Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hamdala tare da yiwa annabi salati, kafin ya d'ora da cewa "Dukkan godia ya tabbata ga Allah. Na San dikkan Ku kun ga abunda ya faru a yanzu ,za kuma kuyi mamakin wani irin nau'in al-amara ne wannan?" Hajiya tace "wannan gaskiya ne" Dr. Imam yaci gaba da cewa "Ciwon nan da Haajar d'in ake ta sanya mata jini alal haqiqa ba ita ake sanya wa jinin ba ,saboda masu shanye shi daban. Idan kuma da za'a yi shekarun annabi Nuhu A.S ana sanya mata jini ko makamancin wannan ba za Ku tab'a ganin ci gaba ba, sai dai ma daga k'arshe Ku rasata ma'ana ta mutu ,saboda jinin jikin ta da ake zuqa daga wani wurin daban. Wannan siffar da na fiddo daga jikin ta nasan kunsan ta?" Hajiya tace "shakka babu wannan Abokiyar zaman Haajar ce data mutu a gobarar da akayi a gidan ba da jimawa ba". Dr. Imam yace " to ta mutu ne amma kuruwar ta na nan na yawo. Ta kuma lashi takobin hana wannan ahali zaman lafiya. To amma da yake Allah ke yi ba wanin shi ba. Wannan kundi da kuka gani ,kundi ne na k'ona rauhanai. Saboda haka na nayi nasarar k'ona kuruwar wannan baiwar Allah da ke cikin jikin Haajar. Ba'anan matsalar take ba. Wannan ba ita bace asalin ruhin. Kuma muddin ba'a Nema ta asalin an k'ona ta ba ,to fa akwai gagaruwar matsala. Saboda haka na yi mata tambayoyi tun kafin na qona ta. Ta kuma gayamin inda za'a samu wannan babban kundin ,da an d'auko shi aka k'ona komai zai zama tarihi da izinin Allah." Wani irin ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da cewa "To yanzu a ina za'a samu wannan kundi malam?" Sunan wani daji Dr. Imam ya fad'a mai matuqar hatsarin gaske. Wanda ba lallai ka shiga wannan dajin ka dawo ba ,idan kuwa ka dawo to ba shakka zaka iya tab'uwar hankali. Ya kuma shaida musu akan lallai lallai Haajar d'in ake buqatar da ta je da kanta. "Kai ina!" Inji daddy "bazan tab'a barin Haajar ta je wannan wurin ba". Dr. Imam yace " Wannan itace mafitar mu ta k'arshe ,idan ba haka kuruwar zata dawo ,kuma idan ta dawo to dawowar bazai wa kowa kyau ba". Shiru kowa ya yi yana jimanta al-amarin. Kafin Dr. Imam yaci gaba da cewa "Zan shirya komai a Daren yau insha Allahu rabbi." Daga haka yace a rufe sashen Haajar d'in kowa da kowa ya koma sashen Hajiya. Haka kuwa aka yi.




Misalin k'arfe sha biyu na dare babu Wanda ya iya runtsawa banda suxee da auta da basu San wainar da ake toya wa ba. Wata farar mata ce ta shigo su Dr. Na zaune. Dr.imam yace ta zauna. Bayan ta zauna suka tattauna da shi cikin harshen larabci. Suna gama magana daddy yace wa Haajar "ki yi wa baquwa ta rakiya". Ba musu Haajar ta bi bayan wannan farar mata ,ita kuma Matar ta rik'e hannun Haajar suka fita.






Bayan sun fita daddy ya dubi Dr. Imam tare da cewa "Wannan wacece da suka fita da Haajar?" Gyara zama Dr. Imam ya yi tare da cewa "Wannan da kuke gani ba mutum bace aljana ce, Sunan ta maimunatu. Maimunata aljanar zuri'a ta ce ta amana." Cike da tashin hankali daddy yace "ina kuma zata kai Haajar?" Dr. Imam yace "dajin da fad'a muku za'a d'auko wannan kundin. Da taimakon Allah da taimakon maimunatu Haajar zata kai ga wannan kundi". A gigice daddy ya fita da gudu yana kiran suna Haajar! Dr. Imam yace " da'ace zaka dawo ka kwantar da hankalin ka da ya fiye maka kwanciyar hankali. Dan babu Haajar take so a wurin mu yanzu sama da addu'a." Kuka daddy ya fashe da shi ya na mai ci gaba da kiran sunan Haajar d'in babu qaqqautawa Sai da ya bawa kowa tausayi. Aiki Dr. Imam ya shiga yi tuk'uru. Dan kusan saida ya yi saukar alqur'ani. Su Hajiya kuwa alwala suka yi suka duqufa sallah har garin Allah ya waye. Banda daddy dake zaune cunkus kamar wani Mara lakka ,tun yana kukan mai sauti har ya koma sai dai hawaye kawai ke yi masa zuba.






















