Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bare tayi min."

Maganarshi ta k'arshe ce tasa ta jin wani irin duka da k'arfin gaske a zuciyarta, shirun da dukansu sukayi yasa ta jin idonta taf da hawaye, lumshe ido tayi murya na rawa tace "Abdul zuciyata rawa take, bana jin dad'i kaji, ban da lafiya yanzu bacci zanyi."

Shiru yayi yana saurare da karantar yanayin muryarta, a sauk'ak'e yace "Shikenan rik'e waya zan tofa miki addu'a."

Wayar na kunnenta ta ji yana karanta mata addu'ar bacci, yana kammalawa cikin muryar rad'a yace "Saida safe yan matan tsohonta, kiyi bacci lafiya, ina k'aunarki."

K'it! Ya kashe kiran yana k'urawa wayar ido, maganarshi ta k'arshe da maganarta ta k'arshe ya shiga d'orawa a mizani yana san yasan me ya jawo mata rashin lafiyar data fad'a a nan take? Da wannan har ya yi addu'ar bacci ya gyara kwanciyar kafin ya tashi anjima ya gana da mahaliccinsa.

*03:00* daidai goshinsa na k'asa yayi sujada ga ubangiji yana fad'a masa buk'atunsa idonshi na zubar da ruwa, cikin k'ank'anr da kai da kadnaita Allah da mayar da kai ba kowa ba yake kuka yana fad'in "Ya Allah ka gafarta min zunubaina, ni mai laifi ne a gareka Allah ina tuba a duka kurakuraina dana sani da wanda ban sani ba, Allah ka yafe min zunubaina, Allah nagode abisa ni'imominka gareni, Allah nagode da ni'imarka gareni, buwayarka mafi d'aukaka, izzar mulkinka mafi guda, tsarkakar mulkinka wanzanjiya, kyautarka mafi anfanuwa, Allah ina k'ara gode maka. Allah ka shirya min yarana shiri irin na addinin musulunci, Allah ka shirya min kan iyalina su zama mafiya kyawan alak'ar zumunci, Allah ka raya min *Khadija* ka inganta lafiyarta, Allah ka bawa mahaifiyarta lafiyar shayar da ita, Allah ka bata juriya da ikon tarbiyar yaran. Ryam! Allah ka fini sanin sirrin dake cikin tarayyata da ita, bansan komai ba Allah face ilimin daka yarje min na sani a bayyane, ina k'ara neman zab'inka akan lamarina da ita, idan har alkairi ce a gareni Allah ya ka dawwamar da alak'armu tare da saka mana fahimtar junanmu, idan kuma akasin hakane Allah ka gaggauta yin nesa da ita dani da kuma ahalina, Allah na rok'eka da zuciya d'aya inhar Ryam ba alkairina bace duk son da nake mata Allah ka cire min ita a zuciya sannan ka nesanta ta dani da iyalina na har abada. Idan kuma aurena da ita yana nufin koya min darasi akan kalamaina da suke nuna k'yamar mace mai biyar maza ne, Allah gani a gabanka kaina k'asa, ka fini sanin abinda ke cikin zuciyata, idan har tubana na gaskiya ne Allah ka shirya min yarinyar nan ka d'auke idonta da hankalinta daga kowane namiji bayan ni mijinta, Allah na rok'eka inhar tubana na gaskiya Allah ka saka farin ciki a rayuwata data iyalina, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah-alzeem, astagfirullah wa'atubu ilaikh."

D'agowa yayi hawaye na ci gaba da zarya a fuskarshi, sunkuyar da kai yayi tsabar k'ask'antar da kai yana tahiya kafin ya yi add'u'oin bayan tahiya ya sallame, jim ya d'anyi kafin ya d'aga kanshi ya kalli gabanshi, wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke, cikin muryar data sha kuka a shak'e yace "Nayi alk'awari tsakani na da ubangijina, Allah kaine shaidata kan alk'awarin nan da zan d'auka a yanzu, *Ryam ta riga da ta zama matata, nayi alk'awarin tsare mutumcinta da k'arfina, sannan nayi alk'awarin rik'eta abisa gaskiya da amana, nayi alk'awari ba zan tab'a k'yamarta ba saboda laifin data aikata a baya, nayi alk'awarin ba zan gujeta ba haka kuma ba zan tab'a fallasa sirrinta*, Allah na rok'eka idan har wannan nayi shi ne saboda kai ina fatan zan samu sakamako na a wajenka kamar yanda kayi alk'awarin kyakyawan biya ga ma'abota kyauta da kyautatawa."

