai tace "Akan me zata marar min yarinya? Ni ko kai akwai wanda ya tab'a dukansu ne bare kuma mari a fuska mai daraja, fuskar da ubangijinmu kad'ai muke turmusata a k'asa dan bauta masa, me ta mata da zata mareta haka har hannunta ya kwanta a fuskar yarinya?"

D'auke idonshi yayi a fuskar Hafsat d'in ya kalli Aisha yace "Me kika mata?"

A tsorace ta kalleshi cikin shakakkiyar murya tace "Abie ban mata komai ba, kawai daga zata raki k'annanta da suka zo, daga sun wuce nayi murmushi shi ne kawai ta mareni, har zagina ta dinga yi tana ambatar sunanka da sunan Amie tana fad'in wai ita ma matarka ce kuma zata..."

A tsawace yace "Shiru!"

Shiru tayi tana kallonshi tana sauke ajiyar zuciya, da mamaki Hafsat ta kalleshi tace "Tsawa ma kake mata? To wallahi ba zan d'auki wannan wulak'ancin ba, nayi hak'uri akan abubuwa da dama sannan na shanye b'acin rai bila-adadin, amma ba zan tab'a d'aukar cin zarafin 'ya'yana ba."

Kusa da shi ta matsa tana kallon idonshi tace "Ka fad'awa matarka karta sake sauke gigin haukarta akan yarana, inba haka ba wallahi da kaina zan d'auki mataki."

Tana fad'a ita ma ta shige ban d'akinta dan samo ruwan d'umin da zata gasa mata fuskarta data kumbura.

Kallon Aisha yayi ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta."

Fita yayi a d'akin shi ma ya nufi d'akin Mimi, tana ganin ta mik'e dan cike take da bala'i ita ma, saida ya tsaya gabanta cikin halin ko in kula yace "Me ya had'aki da Aisha? Shin baki san 'yarki bace ita da zaki zauna d'aukarwa kanki raini a wurinta."

A gadarance ta yatsina fuska tace "Sanin haka yasa ni gaggauwar d'aukar matakin dakatar da rainin da take son d'ora min saboda na tuna mata ni ma uwarta ce."

K'ank'ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki yace "Shiyasa kika d'aga hannu kika mareta?"

Rumgume hannaye tayi a k'irji tace "E, saboda ta raina min yan uwa, ni kuma ba kowane raini nake d'auka ba."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Na ji to kiyi hak'uri, Aisha ba zata sake miki rashin kunya ba na miki wannan alk'awarin."

Shiru tayi tana wani kumbura baki ba tace komai ba, matsawa yayi kusanta ya rumgumota jikinshi yace "To saki fuskar mana, ko sai na had'aki da aljanuna?"

Da sauri ta saki hannayenta daga rumgumesu da tayi a k'irjinta tana dariya tace "A'a Abdul karka kirasu."

Dariya yayi shi ma ya rad'a mata a kunne "Ko ke fa, bana so irin wannan hatsaniyar na d'aga min hankali a gidan nan, kamata yayi ki nuna musu ke ma fa gyatumarsu ce."

Dariya ta k'yalk'yale da ita ta d'aga k'afafunta sosai ta rad'a masa a kunne cewa "Shiyasa nake so na kama girmana, dan ni d'in ba matar yaro bace."

Dariya yayi ya bata hannu alamar su bige yana fad'in "Gaskiya ne matar old man."

Farin cikonsu suka ci gaba da yi kamar babu abinda ya so faruwa yanzun. Saidai a daren bayan fitar sheikh da su Heezam zuwa masallaci, Hafsat da Aisha basu fito cin abinci ba, Mimi kuma bata damu ba hasalima ita ma tana b'angarenta, sai kusan 10:54 na dare suka dawo gidan, da kan ta ta zubawa su Aswan abinci suka ci sannan ta d'iba ta kai wa sheikh falonta shi ma ya ci.


Saida kowa yayi bacci a gidan baka jin komai sai k'arar panka da ac, a lokacin sheikh ya mik'e ya nufi d'akin Aisha, cikin nutsuwa ba tare da tunanin komai ba ya bud'a k'ofar d'akin, ganinta kwance akan gadon tana bacci a nutse ba k'aramar salama ya sama mishi a zuciya ba, dan sosai yake tsoron zamanin nan da mutanen cikinshi, k'arasawa yayi gaban gadonta ya tsaya ya daddab'ata, cikin magagi ta bud'a ido ganinshi yasa ta yin zunbur ta tashi zaune tace Abie?"

Yanda ya tsaya gabanta k'ik'am yasa ta sauka daga kan gadon tana lalubar hijabinta kan gadon, sakawa tayi ta b'oye rigar baccinta tana zaunawa k'asa.