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[8/24, 12:09 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA SHIDA_


*____________________________*


















Har wuraren shida na safe babu Haajar babu alamar ta. Gaba d'aya ahalin gidan sun shiga damuwa ainun. Shida da rabi, Dr. Imam ya fito wajen sashen da suke ciki. A bakin k'ofa ya ga Haajar d'in a yashe ta yi wani irin baqi ta sauya kala kamar ba ita ba. Koma wa ciki ya yi ya yiwa daddy magana akan yazo ya d'auko matar shi. Da sauri daddy ya miqe yana fad'in "Ina take?" Ganin kwance a qasa a k'ofar shiga ya sa yayo saurin yowa kanta ba shiri ,ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan ta. Dr. Imam yace "ka shigo da ita ciki". Daga haka ya yi shigewar shi. Ba shiri daddy ya sunkuci Haajar d'in ya bi bayan Dr. Imam. A tsakar d'aki Dr. Imam yace ya ajiye ta. D'ankwalin dake k'ulle a jikin zanin ta ya kwanto tare da warware k'ullin ya furta " Alhamdulillahi! Wannan shi ne kundin da ake da buqata". K'ok'arin k'ona kundin ya shige yi da ayoyin Allah. Nan take wannan kundin ya ka ma da wuta ,wani bak'in hayak'i na tashi. Sai da ya cinye tas sannan ya yiwa Haajar d'in yayyafin ruwan magani. A zabure ta tashi zata ruga a guje ,ya rik'o ta, Tare da ci gaba da karanto mata ayoyin waraka daga ubangiji. Sambatu Haajar d'in ta shiga yi kamar wata zararriya. Addu'o'i sosai Dr. Imam ya dinga yi mata, daga haka wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Ya sake furta "Alhamdulillahi! Sauqi ya samu daga Allah! Yanzu ta samu bacci. Sannan wannan baccin idan zata kai sati d'aya tana yin sa kar a tashe ta ,sai lokacin da ta farka da kanta. Kar kuma Ku damu, babu abunda zai sake faruwa da izinin Allah. Za kuma Ku iya ci gaba da sabgogin ku". Hajiya tace " Insha Allahu za mu yi k'ok'arin kiyaye wa. Sannu da aiki malam, Allah ya saka maka da alkhairi. Da ba Dan kazo ba bansan yadda za mu yi da wannan rikitaccen al-amarin ba mai kama da al-mara. Duk da cewar Haajar 'yar ka ce ,amma mu ka yi wa wannan taimakon, Dan Haajar wata jigo ce daga cikin wannan ahali da ba zamu tab'a qaunatar abunda zai same ta na rashin dad'i ba. Mun gode sosai". Dr. Imam yace "Allah ya tsare gaba".




