Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su.


A b'angaren lubabatu kuwa ,tun lokacin da ta shiga hannun hukuma take cin bak'ar wuya. Dan safe ,rana, dare azabtar da ita suke yi har lokacin da ta amsa lefin ta. Saboda an same ta dumu-dumu da laifin kashe mijin ta Alh sambo. Alh sambo shine mijin lubabatu na farko. Mutum ne hamshak'i mai azziki, Wanda ya tara 'ya'ya tsakanin maza da mata har su goma sha tara. Bayan mahaifiyar su ta rasu ya auri lubabatu. A wannan lokacin ita kuma lubabatu bata son shi ,Dan haka Bayan an yi auren ta koma juya shi ta yadda ran ta ke so, shi kuwa ya dinga biye mata a duk yadda tace to hakan za'ayi ,saboda son da yake mata. Wata rana ta sa Allh sambo ya tattara 'ya'yan nan nashi su goma sha Tara ya kai su kotu akan ai masa farar takadda da su ,babu shi babu su shi ba uban su bane. Wannan al-amari ba kad'an ba ya d'aga wa mutane hankali ,Dan duk Wanda ya ji ma cewa yake ba'a hayyacin shi yake ba. Inda Allah ma ya taimaki 'ya'yan ba yara bane. Daga chairman na lokal gobmen se 'yan kasuwa da sauran su. Autar cikin su itace sa'ar lubabatun wannan ze tabbatar wa mai karatu Alh sambo dattijo ne mai tarin 'ya'ya da jikoki. Bayan wannan al-amari ya faru kwatam wata rana aka wayi gari lubabatu ta kashe zuba wa Alh sambo guba a fura ya sha ya mutu, ta kuma tattara dukiyar shi gaba d'aya ta gudu, bata tsaya ko ina ba sai k'asar Ghana...




Wannan Abu shi ne sanadiyyar daya haddasawa mahaifin lubabatu ciwon sashe ,Wanda har sai da ya zama ajalin shi. Mahaifiyar ta kuwa bak'in ciki ya sa ta tattara kayan ta tabar k'asar. Duk irin abubuwan da suka yi ta faruwa lubabatu ba ta sake waiwayo gida ba sama da shekaru goma. A can k'asar Ghana ta sake yin wani aure ,inda ta auri wani bawan Allah mai suna malam Alasan. Ko da aure shi yana da matar shi d'aya mai suna Wasila da 'ya'yan su bakwai. Wata rana 'yar hatsaniya ta had'u da malam Alasan. Lubabatu ta faki dare dama ranar girkin ta ne ,ta kwankwantse masa Al'aura, ta haura ta bar k'asar. Daga nan ta dad'e ba ta sake waiwayo gidan Nigeria ba ,sai bayan wani lokaci ta dawo kano da zama. Inda take zaune tare da wasu dattijawa ,bayan k'aryar da ta shata musu na cewa ta yi hatsari ne ta manta komai na rayuwar ta. Tun da suka ji haka suka rik'i lubabatu tamkar 'yar da suka Haifa ,da ma ba suba haihuwa ba. Daga wannan lokacin lubabatu ta zama tamkar 'ya a wurin wa'yannan bawan Allah. Inda anan ne Hajiya Gwaggo ta gan ta taji kuma ta kwanta mata ,har ta yi sha'awar ta had'a auren su Daddy.






