Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ke ni ne jakin?"

A harzuk'e tace "E kai d'in, an fad'a da abinda zakayi ne?"

Wani sakaran murmushi yayi ya sha wani d'an iskan sajenshi yace "Ba komai yarinya, soyayya ta jawo haka, yanzu fad'a min me yasa wai ba kya d'aga wayata ne?"

Kai tsaye tace "Saboda zanyi aure." A firgice ya waro idonshi a kan fuskarta yace "Me! Aure fa kika ce?"

"Eh." Ta fad'a tana yatsina fuska tace "Ko da matsala ne?"

Gyara tsayuwa yayi yace "Babba ma Mimi, kinga fad'a min gaskiya?"

Gyara tsayuwa tayi ita ma tace "Wallahi gaskiya nake fad'a maka, yanzu haka ma daga kan d'inki nake na shigar biki na, aure zanyi da wanda ya dace dani."

Girgiza kai yayi tare da sunkuyar da kanshi, ya d'an jima kafin ya d'ago ya kalleta ba alamar wasa yace "Mimi, na fad'a miki a baya cewa idan har ban sameki ba babu wani d'an iskan da zai sameki, wallahi wallahi Mimi idan na rasaki kowa ma saidai ya rasaki."

Cikin rashin tsoro tace "Me zaka min? Kasheni? To bismillah kasheni Muttaka, idan ka min haka ni ka hutar dani dakon tunanin abinda ke neman lalata min rayuwata, amma ka sani hakk'i'a da alhakina zasu rataya a wuyanka ne."

Sama da k'asa ta harareshi zata wuce ya rik'e hannunta gam, jujjuya hannun ta shiga yi tana son k'wacewa amma ya rik'e jim a hannunshi, had'e fuska ya sake yi sosai cikin dakakkiyar murya yace "Na rantse miki da Allah indai ina raye babu wanda zai sameki Mimi, ko dai ki aureni hankalinki ya kwanta, ko kuma ki ci gaba da shirye shiryen bikinki da wani amma fa tabbas ba za'a d'aura auren ba."

Cikin tsiwa da haushin rik'e mata hannu tace "Insha'Allahu zaka ga d'aurin aurena da mutumin da bakayi zato ba, sunanshi kawai zaka ji ya jijjigaka dan ko kusa dashi ka tsaya sai kayi fitsari a wandonka, kallon fuskarshi kula yafi k'arfin idaniyar mashayi kamar ka, kusa dashi ma idan ka tsaya sai zuciyarka ta buga tsabar tsoro da kwarjinin *mijina*."

Sakin hannunta yayi yace "Shikenan zaki gani kuwa, ba dai ni kika wa haka ba saboda nace ina sonki? Wallahi ko a haukace sai kin zauna dani, banza 'yar k'ananan mutane."

Juyawa yayi a fusace Mimi kam takaicin an tab'o iyayenta yasa ta duk'awa ta kwashi tsakuwa ta watsa mishi cikin k'arajin murya tana fad'in "Kai ne banza d'an k'ananan mutane, mashayi da baisan ciwon kanshi ba, kai baka san miye soyayya ba ma bare har ka samu wacce zata so ka, banza alade kawai."

Da matsiyacin mamaki ya juyo ya kalleta, takowa yayi a hassale yana zuwa ya d'aga sangamemen hannunshi ya kasheta da mari yana fad'in "Ni ne banza alade? Ni ne aladen? Bari na nuna miki abinda dabba irina take aikatawa."

Yanda ta fad'i k'asa ne yasa shi yunk'urin fad'awa kan ta, cikin k'arfin hali Yaseen ya jawo rigar Muttak'a yayi baya dashi da k'arfin da Allah ya hore mishi, yana tangal tangal kamar zai fad'i ya kalli Yaseen, cikin zafin nama ya sake kawo mata hari, durk'usawa yayi duka gwiwoyinshi k'asa ya shiga kiciniyar rik'e hannayenta da take kai mishi duka dasu.

