Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Na ji sauk'i ma."

Da fara'a yace "Masha'Allah, a ci gaba da hak'uri kinji, insha'Allahu zai samu lafiya, dan muna shirin fitar da shi waje."

Jinjina kai tayi cikin girmamawa tace "Allah ya aminta."

"Ameen." Ya fad'a yana d'an satar kallon mutuniyar da tayi tsaye k'erere tana ta sinne kai alamar rashin jin dad'in had'uwa da shi duk ta bayyana a tare da ita, d'auke idonshi yayi ya mayar kan Asma'u da ita ma kan ta ke k'asa yace "K'arasa ciki."

Gyad'a kai tayi da ladabi zata wuce Mimi ma kamar wutsiya ta bi bayanta, cikin dakakkiyar murya yace "Inna Issa."

Kyab'e fuska tayi ta juyo ta kalleshi, wani kallon gargad'i ya mata yace "Zo mana."

Turo bakinta tayi ta kalli Asma'u data shiga tafiya, a hankali ta shiga takowa tana ta turo baki gaba, ba tare daya kula da mutanen dake kai kawo ba ya rik'o hannunta dake waje dan ta saka hannayen hijabin, shi kuma abinda ya b'ata masa rai kenan yanda jan lallenta ya fito sosai kowa na kallo, cikin nutsuwa ya shiga nufa da ita wurin da motocinshi ke pake, jami'an na ganin haka su ma suka bud'e mishi mazauninshi, da hannu ya mata alamar ta fara wucewa. Kallonshi tayi ta fashe da kuka ta girgiza kai alamar a'a, wurga mata ido ya sake yi alamar fa ta shiga, d'aga kanta tayi tare da d'add'age yanda zata hangi Kabiru dan yanda yake tsaye gabanta masha'Allah ya gaje wurin da girman jikinshi da kuma manyan kayan.

Tana hangen Kabiru sai kuwa ta d'aga murya iya k'arfinta cikin kuka tace "Kabiru, ka fad'a ma Hajia an d'aukeni...."

Hararar daya wurga mata yasa ta saurin shiga motar tana sake fashewa da kuka tana ja baya har ta dangane a d'aya murfin k'ofar tana fad'in "Ustaz kayi hak'uri, kaga dai ni wallahi ban yi komai ba, ai ka karb'e wayata tun jiya ko? Kuma na hak'ura ban ce komai ba, dan Allah yanzu kuma me na yi? Kuma kuka hana cin zalin na k'asa, ni dai yanzu kayi..."

Jin an tayar da motocin sanda ya shiga yana kallon zasu bar asibitin yasa ta jujjuyawa, duka motocin guda uku kuma suka bar asibitin, shiru tayi da bakinta ta sinne kan ta da k'ura mata ido ne yayi yana kallo kamar zai cinyeta d'anye.

Tunani ne kala kala ke ta bijiro masa na yanda zai tsawatar mata ta fara gane idan ya ce tayi to kawai tayi ko bata so, zuciyarshi na ta hasaso mishi abubuwa da dama saidai ba d'aya wanda yayi ammana da su. Amma fa k'wala kiran sunan Kabiru da tayi ya masa zafi, a bainin nasi zata fitar da muryarta haka, to wai ko bata da ilimin addini ne? Amma kuma ai tana zuwa islamiyya.

Numfashi ya sauke a ranshi yana fad'in "Watak'ila asarar lokaci ne bata fahimtar komai."

Da sauri ta kalleshi dan abinda ya fad'a ya fito fili, yanda ta kalleshi yasa shi farga da abinda ya aikata, fuska kawai yayi yace "E, ko kina ganewa ne?"

Had'e fuska tayi ta kumburo baki alamar fa ranta ya b'ace, waro idonshi yayi yace "Idan da kina ganewa ai da kin zama mai suturta kanki a cikin gida ma bare idan zaki fita, kinsan kuwa me Allah ya fad'a akan ku mata yanda zaku saka jalbab d'inku?"

Girgiza kai yayi yana sake tausasa murya yace "Ba zaki sani ba, shiyasa nake so na mayar dake islamiyya."

