Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ranar suna yaro yaci suna Mahmud. Kusan tare Haajar da suxee suka yi jego...






















MUJE ZUWA πŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[9/1, 3:04 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*






πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


_BABI NA HAMSIN DA BIYU_


*____________________________*


















Bayan suxee tayi arba'in ,Haajar ta rok'i daddy akan tana so ya bar su suje suga dangi itada suxee da kuma auta ,bai gaddama yace Allah ya kiyaye hanya, sai dai ya musu fad'a saboda jariran yara da suke da su ,har ma yace ze had'a su da 'yar taya raino Dan kar abun ya musu yawa. Su Haajar suka shirya tsaf, saida suka fara zuwa kano wurin Hajiya sakina ,Hajiya sakina tayi murna da ganin su matuqa, gidan yayyin baban daddy ma duk sai da suka zaga gidajen wa'yanda ke aure a nan jahar kano. Duk Wanda yagan su sai ya ji dad'i ,abun azziki kuwa sun samo su ,su turarukan wuta ne ,humra ,zannuwan gado ba'a magana ,kowa so yake aje idan gidan shi, idan aka je kuma baya barin su su fita hannun rabbana. Haqiqa dangin daddy masu karamci ne ,Dan iya kara su Haajar sun gan shi. Satin su d'aya a kano zuwa wuce jigawa gidan su Haajar, nan ma fa kar kaso kaga yadda jama'a ke sintirin zuwa gaishe su. Nan ma saida suka yi sati biyu ,kafin suka fara shirin tafiya. Daren da zasu tafi Haajar ke tambayar suxee inda dangin Kubra suke? Suxee ta dad'e tana jimanta tambayar ,kafin ta sauke wani guntun ajiyar zuciya tace "A gaskiya Anty Haajar idan nace miki ga inda suke na yi k'arya. Dangin mahaifin ta ne dai kam sunan nan a katsina ,an tab'a zuwa dani tun ina qarama ,amma idan nace miki zan gane wurin yanzu gaskiya na fad'i ne kawai Dan inji dad'in baki na". Haajar ta jimanta maganan kafin tace " to wai Dan me baku San su ba? Ba'a kai Ku ne?" Suxee tace "wacce ma ta zama musu dole ba zuwan take ba ,Dan tunda nake da mummy so d'aya naga taje katsina shine zuwan da aka yi dani da kuma Haseena lokacin ba'a haifi Auta ba. Sannan idan suka zo wurinta wulaqanta su take yi tana ganin kamar Allah ya fifita sama da su ,gani take kowa d'an cin azziki ne ,ganin haka yasa ka kanta yace duk Wanda ya sake takawa zuwa wurin ta Allah ya isa ,ba da miyon bakin shi ba, ya kuma yi mata mummunan fata. Allah ya jiqan Haseena da gafara ,,ta yiwa Mummy fad'an akan ita idan ba zata je ba mu tasa akai mu ,amma taqi. Ita ala dole ubanta mai kud'in da Dan ba na yanzu ba ,kuma tana auren 1 in town billionaire." Haajar ta dad'e tana jinjina magana kafin daga bisani tace "to yanzu baki San Wanda zamu iya samun labarin inda suke ba a katsinan?" Suxee tace "gaskiya bansani ba. Amma meze hana ki kira Hajiya inaga ita zata iya Sani, tunda mijin ta abokin Baban mummy ne lokacin yana da rai."






Da wannan Haajar ta yanke shawarar kiran Hajiya ta tambaye ta. Da har ta bari sai zuwa da safe ,sai kuma ta duba agogo taga 11 saura na dare ,tasan Hajiya tayi bacci a wannan lokacin amma ba ta da wani zab'in daya wuce ta kira ta. Wayar ta ta d'auko tare sa kamo lambar Hajiya, sai sa kiran ya kusa tsinkewa sannan Hajiya ta d'aga, Haajar tayi sallama ,Hajiya ta amsa cikin muryar bacci tare da cewa "lafiya kuwa Haajar naga kiran ki da daddare?" Haajar tace "bakomai wallahi Hajiya. Kiyi hak'uri na tashe ki daga bacci. Dama so nake in d'an tambaye ki?" Hajiya tace "alhmdllh tunda ba wata matsalar bace. To inajin ki" nan Haajar d'in ke tambayar ta akan ko tasan inda dangin mahaifin Kubra suke a katsina? Hajiya ma jin maganar tayi kamar daga sama, amma tunda ta yadda da Haajar bata da wani sauran shakku akan ta, nan tayi mata kwatance ,ta kuma gaya mata sunan Wanda zasu tambaya idan sun je garin Rinjim. Haajar tayiwa Hajiya godia sannan ta yanke kiran...








