Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana sauraren na ta bugun numfashin a kunnenshi, a sanyaye sosai kamar mai rad'a yace _"A'a Ryam, karki d'auko min abinda zai fi k'arfina dan Allah, ni ban yi maganar karatunki da iyayenki ba, bana so gaskiya, ki hak'ura kinji."_

Mik'ewa tayi tsaye tana dafe k'ugu irin fa da gasken nan take tace _"Me? Baka so fa ka ce? Kasan matakin karatu na ne da za'a datse min shi ban shirya ba? Ina so na zana jarabawar bac shekara mai zuwa, dan Allah Abdul ka barni na tafi ka ji."

Saurarenta yake tas yayi shiru abun shi, yanda ta fara maganar da zafi da farko sai ya bashi mamaki, amma a k'arshen nan da ta kashe murya tayi a sigar rarrashi ta kirashi da sunan da saka mi shi jin k'uruciya sai ya murmusa akan labb'enshi, tunani ya shiga yi ya barta ne ko kuma dai ta hak'ura, sanda aka yi aurensu da Hafsat ma tana tsaka da karatu kamar yanda shi ma yana tsaka da na shi karatun a Madina, yana tafiyarshi k'arasa karatunshi ita ma ta ci gaba da na ta a gidan Hajia, saidai inda matsalar take Hafsat da Mimi ba d'aya bane a halaye da yanayin zubin halitta kai har ma yanda yake jin su a zuciya, yana da yak'ini d'ari bisa d'ari Hafsat bata karya dokoki da sharud'an daya gindaya mata ba, amma Mimi? Wani iska ya feso yace "Ba zai yiwu ba gaskiya."

Da sauri Mimi tace _"Yanzu duk magiyar da na maka ba zaka barni ba? Haba sheikh na Allah, haba ustaz haba Abban Humaira da Munzeer, haba an tsohon yan matanshi."_

K'yalk'yalewa yayi da dariya yana fad'in _"Ryam, na ji to na ji."_

Da zumud'i tace _"Yawwa ka amince?"_

A take yace _"A'a, yanzu ki fara fad'a min me ye burinki idan kin kammala karatun?"_

A sanyaye ta feso iska ta koma ta zauna tace _"Abdul."_

A tausashe kamar zai k'urma ihu saboda yanda ta kirashi yace _"Na'am."_

Cikin shagwab'a tace _"Kud'i na zasu k'are, ka kirani da wayarka."_

K'it ta kashe kiran tana murmushi, shi ma dariya yayi yana maida mata kira da fad'in "Allah shirya min baiwar nan ta ka ta min sauk'in juyawa."

Tana ganin kiran ta d'aga shi kuma yace _"To ina jinki."_

A ladabce tace _"Ka ga dai idan na gama karatu ina so na samu babban aikin da zan siyawa Abbana gida, na siya mishi mota na siyawa Mama mota na had'ata da dreba, sannan na d'auki nauyin karatun su Yaseen a makarantar kud'i mai kyau ba kamar ni da nayi ta gwamnati ba, sannan na cika musu d'aki da kayan abinci da masu aiki a kewaye dasu, sannan duk shekara ina kaisu aikin hajd, shikenan."_

Cikin farin cikin jin burinta ba wani mai tsanani bane yace _"To ke kuma baki da abunda kike son yi ma rayuwarki ne?"_

Sauke ajiyar zuciya tayi tace _"Ni kam ba wani babban abu na ke so ba, dama dai burina bai wuce na samu d'an yaro ba na aura, wanda zai dinga kai ni shan ice cream sannan duk shekara ya kai ni k'asar waje nayi yawon bud'a ido, sai kuma na dinga haihuwa duk bayan shekara bakwai bakwai."_

Dariya ya shiga shek'awa kamar yaron daya samu kallon kartoon d'in Tom and Jerry hannunshi rik'e da sweet, sakin baki tayi tana mamakin me ya bashi dariya haka? A marairaice ta sake fad'in _"Abdul in tafi ne? Lokaci na tafiya."_

