Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'ora a k'irjinshi ya k'amk'ameta, numfashi mai zafi ya shiga saukewa a saman kan ta daya dunk'ule sosai ya cukurkud'e saboda rashin gyara dan halin da take ciki ya fi k'arfin wasa, yanda zuciyarshi ke suka tana k'onewa, tausayinta na ratsa duk wata gab'a ta jikinshi sai ya ji idonshi sun cika taf da k'walla, a hankali ya lumshe idonshi sai kuwa hawayen suka sauko a kumatunshi, hakan yasa shi k'ara rintse ido ya furta "Ya isa haka Ryam, baki min komai ba kinji, na yafe, na yafe miki, ni ma ki yafe min dan Allah, duk ni ne silar shigarki wannan halin, ki yafe min dan Allah."

D'ago kan ta tayi suka kalli juna tana zaro ido tayi saurin saka hannunta ta share mishi hawayen tana fad'in "Lahhhhh! Sheikh? Kuka kuma? Haba dai, sai ka karya min zuciyata ai."

Sake kwantawa tayi a k'irjinshi tayi luf tana fad'in "Ni ma baka min komai ba, kawai ka tayani da addu'a na sauka lafiya."

Yana k'ara k'amk'ameta shi ma yace "Ina ta miki addu'a Ryam d'ina, tunda kika samu cikin nan nake miki addu'ar sauka lafiya, insha'Allah zaki haihu lafiya."

Shiru sukayi babu wanda ya sake magana saida ya ji tana sauke numfashi a hankali a hankali alamar bacci, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinshi ya gyara mata kwanciyarta, d'aukar k'afafunta yayi da suka zama sumtuma sumtuma ya d'ora a kujerar, tsaye yayi yana k'are mata kallo yanda ta sauya kamar ba ita ba, tayi fuyau da ita alamar babu jini a jikinta, babbar damuwarshi da tashin hankalinshi da suka jawo masa rage walwala da cin abinci bai wuce yanda Rakiya ta fad'a masa wai jinin Mimi ya hau a awon ta na satin daya wuce, jinin Mimi ya hau kamar ya? Me ya kawo mata hawan jini? Ga matsalar rashin jini ga ta rashin cin abinci ga kuma kumbura da kullum k'afafunta ke k'arawa, ga nauyi da take jajen jikinta na dad'a yi mata kullum, hatta da alwala fa yanzu indai yana gidan sai ya taimaka mata, akwai ranar da taimama ya ce tayi dan shi baya gida kuma ta kasa ta shi a inda take ga lokacin sallah n wuce kawai yace tayi taimama a waya.

Madarar ya d'auke ya kai fridge kafin ya rufo mata k'ofar da makulli saboda ko Munzeer ba zai so ya tasheta ba, dan baccin kan shi ba samu take yi da dare ba, sauk'inta d'aya da Hafsat ta d'auke mata aikin gidan.


*09:20*


Sai wannan lokacin kad'ai Allah ya sauke mama lafiya ta samu 'yarta mace, sanda sheikh ya samu labari saida yaje asibitin, kuma bayan ya je gida ya fad'a ma su Hafsat suka ce zasu tafi, haka ya kaisu duk da dare yayi kuma har da Mimi dake fama da ciwon k'afafu.

Da suka je Iya na ganinta ta shiga bin ta da addu'ar sauka lafiya, dan tana ganinta tasan ita ma lokaci ya kusa, sun jima asibitin suna ta hira ana dariya kafin suka bar asibitin.


Kwana biyu da haihuwar Mama sheikh ya bawa Mimi kud'i yace ta yi wa iyayenta bajintar da zata birgesu, saida ta shawarci Hafsat ta bata shawara kafin ta raba kud'in uku kamar yanda ta ce, kaso d'aya a cikin uku ta ba wa aunty Sahura tace su yi siyayyar kayan cefanai na ranar suna, kaso biyu kuma ta bawa Abba tace yayi hidimar gabanshi, sai ga Abba na neman yin kuka da hawaye dan a lokacin ba wai sheikh ba daya masa kyauta data zautar d shi, Asas kan shi saida ya d'auke masa nauyin ragon suna da wasu abubuwan dayawa, gashi kuma 'yar Mimin sa ita ma ta kai lokacin da zata iya tallafawa rayuwarsa, sai kawai ya nemi fshewa da kuka, da k'yar Mimi ta dakatar da shi daga barin hakan.



