Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da sauri Ayaan yace "Pops are you okay, zan bata koma me take so am going to save u, Popsy be strong for me okay, Ina mamina, a ina ta har...harbe..k" yakasa karashe maganan sabida kuka jin yanda Abba ke wani irin nishi, kukan shi yasa wani jarumta yazoma Abba yay murmushi yace "is okay my Boy am fine, karka sake kabama makirar nan dukiyata, dakabata dukiyata gwara ka zuba musu petrol ka kona, karka sake ka bata Bilkisu stay with your wife, don't give her anything, dan koka bata kasheka zatayi, da abu yasaman min kai Boy gwara in mutu, idan wanan shine saduwar mu takarshe na yafema kome kamin aduniyar nan, ga Mamin kanan she's unconscious" sosai Ayaan ke kuka ya kankame wayar a kirji yanajin muryan Abba, CP kuma yadauko wani sabon laptop suna kokarin tracking, Bala ne yazo zai fizge wayar Big Mum ta hanashi tana murmushi tace "barsu suna bidding farewell ne shima yasan he's not leaving here alive" wani irin kallon ta Abba yake cike da tsana saikuma yakara wayan abakin shi da wani irin mugun sauri dakuma karfin bala'i yace "Boy muna wani uncompleted buildi...." tus tus Big Mum tamai harbi har biyu akafar daman shi amma dayace ta shige shi, Bala kuma ya zubamai wani irin naushi ahanci dayasa ya sume warwas.
Tashi tsaye Ayaan yayi kaman mahaukaci yana ihu a wayan "Pops Pops Pooooopsss" yawani irin ja sunan kaman wanda ya zare, maganar big Mum yaji ta wayan tace "nabaka 15 minutes take Bilkisu, documents, da yarana zuwa kasuwar kwari wurin yan kaji ka ijiye su anan kajuy.." Ayaan da zuciyar shi kaman tafashe ta fito yamata wani irin ihu a haukace da intonation dinshi daya koma nayan Austria yace "f*ck yhu mah nigga, I said f*ck yhu, f*ck yhu mah nigga, f*ck, f*ck you b*tch, I will kill you, I gonna kill yhu, u kill my pops I will gonna yhu wallah" dip big Mum ta kashe wayan jin yanda ya haukace mata kirjinta na wani irin bugawa, hannu yasa ya fizge bindigar dake cikin jakar bindiga dake jikin CP azuciye yajuya zai fita daga office din rikoshi CP da polisawan sukayi awani irin zuciye ya turesu dukan su suka zube kasa yafita amugun zuciye yana share hawayen dayake yi, su CP suka biyoshi kafin su fito harya bide wajen da kura.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

88...

Address din gidan ta dayagani adakin big mum yake son yaje gashi chan karshen garin kano ne address din gidan, hakan yasa yawani kara gudun hauka yana cikin gudun wayarshi ta shiga kara, dauka yayi batare daya kalli screen dinba muryan Musa yaji yace "hello abokina can u hear me" da kyar ya Iya yace "uh" cikeda murna Musa yace "yanzun nan daya daga cikin number Bala was on call hakan yabamu daman tracking down d location, I will forward d address to you now" ya katse wayar cikin one minute sako ya shigo gangarawa yayi yay parking hanunshi har rawa yake ya bude ya karannta sakon yafi sau uku ganin address din gidan big Mum daya gani dazu a file dinta ne, yasa ya kunna motar gabaki daya kure gudun motan yayi, cikin 35 minutes yakai wajen, daji daji ne duk ba'a wani gina filayen ba, hakan yasa yay parking yafito yarufe motar yabude booth, baida any weapon tsaki yayi yarufe booth din ya shiga dajin yana karanto addu'oin tsari, bawani dajin kirki bane, bishiyoyi ne kawai da ciyayi, yana gama wucesu yadan shiga ciki kadan saiga wani gida daduk shukoki sunbi jikin gidan, labewa yayi abayan bishiyan yana kallon gidan dan har yanzu gari dadan sauran haske, samari biyu ne awajen gidan suna zukan wiwi, tunani yafara me zaiyi yanzu, waige waigen yafara yana neman dan makami dan bayason ya harbe su, wani babban ishe ya hango akan yar bolan da aka tara awajen, takawa yay ahankali ya dauko iccen ya koma inda yake da, tsugunnawa yayi yadau dutse ya rike a hannu yana gyara zaman bindigar shi abayan wandon shi, yakara lekawa akaro nabiyu daya daga cikin sune yaga yataso yana bude belt din wando yana zuwa ta inda yake yana zage zip alamun fitsari zaiyi da sauri ya koma bayan bishiyar kusa da wacce yake daidai lokacin shikuma ya iso yaciro yana fitsari yana shafa ciki, fitowa Ayaan yayi daga bayan bishiyar ya daga itcen yawani irin makamai akai da karfin bala'i sai jini ko numfashin bai kara ba ya sume, zai fadi akasa da sauri Ayaan yatare shi gudun karya mai kara ya kwantar dashi a wurin ahankali kafin ya shige, har lokacin dayan na wurin yana zukar da dayan ya barshi, da rarrafe Ayaan yay wurin ya labe abayan motar big mum dake pake a wurin, dan lekawa yayi dakai yana gyara dutsen hanunshi yana wullawa sama yana chabewa, daddagewa yayi ya jefamai dutsen sai akan idonshi ba karamin bugamai ido yayiba saiga jini, da gudun bala'i Ayaan yafito yay kanshi kafin yabude baki ya sakin mai wani irin gula a jijiyan gefen wuyanshi ko numfashi bai karaba ya sume, kifeshi Ayaan yayi ya mikar dashi kaman mai bacci ya labe abangon wurin yana sauke ajiyar zuciyar, muryan Big Mum yaji daga ta Chan ciki tace "Bala jeka kirasu mana su gama shan wiwin su suzo suje su siyomana abinci Garba na najin yunwa" da sauri Ayaan ya tsugunna jin alamun tafiyar mutum yana kara gyara rikon iccen hanunshi, tsaki Bala dake fitowa yayi yace "amma isuhu anyi baho kagama zuka saikai bacci awurin" fitowa yayi danya tadashi kaman daga sama yaji saukan abu a kanshi dafe wajen yayi idanunshi na juyawa ya juyo suka hada ido da Ayaan kafin ma yay magana Ayaan ya daga iccen da duka karfin shi tunawa dashine ya sacemai Baby sai kan fuskar shi yasami bakin shi da hancin shi kafin ma yakai katsa hakoran shi guda uku sukai kasa ya fada kansu asume, wani irin gyara wuya Ayaan yayi harsaida yay Kas Kas, yawani irin dunkule hannu yawani irin bankare yana twisting jiki, kasusuwan shi Sai Kas Kas suke, jijiyoyin kanshi sun fiffito yay taking long breath kafin yasaki yay cikin ya shiga cikin gidan sadaf sadaf babu kowa afalon daya gani saida bathroom slippers din Mamin shi, yana cikin bin wurin da kallo Pilot din Abba yafito daga wani daki yana zage zip din wandon shi baima lura da Ayaan ba sai cikin shi dayake shafawa yace "Hajjaju ta yakama ta mukara kiran yaron nan mu karbi dukiyar mubar ka..." saukar abu yaji acikin shi yasa yay shiru, bugamai iccen yake ta ko ina azuciye, karan da Big Mum taji yasa tafito daga dakin dasu Abba suke aguje, ganin Ayaan yasa takoma cikin dakin da gudun bala'i tana kiran sunan su Bala ,"Bala Bala, isuhu Isuhu" wani irin jefar dashi Ayaan yayi yay dakin yana tafiya kaman zai fasa kasa tsabagen yanda foot dinshi ke kara ya shiga dakin daidai lokacin Big mum ta saita bindiga akan Mami da idonta biyu