Zaune yayi bakin gadon ya had'e hannayenshi yana kallonta, saida ya gama mata kallon tas kafin ya d'aga hannunshi ya kwad'a mata mari, a gigice a rikice ta dafe kunci tana sakin k'ara.

Kallonshi tayi tana sako hawaye inda shi kuma ya nunata da yatsa cikin taushin murya yace "Wannan marin dana miki tun ranar da kika ma Mimi rashin kunya da safe ya dace na miki shi, ya kamata ki sani ita ma uwarki tunda ni ke aurenta, darajar aure ya siya mata darajar da zaki kalleta kamar uwa, addininmu ya koya mana yanda zamu mutumta d'an adam ko baka san shi ba bare wanda kake da alak'a dashi."

Kama kunnenta yayi a cikin hijabin cikin sigar fad'a yace "Aisha har na zauna na nuna ga yanda za'ayi saboda gudun matsala amma ke ki nuna ba haka, da kika ma yan uwanta fitsara me kike so ki nuna musu kenan? Ke *tantiriyar gidana ce*? Haka kawai zaki tarwatsa min farin ciki da zaman lafiyar gida, tunda kike kik tab'a ganin b'acin ran mahaifiyarki a zahiri? Ko kin tab'a ganin ta kalli idona ta fad'a min abinda ke ranta kai tsaye? Sai yau kuma duk a dalilinki."

Jinjina kai yayi sanda take neman tashi daga zaunen tana rik'e kunnenta tana fad'in "Abie zafi zafi, kayi hak'uri na tuba wallahi."

Mik'ewa yayi ya sake nunata da yatsa yace "D'aurin aurenki ba fashi Aisha ranar juma'a, ko ki shirya ma hakan ko karki shirya duk d'aya, amma ki sani kin fara sani tunanin ko dai kin san me aure yake nufi shiyasa kike kishi da wata wacce kike ganin ita ma ta rab'i jikin ubanki, to koma a ya ya dai kika d'auka ki sani hakan ne."

Yana fad'a ya wuce ya barta nan tana wani kukan tare da gyara zamanta a k'asan ta had'a kai da gwiwa.


Daren yau ma sheikh ya so ratsa gonar Mimi amma ta buga kai k'asa tace bata warke ba, dole ya hak'ura ya d'anyi wasa da ita kamar dai jiya sannan yayi wanka ya shiga karatun Qur'ani.


*Da* safe ma haka yara suka shirya suka fito, saidai Aisha kai tsaye ta wuce farfajiya sai su Aswan ne suka tsaya suka karya kumallo, suna gamawa suka fita Mimi na musu a dawo lafiya, saida suka fita ta nufi d'akin Hafsat da sallama a bakinta, zaune ta sameta bakin gado da wayarta a hannu, k'asan mak'oshi ta amsa sallamarta, bata damu ba haka ta k'araso tsakiyar d'akin tace "Aunty Hafsat abincinki na ce ko na kawo miki nan? Na ga baki fito ba yau."

Yatsina fuska Hafsat tayi tace "A'a ki barshi ma na k'oshi."

D'an satar kallonta tayi sai kawai ta jinjina kai tana murmushi tace "Shikenan, na barki lafiya."

Fita tayi a d'akin tana jinjina kai a ranta tana fad'in "Ku kaini bango kuka aiki da cikawa."

Fita tayi ta kai wa sheikh na shi abinci yana gama ci sukayi sallama ya fita. Haka har rana ta dora girki ta gama bata ga Hafsat ba sai zuwan yaran daga makranta ta dinga jin hayaniyarsu a d'akinta, tana gama aikinta ita dai ta shige d'akinta uta ma da abincin dan tayi niyya bama zata fito ba sai yamma in zata d'ora girki.

*Dare* ma haka suka kasance kasancewar sheikh bai shigo da wuri ba Mimi ta nemi su ci abinci, kowa ya zo amma ban da Aisha da Hafsat, saida ta gama zubawa su Heezam ta kallesu tace "Ina zuwa, bari na kira aunty."

Jinjina mata kai sukayi alamar to, tana zuwa ta fara k'wznk'wasa k'ofar tana sallama, jin ta amsa yasa ta turawa a hankali ta shiga, da ladabi tace "Aunty Hafsat ina kwana?"

"Lafiya lau." Ta amsa ba yabo ba fallasa, sharewa Mimi tayi tace "Abinci na ce ko zaki ci?"

Yatsina fuska tayi tace "Um um! A ci lafiya."

Ita ma yatsina fuskar tayi ta juya dan fita, k'wafa Hafsat d'in tayi ta jin haushin takurawar Mimin, juyowa Mimi tayi cike da shak'iyanci tace "Magana kike?"

