Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta. Suxee kamar tasan dama ze zo Neman ta ,sashen ta nufo shi kuma lokacin daddy na saukowa ,Duk lokacin da suxee zata ci karo da Daddy se kariyar zuciya tazo mata ,gaba d'aya ya lalace ya rame ,yadda kasan wani mahaukaci ,har takai ta kawo yana tafe yana 'yan sambatu shi kad'ai._


Murmushi ta sakar masa a lokaci d'aya hawaye ya taru mata a ido. "U-um! Wannan hawayen fa Hajiya k'arama?" Daddy ta tambaye ta tare da maida kanshi gefe yana goge hawayen tausayin 'yar sa. Hannun ta ya janyo ta matso daf dashi ,kan ta ya d'aga sama tare da kiran sunan ta


"Hajiya k'arama!" A maimakon yaga ta amsa se kawai ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro. Haseena dake gefe Wanda fitowar ta kenan tagan su a tsaye ,itama kukan take yi. Hango ta da daddy yayi yasa ,ya goge hawayen shi ,itama suxee ya share mata nata ,sannan yace


"Duba ki gani amma dai munyi girman kawai! Ji fa itama ga haseena can kukan take saboda ta gan mu muna kuka. To ya isa haka ,muje Ku gama shirya kayan Ku ,Dan gobe ne tafiyar mu insha Allahu."


Murmushin k'arfin hali ya mata ,ita ma ta k'ak'aro ta maida masa ,a haka suka k'arasa sashen shi, yana k'arasowa inda haseena take tsaye ,hannu yasa ita ma ya mak'alo kafad'an ta ,a haka suka k'arasa ciki...


Wunin ranar Daddy da yaran shi a sashen shi suka wuni ,da daddare misalin k'arfe 10 suka ji k'arar sauti na tashi ,wannan karon ba'a sashen kubra kawai bane ,a gidan ne duka. K'arar sautin yayi yawa Wanda har ze iya hana mutum bacci, wannan ne yasa suxee da haseena fitowa Dan ganin meke faruwa.


Gidan cike yake cindim da mutane maza da mata ,ga motoci nan na gayu an pappaka yadda kasan club. A haka har suka k'araso inda Mutanen suke. Haseena ce tayi k'arfin halin tambayar wasu data gani d'an nisa dasu.


"Dan Allah taron me ake yi ne haka?" ...shiru ba Wanda ya amsa ta ,maimaita tambayar ta sake yi nan ma ba Wanda ya amsa ta ,d'aga idon da zata yi base ganin kubra da khaltum tayi ba akan stage ,sun sha mayen kyau ,suna kissing d'in juna ,ga kayan shaye-shaye nan a gaban su an jera kamar baza'a mutu ba. Cikin tsananin tashin hankali ta waigo ,se jin tayi taci karo da mutum ,wani razana ta k'ara yi ,koda ta juya ba se ganin tayi wasu gayu a tsaitsaye akan ta ba ,mammatso ta suke yi tana matsawa baya a haka har taji ta matse ta wata mota dake bayan ta. Kuka take yi ,tana fadin




"Me nayi muku? Let me go please!"


Suxee na hango haka ta nufo su da sauri ,dukan su tashi ga ta baya iya k'arfin ta tana fad'in "let mah sister go please, please ah beg of u!" Amma a mamakin ta ko gezau. D'ayan ne yakai hannu yana Shafa gefen fuskar Haseena ,tare da cewa


"So cute and sexy"


Wani uban ihu haseena tayi ,Wanda yayi daidai da fitowar daddy ,Dan shi ko kad'an be San sun fito ba ,da baze barsu ba ,a guje yake yafe ,musamman da yake cin karo da wasu gurb'atattun mutane a gidan ,kai ko ba'a fad'a maka ba kasan wa'yan nan Mutanen bana gari bane.


Ihu haseena keyi ba k'ak'k'autawa ,a lokaci d'aya suxee na ihun kiran sunan shi


"Daddy!!!Daddy!!!"


Cikin tsananin tashin hankali da kid'ime wa daddy yake tafe yana waige waige ,ko ze gane ta inda ihun ke fitowa...




Abunda ya gane wa idon shi yasa yayi mutuwar tsaye ,a lokaci d'aya numfashin shi da bugun Zuciyar shi suka tsaya cak...






