Lokacin da Hajiya khairi mahaifiyar Khaltum ta ji abun da ya faru da 'yar ta tilo, ba kad'an ba ta yi kukan bak'in ciki da nadamar irin turbar da ta d'ora 'yar ta ta akai ba ,mugun hali irin na ta ya sa mahaifin Khaltum ya ji ba zai iya ci gaba da zama da ita ba tun a wancan lokacin ya rabu da ita. Ya so ya karb'i Khaltum amma hajiya khairi ta hana shi saboda ita kad'ai ce 'yar shi a duniya k'arshe ma daya matsa kotu ta doka shi inda ta zuba kud'i aka mata farar takadda da mahaifin Khaltum akan babu shi babu Khaltum sakamakon sharrin da Hajiya khairi ta yi masa akan yana Neman ran su ne ita da 'yar ta. Tun daga wannan lokacin bai sake Neman su ba ,ya dad'e yana jinya sakamakon abun da ya faru da kuma irin son da yake wa Hajiya khairi da 'yar shi Khaltum. Sai da dangin shi suka yi da gaske kafin ya samu abun ya fita a ran shi ,daga baya ya sake aure ,ya kuma ta ra zuri'a da wannan matar da ya sake aure. Ko so d'aya kuma Hajiya khairi bata tab'a tunanin tura Khaltum wajen mahaifin ta ba. Yanzu da wannan al-amarin ya faru Hajiya khairi ta yi nadama iya nadama ,in da ta d'ora wa kan ta laifin duk wani abun da ya faru da Khaltum a rayuwa. Lokacin da labarin wannan abun ya isa wajen dangin mahaifin Khaltum iya Allah wadai sun yi da halayen Hajiya khairi ,a gefe d'aya kuma suna tausayin Khaltum dan duk wani abunda take yi mahaifiyar ta ce ke sanya ta. A yanzu haka ita ke zaune da Khaltum a babban asibiti Wanda iya wuya ne ace Khaltum zata sake wata rayuwar a wannan duniyar. Sakamakon k'onewar da tayi ,abun har ya tab'a k'wak'walwar ta dan kusan bata iya gane waye a kan ta. Sai dai da yake rayuwar a hannun ubangiji ta ke takan yu Allah ya yi ikon shi akan ta.


Ranar da daddare Haajar da daddy suna zaune a sashen shi. Take masa magana akan ya kamata su je su gano Khaltum. Wannan batu yayi matuqar b'ata ran daddy. Ya nuna akan ba inda za su. Washe gari Haajar ta samu Hajiya ta ke fad'a mata akan ta yi wa daddy magana kan ya kamata su je su gano jikin Khaltum. Ta nuna wa hajiya akan har yanzu khaltum matar daddy ce tun da bai sake ta ba, saboda haka bai kamata ya manta da haqqin ta dake rataye a wuyan shi ba. Ba ta kuma so allah ya kama shi da wannan laigin. Jin haka yasa Hajiya ta k'ara yabawa Haajar tare da qara tabbatar da Lallai yanzu daddy ya yi aure. Hajiya ta yi wa daddy fad'a akan batun ta kuma nuna masa hakkin Khaltum dake kan shi ,sarai daddy yasan wannan aikin Haajar ne ,badan ya so ba haka ya hak'ura akan su je d'in.




Washe gari gaba d'ayan su suka shirya dan zuwa dubo Khaltum. Wanda a ranar mahaifin khaltum shi da iyalan shi suma suka zo duba khaltum d'in. Dak'yar aka bari su daddy suka shiga inda Khaltum take. Mahaifiyar ta na kan dadduma tana Neman gafarar Allah kan abubuwan da ta aikata. Lokacin da hajiya khairi ta gan su ba kad'an ba ta ji kunyar had'a ido da su. Musamman hajiya da ta yadda da ita fiye da tunanin mai karatu ,Wanda yaddar da ta yi mata ne yasa har ta yi sha'awar su had'a jini. Shine lokacin da Hajiya ta had'a auren daddy da Khaltum d'in.




Duk Wanda yaga Khaltum a wannan halin da ta take ciki a yanzu sai ya tausaya mata matuqa. Ga ta a kwance da ita da gawa ba su da banbanci ,ba um ba u'um.


Hajiya khairi na kuka ta shiga Neman yafiyar hajiya akan abubuwan da suka faru. Duk da hajiya na takaicin sanin hajiya khairi da ta yi. Be hana ta yafe mata ba. K'anwar mahaifin Khaltum da aka zo tare da ita ne ta dinga maidawa Hajiya khairi da martanin abubuwan da suka faru. Hajiyar daddy ta yi ta mata fad'a akan ya kamata su yadda da qaddara komai ya wuce. Mahaifin Khaltum har hawaye sai da ya zubar lokacin da ya halin da 'yar shi ke ciki. Da Hajiya khairi ta nema yafiyar sa ko kad'an bai yi qasa a guiwa ba wajen yafe ta ba saboda 'yar shi.


Dikkan su suna zaune kowa sai sannu yake wa Khaltum da bata San suna yi ba. A hankali Khaltum ta bud'e idon ta ta zuba su kan k'ofar shigowa. Hannu take k'ok'arin d'agawa tana nuna k'ofar ,amma ba su ga kowa ba. Jini ne ya shiga fito ma ta hanci da baki, a gefe d'aya kuma tana ci gaba da nuna k'ofa.