Kawar da kanta tayi tana gunguni tare da fatan ya kaita inda zata sauka ta fad'i abinda ke ranta. K'ofar gidansu Hajia taga motocin sun paka sun tsaya, a hankali cikin nutsuwa ya bud'e b'angarenshi ya fita, mamaki da rashin sanin me ya dawo da ita nan yasa tana kallo har y'a zagayo b'aren da take, bud'e mata k'ofar yayi ya mik'a mata tafin hannunshi yana sakar mata murmushi da fad'in "Yan matan tsohonta muje."

Marairaicewa tayi ka rantse da Allah marainiya ce, k'in mik'a masa hannun tayi ta fita a motar ta rufe da kan ta, gaba ta shiga zata wuce cikin sanyin murya mai kama da rad'a yace "Jirani."

Cak ta tsaya amma bata juyo ba, saida ya tsaya kusa da ita kafin suka k'arasa shiga ciki, bai bi ta kan kowa ba sai wucewa da yayi har d'akin daya zama na ta a yanzun, tana kallo ya d'auki makullin d'an wani fau da fleurs alamar dai yasan inda ake ajewa ko kuma aljanunshi ne suka fad'a mishi, bud'e d'akin yayi tare da mata alama ta shiga, jiki a mace ta shiga kafin shi ma ya shiga maida k'ofar ya rufe.

K'yak'yabta mishi ido ta fara yi wanda suka kawo ruwa dan gani take irin na jiya zai sake mata, jan majina ta faraa yi a dole ita kuka take, cike da rarrashi ta kalleshi sanda yake zama bakin gadon ta shiga fad'in "Bawan Allah, ai dai yau ban maka komai ba? Amma idan akwai laifin dana maka wanda ban sani ba dan Allah ka yafe min, kaga kai babba ne mai halin girma, biye ma yarinya mashiririciya iri na b'ata lokacin ka ne zakayi."

Cike da izza da gadara ya d'ora gwiwar hannayenshi akan cinyoyinshi yana kallonta, a dak'ile cike da d'aure fuska yace "Ina kayan dana kawo miki jiya?"

Da sauri ta nuna wurin kayanta tace "Suna can."

"D'auko." Ya fad'a ba alamar wasa, jiki na rawa ta nufi kayan ta shiga kakkarwar d'aukowa, tana zuwa ta zube gabanshi tare da durk'usawa tace "Gasu."

D'an d'aga hannayenshi yayi daga tangalewar daya musu ya kalleta da kyau yace "Ryam."

Tarr! Ita ma ta sauke nata idon cikin nashi, a ladabce ta amsa da "Na'am."

A sanyaye ya shiga fad'in "Mutum ne ni dake da tsari a rayuwa, ina so idan na ce wa mutum yayi to yayi abun nan ba tare da nayi maimaici ba, kamar yanda kika fad'a ni babba ne ke kuma yarinya mashiririciya, Ryam na fahimci kanki yana rawa sosai, hankalinki ba wuri d'aya yake ba, sannan nutsuwarki bata tare da ke. Abu d'aya nake so ki sani shi ne idan na baki uamrni kawai ki bi, kin fahimta?"

Samun kanta tayi da kallon cikin idonshi tare da furta "Ko da umarnin ya sab'awa ubangiji?"

Yanda ya kalleta yasa ta sunkuyar da kai, cikin muryar shan k'amshi yace "Bana fatan na umarci wanda ke k'asa dani da sab'awa mahaliccina."

Numfashi ya sauke yace "Yanzu d'auki hijab d'in nan ki saka, dan wannan na jikinki ba hijabi bane shirme ne da hauka."

Da sauri ta kalleshi ta bud'e baki irin mamakin nan, sai kuma ta jinjina kai ta mik'e, d'aukar d'aya daga cikin hijaban tayi ta cire wannan ta saka, yanda ya sauka k'asa ya rufe mata k'afafu ne yasa ta kallonshi tace "Abdul amma wannan hijabin na mamansu Aisha ne ka d'auko min ko? Dubeshi fa sharb'eb'e ya zanyi tafiy..."

Shiru tayi dan ashe kallonta yake tana maganar nan, mik'ewa yayi tsaye tare da figota da k'arfi ta fad'a kan shi, lab'e fuska tayi alamar zatayi kuka tayi k'asa da kanta, cikin tsatsareta da ido yace "Maimaita na ji."