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️




[7/18, 10:21 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA GOMA SHA D'AYA_


*_______________________*






















_Wani irin mututwar zuciya ce ce tazo wa daddy lokacin daya ga wani gaye na k'ok'arin yiwa haseena fyad'e ,a gefe d'aya kuma ga suxee a hannu wani ya damk'e ta. Wani irin kuzari da jarumta daddy ya tattaro had'id'a duk wani k'arfi daya San Allah ya bashi ,Wanda shi kanshi be San dashi ba ,wani tuma yayi ya daka tsalle se akan gayen nan dake k'ok'arin ciwa haseena zarafi ,fyad'a guda daddy ya masa seda ya sumar dashi ,d'ayan gayen dake rik'e da suxee na ganin haka ,ba shiri ya sake ta ,ya ari na kare ,da gudu daddy ya tattaro 'ya'yan shi dake ta faman kukan wahala ,duk jikin su Yaya jawur abun ka da farar fata._




_Ciki ya shige dasu ,se faman lallashin su yake yi. Daddy kasa barin garin Allah ya waye yayi ,cikin Daren ya tattara 'ya'yan shi da kayan su sukar bar gidan, suxee ce ta shiga gidan baya tare da Auta dake ta faman sharar bacci hankalin ta kwance, haseena kuma ta shiga gidan gaba. Daddy tunani ya farayi ,ina ze nufa? Har yayi tunanin ko su wuce hotel ,se kuma ya tuna da gidan Aminin shi haji jamil, har ya d'au hanyar KARAMCI HOTEL ,se kuma ya karya kwana zuwa GUIWA LOWCOST, Wanda acan Haji jamil ke zaune._


_Yana isa k'ofar gate d'in gidan ,ya kira shi a waya ,tare da sheda masa zuwan sa. Hankalin Hajj Jamil idan yayi dubu ya tashi ,musamman daya duba ogogon bango ,yaga kusan sha biyu saura na dare ,shi kanshi har ya rufe gida ,wani d'an aiki ne ya hana shi bacci ,shi kanshi da tuni ya dad'e dakai Lagos. Yanayin muryan Daddy ya k'ara tabbatar masa da akwai matsala ,Dan haka be wani b'ata lokaci ba ,jallabiya kawai ya zura wa jikin shi tare da d'aukan makullan gida ,ya fito._


_Seda yad'anyi tafiya kamar na rabin kilo meter kafin ya kawo bakin gate d'in. Addu'a yayi tare da bud'e K'aramar k'ofa . Fitillun mota daddy ya hasko masa ,alamar ya bud'e masa gate ,maida k'ofar yayi ya rufe sannan ya saka makullin babban kwad'on gate d'in. Yana aniyar bud'e wa ne ,me gadin shi yayi firgigit ya fito hannun shi d'auke da gora da adda, hasken toci ya dannawa hajj Jamil a ido ,kan kace me har ya mamaye shi yana aniyar rafka masa gora a tsakaiyar baya. Seda Hajj Jamil ya daka masa wata uwar tsawa ,sannan ya shiga taitayin shi._


"Dan Allah kayi hak'uri Alhaji ,wallahi ban gane kai bane ,saboda nasan abune me wuya ka fito tsakar dare haka ,muddin ba tafiya kayi ba". Cewar Tukur me gadi.


Wani siririn ajiyar zuciya Hajj Jamil ya sauke kafin yace " Ba komai ,nasan ai baka gane waye ba, nima dole ce ta fito dani"...


Cike da nuna damuwa Tukur me gadi yace "to amma Alhaji lafiya kuwa ka fito cikin Daren nan ,kuma baka tashe ni ba?"


"Kar ka damu lafiya qlau Tukur ,Bak'i nayi ne ,kuma tafiyar dare sukayi shine suka mun waya sun iso" Hajj Jamil ya bashi amsa.


Daga nan ya maida hankalin shi wajen bud'e gate d'in. Shidai Tukur hankalin shi be kyauta ba seda yaga shigowar su daddy ,Hajj Jamil ya maida gate d'in ya rufe tare da yin Addu'a sannan ya koma d'aki.