A gatsala ita ma tace "Kika ji nayi?"

D'aga gira tayi tace "Ok, Allah ya kyauta."

Juyawa tayi amma dake Hafsat dama can fin k'arfin zuciyarta ne takeyi sai kawai tace "Ke! Rashin kunya zaki min?"

Juyowa Mimi tayi cike da rashin tsoro tace "Rashin kunya kuma? Kika ga alama zan miki?"

Sai kuma ta gyata tsayuwarta tace "Wai tsaya, ko dai haushina kike ji saboda na daki 'yata? To ai ke ma na ga kamar uwa kike gareni kina iya rama mata."


Mik'ewa tayi tsaye ta nunata da yatsa tace "K'arya kike wallahi, Aisha ba 'yar ki bace, da 'yarki ce ai da baki mareta a fuska ba, saboda baki san darajar haihuwa ba."

Bushewa tayi da dariya tace "Haihuwa? To ai ban tab'a yinta bane shiyasa, amma kwana nawa ne ya rage ni ma na haifo nawa."

Ta fad'a tana shafa mararta, girgiza kai Hafsat tayi tace "Dama da ganin idonki zakiyi fitsara, to ki ji da kyau karki k'ara dukar min yarinya dan bΓ’ jakarki bace, da fari na so baki girma da darajar da zasu dinga kiranki da Amie, amma tunda baki da mutumci na fasa."

Gaba d'aya jikin Mimi ne yayi wani irin sanyi har tsakiyar ranta ta ringa jin wani iri, yau gata ta daki yarinyar data mata rashin kunya a kan gaskiyarta amma mahaifiyarta da take jin k'aunarta a zuciyarta tamkar 'yar uwarta har tana jin ta samu 'yar uwa ta kalleta ta wulak'antata a kan hakan, anya kuwa idan jininta ce koma ta ce idan 'yar uwarta ce ko zane mata 'ya ta yi zata kula? Zata d'aga kai ta kalleta? Duk da zamani ya cenza amma akwai na kirki har yanzu, akwai zumunci har yanzu.

Shin Hafsat bata ganin irin abinda 'yarta ke yi ta katseta tunda wuri ko hakan na mata dadi? Shin Hafsat so take su fara zaman kishi da juna ko menene? A matsayinta na babba, babbar ma wace ta san ba haka kawai ta d'auko kanta ta kawo gidan mijinta ba a ganinta ya dace ta mata adalci.

Muryarta a sanyaye ta d'ago tana kallon Hafsat cikin ido tace "Allahn da ya baki aunty nima bai manta da ni ba, kuma ina rok'onsa idan ya tashi bani ya bani masu tarbiyar da ko da Abdul na da damar k'ara wani auren nan gaba su kirata da Amie, bare kuma ke, ke ina so yarana su kiraki da Mama, haka kawai na ga kin isa ki zama uwarsu dan a d'an zaman da na yi da mijinki sai nake ji da kuma ganin girma da darajar wani ma wanda ya rab'e shi bare matar daya hayayyafa da ita."

Suna tsaka da muhawarar nan sheikh ya shigo, rashin sa'a kuma shi ne daidai Mimi ta kuma sakin wani murmushi tana girgiza kanta ta bud'i bakinta zata yiwa Hafsat wata maganar wacce Hafsat d'in kuwa gaba d'aya yanayi na b'acin rai ya saka har wata k'walla da b'acin rai sun nuna a tare da ita, uwa uba a yau idonnta ko kwali babu tsabar ta sakawa kanta damuwa bayan ba haka Hafsat take ba, hakan ya saka hankalinsa tashe ya kuma nazartarsu kafin muryarsa kamar a d'an kausashe yace "Ryam, rashin kunya kika zo har d'aki kike yi wa matata ko me? Shin rashin kunya kike yi wa Hafsat? Kin kuwa san zan iya take komai na had'iye komai na danne komai amma banda cin zarafin uwar gidana? Kar na ji, kar na gani kar na ji kar na gani ko da wasa kar ki saki ki kuskura na kama ki da y iwa matata fitsara domin zaki yi mamakina Nana."

Da mamaki take kallonsa, yanayi na yarinta da d'anyen kai da b'acin rai ne ya sakata kuma kallonsa idanunta a bayyane tace "Wato ni ga matar kutse ko Abdul? Ni matar haye? Allah ya sa nima ce min aka yi jeki ga mijinki ba hauka nake a kanka ba bare daga kai har matarka ku wulak'antani!"

Ta karashe tana mai danne muryarta dake rawa sakamakon b'acin rai da kukan dake son k'wace mata.

