Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taimake ka kenan dan iskanci, oya bashi hakuri right dis minute" tsaki Baba Sulaiman yaja aranshi dan yazaci Abba zaidan zubama Ayaan mari ne ya ramama yaron amma ina bazai iyaba, tashi ma yay daga wurin yakoma bayan mota ya bude ya shiga abinshi ya xauna. Ayaan dako dago kai baiyiba Abba yace "badakai nake ba bashi hakuri" dago kai yay ya zubama Muji ido batare dayace komiba, bakaramin kwarjini yama Muji ba, dauke kai Muji yayi ya kalli Abba yay murmushi yace "haba alaji basai yabani hakuri ba, mu dan Allah muka yi kumama wlh inda nasan dan kane daban fadama ba saiyanzu naga kaman ku wlh kaman kai kaki" murmushi Abba yay kaman bashine ya daure fuska ba yanzun nan yace "nagode dan albarkan yanzu kaimu gida mu godema mahaifin naka da ita yarinyar ko" rasa yanda Muji zaiyi yasa yakoma keken shi dan kunyan tsohon yake ya kunna keken shikuma Abba yashiga mota sukabi keken nashi abaya har kofar gidan su Bilkisu dake cike da almajirai anata karatu.
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

21 - 22

Parking Muji yafara yi kafin babbar jeep dinsu kirar range rover tai parking, Muji ne yafara fitowa kafin Abba da Baba Sulaiman, gaban motar Abba yabude ganin baida niyyar fitowa ya kalleshi yace "fito mah boy" fitowa yay sai wani cin magani yake, Abba yasa hannu yacire shegen bakin gilashin dake idonshi tareda turawa a aljihu, Muji ya kalli Abba yace "bari nagaya mai" shiga zauren yayi almajiran dai sunata karatu sai kallon su Abba suke, karasa wa zauren Muji yayi ya tsugunna agefen malam dake biyama wani karatu saida yagama sanan ya dago kai yace "Mujittapa ba'aje sana'a bane yau" dariya yay yace "Baba baki nakawo ma, kai ake nema suna kofar gida" Baba ya mike tsaye yace "muje" fita sukayi daga xauren shida Muji, Abba na ganinshi ya washe baki dudda zai girmi Baba bai hanashi dukawa ba lokacin daya mikomai hannu, shima Baba kunya yaji ya duka ya karbi hanun nashi suka gaisa, sanan ya mikama Baba Suleman hannu suka gaisa, bugeshi Abba yay tabayan shi hakan yasa yamikama Baba hannu yanadan murmushin dabaikai ciki ba yace "barka da warhaka" karba Baba yay cike da fara'a dudda dai bai sansuba amma yaga kaman daga gani dan tsohon nanne, ya kalli Muji yace "shiga gida kace su gyara zan shigo da baki" da sauri Muji yajuya yay cikin gidan yayinda Malam yajuya aka cigaba da gaishe gaishe kaman ansan juna, Muji yafito yace "Baba zaku iya shiga" Malam ya kallesu yace "to Bismillan ku" Muji ne yafara gaba Baba biye dashi abaya sai Abba daya fizgo hannun Ayaan da baida niyyar zuwa sai kallon almajiran yake kaman baitaba ganiba, daure fuska yay yabi Abba suka shiga zaure ya nunama Abba allo yana wani yatsine fuska yace "wats dat Pops" gaba Abba yay abinshi ya barshi tsaye yanata kallon bangon da yaran daketa kallonshi suna washemai wani harda lashe majinan daya fito daga hancin shi da sauri yajuya ya tabe baki kafin yabi bayan Abban nashi dayaga ya bude kofa suka shiga cikin gidan dake a gyare tsaf dashi, simintin sai kyalli yake, babu kowa a tsakar gidan sai kamshin turaren wuta mai dadin kamshi dake tashi, iso Malam yamusu afaddadden falonshi dake gyare tsaf an shimfida babbar tabarma a tsakiya duk suka zazzauna