D'an tsagaitawa yayi da dariyar yace _"A'a Ryam, zamuyi magana a kan karatunki idan kin dawo gidana."_

Kyab'e fuska tayi irin zatayi kuka tace _"Yanzu duk yanda na gamaka da Allah baka ji ba, ku fa malamaina magada Annabawa, ko bakuyi niyyar abu ba aka had'aku da Allah kuna yi, ka tuna da cewa Imam Malik har mata ya aura saboda kawai ta had'ashi da Allah, kuma ya zauna da ita da kyautatawa duk da baya sonta a zuciyarshi, amma kai...shikenan sheikh ba komai, ka nuna min ban da mahimmanci a wurinka da zaka iya yi min wannan alfarmar."_

Sheikh ban da saurarenta da girmama lamarinta babu abinda yake yi, rik'e hab'a yayi a ranshi yace "Oh Allah! Wai ka haifi mutum a shekaru amma ya ce da tsiya zai maka wayo."

Cikin sakin murmushi yace _"Ya kike so na yi Ryam? Bana so ki je gaskiyar magana, amma tunda kika had'ani da Allah zan miki wani lamuni."_

Gyara zama tayi da zumud'i tace _"Yawwa ina ji."_

Sanyaya murya yayi yace _"Ki girka min abinda zan ci anjima."_

Yatsina fuska tayi tace _"Girki kuma?"_

A hankali yace _"Um! Ko ba zakiyi ba dan ki samu lada?"_

Da sauri tace _"Ni d'in me da zan ce ba zan yi ba? Zan yi mana."_

Murmushi yayi yana hangen falon Hajia dan tun d'azu suka shigo kafin yace _"Da kyau yar albarka, Allah ya faranta miki yanda kika faranta min."_

Wata dariya tayi tana nunashi da hannu kamar yana gabanta tace _"Abdul wannan addu'ar wallahi ta wayo dan kayi galaba a kai na, ba komai ka ci gaba da yi min yawo, wata rana zan rama ni ma."_

Dariya yayi yana fitowa a motar yana me jin kamar ya zauna yayi ta hira da ita yace _"Ai kin rama tun jiya, ko kin manta na je bikonki kika min wayon baki da lafiya, haka na dawo ni da k'atuwar rigata."_

Tintserewa tayi da dariya _"To wai idan na dawo yanzu me zan maka? Ga matarka nan da kake so da kuma 'yarka da kuka shigar ma fad'a kuka min taron dangin, dan kunga bana da wanda zai shigar min ne ai."_

Cikin murmushi yace _"Ryam ba na bayar da hak'uri ba? A yafe mana dan girman Allah mana."_

D sauri tace _"Na yafe, wallahi na yafe tunda ka ce girman Allah."_

Da jin dad'i yace _"Yawwa ko ke fa, ina sonki Ryam, na sumbaceki a bakinki."_

Da baki sake tace _"Ta ya ya? Bayan ban ji sumbatar ba."_


Dariya ya bushe da ita cikin tsokana yace _"Ke wata Mairama, ashe ma kina so na sumbaceki."_

Rufe fuska tayi da kunya tace _"Ni bana so, kawai tambaya ce na yi."_

K'it ta datse kiran tana dariyar jin kunya, shi ma soka wayar yayi aljihu yana girgiza kai da murmushi a fuskarshi yana shafa k'eyarshi, jami'an su dai da kallo suka bishi har ya shige falon suna mamakin wannan sabon shehi na su, su dai kam tun daga ranar da aka d'aura aurensu suke ganin bak'in abubuwa a tare da shi, kuma basu ga laifinshi ba tunda yarinya ya aura wacce ko su dake da k'uruciyar da baya da suka auri sa'arta zasuyi fiye da haka ma bare kuma shi.

A nutse yake zaune k'asa gaban Hajia yana d'an jujjuya kofin tangaren d'in data aje masa da zazzafen shayin na'a na'a a ciki, bayan sun gaisa ne Hajia ta numfasa cikin d'an fad'a fad'a da dattijuwar uwa kuma wacce take gaba dashi ta kalleshi a zafafe tace "A ce duk abubuwan nan na faruwa amma ni babu wanda zai iya fad'a min, ba ma wannan ba sheikh akan menene zaka zauna k'aramar yarinya 'yar cikinka har tayi sanadiyar barin matarka d'akinta? A kan me?"

