Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dana aura ce har yanzu baka cire a zuciyarka ba? Idan hakane ka fad'a min, yanzun nan a gabanka zan saketa sai ka aura inhar hakan zai sakaka farin ciki."

Da sauri duk suka kalleshi har da Asma'u dake ganin kwarjininshi, da sauri Asas hankali tashe ya girgiza kai yace "A'a sheikh, wallahi na hak'ura har abada, na rumgumi k'addarata da hannu biyu, kuma insha'Allah zan ci gaba da rik'ewa."

Wani nauyayyan numfashi ya sauke a sanyaye yace "Daga mu mazan har matan ya kamata mu d'auki wannan auren a matsayin k'addararmu, dukanmu babu wanda yayi hasashen hakan zai faru, babu wani mahaluki daya zauna ya tsara hakan, yin ubangiji ne, haka ya so ya kasance, shin da wace ni'ima ce muke k'aryatawa? Ikonshi ya fi gaban wasan bawa, komai yahudancin mutum idan mu'ujizarshi ta faru dole ya kan karya zuciya, saidai kawai mutum ya k'i gaskiya amma fa ya tgidanmu akan k'arya yake. Mu musulmi ne Ashraf da muka yarda a jerin rukunan imani guda shida akwai yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau, tunda muka amsa sunan musulmi mu yarda da duk jarabawar da zata samemu, ko kana so ko baka so dole ta zo, ta maka dad'i ko bata maka dad'i ba dole a jarabceka, saidai fa mu sani duk jarabawar da za'a wa mumini matuk'ar yayi imani kuma yayi hak'uri, to yana da sakamako mai tsoka. Yanzu wane gata ne ya fi wannan? Wane addini ne ya zo da irin wannan alkairan ga mabiyansa? Zazzab'i zakayi mai mugun zafi da zai saka ka fita hayyacinka, amma daga sanda ka kwanta har ka tashi lada ce mala'uku ke rubuta maka na sannan ana kankare zunubanka, da wannan zan rok'eka kayi hak'uri da jarabawarka sannan ka rik'e 'yar mutane da amana, ban da cin zarafi da halayen mata wato gori, watak'ila yarinyar nan ita ce warakarka da kake yawan fad'a mana."

Sosai jikinshi yayi sanyi har yana share k'wallar dake taruwar masa, dan gaskiya da ya so yayi sati kafin ya zo gidan nan, sannan Asma'u ya so ya zauna da ita dumkum d'in nan har sanda zata gaji tace sallameni, amma yanzu sai yaji wata sha'awar son zama da ita na shigarshi da kuma kyautata mata.

A tausashe sheikh ya sake fad'in "Mahaifiyarka da shaid'an ya zigaka har kake ganin ta maka ba daidai ba har da tagomashin hukuntata ta hanyar nesanta kanka da ita, ka bata hak'uri yanzun nan ka kuma nemi yafiyarta, sannan karka sake maimaita min irin wannan kuskuren dan ba zan d'auka ba, uwa daraja ce da ita, kima ce da ita da babu wani abu mai daraja da zamu iya had'awa da ita, munyi sa'a Allah ya bar mana ita, ita muke zuwa mu fad'a ma kukanmu da farin cikinmu, Ashraf kayi sa'a kai ta ka mahaifiyar ma tana raye, ni ina tawa take a yanzu? Nayi imani da zata dawo yanzu a duniyar nan na minti d'aya kawai ta umarceni da na auro biyu akan biyun da nake da a yanzu, wallahi tallahi zanyi dan farin cikinta, ita ta tsaya min na taka matakin da nake kai yanzu, ita ce k'ashin bayana da har na iya zama da d'uwawuna, addu'arta ce har yau take tasiri a gareni, kullum fata da burinta shi ne na zama babban malami kuma babban mutum."

Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya sa bakin hiraminsa ya share k'wallar data tarar masa a gefe, ya d'an jila yana shashek'ar kuka kafin yace "Sanda na fara hawa matakin da take da burin ganin na hau, sai Allah ya karb'i rayuwarta gaba d'aya ta bar duniyar, na d'auki hakan a matsayin jarabawata mafi girma, har yanzu ina kukan rashin mahaifiyata, ina kewarta, ina neman sa war albarka daga bakinta."

Sake duk'ar da kai yayi dan sosai kukan nan ya ci k'arfinsa, mik'ewa yayi da sauri ya nufi hanyar fita, da kallo suka bishi jikinsu duk a tsume Hajia har da kuka ita ma, da sauri Asas ya taso ya zo kusanta ya zauna k'asa ya rik'e k'afarta yana magiyar "Dan Allah Hajiata, dan girman Allah ki yafe min, Hajia kar na mutu a yau kina hushi da ni, Allah k'onani zaiyi Hajia ki yafe min."

Rik'e hannunshi tayi tana share k'walla tace "Ba komai Ashraf na yafe maka, ai tun jiya ma sheikh yasa na yafe maka."

D'ora kanshi yayi a cinyarta yana sauke numfashi yace "Nagode Hajiata, Allah k'ara miki lafiya da nisan kwana."

"Ameen." Ta fad'a tana kallon Asma'u da tayi shiru jikinta yayi sanyi ganin sheikh na kuka, da hannu Hajia ta mata alamar ta zo, mik'ewa tayi tana gyara hijabinta ta zauna k'asa ita ma, dafa kanta tayi tace "Allah ya miki albarka Asma'u, kuyi hak'urin zama da junanku kunji."

A tare suka jinjina kai kafin ta rik'o hannayensu ta had'a wuri d'aya, a take suka kalli junansu sabida yanda ta had'a hannayen nasu, cikin fara'a tace "Zaman lafiyarku shi ne farin ciki na, ku girmama junanku ba tare da tuna ta yanda aurenku ya kasance ba, na tabbata akwai abinda Allah yake nufi da auren na ku, komai k'ank'antar alama a cikin tarayyarku zamu d'auketa mu rik'e a matsayin abinda Allah ya hukunta, dan haka kuyi hak'uri ku tallafi junanku wajen samar da kyakyawan sakamakon da zamuyi nuni da shi."

Jinjina kai sukayi sosai kafin ta saki hannayensu, kallon Asma'u tayi tace "Ki shiga ciki k'awarki na nan."

Da murmushi ta mik'e ta nufi inda Hajiar ta nuna mata, da sallama ta shiga d'akin tana tura k'ofar. Mimi da har lokacin take zaune a k'ofar ban d'akin da sauri ta mik'e jin saallamar Asma'u, bud'ewa tayi ta fito suka hada ido, wani kukan ta fashe da shi tare da tahowa a guje ta rumgume Asma'u tana fad'in "Asma'u mugu ne, ki tafi dani dan Allah ki kaini gidanmu, cire min kayana yayi."

Cikin tashin hankali da rashin sanin inda zancen ya nufa Asma'u ta d'ago tana fad'in "Ya cire miki kaya? Wanene?"

Cikin turo baki tace "Waccen malamin mana."

Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke, kama hannun Mimi tayi suka zauna kan gado, a tsanake ta kalleta tace "Mimi me ya faru? Nasan dai haka kawai sheikh ba zai miki rashin kirkin da har zaki kirasa da mugu ba idan ba ke kika tsokano shi ba."

Share hawayenta tayi dan zuwan Asma'un yasa duk ta ji babu wannan tsoron da k'uncin, cikin rashin damuwa tace "Ke ni bansan me na masa ba, kawai dai ya hau ni da masifa da tijara."

D'an guntun tsaki tayi tace "Kinji fa yana malami amma yake fad'in idan iskanci zaiyi a niger zan d'auka shi kad'ai ne ya iya iskanci, hmmm."

Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, da kallo Asma'u ta bita tace "Ai gaskiya ya fad'a miki, mahaddacin Alk'ur'ani masanin sirrin yahudu da nasara kina ganin akwai wani abun ne da zai shige masa duhu?"