Rarraba ido tayi tana d'an jan majina a hancinta sakamakon yanda k'amshin turarenshi ke shiga hancin na ta, cikin rawar murya tace "Mmm..ee?"

Ba tare daya d'auke idonshi a kan ta ba ya saka yatsanshi manuniya ya shiga zagaya labb'enta yana fad'in "Abdul mana, maimaita na ji."

Wasu yawu ta had'e masu nauyi tana kakkauce fuskarta tace "Kus...kure.. ne."

Tallabo hab'arta yayi yana son tilastata ta kalleshi, duk da fuskarta suna kallon juna ne amma idonta k'irjinshi suke kallo sai kuma hawaye masu d'umin gaske da suka shiga kwaranyo mata, cikin tattausan murya yace "Ni kuma kuskuren na ki nake so, sake fad'a naji."

Idonta rufe ta girgiza kai alamar a'a, ba tare da shi kan shi yasan yayi ba y'a marairaice yace "Dan Allah Ryam, sake fad'an Abdul na ji."

Rintse idonta ta sake yi gaba d'aya take ji kamar an zare mata rai dan ta kasa motsi, labb'enta ne suka shiga hard'ewa tana fad'in "Aaaaabbbbdulll."

Murmushin gefen labb'a yayi tare da jan dogon hancinta yace "Mai tsiwar tsiya."

Sakinta yayi yana fad'in "D'aura nikab d'in."

Sharb'ar majina tayi irin shmmmmm! D'in nan kafin ya d'auki nikab d'in, d'orawa tayi zata d'aura sai kuma wata zuciyar tace "Kenan ma yin abinda yace kiyi zakiyi ?"

Sai kawai ta d'aura ta ba daidai ba ta fito da ido da hanci duk waje, wani k'ayataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, matsawa yayi daf da ita yana kallon k'wayar idonta yace "Wato dai ni za'a ma wayo ko? Kin manta sanda aka haifeki ina daf da haifo kamarki ni ma."

Cike da sangarta da sub'utar baki tace "Ai mamanmu ma ka girmeta."

Sake bud'e idonshi yayi fes a kan ta yace "Inji wa?"

K'asa tayi da idonta tana turo baki, hannu ya kai tare da kunce d'aurin da tayi, a tsanake kamar yanda yasha ganin Hafsat na yi ya d'aura mata, cas kuwa ya fito mata da idonta biyu tare da kallonta ya saki murmushi yace "Daga yau haka nale son ganinki, ya kamata kisan cewa ke yanzu matata ce, akwai buk'atar shigarki ta nuna kamala, nutsuwa, tarbiyya da kuma ilimi, kin fahimta?"

K'ala ba tace ba hakan yasa shi zaro mata ido yace "Ryam..."

"To." Ta fad'a tana kawar da kan ta, hannu yasa ya d'aga nikab d'in yasa yatsu biyu ya cabki leb'enta na k'asa kamar yanda ya mata shekaran jiya, wata k'walla ta matso cike da azaba tana rintse idonta sosai, ba alamar wasa a tare da shi yace "Muryarki, fuskarki, surarki, mutuncinki, duk mallakina ne a yanzu, kuma ina matuk'ar kishin wani ya hangi inuwar gonata, kada ki sake min d'anyan kan da kika min d'azu wajen kiran sunan Kabir, idan kika sake kuma wallahi kinji na rantse saina taune bakinki."

Cikin wahala taa jinjina kai alamar to, sakin leb'en nata yayi tare da shigewa gaba yace "Saki nikab d'inki ki biyo bayana."

Hannu d'aya ta d'ora a kai ta fashe da kukan da babu sauti tace "Wayyo Allah na ni Maryam, wannan ita ce jarabar da nake gudu ta auren tsoho, sam bai san miye soyayya ba bare ya nuna min, sai wasu dokoki da sharud'ai kawai yake gindaya min, yanzu ni gidan uban wa zan kai wannan hijab?"

K'wank'wasa k'ofar da yayi yasa ta zabura ta juya, tsaye yake yana jiranta da sauri ta fita a d'akin ya rufe kafin suka fita, da kanshi ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe kafin ya shiga shi ma suka sake d'aukar hanyar asibiti.

