Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA SHA HUD'U_


*__________________________*


















_Daddy na isa kai tsaye sashen Hajiya Gwaggo ya nufa ,be ko yi tunanin fara ganin hajiyar shi ba ,Dan kuwa matuqar Hajiya Gwaggo ta samu labarin seda ya biya can kafin ya shigo wurin ta ,to fa jarabar duniya se Wanda ta manta ,kai bashi kad'ai ba hatta hajiyar tashi ya ja mata jangum. Gashi dai asalin mijin Hajiya Gwaggon ya rasu ,wato kakan daddy namiji ,amma bashi yasa Hajiya Gwaggo ta canza wasu halayen nata ba ,ita ke mulkin komai tun kakan daddy Nada rai ,ba Wanda ya isa ya d'aga d'an tsaya matuqar tana wuri ,da tace 'Eh' kuma ba a haifi Wanda ze ce a'ah ba, kishiyar ta Hajiya sakina ba k'aramin wahala tasha ba a hannun Hajiya Gwaggo ,musamman ita da yaran ta mata ne gaba d'aya ,bata tab'a haihuwan namiji ba ,ita ko Hajiya Gwaggo yaranta biyar maza ,kakan daddy shine Auta ,to fa se abunda ta b'ata, wannan yasa lokacin da me gidan ya rasu ,ta kame komai tayi kane -Kane ,rabon gado ma da akace za'ayi hana wa tayi ,daga k'arshe ma kawai se ta kuka ,wai dama so ake ya mutu aci gado ,to ba abunda ya isa matuqar tana da rai , ba yadda za'ayi da ita ,haka aka hak'ura aka k'yale ta ,haka dai kishiryar tata ke zaman hak'uri a gidan ,da Allah ya tashi nuna ikon shi ma ,gaba d'aya yaran Hajiya sakina biyar mata ,manya-manyan attajirai suka aura ,daga wacce ta aura mijin ta bako sisi ,suka kud'ance tare ,se wacce taje ta taradda azzikin, ba yadda basu yi ba akan ta koma d'aya daga cikin gidajen da aka Gina mata amma ina k'yameme Hajiya sakina tak'i ,saboda ta saba da zaman wannan family house d'in. Duk kuma lokacin da zasu zo da abun azziki ,ko da basu yi niyyar bawa Hajiya Gwaggo ba ,tilas Hajiya sakina ke matsa musu se sun je sun bata, saboda a zauna lafiya ,sannan rayuwar mu ba d'aya ba ,Hajiya sakina mace ce me sauqin hali da faranfaran da mutane ,ita ko Hajiya Gwaggo tak'adarin budurci ne ke yawo akanta sama da shekaru aru aru Ana Abu d'aya, da Allah ma yaso nuna mata ishara ,kaf a 'ya'yan ta mazan nan data ke tak'amar ta Haifa gwal ,Alhaji k'arami Baban Daddy shine kad'ai Wanda Allah ya d'aga a cikin su ,shiyasa komai nashi take ham-ham. Sannan kaf a sauran 'ya'yan daga Wanda yabar 'kasa zuwa Neman nakan shi ,se Wanda yana wani gari da iyalan sa ,Baban daddy ne kawai tayi wa kafi a kusa da ita. To sauqin suma tsufa daya kamata gadan-gadan ,ciwon yau daban na gobe daban. Wannan kenan..._




_Sallama yayi ,ba kowa a sashen duk mutanen gidan suna sashen Hajiya sakina ,Dan kusan kullum acan ake wuni. K'arasa wa yayi suka gaggaisa ,Hajiya sakina na tambayar shi iyalan sa ,yace duk suna lafiya. Ba wani jimawa yayi ba ,Dan yasan masifar kakar tashi ,yace wa Hajiya sakina_


"Bari inje mu gaisa da Hajiya Gwaggo"


Tace "To shikenan. Ga wannan hurar me sanyi kaje da ita kasha ,yanzu na gama damun ta kaga ludayi nan gashi, nasan an kwaso hanya" ta mik'awa daddy k'waryan furan ,daya ji kidirmo ,ga k'ank'ara an farfasa a ciki. Kai daga ganin furar nan zata yi dad'i musamman irin lokacin zafin nan...lolzπŸ˜›


Godia Daddy ya mata sosai, sannan ya d'auka ya nufi sashen Hajiya Gwaggo, a lokacin ta fito daga ban d'aki. Har k'asa ya zube ya gaishe ta a ladabce kamar yadda ya saba. A yatsine ta amsa shi. Kafin ta soma halin nata




