Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalleta yanda ta tsareshi da ido, dan murmushi dole yasake yimata yay yunkurin kulle hannun, wani irin ihu datayi wlh saida ya firgitashi dan mutum ne shi marason hayaniya tawani irin fashe da kuka tace "ci" baisan lokacin daya hadiye apple dinma, tafashe da dariya tana kallonshi tacigaba dacin apple dinta shikuma ya kunna motar ya cigaba da tafiya har gidan gona, bishiyoyi kala kala da shuka ne daban daban, ta gefe kuma wani flat ne kwara daya babba sosai, parking yayi yafito ya zagayo ya bude mata da sauri tafito tana waige waige rike da apple dinta ahannu, gaba yayi hakan yasa tabishi da sauri ya bude kofa ya shiga, babban palour ne dayasha kujeru sai tv bango akan dogon kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa dashi da sauri tana kallon fuskarshi, shima ita yake kallo saikuma yaciro wayarshi yay dailing number wani mai kula da kajinsu ahankali yace "Umar dan Allah turomin Zainab" katse wayar yayi ya ijiye ya tashi, da sauri itama ta tashi dan juyowa yay ya kalleta saikuma yay Jim yacigaba da tafiya abinshi, kitchen ya shiga tana biye dashi tea yahada mata mai kauri a cup yadau slice bread ya shafa mata butter ya daura mata akan plate ya dauko ya juyo ya kalleta ganin yanda take kallonshi tana kallon abincin yasa yace "zaki ci?" da sauri ta gyadamai kai yace "okay to muje kici" yajuya yafita daga kitchen din da gudu tabiyoshi falo suka shiga ya ijiye mata cup din tea da plate din akasa da sauri ta zauna tana kokarin cire hijabin takasa saita dago kai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta kwaye fuska tace "yaki fita" daidai lokacin wata yarinyar yar budurwa haka doguwa sanye da hijabin ta ta shigo bakinta dauke da sallama tace "gani Uncle" murmushi yamata yace "yauwa Zainab dan tayani cire mata hijabin nan" murmushi tayi ta shigo dakin tace "Uncle bakuwa kayi" kwanciya yay akan kujera yace "yeah bamata da lpy ne" daidai lokacin zainab takaraso gabanta da sauri takoma baya ta make ajikin kujeran dayake kai tanason tai kuka, ahankali yace "hijabin xata cire miki karki damu she's my sister" kallonshi tayi idanunta sun ciko da kwalla ya gyada mata kai tareda nuna idonta ahankali yace "don't cry, bari tacire miki" ya kalli Zainab yamata alamun datazo, zuwa tayi da kyar ya samu tabari zainab tacire mata hijabin sanan ya dauko mata tea ta tacigaba da sha, saida tagama sha, nan ma bakaramin daru yasha da itaba kafin ta bari zainab ta kaita ciki dantai wanka da kyar yasamu ta yarda suka shiga bedroom, suna shiga yadau key yafita dan zuwa yasiyo mata kaya sanan yayo take away danshi bai iya girki ba.