Da sauri Haajar ta je ta kira likitocin da ke kula da ita. Amma kafin su k'araso rai yayi halin shi. Dan kuwa Allah ya yiwa Khaltum rasuwa.


Hajiya khairi ta yi kuka kamar ba gobe. Kowa sai da ya tausaya mata. A ranar da jimamin abun su hajiya su ka koma gida. Washe gari aka wuce aka wuce da gawar Khaltum Dan ayi mata sutura akai ta gidan ta na gaskiya, Wanda tare da mahaifin Khaltum d'in aka wuce...


























MUJE ZUWAπŸ’ƒ




TAKU HAR KULLUM


SIDIYA...✍️
[8/20, 12:19 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA UKU_


*___________________________*
















Washe gari da yamma su Haajar na zaune a sashen Hajiya su na ta qara ji manta al-amarin da ya faru jiya a asibiti, sai ga wani al-amarin ya sake zuwa. Dan kuwa Barr Kabir ne ya zo musu da labarin cewa an yanke wa Lubabatu kisa ta hanyar rataya ,sakamakon kisan kai da ta yi har so biyu ta kuma yi yunqurin sake aikwatar da wani a karo na uku ,wannan ne yasa babu wani hukunci da alqalin ya ga yafi cancanta da Lubabatu bisa ga doka sama da rataye ta ,a hakan mai wai an yi mata da sauqi ne. Wannan labari shi ma ba kad'an ba ya sake d'aga hankalin su hajiya ,Haajar hadda zubar da 'yar k'walla saboda tausayi. Barr tambayar Hajiya ya yi akan ina Daddy? Hajiya tace "ai tun lokacin da komai ya warware Daddy ba ya zama Dan yanzu ma harkokin kasuwancin sai dad'a bud'e masa suke yi". Abu mai San yi Haajar ta kawo wa Barr tace wa hajiya " ni zan je in kwanta kai na ne ke d'an mun ciwo ". Hajiya tace " to Allah yasa kaffara ne. Ki tabbatar kin sha magani kafin ki kwantan. Tukunna ma kin ci abinci?" D'an sosa k'eya Haajar ta yi tare da cewa "Na sha shayi d'azu hajiya" hajiya tace "to ai ka ji shashanci. Wai shayi? Naga shayi ai ruwa ne ba abinci ba. Mutum yasan ba shi kad'ai ba amma sai sakaci. To maza kije ki nema abinci ki ci kafin ki fara aikin baccin". Murmushi Haajar ta yi tace " To insha Allahu zan ci hajiya". Hajiya tace "to ai shikenan. Sai kin fito" daga haka Haajar ta yi sallama da Barr ta wuce sashen ta. Kusan duk lokacin da Haajar za ta ji abunda ya d'aga mata hankali sai kan ta ya yi ciwo Wanda idan ba bacci ta samu ba bata samun sauqi, ita kuma da haka laulayin yazo mata.


Barr kafe Suxee da ido ya yi, da ke kwance tana aikin daddanna waya. Hajiya tace "tashi Hajiya k'arama ki canza mana tasha zuwa sunnah tv saboda k'aratowar magriba." Ta shi suxee ta yi ta canza tasha kamar yadda Hajiya tace sannan ta dawo ta kwanta. Barr yace "Hajiya na ji kince Hajiya k'arama? Ba dai ita bata wannan ta girma haka?" Murmushi Hajiya ta yi irin na su na manya tace "Yo kai da kabiru da wautar ka da wacece?" Yace "wallahi Hajiya ban d'auka ita bace ,saboda nasan ai ke d'in ta mutane ce ba'a raba ki da jama'a. Na ga ta girma ne sosai". Hajiya tace " Lallai kuwa ga ta nan dai. An gama makaranta tuni ,banda Hajiya Gwaggo ma ta hana da yanzu ta yi nisa a karatun jami'a. Ina ga ko dan ba'a k'asar ka ke zaune bane tun wancan lokacin shiyasa ,kuma kaga ba Ku tab'a had'u wa a kano waje na ba. Lokacin da zasu zo sai sun tafi da jimawa kai kuma sai ka zo."


Da mamaki Barr yace "wannan haka yake. Amma kuwa na ji kunya ,mutum da jinin shi ace ya kasa gane shi". Iya Murmushi kawai Hajiya ta yi. Barr yace " To ai ita d'in ne ma naga bata fiye magana ba". Hajiya tace "Ai haka ta ke Hajiya k'arama ba ta wani fiye magana ba musamman ma idan ba ta San mutum ba. Da dai marigayiya Haseena ce idan ka zo sai ka gaji da surutu" Barr yace "Allah sarki. Allah ya gafarta mata yasa ta huta. Hajiya ta amsa da " ameen". Daga haka tace "bari in shiga daga ciki kafin lokacin sallah ya k'arato." Har k'asa Barr ya zuqunna yace "a fito lafiya hajiya". Hajiya ta shige ,shi kuma ya koma ya zauna. Sun dad'e a zaune tsakanin shi da Suxee ba Wanda yace wa kowa komai ,ganin haka yasa ya kauda shirun da d'an d'auko wa Suxee hira. Sama sama dai suka d'an dinga hira anan har yake gaya mata yadda alaqar shi ta ke da Hajiya. Sai a lokacin ne ma suxee ta d'an sakar masa fuska. Ranar anan Barr ya ci abincin dare ,ya ta jiran daddy ya dawo su gaisa amma bai dawo da wuri ba ,ganin dare na yi yasa ya yi musu sallama ya tafi.




Wani daren asabar Haajar na zaune tare da daddy suna hira. Ya na bata labarin irin ci gaban da ya samu a harkar kasuwancin shi cikin d'an k'ank'anin lokaci, Wanda duk ya ta'allaqa samun nasarorin akan Haajar. Haajar ta nuna jin dad'in ta ma matuqa game da yabon da ta samu a wajen daddy tare da yi masa fatar samun nasorin da ya fi wannan.






Wani abunda mai karatu bai sani ba shine. Tun bayan lokacin da wancan al-amarin ya faru ,daddy bai sake kusantar Haajar ba, ba kuma Wani abun bane daban ,tsabar nauyin Haajar d'in yake ji ,ya ke kuma ganin idan ya nema ta kamar bai kyauta ba sakamakon abunda ya faru tsakani shi da ita a baya. Dukda kuwa yaji cewar a wancan lokacin duk Haajar d'in na a matsayin matar shi, amma ya kasa yafe wa kan shi. Tun Haajar na tunanin ko akwai wata matsalar ce a k'asa Wanda bata San da shi ba da yasa daddy ya k'i Neman ta a shimfid'a, har ta gano ba komai kawai nauyin ta daddy ke ji ba kuma Dan baya sha'awar ta ba ,kawai yana kai zuciyar shi nisa ne. Ganin haka yasa Haajar ta shirya tsaf Dan k'arawa kan ta daraja da k'ima a idon mijin ta. Washe gari da daddare bayan ta yi sallama da su Hajiya ta dawo sashen ta. Ta sake yin wani sabon girkin da ta San mijin ta ya fi son shi sama da kowani abinci. Bayan ta gama ta ci ado matakin k'arshe ,sannan ta zauna tana jiran dawowar farin cikin ta.


Sai wuraren goma na dare daddy ya shigo gida. Sashen hajiya ya fara zuwa ya taradda sun yi bacci, bai yi k'ok'arin ta shin su ba. Ya wuce zuwa sashen Haajar. Tun farkon shigar shi ya ga wasu sababbin sauyi. Da wani irin k'amshi mai matuqar sanyaya ruhi ya fara cin karo. Haajar ce ta fito cikin wasu k'ananan kaya Riga da wando masu matuqar d'aukar hankalin mai kallon ta. Wannan ya k'ara tabbatar wa daddy da cewa yau d'in na musamman ne. Wani salo na mai tafiyar da nutsuwa ta dinga yi masa. Ruwan wanka ta fara had'a nasa ,ta taimaka masa ya cire kayan sa. Daddy shi dai sai bin ta da ido ya ke yi yana kallon ikon Allah, Haajar d'in ce duk ta canza masa yau d'in kamar ba ita ba.


Wani abun mamakin ma bai wuce ta yaga alamar cewa tare take son suyi wankan ba. Dan bai tab'a ganin tsaraicin ta ba. Kullo band'akin tare da zare kayan da ke jikin ta d'aya bayan d'aya. Zaro ido daddy ya shiga yi yana mazurai kamar yau ne rana ta farko daya fara ganin tsaraicin mace. Kusan sumar tsaye ya yi lokacin da ya yi tozali da kyaky-kyawar surar jikin Haajar mai matuqar rikitarwa.




Salo ta dinga yi masa ko a wajen wankan ,da k'yar daddy ya iya k'arfin halin had'i yawun sa. Bayan sun fito ba shi wuri ta yi ya kimtsa ita kuma ta koma d'ayan d'akin ta shiryo cikin wasu kayan bacci masu masifar kyau ,Wanda kusan da su da babu ba suda banbanci. Abinci ta fara gaba to wa daddy. Da kanta ta dinga ba shi a baki ,daddy kuwa dak'yar abincin ke wuce masa a mak'oshi Dan kusan ma ko gard'in abincin baya ji saboda abun da yake gaban sa ya kauda duk wani d'and'ano dake bakin sa. Bai wani ci sosai ba sakamakon ya k'agu. Haajar kuwa da ta ga yana bakin hanya ,sai ruwan shagwab'a take zuba masa tana wani narke masa a jiki. Wannan yanayi da daddy ke ciki a yau sai yake jin kamar kar ya wuce. Iya soyayya, salo da k'arshen kissa da kisisi na irin na mu na manta wajen Jan hankalin namiji sai da Haajar ta baje shi a wannan Daren.




Daga nan ta ja su sai d'akin baccin su da ta k'awata da nau'in furai launin jajaye, ga wasu k'yandura a aka kunna suna fidda d'oruwar wuta. K'awa irin na masoya. Tsarin ya yi matuqar burge Daddy Wanda har sai da ya furta "ya yi kyau".




A wannan Daren saida Haajar ta tabbatar wa da daddy ita d'in ta musamman ce kamar yadda komai na ta yake na daban ko a cikin mata. Dan kusan ma sai ya ji ya fi jin ta gam fiye da wancan lokacin da ya yi mata shigar gangancin. Duk wani gudunmawa Haajar ta ba shi a wannan Daren Dan su mori rayuwar su yadda ya kamata. Ba kad'an ba daddy ya murji Haajar son ran shi ba gajiya balle k'orafi. Kusan wannan dare na daga cikin dare mafi soyuwa ga wa'yannan masoya.


Albarka sai kalan Wanda daddy ya manta ne bai saka wa Haajar ba a wannan Daren. Tun dare suke Abu d'aya, har wuraren asuba ,sannan su ka hak'ura ba Dan sun gaji da shak'ar d'umin junan su ba.




Washe gari tun bayan da su daddy su ka yi sallar asuba ,suka koma bacci ,ba su suka farka ba sai sha biyu na rana. Hajiya da suxee tun suna jiran fitowar su har suka cire rai. Su kan su masoyan irin baccin da su kayi ya d'aure musu kai.




Sai yanzu daddy ya k'ara tabbatar da abunda Hajj Jamil yake gaya masa na cewa matuqar yana tare da abunda ya ke so ,ya kuma samu yadda yake so, to ba shakka zai iya mantawa da komai".










Wanka suka yi suka shirya cikin wata had'ad'd'iyar shadda mai tsada da taji aikin wuta. A tare suka nufa shashen Hajiya. Haajar sai sunne kai k'asa take yi ,Dan gani take Hajiya zata gano abunda ya faru tsakanin su. Ba ta san tun lokacin da hajiya ta ga yanayin shigar su ba ,da kuma irin farin cikin da Daddy ke ciki a yau ,ya tabbatar mata da komai. Iya murmushin ta kawai ta yi irin na su na manya tare da saka musu albarka.




















MUJE ZUWAπŸ’ƒ






TAKU HAR KULLUM


SIDIYA....✍️
[8/22, 10:23 AM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠


*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSOπŸ“š_*
(On ward together)