"Se yau kaga damar zuwa ,ko da yake inaga se yau uwar taka suwaiba ta baka izinin zuwa inajin ,wato ni ban isa ba ,ban kuma da muhimmanci a wajen Ku dahar zaku yi Abu ba tare da kun sanar dani ba ,tun ba yau ba ,na riga na gane dakai da uwar ka suwaiba so kuke in mutu, to wallahi ahir d'in Ku ,k'walelen kare da antar kura ,ni d'in nan da bakwasan gani wallahi se kun ganni.
To kunyi yadda kuke so ,yanzu nima zakaji nawa hukuncin ,saboda haka ka bud'e kunnuwan ka dakyau kaji ni. Kai bama zan fad'a a gaban ka kai kad'ai ba tashi muje ayi a gaban suwaibar".


Tana gama fad'in haka tayi gaba. Shidai daddy be ce mata ci kanki ba ,Dan Allah yayi mai sanyin hali ,girgiza kai kurum yayi sannan ya tashi yabi bayan ta.


A b'angaren hajiyar daddy ,tun da taji sallamar Hajiya Gwaggo gaban ta ya shiga dukan tara-tara ,Dan tasan azziki baya kawo ta se dai akasin shi. Tsaye ta tashi tana mata sannu da zuwa ,sallamar Daddy yasa ta maida duban ta gun k'ofar shigo wa ,a mamakin shine yaushe Daddy yazo? Kuma meya kawo shi a wannan lokacin? Gashi ta ganshi da Hajiya Gwaggo, tasan ko ba'a fad'a mata ba ita ta kira shi. Nan fa hankalin ta ya k'ara tashi ,Dan tasan wani matsalar ce zata kunno kai.


Daddy gaida Hajia yayi ,ta amsa fuska a sake. Bata ko zauna ba ,ta mike ta d'auko wa Hajiya Gwaggo ruwa ,taje a gaban ta




"Ba ruwan ki ya kawo ni ba ,ni za'a gaya wa ruwa ,nida keda ruwan tukunyar k'asa ta dauri ,masu k'ara lafiya. To ki saurare ni dakyau. Kunyi San ranku ,azzikin Ku d'aya da bana nan. Kinje kin nemo masa mata kin aura mata ,kuma 'yar wannan battalalliyar qawar taki, saboda kun ga jini na me kyau ne ,anga azziki ,shine Dan mugunta Dan kika nema masa aure, to bazan ce ya sake ta ba ,tunda an riga anyi ,amma ina me tabbatar miki ,Wani auren ze sake ,kuma nice nan zan sama masa mata 'yar azziki..."


Daddy ji yayi kamar an buga masa guduma... Hajiya ma haka taji abun kamar saukar aradu, wai Aure...




"Aure kuma???" Daddy ya furta ba tare dama yasan maganar ta fito fili ba


"Eh aure. Wannan umurni na ne ba shawara ba". Hajiya Gwaggo ta fad'a tana wani irin gimtse fuska ...




















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/21, 3:08 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA GOMA SHA BIYAR_


*________________________*























_Magana daddy yaso yi amma Hajiyar shi ta katse shi. K'ak'aro murmushin dole tayi ,kafin tace "Hajiya Gwaggo insha Allahu zaki same mu masu yi miki biyayya, kada Allah ya kawo randa zaki yi magana ni suwaiba ince ba haka ba ,ki qaddara bani bace insha Allahu Rabbi. Aure kuma ba wai nayi wa Daddy shi akan wata manufa bane, nayi mishi ne ko Dan in Samar musu nutsuwa shi da iyalan shi. Amma Dan Allah kiyi hak'uri idan kina ganin an miki ba daidai ba"_


_tsabar jaraba irin na Hajiya Gwaggo duk lallamin nan da Hajiya tayi mata be yi nata ba ,a'a wai Dan me za'a ce mata idan tana ganin an mata lefi tayi hak'uri, nan fa ta fara zazzaga musu ,se abunda ta manta. " Nace dai ba ke kad'ai kike da iko dashi ba ,har wani wai idan an mun lefi in yi hak'uri, to bazan yi hak'urin ba da guntun tsugudidin ki, ba abunda ya kawo ni ba kenan. Kai kuma..."_ _ta fad'a tana nuna Daddy dake zaune ya sunkuyar dakai ,shi kad'ai yasan me yake ji a k'asan ran shi. D'an d'agowa yayi yana duban ta ,ai fa wannan be yi mata ba "Au bazaka iya amsawa ba ,kai kurma ne? To ka amsa ko kar ka amsa wannan matsalar ka ce"_