Shirun daya ratsa motar yasa Mimi sauke numfashi a hankali, d'an kallonshi tayi da idonta dake waje cikin sanyin murya tace "Ni fa ba jahila bace, kuma Abbana ba a banza yake biya min kud'in laraba ba, ina da ilimin addini daidai gwargwado, karambani ne kawai da bud'ewar ido na 'ya'yan yau da aka haifemu ba'a haifi halinmu ba, iyayena a tsaye suke kan tarbiyata, ni ce kawai nake ja musu zagi da zund'e, amma na tabbata duk wanda ya zageni iyayensa ya zaga, dan ni ban yi wa iyayena rainin da har zanyi cacar bakin da zata kaini ga zaginsu ba."

Duk da maganarshi ta so tsaya mishi sai yayi gaggawar kawar da ita a rai ya d'an tab'e baki yace "Kin tabbata ba asara ake yi ba?"

Kallonshi tayi rai b'ace tana sako hawaye tace "E, na tabbata."

Wani shak'iyin murmushi yayi yace "A Alk'ur'ani mai girma Allah yana fad'awa manzonsa cewa " Qumi-llaila illa k'alila, (suratul muzammil, aya ta 2) me ye fassarar hakan?"

Kallonshi tayi tana malalacin murmushi tace "Ka tsaya a kowane dare sai kad'an kawai."

D'orawa yayi da "A wata ayar yana cewa, Yah ayyuha-llazina amanu qu anfusakum wa'ahalikum nara'waquduha-nasu walhijara,alaiha mala'ikatun gilazun, shidadun-laya-asunallaha ma'amarahum wayaf-aluna ma'yu'umarun (suratul tahrim, aya ta 5)."

Ba tare data daina kallonshi ba dan mamakinshi take a yanzu kam tace "Yah ku wad'anda sukayi imani, ku kare kawunanku da iyalenku daga shiga wuta-wacce mutane da duwatsu ce makamashinta'a cikinta kuma mala'iku ne masu tsananin k'arfi da basa sab'a umarnin Allah kuma suna yin abinda aka umarcesu."

Ba tare daya kalli sashen da take ba yace "A wata ayar cewa ake, Wa'iza sa'alaka ibadi anni'fainni qarib-ujibu da'awati-da'i iza'da'an, falyastajibuli-walyu'uminubi-la'alahum yarshudun (suratul baqara aya ta 185)."

A kaikaice ita ma ta amsa da "Idan bayina suka tambayeka a game dani ka fad'a musu ina kusa da su, ina amsa rok'on mai rok'o a a sanda ya rok'eni, ku rok'eni kuyi imani dani i..."

Kallon daya mata da sauri yasa tayi shiru tana d'auke kallonta daga kanshi gaba d'aya, sake d'auke idonshi yayi yana jin zuciyarshi na wani daka da k'arfi k'arfi, cikin k'arfin hali da son rikitata ya fita a b'angaren Alqur'ani ya koma hadisi ta hanyar fad'in "Fawallahu lazi-la'ilaha gairuhu, ina ahadakum-laya'amaluahalin-janna hatta'mayakunu bainahu-wabainaha illa'zira'un, fayasbik'u'alaihul kitab faya'amalu ahalin'nar fayadakulaha..."

Kallonshi Mimi tayi a ranta tana fad'in "Wato ita zai wa wannan jirgen?"

Cije leb'en k'asa tayi kafin tace "Hadisi na 4 mai taken ahwalul insan, Abi Abdul-Rahaman Abdullahi bin Mas'ud ne Allah ya yarda dashi ne yake fad'a, fassarar kuma ita ce na rantse da Allahn da babu wani bayan shi, lallai d'ayanku yana aikata aiki irin na yan aljanna harsai ya kasance tsakaninshi da ita saura zira'i d'aya, sai a rufe littafinshi sai ya dinga aikata aiki irin na yan wuta, kuma sai ya shigeta...Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi."

Kallonta yayi cike da gatse yace "Wane hadisi ne a gaban wannan?"

Murmushi tayi tace "A wane littafin hadisin???"