Ko minti talatin baiyi ba ya dawo ya paka motar shi a tsakar gidan, tun daga waje yakejin kukan ta girgiza kai kawai yayi ya bude bayan motan ya dauko katoton babban leda daya siyo mata kayan sawa na mata, sai kuma ledan take away ya dauko yay hanyar cikin gida dashi da sallama ya bude kofan ya shigo falon da gudun ta tafito daga uwardakan tana sanye da doguwar rigar atampa ja daga gani zainab ce ta bata kayanta, tazo da sauri tana kuka ganin shirin fadawa jikinshi take yasa ya juya da sauri yay facing kujera yana daura ledokin akan kujera hakan yasa ta tsaya abayanshi tana goge kwalla, ahankali ya juyo ya sauke idanunshi akan fuskarta yanda hawaye ke gangarowa yanabin kuncinta, anatse yace "mesa kike kuka" hanyar uwardaka ta nunamai daidai lokacin Zainab tafito tana kokarin saka hijabi kayan jikinta duk sun jike, yace "ita ta jikaki haka zainab?" dariya zainab tayi tazo wajen tace "ihu tadinga yi wai bazata yi wankan ba dana hada mata ruwa shine ta dinga zubamin da kyar dai tayi, Uncle wlh tanada kyau bakuwar nan naka ya sunanta?" da sauri itama Bilkisu ta kallai tanuna kanta tace "ya sunana uncle?" dauke kai yayi dan idanunta namai wani irin ya zauna akan kujeran yadau leda daya na take away ya mikama zainab a kunyace ta karba tana godiya, da sauri ta zauna kusa dashi harda leka fuskarshi dago kai yayi ya kalleta hakan yasa ta washemai fararen hakoran ta, dan murmushi yamata yana mamakin ta, tuntsirewa tayi da dariya takara matsowa kusa dashi tace "ya sunana?" Ahankali yace "kinaso na baki suna?" da sauri ta gyadamai kai tana washe baki lumshe ido yayi kafin ya budesu yakara daurasu akanta yace "okay dagayau sunanki Ameerah" da gudu ta mike tsaye tana tsalle "yeeeee Ameerah, Ameerah" ta kalli Zainab data tsaya tana kallon ta tana yaba kyanta aranta ta murguda mata baki tare da hararan ta turo baki tace "sunana Ameerah ko Uncle" daga mata kai yayi Zainab tace "Uncle natafi" kudi yabata taki karba tafita da sauri.
Ahankali yabude dayan ledan dayan take away yaciro jellof rice ya kalleta inda take tsaye tanata kiran kanta da Ameerah tana juyi ahankali yace "Ameerah" da sauri ta dago kai ta kalleshi tareda washemai baki abincin ya nuna mata hakan yasa tazo ta zauna kusa dashi yasa mata spoon yabata tafara ci saida taci kusan rabi ta ture tana yatsine fuska, maganin ta yabata da ruwa tasha da kyar tasha sanan tadau abincin tanaci tana wasa dashi shikuma chatting yake a watsapp da Dr Ameenu, kanta dayaji ya kwanto akan kafadar shi yasa ya dago kai ya kalleta tai bacci ga takeaway akan cinyarta shinkafan dukya zuzzuba akan rigarta yakai kusan 5 minutes yana kallon fuskarta kafin ahankali ya janye kafadar shi ya gyara mata kwanciya akan kujeran tareda karbe take away ya kakkabe shinkafar jikinta acikin roban yawuce yakai kitchen sanan yadawo ya zauna kujeran nesa da ita yana kallon fuskar ta, addu'a kawai yake ko ina iyayen ta suke Allah ya bayyana su.