*Alhamdulillah*
8/6/21, 8:03 AM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*59*



A nauyaye ta tashi zaune tana furta "Hasbunallahu wani'mal wakil, hasbunallahu wani'imal wakil."

Gefenta ta zura hannu ta kunna siririn haske ta shiga rarumar wayarta dan kiran sheikh dake d'akin Hafsat yau, saidai wata zungura da aka mata a ciki tasa ta dafe mararta ta rintse ido tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Sheikh, Abdul, aouch!"

Zuro k'afafunta tayi da k'yar ta sauko a gadon tana sake kai hannu zata d'auki wayarta, wani irin ciwo ne marar misaltuwa bayanta ke yi da ba zata iya kwatantashi da komai ba, tana mik'ewa tsaye tayi saurin durk'ushewa tana sakin k'ara da fad'in "Wayyo bayanaaaaa! Wayyo Allahna."

Durk'ushewa tayi sosai k'asan gadon ta shiga cakumar darar dake kan gadon tana girgiza kan ta, wata zufa ce ta shiga tsatsafo mata tana ta sauke numfashi tana cika bakinta da iska.

Tun k'ararta ta farko ta sauka kan Hafsat dake zaune kan gado tana karatun Qura'ani, da sauri ta zabura tana kallonshi ta sauko daga kan gadon tana waiwaya wa inda zata ga hijabinta, tana d'aukar hijabin zata fita sheikh ma dake tsaye yana sallah ya kalleta yace "Ina zaki je?"

A rikice tace "Mimi, ihun Mimi ne, ina ga fa nak'uda take."

Juyawa tayi shi ma da sauri har doguwar rigarshi na nad'e mishi k'afa kamar zai kifa ya fad'i, saidai bud'a k'ofar da Hafsat tayi ya farkar da Khadija da yanzun ta saba kwana da ita kuma bata rabuwa da mahaifiyarta, fashewa tayi da kuka hakan yasa Sheikh saurin dawowa gareta ya d'auketa cak ya fita da ita hankali tashe.

Suna shiga suka sameta durk'ushe kan gadon ta fita hayyacinta ta canza kala, a rikice Hafsat tace mi shi "Nak'uda take, muyi gaggawar kai ta asibiti gaskiya."

Aje Khadija yayi kan gadon Mimi yace "Taimaka mata ta canza kayan jikinta to."

Da sauri Hafsar ta nufi inda kayan Mimi suke ta bud'a ta shiga duba mata riga da zane simple, sheikh daya durk'usa kusanta gashinta ya shiga gyara mata cike da tausayi yana fad'in "Sannun kinji Ryam, zamu tafi asibiti yanzu, komai zaiyi...haaaa"

Wani yunk'uri yayi ba tare daya ankara ba sanda ta shak'o wuyan rigarshi ta had'a goshinsu wuri d'aya, huci ta shiga saukewa tana fad'in "Zan mutu, zan mutu, sheikh mutuwa zan yi, Abdul bayana, bayana ciwo yake..."

Cikin dubara ya zura hannunshi ya b'amb'are na ta hannun a wuyanshi yace "Ba zaki mutu ba, insha'Allah zai bari kinji ko, kiyi ta addu'a."

Da sauri Hafsat ta dawo kusansu ta shiga k'ok'arin kamata ta mik'e tsaye, sheikh ma kamata yayi suka mik'ar da ita tsaye, kayan Hafsat ta mik'a mi shi tace "Ka taimaka mata ta canza wnnan, bari na dubo kayanta da aka siyo."