sai bin dakin yake da kallo yanda yaga littatafai kala kala sun cika bangon dakin an jerasu kaman mesuim, Baba ya kalli Muji tareda ciro kudi a aljihu yace "jeka sawo ruwan gora" ganin yanayin su na yan gayu ne, da sauri Abba yace "ina ga randa nan ina gani kawani ce ruwan gora malam, ban yarda ba gaskiya" yay maganan yana nuna randar dakin yana dariya, tashi Muji yay yadebo ruwa ya cika babbar jug din malam mai tsafta yadaura akan tray dinshi sanan ya sanya kopuna biyun a kai yakawo musu Abba ya karba yana washe baki diba yay yasha Baba Sulaiman ma yasha ruwan dadi ga sanyi, tsiyayawa Abba yay ya mikama Ayaan dake gefenshi duk atakure, murmushin dole yay yace "ina azumi kamanta ne Popsy" shanye ruwan Abba yay sanan ya ijiye cup din, Baba yay murmushi yace "Masha Allah sassannun ku da zuwa saidai ban ganekuba wlh" Muji ne yadawo kusa da Baba yace "Baba uhm dama" saikuma yakasa magana Baba yace "ina jinka" ahankali Muji yace "Baba dan Allah kayakuri daga ni har Bilkisu bamu fada muku komi akaiba, dama akwai wani.. ...." nan Muji yafadi ma Baba komi, Abba ya chabe da. "Malam babu abinda zamu iya ce muku sai ubangiji Allah ya saka da alheri yakuma biya bukata yakara daukaka ka, ai da Ayaan yafada mini shine muka shirya tundaga kano mukazo neman ku, munsha wuya kafin mu gano nan, Allah ubangiji ya biya muku bukatun ku duniya da lahira, yanda kuka taimaki dana kuka sani farin ciki ubangiji Allah yasaku ku farin ciki ranan gobe kiyama, watana daya da kwana goma sha biyu banga Ayaan ba rana daya kawai yadawo ta sanadin ku, nagode nagode malam" murmushi Malam yay yace "Ameen Alaji mugode ma Allah, a'aa ikon Allah kaji magana fa, shine kuma yaran nan sukamin karya, inda ace Bilkisu tafadamin ai danasa ma har gida anje an dauko shi namai addu'a nabashi magun guna anan, to ubangiji Allah ya kara mana katanga da makiyan mu, ko lokacin dana bata addu'an nace mata inhar sihiri ne dazaran yasha zai karya ashe kam sihirin ne" Abba ya girgiza kai cike da damuwa yace "bamusan waye ke neman shi da shairi hakaba, amma muna kan rokon Allah daya bayyana mana gaskiya" Baba yace "ai wanan ba matsala bace zan bashi addu'o'i dazai dingayi kullum safe da maraice in sha Allah babu abinda zasuyi dazai kara kamashi da izinin Allah kuwa dan kariya ce" Abba da kaman yazuba ruwa akasa yasha yace "mun gode, mun gode akaramakallahu, Allah ya biya bukata" sukadan yi shiru shidai Ayaan kanshi akasa Allah Allah kawai yake Pops yagama surutun shi sutafi, gashi yakasa daddana waya hakanan yaji malam ya cikamai ido, maganan Abba ne yadawo dashi daga zancen zucin dayake yi. "Malam ina diyar naka Bilkisu zanzo mu ganta mu kara yimata godiya idan ba damuwa" murmushi Baba yay yace "tana makaranta chan dogon bauchi, dayake na rana takeyi sai biyar da rabi zata dawo" Abba yay shiru chan yace "inba damuwa zamu jirata tadawo Malam" Malam yace "babu komi ai tama kusa tunda gashi yanzu hudu saura" nan fa hira yakachame tsakanin Abba da Malam da Baba Suleman kaman sunsan juna ataba nan ataba chan, suna yin la'asar Muji yamusu sallama yatafi nan Umma ta gabatar musu da abincin da aka dafa musu farar shinkafa da jar miya bayan ta gaisa dasu ta fita, abincin su Abba sukaci sosai abinsu dan wlh yay dadi.


Wuraren biyar da rabi ta shigo gidan nasu da sallama a gajiye, tun awaje take mamakin babar motar data gani a pake akofar gidan su, gashi kuma gidansu nawani fitinannen bakon kamshi, abakin kofar su ta zaunar ta ijiye jakan makarantar ta agefe tana kokarin cire takalmi da safa dan bama ta lura da takalman dake gaban kofar dakin Baba ba, cikin yar siriyar muryan ta ta kwalama Maman su kira "Mama nadawo" safan tacire tarike su ahannu tana kallonsu ganin sunyi datti yasa ta taka farar kafarta datama jan lallin salatef jiya dayay kyau sosai zuwa wajen botikin dake gefen rijiya ta wurga zafan tajuya zata shiga daki taji muryan Baba daga dakinshi yana kiranta. "Bilkisu" "Na'am Baba" tajuya zata tafi da sauri Raiyana dake falo zaune tace "Baby bakine fa kizo ki chanza kaya" turus tai a tsakar gidan tana kallon takalman da sauri tadawo daki hijabin makarantar kawai tacire sanan tadau pink hijab dinta data goge dake makale ajikin kusa tasaka, har kasa hijabin ya kaimata mai hula aiko bakaramin kyau yamata ba yafitar da baby face dinta sosai, ko silifas bata sakaba tai hanyar dakin Baba, abakin kofa tai sallama sanan ta shiga, gani tai kowa na dakin ita yake kallo banda mutum daya da kanshi ke kasa, murmushi tadan kakalo daya lobar da dimple dinta sanan ta shiga tsakar falon, dukawa tayi tafara gaida wanda bata ganin fuskarshi danya dukar dakai, sanan tadan matsa batare data jira amsar shiba ta gaida tsohon na tsakiyan su wanda tunda ta shigo yake kallonta yana washe baki ahankali tace "ina yini Abba" murmushi Abba yay yace "andawo yan makaranta Bilkisu ya karatu?" a kunyace ta sunnar dakai tace "Alhamdulillah Abba" sanan tagaida Baba Sule da shima ya amsa mata cike da fara'a kafin ta koma gaban Baba ta tsugunna kusa dashi tace "gani Baba" Baba da tunda tashigo yake kallonta yadan nisa yace "wajen ki akazo?" dan zaro ido tayi dan bataga wanda tasani cikin suba hakan yasa Baba ya gyara zaman shi ya fuskanceta da kyau yace "yaushe kika faramin karya Bilkisu? Maisa baki gayamin gaskiya ba ranan dakika zo kika karbi addu'an nan? Eh? Inda nasan gaskiyar zancen aidana hadaki dasu Isyaka kun kawoshi nadinga mai magani agida" rasa abinda zatace yasa tafashe da kuka mara sauti, jikinta ta har rawa yake tasa bayan hannu ta goge idanunta ahankali tace "Baba kayakuri, tsoro nakeji na dauka xakamin fadane" takarashe maganan cikin kuka, akaro nafarko kenan daya dago kai yadan saci kallonta da sauri ya kawad dakai kuma. Malam ya nisa yace "shikenan ya wuce haka Allah ya kaddara faruwan lamarin, gashin nan shida iyayen shi zunzo yimana godiya tun dazu ke suke jira ki dawo daga makaranta, daga kano suke"Juyo dakai tai tadan saci kallon su daidai lokacin shima yasake dago kanshi suka hada ido da sauri ta janye nata kirjinta na bugawa, yanzu wanne ne dama mahaukacin nan kai anya kuwa. Maganan Baba yadawo da ita daga duniyar tunani ya kalli su Abba yace "bari indan leka yaran nan Alaji" Abba yace "to Malam, saimun fito muma" fita Baba yayi Abba ya gyara zama ya kalleta yace "yar arziki Allah yamiki albarka y'ata, yabiya miki bukatun ki duniya da lahira, duk mai taimako baya tabewa ladanki na wajen Allah, Allah ubangiji ya baki duk abinda kikeso anan duniya da lahira banda abinda xan ce miki Bilkisu amma nagode, nagode, Ayaan yafadan mana abinda kika mai shine mukazo mu gode miki, Allah ya saka da alheri" wani irin kunya ne ya lullube ta mutumin da yamafi Baba tsufa ne yaketa gode mata haka lullube fuskar tai da hijabi kanta akasa hakan yasa Abba yay murmushi sosai ya kalli Baba Suleman yace "kaga yar albarkan kunyamu take ji, zomu basu waje sabida shima yamata tasa godiyar" yay maganan yana hararan Ayaan dake kallonshi kaman zaiyi ihu, fita sukai daga dakin sukai zaure wajen Baba, hakan yasa dakin yay shiru tamaki dago kai sai wasa take da yatsunta dasuka sha jan lalle a kumba.
Daga chan tsakar gida Raiyana ta kwala mata kira. "Anty Baby kizo wai" tashi tayi ahankali batare data kalleshi ba tafita daga dakin, Raiyana dake wurin zaure tace "Baba yace kikai mai charbin shi" tana fadin haka tafice daga gidan ahankali tajuya jiki asanyaye tai hanyar dakin Baban idanunta ne suka sauka akan Layla dake labe a kitchen tana mata game da waya, "lalala wayata Layla jeki ijiye kafin kija arufemin sim" tai maganan tana tafiya, tana kaiwa bakin kofar Baba takara juyowa ta kalli kitchen din dan taga ko Layla ta ijiye wayar ganin bata ganta ba yasa tahau kan dakalin da zaka tsallake ka shiga dakin Baba, ta kama labulen ta rike gam kafin ta daga kafa tana leken kitchen din ta window ko ta labene awani wajen, daidai lokacin shikuma yazo zai fita yasa hannu yakama labulen yaja zai bude, jan labulen dayayi yasa kafarta ta turgude tayo baya gabaki daya tafada jikinshi tabaya tareda sakin labulen yakoma jikin kofa, mugun firgitan datayi ne yasa takasa motsi saima sauke ajiyar zuciya datake yi jin kirjinta kaman zai fado waje gashi takasa juyowa takuma kasa barin jikinshi, kafarta datasha jan lallin salataf yabi da kallo yana kallon gashi gashin ta daya leko ta hular hijabin ta zufan datayi yasa sun kwanta luplup, yafita tsawo sosai hakan yasa har kwakwalwanta yana gani, hannu yasa ya juyo da ita atsorace ta kallai, daure fuska yay kaman baitaba dariya ba yace "banason rawan kai, ki natsu, karki sake barin irin haka yasake faruwa" yay maganan yana mata wani irin kallo sanan yawuce yafita daga dakin cike da izza duk takun dazaiyi saitaji a kirjinta harta dena ganinshi, tafi minti biyu a tsaye a wurin sanan ta share yan guntun hawayen dasuka zubomata ta rufo kofar tafito tai dakinsu.
Sai bayan sallan magrib suka tafi Baba yamusu rakiya har wurin mota sanan yakoma ciki, ba'a dadeba saiga amajirai sun kawoma malam manya manya ledoji da rapan kudi yan dubu daidai guda biyu malam baiyi niyar karbaba yafita waje da sauri dan ya maida musu amma harsun tafi haka yadawo yabama su Isyaka leda daya su rarraba tunda kayan kwalama ne dayan ledan kuma ya shiga gida dashi da kudin.

Abba ne zaune gefen Ayaan dayay bacci abinshi a dakinshi na hotel yay tagumi yana kallon fuskar Ayaan yayinda dayar hanunshi ke shafa kwantacen gashin shi, sosai ya zurfi a tunani hoton Balkisu yakasa barin ranshi, for d first a duniyar nan yaji lokaci yayi da Ayaan zai ijiye mata ya ijiye iyali zaizo yaga jikokin shi kafin yabar duniyar nan, yana mugun kwadayin ma Ayaan Bilkisu, yarinya hafiza, ga ilimi natsuwa da kunya ai itace tafi dacewa da Ayaan sanadinta hala ya natsu. Sai wajajen karfe daya sanan yabar dakin Ayaan din yawuce nashi.