Wata ajiyar zuciyar ya sake sauke yana jin wata nutsuwa na ratsashi a sanyaye, gyara zama yayi ya tokare k'afarshi d'aya ya fara zikhri da hannayenshi, bai gushe a wurin ba saida wayarshi ta alamta mishi k'arfe 05:00 kafin ya mik'e ya kabbara sallah subh dan a nan ba masallaci zai ji ba.



*Niger*


Masha'Allah kam Mimi dake akwai wayewa da kuma kunya, tuni ta sake a cikin gidan dan kuwa ita da Asma'u da Fanna cousine d'in su Hafsat sukayi girki na rana dana dare, sosai ta saki jikinta saidai bai hanata kama jikinta ba, dan ko abun dariya akayi zata murmusa, aiki dai nai zata mik'e ta taimaka ko ba'a nemeta ba, yamma nayi ita da Asma'u suka gyara falon tsaf sukayi turaren wuta dana tsintsiya dan sun fahimci a fannin tsafta dai kam Hafsat bata da tsara, dan in maganar gaskiya za'ayi to Mimi zata iya cewa gabanta ya girgiza sanda ta shiga d'akinta ta samu ko ina k'al-k'al kamar ba mutum ke rayuwa a nan ba, amma dake ita d'in yar sa kai uku ce sai ta yatsina fuska ta nuna inhar zasu zauna a matsayin kishiyoyi to zata zauna da ita kuma zata iya ita ma.

Sun idar da sallah magriba tana zaune a falon tare da Munzeer da Aswan kasancewar akwai d'akin da aka ware ana shiga ayi sallah, Hafsat ne gefe zaune akan katifa tana waya k'asa k'asa tana murmushi da alama da sheikh suke magana, Mimi kam da bata damu ba ma remonte ne a hannunta tana ta canza tasha (🀣Baiwar Allah mbc take nema), kallon Munzeer tayi dake kan k'afarta tana murmushi tace "D'an tanti, wai ku baku da wasu tasha ne bayan wannan?"

Cikin maganarshi ta yara yace "E aunty, duka wannan ne kawai."

Aswan dake jinsu ne yace "Auntynmu ai idan nishad'i kike so saidai in kin fita mak'wabta."

Harara Hafsat ta cilla mishi daga nesa hakan shi mik'ewa ya fita waje, Mimi kam aje remonte d'in tana ji a ranta ai ba nishad'i babu mbc, fitowar Asma'u yasa ta fad'in "Asma'u mu wuce gida ko?"

Hafsat dake jinsu d'an d'auke wayar tayi a kunne tace "Ku tafi kamar ya? Tun yanzu?"

Cikin jin kunya tace "E aunty, naga dare ya fara ai."

Girgiza kai tayi tace "Ba yanzu ba gaskiya, to ke Mimi me zai hana kiyi zamanki ma kawai tunda gidanki ne?"

Da sauri ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kanta, murmushi Hafsat tayi ta d'ora wayar a kunne, duk da ya ji me take fad'a kuma yaji kamar yace "E hakane Manga, ki matsa mata ta zauna dana dawo ba sai na wahala d'aukota ba."

Amma kuma sai ya nuna kamar ma bai ji ba suka d'ora a inda suka tsaya, fitowar Hajia ne tasa su shiryawa suka d'auki hanyar gida tare da Kabiru dreba.

Suna hanyarsu ta komawa gida Mimi ke fad'in "Wai ita matar nan bata kishina ne? Sai tayi ta abu kamar ba mace ba."

Murmushi Asma'u tayi tace "Hankalin data nuna ne baiyi kama da d'abi'ar mace ba? Ko kuma dai iliminta da take anfani dashi ne ya zama illa?"