Yanda ta gama harbo jirginshi yasa shi saurin kallonta da ido cirrr kamar zai had'eta, d'auke idonta tayi daga kanshi tace "Idan a matin-l'1arba'una nawwiya fi ahadisin-lsahiha nabbawiy, hadisi na 6 shi ne hani akan bidi'a,, wanda uwar muminai uwar Abdullah A'ishata Allah ya k'ara yarda a gareta tace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace "Duk wanda ya zo mana da wani abu cikin lamarinmu ba'a cikinmu ba to mun mayar mishi" Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi, a cikin wata rawaya ta muslim kuma yace "Wanda ya aikata wani aiki ba'a cikin lamarinmu ba to mun mayar mishi."

Wani nauyayyen numfashi ya sauke a sirrince yana jin abun wani iri kamar mafarki, to dama tana da sani haka take sanin ne tayi take tsula tsiyarta? Kafin ya samu gamsashiyar amsa dreban ya kutsa hancin motar cikin asibiti, a inda motocin suke da farko yanzu ma aka paka, yana shirin bud'ewa tayi saurin cewa "Abinda nake yi ai baiyi kama dana jahilai ba, kuma bai aikata abunda ya sab'awa shari'a ba bare har kayi tunanin rashin ilimi ne ya jawo hakan."

Saida ta bud'e motar zata fita ta sake kallonshi tace "Yana daga cikin kyautata musuluncin mutum ya bar shiga abinda bai shafeshi ba, hadisi ne ingantaccen, idan ka manta ka tuna hakan."

Ficewa tayi ta shiga takawa da sauri tare da d'age nikab d'in ta kwanceta gaba d'aya har ta shige duk da bata san d'akin da zata shiga ba, tana shiga ta corridor suka had'e da Alhaji Saleh ya fito zai tafi, gaisheshi tayi har k'asa ya amsa da fara'a ya nuna mata d'akin, wucewa tayi da sallama aka amsa da bata izinin shiga, a hankali ta bud'a k'ofar tana mai sauke idonta akan Hajia, k'arasa shiga tayi daga Asma'u sai Hajia sai kuma wata matashiya da bata san ta ba tare da Aisha da kayan makaranta a jikinta.

Da fara'a Hajia tace "Mimi sai yanzu? Nayi taa jiran shigowarki ai."

Murmushi tayi tana sunne kan ta, Asma'u ma murmushi tayi tace "Da alama gida ta koma ta canza hijabi."

D'aga kai Mimi tayi ta kalleta tare da satar kallon Asas dake kwance yana bacci, d'auke kallonta tayi daga kan shi ta kalli Aisha dake fad'in "Aunty Mimi ina kwana?"

Da sakin fuska cike da jin kunya tace "Aisha sannu."

"Yawwa." Ta fad'a da fara'a, d'ayar ce tace "Ina kwana aunty."

A sanyaye tace "Muna lafiya?"

"Lafiya lau." Ta fad'a da sakin fuska ita ma, Hajia ce tace "Mai aikin gidanku ce ai, Hafsat take kama ma aiki."

Sunkuyar da kai tayi a ranta tana fad'in "Gidan mu dai, ni ba zan zauna da tsohon nan ba, d'an rainin wayo ne."

Yanda tayi maganar a zuciyarta yasa har bakinta saida ya motsa, mik'ewa su Aisha sukayi tana fad'in "Hajia ni zan wuce makaranta dreba na jirana a waje."

Tab'e baki Hajia tayi tace "To Umma ta gaida Aisha mana."

Kallonta Aisha tayi tace "Kuma dan kin samu ma na miki magana?"

"Kar ki min mana." Ta fad'a tana d'auke kai, murmushi tayi tace "Nasan me ye matsalarki, idan na dawo zamu zauna dake Hajia."

Zasu fita shi kuma ya bud'o k'ofar da waya a hannunshi, juyawar da tayi yasa suka fara had'a idonsu, da sauri ta janye nata gabanta na fad'uwa da sauri sauri, takawa tayi ta koma bayan Hajia ta lab'e tare da yaye hijabin ta baya ta d'orashi akan kafad'unta, hakan yasa bayanta ya bayyana a waje.

A sanyaye ta ji yace wa Aisha "Har yanzu baki tafi ba?"