Kuma sunkuyar da kai yayi bai yi magana ba yana son bata damar fad'an abinda take son fad'a, d'orawa tayi da "Yanzu fa kwana biyu kenan, tunda Hafsat ta fad'a min tun shekaran jiya ta tafi, ni abunda ya ke k'ona min rai shi ne yanda ku ma dana haΓ―fa kuka min biyayya kuka karb'i Mimi da hannu biyu, bare kuma 'yar da kuka haifa a ce ita ce zata bamu matsala."

Cikin ladabi da nutsuwa da girmamawa ya kuma sadda kan shi yace "Ayi hak'uri Hajia, insha'Allahu zamu gyara kurenmu."

Kawar da kai tayi tace "Shikenan Allah yasa, amma ku sani ban ji dad'i ba, kuma nayi niyyar tafiya gidan na ci uwar Aishan a gabanku, in ya so na ga zaku rama mata ne kamar yanda kuka taru akan baiwar Allahr yarinya, wannan ma ai shirme ne sai kusa na ji kamar tusa muku ita ne nayi a dole kuke zaune da ita."

Girgiza kai yayi ya d'an d'aga kai ya kalleta yace "A'a Hajiarmu, sam ba haka bane, mu kanmu iyayenta kun isa damu bare kuma ita."

Sake d'auke kai tayi tana sauke numfashi da k'arfi, dan har ga Allah jarumta ce tayi wajen yi mishi fad'an nan, abu ne da bai tab'a faruwa ba a tare dasu, shiyasa ko da Hafsat ta fad'a mata a waya abinda ya faru tare da cewa ta rok'a mata gafararshi yasa ta yanke shawarar dole ta nuna masa ita ma kamar uwa ce a gareshi. Cikin sanyin murya kuma ta d'ora da fad'in "Sannan Hafsat ta ce tana mai baka hak'uri akan abinda tayi, ta fad'a min ita ce da laifi ba Mimi, ita ta fad'a mata magana mai zafi, sannan ta ce na fad'a maka a d'an zaman da sukayi babu wani abu mai sunan raini daya shiga tsakaninsu, Mimi yarinyar kirki ce kawai wannan ma shed'an ne ya shiga tsakaninsu, kayi hak'uri ka ji."

Shi ma wani sanyayyen numfashi ya sauke yana lumshe ido lokaci d'aya kuma ya bud'e, kallon kofin hannunshi yayi yace "Ba komai Hajia na yafe mata, dama kuma ni babu abinda ta min, abinda na gani ne a ido ya min kama da za'a ci mutumcinta, ni kuma ba zan bari haka ta faru ba indai ba na daina numfashi bane, shiyasa na yi haka."

Jinjina kai tayi cike da k'aunarshi tace "Mun gode Allah ya biya, kuma ni ma insha'Allah zan je na samu iyayen na ta na sake basu hak'uri, dan kuwa ni ce nan na karb'a maka aurenta, dole wasu abubuwan su rataya a wuyana, kamar yanda idan kuka cuta mata to ni kuka ci amana."

K'anshi sadde kasa yace "Insha'Allahu ma haka ba zata sake faruwa ba Hajiarmu, amma kuma..."

Da kulawa ta kalleshi tace "Amma me?"

Cikin jin kunya yace "Bata gidansu tana wajen kakaninta, ina ga kamar bata san komawa ne ita ma shiyasa da muka tafi jiya tace bata da lafiya."

Dariya Hajia tayi tace "Allah sarki Mimi, ina k'aunar yarinyar wallahi, ai ko ni ce ita zanyi abinda ta yi, dole ta tsorata daku ta ga baku da adalci a rayuwarku."

Rufe ido yayi sai kuma yayi saurin d'aga kan shi yace "Hajia ki je ki bata hak..."