A akwati d'aya suka shirya kayan su ,suka bar sauran anan ,haajar tace sai idan sun dawo su biyo tanan dan kar su yita yawo da kaya. Washe gari suka shirya tunda sassafe suka kama hanyar katsina, Auta na bacci bata ma San sun tafi ba. Basu wani sha wahala ba suka isa garin Rinjim. Nan Haajar tayi tambayar sunan Wanda Hajiya tace su tambaya idan sunje garin wato MALAM NA ALLAH. Sanannen mutum ne kuma babban Malami ne a garin Rinjim. Cikin ikon Allah basu wani sha wahalar da suke tunani ba aka kai su gidan. Gidan gidan k'asa ne ,daka gani kasan irin ginin da ne ,daga cikin gidan idan ka shiga kai da ka gani kasan anyi kud'i a gidan ko yanayin tsarin kawai ka duba. Ko ina a share tsaf ,da alama masu gidan Nada tsafta. Sallama suka yi ,shiru ba Wanda ya amsa ,suka sake yi a karo na biyu ,nan ma shiru ,suxee tace "anya kwatancen nan daidai ne ma kuwa?" Haajar ta sake yin sallama ,sai ga wata tsohuwa ta fito, tace "sannun Ku yara! Wa kuke nema?" Haajar ta sunkuya ta gaishe ta ,sannan ta fad'a mata wurin malam suka zo. Tsohuwar nan tace "daga ina za'a ce masa?" Haajar tace "kice masa daga sakkwato". Nan wannan dattijuwa ta koma ciki dan sanarwa malam zuwan bak'in...








Mintuna biyar da shigar tsohuwar nan sai ga wani dattijo ya fito yana duban k'ofar shigowa ,da fara'a ya tarbe su kamar yasan su yana fad'in "lale maraba da bak'i". K'arasawa suka yi suka kwashi gaisuwa ,sun san ko ba'a fad'a ba shine Malam Na Allah. Ciki ya shiga dasu yasa aka yi musu shimfid'a ,aka kawo musu fura mai sanyi damun kindirmo zallah. Haajar tasha sosai tayiwa Allah godia sannan itama suxee tasha. Nan take garin Ringim ya d'auka ,malam yayi bak'i ,aifa sai zuwa gaishe da su Haajar ake yi. Abun yata basu mamaki ,bayan sun yi sallar azahar malam ya dawo ,suka sake gaisawa ,Haajar tace " malam baka tambaye mu mu su waye ba?" Murmushi dattijon nan yayi tare da cewa "Haba jikata! Kun fa ce daga sakkwato kuke? To ai ko baku fad'a ba nasan ko Ku su waye ,ga kama nan. Wannan ko ba'a fad'i ba nasan jinin Hadiza ne" ya fad'a tare da nuna suxee dake zaune. Mamaki ne ya cika cikin Haajar. Aifa nan malam ya dinga basu tarihi ,da labaran ban dariya. Su Haajar sun yi matuqar jin dad'in kasancewa da shi. Haajar tace "Baba amma kunsan kuwa Allah ya yiwa Kubra rasuwa?" Murmushi malam ya sake yi Wanda yayi nasarar bayyana jajayen hak'oran shi yace "K'warai kuwa mun Sani jikata." Haajar tace "baba to amma meyasa Baku je ta'aziyya ba?" Malam yace "Allah ya gafarta Mata ya kuma yafe mata". Mun yi mata addu'a daga nan ,karki damu.