Da ladabi kanta a k'asa tace "Abie Amie ce ta aikoni tare da Assia muka kawowa su Hajia abinci."

Lumshe ido yayi tare da kaucewa a k'ofar suka fita, k'arasa shigowa yayi yana kallon yanda ta yaye hijabin, wato har tayi halin? Girgiza kai yayi ya kalli Hajia dake fad'in "Hajiarmu, mun gama shirin tafiya komai da komai, insha'Allah yau da k'arfe 08:00 na dare jirginmu zai tashi."

Kallonshi tayi da mamaki tace "Yau kuma? Da wuri haka?"

Lumshe ido kawai yayi alamar eh, jinjina kai tayi daan ta fahimci ya gama kenan, a sanyaye tace "To da wa zaku tafi?"

A dak'ile yace "Ni, da kuma shi."

Nan ma jinjina kai tayi ba tace komai ba, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya, kallon Mimi yayi da ita ma ta kalleshi ganin ya tsaya, nunota yayi da yatsa yace "...



_Nasan kunsan da gani posting da wuri ya nuna komai ya tafi zan-zan, hak'ik'a comment k'arfin gwiwa ne da kuzari😁 dan gashi allurarku ta sokeni da kyau, a ci gaba da gashi._



*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:58 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*35*


Nunota yayi da yatsa yace " *Maamah* wallahi idan baki gyara hijabin nan ba saina ajeta hulata gefe na miki abinda baki tsammani."

Wani bazawarin murmushi ta saki tare da yin durk'ushe bayan kujerar Hajia tana fad'in "Hajia ai kinsan tun ina yarinya bana son zafi, shiyasa Mamana ma a waje take min shinfid'a ina kwana, wannan hijabin zai iya kasheni saboda girmansa yayi yawa."

Hajia daketa rik'e dariyarta rufe baki tayi da tafin hannu, Asma'u kam kallonta tayi tace "Yaushe haka ta fara faruwa?"

K'wafa sheikh yayi ya juya zai fita Mimi dake hararan Asma'u ta sake fad'in "Sheikh baka bani wayata da ka ce ba."

Da sauri ya juyo jin ta kimkima wata k'aryar, kallonta ya shiga yi irin mai nuna "Ke Mimi dan Allah zo ki kasheni ki huta."

Jinjina kai yayi yasa hannu aljihu ya ciro wayar dan dama tana tare dashi, mik'a mata yayi yace "Gashi."

Karb'a tayi tana washe baki har kunne, juyawa yayi ya fita da sauri ta zagaya kusan Asma'u ta zauna tana bud'e wayar, abubuwan data fi damuwa da su ta fara dubawa, saidai mummunan gani tayi dan komai ya shafe hotunanta da girki kawai ta gani, sannan an yi dΓ©sinstaller WhastApp d'inta alamar ba'a son ta dashi, gumtse baki tayi ta kalli Asma'u kamar zata kifa mata mari tsabar takaici.

Zuwa k'arfe 10:20 aka sallamesu a asibitin, har gida suka rakasu saidai daga cikin mota Hajia ta musu sallama ban da Mimi dake kunyar had'a ido da Asas, dan shima kunyarta yake ji fiye da yanda ita take jin kunyar shi ma, suna shiga gidansu su kuma dreba ya wuce dasu gida.



*07:00*

Cike da son danne kewarta ko na ce buk'atuwar mace ya sake matseta a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, tun ranar da ifiritiyar yarinyar can ta tashi boma-bomanshi sun kasa kwantawa, dan ya fahimci Hafsat bata jin dad'i sosai, dan haka bai ma nuna mata buk'atar hakan ba, lumshe ido yayi yana sake jin komai na dad'a mik'e mishi tsaye cikin muryar dake nunawa duk mai hankali halin da mamallakin muryar yake ciki ya shiga rad'a mata "Zzzanyi...kewarki manga na, ki kula min da kanki."

Sake d'an rumgumeshi tayi ita ma tana yatsina fuska saboda rik'ewar da bayanta keyi tace "Insha'Allah, ka kula min da kanka kai ma, Allah ya tsare mana ku ya kareku."