Karb'a yayi yana jinjina kai, juyawa Hafsat tayi ta fita a d'akin zuwan d'akin da aka ware na zuba mata kayan haihuwa har abinda yaro zai buk'ata, zare mata rigar baccin yayi ya saka mata wanda Hafsat d'in ta bashi, a hankali ya shiga jan ta zuwa fita a d'akin yana fad'in "Muje to."

Shigowa Hafsat tayi ta kalleshi da mamaki tace "A'a, hijabinta fa."

Sakin hannun Mimi yayi ya juya dan d'auko mata hijabin Mimi ta matse hannunshi gam gam ta durk'ushe tana fashewa da kuka da fad'in "La'ilaha illalahu Muhammad rasulillahi sallalahu alaihi wasallam! Wayyo Allah na bayana, bayana wallahi zai tsage."

Da sauri ya tallabota ya kalli Hafsat yace "D'auko mata hijabin dan Allah."

Da sauri ta nufi kayan na ta ta d'auko mata suka saka mata kafin suka fita, sai gashi yau sheikh da indai yana tare da matanshi bai cika barin ana tuk'ashi ba amma yau duka matan dole ya bari dreba ya jasu, dan kuwa Mimi ta rik'e rigarshi gam ta k'i saki, a haka har suka isa asibitin yana godiya ga Allah da yasa ba shadda ce jikinshi ba da tayi biji-biji a jikinshi, dan ba laifi fa yasha matsa daga gida zuwa asibitin nan, dan har akaifu take luma mi shi a cinyoyinshi ko kuma ta dinga bubbuga cinyarshi tana sallalami da salati.

A gaggauce aka shiga da ita d'akin haihuwa inda Rakiya ce ta jagoranci tsayuwa a kan ta, saidai tabbatarwa da tayi Mimi ba zata iya ba yasa ta fitowa ta shiga ofishinta ta cike takardar daya kamata sannan ta fito wurin sheikh dan bΓ’ shi ya saka hannu, suna zaune shi da Hafsat dake goye da Khadija sun buga tagumi, dan Hafsat d'in ce tace kar suyi gaggawar sanar ma gida tukuna su ji me ake ciki, zunbur ya mik'e yana kallonta yace "Ya ake ciki Rakiya? Ta haihu ne?"

A sanyaye ta sauke numfashi ta girgiza kai tace "A gaskiya sheikh Mimi ba zata iya haihuwa da kan ta ba, kwal d'inta k'arami sosai kuma gaskiya abinda ke cikinta ba k'arami bane, yana da girmama sosai shiyasa ba zata iya ba."

Wani iska ya furzo ya sunkuyar da kai yana tasbihi, ya d'an jima kafin ya d'ago jin Hafsat na fad'in "Yanzu miye abun yi Rakiya?"

Kallonta tayi tace "Zamu mata aiki ne a cire shi indai ana son ceto rayuwarta dana abinda ke cikinta."

Da sauri sheikh ya kalleta yace "A yi mata, a mata Rakiya indai zata rayu, dan Allah ki k'ok'arta ki ceci rayuwarta."

Da mamaki Hafsat ta kalleshi tace "Rakiya tayi iya k'ok'ari, muyi fatan Allah ya bata damar ceto rayuwarta."

Baya baya ya ja ya zauna inda Rakiya ta mik'a masa takardar hannunta da alk'alami, karb'a yayi ya saka hannu tare da mik'a mata, da sauri ta nufi d'akin nak'udar suka shiga kimtsa duk abun buk'ata ita kuma Rakiya ta kira babban docteur d'in dake wannan aikin.

Lokacin da aka fito da ita zasu shiga d'akin tiyata lokacin sheikh na waya da Abban Mimi suna sanar musu halin da ake ciki, Abba sai da yayi hawaye tare da koro musu addu'a, da kallo ya bita sanda suke wucewa tayi lak'was kamar bata motsi, saida ta b'ace ma ganinshi kad'ai ya lumshe idonshi, sannu ya shiga taro 'yar gajeruwar rayuwarshi da ita, k'iriniyarta da rashin jin ta, kwalliyarta da shan k'amshinta, a hankali ya d'an murmusa yace "Allah ka bata lafiya."