Misalin karfe biyar na yamma suka fito daga cikin school dan anatashi su biyar ne na yamma, suka jero ita Aisha shehu, Walawa, Fa'iza dakuma Fatima, itace a tsakiyar su cikin dogon farin hijabin ta dayasha guga da wandonta purple kafarta sanye da farar safa tasaka brown takalmin makaranta mai igiya, babu komi a fuskar ta sai kwalli dakuma mai data shafa a lips dinta bayan sallan la'asar wanda yasa har yanzu pink lips dinta ke shining sosai da black din abin sai yay kaman tasa jan baki, murmushi dukan su sukeyi dan Fa'iza ke basu labarin yanda sukai da saurayinta jiya dayazo tadi sunata murmushi, bayan Fa'iza tagama duk sukai dariya, takara yin wani irin murmushi daya lobar da dimple dinta tana dan tunani tace "niko jiya da Isyaka yazo ko" sai kuma tai shiru tana fari da ido hakan yasa Walawa ta dafata tace "fada mana yar malam meya faru dayazo ke badai ya mammatse kiba" hararan ta tayi tace "Allah kyauta bama iskanci mu" murmushi duk sukayi suna kallonta, sai kuma tasake yin fari da ido tace "anbiya shi kudin aikin hannu shaddan dayayi aiko ya siyomin ice cream jiya, muka sha nida su Raiyana" ihu suka hau yi suna tafi. "woh ke woh ke, ashe dai ustaxai sun iya soyewa su isyaku an iya sawo ice-cream" dariya tai kafin ta dauke kai tace "an sa fa, nan da 2weeks da some days ne?" "mene!" dukan su suka tambayeta atare Aisha Shehu ce tace "amma kin cika yar iska Billyn Malam, keda kikace mana sai bayan kun gama exam?" kaman zatai kuka tace "wlh bahaka bake fa, Babane yace ranan walimar shi kawai ahada da auren" duk shiru sukayi suna tafiya ahankali saikace ba gida zasu ba sai kallon su take tana murmushi, chan Walawa tace "inko hakane bazamu yarda ba wlh dole mutaba mu mulmula su kafin Isyaka yataba" ihu sosai tayi da saida sauran daliban gabansu suka juyo ta arce da gudu sosai tana dariya saida ta musu nisa sosai dan har bata hangosu sosai sanan ta jingina dawani mota tana mayar da numfashi tana dariya tana kallon layin data kusa kurewa da gudu, kirjinta ta dafe tace "wayyo Allah na" jin yanda ya wani irin buga sanan tacigaba da nishi tareda lumshe ido tana kokarin saita numfashin ta, wani irin kamshin turaren kamshi daya daki hancin ta yasa ta bude ido ahankali ta saukesu akanshi ya tsaya agaban ta yay folding hannu akirji yana sanye cikin wani black bodyhug daya kama shi dan kana ganin layi layin six pack dinshi, da fadadden kirjinshi dake nan kaman ya rabe biyu, sanan hannun rigar yakama muscle 💪 dinshi jijiyoyin sun fito, kafara shi cikin wani original tomford sneakers, ya sanya wani dan iskan crazy jeans dayay tokin rigar aciki sanan yasaka belt mai bala'in kyau, kana iya hango sarka dake kyalli ta wuyarshi gawani sheken dan kunne na diamond wanda maza ke makalawa da gum, dan dan kunnen da gum dinshi yake zuwa, idanunshi sanye cikin dark shade da bata iya tantance mema yake kallo, yanda ya tsaya a gabanta sosai yasa tama kasa janye jikinta daga motar dan go tafiya daya kacal tayi zata iya gogan jikinshi ta lafe ajikin motar numfashin ta nafita da sauri da sauri, hannu yasa a aljihun bayan wandon shi yazaro bandir din kudi yan dubu daidai ya rike kudin kafin ya kalleta, kanta akasa tana wasa da bakin hijabin ta, wurgamata kudin yay a fuska wanda har saida ya bugi bakinta kafin ya fadi akasa tsakakanin