Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saita turama Mami Friday message mai dadi da ma'an hakan ko ba karamin faranta ran Mami yakeba.
Cikin iko na ubangiji ta fara zana jarabawan ta abinta sosai ta dage tana karatu ta manta zance wani Ayaan da Isyaka, inbama su Walawa sun kirata da matar Ayaan ba wanda yanzu shine sunanta har mantawa ma take ita matan aure ce, kumama wai Matar dan iskan nan maisa sarka da dan kunne hmm.

Zaune yake akan daya daga cikin kujerun platinum table dake cikin club din wanda aka jerasu mussam sabida mayan, non alcoholic wine mai sanyi waiter ya zubamai a glass cup kasancewar sunsan shi bayashan alcohol, gefenshi wasu maza ne hadaddu guda biyu wanda suke friends dinshi tare sukai school, daya daga cikin sune mai suna Fawaz yace "wai kai bazaka je ka dubo matar kaba yanzu more than a month kenan da bikin ku da baka gayyace muba" jan tsaki yayi tareda kara relaxing ajikin kujeran dayake kai yanabin wankan dake tashi a club din na Drake, dariya su biyun sukayi banda shi daya wani lumshe ido dayan ne mai suna Paul yace "yo wai tayaya ma wanda zai aureta kace yafasa awurin daurin auren, mekayi Ayaan? I know u have something to do with him saying bazai aureta ba" sai a lokacin yadan yi murmushi kadan kafin yawani tabe baki yana girgiza kai yace "nothing much, I just threaten d poor guy, bayan nasa an kamomin shi na kusan harbinshi da bindiga ya tsorata harda kuka fa wai bayason ya mutu yanzu he's just 25, yadan ban taudayi so saikuma na cikamai aljihu shikenan" dariya sukahau yi dukan su Fawaz yace "shege mugun iche, ashedai kana son yarinyar" da sauri ya kallesu kafin ya murtuke fuska yace "guys banson iskanci, ni" yanuna kanshi yace "ni, ni, me fa, inso yarinyar nan wanan yar kauyen? God forbid, Allah ya kyauta, she is not my type infact tamamin kadan as my woman, i did wat i did for Pops, u know he's old yo, so banison abinda zaisa yay breaking down, i gats make d old man happy now" atare samarin suka gyada kai suna "yeah hakane, we gats make our Pops happy kam" drinks dukansu sukai sipping atare Fawaz ya kalleshi yace "wat about ur Meram?" kallonshi yadanyi kafin ya maida mai da tambayar. "wat about her?" Fawaz yay yar dariya yace "i mean baka sonta bazaka aureta ba ita? Me relationship din dake tsakanin ku dont u have feelings for her" tabe baki yay yace "Gee, get this straight nifa aure ko soyayya bayama ajenda na, infact inda baku tunamin da dat low life girl da Pops yahadani da itaba ninama manta inada wata so called wife, and Meram, Meram" yakira sunan sau biyu yanadan rolling eyes dinshi saikuma ya tabe baki yace "ina more rayuwana da ita ne kawai anytime am in d mood, babu komi tsakanina da ita, she's just a girl dat love giving her self to me okay" dariya duka sukayi Fawaz yaciro wayarshi yace "lemme call my babe nima" tabe baki yayi kafin ya mike yaje dance floor yafara rawa abinshi yana sipping wine din glass cup din hanunshi.

Sai gurin sha biyu suka fito daga club din kowa yaja motar shi dan zuwa gida. Abangaren shi yay parking yafito yana kwance belt din wandon shi ya bude kofa ya shiga daki, zaune yaga Abba a kujera ga dukkan alamu shiyake jira, dan sosa kai yayi yamaido kofan ya rufo yazo kusa da Abban daya kafeshi da ido dan murmushi yayi yace "Pops bakayi bacci ba" yay maganan yana zama tareda daura kanshi akan kafadar Abba, sosai yay niyar mai masifa amma saiya sassauta murya cikin lallashi yace "Boy lokaci yayi da u will stop clubbing, da nabarka ne sabida inama kallon yaro but yanzu ai ka girma tunda ma har ka ijiye mata, ehen talking of mata wat do you mean ne eh? More than a month yanzu bakasan kaje ka duba matar kaba, ina so gobe goben nan ka shirya kaje" daure fuska yay tamau kaman zai fashe yace "zanje hospital gobe akwai aikin da zanma wata" "karya kake" Abba yatari maganar shi afadace ya nunashi da yatsa yace "wlh inhar baka tattara komi ka ijiye gefe ka wuce kadubo matar ka gobe ba saina saba maka" ya kamo kunnenshi tareda daye dankunen diamond din daya makala da gum kara yayi. "Pops zafiiii" ya dafe kunen kaman zaiyi kuka Abba ya cillar da dankunen yace "wlh karna kara ganin ka dasu, wanan shegiyar sarkar ma kacire, kai ai ba mace bane" turo baki yay yace "sarkan ma ai bana mata bane, baka gani bane Pops namaza ne fa" "I've said my own, first thing tommorow morning kabar gidan nan kawuce kaje ka dubo matar ka, hakkin ta na kanka be careful" Abba ya wuce yafita yana masifa.


Da gudu take tafiya danyau ko tsayawa karban waina batayi ba daga wurin Baaba, yaune take rubuta last paper ta Civic education kuma karfe biyu ranane paper bacci tayi babu wanda ya tasheta dan Mama da Umma sunje barka, biyu saura minti goma ta tashi hakan yasa ta zabura tasaka kayan makaranta tafito tana kaiwa bakin titi tasami Bus ta shiga, abinka da bus sauke dauka ba ita takai makaranta ba wuraren karfe biyu da rabi, sunayen Allah kawai take kira ta shiga makarantar da gudu tai exam hall atsorace takai bakin class din ta tsaya yan aji sai kallonta suke su Walawa dake rubutu suna mata alamu data shigo, kallon fuskar invigilator tayi ganin baice karta shigo ba saima wani kallon wulakanci dayake mata irin na kinyi latti kinkuma tsaya awaje dinan yasa ta kwasa da mugun sauri tai cikin hall din, tsayawa tasake yi dan tsoron zuwa ta karbi booklet da question paper take ganin ya mikomata daga inda yake zaune yasa tai inda yake da saurin ta, zuiiii tai wani irin mugun faduwa sakamakon bawan ayabar dake kasa data taka wani irin mugun ihu tayi dan saida ajin duka ya dauka sakamakon faduwa datayi gabaki daya ta saitin ciwonta, dan ciwonne ma yafara buga kasa kafin sauran ilahirin jikinta, da sauri shi kanshi invigilator ya sauko daga kan kujera su Walawa ma haka duk aka zagaye ta, Walawa tasamu ta damke da karfin bala'i cikin kuka tace "Walawa na bige ciwona uhm uhm uhm" wani irin nishi take tana kuka sosai tama kasa magana, invigilator yace "ku kira principal dinku" da gudu yan ajin aka fita aka kira principal koda tazo tuni Bilkisu tafice hayyacin ta sabida azaba kuka kawai take da ihu, Keke napep principal tasa aka kira ta dubi dabilan ajin tace "wayasan gidansu?" su Walawa ne suka daga hannu hakan yasa principal din tace "kuzo ku maidata gida wurin iyayenta ku dawo yanzun nan sabida kuyi jarabawar ku" kokarin mikar da ita ake ta kankame Walawa tana ihu "dan Allah dan Allah nace wlh inna tashi fashewa cikin nan zaiyi" tana maganan tana kukkule ido kaman mai shirin suma, principal tace sudauketa, taruwa sukayi suka dauketa suka saka a Keke Walawa da Aisha shehu suka bita sai gida.
[7/17, 12:04 PM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

35 - 36

Yafi minti biyar da parking a kofar gidan nasu amma yaki fitowa saima kallon kofar gidan yake daba kowa dan duk almajiran sun tafi bara, yana sanye da dark blue shadda da akamai aikin hannu mai shrgen kyau, jumper ne rigar danshi ya tsani tazarce, kanshi ba hula saidai gashin shi dayay lub lub dashi sai uban kamshi yake, tsaki yakara ja ya dunkule hannu ya daki iska "f*ck! hanayinyar dayaji yasa yadan dago kai, yan mata biyu yagani da fararen hijabi da purple dankwali da purple wando alamun yan makaranta ne sun tsaya gaban keke suna mika hannu suna magana alamun da wani akeken dasuke ma magana, daya daga cikin su yaga ta juya ta shiga gidan su da sauri chan sai gashi tafito da Baba yasa babban kaya kanshi da rawani irin ta malamai, magana yaga Baba natayi baya iyaji sabida glass din motar arufe suke fararen hannu yaga an miko daga keken wanda kumbunan hannun ke zagaye dajan lalli dayay jajir, hannun Baba ya kama, ya kara daya ta bayan wuyan shi da kyar ta sakko da kafa daya kasa saikuma ta kece dawani irin kuka da shida kanshi saida yaji daga motar, kamota Baba yayi hakan yasa tafado jikinshi tama kasa mikewa da kyau tana neman yin kasa tana wani irin kuka da sauri su Walawa suka taya Baba riketa dukansu, hankali tashe Baba ya rikota da taimakon su sukai cikin gida tana mugun kuka, dan tabe baki yayi kafin yace "wats wrong with her?"


Shimfideta Baba yayi akan tabarman dake dakinshi sabida tsakar gida yajiku dan dazu anyi yayyafi, Baaba dasu Umma suka zagayeta dan bama su dade da dawowa daga barka ba, ganin yanda take ihu tana kuka yasa Malam ya tsugunna ya daga hijabin tareda rigar ya janye farar shimin datasa ya kalli ciwon bugewan datayi yasa wurin yay ja sosai abunku dafara, mikewa tsaye yay yakalli Mama yace "cire mata kayan nan iska yadan shigeta kotaji dadi, bari naje na nemo taxi abakin hanya saimu kaita asibiti" to Mama tace jiki asanyaye ta tsugunna tana kokarin maida hawayen dataji yana kokarin zubomata, cire hijabin da rigar tayi ta barta da farar shimin kadai sai kuma wandon makaranta jikinta zata mike ta cafko hanunta tana kuka tace "ina zaki Mama? Dan Allah ki rikeni, Umma, Baba" takirasu duk awahale, dan uban kukan datake yasa ta galabaita, zuwa wajen Umma tayi ta rike, Baaba kuma dasu Raiyana duk suka tsaya akanta suna mata addu'a.

Bude mota yay yafito sabida hango Malam dayayi yana shirin fitowa daga gida adan kunyace ya dukar dakai ganin Baba na kallonshi dudda hankalinshi atashe yake hakan bai boye farin cikin ganinshi dayayi ba, ahankali yace "ina yini Abba" murmushi Baba yayi yace "barka dazuwa saukan yaushe? Yasu Alaji da kowa da kowa" ahankali yace "Alhamdulillah sunce agaishe ku" girgiza kai Baba yayi yace "kaga ikon Allah yanzu hakafa fita zanyi nem mota ahanya, dan matar takace ba lapiya yanzun nan daga wajen jarabawan tasu ce aka kawota ma, cha nayi nasamo sai muzo akaita asibiti amma tunda kaga Allah yakawo ka ai sai kadubata" dan murmushi yayi yace "meke damunta Abba?" ajiyar zuciya Baba yadan yi yace "wanan dai matsalar cikin dana fada muku tanada shi, wai bawon ayaba ta taka a makaranta shine fa tafadi, mu shiga ciki ka dubata" gaba Baba yayi yana biye dashi a tsakar gida har dakin nashi, aiko tundaga zaure yakejin ihun nata tsaki yadanja wanda shi kadai zai iya jin karanta. Sallama Baba yayi ya shiga dakin daidai lokacin ta kara kankame hannun su Mama kaman zata shide tace "Mama Mama wlh zafin yakaru kaman wurin zai farke" dan leko dakai yayi tabayan Baba ya kalleta kitson shiku ne akanta manya da kanana idan akai babba daga sai ayi karami siriri guda daya, tsawon shikun har bayanta yakai jelar nata lilo sabida yanda take jujjuya kai, dan makalen dan kunnene akunnenta ja, ya gangaro xuwa jikinta dake cikin farin shimi dayabi jikinta gabaki daya saikuma purple wandon da farar safan makarantar dake kafarta, gashin gaban kanta sunbi zufan datakeyi sun kwanta lub lub idanunta sunyi jajir danhar kumbura sunyi tsabagen kuka, yanda ta kakkame su Mama tarike su kace a nakuda take, ganinshi yasa su Mama duk suka mike tsaye a kunyace siriki yazo, dukar dakai yay ya gidansu suka amsa sunamai barka da zuwa kafin duk su fita dakin su ka barta akan tabarman tana uban kuka, karasawa inda take Baba yayi ya kalli Ayaan da har lokacin yake tsaye a inda yake kai akasa yace "karaso ka dubata Ayaan" kara fashewa tai dawani sabon kuka jin sunan da Baba yakira, ahankali ya tako yazo gefen Baba ya tsaya akaro nabiyu ya daga kai ya kalleta aiko suka hada ido da sauri ya dauke kai, Baba yace "dubata ina zuwa" fashewa tayi da kuka sosai ta damke babbar rigan Baba tana kuka tace "Baba ni bazai dubani ba nidai ka kaini asibiti Baba zafi yakeminin sosai wlh" karban babbban rigan shi Baba yayi yace "kagamin shirme keda baki da lpy kuma kice likita bazai dubaki ba" ya kalli Ayaan yace "karka biye mata dan Allah rakinta yawa ne dashi wlh, yarinya ba dauriya ko kadan" Baba yay ficewar shi yana korafin halinta.
Ihu tayi da saida ya daura hanunshi akunne. "wayyo Allah na Baba dan Allah kadawo, cikina Baba, mutuwa zanyi, wayyo Allah na na banu na" kukan ta taciagaba dayi tana jujjuga kai ta daddaga hannayen ta sama tana yayyarfe su tsabagen raki, ahankali ya daga kai ya kafe cikinta da ido dake a shafe ta shimi, ta gefen haggunne yaga shimin yadanyi tudu, dan matsawa yay kusa da ita fuska adaure, duk uban kukan datake da zafin da cikin ke mata bai hanata tattaro ragowan karfin daya ragemata ba ta matsa baya da sauri cikin kuka tace "mehaka malam" wani irin wulakantattcen kallo yamata batare daya daga murya ba gudun kar ajisu yace "ke banason rashin hankali" yakara matsawa kusa da ita matsawa tayi da sauri sai kuma tafasa uban ihun dayasa ya bugi bakin ta yace "wlh kika karamin irin ihun nan saina fasa miki baki" yana fadin haka yasa hannu akan shimin jikinta yana wani irin tabe fuska ya yaye shimin zuwa sama hakan ya bayyanar da shafefen cikin ta fari, wajen ciwon ya dade yana kallo yanda wurin ya kumbura yay ja kafin ya kalli fuskarta yanda take hawayen ba kakkautawa ga uban zufan da goshin ta keyi sabida wahala, ahankali ya mika hannu zai taba wurin da sauri ta rike hanunshi tafashe dawani irin kuka tana kokarin tashi zaune amma takasa ta kalleshi da rinannun idanunta tareda kara cukwuikuye hanunshi cikin nata tace "dan Allah, dan Allah, karka taba wlh zafi yakeyi inka taba mutuwa zanyi dan Allah" hanunshi yabi da kallo hakan yasa ta sakeshi atsorace tana kuka, yabi hanun da kallo yanda zufan hanunta ya jikamai hannu kaman yasa hannun aruwa, dan ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya dayar hanun nashi a aljihu yaciro handky ya goge zufan sanan yakara maida hanun zai taba wurin cikin kuka sosai tafara kokarin tare hanunshi kama hannayen nata yayi da hannu daya fuska adaure kafin yakai hannunshi ahankali ya daura akan wurin, ihu tayi cikin kuka kirjinta na bugawa sosai, shiru yadanyi kaman mai nazarin abu kafin ya gangaro da hanunshi kasan ciwon kadan ya danne da karfi, wani irin ihu tayi da saida ta zaburo ta dago kanta ta daura akan fuskarshi dan yadan rankwafo sabida akwance take, tsabagen azafa yasa tafara jujjuya fuskarta akanshi gabaki daya zuban datai agoshi da hawayen ta sharemai su tass a fuskarshi tana kuka, cire hannun yay ya tureta da karfi takoma ta kwanta tana kuka yace "wat d heck! Are u mad" tsaki yayi yamike tsaye yadau handky yana share fuskarshi dashi, sanan yafita daga dakin rai abace. Ganin su Baba a tsakar gidan yasa yadan kakalo murmushi, Baba yace "mecece matsala Ayaan?" dan dukar dakai yayi sabida kunyar Abba dayakeji ahankali yace "Abba tun yaushe take ciwon nan?" karaf Baaba ta chabe tace "yafi shekara biyu fa tafara har yazo yafara girma kullum inyafara saidai ai addu'a abata" ahankali ya gyada kai yanadan tunani saikuma ya kalli Abba yace "ina ganin Appendix ne, yay girma har ya rika haka, yanzu inaso zan tafi da ita asibitin danake aiki a kano zamuje ai yan gwaje gwaje inhar shine to dole operation za'a mata acire tahuta" salati su Mama keyi kaman wani baban abu, shi abin ma yaso bashi dariya yadan daure Baba ne ya nisa yace "shikenan Ayaanu ai matar kace duk yanda kace hakan za'ayi Allah dai ya bata lpy, yasa kuma muji alheri" Ameen duk sukace yadan kalli Mama yace "wazai bimu dan dole wani yabimu dazai riketa amota ni ina tuki" Mama da Umma shiru sukayi ina zasu wani iya zuwa gidan surukai hakan yasa Baaba tace "muje nabiku, bari naje nahado kayana" takalli Mama tace "hada mata nata itama" da sauri yace "a'a tanada kayanta achan" murmushi kowa yayi, Baba yace "muje waje sa fito da ita insun shirya" bin Baba yayi sukai waje, nan da nan Baaba taje tahado kayanta karban jakan yayi yasaka mata a boot itakuma ta shige gida, ba'a jimaba suka fito dauke da Bilkisu da aka chanxa mata kasa zuwa doguwar rigan atampa brown da hijabi milk sai uban kuka take kaman ana yankata sata sukai amota Baba ma ta shiga Baba yamusu sallama Ayaan yatada motar su Baba suka bisu da addu'a sai kano.
[7/17, 12:31 PM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

37 - 38

Acikin mota haka ta dinga uban kuka dukta rukunkume Baaba daketa bata baki, sai satan kallonta yake ta madubin gaban mota ahaka ta dinga kuka har daga baya wani irin wahalallen bacci yay gaba da ita. "thank God" yafada dan wlh kukan ya cikamai kunne, Baaba dake wurin ne daya mata tsawa shifa bayason iskance iskancen mata da rakin nan fa, nonsense.

Acikin wani ubansu asibiti yay parking yafito da hannu yama wasu nurses guda biyu dake reception alamun suzo da gado da sauri ko suka gangaro gadon suka zo suka gaishe shi batare daya amsaba ya bude bayan motar inda suke ya sakanma Baaba murmushi sanan ya nuna musu ita yace "kuciro ta ahankali karta tashi" matsawa baya yayi yaciro waya yana daddannawa suna fara dagata ta bude idanunta dake buduwa da kyar sabida nauyin dasukai mata fashewa tai da wani irin wahalallen kuka ta rirrike Baaba hakanan dai suka fito da ita suka sata akan gado sai alokacin ya dago kai ya kallesu batare daya kalleta ba dan mugun haushin kukan datake yi yake yace "to my office" wucewa da ita sukayi Baaba nabiye dasu yadau waya yakira matar dake scanning a hospital din yace amata, nan fa aka kaita hadadden office din nashi akazo akafara scanning.

Fita yay daga asibitin yaje wani eatry yaci abinci iya cinshi sanan yayo musu takeaway dan ita yanzu daza'ama operation bazata iya ciba, wuraren 7:30 ya shigo asibitin saida ya tsaya ya karbi report dinta yagama dubawa sanan ya kalli Nurse din wajen yace "set d theater" yawuce office din nashi, yabude ahankali tareda yin yar gajeren sallama zaune ya ganta akan gadon ta make da bango tana kuka kuka gyangyadi gyangyadi dan yanzu hakama bama taji shigowan shiba, juyowa yay yace "sannu Baaba" ya ijiye ruwa da takeaway din abincin agaban ta ahankali yace "Baaba ga abinci kici, nakira su Mami zasuzo sutafi dake gida kihuta dan theater zamu shiga yanzu, nariga naduba hoton da aka mata dole aiki za'ayi acire" tagumi Baaba tayi tace "oh ni Salamatu shikenan anjama yar karaman yarinya operation, duka duka sha takwas take fa, inda tunda cikin yafara ciwo Malam ya kaita asibiti ai da abu baikai hakaba, amma shi ina saida addu'a da magungunan hausa yarinya sai wahala take" dan murmushi yayi ya mike ya bude wani kofa ya shiga wani hadadden dakine ya bayyana, bathroom ya shiga yayo wanka sanan yafito ya shirya cikin wani green riga ta likitoci wacce ta tsayamai a cinya an rubuta Dr Ayaan ata wurin kan aljihun dakuma doguwar wando yasa hular kayan blue yadau wayarshi yafito yana kamshi daidai lokacin nurse din tai knocking office din afirgice ta farka tana kokarin bude idanunta duka, dan kallonta yayi kafin ya dauke kai ya kalli kofar yace "yes come in" shigowa nurse din tayi tana gunguro wani hadadden gado tace "sir everything is set" gyada mata kai yayi tareda nuna mata Bilkisu dake kuka wanan karan mara sauti dantai bala'in gajiya, ahankali nurse din tadafa Bilkisu tai murmushi tace "my shagwaba friend yama sunanki" cikin kuka ta turo baki tace "Bilkisu kuma niba shagwababbiya bace, ciwo yakemin saisa nake kuka ai" kama baki nurse din tayi dan tasan aikin ta ta iya lallaba patients tace "ai yama rage ciwon tunda gashi baki ya bude, dazu ko uppan baki cewa sai uban ihu dakike mana kunenmu duk ciwo suke yanzu" kara matso wasu sababin hawayen tayi batare datace komiba, hanunta nurse din takama tana dariya Baaba ma dariya tai tace "Bilkisu uwar raki" nurse din tanuna Baaba tace "nuna mata keba mai raki bane taso kihau gadon da kanki" baki Baaba ta rike jin dariya na neman fitomata Bilkisu dai data sani inbadai tadane jin zafin gabaki daya bane shine zata mike da kanta amma inhar tanaji ko kankanu ne wlh bata mikewa, kallon Baaba tayi idanun nan sai shining suke sabida hawayen daya cikasu da sauri Baaba ta mike tsaye tana lullube fuskarta da hijabin ta tace "ke nifa ba dariya nake ba haba mai gadon zinare yar wajena guda" karaf suka hada ido da Ayaan da tuntuni yake tsaye yana daddana waya kaman da gaske nanko kallon su yake kawad dakai tayi kafin ahankali tai yunkurin mikewa tsaye ihu sosai tayi. "wayyo Allah na Mama" komawa tayi zata zauna da sauri nurse din tarike ta daurata akan gadon ta kwantar, fashewa tayi da kuka sosai danji tayi gabaki daya wurin yafara wani sabon ciwon dan dan baccin datayi yasa ya lafa amma yanzu yafara, gungura ta nurse din tayi suka fita daga dakin, dan murmushi yayi yatura wayar aljihun wando ya kalli Baaba yace "ki zauna anan, zaki iya shiga ciki kiyo alwala idan zakiyi salla su Abba nanan zuwa saiku tafi tare dan bansan lokacin dazamu fito daga operation dinba" kaman Baaba zatai kuka tace "to dannan ubangiji Allah yasa ayi a sa'a, Allah yabata lpy Allah kuma yabaku nasara" Ameen ya amsa ciki ciki sanan yabude kofa yafita.