D'akin Hajiya aka maida Haajar d'in. Sai a lokacin kowa ya samu kwanciyar hankali. Hajj jamil jan Daddy ya yi suka tafi gidan shi ,a can suka yi bacci , ba su suka farka ba sai wuraren sha biyu na rana. Anty zuwaira ma zuwa tayi ta kwanta. Dr. Imam kuwa labari ya shiga baiwa Hajiya, kan abunda ya faru da kuma dalilin faruwar abun ,ya tabbatar mata cewa asalin tushen gurb'acewar rayuwar Kubra akwai sanya hannun mahaifiyar ta ,Wanda tun farko aka gina rayukkan akan b'ata da sagba ta miyagun jinnu, Wanda shi ne dalilin da yasa ko bayan ta mutu ta dawo a matsayin kuruwa. Wannan kundin kuma da aka k'ona shi ne asalin rayuwar Kubra... Ya faffad'awa Hajiya maganganu da dama na firgi ,al-ajabi da kuma ban tsoro. Hajiya ta yi ta mamakin dama hakan na faruwa a wannan duniyar ta mu? Dr. Imam ya tabbatar mata da akwai abunda ma ya fi wannan d'aure kai idan ta ji shi... Kusan kwanan Haajar uku ,ko k'wak'k'waran motsi ba ta yi ba. Wanda kowa ya damu da hakan. A gefe d'aya kuma mahaifin ta na ci gaba da yi mata addu'o'i da taimakon magungunan musulunci da yake da k'warewa akan su. Sai a rana ta biyar sannan Allah ya yi mata farkawa. Farin ciki ya dawo sabo. Kar ma daddy ka ji labari, Dan har rumgume ta ya yi Dan murna, ya ma manta cewar akwai mahaifiyar shi da mahaifin Haajar d'in a wurin. Nasihohi sosai Dr. Imam ya yi musu. Ya kuma ba da magungunan da Haajar d'in za ta ci gaba da amfani da su. Washe gari Dr. Imam ya yi musu sallama ya tafi. Haajar hadda kukan ta ,Dan sosai take kewar mahaifin na ta. Ya sha gaya mata a baya cewa duk soyayyar nan da yake mata ,za'a yi wani lokacin da wani ko wasu sun fi shi buqatar ta'. Shakka ba bu wannan lokacin ne. Bai tafi ba sai da ya yi mata nasihohi sosai itama, ya kuma k'ara gaya mata yadda mijin ta da ahalin shi ke matuqar Kaunar ta. Gargad'i Dr.Imam ya yi mata akan komai wuya wannan ahali sune abokan rayuwar tana duniya...




Kusan har aka yi sati Haajar bata gama dawowa yadda take ba, gaba d'aya jin ta take kamar ba ita ba. Daddy musamman ya shirya walima Dan yiwa Allah godia. Satin Anty zuwaira biyu ,ta koma gida jigawa a inda daddy da Hajiya suka cika ta da tarin abun alkhairi... Bayan wata d'aya. Komai ya lafa ,rayuwa ta dawo musu sabuwa. Haajar ta sake samun wani cikin. Kowa sai murna ya ke yi. A b'angaren d'aya kuma an so a saka ranar bikin Suxee da Barr Kabir ,duba da yadda soyayyar su tayi k'arfi. Haajar ta nema alfarman da a bari idan Allah ya sauke ta lafiya. Hajiya tace "duk yadda take so hakan za'ayi. Dan itace uwar amarya kuma uwar biki". Wannan batu ya yiwa Haajar d'in dad'i. Sannu da hankali cikin ta sai girma yake yi. Ta k'ara kyau ta yi haske gwanin sha'awa. Kulawa da tarairaya kuwa daga wurin daddy sai Wanda ya manta ,wannan ne ya k'ara bata damar murje gwad'arta take zuba masa zallar shagwab'a tare da nuna masa so da qauna a koda yaushe.




A b'angaren d'aya kuma Matar hajj jamil Hajiya zaliha ta dawo daga wurin aikin ta da take yi a wata qasa, Bayan tafiya na dogon zango da ta yi na tsawon watanni tara zuwa goma. Wanda a Qa'ida duk bayan wata biyar ta ke dagowa gida, tare da d'anta d'aya mai suna SAMEER. Abun ya yi matuqar d'aure Mata kai yadda ta dawo wannan karon Hajj jamil baya d'aukin ta ko kad'an kamar yadda ya saba. Hasalima ko kad'an bai nuna alamun jin dad'in ganin ta ba. A tunanin ta ko dad'ewar da ta yi ne bata dawo ba ya sanya ya ke fushi da ita, bata San abunda ya ishe shi bane ya ishe shi. Shi damuwar shi d'aya ne akan auren Suxee da Barr Kabir. Hajiya zaliha mace ce ta tsara daidai gwargwado da ta San abunda ya kamata ,tana da duk wani kwalitis d'in da namiji ke buqata, amma a zahiri bansan mai yasa ta fifita aikin ta sama da bautar auren ta ba, aikin ma a wata uwa duniya. Ta yi ta k'ok'arin ganin ta tambayi hajj jamil abunda ke damun shi. Hajj jamil mutum ne da baya tab'a iya b'oye damuwar sa idan ka tambaye shi. Ko kalma d'aya bai rage mata ba akan yadda yake matuqar son Suxee ,farin cikin shi shine ya ga ya auro ta tazo gidan shi a matsayin Matar shi ta sunnah. Hajiya zaliha ba ta gane wacce suxeen yake magana akai ba ,sai da ta sake tambayar shi, ya tabbatar ma ta da Suxee 'yar daddy da ta sa ni. Iya tashin hankali Hajiya zaliha ta shiga tashin hankali, Dan bata tab'a tunanin irin rana mai kama wannan zai zo mata ba. Ta yi kuka kamar ba gobe musamman yadda ta ga mijin ta ya susuce akan son 'yar aminin shi. 'Yar da idan da kara yace ya ba da ita ,ta badu kenan. Sosai tayi kaico da irin halin da ta sanya mijin ta a ciki ,ta yadda duk wani abun da zai je ya dawo laifin ta ne. Ta San bata kyauta wa mijin ta, d'anta da rayuwar auren ta ba ,kai hadda rayuwar ta kacokam. Ta yi matuqar tausaya wa mijin na ta da ita kanta. Gafarar ubangiji ta shiga nema ba dare ba rana ,Dan tasan matuqar ta mutu a haka ta shakka babu aljannah ko a gidan ubanta ake raba ta sai dai a raba babu ita. Da yake tana da rabo, watsar da duk wani rud'in duniya ta yi ,aikin ma tace ta aje ,ta dawo ta rumgumi auren da mijin ta hannu bibbiyu. Ta fara basa kulawar da a da can bata basa makamancin sa ba. Ta je ta cire tsarin iyalin da ta yi, a cewar ta bata son haihuwa da yawa ,Dan idan ta tara 'ya'ya za su hana ta aiki.. Ita dai aiki... Sosai ta ke iya bakin k'ok'arin ta na ganin ta kula da mijin ta. Hajj jamil ya ji dad'i sosai yadda Hajiya zaliha ta sauya lokaci d'aya, sai dai fa a gefe wutar son Haajar ne kawai ke dad'a ruruwa a zuciyar shi.






