Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake ta sharar hawaye, wani iska ya feso dan gaskiya zuciyarshi na son ya bi *yarinyarshi*, amma kuma ga Sawwama na kukan b'acin rai wanda bai tab'a ganin hakan daga gareta ba, duk da bai san asalin me ya kawota d'akin ba yasan dai zaiyi wuya a ce bata da gaskiya.

Zaunar da Hafsat d'in yayi ya zauna gefenta yana shafa bayanta ya kasa ceewa komai dan hankalinshi da nutsuwarshi na wani wurin gaskiya.


Mimi kam na fita ai kuwa da gaske take dan akwatin da aka mata na lefe ta d'auko guda a ciki ta shiga zuba mata kaya saida ta mata nak da kaya ta d'auki hijab ta saka ta fito, su Heezam na zaune suka ga fitarta babu wanda ya mata magana saidai suna fatan ba matsalar Aisha ce ta jawo wannan babbar matsala ba.




*Alhamdulillah*
7/26/21, 9:12 AM - Maman Husna: Sannu da qoqari
7/26/21, 11:55 AM - Ummi TandamaπŸ˜‡: Yauwa Maman husna
7/26/21, 7:22 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*50*




Jin yanda zuciyarshi ke ta buga mishi da sauri har sai ya bud'e baki yake sauke numfashi yasa shi d'an janye Hafsat daga jikinshi ya mik'e, zai fita ta rik'o hannunshi ya juyo suka kalli juna, cikin dakusashiyar murya tace "Kayi hak'uri idan na b'ata maka rai."

Kasak'ai yayi yana kallonta kamar baya hayyacinta sai kuma ya kawar da kan shi yace "Ya zanyi idan ba hak'urin ba, tunda kun sani mun taru mun wa yarinya rashin adalci, mun nuna mata mu jahilai ne marasa tunani..."

Sab'ule hannunshi yayi daga rik'on data mishi ya juya ya bar mata d'akin, da kallo ta bishi tare da jin wata matsananciyar kunya ta rufeta, sai ta samu kan ta da jin nauyin kan ta da kuma mijinta da Mimi, tabbas tasan abinda ta aikata har da rashin fitar da abinda ke ranta da tayi na wani lokaci, shiyasa yanzu ta fake da abinda ya faru ta d'an furzar da abinda ke ranta, gashi sun tafi sun barta da tunani kamar kan ta zai fashe. Alamu sun nuna sheikh yayi hushi da ita, ga kuma mamakin yarinyar da take kallon fuskar mijinta tana kiranshi da Abdul.

Wani lallausan murmushi ta saki ta furta "Har yanzu bana iya kiransa da sunan Abdul Waheed ko da bayan idonsa ne, amma ita kai tsaye a gabanshi take kiran Abdul Abdul."

Yana fita a rud'e ya nufi d'akin Mimi, ganin bata nan sai kaya dake kan gado a barbaje yasa shi durk'ushewa ya kifa kanshi a gadon yana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."

Ya maimaita haka sau uku kafin ya mik'e yana lalubar wayarshi tare da fita a d'akin ya nufi waje, d'aya daga cikin jami'anshi na ganinshi ya taso a sukwane, da sauri ya tara masa hannu yace "Makulin mota?"

Da girmamawa yace "Sheikh mu je sai na sauk..."

Bai gama fad'a ba a tsawace yace "Ka bani makulli bana so."

Da sauri ya mik'a mishi yana ja baya da d'umbin mamaki, tunda suke haka bai tab'a faruwa ba sai yanzu, bak'ar Mercedes ya shiga yana d'ora waya a kunne yana kiran lambarta, data fara k'ara sai ta kashe kiran hakan ya k'ara d'imauta tunaninshi, yana fita dama ya nufa da fatan had'uwa da ita, saidai sam bai ga alamarta ba har saida ya iya kwanar unguwarsu.

K'ofar gidan ya k'urawa ido yana kallo dan yasan dai nan zata zo, amma shiru bai ga alamarta ba saida ya d'auki waya ya sake danna kira, k'it ta datse kiran da sauri ya shiga rubuta mata sak'o kamar haka _"Ryam ki rufa min asiri, karki d'ora min hawan jini da tsufana, dan Allah na rok'eki."_

*Mimi* kam ta jima da shiga gida dan haka ma bai ganta ba, tunda ta shiga taxi take kuka kamar an mata mutuwa, tana fita ta mik'awa mai taxi jaka guda ta shige gida da jakarta, Abba dake shirin fita kicib'us sukayi a k'ofar shiga, kaucewa yayi a hanye ta wuce yana d'aga kai sosai yana kallonta da fad'in "Ke daga ina? Uwata anya kuwa baki da aljanu? Me ya fito dake yanzu daga gidanki?"