Tab'e baki tayi tace "Ke maganar gaskiya idan ni ce ita ko yaya sai nayi kishin mijina, haba ai ko d'an tayar masa da hankali sai nayi ko da nayi masa kuka ne na kwana bakwai."

Dariya Asma'u tayi tace "Ke sarauniyar kuka ba?"

Kallonta tayi dan a take ta tuna mata da shi, rabonta da shi dai tunda safe da zasu zo gidan sukayi waya, a sanyaye ta furta "Ko me yake?"

Sai kula tayi saurin yin k'yaci tace "Ina ruwana ma." Kamar kuwa yasan me take yi yana kuma son k'aryata ta sai kuwa kiran wayarshi ya shigo, tana ganin lambar kuma sai tayi d'an murmushi, dama tun fil'azal kiransa bata gagara d'aukarshi, dan haka yanzu ma da sauri ta d'auka, shiru tayi har saida ya furta "Ina fatan kina cikin aminci?"

D'an satar kallon Asma'u tayi kafin ta matse bakinta tace "Lafiya lau."

Murmushi yayi jin tayi shiru yace "Har kun tafi kenan?"

"Um." Ta fad'a shi ma a tak'aice, ba tare daya gaji ba yace "Me yasa kika k'i zama a gidanki? Kinga fa da ina nan da tun jiya kika tare."

Tsam tayi sai kuma tace "Kamar wata yar beby? Kuma ma ai ni ba yanzu zan tare ba."

A take yace "Sai yaushe kenan?" Cike da lalata tace "Sai na k'ara girma."

Wani malalacin murmushi yayi yace "A gidan Hajia zaki zauna kuma?"

A hankali tace "Me yasa ka tambaya?" A zuciyarshi cewa yayi "Saboda na ji a inda zaki min rainon cikina mana."

A zahiri kuma sai yace "Saboda nasan inda zan dinga aika miki madara."

Yatsina baki tayi tace "Ni bana shan kowace irin madara sai lacstar."

Da wani shak'iyin murmushi a fuskarshi yace "Ni ma ita nake nufi."

A wani d'arare yace "Ryam."

A sanyaye tace "Na'am."

Cikin muryar saukar da kasala yace "Zan sa Hajia ta fara miki shirin tariyarki, ina so ranar da zan dawo garin nan ki tare a d'akinki."

Baki sake tace "Yaushe kenan?"

Cikin muryar rad'a yace "Insha'Allah ina sa ran zamu dawo ranar laraba, dan maganin da aka d'ora Asas talata zai k'are, laraba mu kuma zamu juyo."

Waro ido tayi tace "Ana gobe bikin aunty Hafsat fa kenan?"

Yar dariya yayi yace "Yan matan tsohonta kenan, ban da abinki yarinyar dake cikin kwalba a asibiti ne za'a wa biki? Kuma ni ai a tsarina ba'a min wannan bidi'ar, ana zanawa yaro suna ne ranar da yayi bakwai sai yan uwa da akan gayyata a ci abinci dan godiya ga Allah, sannan a lissafinki ya nuna a al'adance kike lissafi shiyasa kike tunanin ranar alhamis ne sunan."

A girmame ta furta "Tabbd'!" Baya biki fa? To yanzu da yake son ta zauna da shi idan ta haihu shikenan ba zatayi biki ba? Cikin rashin fahimta tace "Yanzu nan shikenan ba za'ayi biki ba ayi shagali? To yaushe ne sunan ya kama?"

Cikin sakin murmushi yace "Ranar laraba, idan kika k'idaya kwanakin zaki ga a ranar ne bakwai."

Shiru tayi ta ma rasa me zata fad'a, jin haka sai kawai yace "Katin dana bar miki na ga har yanzu bakiyi aiki dashi ba, ai ya kamata ke ma ki bawa Khadija wata kyauta ko?"

A sanyaye jiki a mace tace "Zan yi, sai gobe insha'Allah."

Cike da rarrashi yace "Ryam, dan Allah idan zaki tafi karki manta da hijabanki manya da kuma nik'abi kinji, sannan karki jima ki dawo gida ki huta."