Ranar hutun k'arshen mako wato weekend Hajj jamil da Matar shi Hajiya zaliha tare da d'an su suka je gidan daddy. Fad'a sosai tare da nasihohi mai shiga jiki Hajiyar daddy ta dinga yi ma ta. Hajiya zaliha hadda hawayen ta. Ta yi wa Hajiya alqawarin insha Allahu za ta gyara. Yadda Haajar ke tafiyar da rayuwar ta yayi matuqar burge Hajiya zaliha ,wannan ya sa Hajiya zaliha ta so su had'a k'awance duk da cewar za ta girmi Haajar d'in. Kuma Haajar 'yar yayan mijin ta ne. Sai dai da yake babu wata shaquwa mai qarfi tsakanin su. Amma ta tabbata girman huhun goro ba shi bane. Saboda haka suka sha hirar yaushe rabo da Haajar. Har dare su Hajiya zaliha su na gidan daddy kafin su ka tafi. Tun daga ranar Hajiya zaliha ta samu wurin zuwa dan ta maida Haajar tamkar qawarta. Bayan sati d'aya sati biyu haka takan zo su sha hira sosai da Haajar. Shakka babu Hajj jamil ya ga amfanin zaman Matar shi da Haajar. Dan ba iya rayuwar su komai ya canza ba ,hatta a shimfid'a ya ji bambamcin na daban.
Bayan wata tara Haajar ta haifo santala santalan 'ya'yan ta mace da namiji. Namijin kama yake da daddy sak macen kuma kama ta ke da marigayiya Haseena. Murna a wurin wannan ahali abun Sai Wanda ya gani. Tun randa aka haihun Hajiya zaliha kullum ta na gidan ta na yiwa Haajar d'awainiya. Saura kwana biyu biki ,dangi na kusa da na nisa suka halatto ,da ma ga shi an dad'e ba'a yi sha'ani a gidan daddy ba. Musamman dangin Haajar d'in da wasu daga ciki sai dai suka ji labarin d'aurin auren. Yayyin ta da k'annen ta rankatakaf babu Wanda aka baro ,tare da Matar mahaifin su da ta zamo tamkar uwa a gare su. Kai! Haajar ranar ina ruwa ta tsoma kan ta Dan murna. Daga b'angaren daddy ma anga gayyar mutanen kano da kewaye. Hajiya zaliha ma ba'a barta a baya ba wurin yo tata gayyata. Ranar suna namijin yaci sunan Hajj jamil ana masa laqani da Hassan d'in shi, macen kuma taci sunan marigayiya Haseena ana kiran ta da hussaina. Taro ya yi taro anci ansha ,mai jego da 'ya'yan ta sun yi shiga daban-daban gwanin ban sha'awa. Duk Wanda ya zo taron suna da abun azziki yake tafiya. Banda kyaututtuka da zunzurutun kud'i da jariran suka samu daga wurin abokan su daddy. Hajj jamil kuwa kamar shi aka yi wa haihuwa ,Dan kusan komai shi ya yi. Barr Kabir ma sai da ya yiwa yaran kyautar naira dubu d'ari tare da akwatin kayan jarirai biyu. Hajiya ma ba'a barta a baya ba ,Dan kyauta ta yi Haajar d'in na musamman. Hatta Dr. Imam mahaifin Haajar sai da ya yo aike. Kai lissafa tarin alkhairan da Haajar da yaran ta suka sa mu b'ata lokaci na. Dan idan za mu kwana mu wuni ba zamu gama lissafe adadin abubuwan azzikin ba. Bayan su na mutane na ta watsewa. Ranar da 'yan uwan Haajar za su tafi ,kyauta daddy ya musu ba ni da kyauta ba. Sun ji dad'i matuqa sun kuma yaba da irin mijin ta Haajar ta samu. Bayan kowa ya gama tafiya. Haajar Sai da ta nemi inda za ta ajiye kayan yaran ,dan tsabar sun mata yawa. Uban gayyar kuwa wato daddy ,kyutar gidan gonar shi sukutum ya yiwa yaran shi. Haajar ba ta so ba Dan gani take abun ya yi yawa. Ga wa'yancan ga kuma wannan. Hadda k'wallan ta Dan farin ciki. Account Daddy ya bud'ewa yaran ya zuba musu duk kud'ad'en da suka samu. Haajar ta tambaye sa akan ya za'ayi da su yace ta yi amfani da su idan ta na da buqata Dan shi dai idan bai qara musu ba bazai karb'a sisi ba. Shawartar shi Haajar ta yi akan to ko ta bud'e gidauniya na taimakawa gajiyayyu da nakasassu. Daddy yace wannan shawara ce mai kyau. Hakan kuwa aka yi. Kafin kace me sunan Haajar da tallafin ta ya zaga sakkwato da kewaye.






