Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BUSHEWAR GABA NA MATA DA KUMA KARANCIN NI'IMA (VAGINAL DRYNESS AND LOW SEXUAL PLEASURE) DA KUMA HANYAR MAGANCE MATSALAR A SAUKAKE


Idan muka ce ni'ima to muna magana ne akan sha'awa waton (libido) a Turance kenan. Tana taruwa ne ga matan da suka balaga, masu koshin lafiya, walau budarwa ce ko kuma matar aure.
Sha'awa halittace wacce ta banbanta daga wata mace zuwa wata macen. A lokacin da mace take jin sha'awa haka kawai ko sanda take karanta wani labari ko tinanin wani abu dake motsa sha'awa ko a yayin da ake gabatar da wasanni (fore play) kafin saduwa to idan dai har tana da ni'ima to zata ji duk ta jike dan wasu fararen ruwane masu yauqi zasu rinka fito mata. A lokacin ta riga ta kamu kenan wannan ne ake kira Natural lubrication ko Vaginal wet wanda idan har za a sadu da ita a lokacin to a shirye take. A hakika shima mai gidan zai yi matukar gamsuwa da ita. Bazata ji zafi ko ciwo ba saboda ta jika sosai ta yanda bata bukatar ayi amfani da wani vaseline ko ointment. To wadannan ruwan masu yauqi dake fitowa mace a sanda sha'awarta ta motsa to ita ke nuna alamun tana da ni'ima. Wasu matan sun fi wasu yawan sha'awa da samun ni'imar jiki dan yanayin halitta da lafiya, da ma abincin da suke ci ya sha banban. Wasu matan tun fil azal suna da ni'ima mai tarin gaske. Amma daga baya takan gushe sai su rasa sanin dalili. Hakan zai sa su tsunduma suyi ta neman kayan mata suna cusawa kansu abubuwa masu cutarwa duk da sunan ni'imarsu ta dawo. matsaloli da dama kan faru a sanadin haka.
Akoi matsaloli da rashin lafiyoyi da dama dake haifar da gushewar ni'ima ga mata, wadanda suke bukatar bincike a maimakon haka mata da dama sukan yanke hukuncin cewa ai ciwon sanyi ne ke gare su alhali wata matsala ce ta daban. Akwai matan da basu da ni'ima a koyaushe gabansu a bushe yake ba wata ni'ima ko jin sha'awa. wasu matan sai sun shafa vaseline kamin a iya saduwa dasu. Hakan kan haifar da rashin samun gamsuwa musamman ga maigidan. Cushe cushen da mata ke yi da sunan matsi yana daya daga cikin abinda ke zuqe ni'imar mace ya haifar mata da bushewar gaba Musamman in abinda suke cusawar bai dace da Farjinsu ba, misali amfani da ruwan bagaruwa wacce tana matse fata amma kuma tana zuqe damshin dake ga wurin gaban mace, zai matse amma kuma zai kasance a bushe.To miye fa'idar yin haka kenan ?
Maigida na saduwa dake amma yana jin kamar ana zoza mashi katako.
wasu cushe cushen na haifar da cutukan gaba da kuraje da kaikayin gaba da irin wani wari wanda ke kanki sai ki rasa wanne irin wari ne? Dan an dauki wani abun na daban an tura a inda bai dace ba. Akwai magani Natural fruits da mata zasu iya rinka amfani dasu dan su karawa kansu shawa da ni'ima kai hattama da koshin lafiya.
Kamarsu kankana ,ayaba, gwanda abarba, lemu ,timatir ,rake, dabino, kwakwa, dafaffiyar gyada, zuma ,nono, zogale, ridi, ruman cukwi(Nonon Rakumi), inabi, tuffa, zaitun, tafarnuwa, albasa, da dai Sauransu


Wallahi wadannan duka sun fi duk wani cushe cushe ko kayan sha na mata da kuke gani amfani da kuma saukin saye.