"To." Ta fad'a a hankali, da haka sukayi sallama ta aje wayar kan cinya tana kallon Asma'u tare da labarta mata abinda ya faru, dariya Asma'u tayi haka ma Kabiru dake tuk'i murmushi yayi yana jinjina lamarin wannan sabuwar sirika ta gidan yar gayu kuma da alama ma yar casu ne.

Washe gari tsaf suka shirya ita da Asma'u zasu je banki, Hajia dai da addu'a ta rakasu dan tasan da mijinta bai bud'e mata bakin aljihu ba me zai kawo maganar zuwa banki, Kabiru ne ya kaisu kuma basu jima ba dan tana nuna katin wa wani ma'aikaci aka shiga girmamata alamar sani, saida ta d'ibo kud'in sai kuma ta kalli Asma'u ta fashe da dariya tace "To wai me zanyi da kud'in nan ma?"

Tab'e baki Asma'u tayi tace "Kud'i ana rasa abunyi ne dasu dama?"

Rik'e hannunta tayi suka nufi mota tana fad'in "Muje zanyi tunanin abun yi."

Bin ta tayi tana fad'in "Allah yasa dai ba a leshe da atamfa zasu k'are ba."

Dariya tayi tace "A'a zan san me zanyi kedai, ba mijinki zai dawo ba?"

Mota suka shiga Asma'u na fad'in "Me ya shafi kud'inki da shi kuma?"

"Zaki gani kedai." Ta fad'a suna barin wurin, daga nan gidan Hafsat ya ajesu dan yau ma nan zasu wuni, suna zuwa sun samu Hafsat dake zaune tana magana da Salamatu tana fad'in "Baaba Salamatu ki fara d'ora min su na fi so na yi anfani dasu anjima."

Juyawa tayi zata shiga madafa tace "To bari na wanke su sai a d'ora silalarsu."

Da ladabi Mimi tace "Aunty Hafsat me za'a d'ora ne?"

Da fara'a tace "Hanji ne na ke son romonsu, ita kuma da tana so ta fara da girkin rana."

Mik'ewa tayi tana cire zumbulelen hijab d'in tace "Bari na d'ora miki to."

Asma'u ma mik'ewa tayi tana fad'in "Bari ni saina kama ma Salamatu girkin to."

Da jin dad'i tace "Ba kwa gajiya da aiki, to sannunku." Wucewa sukayi madafar suka shiga aiki gadan gadan.

Sanda ta gama silala ganin ta juye ruwan silalar zata zubar yasa Salamatu saurin fad'in "Ke ke! Baki da hankali ne zaki zubar? Ko dai baki san miye silala ba?"

Numfashi ta sauke ko kallonta ba tayi ba ta juye ruwan ta zubar, Asma'u ma kallonta take saidai tasan akwai dalilin da yasa tayi haka, saida ta tsane hanjin kafin a tsanake ta shiga soya miyarta da kayan miya masu yawa, sanda ta gama girkinta tsaf ta zubawa Hafsat a kula mai kyau ta kai mata falo, dawowa tayi ta zuba a k'aramin plate ta bΓ’ wa Salamatu tace "Iya ne sunanki ko Baaba? Ki d'and'ana ki ji kiga kalar dahuwarki ce, a ido kawai zaki tabbatar da banbanci."

Tana fad'a ta fito daga madafar, cikin sakin fuska ta kalli Hafsat tace "Aunty ko na zuba miki ne?"

Da fara'a tace "Da kin barshi ma ai."

Mik'ewa tayi ta d'an zauna bakin katifar ta shiga zuba mata, mik'a mata tayi kafin ta koma kan kujerar, Hafsat na kai lomar hanta bakinta ta kalli Mimi ba tare da bak'in ciki ba tace "Mimi dahuwar nan ta min dad'i, kinga kuwa miyar batayi irin kaurin nan ba wani har kaga yana tayar ma da zuciya."

Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, sosai Hafsat ta ci naman nan kamar zata tsinka harshenta, saida ta kammala tasha ruwa tace "Wannan a ranar da sheikh zai dawo zaki girki masa wannan, dan mutum ne shi mai son miyar hanji sosai."