_Taci gaba da cewa " Yarinya dai ba wata bace in la wacce nasani kuka Sani ,yarinya 'yar gidan mutunci ,ga kamala da tsari. Sama da shekaru aru-aru da muke zaune a layin nan ban tab'a jin ance sunyi rigima da wuni ba, ba kowa bace illa LUBABATU... Kai idan baka sheda ta ba , ita suwaibar uwar ka ai ta Santa farin Sani ,balle ma baka isa kace baka gane wacce Lubabatun ba, saboda duk zuwan da kayi tana zuwa yi maka sannu da zuwa ,har ma tayo maka girki. Saboda haka na gama magana da iyayen ta ,se da nayi da gaske ma kafin suka amince ,mun kuma tsaida ranar biki ,nan da wata biyu me kamawa, se ka fara shirye-shirye ,ka kuma turo mana da isassun kud'i ,kar muji kunya ,kaji na gaya maka, kafin ka tafi se ka leqa Ku gaisa"_ _Hajiya Gwaggo ta k'arasa fad'a yayin da take barin d'akin..._




_Wani takaici ne ya tokare wa Daddy mak'oshi ,babu ma abunda yafi bak'an ta mishi rai ,irin da Hajiya Gwaggo ke cewa ,seda tayi da gaske sannan aka bata wannan auren ,kai kace saka ta yayi. Wani abun takaicin ma wai ya leqa ,kamar shi ,maimakon ma tace zan tura a kira maka ita ,shine zata ce ya leqa da girman shi"... Daddy ke ta zancen zucin shi shi kad'ai.




Ita dai Hajiyar Daddy kusan bugun zuciyar ta ne ya kusa tsayawa cak ,,,, Dan wannan ba k'aramin al-amari bane. Ta gane Lubabatun da ake magana ,se dai tana jin wasu rad'e-rad'in maganganu marasa dad'i akan gidan su ,ta kuma ji ance ta tab'a aure ,amma fa badan ta tabbatar ba. Wani gajeren ajiyan zuciya ta sauke ,tare da zuba wa Daddy ido, ita gaba d'aya ma wallahi tausayin shi take ji ,shi ba wani babba ba can amma duk an taru an kashe masa rayuwa da gurb'atattun mata marasa tsoron Allah. Gashi bata da wani abun yi daya wuce ta dage wajen gayawa Allah... Hajiya keta sak'e-sak'e a ranta. Kafin ta kira sunan daddy cikin Muryar lallashi.


"MISBAHU!!!" Da sauri Daddy ya d'ago ,Dan idan baze manta ba wannan shine karo na biyu da Hajiya ta kira sunan shi ,tun da kuwa yake da ita.


A sanyaye ta fara basa baki "Kayi hak'uri kuma ka d'auki abunda abunda yake faruwa dakai a matsayin qaddarar rayuwar ka. Allah na sane dakai ,be manta dakai ba. Cewar kawai kayi imani bashi ze sa Allah ya kasa jarabtar kaba, dole ne ayi maka gwaji ,musamman ma kai da Allah yayi wa bud'i. Menene Allah be baka ba na duniya? To se kuma kace a had'a maka dad'in duniya gaba d'aya? Baze yu ba ,Shiyasa Allah ya maka jarabawa da mafi girman jarabta, Dan mace qalubale ce ,kuma babbar jarabawa ce a rayuwa. Dan haka kayi k'ok'arin danne zuciyar ka wajen ganin ka ci wannan jarabawar. Sannan kar ka damu zanyi iya bakin k'ok'ari na wajen yin bincike akan ita wannan yarinya ,Addu'a kuma ba fasawa nayi ba koda yaushe albarka ta na tare dakai. Kar ka kuma yi mamakin wannan itace jarabawar ka ta k'arshe ,ta iya yuwa kuma a wannan karon kaji dad'in aure ina fatar hakan..." Shiru ne ya biyo baya nad'an wani lokaci kafin Hajiya ta tambaye shi "to yanzu ya zaman iyalan naka yake a can?"


A tunani na ko Daddy ze gayawa Hajiya duk abunda yake faruwa ,sedai Banyi mamakin jin be wani tsawaita zancen ba ,Dan Allah yayi Daddy wani mutum me matuqar zurfin ciki. A sanyaye yace


"Suna can lafiya qlau ,sedai zaman ba dad'i gaba d'ayan su ,Dan kusan duk wani Abu da kubra keyi shi khaltum ta koma yi ita ma ,duk dai abun se hamdala".