*kano*

Ahankali Abba yay sallama ya turo kofar dakin Bilkisu wanda Ayaan ya mayar nashi, abu dayane ke fitar dashi daga dakin shine salla ko wani irin zazzabi yake saiya tashi yana dafe bango yatafi masallaci. Mami itama ta tare gidan dan kula dashi, Big Mummy kuma takoma gida sabida bakuwar ta Munari wacce yanzu take neman kusan sati hudu da zuwa kenan amma dai kullum saitazo ta duba Ayaan. Shigowar Abba kenan bayan ya raka Dr Ibrahim dayazo dubashi dan anyi anyi dashi yaje asibiti yaki.
Ahankali Abba ya zauna kusa dashi akan gadon hanunshi rike da tray na abinci dan yau throughout yakicin komi, dafa goshin shi Abba yayi hakan yasa yadan bude idanunshi da sukai jajir, gashin shi da gemunshi sunyi busu busu, hannu Abba yasa ya taimaka mai ya tashi zaune ya jingina da gado, Abba yace "zoka ci abinci Boy so kake ka kashe kanka wai, dare da rana police nakan case dinan, nasa amana rokon Allah, in sha Allah, Allah zai bayyana mana gaskiya, da kansu zasu dawo da ita" Abba yay maganan yana mika mishi bowl din pepper soup, ture bowl din yayi da hannu ya dau pillow ya rike muryan na rawa yace "bazan iyaci ba, tana chan hala ma basu bata abinci ba halama sunata dukan tane yanzu haka, kullum da tunanin ta nake wuni na tashi Pops..." yanda muryan shi ke rawa yasa Abba ya jawoshi jikinshi yana bubbuga bayanshi kafin ahankali ya ciroshu yama forehead dinshi peck yace "za'a ganta da izinin Allah yanzu dai ko 3 spoon ne kasha kaga zaria zani inaso naje nasami mahaifin Bilkisu, yakamata susan wats going on, idan bamu fada musu ba bamuyi adalci ba" dafe kanshi dayakeji kaman zai fashemai yayi Abba kaman zaimai kuka yace "sannu Boy oya sha sha saika sha magani" da kyar ya bude ido ya karbi coffee da Mami tasamai madara, saida yasha sanan Abba ya lullube shi da bargo yafita baitaba sanin haka Boy keson Bilkisu ba, driver yajashi sai zaria.

Kiran sallan la'asar ya farkar dashi daga baccin wahalar daya dauke shi da kyar ya sauko daga gado ya shiga bayi yaje ya dauro alwala yafita daga dakin a stairs ya hadu da Mami ta hado abinci a tray zata kawo mai da sauri ta ijiye tray akasa ta rikeshi ganin kaman zai fadi, kaman zatai kuka tace "ina zaka ahaka Ayaan kana layi?" da kyar ya ware idonshi ya kalleta yace "masallaci zani Mami" girgiza mai kai tayi tace "Ayaan no mukoma daki kayi achan u don't look good, baxaka iya zuwa masallaci ba" ahankali yace "zan iya Mami please ki barni nasan nama Allah laifuffuka da yawa, cikinsu harda rashin sonyin salla, amma yanzu in sha Allah ba ciwo ba koma me saina je masallaci" ahankali ya zame hanun daga nata yana tattaba karfen stairs ya sauka kasa Mami tabishi da kallo da sauri ta share hawayen daya zubomata suna ganin jarabawa.