Ganin kamar baya son maganar yasa Haajar ta bar shi suka d'auko wani. Bayan magriba bayan malam ya dawo daga sallah ,ya aika aka kira masa Haajar. Ya tambaye ta game da labarin kubra, Haajar bata b'oye masa komai ba ,ta fad'a masa cewa ita matar daddy ce ta kuma sanar da shi duk abunda ya faru Wanda aka yi tana nan dama Wanda hajj jamil ya bata labarin anyi kafin zuwan ta. Har zuwa mutuwar kubra da dawowar kuruwan ta jikinta... Malam ya girgiza Kai yace "kaico!!!kaico!!! Albasa bata yi halin ruwa ba. Bazan dena tir da Allah wadai da jinin Hadiza ba Dan ita tazo ta yad'a mana gurb'ataccen jini a zuri'ar mu." Haajar ta tambaya wacece Hadiza? Dan tasan sunan kubra ne. Malam yace mata "mahaifiyar kubra itace me wannan sunan Wanda a wurinta kubra taci wannan sunan." Nan malam ya fara bama Haajar tarihi tun kafin d'an shi ya auro mamar kubra. Da tarihin tsafin ta. Malam yace har yakai ya kawo saida aka raba shi da d'an shi daya Haifa ,daga k'arshe yaji labarin mutuwar sa ,daya tsananta addu'a sai ya gano Ashe abun tsafi aka sadaukar wa jinin d'an shi. Daga baya itama mutuwar ta bai yi kyau ba ,Dan mafi munan mutuwa tayi Wanda har yakai ya kawo tana fizgar naman jikin ta tana ci. Malam yace kubra ita kad'ai ce 'ya a wurin Hadiza ,kuma itama a binciken shi ya gano cewa ta sadaukar wa tsafi da ita tun kafin ajali ya riske ta. Malam ya tabbatar wa Haajar cewa gawar kubra ne kawai a makwancita amma a zahirin gaskiya kuruwar ta nacan ana tsafi da ita. D'aukar fansan data mutu da shi yasa kuruwar ta ke fitowa tana rab'ar Haajar ,Wanda daga baya da mahaifin Haajar ta gano haka ,sai ya yanke shawarar daya bar kuruwar aci gaba da tsafi da shi gara ya k'onata ta koma kabarin ta. Haajar tayi mamakin jin ance mahaifin ta yasan komai. Malam ya qara da cewa "hikimar k'ona wannan kuruwar shine Dan kada rayuwa da yawa su salwanta. Wannan ya ishi mutane ishara ,kubra ta mutu lokacin da take cikin jin dad'in duniya, ta qullaci d'aukar fansa ba tare da sanin cewa itama abun tsafin mahaifiyar ta neman fansa a kanta ta ba. Mafi munin mutuwa bai wuce ace an raba mahad'in rayuwar ka da gangan jikin ka ba ,wato acire kuruwar ka ana aikin tsafi da shi." Yace "to kinga Allah kenan buwayi gagara misali Wanda ba'a saka shi ba hana shi ,kuma shi keda iko akan komai da kowa. Fata dai Allah ya mana k'arshe mai kyau" Haajar da take jin maganganun malam kamar almara ta amsa da "Ameen". Ta jima suna hira da malam kafin ta koma cikin gida inda ake sauke su. Washe gari malam yasa aka zaga da su Haajar wurin ragowar dangin shi, suxee ta basu hak'uri a maimakon kubra ,sannan tayi musu alqawarin ci gaba da zumunci. Kowa yaji dad'in hakan. Haajar tayi musu alkhairi mai tarin yawa, Kwanan su uku suka koma jigawa. Washe gari daddy ya aiko da mota suka koma can gida sakkwato.