Hadadden theater ta gungurata suka shiga duk tana kuka, ko ina haske wajen, dagota tayi ta zauna da kyar sanan tacire mata hijabin jikin nata tana murmushi ta linke ta ijiye, sanan ta wuce wajen wani hadadden wardrobe din bango ta bude taciro sabuwan rigar nan da ake bama Wayan da za'a musu aiki su saka, tadawo tace "kinga rigar nan zaki saka, dole ki cire na jikinki" ta bayanta ta koma ta zuge zip din doguwar rigan dake jikinta tana kokarin saukar da kafadun rigar ta rike mata hannu tana kuka ahankali tace "zan iya" ahankali nurse din tace "are you sure zaki iya" gyada mata kai tayi da kyar, nurse din tace "okay to bari na taimaka miki ki mike tsaye, komifa na jikinki zaki cire, wanan rigar kawai ake bukata kisa" aranta cewa take to uban me za'a matane daga dan ciwon cikin nan dahar ake cewa tacire komi najikin ta, tsaki taja aranta, nurse din tarike hannunta ta mike tsaye da kyar tareda dafa gado tana hawaye, nurse din tace "sannu kinji kinama kokari" hannu takai ta zame rigar daga sama yay kasa yarage daga ita sai bra da dogon sket daya tsaya a gwuiwa kasa tai dakai duk kunya ta isheta, dan murmushi nurse din tayi tace "bari nabaki wuri to kicire sauran nan ki ijiye agefe, bari naje nadauko file dinki idan nadawo zan tattare kayan nasaka miki a wardrobe kafin Dr yazo" tana fadin haka tafita daga dakin tareda rufo mata kofa.
Hawaye ta goge kafin ahankali tadanyi bendi kadan ta tube sket din batare data cire white pant din dake jikinta dayabi fatarta yay wani irin kyau kaman jikin wata celebrity, hannu tasa tabaya da kyar ta balle maballin clean white bra dake jikinta, kirjin masha Allah luhu luhu dasu a tsaye, hannu ta mika tadau rigar tabude tana kallo tana kuka mara sauti, tama rasa ta yanda zata saka dan igiyoyi ne ajikin rigar takasa gane inane wuya inane hannu, karan bude kofa dataji yasa ta dago kai atsorace suka hada ido wani irin ihu tayi ta daura rigar agaban kirjinta ta danne da hannu dayan hannun kuma ta daura ta danne ta wajen cinyarta tana wani irin kuka, mayadda kofan yay ya yarufe ya shigo dakin, wani irin firgicewa tayi tana waige waige inda zata gudu tsabagen yanda jikinta da hannayen ta ke rawa yasa rigar fadi akasa, wani irin ihu tayi zata

Please Login or Register in order to submit comment