Bayan sun yi arba'in. Suka shirya Dan zuwa gano Hajiya Gwaggo da ta dad'e a kwance ba tada lafiya. Gaba d'ayan su suka tafi. Yadda su ka samu Hajiya gwaggo kam rai hannun Allah. Washe garin zuwan su wata tsohuwa mai suna TANI ta zo gidan. Hannun ta d'aya a shanye. Aka tambaye ta wa take nema? Tace Hajiya Gwaggo. Nan aka kaita taga yadda jikin Hajiya gwaggon ya yi. Matar nan ta fashe da kuka. Nan ta soma basu labarin abunda ya wuce shekaru aru-aru. Ga Hajiya sakina a zaune kishiyar Hajiya Gwaggo ,ga hajiyar daddy da daddyn kan shi ,ga wasu daga cikin 'ya'yan Hajiya sakina. Haajar ma na daga gefe a zaune. Matar mai suna TANI tace "Tun suna 'yan mata sun gina rayuwar su akan Neman duniya da son zuciya ita da Hajiya Gwaggo. Ba su da aiki sai shiga malamai. A haka har suka yi aure. Ko da mijin Hajiya Gwaggo zai auro Hajiya sakina babu inda ba su shiga ba Dan su hana wannan auren ,amma duk inda suka shiga sai a ce musu wannan aure ba fa shi. A haka aka zo aka yi auren har Hajiya sakina ta fara haihuwa. Duk lokacin da Hajiya sakina ta samu ciki sai sun je an yi musu duba. Har lokacin da ta samu cikin mahaifin daddy aka fad'a musu cewa namiji za'a haifa, kuma mai arziki. Nan fa muka dinga k'ulla tuggu akan yadda za mu zubar da cikin amma Allah ya yi sai abunda ke cikin nan ya ta ka doran k'asa. To dama a lokacin Hajiya Gwaggon itama tana da ciki. Allah kuma yasa lokacin haihuwar su yazo rana d'aya. Mu ka yi amfani da wannan damar muka canza 'ya'yan. A inda muka d'auke d'an Hajiya sakina wato mahaifin daddy mu ka sauya shi da 'yar Hajiya Gwaggon Dan ace ita ta haifa. Ashe da ma 'yar da muka sauya wa muka ba Hajiya sakina ba mai zama bace, Dan tun kafin a yi suna Allah ya yi Mata rasuwa. Hajiya Gwaggo kuma ta ci gaba da rik'e d'an Hajiya sakina a matsayin na ta." Tsohuwar nan ta sake fashewa da kuka. Tace "Na ga jarabawar rayuwa da mugayen qaddarori da bazan so ace na mutu a ciki ba. Duk Wanda muka zalunta na yi ta k'ok'arin ganin na nema inda yake na ba shi hakuri. Nan ma kusan sama da shekaru goma ina Neman gidan amma Allah bai sa na gane gidan ba Sai yau." Tsohuwar na kuka tana Neman gafarar su. Hajiya sakina tace ta yafe mata ta ta shi ta tafi. Hajiya Gwaggo ko hawaye ne ya shiga wanke mata fuska ,tana so ta nemi yafiyar su amma ba dama ciwo ya ci qarfin ta. Hajiya sakina na hawaye tace wallahi ta yafe mata har ga Allah ta kuma gargad'e su akan ba ta yadda a fitar da zancen ba. Tun da har Wanda ake yi Dan shi ya mutu. Ranar kowa da abun ya kwana a rai. Abu sai kace wasan kwaikwayo. Washe gari kiran sallar farko na asubahi Hajiya Gwaggo ta amsa kiran ubangiji. Hajiya sakina ta yi kuka kamar ba gobe ,Dan ita har ga ba ta tab'a rik'e Hajiya Gwaggo a ran ta ba. Tana kuma matuqar qaunar ta har cikin zuciyar ta ,musamman jiya da ta ji ance ta riqe d'an da ta haifa. Abunda ta yadda da shi shine ,babu Wanda zai so naka har ya rik'e face masoyin ka...


























MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[8/26, 7:29 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI_


*____________________________*
















Misalin k'arfe Tara da safe aka yi jana'izar Hajiya Gwaggo aka kai ta makwancin ta. Kusan duk Wanda ya bud'e baki Allah wadai yake da halayyar Hajiya Gwaggo. Banda Hajiya sakina da ke ta faman kuka tana fad'in ta yafewa Hajiya Gwaggo duk abunda ta yi mata duniya da lahira. A gefe d'aya kuma ahalin gidan sai k'ara jimanta lamarin suke yi wai Hajiya Gwaggo ba ita ce ta haifi Baba Alhaji ba mahaifin Daddy,,, kai wannan Abu da d'aure kai yake. Ran da aka yi addu'an uku jama'a suka fara watsewa, yayinda wasu daga cikin ahalin wannan gida ke jin dad'in mutuwar Hajiya Gwaggo, a cewar wasu daga ciki ,ta gallaza musu ta addaba musu, su da gidan mahaifin su amma ba su da saqat. 'Ya'yan Hajiya sakina sai murna suke yi na kasancewar daddy d'an d'an uwan su ne. Suka zauna suka tattauna akan yadda za su k'arfafa zumuncin su, a ka saida magana cewa za'a dinga had'uwa anan gida duk bayan wata uku lokacin 'ya'yan su dake makaranta sun samu hutu, ya ka ma zama hud'u kenan a shekara. Wannan batu ya yi wa kowa dad'i. Daga su Haajar ba su baro ba sai da aka sanya ranar auren Suxee da Barr Kabir nan da wata uku me kamawa. Aka sanya na wasu 'yan matan wa'yan da 'ya'yar daddy wata biyu bayan bikin Suxee. Ba'a tashi daga taron ba saida Hajiya sakina ta yi musu wasu 'yan nasihohi masu ratsa jiki. Kusan dikkanin su da farin ciki suka watse cike da d'aukin junan su. Daga haka kowa ya watse, ciki yadda su daddy. Rayuwa ta dawo musu sabuwa.


Sannu a hankali 'ya'yan Haajar sai wayo suke yi. Bayan sun dawo kano ba Dad'e wa ba, Haajar ta fara shirin ta na zuwa gida Jigawa Dan dubo 'yan uwanta. Tare da suxee ta tafi, a yayin daddy ya ba su driver sannan ya cika su da kayan arzuka a cewar shi su yi tsara. Ya kum shaida masa ze biyo bayan su shima ya gaida ahalin ta. Kwanan su Haajar biyu da tafiya Daddy ya shirya shima ya tafi. Babu Wanda bai ji dad'in zuwan su ba. Dan kusan lungu da sak'o na 'yan uwan Haajar babu inda daddy be sa Ankai shi ba ,duk

Please Login or Register in order to submit comment