Zaki iya cin ayaba da dabino a yau.
Gobe sai ki canza ki nemi kankana ki sha, jibi ki nemi dafaffiyar gyada ki ci, gata ki nemi zogale da albasa da quli quli kiyi datu/Kwadanta ki ci. sai kiga kina ta canzawa lokaci zuwa lokaci.
Wallahi ina baki tabbaci idan kinka rike haka to ba wai ni'ima ba ko lafiya da fatar jikinki zaki ga tana canzawa.
Amma an rungumi kayan maiqo da kayan zaqi da kayan yaji kawai ake ci dare da rana ana ta faman shan kayan mata da cushe cushe amma a banza dan ba sune abinda jiki keda bukata dasu ba ai dole shawa ta ja baya.
Haka kuma zaki iya hada wadannan dan karin ni'ima da gamsarda mai gidanki. Amma akwai bukatar a kiyaye da tsabta. mata a daina cusa duk wani magani a cikin gaba wanda Bai dace da farji ba, farjin mace kaman ido yake baya son bako. A dinga tsarki da ruwan dumi amma banda sanya sabulu.
A daina sanya pant da bai bushe ba. Idan an wanke to a rinka shanyawa har sai ya bushe.
A ringa yi ana canza shi akai akai.
Banda yin musanya da fatar za a kula.


Ga wannan hadin sai a jarraba
za a iya daukar daya ko biyu daga ciki ayi amfani dasu.


1-Qwai (Egg) da albasa da timatir, sai a soya amma kada a bari suyar ta kone. Banda sanya maggi da gishiri da yawa.zaki iya sakawa amma dan kadan ake so.
Namiji zai iya ci hakan zai kara mashi da yawan ruwan maniyi.


Za a iya neman garin dabino da ruwan kwakwa sai a dama a rinka shan cokali biyu manya chokali safe da yamma.




KARIN NI' IMA═
"Yan mata ya kamata kusan mene yake kone muku fadamarku kafin jika lambunku da ruwan taimako! Kisani babbar lillah ce kice ke baki da sanyi ajikin ki wannan abinda bazaiyuba ne sannan baki shan magani da neman sa wannan jahilci ne anan inaso ince sanyi shine musabbabin kowace chuta ajikin dan Adam haka annabi ya fada hk km binkicen kowane sashi na binkeci ya nuna. Saidai sanyi ya rabu izuwa kasu dayawa dan bazan ace ga adadinsaba amma sanannu guda 2 ne wato sanyi na maza dana mata ackn 2 akwai kashe kashe misali sanyin mara sanyin daji sanyin laka sanyin hakori sanyin qashi sanyin dubura.
Sanyi yana da siffa kala kala ya danganta da larurar data kawoshi mu anan zamu dau sanyin mara wanda shi ke kawo bushewar niimar mata.


Abubuwan dayake janyo sanyin Mara
~1 samu daga miji mai namijin sanyi
~2 yin tsarki da ruwa me sanyi
~3 zama a inda danshi ko raba take
~4 yawan shan abu me sanyi sosai
~5 rashin kula da al'aura
~6 sanya yatsa ackn fari
~7 gada daga mahaifa
~8 yawan zama a turbaya
~9 yawan tayarwa da kai sha'awa
~10 rashin abinci me gina jiki
Wadannan sune abubuwanda samuwar su duka ko mafi yawa dg ckn su yakan jawo gushewar ni'ima_


magani
~Kankana
Kaninfari
~Zuma
~Tafarnuwa
Wannan hadin bashi da bukatar a hada da yawa daidai yanda za a iya sha za ayi kuma sau daya ake sha a rana har tsawan sati 2 wato kwana 14
Za a sami kankana ynd ake da bukata ko a yanka ko burgeta a blander duk dayane sai asami dakakken kaninfari chukali daya na yara azuba sanan zuma karamar roba a zuba duka ack sannan tafarnuwa danya adaka guda 4 in qananuce in babbace kwalli 2 ko 3 ta isa faffasata za ayi ta dandaku sai azuba a bashi kamar minti bakwai 7 sai asha kenan za a iya hadawa bayan angama cin abinci sai ashanye gaba daya.
In akabi doka to za a zauna lfy Allah kasa mudace!