" Oh Allah! Ka kawo mana d'auki da sassauci acikin wannan al'amarin" cewar hajiyar Daddy.


Daddy yace "shiyasa naso ace da Hajiya Gwaggo zata bar maganan auren nan ,jna ga zefi sauqi ,wancan wutar ma dake gaba na se dad'a huruwa take ,balle kuma ace na kai wata ,Hajiya kar fa su kashe ni"


Murmushi irin nasu na manya Hajiya tayi tare da cewa "bame kashe wani se kwanan shi ya k'are ,rayuwar ka ba'a hannun su take ba ,a hannun Allah take, idan ma wannan bashi bane k'arshen ijabar ,to ina ji a jiki bada jimawa ba ,Allah ze musanya maka da mafi alkhairi insha Allahu."""


A ranar dai daddy da Hajiya kwana suka yi suna tattauna matsalolin gidan shi, da daddare yaso ya tafi sashen bak'i ya kwana ,ko ya samu yaji rad'ad'in da zuciyar sa ke masa ya ragu ,amma tsakanin d'a da mahaifi se Allah ,tunda Hajiya ta karanto akwai damuwa a tattare dashi ,hana shi fita tayi ,se dai suka kwana a sashen ta. Ko parlour bata bari ya tako ba ,gadon ta ta sauka ta bashi ,ita kuma tayi shimfid'a a k'asa, ranar kwana yi masa nasihohi tayi ,tare da lallashin zuciyar shi ,a haka Daddy be ma San bacci yayi awon gaba dashi ba...




_washe gari tunda sassafe Hajiya sakina (kishiyar Hajiya Gwaggo), ta auko wa daddy da abun karin kumallo..._
















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/23, 2:19 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA SHA SHIDA_


*_________________________*
























_Tun bayan tafiyan Daddy kano ,su suxee ke cikin walwala da kwanciyar hankali. Sosai Haajar ke saka su nishad'i ,musamman data gane kamar akwai damuwa a tattare dasu, ba kuma wai sun gaya mata bane , a'a hasalima wani magana ta b'angaren rayuwar junan su be shiga tsakanin su ba ,saboda Haajar ba mace bace me yawan magana musamman akan abunda be shafe ta ba ko ba'a saka ta a ciki ba ,amma tana da Abu d'aya Wanda zamu iya cewa yana daga cikin baiwar da Allah ya mata ,duk yadda mutum yake cikin damuwa kuma yake k'ok'arin b'oye ta ,to hakan a wurin Haajar kamar ma k'ok'arin bayyana mata kake yi ,ba dai zata ga abun bane saboda batasan gaibu ba ,amma tana da hasashe nad'an Adam, da ace zata nazarci matsalar ka sosai ,to idan da zata furta cewa ga abunda ke damun ka ,kuma seka ga insha Allahu kamar ta sara akan gab'a ,ko kuma k'anin hakan. Sosai take kutse cikin rawar su haseena Dan ganin ta kwatanta wargatsa abunda zata iya na damuwar su ,seda tayi duk yadda tayi suka sake da ita ,Auta kam ta samu sabuwar Anty Dan ko abinci idan dai ba Haajar ce zata bata ba ,to bafa zata ci bane ,idan ma aka matsa mata se ta tsiri k'ananan kukan ta ,haka dai Haajar ke biye ta ,Ashe dama Auta fili take nema ta b'arje gumin ta ,samun wuri yasa har ta fara wani shagwab'an iyayi da bata yi da a gidan su. Sautari idan Suxee tana ganin yadda Auta ta samu kyaky-kyawar kulawa a wurin Haajar, har k'wallan tausayin kan su take yi, saboda a rayuwa su basu tab'a sanin menene soyayyar uwa ba, se dai ta uba ,shima ba wani kyaky-kyawar kulawa ba saboda d'an kasuwa ne ,ba zama yake yi ba. Ba Auta kad'ai ba ,hatta su d'in da suke manya Haajar bata saka musu ido ba. Bata tab'a barin su cikin kad'ai ci ,ko wani lokaci takan nemi abunda zasu yi me amfani Dan karta barsu zaman tunani._