Fuska a sake Hajj Jamil ya tari Daddy ,se anan take gaya masa tare dasu Haseena yake. Marfin motan gaba Hajj Jamil ya bud'e ,a lokaci d'aya kuma suxee ta bud'e marfin baya ta fito. Nan take Hajj Jamil ya d'aga waya ya kira Hajar ,Dan yasan ita kad'ai ce bata isa bacci ba a wannan lokacin kasancewar ta ma'abociya karatun alqur'ani da sallar dare ,bata runtsawa se ta tabbatar tayi raka'atanul fajr ,ta kuma jira an tada sallan asuba tayi ,sannan bata tashi a inda take har se ta tabbatar rana ta hudo sannan take samun yin bacci ,shima ba wani isash-she ba ,saboda aikace-aikacen gida...


Bugu d'aya biyu ,ta d'auki wayan tare da yin sallama ,cikin siririyar muryatta be matuqar dad'in sauraro. Amsa sallamar yayi tare da cewa "Haajar ki zo ki shiga da bak'i a haraba!"


"Tohm gani nan zuwa insha Allah!" Ta fad'a tare da mik'e wa ,dama akwai Baban hijabi a jikin ta har k'asa. Tafe take tana d'an rare karatun alqur'qni k'asa-k'asa ,a haka har ta k'araso inda suke a tsaye.


D'an gurfa nawa tayi ta gaida Daddy a nitse ,kafin ta mik'a wa suxee hannu tare da yi mata sallama suka gaisa ,haka da haseena ma. Duk da irin tashin hankalin da daddy ke ciki ,be hana yaji Haajar ta burge shi ba.


"Ki shiga dasu ciki!" Cewar Hajj Jamil.


Daddy ne ya bud'e mota ,ya d'auko Auta ,da sauri hajar ta k'araso ta karb'e ta a hannun shi. Sannan ta maida duban ta gun su suxee tace


"Sisters muje ko?"


Jiki a sab'ule suka rufa mata baya ,har suka k'arasa ciki.


Seda suka tafi sannan hajj Jamil ya maida duban shi wajen Daddy tare da cewa


"Daddy mu k'arasa ciki muma ko?"


A tare suka shiga sashen Hajj Jamil ,kasancewar me d'akin shi Hajiya zaliha tayi tafiya. Hajj Jamil beyi k'ok'arin tambayar Daddy meke faruwa ba ,seda ya kawo masa lemu me sanyi yasha ya sarara ,sannan yake tambayar sa


"Daddy wai meya ke faruwa ne haka ,ka kwaso 'ya'ya cikin Daren nan ,kuma daga gani ma yaran suma ba'a hayyacin su suke ba?"


Wani guntun ajiyan zuciya daddy ya sauke sannan ya fara zayyanawa Hajj Jamil duk abunda yake faruwa ,daga auren khaltum ,zuwa had'e masa kai da suka yi ,har kawo abunda ya faru a Daren yau d'in...




Cikin tsananin tashin hankali ,da rud'ani hajj Jamil ya dafe kai tare da furta


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Hasbunallahu wani'imal wakil"...


A Daren ranar kusan daga Daddy har Hajj Jamil basu iya runtsawa ba ,jamamin lamarin suka kwana suna yi...


















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/19, 3:43 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA GOMA SHA BIYU_


*_________________________*



























_Sai wuraren asuba su daddy suka samu damar runtsawa ,ko kiran sallan da akayi daga shi har Hajj Jamil ba Wanda yaji. A b'angaren Haajar kuwa ,har ta tashi su suxee ,ganin ana k'ok'arin tada sallah su Daddy basu fito ba yasa ta kira Hajj Jamil a waya. Har wayan ya gama ringin be d'aga ba, mamaki ne ya kamata ,cikin ranta take cewa "yau kuma wani irin nauyin bacci Abbu samir yayi" (haka take kiran shi ,Wanda suna ne na alkunyar d'an shi na farko). Sake kiran wayar tayi a karo na biyu ,nan ma ba'a d'aga ba, ganin lokaci na k'urewa yasa ta fito zuwa sashen shi. Batayi tunanin ganin kowa a parloun ba ,Dan haka kawai ta murd'a handle d'in ta shiga bakin ta d'auke da sallama, se ta kunne bulb d'in parlourn (wato haske), A mamakin ta se ganin su tayi kwakw-kwance akan kushin da alama hira suke bacci ya kwashe su ,kuma daka ga yanayin baccin kai kasan basu San suna yi ba, baran ma daddy da k'afar shi d'aya ke kan kushin d'in, d'aya kuma a k'asa, shi kuwa Hajj Jamil ga system nan a gaban shi se aiki take ita kad'ai ,kan shi jingine da kujera._