"Ameen." Hafsat ta fad'a tana kallonshi, da sauri ya bud'e ido ya kalleta dan ya d'auka a zuciyarshi ne yayi addu'ar.

*02:00* aka fito musu da santaleliyar yarinyar aka mik'awa Hafsat data rigashi tara hannunta, k'urawa yarinyar ido tayi mai d'auke da gashi luf luf a gaban goshinta kamar zai rufe mata ido, ba tayi mamakin ganinta mai gashin nan ba dan Mimi ba laifi tana da yalwarshi uwa uba kuma sheikh dake bafulace. Saidai wani abun mamaki a tare da yarinyar shi ne irin girmanta, tubarkalla gata jaririyar amma wata b'ulleliya ga kuma kan ta masha'Allah mai fad'i, haka kuma daga yanda halittar hannayenta da k'fafunta suke zaka san tabbas yarinyar nan irin hallitar iyayen Mimi ce da ita indai ba wani nufi na Allah ba kuma.

D'agowa yarinyar tayi sosai ta sumbaci goshin yarinyar tare da sakin murmushi tana kallon sheikh ta mik'a masa ita, karb'a yayi hannayenshi na rawa shi ma ya k'ura mata ido, murmushi ya saki ya kalli Hafsat yace "Kinga kamar uwarta, ja'ira Allah yasa kada tayi k'iriniya irinta uwarta, dan ta wahalar dani ba kad'an ba."

Hafsat da Rakiya a tare suka k'yalk'yale da dariya sai kuma ya kallesu yana had'e fuska yace "Ya mahaifiyarta take? Tana lafiya?"

Murmushi Rakiya tayi tace "Tana lafiya, insha'Allah za'a fito da ita nan da awa biyu a kai ta d'akin hutu."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah."

Kallon yarinyar ya sake yi yana jin k'aunarta ita ma kamar sauran yaranshi a sanda ya d'ora idonshi a kan su, duk da wannan d'in yafi wahaltuwa wajen rainon cikinta, amma ganinta na yanzu ya zama sanyin idaniyarshi tare da jin ya manta kowace azaba har da ta murzar daya sha yau sanda uwarta ke fama. Iya ce ta zo tare da Abba saidai shi ya koma ya barta nan ta kwana tare da Mimi.

Kwanansu hud'u aka sallamesu bayan an tabbatar da ingancin lafiyarta data abinda ta haifa wacce ta ci sunan *Halimatu-Sadiya*, sunan mahaifiyar sheikh kenan wanda sanda ya rad'a sunan Mimi ta kalleshi tace "To yanzu ya zan kirata kenan? Mimi ko Maama?"

Murmushi yayi yace "Ya rage na ki."

Iya ma tab'e baki tayi tace "Gaskiya kam, idan tana so ma ta ce Uwani."

Turo baki tayi tace "To Iya na k'i na ce Uwanin, ba zan ce ba."

Hafsat dake ta musu dariya ne tace "Gaskiya Iya sunan gayu zamu dinga kiranta da shi."

Kallon Mimi tayi tace "Kinga k'anwata mu dinga kiranta da *Amatullah*."

Dariya Mimi tayi tace "Shiyasa nake son aunty na, ba kamar yan cikin bak'in ba."

Dariya sukyi dan sun fahimci da Iya take. Sun isa gida kuma Mimi ta fara gurza kalar na ta jegon mai cike da wuyar sha'ani, a zahiri ita ake ganin wautarta na k'in wasu abubuwan da take yi, bata shan kunu saita gaurayashi da madara yayi fari fat tasha sugar sannan ta kifa kai ta shanye, shan maganinta kam wannan k'a'ida ne sai sheikh ya zo yake bata shi ta sha, inba shi bΓ’ kam kowa aikin banza ne, duk wani abu da za'a ce tasha dan ruwan nono su zo ko 'yar ta mulmuje ta k'i, kuma a bad'ini sheikh ne ke zugata yana nuna mata ba addini bane, ta ci ta k'oshi kawai indai abun mai anfani ne a jiki zata samu ruwan nono ba sai tasha komai ba.