_Hajj Jamil ma ba'a barshi a baya ba wajen basu kulawar data dace ,haka yake jan su a jiki tamkar 'ya'yan daya Haifa na cikin su ,Dan tsakanin shi da Daddy fad'in alaqar b'ata lokaci ne , 'yan uwa ma na jini sunyi kad'an su nuna musu so da qaunar junan su. Shi gaba d'aya ma yaran tausayi suke bashi ,kusan da abun yake kwana arai dashi kuma yake tashi ,koda yaushe tunanin shi shine ina mafita ,haka dai ya fawwala allah al-amarin ,be kuma yi k'asa a guiwa ba wajen ci gaba da gayawa ubangiji matsalar da suke ciki. Wannan yasa idan ya dawo da daddare se ya tafi can sashen nasu ,yayi ta Jan su da hiran ban dariya ,a haka se sukai k'arfe goma na dare, kawo lokacin wani shak'uwa me k'arfi ne ya sake shiga tsakanin shi dasu suxee Wanda ada babu._


_Kwanan su suxee uku ne kawai a gidan Hajj Jamil ,Amma idan ka gansu kai kace sun shekara ne. Sosai suka sake suka gudanar da al-amarin su ,tamkar suna gidan Daddy, kai wani abun ma da suke anan basa yin shi acan ,saboda sun San a gida ko sunyi ba duba musu za'ayi ba. Rayuwar se ta koma musu sabuwa fil ,se dai idan suxee ta tuna cewa ,idan fa Daddy ya dawo zasu koma gida ,duk se wani bargon tsoro ya lullub'e ta ,Dan ta riga ta gama tsorata da gidan zuwa yanzu._




_Se da daddy ya kwana uku ,yana shan nono wajen Hajiya ,Dan gaba d'aya kulawar da Hajiya ke bashi a kwana ukun nan yasa ya fara mantawa da wasu matsalolin. Zallar soyayya da qauna ,so irin na d'a da mahaifi ,shi Hajiya ke nuna wa daddy ,ji take kamar ta hana shi komawa ,amma hakan baze samu ba. Daze tafi Hajiya harda 'yar k'wallan ta ,ba tada dai matsalar komai na buqatun rayuwa Dan gaskiya Daddy na k'ok'ari ta wannan fannin ,ba ma ita ba ,na tare da ita ma na cin albarkacin ta. Be yiwa Hajiya Gwaggo sallama ba ,Dan ita a tunanin ta tun ranar ya koma, sashen Hajiya sakina kawai ya shiga ,Fura ta bashi manya-manya da aka saka a cikin bakko guda uku tace "ga wannan akaiwa iyalin ,nasan Hajiya k'arama dason fura". Godia sosai Daddy ya mata ,kafin ya kama hanya ,a ransa yake raya cewa ina ma Hajiya sakina ce kakar shi ba Hajiya Gwaggo ba ,Dan kwatakwata rayuwar su ta banbanta._


_tun bayan fitowar daddy gaban shi ke fad'i ,har zuwa lokacin daya kira Hajj Jamil ya sheda masa yau ze dawo ,gaban sa be dena fad'uwa ba. Be kawo komai a ranshi ba ,Se da ya shigo garin sakkwato ,nan fa zuciyar shi ta fara wani irin tsalle kamar zata fad'o k'asa. Yanayin yadda yake ji kamar wani al-amari ne ke shirin faruwa dashi, se kuma tunanin shi ya rabu gida uku ,Hajiyar shi ya fara tunowa ,musamman daya San yadda suka rabu bata so ba ,wata zuciyar tace masa kai ba ita ba ,se kuma ya fara tunanin su suxee ,nan ma dai zuciyar shi ta k'aryata shi ,Gidan shi ya tuno ,Sam zuciyar shi ma ta kasa bari ya tuno su ,A haka dai ya kama hangar gidan Hajj Jamil, sosai bugun zuciyar shi ya tsananta ,hankalin shi se ya k'ara tashi ,Allah Allah yake yaje yaga 'ya'yan shi, Dan gaba d'aya ya kasa samun natsuwa..._




_A bakin gate yaci karo da Hajj Jamil ,da alama shima dawowar shi kenan. Da fara'a sosai a fuskokin su ,suka yi musaba. Se a lokacin Daddy ya fara jin sauqin abunda yake ji ,Dan ganin Hajj Jamil da yayi cikin walwala da annashuwa a yanzu ya tabbatar masa daba wata matsala. A tare suka k'arasa cikin gida. Se hiran yaushe rabo suke yi ,se kace wa'yanda suka dad'e basu ga juna ba.