Shiru yayi dan ya tuna zai yi kwafsi fa a gaban suruka kuma uwar ta shi, murmushi Hajia tayi tana girgiza kai tace "Ba damuwa zan je na bata hak'uri, sannan na fad'a mata ba haka kake ba akasi ne aka samu yanzu ma, amma kai ma abinda nake so da kai shi ne ka bita a hankali kana lallab'ata har ta koma, kaga fa haka kawai sai kirana kayi a waya ka ce min ta tare a gidanta, na tabbata bata ji dad'in haka ba, to bana so yanzu ma tayi yaji a tilasta mata dawowa."

Yar dariya yayi yana jin wata kunya na rufeshi tare da tuna washe garin ranar daya angwnce ya kira yace ai ta tare gidanta, k'eyarshi ya shafa yana mai d'an turo hularshi a gaba yana sissine kai. Murmushi t sake yi tace "Shikenan Allah yayi albarka, Allah ya baku zaman lafiya da hak'urin zama da juna, ka tashi ka tafi lokaci na wucewa."

Da ladabi yace "Ameen Hajiarmu, nagode Allah k'ara lafiya."

Mik'ewa yayi suka sake sallama ya fita yana mai godiya ga Allah da yasa yau akwai wanda zai iya zaunawa gabanshi kanshi k'asa ya masa fad'a, lallai wannan ma babbar ni'ima ce a gareshi ace akwai mai fad'a maka ka ji.

Yana daf da shiga mota motar Asas ta danno hancinta cikin gidan, shiga yayi suka saita na su motocin zuwa k'ofar fita, tsayawa sukayi inda Asas ya tszya a daidai da motar sheikh, sauke glas duk sukayi suka kalli juna, dukansu mamakin yanda zumuncinsu ke neman ja baya sukeyi saboda mata, tunda akayi aurensu ta waya dai babu wanda ya nemi wani, Asas bai sake zuwa gidan shi ba har yau, hakan duk saboda abinda ya faru ne?

Murmushi Asas yayi cike da kunya yace "Sheikh barka."

Lumshe ido yayi alamar amsawa, cike da zolaya yace "Gashi kuma ganinka na zo kai zaka fita, tunda na ga yanzu amarci yasa ka manta da d'an uwanka."

Harara ya watsa mishi yace "Tunda kasan inda nake ka sameni a can."

D'aga gilashinshi yayi ya ma dreban umarni da su tafi, dariya Asas yayi yace "Zan zo har gidan na sameka."

K'arasawa yayi shi ma su kuma suka fice a gidan zuwa wurin aiki.


*10:46*




*Alhamdulillah*
8/3/21, 10:05 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*53*



Sak'o ta tura masa gahere kamar haka _"Me za'a dafa?"_

Sanda sak'on ya riskeshi dubawa yayi da kyau dan baya tunanin ta tambayeshi, a gajarce shi ma ya maida mata da _"Idan zan samu had'in salade ma ya wadatar."_

A gajarce ta sake maidawa da _"An gama."_

Shi ma a gajarce ya maido da _"Nagode."_

Fitowa tayi ta samu Iya zaune a cikin rumfar da take girki, zaune tayi Iya ta kalleta sama da k'asa ta girgiza kai tace "Mimi Allah ya shiryaki, kuma tun jiya ciwon bai sake dawowa ba."

Dariya tayi irin ta 'yan zamani tace "Haba Iya share zancen nan, kin san wani abu ma?"

Tab'e baki tayi tace "SaΓ― kin fad'a."

Cikin nutsuwa tace "Kinga sheikh ne yace na had'a masa salade, kinga kuma yanzu ba yara ke akwai ba da zan aika, shi ne na ce na aikeki mana."

Dak'uwa Iya ta mata tace "Uwarki! Wato ni da aurena ba aure bane ko?"

Dariya Mimi tayi tace "Ba haka bane Iya, to idan kinyi niyya ki barni na je da kaina mana na siyo."

Wata dak'uwar ta kuma yi mata tace "Uwaki, an k'i a barkin."

Turo baki tayi ta tura k'afafunta kamar zata hamb'are Iya tace "To ni wanga tsohuwar na rasa gane miki, yanzu kuma so kike na sab'a umarnin mijin na wa ko me? Na ce ki je kin ce a'a, na ce zan tafi kin ce a'a."