_🀣Dole fa mu k'are yan uwa, komai yayi farko da ma yana da k'arshe ai, wasu ma😁 a account d'in aure yak'in mata suke ta tura kud'i wai na matar mutum, ai da kun fad'a min tun farko dana siyar da littafin tunda na ga ya kawo wuta😎😜 amma zan muku *Mim-Sheikh* returns._


*Bayan wata biyu*


Da k'arfi ta fizge zata yi waje tana fad'in "Wallahi ban yarda."

Sake rik'ota yayi ya had'a da jikinshi yana kallon cikin idonta yace "Da gaske Ryam, ba an miki allura ba ranar da kika kai Amatullah wajen tsaga ba? To ai a ranar kema na sa aka miki, ba zaki d'auki ciki yanzu ba."

Marairaicewa tayi muryar na b'arin tsoro tace "Abdul kaga dai cikin Ama ai na kusa mutuwa ko? To dama baka so na ne shiyasa yanzu ma ka lallab'o kake son sake min wani cikin?"

Sinne kan shi yayi yana ta k'ok'arin lalabo bakinta, d'ago da kan shi tayi tace "Fad'a min gaskiya sheikh na sani."

Kallonta yayi da idonshi da sukayi jajir suka rine yace "Ryam ina sonki mana, ke yanzu fad'a lin zaki ji dad'i idan na shareki bana kulaki?"

Da sauri tace "E, ni babu abinda zan ji, kawai ka tafi wajen Aunty Hafsat ta maka abinda kake so."

Had'e fuskarshi yayi yana kallonta yace "Korata kike ne?"

K'wacewa tayi daga rik'on daya mata ta ja baya tace "Ni ba korarka nake yi ba, amma dai ka je wajenta na yafe mata har zuciyata."

Da irin kallon nan mai nuna ran shi ya b'ace kuma zai iya yin komai ya kalleta yace "Kin tabbata na je?"

Ba abinda ya dameta tace "E, ka je."

Jinjina kai yayi ya juya inda Amatullah ke kwance cikin d'an gadonta, sumbatarta yayi a goshi d'aga hannayenshi ya tofa addu'a ya shafa mata sannan ya juya ya fice a d'akin bai kulata ba.


Tun daga ranar Sheikh yayi wuri ya aje ta, dan yana so ya nuna mata akwai abinda dole ko yana cikin ran ta ta b'oyeshi indai akan shi ne, dan shi ba banza bane mijinta ne? Ko d'akinta ya shiga Ama ce ke kai shi ya d'auketa ya fito yasha wasarshi da ita sannan ya mayar d ita ya aje, yanzu dake tana zuwa d'akinshi gaishe shi ko taje gaisuwart yake amsawa ya shiga sabgar gabanshi.

Wasa wasa sai hakan ya fara damunta, musamman kayan marmarin data dinga had'awa tana ta kambama tana sha sai abun ya fara zam matsala, dan kuwa dan sha'awa ke neman haukatata inda k'amshin turarenshi kawai take ji ta dinga jin tsigar jikinta na amsawa.

Gashi kuma ya k'i kulata bare ta bada kai bori ya hau, sai hakan yasa ta zama kullum a b'acin rai take, dan danan ta hau ta tunzura, gudun kar a samu matsala tsakaninta d Hafsat sai t zab'i zaman d'akinta kawai indai t gama abinda take.