MUJE ZUWA💃




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️




[8/26, 7:29 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARABA'IN DA TARA_


*____________________________*








GYARAN JIKIN AMARE DA UWARGIDA


Amfanin Garin Hulba Don Gyaran Jiki Gyaran Fuska. Za ki samu garin hulbar ki dama da madara da zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskar ki, ki barshi kamar minti talatin kafin ki yi wanka, fuskar ki zata yi sheki zai kashe miki pinples ya gyara miki fuska.


BAMBAMCIN MACE MAI DADI DA MARASHI:


Maza da yawa suna tafka muhawara akan shi mata suna da bambamcin dadi a wajen jima'i kodai dukkaninsu haka suke. Wasu sunce duk abun iri daya ne. Wasu kuma suce sam da akwai bambamci. Gaskiya ne mata sun bambamta a dãɗi na jima'i. Sai dai kuma wannan dãɗin ba abune da ake haifar mace mai dãɗi ko mara dadi ba. Ita macen ce take maida kanta mai dadi ko ta zama mara dadi. Akwai wasu mahimman abubuwan da suke sa mace tayi dadi ko kuma akasin hakan. Waɗannan abubuwan idan mace ta sansu, ta iya su kuma tana yinsu dole ne mijinta yace tana da dadi. Idan kuwa bata yinsu bata sansu ba to irin waɗannan matan ne maza suke kira da suna jaka. Sai dai kuma ba duka abubuwan dake sa mace dadi ake samu daga gareta ba. Akwai wasu daga shi mijin nata suke wanda idan babu su a gare shi to babu dãɗin da zai ji duk lokacin da zai yi jima'i da matarsa.


Ga wasu abubuwan da suka bambamta mace mai dãɗi da marashi.


1: Soyayya - Duk yadda mace take muddin babu soyayyarta a zuciyar mijinta ba zai taba jin dãɗin ta ba ko sau nawa zai kwanta da ita. Don haka danƙon soyayya a tsakanin ma'aurata yana kara sawa namiji yaji dãɗin matarsa a lokacin jima'i.
2: Shauƙi: a lokacin da namiji ya kamu da sauƙin son yin jima'i da matarsa a wannan lokacin yana samu jin dadi na musamman idan yana saduwa da matarsa. Ba kamar lokacin da bai da sha'awar yi ba amma aka nemi yayi.
A lokacin da namiji da kansa yake cikin bukatar matarsa a wannan lokacin idan zai yi jima'i da ita yafi jin dãɗin ta.
3: Tsafta-duk yadda miji yake son matarsa kuma yake da shaukin son yi jima'i da ita idan batada tsafta zai dai biya bukatarsa ne amma ba wai saboda yana jin dadi ba.
Matan da suke barin gaban su babu tsafta ko bakin su, hamata da sauran lungunan jikunansu babu tsafta. Irin waɗannan matan namiji ba zai taba jin dãɗin yin jima'i dasu ba sai dai kawai ya biya bukatarsa amma ba domin yaji dãɗin ta ba.
Ita mace mai tsafta bayaga dãɗi da take sawa mijinta yaji, ta kan kuma sashi a kullum yaji ya kamu da son yin jima'i da ita.
4 :Ni'Ima- ba kowace mace take da ni'ima ba. Wasu matan gaban su a bushe yake karas. Wasu kuwa a jike yake cakaf.