Ransa ne ya b'aci saboda jin ya ya zata ringa maida masa magana ta wani siga wai kenan shi ga sakarai shi da bata so ko? Ransa b'ace ya nufota yace "Me kike nufi da maganarki? Kenan kina so ki nuna ni d'in banza wofi ne a wurinki? Ya zaki nemi raina min matata na miki magana kuma ki nemi yi min fitsara."

Cikin d'aga murya da kwaratsi Mimi ta ja baya tace "Ya isa! Ya isa haka."

Kallonshi tayi tana sako hawayen da take rik'ewa tace "Kowa sai ya dinga kirana da fitsararriya ko marar mutumci, to na gaji kunji na fad'a muku, idan zaman gidan nan ba zai yiwu ba ka sallameni na tafiya ta mana, a'ah, wai ana dole ne?"

Da wani irin sauri ya kai hannu zai shak'o wuyanta ya gaura mata mari, sai kuma ya tsaya tare da dunk'ule hannunshi yana kallon fuskarta, girgiza kai yayi ya feso iska dan maganar sakin nan na tab'a mishi zuciya wallahi, kai dole ma ya zauna zama na musamman da ita ya nuna mata babu kyau abinda take fad'a, wani numfashi ya kuma saukewa yana ci gaba da kallonta yace "Ryam ban tab'a dukan mace ba, ba zan fara yau ba, amma ki sani ita mace da kika gani kamar abun tuk'i ce, idan har kika zamar min mummunan abun tuk'i har tuk'inki ya k'wace min zan zama sakarai kuma malalaci, a gaskiya ba zan bari haka ta faru ba."

Ja baya yayi sosai ta yanda yake hangensu tsaye dukansu kuma yana kallon kowace yace "Na yardaina sonki ne daga lokacin da muka fara zama a matsayin ma'aurata, soyayyata ta farko gareni na farata, k'aunarki na gaba d'aya zuciyata saboda ke d'in nan ke ce b'angare na jikina, zubar hawayenki ba k'aramin d'aga min hankali yake ba, karki so kiji yanda zuciyata ke bugawa musamman dana shigo d'akin nan na fahimci ba kya cikin farin ciki, ina son ki, na fad'a miki haka bila-adadin, ki yarda, ki yarda da ina sonki kinji."

Kamar shed'an nan da aka tofawa a'uziya haka duk suka zuba mishi ido sukayi tsuru, kowace tana d'aukar kalamai tana d'orasu a muhalli, saidai kuma wani b'angare na zuk'atansu na sa musu wasi-wasin da wa yake a ciki? Musamman Mimi da tafi raja'a ce wa da Hafsat yake, a wajen k'arshen ne kawai zata ce da ita yake dan yana yawan fad'in yana son ta kuma ta yarda. hafsat kam ta yarda tabbas da ita yake, tafi kokonton me yasa bai tsayar da kallonshi kan ta kawai ba.

Mimi kam juya baki tayi tace "Ni da ba'a so sai naje na nemi mai sona ai."

Tsai yayi yana kallonta, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Ya fad'a a zuciyarshi, wallahi wani irin gudu zuciyarshi tayi sanda ta anbaci ya sallameta, anya kuwa ba mutuwa zaiyi ba ko kuma dai yarinyar nan ce hawan jinin shi ba? Kasa maganar da yayi yasa ta kallonshi tace "Ba ma kada lokaci na ko? Shikenan ka tura min takardata a gidanmu."

Juyawa tayi zata fita ya rik'o hannunta a mugun firgice, kallon juna sukayi tana kallon yanda yake sauke numfashi. Sautin kukan Hafsat daya ji ya dawo dashi daga shirin fad'in "Ryam kiyi hak'uri, karki tafi dan Allah."

Kallon Hafsat yayi cikin fizgo kalamai yace "Me ya had'u Manga? Ban san ki da rikici ba."

Da sauri ta nuna Mimi tace "Ka tambayi dak'ikk'iyar yarinyar nan mana."

Kallonta Mimi tayi da mamaki tace "Dak'ikk'iya kuma?"

Kallon sheikh tayi tana jiran ta ga me zaiyi amma sai wani kakkawar da kai yayi kamar mai kokarin b'oye kukanshi, fizge hannunta tayi ta kallesu da kyau tace "A tare na sameku dama, zan tafi na barku yanda na ganku, ni ma Allah zai had'ani da wanda zai iya kare kima da darajata, amma wannan ba gidan zama bane."

Tana fad'a ta juya da sauri ta fita a d'akin wanda kowane tako ke sauka kan k'irjin sheikh, iya yanda mazaunanta ke juyawa cikin tafiyar b'acin rai yasa jinin jikinshi rage saurin gudu. Juyawa yayi ya kalli Hafsat

Please Login or Register in order to submit comment