Cikin fad'a Iya tace "Tashi d'auko kud'in ni zan je na siyo miki, amma ba zan bari ki fita ba kinji na fad'a miki."

Galala ta kalleta tace "Taya zan baki siyayyar nan mai yawa haka? Wallahi na san ba zaki iya fad'in sunan kokombre ba bare kuma su karas da mayonnaise."

Jim Iya tayi tana kallonta sai kuma tace "Ai shegun abubuwan nan naku ne na yan zamani da wuyar fad'a."

Dariya tayi tace "Yawwa to na je ko?"

A hankali ta kalleta tace "Gaskiya Mimi ina tsoron fitarki, ba wai dan ban yarda dake ba saidai kinga yanzu kamar amana ce ke a wurina, in wani abu ya faru ni za'a ce da sanina."

Marairaicewa tayi tace "Iya na miki alk'awarin babu abinda zai faru, kuma ba zan jima ba zan dawo tunda kinga ba k'asa zan tafi ba."

Sallama suka ji a farfajiyar gidan suka amsa yaron ya shigo, cikin girmamawa ya kalli Iya yace "Ina kwana Iya?"

Da kulawa ta amsa da "Lafiya lau Sadam."

Mik'o mata k'ullin goro yayi yace "Gashi wai in ji mamanmu ta ce goron Nuseiba ne aka raba."

Da fara'a ta karb'a tace "A'a masha'Allah, har an raba kenan?"

"E." Ya fad'a yana juyawa zai fita, da sauri tace "Sadam zo nan d'an albarka."

Dawowa yayi yana kallonta ita ma ta kalli Mimi tace "D'auko kud'in ki bashi ya siyo miki."

Cikin kumburo baki ta mik'e ta nufi d'akin ta d'auko kud'in, kawo tayi ta zauna ta lissafa mishi komai sannan ta ce ya shiga taxi zuwa kasuwa, cike da dattako yaron yace "A'a ki bar kud'in taxin, akan moton yaya Bello na ke."

Da jin dad'in dattakon daya mata tace "To nagode sosai Sadam, ka kula da titi kaji."

Fita yayi ita kuma ta d'auki wayarta ta kira Jamila dake kusa da gidan Iya, tana d'agawa daga b'angarenta ta fara fad'in "Shegiya Mimi amarya, sai yau kika tuna damu?"

Tsaki Mimi tayi cike da jin sarauta akan ta ta yatsina baki tace "Ke bana son iskanci, wai ku baku san inda mutum yake bane?"

Cikin dariyar mugunta Jamila tace "Ke tafi can marar mutumci, waye zai je gidanki kina kwasar amarci ke da sugar Dady d'inki."

Wani irin b'acin rai ne ta ji ya taso mata da bata tab'a jin shi ba, haka kawai ta ji ta bata masifaffen haushi, da k'unar zuci ta katseta da fad'in "E d'in, sai me? Na ci amarcin da shi da matsala ne?"

Tsagaitawa tayi da dariyarta tace "Ke ni ba masifa nake ji ba yau, fad'a min me ke labari? Zaki zo ranar k'umshina ne?"

Cikin dak'ilewa tace "K'umshin me?"

Da mamaki tace "Baki san ni zanyi k'umshin Salma ba na farko?"

Ba tare da wani kulawa ba tace "Ko? Ya akayi ta baki k'umshinta kamar ta rasa dangi?"

Cikin jin haushi Jamila tace "Ban gane ba Mimi? Wannan ai wulak'anci ne ma, yau a makaranta mun d'auka zaki zo ai shiru."

Cike da iskanci tace "Ke ni fa ba lafiya ma gareni ba, laulayi nake, ciki ne da ni."

Cike da zumud'i Jamila tace "Da gaske? Kai amma na ji dad'i, ashe dai shehinmu da saurenshi, da wuri haka?"

Wani lalataccen murmushi Mimi tayi a ranta tace "Can da yawonki, wai ciki, mtsss?"