Dariya ita dai kawai tayi ba tayi magana ba sai a zuciyarta da take fad'in "Sheikh d'inki dai, zaki dafa masa ne yarinya in kuma ba haka ba to yunwa zata kamashi."

Ko da k'arfe 01:00 tayi su Asma'u ma suka gama girkinsu suka cire ma kowa na shi, lokacin Mimi ta shiga sallah a d'akin da aka ware bak'i na sallah Mamanta ta zo gidan yin barka tare da Shapi'a da Sahura.

Asma'u ce ta karb'esu inda Hafsat ma ta shiga girmamasu ta nuna musu murnarta a fili, Mimi na fitowa ta gama sallah ganinsu yasa ta k'arasowa da farin ciki tana fad'in "Mama, aunty."

Tana zuwa bata zauna akan kujera ba k'asan carpet ta zauna tana rik'e hijabin Mama tana fad'in "Mama yanzu kuka shigo? Me yasa baku fad'a min zaku zo ba? Mama ina su Yaseen? Ina Abba na Mama?"

Mama sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ita Mimi ma kunya ta bata sosai, ganin ba zata amsa ta ba yasa ta kallon su Shapi'a tace "Aunty Ina wuninku?"

Da fara'a suka amsa mata suka gaisa sosai, Hafsat ce tace "Mimi ki kawo musu abinci ko?"

Mik'ewa tayi zata tafi su Sahura tace "A'a Mimi barshi, saida mukayi abinci a gidan kafin muka taho."

Duk yanda Mimi ta so matsa musu su ci abincin k'iyawa sukayi saboda dattako, basu fi minti ashirin ba suka mik'e zasu tafi, cikin kukaan shagwab'a ta bi bayansu dan rakiya Mama na fad'in sa ta ci uwata idan tana mata shiriritar nan, saida suka kai farfajiyar Shapi'a ta mik'a mata wani dogon bidon da zuma a ciki tace "Yar albarka karb'i tsaraba kinji ki sha abarki."

Karb'a tayi tana kallon robar Mama tace "To dan hauka ki shiga da shi a haka sai kin nunawa kowa sirrinki."

Dariya tayi murya k'asa k'asa tana fad'in "Wai nan su fa tsuma ni suke saboda tsohon nan, ko me ya fad'a musu zai iya?"

Sahura ce tace "Magana kike?"

Da sauri tace "A'a ban ce komai ba." Rakasu tayi suka fita tana jin kewarsu kamar ta bi su."

Tana dawowa kuma Hafsat da kallon birgewa ta bi ta dan yanda suka mik'e suna tafiya daga yanda take bin bayan iyayenta tana risinawa zai nuna maka tana girmamasu ne bata son ta fi su tsayi.



*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:59 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*39*



Da dare suna komawa gida saida sukayi shirin kwanciya ta samu zumar nan saboda kwad'ayi tayi ta sha duk da ana jin d'and'anon magani, saida ta ji cikinta ya fara k'ullewa kamar zai mata ciwo ta mik'awa Asma'u tace "Sha ke ma."

Murmushi tayi ta karb'a tana fad'in "Sai yanzu kika da damar bani saboda kina so ki nuna min ke babban Alaji gareki."

Duka ta kai mata tana dariya tace "Shegiya Asma'u, ke ni me zaanyi da wannan d'an uwan naku, wanda ya haifi kamata?"

Murmushi ta sake yi tace "Ke dai kika sani."

Har suka kwanta cikinta na k'ulle mata daga baya sai taji har mararta ma wani ciwo ciwo take mata,da haka dai bacci ya d'auketa dan abun ba wani mai tsanani bane.


Kullum hakane ke faruwa Mimi da Asma'u sukan wuni gidan Hafsat ne suna kama aiki, kuma duk da ba taron biki ake ba amma lokacin na matsowa sai aka shiga yin lalle da kitso wasu ma har da d'inki kamar Hafsat da Aisha da sauran yaran.

