Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wanda ya ganta ya kaita, yaushe zaka kaita yanzu" lumshe ido yayi yakara budeso ya daura akanta yanda taketa guje guje su Ummy na binta, ahankali yace "i don't want her to leave Man, tun shekaran jiya nagani a news har a Twitter da Instagram saida naga hoton ta a page din Nigeria police sun saka, i don't know what to do banaso ta bar wajena, i don't want her to leave friend" anatse Dr Ameenu yace "i tot we've talked about this, Aaman tayaya zaka fada tarkon soyayyar wacce bakasan ko wacece itaba, u know nothing about her, bakasan iyayen ta ba, bakasan daga ina takeba, yarinyar daka tsinta rana tsaka kawai sabida ta zauna dakai na watanni saika fada tarkon sonta, tun wuri kama tsamo kanka da kanka, and tomorrow banda office, am off tomorrow bazanje clinic ba inka shirya kaita zan iya binku har kanon" shiru yayi har lokacin yakasa dauke kanshi akan Bilkisu yayyafi ake duksu Zainab sun shige barander suna kiranta tabar ruwa amma taki sai tsalle tsalle abinta take, ahankali Dr Ameenu yakira sunanshi. "Barrister Aaman" ahankali yace "na'am" Dr Ameenu yace "you have to make a decision now" dan lumshe ido yayi yace "wat if muka kaita iyayen ta sukazo suka tafi da ita does that mean bazan kara ganinta ba? Yaya zanyi da raina da zuciyata dake cike da kaunar ta?" "mudai fara kaita tukunna, kayi tunanin wani hali iyayenta ayanzu haka suke ciki, wata nawa basu saka yarsu a idoba wani hali suke ciki just imagine irin farin cikin dazasu shiga gobe idan suka ganta, don't think much abinda kamata kayu kenan ka maidata ladan ka naga Allah" lumshe ido yayi yace "alright Allah kaimu goben" katse wayar yayi ya jinginar da kanshi akan kujera ahankali yake karanto addu'o'i da zasu sakamai natsuwa kafin ya bude motar ya mayar ya rufe ya shigo gidan kaman ance ta daga kai ta ganshi yana tahowa wani irin ihu tayi ta taho da gudu tana murna. "oyoyo sweetheart oyoyo sweetheart dinmu, Anty Ummy sweetheart is back" ganin ya tsaya yaki cigaba da tafiya yasa itama ta tsaya tana washe mai baki tunawa da yahanata fadomai, saikuma ta turomai baki kaman zatai kuka tace "oyoyo fa nake maka sweetheart" ledan snacks din dake hanunshi ya mikamata ta karba tana washe baki tana kokarin budewa yay gaba abinshi hakan yasa ta fasa budewa ta bishi da gudu ganin zata bishi har daki yasa ya tsaya ya juyo ya kalleta ahankali yace "jeki chanza kayan nan bakiga kin jike bane" kara washemai baki tayi tana kallon fuskarshi tace "in chanza" gyada mata kai yayi da sauri ta juya tai dakinsu, cire kayan tayi tasake saka wani doguwar rigar atampa black ta daura dan kwali tabar ledan snacks din adaki tafito harda gudunta, afalo ta sameshi rike da ruwa yana sha ta zauna akusa dashi, cire ruwan yayi daga bakinshi yace "ina Ummy" "sun tafi gidan kaji" gyada mata kai yayi kawai dan bayason magana ya lumshe ido da sauri takara matsowa kusa dashi kaman zata shige jikinshi tace "sick?" yagane tambayan shi take ko baida lpy hakan yasa ya girgiza mata kai ya bude ido tareda sauke ajiyar zuciya hannunshi yasa a aljihu yaciro wayarshi daga pocket yana daddannawa kafin ya bude page din policeng inda aka saka hoton ta ya bata wayar ta karba tana kallonshi ahankali yace "look at d screen wacece wanan?" da sauri ta kalli screen din hoton ta kafe da ido sosai sanan ta kalleshi ta nunamai wayan tace "nine?" ta tambaye shi, wani irin ajiyar zuciya yayi yace "yea kene ance sunanki Bilkisu Abdul..." makemai kafada tayi kaman zatai kuka tace "my name is Ameerah ko sweetheart" shiru yayi yana kallonta daidai