Cike da jarumtar data samo asali a jinin yan uwantaka, cike da rashin tsoro da kuma yarda da cewa Allah ya bashi makaminshi Yaseen yayi kukan kura ya bugawa Muttak'a faffad'an kanshi. Yanda abun ya zo a bazata yasa Muttak'a jin wani gummmmmmm! Cikin kanshi, duk yanda ya so ya bud'e ido kasawa yayi saboda gaba d'aya kanshi kamar ba'a jikinshi yake ba, suna ganin ya fad'i kwance a wuri dafe da kai yana mirginawa Yaseen ya kama hannunta ta mik'e da sauri da gudu gudu suka barshi nan wurin, saida suka kai daf da gida ta kama hannunshi ta durk'usa tana sauke numfashi, kallon hannunta yayi dake ta rawa yace "Mimi ba zan fad'a musu ba, nasan abinda zaki rok'a kenan, amma kiyi k'ok'ari ki dakatar da rawar da jikin naki ke yi, zasu iya ganewa."

Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai, shafa kanshi tayi tace "Baka ji ciwo ba?"

Girgiza kai yayi yace "Ai babu abinda na ji."

Murmushi tayi tace "Lallai kaine magajin Abba, tunda gashi ka ceceni."

Murmushi yayi shi ma yace "Kullum fa muka ji fad'anki a unguwar nan akan mu ne ko iyayenmu, ni ma zan tsaya miki babu abinda zai sameki."

Murmushi tayi ta shafa fuskarshi tace "Nagode k'anena."

Mik'ewa tayi suka shiga gidan da sallama, Abba na tsaye ya maida hannaye baya alamar su yake jira, ko sallamar babu wanda ya amsa Abba yace "Me ya tsaidaku har minti shida ya hau kai?"

Kallon Yaseen tayi da yayi saurin cewa "Abba k'asa muka dawo, har zata tare mana taxi na ce mu taho k'asa."

Harara ya dalla mishi hakan yasa Mimi durk'usawa tace "Wallahi Ab..." Hannu ya d'aga mata yace "Dakata, bana buk'atar rantsuwarki."

Hanyar fita ya nufa yana fad'in "Gobe ku k'ara."

Suna ganin fitarshi Mimi ta mik'e ta shiga d'aki ta cire hijabinta ta d'an kwanta a kan gado ta shiga dawo da had'uwarsu da Muttaka baya, tsoro ne fal taji ya cika mata zuciya da tunanin abinda zai iya yi mata, d'an k'waya kam tasan zaiyi abinda ya fad'a, saidai me zaiyi? Kasheta zaiyi ko fyad'e zai mata? Idan kisan ne ta wace hanya zai kasheta? Idan fyaden ne wani iri zai mata? Da wannan firgitaccen tunanin har bacci ya d'auketa a kan gadon.



πŸ₯° *Comment masha'Allah, shiyasa kuka sameni dayawa.*πŸ₯°



*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:53 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*23*


Sosai suke shan hirarsu ita da Rauda suna raharsu, Mama saidai ta shigo tayi wani abun ta fita tana jinsu, 09:05 Hafsat ta zo gidan tare da rakiyar Salamatu, yanda ta shigo da nutsuwa da sallama ya saka mama d'aga kai tana amsawa, masha'Allah ta fad'a a ranta saboda ganin Hafsat d'in, indai had'uwa, kyau, aji, kamala ake nema a gurin mace tabbas alamun Hafsat sun nuna mata hakan, gata jajir da ita gwanin sha'wa ta fito a bafulatanarta sak, ga bak'in hijab kuma dogon daya fito da doguwar fuskarta har k'asa.

Mik'ewa Mama tayi tana fad'in "Lale maraba, sannunku da zuwa."

Da fara'a da girmamawa tace "Yawwa sannu Mama."

Da fara'a ita ma tace "Sannu, ina wuni?"

"Ina wuni?" Ta fad'a a matuk'ar tausashe, saida mama ta d'auko kujera ta aje tace "Lafiya lau, anwuni lafiya?"

A ladabce ta zauna tana sauke numfashi kafin tayi murmushi ta sake gaisheta da mutumtawa, ruwa ta kawo ta aje musu Hafsat kam saida tasha dan kar Mama ta ji ba dad'i duk da bata da k'ishin ruwa, shiru ne ya d'an biyo baya kafin Hafsat tace "Mama baki ganeni ba ko?"