_Tunanin yadda zata fara tashin su tayi ,Dan haka kawai se ta yanke shawaran bubbuga k'ofa, shiru ba Wanda ya motsa. Jin kamar za'a tada sallah ,gashi bata so suyi asarar jam'i yasa ta k'araso da sauri ta shiga tashin su. Hajj Jamil ta fara tadawa ,sannan ta bubbugi k'afar Daddy


"Abbu samir Ku tashi lokacin sallah ya fara k'urewa" ta fad'a cikin siririyar muryar ta. Ba shiri daddy ya mik'e ,kafin Hajj Jamil shima ya wats-tsake ,wani dogon mik'a yayi tare da salati ,ganin sun tashi yasa tabar sashen zuwa nasu sashen. A gaggauce su Daddy sukayi alwalla ,suka fita zuwa masallaci, koda suka fita tukur na jiran fitowar su , a tare suka k'arasa masallacin.




_Haajar koda ta koma taradda su suxee tayi har sun fara sallah, ita ma gabatar da nata sallan tayi ,seda ta kammala ta Shafa Addu'a, sannan ta dubi suxee data lura kamar itace babban, murmushi ta sakar mata tare da cewa


"Kun tashi lafiya sisters?"


Suxee Murmushin itama ta maida mata ,tare da amsa gaisuwar


"Lafiya qlau sister. Ya gajiya?"


"Gajiya ai se Ku masu tafiya" Haajar ta fad'a fuska a sake. Haseena ma gaishe su tayi kafin ta koma ta kwanta.


Haajar maida duban ta tayi gun suxee tace


"Sedai sister bansan sunayen Ku ba?"


Murmushi suxee tayi tare da cewa "Sunana Suwaiba ,amma ana kira na da suxee ,Baba na kuma na kira na Hajiya k'arama ,saboda sunan mahaifiyar shi ce". Nuna Haseena tayi data yi d'aid'ai tana kwasan baccin ta tace " wannan kuma Haseena ita take bi mun, se Auta Shukra"


Jin jina kai Haajar tayi tare da cewa "Sunaye masu dad'i da ma'ana. Naji dad'in had'uwa daku"


"Muma haka!" Suxee ta fad'a cike dajin dad'in kasantuwa da Haajar.




Misalin k'arfe takwas ,Haajar ta fito ta nufi kitchen, koda ta fito babah ta-tata me aiki har ta gyara ko ina, amma bata taradda ita a kitchen d'in ba. Tunani ta fara akan me zata dafa ,Wanda tasan bak'in su zasu so shi. Tuno wa data yi Hajj Jamil yafi son yin breakfast da kunun gyad'a me madara yasa tayi tunanin ma Daddy ze so shi, nan ta shiga shirya musu kunun gyad'a me d'an karan daddy da d'aukan ido, a lokaci d'aya kuma ta soya Arish tare da yi masa mahad'i na sauce din k'wai da soyayyen anta. Seda ta kammala ta zuzzuba a mazubi me kyau, tana k'ok'arin fitowa se ga suxee ta fito ,k'amshi tabi har ya kawo ta kitchen d'in. Haajar na ganin ta suka sakarwa juna murmushi.




Ciki suxee ta k'araso tana fad'in " kai Sister Haajar ,shine baki tashe ni munyi tare ba?"


Haajar dake ta kai kawo tana k'ok'arin tsaftace wajen tace "Haba dai Hajiya k'arama! Idan nayi haka ,ai da ban kyauta ba. Kufa bak'i na ne ,ko kin manta hadisi na manzo s.a.w dayace , " Imanin d'ayan mu baya cika ,har se ya kyautatawa bak'on sa?" To kinga kar nayi missing wannan aikin ladan. Kuma ma kuda kuka zo jiya-jiya ,ina wani kika isa fara tayani aiki? Aikya bari ki huta tukunna"


Dariya kawai suxee tayi, a ranta take jinjina karamci irin na Haajar. A tare suka kwashe komai ,suka kai babban parloun gidan inda aka saba karyawa, sannan suka dawo suka k'arasa gyara kitchen.