Yawan ni'imar gaban mace yana karawa namiji jin dãɗin ta sosai a lõkacin da yake saduwa da ita. Wannan yasa maza da dama suke danganta mace mai yawan ruwa a gabanta itace mai dadi. Shi dai ni'imar gaban mace ba wai halitta bace wanda za ace wata an halicce ta dashi wata kuwa haka Allah Ya yita kandas. Duk mace tana iya samarwa kanta ni'ima idan tana bukatar yin hakan. Saboda akwai abinci da abubuwan sha da suke sa mace ta samu ni'ima da kuma masu kara mata idan tana dashi. A lokacinda namiji yake saduwa da mace mai ni'ima wannan ruwan gaban nata yana kara taimakawa wajen samun sauƙin shige da fita da azzakarin sa ke yi cikin farjin matarsa. Wanda hakan yake samar masa da wani dadi na musamman a lokacin jima'i. Sabanin macen da gabanta yake bushe. Wanda maimakon ta samar da ɗaɗin tana ma iya jin ciwo a gabanta kuma ta jiwa mijin nata shima. Mazan da matan su suke da bushenshen farji fatar jikin azzakarin su yana iya sullubewa ya daye saboda rashin samun ruwan da zai rika taimakamawa wajen shiga da fita. Wanda ita ma gabanta zai iya yin jini kuma ta rika jin zafi idan ana saduwa da ita saboda rashin ni'ima a jikin ta.
Don haka mace mai ni'ima tafi mara shi dadi a jima'ince.
5. Iyawa- Macen data iya jima'i na kwarai ta kuma saki jiki tafi sabuwar shiga 'yar koyo dadi a jima'ince.
Domin ba wai kawai a zura azzakari cikin farjin mace bane kaɗai zai samarwa maigida dãɗi dake kunshe cikin jima'i. Da akwai wasu sinadarori da ake hadawa dasu kamin mace ta samarwa mijinta hakikanin jin dãɗin jima'i. Waɗannan abubuwan kuwa suna hada kamar haka:


I: Iya wasannin motsa sha'awa. Macen data iya wasanni da mijinta ba zata taba yin daidai da wacce bata iya ba. Don haka muddin mace ta san abubuwan da mijinta yake son a masa a lokacinsu na wassanin motsa sha'awa dole ne a wannan jima'in ta jiyar dashi dadi.
Ii: Iya yanayin kwanciyar jima'i - dole mace ta iya yin yanayin kwanciya na jima'i daban daban idan har ta son mijinta ya rika jin dãɗin ta.


Kowani namiji yana da yanayin daya fi so matarsa ta masa a lokacin jima'i. Muddin kuma bazaki iya masa wannan ba babu yadda za ayi yaji dadinki.
Iii: Tsukewa da sakewa- akwai wasu mata yadda aka shege su haka nan suke sakin gaban su ba tare da sun daidaita shi yadda azzakari zai iya samun daidaito a cikinsu. Macen da take da faffadar farji, yana da kyau a lokacin da maigida ya shigeta ta tsuke farjinta yadda zai matsai azzakarin mijin a ciki.
Haka kuma idan karamar gaba ce da ita sai tayi kokarin kara bude kafafuwanta domin baiwa azzakari damar gudanarwa. Wannan yanayin na tsukewa ko matsai farji a lokacin jima'i, yana samar da ɗaɗin na musamman ga namiji. Ba kamar macen da zata saki komai yadda yake ba.
Iiii: Sumbatu: Yana matukar karawa maza jin dãɗin jima'i sosai amma akasarim mata basu da masaniyar hakan. Sumbatu musamman na kwarzanta mai gida ko masa koke koke na kissa da furta wasu kalamai na batsa suna da matukar tasiri a lokacin jima'i. Domin suna samar da jin dadi na musamman a yayi jima'i. Ba mace ta yi gum bata cewa koma ba.
Iiiii: Tallafawa. A lokacin jima'i ba wai namiji bane kadai mace zata bari yana gwatso ba. A duk irin yanayin kwanciyar da zai baiwa mace damar ta motsa jikinta, to idan zata tallafawa maigida wannan ma yakan samar da jin dãɗi maimakon mace bata motsi na yi kamar gawa.
Waɗannan sune wasu mahimman abubuwan da zan iya kawo su a fili da suke sa namiji yaji dãɗin jima'i da matarsa. Kuma sune suka bambamta mace mai dãɗi da mara dãɗi.