kafanta, yabi kudin da kallo sanan ya tabe baki yace "Pops ne yadaman nabiyo ki school dinku namiki kyauta, so here u go" yajuya yay inda ya paka mota zai shiga, bin kudin tai da kallo ranta ya mugun baci da sauri ta share hawayen dataji ya zubomata ta tsugunna ta dauki kudin ta mike ta kalli motar daya shiga ganin baibar wurinba yasa tai wurin motar, kai tsaye tabude daidai lokacin ya dauko bottle water ya bude zaikai baki, ajiye mai kudin tai akan cinya ahankali tace "nagode amma ni bana bukatar wani abu daga wurin ka" tajuya zata tafi karaf taji yarike wutsiyar hanunta, da sauri ta juyo taga bama ita yake kallo ba saima kai bottle din dayay bakinshi yana shan ruwan shi a natse, duk iya karfinta takasa kwance hanun gashi duk yan makarantar su dazasu wuce nata kallonsu duddu su Walawa basu riga sun karaso ba, zafin dataji hannun nayi yasa hawaye ya gangaro mata a kunci, saida yagama shan ruwan sanan ya ijiye bottle din ya juyo da kanshi ya kalleta tareda cire bakin glass din idonshi ya ijiye a gefe ya kafeta da idanu da sauri ta janye nata ta cigaba da kokarin fizge hanunta, muryar ta har rawa yake tace "ka sakeni natafi gid..." "ke!" ya daka mata tsawan da batasan lokacin data fashe da kuka ba ta hadiye sauran maganan, wani irin mugun kallo yamata dayasa ta hadiye hawayen tarasa mesa take shakan shi haka, cikin wata irin kakkausar murya yace "kinsan wayeni kuwa?" dan murmushin gefen baki yayi dayawani irin karamai kyau kafin yasake damke fuska yace "Am Dr Ayaan, a doctor, double degree holder, masters holder and PhD holder, am a surgeon and a pathologist, mace bata kawomin wargi, babu abinda bansani ba na mace, so ki kula! Ki natsu! I don't take shit! dan haka pick dis money and get out of my sight" yafada cikin tsawa tareda jawo hanunta daya damke tun dazu ya daura kan kudin yamata wani irin kallo dayasa ta bude hannun da sauri ta dauke kudin sanan ya turata dahar saida tafadi kasa yaja motar dawani irin gudu yabar wajen yana tsaki, baisan mesa Popsy kemai wanan abinba wlh me zaiwani sa yazo nan, thank God yau zasu bar garin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: [7/13, 10:15 PM] ‪+234 802 916 3341‬: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

23 - 24

*For Sell! idan baka biyaba dont F*ck*ng read it in Ayaan voice. Aha*

Hawaye ta share tabi wutsiyar hanun nata da kallo yanda yay ja abunku da farar fata ahankali tace "kuma ban yafeba mugu kawai" ta tashi da gudu tana kuka tai bakin titi batare data waigi su Walawa dake kiranta ba, ta tare Bus ta shige tana share kwalla ahaka har gida. Tana zuwa gida kofar gidan su tai turus tana kallon baban trailer company Uniform, suna sauke katipu irin na boarding school dinan ankawo ma almajirai kowa daidai, aiko sai tsalle suke suna murna wajen ya kacame da hayaniyan su, karasawa tai wajen Baba dake tsaye yay shiru yana kallon masu sauke katifar tace "Baba waya aiko da wayan nan katipun?" "mutanen dasuka zo jiya ne suka aikoma dalibai dashi, wai suna Allah kadai zai iya biyan mu amma ga wanan abama dalibai" shiru tayi tama rasa yanda zatayi tabama Baba kudin daya bata dan kunya takeji fada zai mata mesa ta karba hakan yasa ta wuce cikin gida tana satan kallon Isyaka dake rubutu a allo yana binta da kallo shima, murguda mai baki tayi