A fili kuma d'orawa tayi da "Ke farantai nake so manya masu, idan akwai ki aiko a kawo min ina nan gidan Iya."

Da sauri tace "Da gaske? Yaushe kika zo?"

Tsaki tayi tace "Ban sani ba, idan zaki aiko min to, in kuma babu ki fad'a min."

Dariya Jamila tayi tace "Zan kawo miki da kaina ma, zan zo gidan yanzu dawowata kenan daga makaranta."

Tab'e baki tayi tace "Wato kuna zuwa kuyi shik'a ou dawo ko? Ai kunsan yanzu ba'a fara komai ba."

Dariya Jamila tayi tace "Ai ki bari kawai, in fad'a miki PC (Physique Chimie) ma wallahi saida ya tambayeki, Lariya ma tana ganinmu ke ta fara tambaya, ga su Sadiq da su Omar, ke kowa fa bakinshi a Mimi."

Wata shak'iyiyar dariya tayi kafin tace "Allah sarki Mimi mai masoya dayawa."

Cike da izgili Jamila tace "Kamar aljanna ba."

D'auke wayar tayi a kunne tace "Sai kin zo." K'it ta kashe kiran tana dariyar saboda tuna rayuwarta ta makaranta, a gaskiya zata sake lallab'ashi dan ta koma makaranta, tana son rayuwar nan sosai saboda rayuwa ce mai cike da 'yanci da nishad'i.



*Bayan kwana biyu*



Dke yammacin alhamis ne aiki take tuburan wajen had'awa sheikh abun bud'a bakin da ita ta saka kan ta ba tare da saninshi ba, 04:30 ta gama da komai ta saka a basket d'in da Jamila ta kawo mata ta ajiye jug d'in lemu gefe ta shiga wanka, wanka ta tsala ta fito ta shirya cikin doguwar rigar leshe wacce ta mata masifar kyau, kwalliya tayi sassauk'an mai ban mammaki ta kashe d'aurin d'an kwali, turare ta shafe jikinta da shi kafin ta d'auki mayafinta mai d'an girma ta rufe duka jikinta da shi ta saka saka da takalmi ta fito.

Kallo Iya ta k'are mata cike da jimami tace "Mimi kina ganin shirin nan baiyi yawa ba kuwa?"

Kallon kanta tayi tace "Iya wane yawa kuma? So kike na je a hargitse ne to ina wari."

Jinjina kai tayi tace "Ba haka nake nufi ba, Allah ya kiyaye hanya."

Dariya tayi tace "Yawwa Iya ta, sai na dawo."

Cikin zolaya tace "Kuma ki tabbatar kin karb'o min na wa abun bud'a bakin a wurinshi."

"To." Ta fad'a tana kallon Jamila dake shirin d'aukar basket d'in kwanukan da sauri tace "To uban wa zai d'aukar miki jug d'in?"

Hararanta Jamila tayi tace "Ban sani ba, ke uban me zaki d'auka bayan jakarki?"

Juyawa tayi ta kalli Iya tace "Iya dan Allah ba gabanki likita aka ce na daina d'aukar abu mai nauyi ba?"

Da mamaki Iya tace "Yaushe? Akan wane dalili kuma?"

Dariya Jamila tayi tace "Iya rabu da ita raina min hankali ne zaatayi."

Matsowa tayi daf da ita tace "Nima dai na kusa auren nan na samu ciki."

Hararanta tayi tace "Kafin kiyi dai ai har cikina yayi k'wari."

Iya dai na jinsu har suka fita suna wannan cacar bakin bayan Mimi ta karb'i basket d'in ta bΓ’ wa Jamila jug d'in lemu, suna fita kam basu sha wahalar samun taxi ba suka d'auki hanya, wayarta ta ciro a jakarta ta dannawa lambarshi kira.