RASHIN GAMSAR DA UWARGIDA / AMARYA INA MAFITA


A kullum na duniya maza ma'aurata suna saduwa da matansu, sai dai kuma abun tambaya anan shine, maza nawa ne suke iya gamsar da matayen nasu a lokacin da sukayi kwanciyar ta jima'i? Maza nawane magidanta suke da illimin sanin yadda zasu gamsar da matansu..? Ko munki ko munso babu yadda zamu kaucewa magana a kan jima'i domin shine ginsheken zaman aure kuma yana cikin manyan lamuran da kan iya sa a samu zaman lafiyan ma'urata ko akasin hakan. Yana da kyau da kuma mahimancin maza su fahimci cewa, duk wata mace tana sha'awar ganin cewa mijinta yana matukar gamsar da ita yayin da suka yi kwanciya ta jima'i. Sai dai kuma abun ban haushi maza da dama suna dauka cewa gamsar da mace a jima'ince shine saduwa da mace da karfi ko kuma da mugunta ko jigatata shine zai iya gamsar da mace. Mafiya yawan maza basu da illimin sanin cewa mace takan dauki lokaci mai tsawo kamin ta kawo, kai duk da yake da akwai wasu matan da suke yinsa cikin karamin lokaci. Don hakane yake da kyau maza su gabatar da wasanni ga mace kamin su afkamata. Kamin mace ta kamu, dole ne sai an tattabamata wasu wurare ta hanyar sumbata, wasa da nonuwanta, gabanta da makamantan su. A wannan lokacin ne mace jinin jikinta yake bin ko ina a jikinta daga nan kuma sha'awa ya motsomata harta nemi bukatar mijinta. Mundin namiji ya jefa matarsa cikin wannan yanayi zai ji dadin yin jima'i da ita haka kuma ita kanta matan bazata yi koken rashin gamsuwa bayan an gama ba. maza masu murza matayensu a lokacin wasannin motsa sha'awa, mazane da suke sa matansu gamsuwa da zuwan kai cikin sauki kuma akai akai. Kada kayi gaggawar shigar matarka, ka tabbatar ka dauki lokacin kamar mintuna 25 zuwa 30 kana wasa da ita har sai lokacinda tayi laushi da kanta tana bukatar ka shigeta. Mata da dama dai sukanyi sha'awar gani
mazansu ne ke tubesu da kansu a lokacin da ake tsaka da wasan, yadda kuma a yayin wasan kana tube mata kayan dake jikinta daya bayan daya kamin kashiga wasa da muhimman wuraren dake motsa mata sha'awa. Da yake bazan yi bayani dalla-dalla na yadda ake wasa da mace da kuma wuraren da ake wasan dasu ba a wannan fagen, yanada kyau maza su fahimci cewa ko wace mace da inda ke tayar mata da sha'awarta. Wata da zaran an soma shan bakinta sha'awata ya motsa, wata kuma wasa da gabanta, wata murza kan nonuwanta watama kunnenta kawai za'a taba ta fara
d'iga, dole ne kowani magidanci ya fahimci meke tayarwa matarsa sha'awa a lokacin wasanni.