Durk'ushewa tayi ta fashe da wani kukan ba tayi magana ba, sake gusawa yayi a bakin k'ofar yace "Ina zaki da k'atuwar jaka haka?"

Had'a kanta tayi da gwiwa cikin kuka tace "Abba ni gidanmu na dawo, Abba na ba zan iya zama a gidan Abdul ba, wallahi bak'in cikin 'ya'ya..."

Da k'arfi ya kai mata bugu a baki yana fad'in "Astagfirullah! Uwata sheikh d'in ne Abdul kai tsaye? Ban gane ba zaki iya zama ba ?"

Juyawa yayi ya kalli k'ofar d'akinsu ya k'walla kiran sunan Mama da "Rabi, Rabi'a kina ina? Zo nan zo kiga haukan 'yarki."

Da sauri Mama ta fito k'undul k'undul kamar zata fad'uwa tana fad'in "Malam lafiya?"

Nuna mata Mimi yayi data rufe bakinta daya buga yace "Ga ta nan ta fad'a miki kiji."

Kallon Mimi tayi hankali tashe tana jin wani suka a zuciyarta bakinta na hard'ewa tace "Mimi lafiya? Me ya faru?"

Abba ne yayi tsal yace "Ba wani lafiya, wai fad'i take ba zata iya zaman gidan sheikh ba, ke dan Allah a nan gidan ba hak'uri kike dani ba ?"

Sunkuyar da kai Mama tayi tana jin kamar tace mishi ya fita ya barsu ita da 'yarta ta ji me ye matsalarta, amma yanda ta ji ya fara fad'in "Ke Maryama bana son shashancin banza da wofi, ni zaki mayar k'aramin mutum da bai san me yake ba, duka yaushe kika tare a gidan na ki da zaki fara min yaji, kenan kinfi k'arfin a b'ata miki rai ke 'yar gwal? Yanzu haka ma ba da izinin gafarta malam kika taho ba, to ni ba za'ayi haka dani ba, maza tashi ki koma gidanki kamar yanda kika kawo kan ki, ba zan zauna na baki mafaka a gidana ba kwana kad'an ki fara min laulayi kamar yanda uwarki ke fama da na ta laulayin."

Da sauri Mimi ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma ta kalli Mamanta, a ranta tace "Mama ciki ne da ita?"

Sai kuma ta yatsina fuska tace "Allah sawak'e ma na d'auki cikin mutumin nan, tsoho kawai da wata akwalar matarshi da 'ya'yanshi marasa kunya."

Had'e fuska ta sakeyi ta kalli Abba ta marairaice tace "Abba dan Allah karka koreni a gidan nan, Abba ka ga fa da shi da matarshi da 'yarsu suka min taron dangi, ni wallahi Abba..."

Takalminshi ya cire yana fad'in "Ke in ban kakkarta miki..."

Ganin Mama ta juya tana rufe bakinta dan dama ya gama kasheta da kunya tunda yayi maganar cikin nan yasa shi binta da kallo, Mimi da tuni ta mik'e da gudu ta fita waje ta fashewa da kuka, akwatin ya kama da nufin cilla mata ita saidai ta fi k'arfinshi dan a tsayi ma kusan kansu d'aya da akwatin, turata ya dinga yi saida ya fito mata da ita ya nunata da yatsa tana tsaye nesa da shi yace "Wallahi kika bani na d'aga murya a kan ki ba zakiji dad'i ba uwata, har gidan na ki zan sameki na zazzabga miki dukan mutuwa."

Cikin sand'a ta jawo akwatin na ta tana kallonshi ya koma cikin gidan yana fad'a, had'e hawayenta ta kalli unguwar ta su da kyau, duk da ba dare bane sosai amma babu mutane sai masu wucewa, numfashi ta sauke cikin disassashiyar murya tace "Kayi hak'uri Abba na ka yafe min, amma ba zan iya komawa gidan Abdul yanzu ba, idan na koma kamar ban da zuciya ne da kuma gata, ku a wajenku haka da kukayi shine daidai, amma ni tunda ni ke zaune dashi dole na bi kowaxe hanya dan samawa kai na mutumci a gurinshi, Mama na ta fad'a min na koyi yanda zan kula da kai na, kuma na yi alk'awarin zan k'watarwa kai na 'yancina ba tare da taimakon kowa ba."