Koda aka idar da salla yafi minti talatin azaune shi kadai amsallacin dan duk an watse sai shi baima da karfin tashi, dafashi dayaji anyi yasa ya dago kai limamin masallacin ne daya shigo daukar wayan shi daya manta dashi yace "baka da lafiya ne na taimaka maka na kaika gida" dago kai yayi ya kalli Imam kafin ahankali yace "tambaya nakeda shi" yanda yay maganan kaman zararre yasa lmam ya zauna ya lankwshe kafa, jingina kanshi dayamai nauyi yayi ya kalli Imam da idanunshi dasuka kankance ahankali yace "a Austria na girma, achan nai secondary school har nazama likita, am a very bad boy, idan nace bad i mean bad baddest, d only thing danasan banayi shine shaye shaye but zuwa clubbing, daukan mata, saka sarka, dan kunne, rashin salla duk nine, bayan nakare karatu na tattas na dawo harna fara aiki a asibitin abokin Pops dina inanan da halina even though Mami na da Abba suna kokarin su barinma Mami suga na dena amma naki, bansan meya sameni ba sai akace na haukace, ranan dai dana farka na ganni cikin kaya masu datti, awaje mai datti da bola ga wari, sanan gani kusa dawata yarinya wacce ita ta taimakeni da ina hauka hawaye duk sun bushe a idonta, ba karamin wulakanci namata ba har ina marinta a fuska amma kasan wani abu Imam?" yatambayi limamin yana bude ido kadan dan idanunshi a lumshe suke Imam yace "ina jinka" cije leben shi yayi cikin jin azaban da kanshi kemai yace "bayan na koma gida dudda fuskar yarinyar data taimaken nata bijiromin koda kulle ido kuwa nayi amma nai shiru naki fadinma babana harsai randa babana ya tamabye ni ya akayi na warke, na fadanmai, shine muka shirya mukaje zaria neman gidansu, bazan taba manta ranan" ya dafe kanshi yana wani irin murmushi yace "kafarta nafara gani da dogayen yatsun kafar dan batasa takalmi ba, kafarta na cikin jan lalle dayay wani irin kyau ta shigo dakin baban nasu da muke ciki tana sanye cikin pink hijabi mai hula, yanayin yanda take magana da komi nata sainaji ta shiga raina sosai, bantaba son wata mace aduniyar nan ba, banma san ya ake so ba amma saina ji ita ta tsayamin arai sosai, kome nakeyi saita fado zuciya ta, bantaba nunama kowaba saidai duk lokacin dazan hadu da ita saina mata wulakanci, naci xalin ta, nasata kuka, ranan da mahaifiya ya bijiromin da zancen aureta ranan banyi barci ba sabida farin ciki amma ban nunama kowaba saima kekashe ido danayi nace banison ta, ni mamakin kaina nake nine keson karaman yarinya haka yar talakawa, aranan da mukaje gidansu mahaifin ta yace mana ansa mata rana bikinta saura sati daya zuciyata takusa bugawa, da gangan nai karyan waya nake nafito ko zan ga wani almajiri ya nunamin waye isyakan da akace zata aura, ina fitowa naganta tana hira da shi jinai kaman na kashe isyakan wlh Imam, luckily sainaji yana fada mata inda zashi koda muka tashi tafiya saiban bisu munkoma kanon ba, adayake nai wayau nadau hoton isyakan saina turama wayan su kanin abokina dake zaria yana karatu a ABU da abokanshi hoton Isyakan nafada musu inda naji yace zaije, haka suka je basu ganshi ba suka fadamin saina cemusu to suzo layin su yarinyar su jirashi, suna zuwa suka kamomin shi aka kaishi hotel din dana sauka, kaga dukan danami kuwa wlh nakusa harbeshi sabida tsananin kishin yanda na gansu tare suna hira harda wani wai yasiyo mata ice cream, to saikuma na kwabi kaina akan kissan kai ba halin da musulmi yakama ta yanayi bane, saina bijiro mishi da ranan biki awajen daurin aure yace yafasa aurenta sanan namai kyauta sosai namai warning daya tsorata yaron ainun, shekaran jiya saida nakira shi na rokeshi ya yafemin bansan ko harda alhakin shi yake binaba yanzu ba, yace ya yafemin yanzu ma yay aure sanan ya bude shago dakuma makaranta da kudin dana bashi" sai yay shiru Imam yace "ina jinka" ahankali yace "Imam inason Bilkisu sama da yanda kake tunani amma inhar zan hadu da ita sau dari saina sakata kuka sau dari da hamsin, inci zalinta in gaya mata bakar magana, har muka tare agidan mu, yanzu haka yan kidnappers sunzo har gida sun dauke min ita, i think Allah na hukunta nine akan laifuffukan dana mishi" hawayen daya zubomai ne ya share da sauri yana sauke ajiyan zuciya ahankali yace "na tuba Imam, bazan kara koma ma aikin alfahasha ba, dan Allah katayani rokon Allah yadawo min da farin cikina Bilkis, ya tsaremin ita duk inda take, yadawo min da ita cikin koshin lpy, wlh na tuba, na tuba, na tuba, nai nadaman duk abubuwan danai ada, I love my wife more than life itself, Imam mezanyi Allah ya yafemin yadawo min da Bilkis?".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




65 - 66


Sassanyar murmushi Imam yamai yace "Allah gafurur Raheem ne, kadage da addu'a kadinga tashi cikin dare kana rokon Allah, kana gayama Allah bukatun ka, matar ka zata dawo, da izinin Allah zan tayaka da addu'a banda hakama duk inda take Allah ya tsare maka ita ya kare maka ita" ahankali yace "Ameen" Imam ya mike ya mikamai hannu yace "tashi na taimaka ma katafi gida" ahankali yamika ma Imam hannu da taimakon shi ya mike tsaye suka fita daga masallacin daidai wajen masallacin suka hadu da securities din da Mami ta turo azo adubo mata shi dan tajishi shiru, mika musu shi Imam yayi suka tafi dashi gida.
Suna shiga cikin gidan idanunshi suka sauka akan motar shi dake parking lot, wajen motar yayi da taimakon su ya bude, idanunshi ne suka sauka akan jakar Bilkisu daya karba ranan dazata bata hakan yasa ya mika hannu ya dauko, ahankali ya rungume jakar sosai ajiki yay cikin gida rike da ita, a parlor ya zauna yana zazzage jakar babu komi ciki sai wayarta da lace dinta da sauri yadau wayarta yana duddubawa amma akashe take ba chaji, da kyar ya mike yay sama ya shiga dakin ya makala wayar achaji, tana dan yi 10% ya kunna da sauri, gallery ya shiga da saurin bala'i kaman mahaukaci nanko yaci karo da hoton ta guda biyu kacal wanda tai selfie daya tayi shine kwance kan gadonta daga ita sai yar rigan bacci kusan rabin kirjinta waje rungume hoton yayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mai sai kuma nabiyun tana sanye da doguwar rigar atampa afalo kan kujera tai hoton azaune, murmushin daya dade baiyiba yayi ahankali yakai bakinshi ya sumbaci hoton yace "i love yhu wifey" hanunshi ya tura cikin aljihu ya zaro sabon wayan da Abba yabashi sabida fashewar da tashi tayi, dailing number Cp yayi yana dagawa da kyar yace "an samu hoton ta kazo" yana fadin haka ya katse wayar yasake kwanciya anan kasan dakin ya rungume wayar sosai, kanshi dayaji ana shafawa yasa yadan bude ido kadan Mami daya gani ne akanshi yasa zai bude baki ta girgiza mai kai ahankali ta zauna ta daura kanshi akafafunta tana mai head massage.

Abba yadade yana magana da Malam a zaure kasancewar dalibai sunje bara saida yagama Malam ya nisa fuskarshi dauke da murmushi yace "da izinin Allah ankusa ganin ta" Abba kaman zaiyi kuka yace "zamu shiga cikine na fadima mahaifiyar ta?" girgiza kai Malam yayi yace "a'a banaso suji komi kasan mata da sa zance arai, yanzun nan saisu iya shiga damuwar dazai haifar musu da ciwo, bari in shiga gida namusu sallama zan bika na dubo Ayaan sanan akwai addu'a danake so namai sanan nayi agidan da aka dauketan, in sha Allah kwann nan zata dawo".

Ba'a jimaba malam yafito dauke da wata yar jakan malamai Abba ya mike suka shiga motar driver yajasu.
Cp na zuwa kasancewa yay bacci Mami ce tabashi hoton ya karba yace "za'a watsa hoton duniyar yanar gizo da gidan talabijin da sauran kafafun yada labarai hakan zai taimaka sosai.

Wuraren 9 nadare suka shigo gidan sabida go slow daya rikesu akano, bakaramin tausaya wa Ayaan dake bacci Baba yayiba.




*Bauchi*

Yau kusan satin ta biyu kenan agidan tun washe garin ranan datazo kanwar shi Ummy wacce yan makarantar su suke cema Ummy fingers tazo Buchin, yarinyar badai kyau da iya gayu ba, da kyar da kyar yasamu tana dan yarda da Ummy harma su kwana daki daya amma dudda haka saita ga dama take kula Ummy gashi Ummy na sonta bana wasaba.