Mahimmancin wasa da mace kamin soma jima'i shine, zai sata ta soma fitar da ruwa wanda ruwan yana taimakawa shigar azzakari cikin farjin mace da sauki. Haka kuma yana taimakawa mace tayi zuwan kai cikin sauki ba tare da ta dau lokaci ba. Girman azzakari, ko tsayinta bashi ne abu mafi mahimmanci ba a wajen mace, abun da kawai yake sa mace ta samu zuwan kai da kuma gamsuwa a yayin jima'i, shine yadda aka motsa mata sha'awarta a lokacin da ake wasa da ita shine abunda yake sata nan take ta samu zuwan kai da kuma gamsuwa irinta jima'i. Babu saduwar jima'i mafi dadi wajen mace irin tayi zuwan kai lokaci guda da mijinta, wanda bincike ya nuna cewa maza 100, 30 ne kawai suke iya yin zuwan kai lokacin guda da matansu, hakan kuma yana samuwa ne ganin yadda suka lakanci jima'i da matan nasu. Shi dai zuwan kan 'ya mace, shine kololuwarn jindadin kwanciyar jima'inta, kuma shine yake jawo gamsuwarta a jima'ince, don haka da zaran wasu matan sun samu gamsuwa to sha'awarsu ta jima'i kuma ta kare a wannen lokacin, duk kuwa da wasu matan da ake samunsu suna iya zuwan kai kamar sau biyu zuwa biyar a kwanciyar jima'i guda, hakan yana danganta ne da irin halittan macen da kuma yadda mijinta yake sarrafata a jima'ince. Shi dai zuwan kai 'yan mace ba kamar na miji bane, domin shi namiji idan yayi zuwan kai abune da ake iya ganinsa a zahiri saboda yadda maniyi yake fita daga azzakarinsa.
Wasu na daukar cewa, ruwan dake fita daga gaban mace a lokacin saduwa da ita
Ruwa iri biyu ne yake fita a gaban mace a lokacin da ake wasa da ita wani ruwa mai yauki ne yake soma fitowa, wanda yake
alamta cewa ta soma kamuwa kenan, haka kuma idan ana saduwa da ita kuma da akwai wani farin ruwa wanda yafi kama da madara shima yana fita daga gabanta, shima wannan bashi ne alaman mace tayi zuwan kai ba.


A lokacin da mace tazo kawowa, a wannan lokacin kamanninta sukan canza, numfashinta yana yawan bugawa da sauri, haka kuma jinin jikinta guduwarsa na karuwa sosai haka kuma jijiyuyin jikinta zasu kara bayyana yayin da zata yi wani kara ko kuka ko fadan wata kalmar dabata sanshi ba a yayi zuwan kan nata, haka kuma mata da dama suna kankame mazajensu a lokacin da suke zuwan kan.
Da akwai yanayin kwanciya na jima'i da yake taimakawa mata domin yin zuwan kai cikin sauki a lokacin jima'i, sai dai kuma ganin babu dama da zamu kawo komai da komai a wannan anan nake baiwa ma'aurata su nemi ilimin jima'i Sai dai kuma kamin wannan lokacin, ya kamata maza su fahimci cewa da akwai illa ga duk namijin da bazai iya gamsar da matarsa ba a jima'ince, don haka ne nake bada shawara ga maza su nemi sanin illimin yadda zasu iya sarrafa mata


MATSALOLIN MA'AURATA KAN SOYAYYA:

Akwai wasu abubuwa da suke canja soyayya bayan aure sai ka ga an sami canje-canje, da ana soyayya kamar a hadiya juna amma da zarar anyi aure bayan lokuta kadan sai ka ga soyayya ta canja. Akwai dalilai da suke kawo hakan gasu kamar haka:


1.Rashin yin aure dan Allah ko kuma an gina soyayya akan karya ko anyi aure dan samun wani abun duniya sai kuma aka rasa. Sai ka ga ana canjawa juna fuska.
2. Rashin abubuwa guda 5, akwai wasu abubuwa guda biyar sune manyan bukatu na dan-adam ba a dakin aure ba koda a gidan kurkuku yake yana bukatar abubuwa 5 a duk inda yake dole ne a samawa mace su in ko ta rasa su to baza ta iya zaman aure ba kuma yanzu soyayya zata canja zuwa mummunan yanayi. Gasu kamar haka:


-Samarwa mata da abunci
-Bata suttura
-Kula da lafiyar ta
-Bata tsaro
-Samarwa mata da mahalli.