*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*









_BABI NA ARBA'IN DA HUD'U_


*____________________________*
















Tun daga wannan lokacin Barr babu ranar da baya zuwa gidan daddy ba Dan kowa ba sai saboda Suxee. Dan shi har ga Allah yanayin nutsuwar ta da hankalin ta yasa ta yi matuqar kwanta masa a rai. Ya na ta Neman hanyar da ze yi ya sanar da Hajiya Dan yasan ina ce zata tsaya masa har abun nan ya yiwu. Bai San Hajiya mace bace mai matuqar karantar yanayin mutum ,ko ince ya Sani mantawa ya yi. Tun yana b'oye-b'oyen har ya fito garan da garan ya gayawa Suxee abunda ke ran shi. Bata nuna masa komai ba Dan haka ya lashi takobin Neman soyayyar ta ta duk yadda zai iya. A b'angare d'aya kuma ga Hajj Jamil da tun ba yau ba yake masifar qaunar Suxee, Wanda kusan za mu iya cewa tun tana k'arama yake d'awainiya da son ta ,har kawo yanzu da ta girma, Wanda daddy ba yada masaniyar hakan. In da matsalar ta ke kuma ko so d'aya bai tab'a furtawa suxeen cewa yana qaunar ta ba. Ba Dan komai ba Sai Dan Hajj Jamil mutum ne mai matuqar zurfin ciki da kawaici. Yana ganin kamar bai kyauta ba idan har ya ce zai auri 'yar daddy. Badan komai ba saidan daddy babban aminin shi ne na har abada Wanda ba ya da tamkar shi ,sannan kuma yana tare da daddy ne tun kafin ya auri Mahaifiyar Suxee wato kubra. Da wannan yake ganin ya zama wajibi ya lallashi zuciyar shi Dan ba ya so ya aikata wannan abun kunyar. Idan da kara ai Suxee 'yar shi ce, ko daddy baya raye shi zai zama uban ta, a gefe d'aya kuma idan ya tuna halaccin abun a addinance sai ya ji baze iya hak'ura ba ko nan da can. Ga shi a yanzu qaunar ta dad'a mamaye ko wani lungu da saqo na kafatanin jikin shi ta ke dad'a yi. Wasu lokuttan idan ya zauna sai ya ga zuciyar shi bata yi masa adalci ba ,ta rasa wacce za ta so sai 'yar shi , 'yar babban aminin shi. Duk da cewa ko a shekaru daddy ya girme masa nisa ba kusa ba. Sai dai ita soyayya ba ruwan ta da wannan. Halittar Allah ce da ke ratsa duk Wanda ta so a kuma lokacin da ta ga dama. Takan iya wa mutum mummunan kamu musamman idan Wanda ta yi wa wannan illar ya yi mata gurguwar fahimta. Son da hajj Jamil ke yiwa Suxee har ya kai ya kawo idan ya ganta baya iya samun sukuni ,zuciyar shi ta dinga bugawa kenan ,ji yake kamar ya ta shi yaje ya rungumo ta ,amma ba dama. Baya tab'a samun sukuni har sai ya d'aga daga inda take. Wannan dalilin ne ma yasa shi ya rage zuwa gidan daddy Dan dole ba Dan ya so ba, ga Hajiya ko da yaushe tambayar sa take akan mai yasa ya rage zuwa kamar da ,a tunanin ta gidan daddy ai kamar na shi ne ,ga shi shi Matar shi ba mazauniya bace, wannan yasa Hajiya ke yawan yi masa fad'a akan ya dena zama shi kad'ai saboda kad'aici ,ka da wani ciwon yaje ya kama shi.




Amma kuma duk randa abun ya tsikaro shi na son ganin Suxee ya zame masa wajibi sai ya je gidan ,ko da baze mata magana ba. Yau ma hakanne ya faru. Bayan ya dawo daga harkokin sa na kasuwanci kai tsaye gidan daddy ya nufa, tun bayan la'asar har kusan bayan isha yana tare da Hajiya su na ta hira. Rashin wurgawar Suxee ya sa duk ya shiga damuwa, sai waige-waige ya ke yaga ko zai gan ta ,amma shiru babu alamar ta. Har Hajiya ta d'ago shi tace masa ko wani abun yake nema? Amma sai yace a'ah. Yayin da ita kuma Suxee ta ke sashen Haajar tana bata labarin Barr Kabir da yadda yake matuqar qaunar ta. Wato wani abunda Haajar ta fahimta game da Suxee shine; Suxee na matuqar son mai nuna mata kulawa. Wannan ne yasa Barr bai sha wahala sosai wurin Neman soyayyar ta ba. Duk da cewar ita din tana da miskilanci amma hakan ba ya hana ta nuna jin d'ad'in ta a fili ga duk Wanda ya b'ata lokacin shi akan ta musamman ta fannin soyayya. Bayan ta gama zayyanawa Haajar komai ,Haajar ta fahimci cewa lallai fa

Please Login or Register in order to submit comment