Haajar ce ta dubi suxee tare da cewa


"Sannu da k'ok'ari"


"Kaji sister Haajar, wai sannu ,se kace wani aikin kirki kika bari nayi ,aike za'ayi wa sannu."


Murmushi Haajar tayi sannan tace " Yanzu dai muje muyi wanka kafin su Abbu Sameer su fito.


A tare suka Jere ,kai idan ka gansu zaka d'auka sun jima tare ne.


Seda suka gama shiri tsaf suka jero zasu fito ,Suxee ta ke k'are wa Haajar kallo, badai wani kwalliya tayi ba ,Dan tana gani ma ko powder bata Shafa ba, iya mai kawai ta Shafa se man baki. Doguwar Riga ne yellow a jikin ,Wanda ya tafi da shape d'in ta. Fuskar ta dauke d'auke take da manyan idanuwa zagaye da zara-zaran gashin ido ,tana da karan hanci ,ga bakin ta daidai ita.



Tana da hasken fata daidai misali, Wanda daka kalle ta kai kasan ba hasken fatar bane kad'ai hadda tsabar Hutu da kwanciyar hankali. Abunda yafi d'aukar hankali a jikin ta be wuce surar taba. Wato idan boobs na wa mace yawa to zamu iya cewa har yawa Haajar yawa ,daga daidai hak'ark'arin ta kuma zuwa cikin ta ,a lafe yake abunda abunda ke kira (flat tummy), daga k'ugunta kuma ya baje. A tak'aice dai Haajar na d'aya daga cikin matan da ake kira a hausance masu siffar koka-kola, a turance kuma tana cikin mata da bature ke kira (MODERATE),,,,,komai nata me kyau ne, ba namiji ba ko mace ta kalli Haajar zata so ta k'ara kallon ta, komai nata me kyau ne da tsari ,se a yanzu suxee ta gane dalilin daya sa Haajar ta lizimci saka hijabi, Dan daga jiya zuwa yau ,so d'aya ta lura haajar ta cire hijabi ,shine da zata shiga wanka, kuma tana gama shirin ta ,wani hijabin ta d'auko ta saka me hannu. Hijabin data saka wa kuma be hana ka gane ita d'in me shape ce ,sedai yana taimakawa wajen rage ido akan ta ,ba kamar idan babu hijabin a jikin taba...






A hankali Suxee ta furta "fataba rakallahu ahsanul khaliqin"...


















MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/19, 9:27 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA GOMA SHA UKU_


*________________________*




















_Koda suka fito a parlour suka taradda su daddy. Cike da k'warewar zamantakewar rayuwa na yau da kullum Haajar ta k'arasa tana fad'in_


_"Allah sarki Dan Allah kuyi hak'uri nasan kuna ta jira ,ni ban ma zata kun tashi bane"_


"Au to bari kar mu tashi ,tunda ana cin bacci a k'washi ne" inji Hajj Jamil kenan.


Shidai Daddy se dariya yake musu. D'an gurfa nawa Haajar tayi ta gaishe da Daddy ,fuska a sake ya amsata ,sannan ta gaishe da Hajj Jamil cike da girmama wa. Su suxee ma k'arasowa suka yi ,suka gaishe su a ladabce. Hajj Jamil janyo Auta yayi yana fad'in


"Autar daddy yaya? Kinsha bacci ko?"


Itadai auta se gyad'a masa kai take yi ,Dan tana da wani Abu d'aya ba ,matuqar tazo bak'on wuri koma wa take yadda kasan ruwa ya tafi da ita ,wannan kuma ba tarbiyyan kowa bane face Haseena, ba kuma wai Dan basu saba da Hajj Jamil bane ,har gidan shi suna zuwa lokaci bayan lokaci ,se dai basu tab'a zuwa sun kwana bane ,shiyasa suka kasa sabawa da gidan ,sannan da ace akwai qawance me k'arfi ne tsakanin kubra da Hajiya zaliha matar Hajj Jamil to da shak'uwar tafi yawa ,to kubra bata qawance se daidai da ita ,Hajiya zaliha bata cikin tsarin irin matan da ajin su yakai a wajen kubra, Hajj Jamil dai da daddy su suke Abokan tan su cike da nuna wa juna qauna, Dan da sun biye matan su ma baza su yi ba ,to se Allah yasa Abokan takan su bana yanzu bane ,Abotar su ta samu asali ne tun suna yara ,komai nasu tare suke yi ,har suka zama kamar 'yan uwan juna ,duk abunda ya shafi d'aya kamar ya shafi d'aya ne...