A gefe guda kuma an gama shirin tariyar Mimi lokaci kawai ake jira, ranar da su aunty Shapi'a suka zo kamar yanda Hajia ta buk'ata dan ganin b'angaren da sheikh ya ware mata da kuma kayan da aka zuba mata bata zo gidan ba sai Asma'u kawai, masha'Allah abun ya birgesu tare da neman zautar dasu, tunaninsu bai wuce yanda yake babban malami ba amma ya daki dukiya haka kamar zatayi kuka, kaya ya mata na kece raini aka cika mata falonta da kuma d'aki biyu.



*Ranar talata*


Cikin tsantsar farin ciki da murmushi d'auke a fuska sheikh ya mik'awa likitan hannu bayan sun gama biyan duk cajin da aka musu yana fad'in "Alhamdulillah, naji dad'i sosai likita, Allah ya saka maka da alkairi, munyi farin ciki sosai."

Shi ma da fara'a yace "Ba komai, wannan aiki na ne dama, d'an uwanka ya samu lafiya kenan."

Kallon Asas sukayi dake ta murmushi shi ma cikin zolaya likitan yace "Idan ka ga yayi ciwon cikin nan mai tsanani, ina tabbatar maka fad'a yayi da madame ta daina kulasa a shinfid'a."

Dariya sukayi shi kuma ya sunkuyar da kai yana murmushi, mik'ewa sukayi suna musabaha kafin sukayi sallama suka fito a ofishin, suna fitowa daga asibitin sheikh ya tari taxi ya kalli Asas yace "Kai kaje masauki ni zan je na ciro mana ticket na komawa gobe insha'Allah."

Zaro ido Asas yayi yace "Da wuri haka? Na warken ma ba zaka barni na d'anyi yawon bud'a ido ba."

Tab'e baki yayi yace "Kana da damar da zaka tsaya bud'a ido amma fa ba tare dani ba."

Murmushin shak'iyanci Asas yayi yace "Sheikh dai na ganoka so kake ka koma wajen matanka ba."

Hararenshi yayi yace "To kaga laifina ne? Mace biyu kamar d'aya ce aka fad'a ma? Sannan karka manta har amarya gareni fa."

Tsuke baki yayi yana shiga taxin yace "Dad'inta dai nima amaryar gareni."

Murmushi kawai yayi shi ya samu wata taxin zuwa filin jirgi dan kam yayi niyya gobe saiya bar k'asar nan dan bayan iyalinshi da yake son had'uwa dasu akwai abubuwa da dama yake so yaje ya d'ora a inda ya tsaya.



*Ranar laraba*


A masallacin aka zanawa Khadija sunanta, sai jibgegiyar sa da aka yanka yan uwa aka shiga sarrafata, duk da ana cewa ba'a biki amma fa dangi an ci kwalliya har mai jego kan ta, sannan mmak'wabta da yan uwa sun cika falo da farfajiya.

Mimi kam tare da Asma'u da su Aisha da Fanna suka je salon aka musu kwalliya, yau kam Fanna duk wayewarta da k'aryar kud'in saita shafawa Mimi lafiya, ba wai kyan da tayi ko tsarin shigarta ba, yanda take kashe tsayuwa ta d'auki hoto su kansu har tana nuna musu yanda zasuyi sai ta jinjina mata. Saida suka gama shirmen hotunansu kafin suka kama aikin da mutane keyi.

*06:00* daidai suka sake gyara shirinsu bayan sunyi wanka Mimi ta sake cab'a kwalliyarta, suna tsaka da shirin Hajia ta shigo d'akin Aisha tana fad'in "Aisho zo mana na aikeki."

Yatsina fuska tayi tace "Kaji tsohuwar nan kuma, ina zaki aikeni."

Dak'uwa ta mata tace "Uwaki, sauri ake mana ki zo, gidan Hajia Kubra zan aikeki ga Kabiru nan na jiranki."

Cikin shagwab'a tace "Hajia Kubra kuma? Ba yaanzu ta tafi daga nan ba."

Dak'uwa ta sake mata tace "Uwaki Aisha, dan Allah ta so mantuwa tayi kuma abu mai mahimmanci."

Mik'ewa tayi tana turo baki tace "Ni faa ko gidan data koma ban sani ba."