Da suxee zata koma gidan ta, kamfani d'aya daddy ya bama mahmud a matsayin kyauta, kowa yaji dad'i matuwa. Bayan shekara biyu Haajar ta sake haihuwar d'anta namiji aka sanya sunan mahaifin daddy ana kiran shi da Abba. Lokacin su Hassan sun fara zuwa makaranta. Suxee ma ta sake haihuwa ta haifi mace Barr Kabir ya yiwa Haajar takwara ,su na kiran ta da Anty. Daga k'arshe aikin Barr Kabir ya koma bangaladash gaba d'aya, ya d'auki Matar shi da 'ya'yan shi suka koma can da zama, duk hutun k'arshen shekara suke dawowa ganin gida, wani lokacin kuma daddy ya kwashe iyalan shi gaba d'aya suje kai musu ziyara. Lokacin da auta ta kammala makaratar sakandire d'inta ,ta samu admission a Bangladesh wato babban birnin india inda su suxee ke zaune. A hannun su daddy ya damqa amanar shukra.




Hajj jamil ma Matar shi ta sake haihuwa ,aka sanya Aisha.


Tun daga wannan lokacin ,farin ciki da alkhairin Allah yaci gaba sauka a *GIDAN MISBAHU* ,rayuwa ta dawo musu sabuwa ,kowa na qaunar d'an uwan sa...








*BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR* Auta shukra tayi aure a can bangaladash ,ta auri wani abokin aikin Barr Kabir har ma Allah ya azurta su da yara uku mata biyu namiji d'aya. A b'angaren daddy 'ya'yan shi tara ,Hassan da hussaina sun gama secondary school d'in su ,Hassan ha samu admission a k'asar paris a inda sameer babban d'an Hajj jamil ke aiki, hussaina kuma ta samu a jami'ar d'an fodiyo dake nan jahar sakkwato itada Suxee k'arama 'yar hajj jamil da suke sa'anni,,, su Amna da ummi kuma na shirye-shiryen gama sakandire ,yayin da Abba ke aji uku a sakandire, Abdul-Ahad na aji biyu a sakandire, sai Abdul-jalil dake aji d'aya ,Husnat da Auta Hafsat kuma na primary...




Hajj jamil shi kuma 'ya'yan shi shida, sameer, suxee ,Aisha, mukhtar, Ali sai Auta Asma'u.




Suxee ma yaranta shida, Mahmud, Anty, Hassan da hussaini, khadija da kuma Hamida.




Zumunci yaci gaba tsakanin daddy da hajj jamil Dan yanzu haka ana shirye-shiryen bikin d'an hajj jamil sameer da kuma hussaina 'yar gidan daddy. Sai kuma Hassan Dan gidan daddy da Aisha er gidan hajj jamil Wannan had'i yayiwa kowa dad'i...




A cikin wa'yannan shekarun kuma an yi rashe-rashe ,Dan kuwa Hajiya sakina ta rasu ,yayar daddy Hajiya bara ta rasu itama, malam na Allah kakan kubra shima ya rasu. Anan sai dai muce Allah ya jiqan wa'yanda suka Riga mu gidan gaskiya.




Bayan bikin su hussaina ,daddy na zaune yadda iyali suka dabaibaye shi, ga 'ya'ya ga jikoki. Murmushi daddy yayi tare da cewa _Bayan wuya sai dad'i_...




*_____TAMMAT__________________________*










ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN. GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOWA WANDA CIKIN IYAWAR SA DA YADDAR SA YA BANI IKON FARA WANNAN LITTAFI MAI SUNA GIDAN MISBAHU ,A YAU KUMA ALLAH YA NUFA NA KAMMALA WANNAN LITTAFI, FATAR ALLAH YA YAFE MIN KURAKUREN DAKE CIKI ,ABUNDA NAYI DAIDAI KUMA ALLAH YA BANI LADAN SHI.


MASOYA NA MASU BIBIYAR WANNAN LITTAFI INA MIK'A SAQON GAISUWA TA GARE KU ,DA ADDU'AR ALLAH YABAR QAUNA. NAGODE SOSAI DA SOYAYYAR DA KU KE NUNA MIN.πŸ˜˜πŸ’–πŸ’–






SAI KUN JI NI A SABON LITTAFI NA INSHA ALLAHU RABBI MAI SUNA...








TAKU HAR KULLUMπŸ’ƒ
SIDIYA...✍️09064458468 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment