Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cire rai dan har yakai shekaru 45, rana daya kawai Allah ya albarka ceshi da da namiji. Lokacin da aka gane Mami nada ciki bakaramin murna yayi ba yakasa boye farin cikin shi hakafa aka haifi yaro namiji kyakyawan gaske kaman bature, yaro sak mahaifin shi, aka radama yaron suna Ayaan, duk wani son duniya Alhaji ya daurama yaron nan, wani zubin ko abu kakeso kabiyo ta hanunshi shikenan kasamu, nursery da primary kawai yay a Nigeria Alhaji ya fitar dashi waje anan yay secondary yay karatun gaba da secondary ko hausan dayakejima dan yana dawowa gida hutu ne. Alhaji da Hajiya Saratu sun bata yaron, kullum cewa suke yarone idan ya girma zai gyaru da kanshi, Mami ce ke tsayin daka wajen tarbiyan tar dashi amma bata sami goyon bayaba dazaran tafara mai fada zai fara kuka yafada jikin Abba, Abba yadinga bala'i kenan har washe gari shida hajiya Saratu. Baba Sulaiman kadai ne ke supporting dinta. Bari nabar labarin haka zakuji sauran nan gaba.


Part dinshi sukayi wanda yafi kowani part kyau agidan, komi na bangaren ma daban ne, kofar Abba ya bude suka shiga ciki dakine da akai komi na ciki dark blue and white iya haduwa dakin nan yahadu, bedroom suka shiga, Abba ya zaunar dashi akan makeken gadon dakin mai kama da gadon president ya zauna a gefenshi tareda kamo kafarshi yaciremai takalmin ya ijiye yacire dayan ma ya ijiye, daura kanshi yay akan kafadar Abba ya lumshe ido kaman xaiyi bacci, Abba ya shafa kanshi yace "tashi kayo wanka Boy, amma kafin nan" tashi yay ya dauko wani memo mai kyau da byro dake cikin drawer gefen gadon ya mikamai yace "rubuta magungunan da za'a siyoma" karba yay ahankali yana yatsine fuska tareda dan girgiza kanshi, da sauri Abba yace "menene?" daura kanshi yay a kafadar Abba ahankali yace "kaine ke ciwo Pops" rubutun yayi sanan ya mikama Abba takardan, ya karba yana dafa kanshi kafin ya sake rike mai hannu yace "muje kai wanka zakadan ji dadi" ahankali yatashi yabi Abban ya bude mai bayi ya shiga sanan yarufo mai yawuce yafita daga dakin.
Wanka yafara yi, yayi sabi kuwa yafi sabi goma, amma dudda haka gani yake baifita ba, dan kanshi yagaji yafito daga bayin daure da bathrobe yazo gaban mirror yana kallon kanshi, yadan fita tunda duk baki bakin jikinshi sunbace, knocking akayi a kofa ya kalli kofan ya harara kafin ya maida kanshi jikin madubin yana kallon kanshi, kara knocking akayi baiyi magana ba saima daukan daya daga cikin uban turarukun daga gaban madubin yana kokarin fesawa yaga anbude kofar, daga kai yayi ya kalli kofar wata maid ce ta dauko tray jikinta har rawa yake ganinshi atsaye da kyar tace "sir, sorry sir, Mami ce tace nakawo ma abincin ka" wani irin kallon wulakanci yamata, hanunta har rawa yake ta ijiye tray din akan gado tajuya tafita da sauri har tana buge kai da bango, yay tsaki yacigaba da abinda yakeyi sanan yakoma ya zauna yadau tray din yana kallo, kasa cin rice din yayi sabida rashin apatite pepper soup na kayan ciki kawai yasha sanan yasa tissue ya goge bakinshi kafin yadan sha ruwa kadan yamike ya kwanta akan gado sai bacci, bawani yi nisa sosai acikin baccin yayiba yaji Abba na kiran shi yana shafamai gashin kai, bude ido yay kadan kafin ya mirgino ya daura kanshi akan cinyar Abba ya cigaba da baccin shi, murmushi Abba yayi yadanyi tapping bayanshi kadan yace "tashi Boy, masu aski sunzo idan aka gyarama kunbunan sai ama massage kai bacci, ince kayi salla?" ba kunya ba tsoron Allah ya gyadama Abba kai, Abba yamike yakamo hanunshi suka fito falon nan fa aka shiga gyarashi Abba kuma na tsaye akansu yana kallon dan nashi dayake ji kaman ya hadiye dan so, duba wani littafin da mai askin yabashi na styles din aski yakeyi sabida yazabi wanda yakeso amai, nan fa yazabo wani aski da ake cema "dakalin shaidan" da sauri Abba ya kalli barber yace "yimai low-cut karkamai wanan" kaman zaiyi kuka yace "Popsy" yawani ja sunan, da sauri Abba ya zauna kusa dashi yaja hancin shi tareda saukar da murya kasa kasa yace "haba Boy, yanzu ka girma yakamata ka daina irin askin nan, kayi low-cut kaji dan albarka zaima fi maka kyau" yatsine fuska yayi tareda cewa "ok" ahankali badan ranshi yasoba aka soma mai askin dayamai mugun kyau yafito shi sak, ana gamawa akamai massage yasha maganin daya aika ya mike sai bacci bai tashi ba sai lokacin magrib, Abba yasake shigowa part dinshi yace "yo alwala mutafi masallaci" dan yatsine fuska yay yace "Popsy kaje bari nai wanka nafito" shiga bayi yay hakan yasa Abba tafiya shikadai, Koda yafito chanza kaya yay zuwa crock t-shirt daya kamshi yafito da six packs dinshi dawani shegen wando crazy jean duk abarke ya zaxxago yasaka belt ajikin wando batare daya rufe belt dinba ya sanya farar kafarshi cikin bathroom slippers yafita daga dakin sai uban kamshi yake zubawa, bangaren Mami yay bata falo hakan yasa ya haura sama ya tura kofa dayar sallama yashiga dakinta, tana kan dadduma tana addu'o'i hakan yasa ya zauna akan gado yana jiranta tashi tayi ta cire hijabi tana kokarin linkewa tana kallonshi ahankali yace "Mami ina wayana?" ajiye hijabin tai kan gado kafin tazo kusa dashi ta zauna tace "yana wurin Abban ka, maisa bakaje masallaci ba?" yatsine fuska yay yace "nariga nayi adaki" kafeshi tai da ido hakan yasa ya dauke kai da sauri, hanunshi ta kamo a natse ta rike ahankali takirashi. "Ayaan" juyo dakai yayi ya kalli Mamin kasa kasa yaki bari suhada ido dan ta iya gane idan yay karya, ajiyar zuciya tayi tace "Ayaan wanan abin daya sameka bai isheka ishara ba ka koma ga Allah ba, ka rike salla karike ibada? Sabida rashin azkar da salla ne yasa koma me akama ya kamaka fa, don't you think is high time ka ijiye all dis bad character da bad ways da bazai amfane kaba ka koma ga Allah, nabaka tarbiya iya karfina ka shiga islamiya kasan me addinin ka ya koyar why did you choose to go astray ha? Oya ga dadduma jeka hau kai sallan magrib kar na sabamaka wlh" tashi yayi yafara shiga bathroom ya dauro alwala kafin yazo yay salla yana idarwa ta kallai tace "and kaje ka chanza wayan nan shegun kayan jikin nan naka, yanzun nan za'a cika gidan nan za'a zo walimar da baban ka ya shirya" fita yay daga dakin ranshi duk adagule, maid din daya gani a falo suna fiffito da manya manyan kuloli daga kitchen ne ya dakama tsawa kaman su suka batamai rai yace "kubar falon nan" da sauri kowacce tabace mai daga gani kafin yaja tsaki yafita daga dakin, abakin kofa yaci karo da Big Mummy taci gayu sosai tana ganin fuskarshi tace "waya batama rai daga dawowan ka yau" kaman zaiyi kuka yace "Mami ne, please big Mummy wats wrong with kayan jikina?" yanuna kayan jikinshi, shafa kumatun shi tayi tace "share ta, daga dawowan ka zata fara takura ma, karka canza, yaro dakai kayan tsofaffi takeso kadinga sawa, jeka abinka zan sa meta, saki ranka kasan yanzu mutane xasu cika gidan" murmushi yay tareda mata peck yace "u are d best big Mummy natafi" murmushi tamai yajuya yatafi part dinshi.
Ba karamin shagali akayi ba sai wuraren goma mutane suka watse ya lallabo yadawo part dinshi danya mugun gaji, wanka yay yazo yay shirin bacci, kwanciya yay sai juye juye yake yakasa bacci idanunshi sunyi ja, agogon dakin ya kalla yaga kusan shadaya, wayarshi ya dauka wanda ya karba daga hannun Popsy dazu yay dailing wani number ringing biyu aka dauka da kyar dan muryan shi batama fita da kyau yace "kisame ni agidana am coming dere now" tashi yay daga kan gadon yadau car key yafita batare daya chanza pajamas din dake jikinshi ba.
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur


17 - 18


Mota yadauka security dake gate yabude mai gate yafita daga gidan, agaban wani hahhaden gida yay horn aka bude ya shiga fitowa yay daga mota, daidai lokacin wata kakkyawar yarinyar matashiya haka dan akalla zatai 26 tafito daga wata mota dake parking anan tsakar gidan wacce shine yasai mata, da gudu tayo kanshi tafado jikinshi tareda rungume tsam tsam tana kissing din ko ina na fuskarshi saikuma tafashe da kuka tace "My Ayaan ina kaje? kawai u stop calling me nadena ganinka, naje club dinmu ance suma sun dade basu ganka ba, nazo nan gidan mai gadi ma yacemin bai ganka ba, laifi nama kai abandoning dina like dis eh?" kara fashewa tai da kuka ta manna kanta afadadden kirjinshi tace "koma menawa ka yakuri don't ever leave me like this, nai kewan ka and ur hot screw sosai" fitowa tayi ta kalli daga jikinshi jin shiru ta kalli fuskarshi ganin ita yake kallo yasa tai murmushi takai bakinta kan bakinshi tafara kissing dinshi, matseta yayi sosai har saida tai kara kafin ya dauketa chak batare daya raba bakinsu ba yay sitting room da ita, sanan suka wuce bedroom, kayan jikinta yahau cirewa itama tana cire nashi kafin ya bugata akan gado yahawo gadon yawani chapko yan nonuwan da dabasu da girma sosai yahau matsesu tana ihu, ya dade awurin dan a rayuwan shi yana mugun sonsu, sanan ya shigeta tana maida mai martani tana ihu, sosai suke abunsu har tasoma galabaita fizge bakinta tayi daga nashi tareda tureshi da karfi tace "Ayaan don't kill me nagaji wlh" fizgota yay yace "uban mesa to kikazo inkinsan kin gaji am not done with u yet, and shut d f*uck up" fizgota yay ya sake matseta ya shigeta da kyau nan yacigaba dayin abunda yahana shi bacci agida, saida yaji shi ya gamsu sanan ya ture ta yatashi ya shiga bayi, fitowa yay daure da towel dakuma karami yana goge jikinshi kallon yanda take maida numfashin gajiya yayi yadanyi murmushin gefen baki duk cikin yan matan shi Meram ce kadai maidan iya jureshi gashi ta mutun mai murus, tabe baki yay yadau kayan baccin shi yamaida ya kalleta yace "will call you tomorrow, idan kin huta kitafi gidan ku, am off" fita yay daga dakin batare dayasake kallonta ba singlet dinshi daya bari akan gadon tajawo ta rungume tana murmushi tana kissing din rigan, tana mugun son Ayaan.

********************


*Zaria*

Kwanan ta biyar kenan tana fama, dan ciwon saiya zo yahade mata da ciwon mara hakan yasa duk ta fita hayyacin ta, Abba ya karbo mata maganin tasha kuma Alhamdulillah tasami lpy dan yau da kanta ta tashi tai shara, ita dasu Raiyana kuma suka hura wuta suka dumama tuwon da za'ai kari dashi.
Isyaka ma duk ya rame sabida ciwon da gimbiyar shi takeyi dan har saida yay zazzabin kwana daya Baba yabashi magani.

Dakin Baba tai sallama ta shiga ta zauna agabanshi tace "gani Baba" littafin dayake dubawa ya rufe ya mayar ya ijiye yace "ya karfin jikin Bilkisu?" murmushi tai tace "Alhamdulillah Baaba da sauki" gyra zama Baba yay yana kallonta hakan yasa itama ta natsu yace "Bilkisu dama inaso naji yaushe ne zaki fara zana jarabawan gama sakandirin ne" ahankali tace "uhm Baba sai karshen watan gobe, talatin ga watan August zamu fara, sai mugama karshen watan September dan wata daya akeyi ana yi" takarashe maganan tana murmushi, Baba dayay shiru kaman mai tunani yana sauraron ta yace "kuma yanzu muna tsakiyar watan July ko?" gyadamai kai tayi tace "eh Baba yau sha biyar ga wata" ajiyar zuciya ya sauke yace "to Masha Allah daman abinda yasa nakiraki shine, kinga Isyaku zai karayin walima haddace Qur'ani akaro nabiyu ranan goma ga watan gobe, August kenan, shine nakeso ranan na daura muku aure, ranan goma gawatan August din sai ya kasance ranan bikin, nan da sati uku dayan kwanaki kenan, kinga ga aure ga walima abin zaiyi kyau ahaka, idan yaso sai na baku dayan gidana ku zauna aciki dazaran kin gama jarabawan saiku tafi sokoton" boye fuskarta tayi a hijabi duk kunya ya cikata, murmushi Baba yay yace "tashi ki tafi Allah miki albarka su Baaba aiduk sunsan zancen, kin shadai maganin ki nayau ko?" gyadamai kai tayi yace "to masha Allah tafi abinki" fita tayi da sauri ta shiga dakin Umma dake tareda Mama suna hira abunsu, kan Umma tafada tawani fashe da kukan iskanci. "Umma shine ko kufadamin zancen ko" dungure mata kai Umma tayi tace "zancen me bayan keda Isyaku kun kasa hakuri har ki gama jarabawa ai wlh malam yamin daidai dayace kawai ranan walimar shi kawai a daura auren". Tashi tai tayo kan Mama tana kuka Mama ta daure fuska tace "kina zuwa nan saina mammake ki" juyawa tai tafita daga dakin tana kuka sosai mara sauti, nan fa aka fara gyara amarya Umma da Mama, ba abar Baaba abaya bama yau abata wanan gobe abata wancan tasha.

****
*kano*
Wani irin mugun kallo yabi yan aikin dake gyara flowers din side din Mami dashi kafin ya bude kofa ya shiga, stairs yahau yawuce dakin Popsy dake nan bangaren ta, da sallama yabude kofar ya shiga dakin yabi kowa nadakin da kallo Daga Pops sai Baba sule da Mami sai big Mummy dake kusa da Mami. gaida su yay Mami tabi tsinannun kayan dake jikinshi da kallo ta nunamai kofa tace "wuce kaje ka chanzo kayan nan" "ke firdausi kibarmin yaro fa yasha iska a gidan nan, shida gidan mahaifin shi ba agida yake yasa ba fita yay dasu kinfa takurawa Ayaan dayawa fa" Big Mummy ta chabe tace "atoh! Duk tabi ta gwanzabi yaro, dududu nawa yake dabazai sa abinda ranshi kesoba bahaka yaran zamani kesa crazy jeans dinan suyi ass down ba is normal suwagan kenan, kifita daga idanunshi gaskiya firdausi" "shekara talatin fa hajiya shine yaro? Sa'anin shi nada yara uku wasu ma fin hakan" Mami ta tai maganan cike dajin haushi, "ahap gorin aure zaki mana? Ai aure nufine na Allah ingaya miki, kuma mata saiya dirja ya dirje ta nunawa duniya wlh, ranan bikin shi dole duniya tasan SANGARTATTCE danmu ke aure" takarashe maganan tana hararan Mami ta gefen ido,
shiru Mami tayi bata sake cewa komiba Abba ya kalleshi yace "shigo kaji dan gata na" shigowa yayi batare daya bari sun sake hada ido da Mami ba yawani shege jikin Abba, Baba Sulaiman dai murmushi kawai yay ya girgiza kai dan agidan nan daga shi sai Mami ne ke kokarin gyara Ayaan tun yana yaro amma Abba da Big Mummy son shi ya rufe musu ido basaji basa ganine akanshi.
Shafa kumatun shi Abba yayi yace "kowani irin kaya kakeso kasaka gidan ubanka kake, idan ban maka abinda kakeso ba inada wani wanda zan mawa ne" ya kalli Mami yace "ki kiyayi fushi na wlh, duk randa kika kara batama Ayaan rai nida kene" yay kwafa yasake juyowa ya maida hankalinshi kan Ayaan yace "son yau kusan sati daya da dawowan ka baka bamu labarin yanda kasamu lpy ba".
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur


19 - 20

"Baka bamu labarin yanda kasamu lpy ba dan from video damuka kalla a haukace kabar gidan nan, maiya sameka bayan nan dazaka iya tunawa?" shiru yayi yana kallon fuskar mahaifin nashi kafin ya maida kanshi kan kafadar shi ya yatsine fuska yace "wata yarinya ce haka Popsy a zaria" saikuma yay shiru Abba yace "wace yarinya Boy? Metayi ita yarinyar? Ya sunanta?" shiru yay yana kokarin tuno sunanta dayaji wanan marakunyan yakira amma yakasa tunawa, karamar tsaki yadan ya yace "namanta sunanta Pops buh her brother yace wai itane ta karbo magani wurin Dad dinta tabani ta dinga kula dani na warke?" Abba yace "yanzu shine baka gayamin tuntuni ba, yaudin ma inda ban tambaye kaba haka zakai shiru ko" shiru yay baice komiba. kallon Baba Sulaiman Abba yay wanda shima shi yake kallo bayan gamajin maganan da Ayaan yayi yace "Sulaiman jeka shirya Zaria zamu yanzu kuwa, muje mu godema iyayen ta da ita yarinyar, sanan kome takeso aduniyar nan wlh sainai mata shi inhar baifi karfina ba dan tamin abinda har na mutu bazan iya biyan taba, ta kularmin da Boy" da sauri Ayaan ya kalli mahaifin nashi murya chan kasa dan bai fiye son magana ba yace "Popsy nifa bansan gidan suba" "badai zaria take ba, koma inane koma kwana nawa zai dauke mu saimun nemota dan haka kama debo extra kaya?" "ni fa clinic zani Pops inada patients" yawani daure fuska hakan yasa Abba ya sassauta murya yace "to idan baka bimu munje ba tayaya zamu ganeta kaine ai kataba ganinta" kaman zaiyi kuka sabida bakin ciki danyau akwai party da zaije yace "ni namanta fuskarta i can't recognize her kona ganta" shiru Abba yay saikuma yakamo kafadarshi tareda jan hancin shi da dan karfi hakan yasa yadanyi murmushi, murmushi shima Abban yay yace "to me zaka iya tunawa ranan dai daka gansun?" shiru yadanyi saikuma yace "wanta nada wanan abun da ake xpress dashi?" Abba yace "machine?" girgiza kai yay yace "a'a ni bansan sunan abin ba, but yellow ne kaman car kaman bike" da sauri Baba Suleman yace "keke napep?" shiru yadanyi jin kaman ranan fa yaji yaron yana cewa napep hakan yasa yace "i think so" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Baba Sulaiman yace "ya za'ayi kenan?" Baba Sulaiman yace "yanzu dai idan munje zai fara kaimu inda yatashi yaganshi ne daganan kuma zamu iya tambayan mutanen wajen idan babu wanda yasansu saimu je duk inda yan keke napep ke taruwa ko parking mu binciko wannata aikasan sunanshi ko?" ya jefoma Ayaan dake danna waya yana jinsu tambaya, maida wayar yay aljihu tareda saukowa daga gadon yace "am not sure but i think she called him Muji" Abba yace "shikenan jeka shirya kasa manyan kaya kaji Boy" shiru yay bai amsaba yafita daga dakin duk ranshi adagule, Big Mummy ta mike tace "Alhaji mu shirya mubiku muma?" girgiza kai yay yace "a'a kudai hadamin kaya, muda bamusan gidan suba idan mun gano gidan next zuwa aiduk sai mu shirya mutafi tare". Ranta bai soba haka tai wajen Wardrobe Mami ma tatashi suka hada kayan tare.
Saida Abba yaje part dinshi da kanshi ya ganshi a kwance sai wani cin magani yake, murmushi yay yawuce gaban wardrobe dinshi yaciro mai manyan kaya shadda fara da blue sai kuma yadi mai laushi black daya ijiye mai agefen gado da hula kube agefe dakuma su singlet da boxers, sauran kuma yahada a akwatin shi karami ya dau turarurukan shi yasaka ciki yarufe sanan ya kwalama Mike kira ya shigo dakin da gudu ya bashi jakan yace "yaje yasaka a mota" karba yay yafita, sanan Abba yadawo gadon da kyar ya lallaba shi ya shawo kanshi sanan ya yarda zaisa kayan, kafin yakamo hanunshi yakaishi bayi sanan yabarmai dakin.

Koda suka fito za'a tafi bai fitoba, Abba yakara komawa part dinshi Mami tabishi da kallo tana girgiza kai dan wlh bata data cewa amma abu na Alhaji ya isheta, tare suka fito da Abba yawani sha mur bakaramin kyau manyan kayan sukamai ba bakin soft yard ne da akamai dinkin half jumper daya kama jikinshi yafito da murdaden jikinshi sosai, ga yadin ya haska shi tareda kara bayyana farin fatar shi da pink lips dinshi, harara Mami ta watsamai dasuka hada ido hakan yasa ya dauke kai da sauri, Abba daya kamata lokacin data harare shi ya nunata da yatsa. "kifita daga idona fa Firdausi wlh inkikace xaki takurawa yaron nan zamu zuba dake nefa" gidan gaba ya budemai yashiga dudda akwai body guard dake wajen wanda aikinshi bude kofa ne, Baba suleman ya shiga baya, driver Abba ya shiga mazaunin shikuma Abba yakoma baya ya zauna Mami da Big Mummy suka musu Allah kiyaye hanya suka tafi.
Wuraren azahar suka shigo zaria agaban wani massallaci suka tsaya sukai salla sanan suka kara shiga mota hakadai yadinga nuna musu hanya har gaban bolar nan.
Kin fitowa yay daga mota saidai ya nuna musu ginin suka shiga Abba harsaida yay kwalla babu komi a wajen sai carpet din data sakamai, fitowa sukayi suka shiga motar Abba nata kallon fuskar shi ta madubin kofar mota yana mamakin wakeson halaka mai da, shi baimasan Abba na kallonshi ba dan danna waya yake. Duk wani samari dazasu gani a anguwar saisun tambaye shi koyasan Muji suce basu saniba, hakadai har suka fara zuwa duk inda sukaga yan keke napep sunyi parking suce basusan wani Muji ba, har akai sallan la'asar suka tsaya sukayi suna fitowa yace "Popsy ni am tired fa" "shikenan to muje hotel kahuta gobe macigaba da neman sun" wani hadadden hotel sukai lodging a The Fabs anan suka kwana, washe gari tun wurin 8 Abba ya shigo yatashe shi yace ya shirya su cigaba da nemanta kaman zaiyi ihu haka yatashi ya shirya cikin farar shadda ya dauko black shade yasaka ta sanan yafito sai uban kamshi yake mai shegen dadi fuskar nan daure kaman zai fashe.
Tasha tasha haka suke zuwa har wurin karfe biyu suna abu daya, ata bakin kasuwan tudun wada sukai parking inda masu keke napep ke parking Abba da Baba Sulaiman ne suka fito suka gaggaisa dasu suka tambaye su ko sunsan wani mai keke sunanshi Muji, wani daga cikin su ne yace "Mujin filin mallawa?" shiru Abba yay chan yace "wlh bamu san dan ina bane mundai san sunanshi Muji" mutumin yace "to bari nakira shi kuga ko shine" godiya Abba yamai cike da fara'a aiko yana gama wayan mutumin yace" yace gashi nan zuwa" Kudi Abba yaciro masu yawa yamasu kyauta aiko sai murna suke nan fa suka fara koda yazo inba shi bane koma waye yake nema saisun nemomai shi. Abba yadinga godiya dan shi mutum ne mai fara'a mara girman kai, dason mutane idan yafita baruwan shi baya yanuna shine mai kudin nan da Nigeria keji dashi. Shidai gogan yana mota abinshi iskan Ac na hura shi yana danne danne awaya dan Meram ta isheshi da message.