Jim ta d'anyi kafin ta kalli Mimi tace "Mimi ai kinsan gidan Hajia Kubra ko?"

D'aga kai tayi a hankali tace "E, amma ban tab'a zuwa ba."

Cikin rarrashi tace "Yawwa yar albarka to tashi rakata dan Allah."

Jinjina kai tayi sai Fanna da ita ma tace "To muje tare ko?"

Kallonta Hajia tayi tace "Ba komai kuje, amma kuyi sauri kafin magriba ku dawo."

Mik'ewa sukayi duk suna gyara mayafensu har Aisha da ba sabonta bane, dan mayafin ma na Fanna ne ta bata ta saka, suna zuwa suka shiga Kabiru ya d'auki hanya da su, hirarsu suke sha sosai har suka isa unguwarsu Mimi a gidan Hajia Kubra, Aisha ce kawai ta fita da ledar a hannunta ta shiga, tana fitowa ba jimawa suka juyo, yanda aka bi ta k'ofar gidansu Mimi yasa Mimi kallon Kabiru tace "Dan Allah Kabiru ka tsaya na shiga na ga gidanmu, wallahi kuka zanyi idan ka wuce."

Tsayawa yayi inda suka shiga mata dariya, dukansu suka fita sai Asma'u da ita ma ta nufi gidansu tana fad'in "Nima bari na ga namu gidan to."

Shigewa duk sukayi saidai Aisha ta bi Asma'u ne Fanna kuma Mimi.

Yanda Mama ke kallonta da mamaki da kuma Abba dake alwala yas ta saurin duk'awa k'asa tace "Abba, mama ina wuninku.

Abba ne yace " Ke uwata daga gidan uban wa kike ana shirin magriba?"

Mama ce tace "Ina ce ma yau ne bikin gidanku? Halan sato hanya kika yi ba wanda ya sani?"

Zunbur Abba ya mik'e yana d'aukar takalminshi da fad'in "Ai kuwa zan ci ubanta a gidan nan, sheikh d'in zaki wa satar hanya?"

Bata motsa daga inda take ba tasa kukan shagwab'a tana rik'o hannun Fanna da ita ma take durk'ushe tana ta kallonsu tace "Wallahi Abba ba satar hanya nayi ba, Hajia ce ta aiko mu gidan Hajia Kubra."

A zabure yace "Wacece hakanan kuma?"

Nuna mishi k'ofa tayi tace "Abba Hajiar data dawo nan gaban gidansu Bello."

Mama ce tace "To kuma sai tace ki zo nan? Yaushe ma aka yi aurenki da zaki zo gidan?"

Cikin tsawa Abba yace "Ke tashi ki koma gidanki."

Sai lokacin Fanna tace "Ina wuninku?"

A tare Abba da Mama suka amsa cikin fara'a, Yaseen ne ya fito daga ban d'aki yana ganinta ya k'araso da murna yana kiran "Mimi ke ce? Lahhh!"

Rik'e hannunshi tayi tace "Yaseen kana lafiya? Shi ne baka jΓ© ka ganni ba ko?"

Dariya yayi yace "Mama ce ta hana, amma zamu je tare da Amir."

Abba ne ya nunota yace "Uwata ki tashi fa ki koma inda kika fito?"

Marairaicewa tayi tace "Abba dan Allah ka barmu muyi sallah magriba to, kaga fa ba kyau fita ana magriba."

Jinjina kai yayi jin an fara kiran sallah yasa shi cewa "To kuyi sauri amma."

Da farin ciki ta mik'e tsaye ta d'auki buta ta mik'awa Fanna, Abba na gama alwala suka fita tare da Yaseen Mimi na fad'in "Yaseen ina Amir?"

"Yana gidan Iya." Ya fad'a yana wucewa, cikin d'aga murya tace "Ka fad'awa Kabiru ya je yayi sallah zamuyi sallah mΓ» ma."

Mama dai kallonta kawai take tana karantar duk yanayinta, ba tace mata k'ala ba har sukayi alwala suka laulaya mayafensu suka kabbara sallah akan tabarmar da Mama ta shinfid'a.

Kamar jira

Please Login or Register in order to submit comment