Yana tsakiyar masallacin dake ma'aikatarsu duk yan ma'aikatar sun zagayeshi suna d'aukar darasin daya zamar musu saurare dole, ba komai kullum yake fad'a musu ba sai rik'o da amana da kuma yin aikin domin Allah, sannan nuna musu mahimmancin aikinsu da tuna musu al'umma suke ma. Wayarshi na fara vibration ya laluba aljihu ya cirota dan ya kashe kiran, sai dai? Wacce take kira tafi k'arfin ya katse kiranta, hasalima mamakin ganin kiran na ta ya shiga yi sanda sunan daya saka mata a lambar ya bayyana da *yan matana*.

Kamar wani marar gaskiya ya saci kallon mutanen dake gabanshi sannan ya d'aga wayar ya d'ora a kunne, cikin rad'a yace "Salam, ina darasi ne, zan sake kiranki."

Da sauri jin zai kashe wayar tace "Abdul."

Sam ba da son ranshi ba ya dakata saboda sunan Abdul data kira, cikin shagwab'abb'iya kuma siririyar muryarta tace "Gani nan fa tafe wajenka, zamu had'u a gidan nan ne ko kuma na zo ma'aikatar?"

Zabura yayi yana nufin tashi tsaye sai kuma ya kalli mutanen gabanshi ya dakata, ture hularshi yayi ta gaba ta koma baya yana tsatsare mutanen da ido da suma dayawa shi suke kallo, gyara zamanshi ya sake yi da kyau ya rufe bakinshi da tafin hannu cikin rad'a yace "Ryam ban gane gaki nan tafe ba? Munyi dake zaki fita ne?"

Cike da shagwab'a tace "To ba kai ne ka fad'a min kana azumi ba, shiyasa na maka abun bud'a baki, ni kawai ka fad'a min inda zan zo na sameka kaga fa ina cikin taxi ne."

A hankali ya lumshe ido ya furta "Hasbunallahu wani'imal wakil."

Bud'ewa yayi fes a kan mutanen dake gabanshi yana jin kamar ya fashe da kuka, ba wai fitowar babu izininshi bane matsalar, tunanin yanda ta fito daga gidan shi ne yake masa yawo a kai, shin ta rufe jikinta da hijab ne? Ta saka nik'ab da safar k'afa? Ko kuma dai yanda ya santa a haka ta fito kowa da komai ya gama kalle masa halalinsa?

Zunbur ya mik'e tsaye yana fad'in "Ku gafarceni, kira ne na gaggawa."

Da sauri ya juya inda jami'anshi suka rufa masa baya da sauri su ma, suna shiga mota yace "Gaggauta dan Allah, Tallague zamu je."

Yana maganar ne yana kiranta a waya, tana d'auka hankali tashe kamar wanda aka shaidawa iyalinsa na d'akin nak'uda yace "Ryam kina ina yanzu?"

Cike da rashin damuwa a tare da ita tace "Yanzu muka baro gida."

Da sauri yace "Hakan na nufin bakuyi nisa da gida ba?"

"E." Ta fad'a kan ta tsaye, wata ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi yace "Ryam ku dakata, ku dakata dan Allah gani nan tafe sai mu tafi tare."

Kallon Jamila tayi dake gefenta tace "Amma fa ba ni kad'ai bace, tare da k'awata muke."

A sanyaye yace "E, har da ita d'in."

D'aga kafad'a tayi alamar shikenan sannan tace "Ok."

Yanke kiran yayi ya mayar da wayar aljihu, maida kan shi yayi ga kallon gabanshi sai sukayi ido hud'u da dreba dake tuk'i fuskarshi d'auke da mamaki, matse bakinshi yayi ya feso wani sanyayyen iska yana tsare dreban da ido yace "Yarinya ce, wahala take bani, amma dai nasan na d'an lokaci da ta k'ara girma zata bari."

Murmushi dreban yayi yace "Hakane." Ci gaba yayi da aikinshi sai sheikh daya sake fad'in "Kana ga na ci gaba da lallab'ata a haka? Wani lokacin kamar mahaukaci nake zama wallahi, ban san ya zanyi ba."

Satar kallonshi dreban ya sake yi a ran shi yana fad'in "Allah ya sauk'ak'a maka sheikh, abun ya ta'azzara kam."

*Bakin* titi aka aje su suka gyara

Please Login or Register in order to submit comment