A hankali ta ja akwatin na ta ta d'auki hanyar zuwa gidansu Iya Delu, haka ta dinga kakkare fuskarta dan bata so yan unguwar su ganeta musamman da take d'auke da akwati shak'e da kaya.

Tana zuwa gidan malam na cin tuwo Iya na gefenshi suna hirarsu a nutse, ko sallama ba tyi ba ta k'arasa cikin shagwab'a tana saki akwatin ta fad'i ta cire hijabi ta zauna tsakiyarsu, mamakinta na neman kashesu da k'yar Iya ta kalleta galala tace "Ke kuma fa daga ina?"

D'ora kan ta tayi a gwiwar Iya ta shiga rera kuka a sanyaye tana fad'in "Kakani na bani da gΓ’ta a duniyar nan, kasheni zasuyi da bak'in cikinsu da bautarsu, dan Allah ku zame min gata kunji."

Cire hannu malam yayi a tuwo ya kalleta ya dafa kafad'arta yace "Ta gaban goshina, waye ya tab'a min ke?"

D'agowa tayi ta kalleshi cikin Luka tace "Malam na gaji da zaman gidan sheikh, dan Allah ku barni na zauna anan na huta, na je can Abba bai ma saurareni ba ya koroni da takalmi."

D'ora kanta tayi shi ma a kafad'arshi tare da rik'e damtsenshi gam, cikin tausayawa da nutsuwa yace "Me ya faru amaryata?"

Ba tare data d'aga kan ta ba ta shiga labarta masa komai daya faru tun daga farkon abinda Aisha ta fara mata har zuwa yau d'in, saida ta gama abinda bata tab'a tsammani ba daga Iya ta ji tace "Maganar banza, yo an fad'a musu ke d'in a bishiya muka tsinkoki? Ya zasu taru gard'ama gard'ama dasu su nuna miki fin k'arfi."

Gyara zama tayi ta jawo Mimi ta shiga daddab'ata tana fad'in "Ke rabu dasu kinji, nan zaki zauna na ga wanda ya isa ya maidaki k'arfi da yaji, kaga iskanci."

Dariya malam yayi yana girgiza kai bai ce komai ba, dan gaskiya yanda yake son Mimi shi ma sai yaji bai ji dad'i ba musamman da ita kan ta uwar yarinyar ta fad'a mata maganganu sannan shi bai tsaya ya bincika ba kuma ya d'ora mata da fad'in matarshi matarshi, yana gama cin abincin shi ya wanke hannayenshi ya d'auki k'aramar rΓ©dion shi zai fita ya kalli Mimi yace "Ki shiga da kayan ciki ki kwanta zuwa safe zan san abun yi."

Mik'ewa tayi da sauri tana fad'in "Ni da safen ma makaranta zan tafi, kawai ka k'yaleshi yana tsohonshi dan ma ya samu na kulashi." Da kallo suka bita malam na dariya ya fita a gidan.

*Ya jima* nan amma bai ga wulgitawarta ba sai kawai ya sake kiran wayarta, a lokacin tana d'akin Iya tayi kwance a gadon k'arfe tana d'an lilawa kad'an kad'an, d'aga wayar tayi ta d'ora a kunne cike da gatsali tace "Ina ji?"

Shiru yayi idonshi lumshe murya k'asan mak'oshi yace "Ryammm."

Tsam tayi tare da dakatawa da lilawar da take a gadon, wani tsammm ta ji gaba d'aya jikinta saida ya amsa, d'an basarwa tayi tace "Ina jinka."

Cikin sanyi da taushin murya yace "Kina ina Ryam? Dan Allah ki dawo."

Cikin shagwab'ar da bata san tayi magana ba tace "Um um! Ni ba zan koma ba tunda ba so na kake ba, Abdul baka so na kuma baka son zamana a gidanka, sannan 'yarka da mahaifiyarta basa so na sun tsaneni, kawai ka zauna da iyalinka na yafe musu kai har abada, kaga ai dama ni ma kawai had'ani ne aka yi da kai ba dan ina so ba."

Da sauri kamar wanda zai fashe da kuka yace "Ba haka bane Ryam, nasan an miki ba daidai ba amma ki yafe mana kinji, Ryam in kin san yanda nake ji wallahi da baki tafi kika barni ba."

Tashi tayi zaune tace "Ba wani nan, kawai wayo kake so ka min dan ina yarinya, to ni ma da hak'orana ashirin da bakwai."