Da fara'a tace "Gaskiya kam ban shaidaku ba? Dan na fara tunanin ko b'atan kai kukayi."

Dariya Hafsat tayi ta kalli Salamatu dake k'arewa gidan kallon tsaf har zuciyarta take jin haushin wannan zab'i na mai gjdan nata Asas, sam abun bai mata ba sai take ganin kamar wannan shi ne *kaska* rab'i mai jini, matsayinshi da dukiyarshi yafi k'arfin a ce yarinyar da zai aura kenan. D'an gyaran murya Hafsat tayi hakan yasa ta maido hankalinta gareta, da ido ta mata alama hakan yasa Salamatu aje ledojin hannunta gaban Mama tana fad'in "Wannan ai ita ce yayar Alhaji Asas, uwa d'aya uba d'aya suke."

Da fad'ad'a fara'a sosai mama tace "Masha'Allah, ko ita ce Hafsat d'in da nake ji?"

Da murmushi Hafsat tace "Ni ce mama."

"Abu yayi kyau kam, ya su Hajiar suna lafiya?" Ta fad'a cike da kulawa, amsa mata sukayi kafin Hafsat tace "Mama dama sak'o na zo kawowa amarya, nasan kunsan babu wani shagali da za'ayi a bikin kamar yanda addini ya tsara, amma daga baya sai muka yi shawara duba da yanayin zamani da kuma ita kanta amaryar, shi ne ango yace za'ayi kamu kawai na amarya, amma fa shi ma ita da k'awayenta ban da shi da abokanshi, haka kuma kowa a dangi ma ga mai buk'ata zai iya halarta."

Shiru mama tayi tana saurarenta tana jinjina kai, saida ta kammala kafin tace "Wannan ai ba wata matsala bace, duba da kwana nawa ya rage Mimi ta shiga a k'ark'ashin ikonku? Ko yanzu kaso mafi girma yana hannunku ai, dan haka ba wata matsala wallahi, saidai idan mahaifinta ya dawo shi ma zan sanar dashi dan yasan abinda ake ciki."

Cike da gamsuwa da maganganun Mama Hafsat tace "Masha'Allah, mun gode sosai Mama, wannan ba matsala bane dama."

Ledar da Salamatu ta aje gaban mama ta nuna mata tace "Wannan kayan da amarya zata saka ne ango ya turo mΓ» dasu, insha'Allah ranar alhamis za'ayi kamun washe gari kuma d'aurin aurensu a babban masallacin juma'a."

Cike da jin dad'i mama ta jinjina kai tace "Hakane, Allah ya nuna mana ya kai mu lokacin da alkairi."

Cikin dariya Hafsat tace "Ina amaryar ne wai mama? Ko bata nan?"

Cike da kunya mama tace "Tana ciki kam, ai kusan wata d'aya ma kenan ta daina fita, shiga ciki tana nan."

Mik'ewa Hafsat tayi tana fad'in "Lallai mama kina kula mana da amaryarmu, Allah ya biyaki da aljanna, wannan sai mun bayar da tukuici ai."

Dariya mama tayi tana amsa addu'arta a zuciya tana kallo har ta shiga d'aki, Salamatu kuma na zaune tana ta yatsina fuska tana wa mama wani gani-gani, mama kam har ga Allah bata ma kula ba bare ta sa wani abu a ranta taji ba dad'i ko kuma tunani.

Mimi kam da suka kasa kunne tunda taji wacece ta d'auko hijabi ta labta ta haye gado tayi shiru, tana shigowa da sallama suka amsa mata da fara'a Mimi kuma na sinne kai k'asa, zaune tayi kusanta tana fad'in "Amaryarmu sannu? Ya hidima?"

Da d'an murmushin jin kunya tace "Alhamdulillah."

"Masha'Allah, yanzu ma na kawo kayanki ne na kamu ranar alhamis insha'Allah." Ta fad'a tana kallonta, k'ala ba tace ba sai ma sunkuyar da kai k'asa, cikin kulawa Hafsat ta sake fad'in "Gashi dai har kin kusa shigowa hannunmu baki sake zuwa gidana ba, na so ya kaiki ki wuni amma Allah bai nufa ba, dan zuwanki na ranar naga kuna sauri."