Tab'e baki tayi ta d'auki dogon towel d'inta ta d'aura a k'irji sannan ta k'arasa cire rigar gaba d'aya, matsowa tayi kusan Asma'u cikin rad'a tace "Ke har da tab'a min d'uwawu yayi, wallahi ki fad'a masa yayi na k'arshe."

Dariya Asma'u tayi tace "Ai sadakinsa ya biya, kad'an ma kika gani yarinya kafin ki tare."

Sake tab'e baki tayi ta shige ban d'akin Asma'u na fad'in "Ke tare da shi fa muke zaki wani shanya ni a nan?"

Tsayawa tayi ta juyo tare da kallonta tace "Tare kuke? Wani gurin zaku je?"

Girgiza kai tayi tace "Ke bakiyi mamakin gani na ba a yanzu? Jiya ne dama yace sheikh ya ce mu zo nan."

D'aga mata gira tayi tace "Wani abu ya muku?"

Girgiza kai tayi tana fara'a tace "Nasiha ya mana mai shiga zuciya."

Yatsina fuska tayi tace "Ki gaishe shi to." Ta fad'a tana shigewa ban d'aki dan yin wanka, girgiza kai Asma'u tayi ta mik'e tana murmushi ta fita a falon, jiranta ta samu Asas na yi tana zuwa yace "Muje."

Yanda ya mata magana d sakin fuska sai ya bata mamaki, sallama tayi da Hajia suka fice a gidan, tun a mota ya so kasheta da mamaki sakamakon hannunta daaya rik'o yana matsawa yana sakar mata murmushi, yanda take sunkuyar da kai yasa shi kallonta yace "Wai kunya kike ji? Lallai ma *Naanah* gwara ki daina, dan babu abinda zai hanani yau dai na sa ki amsa sunanki a matsayin *Asma'ul-Husna* matar Ashraf."

Gabanta ya shiga wani irin lugude yana fad'uwa, sake duk'ar da kai tayi ba tace komai ba sai rawa maa da bakinta ya d'auka, da haka suka k'arasa gida saidai bai sake fita ko ina ba, tare suka wuni kuma sosai suka samu wata irin fahimta da shak'uwa, dan yanda ya fahimceta shi ne ita d'in bata d'auki duniya da zafi ba, duk abinda aka mata ko ta samu zata karb'a da hannu biyu tayi godiya ga sarkin daya nufeta da samun wannan d'in, hakan yasa shi fara jin ta daban a zuciyarshi tare da mata wani kallo na matar aurenshi wacce zai iya yak'i a yanzun dan kare martabarta.


*Yammacin litinin*


Fitar Hajia yasa Mimi shigewa d'akinta ta kunna wak'a a wayarta, duk da ita d'in ba gwanar rawa bace amma sai gashi ta zage tana tik'ar abarta a d'akin tana kuma gyaran d'akin, dan in kid'a ya kai mata har tsayawa take a gaban madubi ta cashi abarta kafin ta ci gaba da aikin.

Sheikh ma na shigowa gidan da niyyar daya bata sak'onta ya wuce gida, dan litilin d'in yau ta zama mai sauk'i aiki a gareshi a ofishi, dan haka yayi saurin baro ofishin ya fara biyowa ta gidan, Salamatu na gad'a mishi Hajia ta fita sai kawai ya wuce d'akin kai tsaye, duk da kuwa zuciyarshi na kwab'arshi k'walwarshi kuma na tuna mishi had'uwarsu ta safe, d'aure fuska yayi ya bud'a k'ofar da tunanin sai fa ya gyara mata zama dole yarinyar nan.

Ai kam turus yaja ya tsaya sakamakon jin kid'a da kuma ganin k'anwar *shakira*🀣, da d'an k'arfi ya furta "Hak'ik'a daga Allah muke kuma gareshi zamu koma."