lokacin Ummy ta shigo tanamai sannu da zuwa ya amsa sanan yamata magana da yaren french. "ki hada mata kayan ta gobe zan kaita garin su police sun bada sanarwa chan police headquarter zamu kaita nida Dr Ameenu na kano, insha Allah once naga sun kira iyayen ta agabana nagansu dakaina saimu juyo mudawo, zainab ta tayaki kwana zanma Umar magana ya barta" gabaki daya jikinta yay sanyi hakan yasa ta juya kawai ta shiga daki dan wani irin kukane yazo mata, sanan ya kalli Bilkisu data tasashi agaba tana kallo yace "wat? Mesa kike kallona haka" dariya tayi sosai dan har tana buge filon kujera suna faduwa kasa sanan ta kalleshi cikin dariya tace "sweetheart wlh ina sonka ne" tacigaba da dariya tsayawa yayi yana kallonta he's sure awajen su Ummy takejin irin maganganun nan, mikewa tsaye yayi jin ana kiran sallan magrib yace "go and pray zanje masallaci" kaman zatai kuka tabishi da kallo harya fita sanan ta share yar hawayen daya zubo ta wuce dakinsu.
Wuraren nine yadawo lokacin hartai bacci yaci abincin da Ummy takawo mai yawuce daki duk jikinshi yay sanyi.

Wahe gari wuraren goma nasafe yafito daga dakin idanunshi sunyi jajir shima sabida uban knocking kofar shi datake tayi tanamai kuka ne, murmushi yamata bayan ya bude ganin yanda take uban kuka yace "stop crying oya je Ummy ta shiryaki mufita" ya kalli Ummy dake zaune akan kujera yamata alamu dakai hakan yasa ta mike tariko ta sukai dakinsu shikuma yakoma ciki ya shirya cikin manyan fararen kaya dasuka karbe shi sosai yafito da baban trolley dinta da Ummy tahada takawo dakinshi tun jiya da night yafito dashi yasa a boot din mota daidai lokacin motar Dr Ameenu ta danno kai compound din dan murmushi yayi yajira haryay parking yafito shima cikin manyan kaya shada blue yazo yace "guy gaskiya da motar ka zamu bazan kona maina ba kafini kudi" tsaki yay ya wurgamai key motar ya chabe yace "kai xakai driving" ya kwalama Ummy kira sabida tafito da ita shikuma ya bude motar ya shiga Dr Ameenu ma ya zaga ta bangaren driver yabude ya shiga, ita tafara fitowa da gudun ta tana sanye cikin black body hug da black straight skirt sai Ummy ta daura mata maroon kimono me shegen kyau akai ta kulle mata belt din kimono ta gaba sanan tamata rolling black vail akai da keda one one stone ta bakin gyalen tasaka mata takalmi baki maidan tudu daya fito da hasken kafarta, gabaki daya Yay nisa a kallon ta yanda tai kaman balarabiya tsaban kyau maganar ta dayaji akanshi ya fargar dashi. "sweetheart wai zamu fita?" gyada mata kai yayi batare dayace komiba, shidai Dr Ameenu waya yaciro abinshi yakira matarshi suna hira, da sauri tace "ina zamuje park zamu?" girgiza mata kai yayi yace "shiga mota garinku zamu" "inane garin mu?" tafada tana murna, dan murmushi yamata yace "shigo mota muje kigani" tsalle tayi ta bude kofar baya ta shiga tanama Ummy bye bye, kudi yaciro dayawa yabama Ummy yace "I will call u anjima" addua sosai tamusu sosai sanan Dr yaja motar suka bar gidan saida suka danyi nisa yace "ka kosan na dauko file dinta na hospital kasan police da tambayoyin banza kafin suce mumuka saceta na dauko file dinta kai ID card dinama na jikina am not ready to enter any gbese" dariya yadanyi sabida yanda ya karashe maganan yace "kai kayi aure nazaci zuciyar ka zata chanza ta dena wanan tsoro ashe babu abinda ya chanza" hararan shi Dr yayi yacigaba da tuki batare dayace komiba itakuma tana baya saiyima teddy ta mai gashi kitso take tana yar wakarta na yar gala gala yarinya yar gala gala wasan yara ahankali, ta madubi yake ta kallonta har daga baya bacci ya kwashe ta.

Dayake wuraren sha daya sukabar Bauchi sai gurin biyu da rabi suka shigo garin kano kafin sukai police headquarter kuma sai wuraren karfe uku da minti biyar, parking sukayi suka fito ya zagayo tabaya rike da pringles din daya saimata a hanya da bottle water sabida bacci takeyi tuntuni ya bubbuga kujeran hakan yasa ta bude ido da sauri ya dauke kai, waige waige tayi tana kallon wurin tace "sweetheart mun iso garinmu?" dan ita tazaci wani wurine mai suna haka, gyada mata kai yayi hakan yasa tafito tana Kalle Kalle shikuma ya maida kofar ya rufe ya kalleta yanda take kallon polisawan daketa harkan su sun ririke bindigogi yace "muje" girgiza mai kai tayi tana neman yin kuka ta nunamai yan sandan ahankali yace " don't worry babu abunda zasu miki muje" gaba yayi tana binshi abaya har inda Dr Ameenu yake suka shiga ciki saida suka rubuta sunayen su sanan sukace inspector Husaini Ahamad suke nema dan sunanshi aka rubuta a page, kujera aka nuna musu shima dan polisawan sungan su sunyi shigan alfarma ne yasa sanan wani daga cikin su yatafi office din inspector yay kusan 10 min sanan yafito yace "muje" tashi sukayi suka bishi har office din inspector dake zaune yana jiran su sanan yafita, inspector na ganinta ya mike tsaye cike da mamaki kafin ma suyi magana yace "am coming ku zazxauna" fita yayi yay upstairs office din CP, yana shiga ya kame yay saluting CP sanan yafada mishi abinda yagani Cp yabiyo shi suna zuwa office din tsayawa yayi baice komiba yana kallon Bilkisu take fama da bude goran ruwa saikuma yasa hannu a aljihu yaciro wayarshi ya duba yaga ai yarinyar hoton nanne wacce akai kidnapping wani irin shan mur yayi ya kalli su Aaman dake kallonsu yace "su waye ku? And waccece yarinyar nan? A ina kuka samota? Menene hadinku da ita?" kafin ma Aaman yace wani abu Dr ya mike yaciro ID card dinshi yace "am Dr Ameenu and my Friend here is Barrister Aaman, nan ya shiga basu labarin komi tundaga kan yanda Ayaan ya tsinceta da lokacin daya kawota hospital yagama sanan ya bashi file din medical record dinta. Saida Cp yagama dubawa yay wani irin hamdala ya mika musu hannu yana godiya sanan yace sutashi suje office dinshi dan gaskiya wanan good news gwara Alhaji ya gani a office dinshi ba'a office din inspecta ba yau ya tabbata sabuwar mota da kujeran maka zai samu, office suka tafi suka zazzauna sanan yadau waya yakira Abba.


Alhaji dasu Baba da Baba Sulaiman wanda yadawo jiya jiyan nan sabida kiran da Mami tamai dan Alhaji ma ciwo ne yarufe shi, yaudai duk dauriyan da Abba yakeyi kasawa yayi yafashe da kuka sosai, babba dashi amma kuka yake ganin abinda yafi soyuwa agareshi, aduniyar nan gabaki daya ma Ayaan baimasan wake kanshi ba, gashi yaki yarda a kaishi asibiti agida Dr Ibrahim yazo yamai allura yamishi fixing drip, Mami dai fita daga dakin tayi ta shiga nata tana kuka sosai, Baba ne ke kanshi yanamai addu'a aka, shikuma Baba Sulaiman yana calming Abba down, ringing da wayar Abba yayi yasa Baba Sulaiman ya mike ya dauko wayar daga kan gadon da Ayaan yake a kwance ganin Cp ne yasa ya mikama Abba yace "ka dauka Cp ne Allah sa Muji alkairi" goge idanunshi yayi da bakin malummalum din dake jikinshi ya kalli Ayaan da aka sakama oxygen dan baya iya numfashi da kyau ya sake girgiza kai yana kokarin tsayar da hawayen dakeson zubomai, yay picking call din tareda yin sallama ahankali, zumbur yamike tsaye yana neman fadi Baba Sulaiman ya taroshi bakinshi har rawa yake yace "Cp kace anganta, Bilkisu Bilkisun mudai?" kowa na dakin kallonshi yake tsabagen murna ma jefar da wayan yahi ya tsugunna yay sujjada sanan yayo gadon baima bi takan Baba Sulaiman dake tambayan shiba yay cupping fuskar Ayaan da idanunshi ke lumshe yana girgiza shi hawaye na gangarowa daga idanunshi na farin ciki yace "Boy, Boy tashi muje police headquarter anga Bilkisu Boy, anga matar ka" da kyar ya bude idanunshi dasuka kankance ya rike hannun Abba da karfi yana kallon fuskar shi batare daya iya magana ba, gyadamai kai Abba yayi yace "yes, yes my baby Boy, anga matar ka, i love u Boy so so much, oya get up let's go get ur wife" da taimakon Abba da Baba yatashi har lokacin kallon Abba yake dan gani yake kaman zafin zazzabi yasa yakejin Abba nakiran anga Bilkisu, ciremai robar oxygen din Abba yayi sanan yacire mai drip din ya kalli Baba Sulaiman yace "ban rigan shi" clean white t-shirt ya mikomai Abba ya dauramai akan singlet din jikinshi suka mikar dashi yay mugun haske lips dinshi jajir ga rama saidai bai hana kyanshi fitowa ba, takalmin yasaka da kyar Abba da Baba suka fitar dashi shikuma Baba Sulaiman ya shiga dakin da Mami take yace "anga Bilkisu kije gida kuyi girki dan zamu dawo da bakin da suka kawota, kibar kuka Boy ya warke haha" yay dariya kafin ma Mami ta jefamai wata tambaya haryabi bayan su Abba da gudu duk suka shiga mota sai headquarter.

Tun kafin suyi parking suka hango Cp yana washe musu baki dan kasa hakura yayi ya zauna aciki so kawai yake dashi Alhaji ma zasu fara haduwa, fito da Ayaan sukayi dake bude ido da kyar Cp yakara so wajen yana kallon Ayaan dake kallonshi da idanunshi dasuka kankance yace "ciwo ya kare, muje Alhaji suna office dina" yana gaba suna biye dashi abaya har upstairs Cp ne yabude office din ya shiga suna biye dashi, daidai lokacin Bilkisu ta daura hanunta akan kafadar Aaman tanason ta leka meyake nunama Dr Ameenu awayan shi dayan hanunta kuma rike da pringles takai baki tana gutsura. Dukansu binta sukai da kallo harda Ayaan daya kara bude ido da kyau yana kallonta tundaga yatsar kafarta har zuwa kanta, dago dakai sukayi jin anbude kofa da sauri Aaman ya ture hanunta daga kafadar shi suka mimmike tsaye shida Dr dan daga ganin su sun gane family tane sabida manyan kayan dasuka sa, hannu suka mika ma su Abba daduk Bilkisu suke kallo barinma Ayaan dako kyafta ido bayayi, itakuma tana zaune tanacin pringles dinta batare datama kallesu ba, ga teddy ta agefe, ajiye pringles dinta tayi tadau bottle wata dinta ta mike tsaye ta kusa da Aaman kaman zata shiga jikinshi ta mikamai ruwan kaman zatai kuka tace "sweetheart budemini" wani irin mugun tari da Ayaan yafara yasa ta juyo dakai tana kallonsu barinma mai tarin da manyan mutanen ke kokarin rikeshi ganin yana neman shidewa, da sauri ta boye abayan Aaman tasa hannu ta dafashi ta leko dakai tana kallon mutanen dai dai, hada ido suk sakeyi da me tarin da idanunshi sukai jajir yana tari yana kallonta jijiyoyin kanshi duk sun fito shikuma Aaman sai kokarin tureta yake daga bayan shi amma taki saima kara rirrike mai riga datayi tabaya tana make kafada tana "oh'oh" shikuma yacigaba da tureta, wani irin kallo Ayaan yama Aaman kirjinshi na wani irin zafi kaman an juye garwashin wuta daidai lokacin wani dan Sanda ya shigo dakin hanunshi rike da kulki, fizge jikinshi Ayaan yayi daga hannun Abba da duka karfin dayazo mai, yatako ya fizge kulkin hanun dan sandan daya shigo azuciye yay kan Aaman.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

67 - 68

Da sauri Cp da dan sanan daya fizge Mullin daga hanunshi harda Baba Sulaiman suka rike gam gam, Baba Sulaiman yace "Ayaan are u okay" kokarin watsa dasu yake yana ma Aaman wani irin kallo shima Aaman kallon shi yake irin kallon wanne wanan Kuma, Abba ne ya karbe kulkin daga hanun nashi ya zaunar dashi da kyar ya zauna akan kujeran amma gabaki daya baida natsuwa ahankali Abba ke tofamai addu'a Cp kuma ya kalli su Aaman da har lokacin suke tsaye ga Bilkisu dahar lokacin ke tsaye abayan shi ta rike mai riga yace "ku zauna" Baba dai har lokacin yakasa daina kallon Bilkisu mamakin yanda tarike wani namiji agabanshi ko kunyar shi da tsoron shi ma da bataji ba shiya hanashi magana, he's totally shock, dauko file dinta dake kan table Cp yayi yazo har gaban Abba dake gayama Ayaan da kanshi ke kasa yana wani irin numfarfashi magana a kunne ya mikama Abba file din yace "gashi Alhaji medical record dinta ne, sanadi yar faduwar nan datayi tasami tabin kwakwalwa banda haka tasami memory loss" da sauri Ayaan yadago kai da jajayen idanunshi ya kalli Cp da sauri ya karbi record din ya bude file din yana duddubawa yana karanatawa hanunshi har rawa yake saida yagama karance wa tass sanan yadago kai ya kalleta tana kusa kusa da Aaman kaman zata shige jikinshi tadau teddy tanata jijjigata tana wasa, wani irin zafi dayaji zuciyarshi nayi yasa yaji wasu irin zafafan hawaye naso su xubomai, Abba daya gama karantan dan nashi tsaf ya mike tsaye murmushi kwance akan fuskarshi ya karasa gaban su Aaman ya mika musu hannu yace "mungode, mungode, ubangiji Allah ya biyaku, dan Allah karku cemin a'a kuzo muje gida munsa muku girki dan Allah ya'yana karkuce bazakuba" yay maganan yana kallon su harda Dr, sosai nauyin Abba ya kamasu hakan yasa yace "to Abba" Cp ya mikama police din daya shigo plain sheet da pen ya kalli Aaman yace "zaka iya suffan tamana samari biyar dasuka fito da ita daga bakin motar" dan shiru yayi saikuma yace "yea" nan ya dinga siffanta su police din na zanasu saiko ga sketch din fuskar su Abba ya karba yana kallo babu wanda ya gane cikin su daga nan Abba yace sutafi, mikewa yayi da sauri tamike itama tana kokarin rikoshi Baba ya daka mata wani irin tsawa. "Bilkisu kewai mehaka" dago kai tayi ta kalli Baba saikuma ta murguda baki tana bobboyewa abayan Aaman tace "ni sunana Ameerah ko sweetheart" baya Ayaan yayi zai fadi sabida wani irin jiri dayake dibanshi da sauri Abba ya rikeshi ya kalli Baba yace "kasan bata hayyacin ta karka ga laifin ta" ya kalli Aaman dake faman tureta daga bayanshi yace "kumu tafi yan albarka" murmushi yayi yace "to Abba" su Abba suka rike Ayaan suka fita dashi. Da sauri Aaman ya juyo ranshi ya mugun baci yace "d next time dakika rikeni ko shigewa jikinta saina mareki naughty girl" yay gaba da sauri tsabagen haushi, Dr ya kalleta yanda take goge kwalla ahankali yace "muje" murguda mai baki tayi tana goge kwalla tabi bayan shi suka fita daga office din. Suna kaiwa waje Aaman ya nuna mata motan su Abba yace "jeki shiga motan su Abba" kallon su Abba tayi yanda duk suka tsatsaya suna kallonta barin ma Ayaan kaman zai hadiye ta, ta murguda musu baki tace "oh'oh ni namu zamu shiga" murmushi Abba yayi yace "bakomi kabarta anan muje" da sauri tabude baya ta shiga sukuma suka shiga gaba Abba ya kalli Ayaan yanda yake kallon su ahankali yace "Boy control your heart kar zuciyan ka ta buga haba dan Allah zaka halaka kanka ne jibi yanda kirjinka ke bugu, let's go" bude mota yayi ya saka shi ciki sanan ya shiga shima driver yajasu sukabar wajen motar su Aaman biye da ita har gidansu sukai horn security yabude, sukai parking suka fiffito tana makale kusa da Aaman har suka je part din Mami dayake Big Mummy taje bikin yar kawarta sai Kalle Kallen gidan take tana washe baki tana kallon fuskar Aaman murya chan tace "sweetheart nanne garin namu" ko kallonta baiyiba, babban falon Mami Abba yamusu iso suka zazzauna tana kusa da Aaman, ahankali Mami ke saukowa daga sama cikin shiga ta alfarma idanunta akan Bilkisu dake zaune kusa da wani tana wasa ta teddy Ayaan sai kallonta yake kaman ya hadiye ta, su Abba ma duk ita suke kallo har gabanta Mami tazo zata rungumeta da sauri ta matsa kusa da Aaman tana make kafada hakan yasa Mami tace "Bilkisu" murguda baki tayi tace "Ameerah sunana" tai maganan kaman zatai kuka, kasa magana Mami tayi ta tsaya tana kallonta Abba ne yay jarumtar cewa. "batada lafiya ne Firdausi, je akawo musu abinci" tadade tana kallon Bilkisu gaisuwar dasu Aaman kemata ne yasa ta farka ta amsa musu tana murmushi kafin ta juya tai kitchen nan tasaka yan aiki suka wadata su da abinci da abubuwan sha amma sun kasa ci sabida kunya drinks kawai suka sha shidai Ayaan jingina yay da kujera ya lumshe ido kaman mai bacci amma Bilkisu yake kallo bakaramin daurewa yayiba danji yake kaman ya kashe wanan mutumin datake ta manne mawa, Abba ne yay gyaran murya yace "godiya zan kara muku yarana yanda kuka taimaka mana kuka taimaki yarmu kuka sakamu acikin farin ciki ubangiji Allah ya faran ta muku haka ranan gobe kiyama" ya nuna malam yace "wanan shine mahaifin Bilkisu, ga Sulaimanu shikuma kanina ne, nikuma nine mahaifin mijin Bilkisu" wani irin bugawa kirjin Aaman yayi kafin ya farka daga hakan Abba yanuna Ayaan dake kusa dashi yace "gakuma mijin ta nan" saiya nuna Mami dake zaune gefen Baba Sulaiman yace "ga mahaifiyar shi chan" innalillahi wa innalillahi raji'un kawai