Dariya ce ta kubce mishi har tana jin sautinta a kunne kafin yace "Ryam, kenan bakiyi hak'oran hankali ba."

Turo baki tayi irin bata ji dad'i ba kafin tace "Ni dai saida safe, kaga yanzu ba gidanka na ke ba."

Zata kashe wayar yayi saurin fad'in "Inna Issa ina kika je?"

Cike da yarinta tace "Ina wani wuri."

D'if ta kashe wayar ta aje gefe ta kwanta, wayar ya bi da kallo sai kuma ya aje ta ya wa motar ky, ba zai iya tafiya gidansu ba a yanzu dan haka zai bari har da safe, duk da yana jin wata irin kunyar had'uwa da iyayen na ta, dan gaskiya abin nan ya dakeshi sosai, kuma yasan yana da laifi ta wani b'angaren, da wannan tunani ya isa gida kai tsaye b'angarenshi ya wuce.

Hafsat ma ta jima zaune kafin ta mik'e dan duba yaran ko sun kwanta, saida ta shafawa dukansu addu'a kafin ta nufi d'akin Aisha, zaune ta sameta tsakiyar gadonta tana karatu da Qur'ani, k'arasawa tayi ta tsaya gabanta tana kallonta, ita ma d'aga kai tayi ta kalleta tace "Amie baki kwanta ba?"

Ba sakin fuska a tare da ita tace "Ta ya zan kwanta bayan bansan halin da kike ciki ba."

Murmushi tayi na jin dad'i tace "Amie lafiya ta lau, kiji ki kwanta ke ma."

Wani malalacin murmushi tayi tace "Yayi kyau, haka yayi kyau tunda gashi har ina ganin murmushinki saboda yau kina farin ciki mahaifiyarki tayi fad'a a kan ki."

Wani kallo ta mata baki sake irin tana jiran k'arin bayani, ruugume hannaye tayi tace "Kin fahimta mana, ya kamata kiyi farin ciki a zuciyarki tunda dai Mimi ta tafi gidansu."

Zabura tayi tana aje Qur'anin tace "Me? Ta tafi Amie?"

Wani dogon tsaki ta ja ta juya zata bar d'akin Aisha ta sauko tana rik'e hannunta tace "Amie da gaske ta tafi? Amie ku yafe mi..."

Tureta tayi ta fizge hannunta tace "Shiru dallah! Hak'urinki na banza da wofi kike ba mutune, kullum ki ce kin tuba kuma ba zai hana anjima ki sake aikata abinda kika aikata ba, Aisha me yake damunki? Me aka miki da zafi haka da kike neman tarwatsa mana zaman lafiyar gida? Tunda kike kin tab'a ganin sab'ani tsakanina da mahaifinku? Kawai saboda an yi min kishiya k'waya d'aya, ba dan mahaifinki ya kasance mutum da bai san matsala da a yanzu Mimi ta hud'u ce ita."

Nunata yayi tana k'yasta hannunta tace "Ki ji da kyau zan daidaita gidana da kai na, wallahi wallahi wallahi kinji uku ko? Na rantse miki da Allah Aisha kika sake wani abun da bai min ba a gidan nan sai na miki d'an banzan duka sannan na wankeki a haka na kaiki d'akin miji."

Harara ta watsa mata sannan ta wuce ta barta nan tsaye, wani iri take ji gaba d'aya ta ma rasa inda zata saka kan ta ta huta, haka ta koma kan gadon ta zauna ta buga tagumi tana tunanin abun yi.




*Washe gari*


Tunda sassafe malam ko da yayi sallah ya samu Abba a masallacin unguwarsu ya fad'a musu abinda ya faru, rai b'ace duk da kunyar sirikina shi saida ya kalleshi yace "Yanzu malam can ta tafi kenan? Dama bata ji magana ta ba?"

Saka takalminshi yayi yace "Malam muje gidan nan dan Allah ka yarje min na daki hancin yarinyar nan."

Dakatar da shi malam yayi yace "A kan me? Kaga ni bana fad'a maka bane dama dan ka je ka d'aga min hankalinta ba, na fad'a maka ne dan ka sani kuma ko da mijin na ta ya nemeka ka sanar da shi inda ta ke."

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace "Shikenan malam, insha'Allahu da kai na ma zan kirashi."