Waro ido yayi da kyau dan shi ko cikin yaranshi a k'iriniya ta yara bai tab'a ganin haka ba. Jin sautinshi ya fargar da ita da sauri ta tsaya tana kallonshi, pik'i-pik'i ta tsaya yi da ido tana neman hanyar dakawa a guje, takowar daya fara yi ce ta sa ta ja baya tana fad'in "Dan Allah malam dan soyayyarka da Allah karka dakeni, kaga dai Hajia amanata ta bari ko?"

Yanda ta k'arashe maganar da nunashi da yatsa irin a dole tambayarshi ne take cikin yanayin yi mishi hannun ya mai sanda sai ta so bashi dariya. Tara mata hannun dama yayi yace "Bani wayar nan?"

Galala tayi tace "Iyee?"

Fito da idonshi yayi yace "Na ce ki bani wayarki?"

Da sauri ta d'auka ta mik'o mishi tana sake fad'in "Malam ai ku an ce ba kwa hushi saboda magada annabawa ne ku, dan Allah kar ka rabani da wayar zan daina daga yau."

Sama da k'asa ya kalleta ya mik'a mata k'atuwar ledar hannunshi, hannu biyu tasa ta karb'a shi kuma ya d'ora da fad'in "Wannan ita ce zata zama suturarki idan zaki fita."

Juyawa yayi kawai ya fita yana sake hangota tana ta kiciniyar rawa a shigowarshi, girgiza kai kawai yayi ya fita a falon, saida ya shiga mota dreba na jan shi ya shiga duba wayar, irin tarikitan hauka daya gani saida yaji kanshi ya fara ciwo, vidΓ©os na wak'ok'i da girki da kwalliya da shirme da shiririta na dariya, hotuna na d'inki da matan da bai ma san dan d'inki ne aka aje hoton ba ko kuma dan kwalliyarsu, tsaf ya tattara komai ya goge ban da girki da yake ganin zasu anfani mace, sai kuma hotunan ta daya samu barkatai wanda ya tabbatar zuwan k'awayen nan nata zata samesu, kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, idan ya ga wani style d'in sai kawau ya tintsire da dariya shi kad'ai, lallai kawai ya gama yarda yarinyar yar zamani ce, da wannan ya isa gida inda suka zauna a duka babban falon shi da ahalinsa suka shiga hira da raha ana tsokanar juna, a sauk'ak'e kuma iyayen ke fahimtar wani kuskure na kalma a tare sa yaran sai su d'orasu a hanya.


Bayan fitarshi kuma Mimi ta bud'e kayan nan, hijabbai ne zumbula zumbula har k'asa ko hannaye basu da, sai nikab da safar k'afa. Kecewa tayi da dariya tana fad'in "Wayyo Allah na akaramakallah, yo wannan ka d'auka ni d'in wata aljana ce? Tabb' lallai ma!"

Tattaresu tayi ta zuba akan gado ta shiga harkar gabanta da tunanin ta yanda zai dawo mata da wayarta ma, dan ita tafi damunta kam.


*Asa-Ma'u*


A wajen amaren kula yau fa daren na musamman ne dan sosai Asas ya zage damtse wajen kwasar amarcin shi da matarshi, kamar yanda yake hari matarshi ce zata zama silar warakarshi hakane ta kasance.

Sosai Asas ya rik'e wuta akan baiwar Allah Asma'u, tun tana jin kunyar nuna gajiyawarta har ta fara mishi kukan tab'ara tana magiyar ta gaji haka, mamaki yake yanda ya kasa sararawa 'yar mutane, jikinshi k'ara rik'ewa yake yana d'aurewa, hakan yasa suka galabaita daga shi har ita. Wata masifaffiyar zufa ce ta shiga tsatsafo masa sanda ya sauke wani curarren abun daya tarar mishi a mara, take kuma sai jikinshi ya kwashi b'ari sosai, cikin tashin hankali Asma'u ta yunk'ura ta shiga tureshi a jikinta saboda ganin yana wani shure shure kamar zai mutu, fashewa tayi da kuka tana jan zanin jikinta da k'yar tana fad'in "Assss...a..." Gaba d'aya sai ma ta manta sunan da zata kirashi da shi.