Cikin minti talatin saiga Muji yazo da keken shi yay parking yafito, ya kalli abokin daya kirashi yace "Maska yane tasamu ne wanan kira dakamin ina masu nemana din?" daidai nan Abba da Baba Sulaiman suka taso daga jikin mota dasuka jingina, dafashi dayaji anyi yajuyo ganin magidanci ne yadafa shi yaci uban babbar riga yasa yay murmushi tareda dan dukar dakai yace "ina yini alaji" murmushi Abba yay yace "Mun wuni lpy, yar tambaya nake dan Allah Kaine Muji" gyada kai yay yace "eh sunana Mujittapa amma Muji ake cemin, kaikasa akirani Alaji dafatan dai lpy?" murmushi Abba yasake mai yace "lpy kalau, dan Allah tambaya nakeson nama kaine kokuma nace kasan wani mahaukaci haka achan wata anguwa haka gaban wani Bola a sabon gari. "wanan mara mutuncin mahaukacin na hanyar dogon bauchi, ai yariga ya warke Alhaji, kanwata data lura dashi tun yana sato buredi ta dinga kawomai abinci yanaci daga bayama ta karbo mai magani wurin baban mu tabashi yasha shine yana warke wa ya zanemu dagani har ita, ya kwada mata mari nikuma ya shakeni yakusa kasheni ai namai Allah ya isa wlh" tunda yake maganan Abba yakasa dauke ido akanshi, saida ya ijiye maganan sanan yace "shine ya shakeku?" da sauri Muji yanuna mai wuyan shi yace "kagani alaji har yanzu wuyana bai dawo daidai ba, har yanzu da shati shatin jan dayayi" dan murmushi Baba Sulaiman yayi dan so kawai yake yaga me Abba zaiyi, ga mamakin shi sai yaga Abba yarike hanun Muji yace "zokaga wani abu" kofar gaban motar ya bude daidai inda Ayaan dake chatting yake, bakin glass din fuskarshi Abba ya cire hakan yasa Ayaan dago kai ya kalli Abba, Abba ya nuna Ayaan da hannu ya kalli Muji yace "wanan ne ya shake kan?" shiru Muji yay yako kafeshi da ido shima Ayaan Mujin ya kalla rass ya ganeshi amma yawani basar ya cigaba da danna wayar dayake yi, ta kwayar idonshi masu kama dana mage muji ya gane shi dan har gobe bazai manta da idanun mahaukacin daya shake shiba aiko ya ballamai harara ganin ya dauke kai ya kalli Abba yace "shine alaji" Abba ya daure fuska tamau yace "Boy dama abinda kama wayanda suka

Please Login or Register in order to submit comment