tana nunamai allon ta shiga gida tana dariya, da sauri yabi allon da kallo yaga ashe afarar rigarshi yay rubutun baima saniba garin kallon ta muurmushi yay ya shafa gemunshi daya cika kaman wani babba sosai yacigaba da rubutun dayake yi. Tana shiga ta debo ruwa daga rijiya ta shiga tai wanka tadawo daure da zani, tana bubbuga kunenta dan ruwa ya shiga gajiya tayi da goge kunen kafin ta zauna gefen mama hanunta Mama tabi da kallo yanda yay ja tace "maiya sameki a hannu?" girgiza kai tayi tace "bakomi bugewa nai a school" kofin magani Mama tabata ta karba tasha sanan a ijiye tana yatsine baki, jakarta tadauko taciro bandir din kudin ta ijiye kusa da Mama tace "Mama mutumin nan najiya nahadu dashi a makarantar mu yabani wanan" kudin Mama tabi da kallo tace "aisai ki kaima Baban ki tunda kinada hannun amsa ni meruwa na" kaman zatai kuka tace "Mama dan Allah kibashi nidai tsoro nakeji, fada zemin wlh" tai kaman zatai kuka ta mike ta shige uwar daka dan saka kaya.


*******
Yau kwanan su biyu kenan da dawowa daga kano.

Mami dake kwance kan gadon Abba danyau ita keda girki ta kalli agogon bangon dakin taga karfe biyu har da rabi nadare kafin tasake kallon Alaji, tun wuraren goma Alaji ke kan dadduma sai salla yake yana addu'o'i data rasa name, kasa hakura tayi ta sakko itama ta shiga bayi ta dauro alwala tafito tadau hijabi ta bishi, bayan sun sallame ta dafa shi, juyo dakai yayi ya kalleta, murmushi tamai dake sanyaya mai rai tace "Alaji matsalar mekake dashi haka? Meke damunka tunda kadawo daga zaria naganka duk wani irin wats d matter talk to me, kasan state of health dinka bai kamata kanasa damuwa aranka ba" dan ajiyar zuciya tayi kafin ta maida kanta kan kafadar shi ahankali tace "meke damun mijina abin alfahari na haka?" murmushin dabai shirya yiba yasaki Firdausi daban ce, koyaya yake cikin damuwa kobai fadi mataba zata gane, duk wani hanyar sanyaya mai rai tasani, murmushi yasakeyi kafin ahankali yace "akan dan mu nake addu'an nan" tabe baki Mami tayi hakan yasa ya girgiza mata kai yace "ba abinda kike tunani bane wlh" yadan gyara zama alamun serious yace "tunda naje zaria naga Bilkisu zancen ta ya tsayamin arai, duk sakan sai maganar ta yazomin rai, ina son Ayaan da yarinyar nan fiye da yanda kike tunani, yarinyar akwai natsuwa ga ilimi, ta sauke fa takuma kusa gama hada hadda inji baban ta, ga taimako, ayanda Boy yake yanzu mace mai irin natsuwar nan yakamata ya aura wlh hala ta sanadiyar ta ya gyaru yasan ya girma, inamai kwadayin auren ta sosai Firdausi" dan tagumi yayi Mami taja hannun ta saukar ya girgiza kai yace "yanzu dai istihara nai akan zancen auren nasu indai alkairi ni na tabbata Allah zai kara natsarmin da alamarin araina, to ni babbar matsalata yanda zan bijirowa da Boy al'amarin ne yanda aure baya gabanshi dinan zaima yarda" tabe baki Mami tayi tsabagen takaici kafin tace "hmm shikenan ai tunda hakane saikaita kallon shi kar yay aure tunda bakason ganin jikokin ka, kana dai ganin shi aure bayama gabanshi baiki yakare rayuwan shi ahaka daga yawo sai saka gantalallun kaya" ta tashi tahau gado danba karamin baci ranta yay ba yanda yadauko zancen da farko tiryan tiryan ba karamin murna yasata ba finally for d first time in long time,

Please Login or Register in order to submit comment