Jinjina kai malam yayi yace "Hakan ma daidai." Da wannan suka rabu kowa yayi gida, Abba na zuwa da fad'a ya shica fad'awa Mama tare da d'aukar wayarshi ya fara kiran lambar sheikh, yana ganin kiran amma bai d'aga ba saida ta tsinke sannan ya d'aga, a mutumce kuma a kunyace suka gaisa kafin Abba ya d'an sosa kai yace "Gafarta malam dama shiriritacciyar yarinyar nan ce jiya da dare ta zo mana da wani hauka, to ko da ta zo ma na maidata ashe bata tafi can ba."

Shiru sheikh yayi kamar bai ji, har ga Allah lamarin yi masa yake kamar a mafarki, da k'yar ya cira bakinsa yace "Ayi hak'uri malam, insha'Allah idan na dawo daga aiki zan zo da kaina gidan muyi magana, ina mai bada hak'uri dan Allah, insha'Allah haka ba zata k'ara faruwa ba. "

Cike da girmamawa Abba yace "Shikenan sheikh ba komai, ban da ma abin yara ina abun hushi a nan? Allah dai ya shirya mana su."

"Ameen." Ya fad'a a hankali, sallama sukayi kafin Abba ya kalli Mama dake kad'a miyar d'umame yace "Ban san me uwata take son zama ba, ki ji yanzu babban mutum kamar wannan yanda yake kwantar min da murya yana bani hak'uri."

K'wafa yayi ya mik'e zai nufi d'aki yana fad'in "Yarinyar nan in batayi sannu dani ba saina b'ata mata rai wallahi."

Mama dai da kallo ta bishi dan ita ban da ganin 'yarta babu abinda take son yi, dan wannan kamar a dakeka ne a hanaka kuka, yarinya kamar Mimi a kai wa dattijo kamar sheikh, shin in bai bita a sannu ba ya za'ayi?


*Mimi*


Tana zaune ta tank'washe k'afafu tana cin tuwo tare da malam hannunta hannunshi suna ta ma Iya tsiya wai ba zasu ci da ita ba wayarta tayi k'ara, juyawa tayi ta d'auka tana dubawa ta ga Asma'u, wani murmushi ta saki ta danna ok ta d'ora a kunne, cikin nutsuwa tace "Hum! Ashe kina iya tunawa da mutane?"

Dariya Asma'u tayi daga wajenta tace "Dan kar na fara miki k'orafin shi ne kika rigani?"

Tab'e baki tayi tace "Ba wani nan, kin manta da mutane saboda kina shan amarcinki."

Asma'u dai na dariyarta tace "Kedai tafi can, yanzu har sammakon da na yi na kiraki ban tsira ba kenan?"

Gwalo ido tayi tace "Oho! Kenan kin kirani da safe ne dan na yafe miki?"

Cikin marairaicewa Asma'u tace "Kiyi hak'uri to, amma ke me ya hanaki kirana? Ke ma amarcin kike sha da yayanmu ko?"

Yatsina fuska tayi tana kallon malam tace "Ba wani nan dan Allah, ni da ma na bar muku yayan na ku ku dafa ku cinye tunda baku san mutumci ba."

Dariya Asma'u tayi tace "Kamar ya? Su waye marasa mutumcin?"

Kai tsaye tace "Ke da yar uwarki mijinki mana."

Da sauri Asma'u tace "Wani abu ya faru tsakaninku? Me Hafsat d'in ta miki kuma?"

Tab'e baki tayi tace "Rabu dasu can su k'arata tunda ni dai na baro musu gidan."

Hankali tashe a kid'ime Asma'u tace "Kamar ya Mimi? Ban gane kin baro musu gidan ba? Kina ina yanzu ke?"

Kallon kwanon tuwon tayi tace "Ina gida wajen Iya gani ma ina cin tuwo da angona."

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tace "Me ya had'aku Mimi? Me yayi zafi haka?"

Mik'ewa tayi ta cire hannunta a d'umamen burabuskon da Iya tayi ta fito waje ta shiga d'akin Iya t zauna ta shiga labarta mata abinda ya faru, Asma'u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta bar d'akin da Asas yake kafin tace "...



*Hohoho, gaskiya fa an sha muhawara, sannunku sannunku, sunana har ya kare😁.*



*Alhamdulillah*
7/27/21, 5:19 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*51*



Asma'u kam kamar tana gabanta girgiza kai ta shiga yi kafin ta saita nutsuwarta ita ma ta d'akin da Asas yake kafin tace "Assha kuwa? Mimi ke da kan ki kikayi kuka a gaban kishiya? Ke ce kika rasa sanin hanyar shawo kan matsalarki har kika bari aka fara sakaki yaji ko kwana bakwai bakiyi ba, ya akayi haka ta faru? Ni da nake tunanin ke ce malamata ta wannan fannin, sabida kin tab'a fad'a cewa ko a cikin mata uku aka kaiki zaki iya zama dasu kuma ki k'waci kanki a hannunsu."