Tsaf ta ga ya daina numfashi bare motsi, a firgice baiwar Allah duk da azabar da take ji a jikinta sai ta manta, da gudu ta shiga ban d'aki da zanin rufa a jikinta ta rufe jiki ta d'ebo ruwa ta shafa mishi, shiru ba alamar Asas zai dawo, ai da sauri ta bud'a kayanta ta d'auko doguwar rigar atamfa ta saka ta fito wajen gidan, cikin tashin hankali take k'wala kiran "Mai gadi, mai gadi."

Kamar daga sama yaji kiran sunan shi ma a kid'ime ya fito yayo kanta, da gudu ta juya ta koma tana fad'in "Muje ka taimaka min, bashi da lafiya."

Da gudu ya bi bayanta suka shiga d'akin, ganinshi kwance babu kaya a jikinshi sai zanin gadon data ja ta rufa mishi, juyawa yayi yana fad'in "Hajia saka mishi ko duguwar riga, bari ni saina kira lambar Hajiarshi."

Fita yayi a d'akin da sauri tana matsar k'walla da cije leb'enta dan sosai take jin ciwo a jikinta, kawai dai tashin hankali ne wani yafi wani, da k'yar ta saka mishi dogon wandonshi na bacci da doguwar farar rigar, zaune tayi ta sakashi gaba tana kallo tare da rik'e hannunshi, babban abinda ke ranta a lokacin bai wuce "Kar a zo *sanadin takaba* ne yasa aure na da Asas ya tabbata, Allah ka tashi kafad'unshi kasa kar ya mutu ya barni, duk da ba son shi ne a zuciyata ba amma zan so ya zama mutumin da zai ci gaba da abonda ya fara."

Mintuna ashirin da biyar suka kawo Hajia gidan tare da drebanta, tana shigowa d'akin Asma'u ta mik'e tana sake fashewa da kuka, cike da dagiya Hajia ta dafata tace "Me ya sameshi Asma'u."

Cikin kuka tace "Hajia ban sani ba nima, kawai...kawai fad'uwa yayi haka."

Sake kallonshi tayi ta kalli gadon, da sauri ta d'auke idonshi daga birbid'in jinin data gani a kan zanin gadon dake jikinshi, saidai tana mayar da idonta k'asa sai kuma akan pant d'in Asma'u, cikin dattako da hangen nesa ta fahimci me ya faru, kallon k'ofar shigowa tayi tace "Kabiru."

Daga falo drebanta ya amsa da "Na'am Hajia."

"Ku shigo ku kama mana shi." Da sauri suka shigo tare da mai gadin, wani ikon Allah yau Hajia sam bata jin wannan rud'ewar da furgicin da take shiga idan ciwonshi ya tashi, sauta samu kanta da fad'awa zuciyarta "Idan har wannan ita ce warakar Allah ya yafe kurakurenshi, idan yana da sauren shan ruwa a gaba, Allah ya tashi kafad'unshi."

Kallon Asma'u tayi sanda zata fita tace "Yata ki nutsu kinji, ki zauna ki kula da kanki kafin jikinki yayi tsami, ina tare dashi insha'Allah zan kula dashi."

Cikin kuka Asma'u tace "A'a Hajia zan biku nima, a tsorace nake gaskiya ina so nasan halin da yake ciki."

Girgiza mata kai tayi tace "A'a Asma'u, ki zauna ki samu euwan zafi kiyi wanka kinji, ki kula da kanki nima zan kula dashi."

Cikin marairaicewa tace "Hajia ina so na je na ga halin da... *mijina* yake ciki."

Murmushi tayi ta shafa kumatunta cike da tausayinta tace "Yanzu ki fara gyara jikinki, idan gari ya waye zan turo k'awarki sai ku tafi tare."