Murmushi ta sake yi tace "Zan je." Dariya Hafsat tayi tace "Yaushe kuma amayar? Kwana biyu ana uku fa zaki shiga lalle, ai k'anena ba zai yarda ki fita ko ina ba."

Cike da kunya ta sake sinne kai tace "Zan je insha'Allah."

Dariya ta sake yi tace "Na yarda zaki je, amma fa bayan aure."

Murmushi tayi sosai tana rufe fuska da hijabi, cike da jin dad'in ganin Mimi ta mik'e tana bud'e jakarta, enveloppe ta fito da ita ta aje kusa da Mimi tace "Wannan angonki ne yace na baki saboda ranar kamu zasu miki anfani."

Juyawa tayi bata jira me zata ce ba ta fita tana fad'in "Sai anjima amaryarmu, sai ranar kamu insha'Allah."

Da kallo Mimi ta bita kafin tayi saurin kallon enveloppe d'in, zaro ido tayi ta kalli Rauda dake ta murmushi tana saurarensu tace "Rauda na shiga uku, ta bani abu ta juya ta fita, ya zanyi da mama?"

Jin su Hafsat na fita a gidan suna ban kwana yasa ta d'aukar enveloppe d'in tana fad'in "Shi ma fa na fad'a masa bana buk'atar komai daga gareshi, me yasa zai min..."

Bata kai k'arshe ba mama ta d'aga labule ta d'auko kayan da aka kawo mata, cikin rashin gaskiya da tsarguwa da kuma sabawa da sabon halin Mama na cajeta yasa ta saurin sakin enveloppe d'in ta durk'ushe tare da fad'in "Na rantse da Allah mama bansan menene a ciki ba, ita kawai ta d'auka ta bani ban tambaya ba, kuma ga Rauda ki tambayeta zata fad'a miki."

Girgiza kai Mama tayi ta zuro k'afarta d'aya ta aje ledar tace "Miye anfanin rashin gaskiya yanzu? Gashi abinda bai kai ya kawo ba ya firgita miki nutsuwarki, me yasa mimi kika dinga yi mana k'arya? Da kina ganin yanzu haka ta faru?"

Girgiza kai tayi ta juya tana fad'in "Ko me suka baki a yanzu indai ba rok'onsu kikayi ba su suka ji suka gani zasu iya."

Tana ganin ficewar Mama ta share yar guntuwar k'wallarta ta d'auki enveloppe d'in ta zauna bakin gado ta bud'e, wani irin fad'uwa gabanta yayi sakamakon ganin kud'i ne sababi far dasu yan jaka jaka, mayarwa tayi ta aje ta kalli Rauda tana fad'in "Nufinshi nayi lik'i da kud'in nan?"

Wani murmushi tayi kawai ta girgiza kanta ta gyara kwanciyarta akan gadon ta shiga neman bacci.


*05:30*


Su Salma na fita a gidan sakamakon k'aratowar magriba yasa ta d'aukar madararta a kofi data b'oye k'ark'ashin gado had'e da yar zuma a ciki da karanfani da dabino data saka Asma'u mata a gida ta kawo mata, da sauri ta kifa kai ta shanye abinta, dan a gaskiya ranar taji su Sahura na fad'in har yanzu fa maganin zahi da kuma na sanyi (infection) ne aka mata, sai shi dai na zafi yanzu haka idan tasha tana jin yana saukar mata da d'umi a jikinta har ya saka ta kama ruwa. Yanzu ma da su Zeinaba zasu fita maltina ta basu su siyo mata amma tace su b'oye kar Mama ta gani (ba'a daddara ba kenan uwata?πŸ˜₯).

Asma'u na shigowa da sauri taa fad'a d'akin hankali tashe, cikin rad'a ta shiga fad'awa Mimi "Ke yanzu na ga Muttak'a a k'ofar gidan nan, ya ce wai na kiraki na fad'a masa an hanaki fita saboda aurenki ya matso, ke kinga tashin hankalin?"