Kasa amsa mata yayi sai wuyanta daya shiga shinshinawa yana goga mata gemunshi a kafad'a, cije leb'e tayi tana rintse ido dan sosai take da buk'atar zama, hannu tasa ta dafe cikinta da sauri ya d'ago ya kalleta yace "Lafiya?"

Murmushi ta sakar masa tace "Ba komai." Da alamar tuhuma yace "Kin tabbata?"

Jinjina kai tayi, ajiyar zuciya ya sauke yana rik'e da hannayenta yace "Ki tayamu da addu'a muje a sa'a da fatan dacewa, idan kika ji jikin nan ya matsa miki dan Allah kiyi k'ok'ari ki kai min kanki asibiti, Hafsa ba'a son zaman nan naki a wannan halin."

Jinjina kai tayi tace "Insha'Allahu zan je."

Jinjina kai yayi shi ma yace "A d'aki na aje miki katin banki na gida, sannan akwai makulin mota guda biyu na bar miki wanda zaki iya buk'ata."

Murmushi tayi tace "Allah ya saka da alkairi, zanyi kewarka."

Sake rumgumeta yayi tare da manna mata sumba yace "Nima haka."

Sakin juna sukayi a hankali yana rik'e da hannunta suka fito falon, yaran suka samu suna tilawar karatu, duk mik'ewa sukayi suna binshi da addu'a, shafa kawunansu yayi dukansu ya sumbaci goshinsu har Aisha kafin ya musu addu'a ya fita zuciyarshi cike da kewar iyalinshi musamman ma matarshi da yake matuk'ar tausaya mata.


*Asa-Ma'u*


Fashewa tayi da kuka duk da bai fad'a mata kalmar so ba, amma dai yanda ya nuna mata jin dad'inshi da godiya akan martaba da kimarta data kawo masa, had'e da jinjina mata akan irin bajintar da tayi a darensu, madadin ace yana kula da ita sai ya zama ita ce ta kula dashi har ta kasa bacci a wannan daren saboda halin da yake ciki. Ganin yayi rarrashin amma ta k'i yin shiru yasa shi aje jakarshi k'asa yace "Shikenan to tunda ba kya son tafiyar, bari na kira sheikh saina fad'a masa kawai na fasa tafiyar saboda ba kya so, kinga sai na zauna a gidan tare dake, amma fa kiyi hak'uri dan kullum zan dinga suma miki a guda."

Da sauri ta rik'e wayar da yake k'ok'arin cirowa aljihu tana fad'in "A'a baan ce ba."

Kallonta yayi ya sauke numfashi yace "To me kika ce yanzu?"

Sunkuyar da kai tayi tana share hawaye tace "Ka tafi Allah ya bada sa'a, Allah ya baka lafiya kamar kowa."

Tallabo hab'arta yayi tare da fad'in "Sannan na dawo miki gida mu d'ora shagalinmu daga inda muka tsaya."

Duk'ar da kai tayi cike da kunya tana Murmushi da sauri ya tallabota ta fad'a jikinshi, rumgumeta yayi sosai yana furta "Na fad'a miki wata magana."

A k'asan mak'oshi tace "Um." Sake matseta yayi yace "Zaki yarda dani idan na fad'a miki?"

"Um." Ta sake fad'a a sanyaye, cike da k'warin gwiwa yace "Ina sonki a zuciyata *Husna*."

Da sauri ta d'ago kanta daga k'irjinshi tana kallon fuskarshi, kamar wanda aka ce mishi zata hango burbushin sauran son Mimi da har yaanzu ke zuciyarshi sai kawai ya sunkuyar da idonshi k'asa, sautin murmushinta ne yasa shi kuma kallonta, cikin raha tace "Kamar ba gaske ba."

Da alamar tuhuma yace "Kenan baki yarda ba?"

Girgiza kai tayi tace "Na yarda mana, kawai dai ina ji ne kamar a mafarki."

Murmushi yayi yace "To ba mafarki bane, zahiri ne wannan."

Murmushi tayi mai k'ayatarwa tare da gyara zaman hijab d'inta, rik'e hannunta yayi yace "Muje dreba na jiranmu a waje."

Jinjina kai tayi tare da bin shi

Please Login or Register in order to submit comment