Su suxee kujera suka ja suka zauna ,inda Haajar ke serving d'in su ,su daddy ta fara zuba wa ,sannan ta zuba wasu haseena ,kowa yaci abincin se santi suke yi ,banda Auta da se wani cakalan abincin take yi, Haajar na lura da ita tace


"Auta ya ke bakya cin abincin?"


Cike da shagwab'a Auta tace
"Ni na k'oshi"


Karaf Haseena ta k'wace zancen "A-hap! Auta ce fa, ai wallahi baki ga komai ba indai wajen cin abinci ne ,haka take"




"A'a ba wani ,Ku dai bakwa mata yadda zata ci d'in ne." Cewar Haajar ,sannan taci gaba da cewa "Auta zaki sha chocolate? " da sauri Auta ta kad'a kai ,Dan an ambato mata favourite d'in ta.

Haajar taci gaba da cewa "yauwa to taso abinki kinji ,indai kika ci abinci sosai naga kinci ,to zan baki chocolate kisha kin ji".
Mak'e ka fad'a Auta tayi alamar rashin yadda. Wanda seda abun ya bama kusan kowa dake wurin dariya , itama Haajar d'in dariya take ,tashi tayi taje d'aki ,ta d'auko mata chocolate d'in tare da cewa " kin gani ko ,to zaki ci se in baki"


Ba musu Auta ta sauka kan carpet inda Haajar d'in ke zaune da plate d'in abinci. A baki tashiga bata ,har seda taci sosai ,sannan ta mik'a mata chocolate d'in. Kowa se jinjina lamarin yake ,yau Auta ce taci abinci sosai haka, Daddy kam abun ba k'aramin burge shi yayi ba ,dan yana matuqar son a nuna wa yaran shi kulawa...




Bayan sun kammala, Haajar da Suxee suka kwashe komai suka kai kitchen, haseena kuma ta tsaftace dinning area d'in. Daga nan daddy da Hajj Jamil suka koma parlour suna ta tattauna matsalolin yau da kullum, a inda su Haajar suka fara shirye-shiryen d'ora abincin rana.




A tattaunawan da Daddy keyi da Hajj Jamil ne yake sheda masa tafiyar zuwa kano. "To amma tafiyan Nada muhimmanci ne?" Hajj Jamil ya tambaye shi


Daddy yace "eh to Hajiya Gwaggo ce ke kirana ,kasan wancan zuwan Dana yi bata da lafiya an tafi da ita Sudan, to nasan baze wuce labarin auren khaltum da akayi bata nan ba"




Ajiyan zuciya Hajj Jamil ya sauke ,kafin yace "To ina ganin kaje kai kad'ai kabar su Hajiya k'arama anan ,Dan kar kaje dasu kuma Abu na babban gida ,se ya zama gutsiri tsoma, in yaso duk yadda kuka yi Seka sanar mun"


Cike dajin dad'i ,daddy yace


"To shikenan.


" kwana nawa zaka yi? Hajj Jamil ya tambaye shi


Daddy yace "Har wani kwana ki zan ke inyi ,inaga cikin ma nayi in kwana d'aya ko biyu".


" to ba damuwa ,Allah ya kaika lafiya ,ya kuma dawo dakai lafiya"


Daddy ya amsa da "Ameen"


Seda suka ci abincin rana ,Daddy ke sheda wa suxee tafiyan shi ,sosai taji dad'in daya ce ze bar su a gidan Hajj Jamil ,Dan dama abun da ke ranta kenan ,badan komai ba sedan Haajar ,lura akwai abubuwan k'aruwa sosai da baiwa a tattare da Haajar. Addu'a ta masa na Allah ya tsare.


Misalin k'arfe uku na rana Hajj Jamil yakai daddy Airport, tare da masa addu'an Allah yasa suji alkhairi, duk da a k'asan zuciyar Hajj Jamil yasan Abu ne me wuyan gaske ace Hajiya Gwaggo tayi wa mutum kiran azziki, amma ba yadda ya iya ,sedai yabi lamarin da Addu'a...






_GARIN KANO, HAD'EJA ROAD..._














MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[7/20, 2:45 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*


Please Login or Register in order to submit comment