Gyara zama tayi tace "Wallahi rantsuwa ya mana wai ba zaki auri wani ba shi ba, tunda har kika wulak'antashi kika yaudareshi to zaki gani."

"Zan ga alheri." Ta fad'a tana mik'ewa dan shiga wanka, cikin nuna damuwa Asma'u ta mik'e ita ma tace "Mimi bana son matsala fa, mutumin nan tunda ba hankaline dashi ba me zai hana ba zaki fad'awa Asas ba? Watak'ila ya mana maganinshi."

Kallonta tayi tace "Na ce masa me? Saurayi na ne dana ci kud'insa kamar hauka shine ya ke min barazana kayi wani abu a kai?"

Tab'e baki tayi ta d'auki hijabi zata saka ta fita Asma'u tace "To ya kike so a yai? A barshi har sai wani abu ya faru marar kyau? Sannan mu sake shiga damuwa da tashin hankali."

Dafa kafad'arta tayi tace "Ba abinda zai faru Asma'u, kwantar da hankalinki."

Ture hannunta tayi tace "Kwantar da hankalin banza, wai me yasa kika cika taurin kai ne Mimi? Haka a baya kike fad'a min kwantar da hankali babu abinda zai faru, da nayi shiru kamar yanda kike buk'ata miye bai faru ba?"

Tsaki tayi tace "Kinga idan wani abu ya faru wallahi babu ruwana ni dai, na fad'a miki d'an giyane mutumin nan kuma yana mana rantse rantse da cin alhwashi."

Gyara tsayuwa tayi tace "D'an giya miye baya fad'a? Rantsuwa ko ruwa zai sha sai yayi rantsuwa da alhwashin shan su alhalin gasu sa gabanshi, dan haka ba zan saka matsalarshi a kai na ba."

Jinjina kai Asma'u tayi cike da jin haushi ta fita tana fad'in "Ke kika sani ai."

Ganin yanda ta fita ya tabbatar mata sunyi fad'a kenan ba zasu shirya ba sai kuma gobe, girgiza kai tayi tana murmushi a ranta take ayyana irin k'aunar da Asma'u ke mata, indai zasuyi fad'a to akan wani abu da Mimi tayi ba daidai bane musamman mai barazanar cutar da ita game da lafiyarta ko kuma zai shafi mutumcinta.


*Sheikh*


Dake a jirgi suka shigo hakan yasa suka zo bayan magriba, tunda yasan yau asabar yasan a lokacin Hafsat tana cikin gidan a b'angaren karatu tare da matan da suke karatun dare, kai tsaye b'angarenshi ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi masallaci, saida sukayi sallah isha'i sukayi karatunsu kafin duk da gajiya kam kafin suka tashi k'arfe tara. Yana shigowa gidan a falo ya sameta tare da Aisha da wata budurwa mai d'inkinsu, gaisheshi tayi da ladabi ya amsa haka ma Aisha kafin ya wuce ciki, mik'ewa tayi a sanyaye ta kalli Aisha tace "Ki duba kayan kiga idan sunyi sai ki bata kud'in, idan akwai wanda bai yi ba saiki bata ta koma dashi a gyara."

Kallon budurwar tayi tace "Dan na sanki da shiririta wani lokacin."

Dariya tayi tace "Insha'Allahu ma anti daidai wannan Mamar Aisha."

"Allah yasa." Ta fad'a tana murmushi ta shige falon yallab'ai, a tausashe a sanyaye ta furta "Assalama alaika sheikh na wa."

Tsura mata ido yayi har ta k'araso sannan yace "Wa'alaiki salam *Manga* ta wa."

Murmushi tayi tare da zama kusanshi tace "Sannu da zuwa uban gidana, an zo lafiya?"

Saida ya d'ora hannu a cikinta yana shafawa yace "Yawwa sannu abokiyata, na sameku lafiya?"

Da fara'a ta amsa da "Lafiya lau muke, ya k'ok'ari?"

Murmushi yayi yace "K'ok'ari muna ta fama da taimakawarku."