Numfasawa tayi tace "Kinga Mimi duk yanda nake k'aunar yar uwar mijina bai kai k'aunar da nake miki ba dan ke tare muka tashi, ban ce ina so ta zama mowa a gidan nan ba, amma kuma ina so ki zama bora a gidanki ke ma, dan haka kiyi wani abu Mimi, a sanina dake kina da shiga mutane da kutsa kan ki inda yafi k'arfinki, kina karance karance da saurare da kallo sannan ga babbar waya a hannunki, dan Allah ki daure ki samu shawarwarin da zasu taimaka miki zama da mijinki da abokiyar zamanki da ma 'ya'yanku."

Mimi da tayi shiru tana saurarenta saida ta ji ta dasa aya ta numfasa sannan tace "Nagode k'awata, kin k'arfafa min gwiwa kuma zanyi aiki da abinda kika fad'a min."

Da fara'a Asma'u tace "Yawwa Mimi ko ke fa."

D'orawa tayi da fad'in "Ni fa na kiraki ne dan muyi wata magana."

Da zumud'i Mimi tace "Wace magana fa?"

Cikin jin kunya Asma'u tace "Dama wani abu nake so ki d'an fad'a min da zanyi na k'arin..."

Shiru tayi hakan yasa Mimi fad'in "Ina jinki?"

Cikin dariya tace "Kedai kawai zan miki magana ta WhastAp."

Kyab'e baki tayi tace "Kin samu babbar waya kenan?"

A sanyaye tace "Na yi, idan mun had'u zaki gani."

A take Mimi tace "Yaushe ma zamu had'un?"

Cike da tsokana Asma'u tace "Ga bikin 'yarki da za'ayi juma'a."

D'an gajeran tsaki tayi tace "Hummm! 'Yar masu ita dai."

Suna sallama Mimi ta fito da sauri ta wanke hannayenta ta koma d'akin, wayarta ta shiga dannawa tana duba abubuwan k'aruwa musamman a WhastAp, duk abinda ta ga an turo a grp ta kan tsaya ta dubashi a tsanake, ita da Asma'u ma hira suka sha inda Asma'un ta fad'a mata tana son abun k'arin ni'ima ne, wanda ta sani ta fad'a mata sannan tayi alk'awarin binciko musu wasu.Tana tsaka da aikin gabanta kiran sheikh ya shigo wayarta, tana ganin kiran kawai ta datse shi tare da ci gaba da aikin gabanta, haka yayi ta kira dan su gaisa amma ta k'i d'agawa, sai sak'o ya tura mata da _"Amincin Allah ya tabbata a gareki, da fatan kin wayi gari cikin k'oshin lafiya?"_

Shiru yayi ta jiran amsa amma bata maida ba dole ya sake tura mata _"Da alama ba zaki yafe min cikin sauk'i ba, Ryam ki yi hak'uri kinji."_

Nan ma shiru bata maida ba sai kawai ya aje wayar ya buga tagumi yana kallon na'urar gabanshi dake jiran ya loda mata wasu bayanai dake gabanshi a takarda amma ya kasa.

Saida tayi sallah azahar ta d'auki wayarta ta rubuta duk abunda take da buk'ata sannan ta shirya ta fito Iya na tsakar gidan tana gyara wake, tsaye tayi gabanta inda Iya ta shiga kallonta da mamaki tace "Ke kuma ina zaki je kika wani shirya haka?"

Turo baki tayi tace "Iya kasuwa zan je akwai wasu abubuwan buk'ata da zan siyo."

Cike da raini ta kalleta tace "Ke fita ido nq in rufe? Wato ga marainiyarki ko? Daga tahowarki jiya zaki ce zaki fita a gidan nan? To da izinin wa?"

Bubbuga k'afafu tayi tace "To Iya dan Allah ba gidanmu ne nake ba kuma na fad'a miki."

Cikin fad'a tace "A'a, dan kin fad'a min a banza tunda ba ni ke aurenki ba, ke Mimi in kikayi wasa wallahi saina hau bishiya na tsinko tsumagiya na ci ubanki

Please Login or Register in order to submit comment