Yauma kaman kullum karfe biyar na asuba ta farka sabida wani shegen ciwon ciki daya tada ta, da kuka ta tashi hakan yasa Ummy dake kusa da ita ta farka daga baccin datake dafata tayi da sauri ta ture mata hannu tana murguda mata baki dariya Ummy taso tayi amma saita gimtse inda sabo yanzu ai tasaba Ya Aaman ne kawai bata murguda ma baki amma kowa kam shan murgudan baki yake, tashin datayi ne yasa taga blood akan gado da sauri tace "ina zaki Ameerah" juyowa tayi tana share kwalla tace "Uncle" dirowa Ummy tayi daga gadon da sauri ta kulle kofar tace "haba my sweet sis muje kifara yin wanka zan baki maganin ciwon cikin zai dena mp kikeyi" da sauri tace "mp?" "eh mp amma karki fadama Uncle fa, muje kiga nahada miki ruwan wanka" saida tasake murguda mata baki sanan tai gaba suka shiga bayin tana hada mata ruwa tafito ta cire zanin gadon ta shimfida wani sanan ta fito mata da kayan dazata saka dakuma magani, fita kitchen tayi dan hado mata tea suka hadu da Ya Aaman yana shirin zuwa masallaci sanye da farar jallabiya kafin ma ta gaishe shi ya jefo mata tambaya. "kin tashe Ameerah tai salla?" "eh yayan mu natashe ta, good morning" juyawa yayi yay hanyar fita sanan ya amsa da "morning" ya sakai yafice.
Wuraren 8 ya shigo gidan dan yabiya gidan kajin su dubusu, yana shigowa tafito daga dakin nasu da gudu tana sanye da bakin riga abaya mai stones kanta har yanzu kitso biyu ne akanta sabida bandejin da aka sa har yanzu ba'a cireba, jiki asanyaye ta fito tazo ta xauna kusa dashi ba kaman kullum data saba zuwa dazaran yadawo daga masallaci da gudu ba, hakan yasa yadan kalleta yana kokarin ciro wayar shi daga aljihun jallabiya, kaman zatai kuka ta lankwasa kai ta kalleshi tace "good morning uncle" shima kallon fuskarta yayi nayan sakanni kafin ya dauke kai ahankali yace "baki da lafiya ne u look somehow" kaman jira take tafashe da kuka daidai nan Ummy tafito daga kitchen dauke da tray data daura cups din tea akai sakin baki tayi tana kallonta tace "kedai Ameerah kinada kukan banza" hararan ta tayi kaman idanunta zasu fadi kasa ta kalli Aaman da tunda tafara hararan ta yake kallon manyan idanuwanta yanda suke sama da kasa tace "Uncle Ummy is looking for my trouble" dan murmushi yayi yace "bakin riga kin harare taba to" wani irin ihu tayi ta mike tsaye tai dakinsu tana kuka dudda uban kiran da Ummy kemata ko juyowa batayi ba, hannu ya mika yadau coffee da Ummy tahada mai yakai baki saikuma yakasa sha sabida yanda kukan ta ke tabamai rai ya kalli Ummy daketa kallonshi tana murmushi yace "me kika mata take rigima yau?" "wlh Ya Aaman babu abinda na mata" shiru yayi kafin ya ijiye coffee yadau tea dinta da chips yay hanyar dakin nasu ahankali ya bude kofar ya shiga tana kwance ta kifa kanta a pilo tana kuka, ajiye tea da abinci yayi ya zauna a gefen gadon yay dan murmushi yace "Ameerah" make mai kafada tayi tace "oh'oh" tai maganan tana dan juyowa tana lekoshi, folding hanunshi yayi a kirji ya daure fuska yace "why are you crying" lankwashe kai tayi ta nunamai kofa tace "Ummy" ahankali yace "okay to sorry tashi kiyi breakfast" tashi tayi ta zauna tana goge kwalla ya juya zai fita da sauri ta riko hanunshi hararan ta yayi. "bana hanaki tabani ba" turomai baki tayi tace "sit down" ahankali ya zauna abakin gadon dan nesa da ita