Murmushi tayi tace "To yanzu me ye abunyi? Nasan dai mijina sarkin tsafta ne bare nayi tunanin baiyi wanka ba, yanzu abinci zaka ci ko kuma karatu zamu shiga?"

Gyara zama yayi yana kallonta yace "Sanin matata sarauniyar tsafta ce yasa na fara wanka kafin ta sakani dole, abinci kawai za'a taimaka min dashi yanzu dan yunwa nake ji, amma kafin nan a amsa min tambayoyi na."

D'an bud'a idonta tayi sosai tace "To fa! Wane tambayoyi kuma?"

Hannunta ya kamo ya rik'e yace "Hafsy na, yanzu kina ji kina gani da had'in bakinki da yardarki da kuma tallafawarki su Asas zasuyi wani abu wai kamu? Miye ma kamun nan ne? Shin bidi'a ce ko sunna? Me ake yi a wurin? Maza da mata ake tarawa ayi rawa a ci a sha a fita tsirara? Mi ye ma anfanin yin shi kamun?"

Wata ajiyar zuciya ta sauke tace "Da fari dai ba sunna bace zamu iya cewa bidi'a ce tunda al'ada ce aka rik'e gam, na biyu kuma ana tara maza da mata amma wannan iya zallar mata ne insha'Allah, abu na gaba kuma ba zamu saka kid'a ba bare har ta kai ga rawar ma, dan mu ba iyata mukayi ba."

Ta k'arashe tana k'yalk'yalewa da dariya, shi ma yar dariyar yayi yace "Yanzu kenan a matsayinki na ustaza kin bada goyon baya d'ari bisa d'ari akan al'ada marar tushe?"

Marairaicewa tayi tace "Dan Allah ayi hak'uri a barmu, kaga fa har na kai wa amarya kayanta da zata saka a ranar, insha'Allah babu abinda zamuyi da ya sab'a k'aida."

Zura mata ido yayi sakamakon fad'uwar da gabanshi yayi sanda ta ambaci amarya, Ryam! Lallai yarinyar ta koya mishi darasi na rayuwa akan karatun mata, hakan ya cire mishi sha'awar k'ara aure gaba d'aya, ita ce ma dai yake ta koyon yanda zai yakiceta a zuciyarshi, ma wani ikon Allah sai ma k'ara samun muhalli take tana zama, babban tashin hankalin shi ne ko waje ya fita aka kirashi da sunan sheikh ko wani suna na ladabi da girmamawa saiya tuna wacce ta iya kallonshi ta ce Abdul, wasu lokuta sai ya ji kamar ya biya kud'i ayi zaune gabanshi ayi ta kiranshi da Abdul, saidai tasirin ba d'aya bane ko kad'an, gashi lokaci na sake kusantata da d'an uwanshi da zasu zama abokan rayuwa mata da miji, shi kuma zuciyarshi na sake daffaruwa da tunaninta.

Jinjina kai kawai yayi bai ce mata komai ba, hakan ya sata mik'ewa tace "Godiya muke sheikh, bari na kawo maka abinci a nan."

Yana kallo har ta fita a d'akin kafin ya gyara zamanshi yana sauke numfashi, cire babbar rigarshi yayi ya aje tare da hula ya shiga shafa kanshi yana lumshe ido yana tuna abinda ya faru a waccen ranar, abunda yafi tsaya mishi a rai shi ne da likitar tace zata je ta samu mahaifinta suyi magana, da sauri ya bud'a idonshi yaja wani dogon tsaki a zuciyarshi yake fad'in "Me yasa Ryam? Me yasa kika ballagazar da kanki haka? Baki san cewa mutumcinki shi ne darajarki ba? Me yasa kika zama mai arha haka? Kika wofantar da abu mafi daraja?"

Wani tsakin ya kuma ja tare da sake muskutawa ya gyara zamanshi, yana haka Hafsat ta shigo da sallama da babban tire a hannunta d'auke da kwanuka masu kyau na alfarma saΓ― d'aukar ido suke.


*Safiyar lahadi*

Su hud'u suka gama shirinsu har da Asma'u da sukayi fad'a jiya amma an shirya da safe, suna zaune tsakar gidan k'aramar wayar Asma'u tayi kuka, d'auka tayi tana fad'in "Abokin ango barka."