*Yau* ma kamar kullum da sassafe ta shiga d'akin na shi sanye d hijab d'inta tayi sallama, amsawa yayi tare da aje Qur'anin hannunshi ya mik'e, dan ba komai yasa shi kakkauce mata ba saΓ― gudun kwafsawa, dan shi ma turarenta na rikitashi ga uwar k'ibar da tayi jikinta yayi wani irin luwai luwai, fatarta ka rantse zallar madara yanda ta kwanta da kyau abu ga fara dama, shiyasa baya son dogon zance ko mu'amula a tsakaninsu.

Zai shige ban d'aki tayi saurin fad'in "Ina kwana."

Ba tare daya juyo ko ya tsaya yace "Ban ganshi ba."

Ba tayi mamaki ba dan tasan baya amsawa dama, saidai ganin ya shige ya barta tsaye yas ta sakin baki tana kallon k'ofar, sai kuma wata zuciyar ta izata kawai ta sa kai a ban d'akin.

Yana tsaka da cire rigarshi t shigo amma bai kulata ba, k'arasa cire rigar yayi dan dai ta fita ta bashi wuri yayi shirin zame wandonshi, ganin bata kula da haka ba sai ma gyara tsayuwa da tayi ta fara zazzga masifa tana fad'in "...



*Alhamdulillah*
8/6/21, 9:46 PM - Ummi TandamaπŸ˜‡: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘?

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


πŸ’«βœ? *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜? *[ T.M.N.A]* β˜? πŸ“–πŸ–ŠοΈ?

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*K'arshe*



*60*




Ganin bata kula da haka ba sai ma gyara tsayuwa da tayi ta fara zazzaga masifa tana fad'in "Wai ni kam Abdul me na maka ne kake wulak'antani a gidan nan? Dama da ake cewa da ka fara haihuwa sai namiji ya canza maka gaskiya ne? Duka haihuwa d'aya sai ka wani fara d'auke min kai? Me na maka dan Allah? Idan ka fara gajiya da ni ne ka fad'a min mana dan nasan inda dare zai min."

Dakatawa yayi daga shirin cire wandon ya k'ura mata ido, tsakaninta da Allah take maganar kuma babu alamar wasa, saidai abu d'aya daya fahimta duk da cikin fad'a take maganar, amma kuma muryarta a sanyaye sosai kamar wacce ke neman wani abu.

D'auke kai yayi yana sake had'e fuska ya kalleta da kyau yace "Kina buk'atar wani abu ne?"

K'yabta masa ido tayi idonta na cika tap da hawaye sai kuma tace "A'a."

Nuna mata k'ofa yayi yace "Fita to ki bani wuri, wanka zanyi kuma dai kinsan ba zan yi tsirara a gabanki ba ko?"

Galala tayi tana kallonshi sai kuma ta ji gabanta ma na fad'uwa dan yanda ya mata maganar ba da wasa bane, a hankali ta juya zata fita jiki a mace sai kuma ta juyo da sauri ta kuma kallonshi, marairaicewa tayi sosai ta sake kashe muryarta tace "Abdul kana hushi dani ne akan abinda ya faru ranar? Kayi hak'uri to kaji na tuba, wallahi ba zan sake ba, Abdul idan kana min irin wannan hushin a gidan nan ya kake so nayi to? Gidan nan dai ai saboda kai nake zaune, kai ne abokin hirata kuma farin cikina, idan ka yi hushi dani ya zanyi kenan?"

Kafeta yayi da ido yana kallon fuskar tausayinta kamar ya jawota ya rumgume, saidai a yanda yasan Mimi kai shi yasan da walakin goro a miya, tabbas akwai abinda take da buk'ata, amma sau nawa suke samun sab'ani saidai shi ya d'auki da dangana da girma ya nemi sulhu, amma ita ta dinga botsarewa kenan tana fusata tana hawa da sauka.

Ita ma kallonshi take ganin yana ta kallonta sai kawai ta fad'a jikinshi ta fashe da kukan shagwab'a tana fad'in "Kayi hak'uri yallab'ai ka yafe min ka ji."