Aaman ke ambata aranshi, da hikima batare dawani ya lura ba yakara matsawa daga kusa da ita yanda ta shige mai, wani irin zafi zuciyarshi keyi wasu irin hawaye masu dumi ne suka taru a idonshi ya saci kallon Dr da shiyake kallo shima, ahankali ya girgiza mai kai hakan yasa ya hadiye hawayen da kyar ya kakalo murmushi yadan kalli Ayaan aranshi yace no wonder dazu yayo kanshi baikawo komi dazu ba dan yazaci hala mutumin ya dauka sune suka saceta saisa yay haka ashe shine mijinta, ashe Ameerah matar aure ce, maganar Bilkisu ce yasa yadawo daga dogon zancen zucin dayake ta matso kusa dashi sosai tana nunamai pin din gyalen da Ummy tasaka mata takama rolling gyalen dashi ashagwbe tace "Sweetheart remove it for m..." bata karashe maganan ba sabida wani irin mugun tari daya turnike Ayaan akaro nabiyu da sauri Abba ya dau goran ruwa ya bude yabashi ture ruwan yayi azuciye yanaso ya mike tsaye Abba ya take kafarshi yasan halin danshi koba komi shiya taimaketa kuma Bilkisu bata hayyacin ta. "sweetheart plz cire" takara matso da kanta tanaso tamai kuka da sauri ya mike tsaye ya kalli su Abba yana kakalo murmushin dole yace "zamu koma yanzu karmuyi dare" kafin Abba dasu Baba da Mami dasuka Mike tsaye suma suyi magana Bilkisu tace "yeee zamu tafi, uhnn sweetheart fitsari nakeji jirani nayi" saikuma takara matsowa kusa dashi tace "where is d restroom" da kyar ya tattaro kalaman dake bakinshi dayay nauyi sosai ya nuna mata Mami yace "ga Mum nan je ta kaiki kiyi" kallon fuskarshi tayi jin yanda yay magana saikuma ta washe mai baki tace "okay wait for me" ta sakamai teddy ta ahannu tace "hold my teddy" da sauri tai wurin Mami dake kallonta ta washe mata baki tace "Mum muje" hanunta Mami takama suka hau stairs sai juyowa take tana kallon Aaman tana washe baki har sukai sama da kyar ya kakalo murmushi yace "mutafi Abba kafin tafito" rakasu su Abba sukayi har waje suka karbi number su shidai Ayaan yana zaune falo suna fita ya mike da kyar yay upstairs yay dakin Mami yabude kofa ya shiga Mami ce kadai adakin zaune tana jiranta tana ganinshi ta mike tsaye tai murmushi tace "bari naje nahado mata abinci bataci komiba" tafita daga dakin, kimono ta da gyalen ta dake kan gadon yabi da kallo ahankali ya zauna akan gadon yadau kimono ya rungume sosai yana shakan kamshin dasuke fitarwa, karan bude kofar bathroom dayaji yasa ya zame rigan daya fuskarshi bama ta lura dashi ba tafito tana kokarin jan straight skirt dinta data tattare ta barshi a cinya zuwa kasa, tundaga kai yake kallonta har yatsa, kallon black body hug din da tasa yayi ba karamin kyau yamata ba gashi ya kamata yabi jikinta hakan saiya kara bayyana cikan kirjinta dago dakai tayi bayan tagama jan skirt din yakai kasa ta kalleshi bata damu da ganinshi ba amma ganin rigan ta da gyalen ta a hanunshi yasa ta daure fuska a tsiwace ta rike kugu tana hararan shi, dan lumshe ido yayi yakara budesu ya sauke akan fuskar ta, cike da masifa tayo cikin dakin agaban shi ta tsaya ta murguda mai baki ta mikamai hannu tace "bani rigana aiba naka bane, sweetheart yasaimin" wani irin fizgota dayayi saida tafado jikinshi, gyara mata zama yayi ajikinshi tana mutsu mutsun ta sauka ya sakala hanunshi ta bayanta ya riketa gam yana numfashi da sauri da sauri yana kallon kwayar idonta,

Please Login or Register in order to submit comment