Daga b'angarenshi ya amsa da "Barka k'awar amarya, kun shirya ne?"

"Mun shirya ai ku muke jira." Ta fad'a tana kallon Mimi, daga can ya amsa da "Da gaske? Ko kuma dai maganar yan matan amarya za'a mana."

Cike da tabbaci tace "Da gaske mana, idan baka amince bΓ’ gwada cewa mu fito ka gani, sai mu tabbatar su waye yan matan amarya da abokan ango tsakaninmu."

Dariya yayi yace "Da gaske? To ku fito mu gamu a k'ofar gida."

Saida ta mik'e tsaye suma suka mik'e tace "Kuma ka yarda idan baku k'ofar gida ku zama yan amatan amarya?"

Dariya yayi sosai yace "Anya Asma'u kina son gaskiya? Yanzu so kike ki rabu da abokin namu?"

Ita ma murmushi tayi tace "Ina so ne dai na nuna muku mu ma jarumai ne zamu iya d'aukan duk wani caji da yan matan amarya zasu mana."

Cikin d'aga sauti yace "Iyeeh! Lallai Naanah Asma'u kin iya azanci, amma dai kina da sha'awar siyasa ko? Ko kuma dai a gidanku akwai d'an siyasa."

Dariya tayi sanda suka fito k'ofar gidan tace "Ko kad'an, wayo ne dana fara koya a wajenka."

A lokacin shi ma ya karyo kwanar gidan yana fad'in "To gashi mun iso tare, yanzu kowa sai ya zauna a matsayinshi ko?"

Shiru tayi ba tace komai ba har ya tsayar da motar, sauke glas yayi yana aje wayarshi yace "Sannunku."

Duk amsa mishi sukayi banda Mimi dake lab'e bayan Asma'u tana sunkuyar da kai, murmushi yayi yace "Ina amaryar ta mu? Asma'u ya zaki b'oye mana ita haka?"

Kama hannun Mimi tayi ta bud'e motar ta shiga haka ma su Rauda, har zata shiga Sadeeq yace "A'a ya haka? Ki dawo gaba mana, ko ba kya son hira dani ne?"

Murmushi tayi tace "Ni dai ban fad'a ba."

"Amma ai aikinki ya nuna haka." Ya fad'a yana kallonta tana zagayawa, bud'ewa tayi ta shiga ta zauna kafin ya tayar da motar, a hankali suke tafiya yana jansu da hira irinta yan matan amarya da abokin ango wacce duk rigima ce a cikinta su ja ya ja, da haka har suka isa salon d'in da Asas ya umarceshi ya kai su. Duk ajin Mimi da son k'aryarta saida ta ji ta raina kaita da suka shiga ciki, babban wuri ne katafare daya tsaru ya had'u, ga ma'aikata suna ta aikonsu ga manyan mata na shiga da fice.

Mai saloon d'in ba musulma bace amma tana ganinsu dake tasan su Sadeeq da fara'a ta mik'e ta tarbesu, fita yayi ya barsu bayan ta tabbatar masa ya dawo bayan awa uku. Nan fa ta shiga yi wa Mimi aiki da kan ta su Asma'u kuma yaranta suka kama musu, gyaran kai aka fara musu da wankin k'afa da hannaye, Mimi kuma saida ta shafa mata wani had'i na gyaran fuska tare da rufe mata idonta da kokonbre, minti k'alilan suka rage Sadeeq ya dawo aka kammala musu, dan haka yana zuwa ya damk'a mata kud'i suka tafi suna godiya inda suka ji Sadeeq na fad'in sai jibi idan ya maido su kuma.

Suna dawowa gida ta samu Iya Delu da mama suna hira ta 'ya da uwa, gaisheta duk sukayi sai Mimi da tace "Ni dai ba zan gaisheta ba dan ina daf da shiga gidanki a matsayin kishiyarki."

Duka Iya ta kai mata tana fad'in "Ke kauce can ja'ira, naga inda zaki je d'in ai."

Dariya sukayi suka shiga d'aki sai su Iya da suka ci

Please Login or Register in order to submit comment