Abunci, suttura, muhalli, tsaro da lafiya su zama dole a kulawa mace su da zarar an rasa su sai kaji ana kace nace tsakanin ango da amarya.


Masu iya magana suka ce abu uku basu haduwa a azauna lafiya, suka ce ango da amarya da kuma yunwa.


3. Gina aure akan sha’awa. Da zarar an gama rayuwar angwanci karsashin sha’awa ta gushe sai ka ga an canjawa juna fuska.
4. Wasu canje janje da suke shafar mace bayan tayi aure. wato kamar lokacin hailar mace kan jin dan damuwa da kunci, hakan kanshafi zamantaker aure.


(samunciki da goyo )suma kan takurawa mace ta ji damuwa har hakan ya shafi zamantakewar ta ta aure.


5. Rashin bawa samari da ‘yanmata cikakken bayani da sirrin rayuwar aure tunkafin suyi aure.
6. Rashin daukar aure amatsayin ibada.
7. Rashin kwanciyar hankali,imma daga ‘yan’uwan miji ,uwar miji.
Kashj 95% na matsalolin ma aurata bayan aure wadan nan matsalolin ne na sama.


Taya za a magance su?


Kada ayi aure har sai an cika sharudan shari’ah kamar samun sana’a,iya samar da mahalli, abunci, suttura, lafiya, tsaro. Yin aure dan Allah da daukarsa a matsayin ibada kamar sallah, azumi. Bawai zaman hutuba dole ne a ware cibiya ta musamman mai wayarwa samari da ‘yanmata kai akan harkar zamantakewa akan hakkin ma’aurata da yadda zamantakewa take. Yana da kyau maza su san cewa mata masu ciki ko haila suna dan samun canji a jikin su dan haka ana hakuri da su a lolacin.


Wace ce Mace?


Mace dai ta kasance tamkar wani furen fulawa. Wanda idanun mutum suke sha’awar kallo a koda yaushe, ita fulawa ta kasance abu ce mai kamshi.


Haka bayan kyawun kallo, tana da bukatar kasancewa a cikin inuwa, domin idan aka sanya ta a rana za tayi yaushi. To tamkar haka mace kan kasance a wajen sanyaya zuciya, da sanya farin ciki a zuciyar abokin rayuwarta.


Wannan kuma tun ran gini tun ran zane, domin kuwa mace, tun tana ‘yar karamar yarinya ta kasance mai kokarin son yin hidima ga wani, domin hatta wasanta na yarinta ba ya wuce na kula da jaririyarta (‘yar baby), ta kara ce, ko ta roba. Tare kuma da son taya mahaifiyarta aikin gida. Kuma a gaba haka za ta kasance har bayan ta girma tayi aure inda take zama rumfa, kuma ta zama garkuwa ga dukkan mutanen gida ta hanyar sadaukar da rayuwarta domin ta faranta masu da haskaka masu hanyar rayuwa.


Wannan ya ta’allaka tun daga mijinta da ‘ya’yanta da dangin mijinta da makotansu. Za ta kasance cikin hidimarsu ta yadda takan kasance tamkar wata baiwa wadda ita ba ta ma san wani abu jin dadi ba. Haka za ta rika gudanar da hidima ga iyalinta, kowa ya riga ta kwantawa domin yin bacci, kuma ta riga kowa tashi don ta share masu fagen fara rayuwa a wannan sabuwar rana.


Da irin haka kuruciyarta za ta tafi cikin hidimar gyaran al’ummarta, kyawunta da kuruciyarta da karfinta da komi nata a hankali haka za su gushe amma ba ta damu ba, manufarta daya ce rak wato sanya wa kowa farin cikin rayuwa da mika su zuwa ga ingantacciyar rayuwa har su kai ga burinsu.


Mace duk a cikin wannan tashi fadin da take yi abu daya kawai

Please Login or Register in order to submit comment