Da sauri ta kalleta tace "Mimi?" Da fara'a ta d'aga mata kai alamar eh, jinjina kai tayi ta bita da kallo harta fita, jiki a sanyaye ta fito falon ta shiga madafa dan d'ora ruwan zafin kamar yanda Hajia ta fad'a.



*Washe gari*

Tunda asuba sheikh ya zo asibitin ganin halin da yake ciki, cikin nutsuwa Hajia ta shiga fad'a mishi abinda Dr. D'in ya fad'a "Ya ce dai wannan karan ciwon ba kaman waccen ba, dan haka ruwa suka k'ara mishi ba tare da alluran da suka saba yi mishi ba."

Numfashi ya sauke yana sake gyara tsayuwarsa yace "Insha'Allah Hajiarmu komai ya kusa zuwa k'arshe, jiya da dare nima na sak'o a email d'ina daga wani abokin karatu na dake Tunisie, kuma ya fad'a min ya sama mana lokacin had'uwa da wani babban likita daya k'ware a wannan fannin, insha'Allah yau zan gama shirya mana tafiyata da shi, gobe ko jibi zamu bar k'asar nan da izinin Allah."

Da farin cikin jin haka tace "Masha'Allah, Allah nuna mana, Allah yasa ayi a sa'a."

"Ameen." Ya fad'a a sanyaye yana kallon Asas, d'an sake kallon Hajia yayi yace "Ina iyalinsa?"

Kallonshi tayi tace "Tana gida, amma na tura Kabiru ya d'auki Mimi a gida saiya kai ta can wajenta, dan na lura hankalinta ya tashi sosai kuma kamar bata da lafiya, amma na ce Salamatu ta fad'awa Mimi idan ta ga jikinta da sauk'i su zo nan tare ta ga jikinshi."

K'uri! Yake kallon Hajia duk sanda tace Mimi yana jin wani b'all! A zuciyarshi, kallon fuskar Hajia kawai yake yi yana tunanin "Anya kuwa Hajia tasan wacece yarinyar nan?"

D'an d'auke kan shi yayi a hankali yana sauke numfashi, jim kad'an ya sake kallon Hajia yace "Hajiarmu zan wuce gida, dama daga masallaci nake, amma idan na shirya kafin na wuce aiki zan sake biyowa na ganshi."

Da sakin fuska tace "To sheikh ba damuwa, sai ka dawo."


*Mim-Ma'u*



*Assalama alaikum*

_Kwanakin da suka wuce zaku ga na zage ina ta baku page bibbiyu a wuni d'aya wata rana ma har uku, ba komai ya kawo haka ba sai ganin kuna comment masha'Allah. Watak'ila lura da kukayi ina yi akai akai ne yasa wasu tunanin ko zaman banza ya min yawa, dan haka zakuyi tunanin barin comment da tunanin ai zan ci gaba da sako muku, magana ta gaskiya abinda yasa a can ma kuke ganinshi a kai a kai comment d'inku ne ya ban k'arfin gwiwa, yanzu kuma da kuka rage sai gaba d'aya na mayar da hankalina kan harkokina da kuma rayuwata, *jiya* da k'yar da taimakon *Kwate ta* (Sajida) na samu na saki page d'in jiya, to da irin haka wata rana ma kasa rubutun zanyi._

_Dan *Allah* mu daure mu k'arasa yan tsirarun page d'in da suka rage mana, dan *MATAR MUTUM* ba labari ne ba da zan ja shi da tsayi ba, kuma ina fata matar mutum ya zama labarina na k'arshe a harkar rubutu, idan Allah bai nufeni da hakan ba kuma ina fatan nayi hutu mai dogon zangon da har za'a fara mantawa da sunana kafin na ci gaba, dan Allah ku karfafa min gwiwa ta hanyar sambad'a comment ko na samu na kai k'arshen labarin nan, a grp d'ina a k'alla sama da mutum 50 suna karanta labarin nan a sanda na turashi, amma mafi aksarinku saidai ku turo stekers da sunan kun yi naku comment d'in shikenan, ba zan sake ganin motsinku ba sai na jinkirta yin posting. To a gaskiya idan haka ta ci gaba da faruwa zan dakatar da posting zan kammala rubutu ne saina had'a document na ajiye kayana, dan ni bana tsayar da rubutu idan na fara, kunga kenan shi ma zai shiga sahun litattafaina dana mallaka._