Wani munafikin murmushi ya saki a ran shi yace "Na-san a rina dama, mata da kurb'e kurb'e musamman idan sun haihu."

Dariyar mugunta ya dinga saki ya shiga shafa jikinta yana zura hannayenshi cikin rigarta, tsam tsigar jikinta ta fara tashi tana rage sautin kukanta sai kuma ta d'ora hannunta na dama kan nonon shi tana shafawa tana rufe ido.

Biye mata yayi shi ma sosai saida yaji suna buk'atar kwanciya kawai ya janyeta a jikinshi ya sake nuna mata k'ofa da idonshi da shi ma ya kamu da jarabar yace "Fi...ta a nan."

Da mamaki ta kalleshi sai kuma ta sake langab'ewa ta matso zata rik'e hannunshi ya sake nuna mata k'ofar alamar ta fita, duk k'ok'arinta saida hawaye suka fito mata dan sosai take jin yanayi marar dad'i a jikinta, juyawa tayi a fusace ta bar d'akin zuwa d'akinta ta cire hijabinta ta kwanta gefen 'yarta dake baccinta ta k'ura mata ido.

Tun tana d'an lumshe ido tana matse k'afafunta har bacci ya d'auketa ita ma marar dad'i. A hankali ya shigo d'akin ya zuba mata ido, murmushi ya saki yana godewa Allah daya nuna mishi lagon yarinyar nan, kamar kowa'e d'an adam yana da rauninshi, haka shi ma yanzun ya hango na ta raunin, ba zai cutar da ita ta haka ba dan cituwar zata iya shafarshi, saidai shi ya d'an samu sauk'in wani abun daga gareta, abu d'aya da zaiyi shi ne ya sake dagewa wajen inganta lafiyarshi dan samun sauke mata hakk'inta, ya sani har ga Allah wasu lokutan idan ya zurfafa tunani ya kan ji kamar ya tauyeta, dan a lokacin da tsufa zai riskeshi ya kai k'adamin da baya buk'atar mace, ita kuma a lokacin ne zata kai ganiyar shekarunta da dole wutar sha'awa ke ruruwa a jikinta, tambayar anan ita ce shin ya zaiyi idan lokacin nan ya zo? Shin zai saketa dan kar ta fad'a halaka? Ko kuma idan ya rik'eta zata fad'a wata mummunar hanya ce?

Nauyayyen numfashi ya sauke yace "Hasbunallahu wani'imal wakil."

A hankali ya k'arasa kusanta tare da sunkuyawa yasa hannayenshi cak ya d'agata gaba d'aya, bud'a ido tayi da sauri tace "Waye?"

Sai kuma suka had'a ido, rufe idonta tayi jin yace "Waye kuwa ban da na ki."

Turo baki tayi tana wuntsila k'afafu tace "Sauke ni k'asa malam, bayan yanzu ka koroni a d'akinka."

Dariya yayi yace "Na gane ban kyauta ba ai, shiyasa na zo bada hak'uri."

"Ni kawai ka saukeni ba zan hak'ura ba." Ta fad'a tana kumbura, cikin fara'a yace "Muje kan gado tukuna na bada hak'urin, sannan ne zan tantance an hak'ura ko ba'a hak'uran ba."

D'akinshi ya shiga da ita ya rufe ya kaita kan gadon ya sauke, rumfa ya mata ya nemi had'a bakinsu sai kuma tayi zurum ta had'a bakinshi da na ta, waro idon da yayi ya kalleta yasa ta jin kunya ta cire bakinta a na shi ta sunkuyar da kai, tallabo hab'arta yayi yana kallonta da tausayi yace "Ryam, ni ne ko? Ni ake da buk'ata a wannan lokacin ko?"

A hankali ta jinjina kan ta sai kuma ta sunkuyar da kai cikin muryar kuka tace "Abdul k'aik'ayi nake ji a jikina, sai na dinga ji kai kawai nake so na ji kana tab'ani, ko k'amshin turarenka kad'ai

Please Login or Register in order to submit comment