A haraban gidan suka ci karo da Auta ta rugo da gudu ,Nan fa hankalin Daddy ya tashi ,a tunanin shi ko wata matsalar ce. Haseena ce ta fito itama a guje da alama ita auta ke wa guje-guje ,kamo ta tayi ,tana wani tsalle-tsalle tare da fad'in "Ni bana so, ni bakya zaki mun ba Anty Haajar ce",,,, wannan yayi daidai da fitowar Haajar ,aiko Auta na ganin ta ,k'wace hannun ta tayi daga na haseena ,ta ruga a guje tare da fad'a wa jikin Haajar. Da gudu Haajar d'in ta d'auke ta cas, suka shige ciki. Gwalo Auta ta dinga yiwa haseena. K'wacci haseena tayi tana fad'in " Zan kama ki ne yarinya ,se kinyi bayani"...




Wani irin sanyin Dad'i ne ya mamaye zuciyar Daddy Wanda ya assasa k'wacewar wani siririn dariya a bakin shi...


















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/23, 10:25 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA SHA BAKWAI_


*__________________________*




















_Sashen Hajj Jamil suka nufa ,dama Hajj Jamil ya sanar da Haajar dawowan daddy ,Dan haka ta shirya masa abinci da abun sha gwargwadon k'warewar ta. Bayan yaci abinci ya huta ,gaba d'aya suka je masa sannu da zuwa ,sosai yaji dad'in yadda yaga yaran shi cikin walwala, godia yawa Haajar sosai akan k'ok'arin da take yi wajen kula da yaran. Auta na wajen shi yana mata wasa ,tana ganin su Haajar zasu fita da gudu ta biyo musu ,tare da rik'e hannun Haajar_


_Bayan sun fice ne ,daddy ya maida duban shi ga Hajj Jamil. Yake cewa "Gaskiya yarinyar nada natsuwa ,A yadda na fahimce ta kuma tana da ilimin addini dan naga komai nata kamar a k'a'idan ce take yin sa, gata dai daga gani bata wasu shekaru sosai ,amma tasan komai na zamantakewa. Murmushi Hajj jamil yayi tare da cewa " Ai indai haajar ce haka take Abokina ,bata da matsalar rayuwa". "Ta huta" shine abunda daddy ya fad'a a tak'aice kafin ya soma Gaya wa Hajj Jamil duk yadda yayi da Hajiya Gwaggo ,be rage masa komai ba. Sosai Hajj Jamil ya jinjina lamarin. Shiru ne ya biyo baya nad'an wani lokaci kafin Hajj Jamil ya sauke wani gajeren numfashi tare da cewa_


"Yanzu zuwa yaushe tace maka za'ayi bikin?"


"Kamar yadda tace dai ,ta Riga ta gama magana da iyayen yarinyar nan da wata biyu masu zuwa, amma kuma ai kasan lokaci na hannun Allah ne!" Daddy yaba Hajj Jamil amsa ,fuskar nan tashi d'auke da damuwa, yaci gaba da cewa "Yanzu menene abun yi kenan?"


Hannu biyu Hajj Jamil yasa rik'e da hab'a, alamar yana wani tunani daban. D'agowa yayi yana duban daddy na wasu 'yan mintuna ,kafin yace


"Ni ina ganin a yadda nasan Hajiya Gwaggo ,ba wani hanya da zamu b'ullo mata Dan tsaida wannan auren ,kamar dai yadda ta gaya maka inda tana da rai ba fa shi ,to fa haka zancen yake. Abu d'aya nake tunanin shine mafita ,Wanda kuma idan akayi dace shine jigon rayuwar ka dama na gidan ka gaba d'aya..."


Cike da mamaki daddy yace "menene wannan kuwa Hajj Jamil" Dan shi fa Daddy a nashi bahagon tunanin ,rayuwar shi kamar ta gama nakasa ne ,gani yake ba yada wata mafita daya wuce yaci gaba da hak'uri har Allah yayi ikon shi akan shi.


Cike da kulawa Hajj Jamil ya maida hankalin shi gaba d'aya wajen Daddy. Shiru ne ya biyo baya nad'an wani lokaci ,kafin Hajj Jamil ya fara magana a nutse




"Ni ina ganin lokaci yayi daya kamata muyi wa toka hanci. A gani na MISBAHU rayuwar Gidan ka na buqatar mace me TAUHIDI,,, ita kad'ai ce zata iya zama dakai da zuciya d'aya ,ta kuma yi yak'i wajen ganin ta dawo maka da martabar kujeran ka na cikakken namiji me inci. Ina

Please Login or Register in order to submit comment