*MOM LATEEF*



*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:58 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*34*



Duk da duhun safiya ce amma haka Mimi ta shirya tsaf abinta a cikin atamfarta riga da siket d'amammu ta saka hijab d'inta mai hannaye iya gwiwa tsayinshi, gashi kuma hijab ne irin na zamani mai wuya biyu ga kwalliya, dreba na ajeta gidan Asma'u ta shiga kallon gidan daga waje har ciki, saida ta kai daf da shiga falon ta sauke wata ajiyar zuciya tana jinjina kan ta, sosai tsarin gidan ya birgeta dan kamar yanda Asas yake fad'a mata haka ta samu gidan.

Saida ta bud'a k'ofar ta shiga a tausashe ta furta "Salam."

Asma'u da dama zaune take tana jiranta da sauri ta fito daga uwar d'akin tana amsawa da "Wa'alaiki salam."

Murmushi Mimi ta sakar mata inda Asma'u ta mata murmushin yak'e, cikin ciccije lab'e ta k'araso gareta tana fad'in "Muje."

Hararanta tayi tace "Wai ke duk kin damu ko? Ke ga mai miji."

A raunane tace "Ba zaki gane ba Mimi, halin da nake ciki Allah ne kad'ai ya sani kuma zai sama min mafita."

Cikin gimtse fuska tace "Wani abu yana faruwa ne?"

Kama hannunta tayi tace "Muje, zamuyi magana."

Yanda ta ga Asma'un na tafiya ita ma sai ta shiga bin ta a haka har ta rufe gidan suka fita, dukansu zaune suke a bayan motar sunyi shiru suna kallon titi. Numfashi Mimi ta sauke tace "Hajia tace min ba kya jin dad'i na zo na taimaka miki, ke kuma hankalinki yana gun mijinki."

D'an murmushi tayi tace "Hummm! Na ji sauk'i ai."

"Kin tabbata?" Ta fad'a taana binta da kallon tuhuma, dan duk da bata da sani akan wannan harkar amma dai a karance karance da kutse kutse tana iya gane kad'an daga ciki, shiru kawai tayi bata sake cewa komai ba har suka isa asibitin clinique de gazobi.

A wajen ajiyar motocin ya paka suka bud'e cikin nutsuwa suka fita. Tsaf daga shigowarsu har fitarsu daga motar duk a kan idon Sheikh da shi ma shigowarshi kenan zai shiga d'akin da Asas yake, tsayawa yayi yana k'are mata kallo kamar ya d'ora hannu a kai yace "Wayyo shi wayyo Allah ya shiga uku!"

Akan me zata fito babu hijab d'in daya bata? Babu nikab a fuska bare safar ta k'afa, kenan ba zata tayashi kare martabarta ba? Wani huci ya sauke mai d'auke da siracin bala'i da gudummuwar kishi ta haifar, a sauk'ak'e ya shiga takowa cikin shigarshi ta kamala da mutumci.

Zasu wuce kenan suka ji drebansu Hajia na gaisheshi cikin girmamawa da ladabi, dakatawa sukayi inda Mimi cikinta ya fara juyawa ga fad'uwa da gabanta ya fara yi, Asma'u ma juyawa tayi tabbatarwa da tayi shine yasa ta sunkuyawa tace "Assalama alaikum."

Da sakin fuska ya amsa mata da "Wa'alaiki salam, ya jikin na ki?"

Tsili tsili tayi da ido da tunanin wai haka Hajia ta mata terere? Da murmushi ta amsa da

Please Login or Register in order to submit comment