da sauri ta matso kusa dashi tana leka fuskar shi ta washe baki tace "Uncle daga yau i will be calling you sweetheart" da sauri ya kalleta sake washemai baki tayi tace "kaga ko Ummy na kiran saurayin ta sweetheart" yadade yana kallon fuskar ta kafin yace "to ni saurayin kine dazaki kirani da sweetheart" da sauri ta gyadamai kai tace "eh kai saurayi nane Sweetheart" tai maganan harda wuntsula kafa tana murna sanan tadau chips dinta ta daura akan cinya tasa fork ta debo takai bakinshi tace "haa sweetheart" dan hararan ta yayi kafin ya mike tsaye yafita daga dakin wani irin tsalle tayi tana rawa adakin. "yeeeee uncle is my sweetheart"
Afalo yasami Ummy harta gama chan tea wani irin kallo yamata ya daura kafa daya kan daya yadau coffee shi sanan yace "wato soyayya kike koyama Ameerah ko?" ware ido tayi tace "laaa haka tacema" saikuma tai murmushi ganin shan coffee shi yake hankali kwance, ahankali tace "Ya Aaman nidai wlh inason ka da yarinyar, she's very pretty and lovely, kaga dama Abba nata damunka kafito da mata why don't you go for her" yakai kusan 5min maganar na waka aranshi harta cire rai dazai amsata saikuma yace "I wouldn't risk dat, yarinyar datai loosing memory saina fara soyayya da ita, wat if tanada wanda takeso kafin abinan yasame ta, karma ki kara irin maganan nan" kaman daga sama yaji tace "amma ai kana sonta" da sauri ya kalleta ya nuna kanshi yace "nina cemiki ina sonta" yanayin yanda yake kallonta ne yasa taji wani irin tsoranshi ya shigeta bakinta har rawa yake tace "dama dama naga ka taimake ta ne, kuma yanzun nan datake kuka ka kasa cin abinci saida kaje ka lallaso ta and a whole lot of things danake ta noticing dis past few days" yadade yana kallonta yana karkada kafa idanunshi har sun dan soma chanza kala har yabude baki zaiyi magana Bilkisu tafito da gudun ta tazo ta zauna kusa dashi tana murmushi tace "sweetheart i want teddy" ko kallonta baiyi ba yace "stop calling me sweetheart" make mai kafada tayi tace "ni u are my sweetheart ko Anty Ummy" sumsum Ummy ta mike tabar falon kafin tasata abala'i, Bilkisu tabita da kallo sanan ta juyo ta kalleshi hada ido sukayi dan ita yake kallo yanason yagano me Ummy tagani harta ce yana sonta, washemai baki tayi tace "sweetheart teddy bear" kaman ba zaiyi magana ba saikuma yace "i want to sleep now anjima zamuje musiyo" tashi tayi tana murna tace "yeeeee" tai dakinsu da gudu da sauri ya runtse ido yana dafe kai ahankali yace "please please don't do dis to me, tayaya zanso wacce bansan ko waccece ba, tayaya zanso wacce ita karan kanta batasan kanta ba" ahankali ya ijiye cup din coffee a wurin yatashi ya shiga dakinshi.

Bayan kwana hudu.

Zaune yake acikin mota ya kafesu da ido yanda suke tsalle tsalle su uku ita da zainab da Ummy basu lura dashiba wasan yar gala gala suke yi, tana sanye da doguwar riga ta daura sweetar akai sai tsallake gida gidan take tana dariya daga gani wasan yakai mata, karan wayarshi dayaji shiya fargar dashi daga dogon tunanin dayake yi ganin Dr Ameenu ne yasa ya dauka daga tachan bangaren Dr Ameenu yace "kaga news?" shirun dayayi yasa Dr Ameenu yace "nama san kagani, wat is your plan yanzu kasan dai yakamata ka maidata garin su ko, ka kaita police headquarter da akace

Please Login or Register in order to submit comment