Ayaan data gani take kallo cike da mamaki, ahankali ya kalli Abba alamun numfashi daya hango ajijiyar wuyarshi yasa ya sauke ajiyar zuciya, ya sauke idanunshi akan kafafun shi dasuke jini duka biyun har yanzu hancin shima jini, dawo da kallon shi yay kan big Mum da itama shi take kallo, ta daure fuska tace "wlh one more step saina kashe uwarka, kadaiga na baban kako" wani irin kallo yake mata, idanun Mami daya gani ta zaro tana nunamai bayan shi yasa ya juya da sauri yana ciro bindigar bayan shi Bala ne yataho da sharbebiyar wuka zai cakamai harbi ya sakinmai akafada hakan yasa ya zube awurin yana ihu, juyowa yayi ya saiti big Mum da bindigar yawani irin daure fuska. "drop dat Gun Ayaan, drop it" ko gezau baiyi ba daidai lokacin kuma motocin police sukai invading surrounding din bakajin komi Sai kukan motocin su dudda basu iso gidan ba, sosai jikin big Mum yafara rawa jin kukan motar police ganin haka yasa Mami ta bangajeta da kujeran da aka daureta akai baya tayi zata fadi bindigar hanunta ya fadi akasa saita kafarta Ayaan yayi ya harbeta kafin ya Kara Kara mata wani a cinya ta fasa ihu ta zube akasa da sauri Ayaan ya shigo dakin yawani irin take hanunta danhar karan karairayewan kashinta kakeji yay kujeran da Pops yake ya warware kullin da akamai yana tapping fuskar shi Pops, kwance Mami yayi da sauri ta mike tsaye itama tazo wajen Abba, rigar jikinshi ya cire ya barka ya rabata biyu, daure inda ta harbeshin yayi gam gam sanan ya daura hanunshi ata wuyanshi Mami ma tama dayan hanunshi haka suka daga shi kaman kaman yamutu, a rude Ayaan yake cewa "Pops stay with me, Pops" sukai hanyar fita dashi daga dakin harsun kai bakin kofa kaman ance ya juya kai daidai lokacin Big Mum tai pulling trigger a saitin Abba dake tsakiyan su, wani irin tura Pops Ayaan yayi da mugun karfi hakan yasa Pops yafada kan Mami dabata san meke faruwa ba suka zube kasa bullet din sai cikin Ayaan, da sauri yawani irin dafe wurin yana kallon fuskar Big Mum yana kokarin magana amma yakasa, sake pulling trigger tayi ta harbeshi acikin akaro na biyu yawani irin bankare, zatamai na uku CP yay pulling Ayaan dake tsaye abakin kofan baya, Polisawa sukai rushing big Mum da bindiga.
Karan bindiga ya farkar da Pops daga suman dayayi rass ya bude ido yana kallon yanda Polisawa suka zagaye wani dake kwance akasa, tureshi da Mami tashiga yi dan gabaki daya kanta yafado da kyar ya matsa gefe ta tashi arude tace "Ayaan, Alhaji look our son" tashi tayi arude ta ture polisawan dasuka zagaye Ayaan da kanshi kekan cinyar CP, ko numfashi mai kyau bata kara fitarwa ba ta sume, jan duwaiwai Pops yayi yazo wajen yana kallon Ayaan da idanunshi ke lumshe, ahankali yabishi da kallo sai a lokacin yaga yanda cikin shi ke bulbul yana zubar da jini, CP ya daura hanunshi da jinin ya wankemai a wurin yana kallon fuskar Dr dake kan Ayaan, girgiza mai kai Dr yayi alamun bashi, wani irin karfi ne yazo ma Abba tashi yayi ya tsugunna ya karbe Ayaan daga jikin CP gabaki daya jikinshi ya saki, sakashi ajikin shi Pops yayi yana tsaki yana kallon fuskar Ayaan kaman mahaukaci ya kalli wani police yace "kai dalla bani ruwa suma dana yayi, Boy bazai mutu yabarni ba Yanzu bako Boy, bazaka mutu karbani ba" rigar da Ayaan yasa ya kullemai harbin da akamai akafa ya cire ya taushe inda big mum ta harbai yana ihu yana jijjiga Ayaan yace "kubani ruwa, kubani ruwa nace, dan Allah badan niba kubani ruwa" wani police ne ya mikomai ruwan gora, budewa yayi ya zubama Ayaan a fuska amma ko motsi, murmushi Pops yayi yace "Boy tashi mana banason wasan nan" sake zubamai ruwan yayi yasa hannu ya share ruwan daga fuskar shi yana tapping kumatun shi. "Boy, mah Boy wake up" bakinshi ya bude yana kokarin zubamai ruwan amma hakoran shi sun datse, wani irin nishi Pops yafara yana girgiza kai yace "Boyyy, Boy, Boyyy, Boy tashi kaji my one and only, Ayaan!" Pops yawani irin kirashi kaman mahaukaci, ahankali CP ya dafa mai kafada ya cire coat din jikinshi ya rufe fuskar Ayaan dashi, wani irin fizge rigar Pops yayi ya yar yay ihu yana kankame Ayaan yace "m..my Boy is not dead kadena rufemin shi, Boy Boy Boy wa..wake ke up.. Boy ka..tas..shi" fashewa yay da kuka jin jikin Ayaan yadau wani irin sanyi.
♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦



Maman Abd Shakur

89...

*Wanan shafin nakine kawata Fido Sodangi*❤

*Sangartattce group I love each and every single member ciki, I appreciate the love. Allah barmin ku*

*kekuma gwuididi dakike watsawa waje weldone woo beratu, hankaka mai kama da kikito Ayaan*

*inka karanta baka biyaba kaida Allah*

*ke wanan zankala kokin kaman TAMACEN JIMINA dakike turo min da sako lemme make this announcement loud and clear, DUK WACCE TABIYA 200, SHE PAID 200 TO GAIN ACCESS TO MY NOVEL, TO BE ABLE TO READ IT, BAWAI TASAYI NOVEL DINA BANE, IF I WANT TO SELL NOVEL BAZAN TABA SAIDAWA DAT AMOUNT BA*

Dawani irin ihu ta tashi daga nauyayyen baccin datake yi da magriba nan, cikinta dataji yana mata wani irin zafi ta shafa saikuma tafara waige waigen dakin da babu kowa sai ita saikuma kiraye kirayen sallan magrib dayacika unguwan, wani irin jumping tayi ta sauko daga gadon tai hanyar kofa batare databi takan hijabin taba, sauka tai kasa tana wani irin kuka tana kalle kalle babu kowama afalon, kofa tabude tafice da gudu tana kuka tai gate kasancewar masu gadi basu santa ba basu hanata fita ba da gudu tai waje tana kuka tana kalle kalle tana gudu, tai saman layi hanyar dazai sadata da titi zata fita daga anguwan daga ita sai doguwar rigan jikinta da black hula ko slippers babu akafarta sai uban kuka take, adaidai tabakin layin Aaman ya sanyo kan motar shi ciki kaman daga sama ya hango Bilkisu yanda take gudu tana kuka tana kalle kalle kana ganin ta kasan batasan inda kanta yakeba, parking yayi da sauri yafito yasha gabanta ganin ko lura dashima batayiba yace "Bilkisu ina zaki? Bakisan ko ina agarin nanba, mutafi gida" bangajeshi tayi tana kuka sosai zata gudu da sauri ya riko hanunta tawani irin fasa ihu tanaso ta fizge hanun tana neman cizon shi, janta yayi da karfi da yaji yasata amota yarufe yajuya ya shiga yaja motar yana kaiwa gate Mum da Ummy harda mai gadinsu suma sun fito hankalin su duk atashe, awajen yay parking yafito, mum takara so wajen da sauri tana kallon yanda take kuka, Bude kofar inda take tayi ta duko ta shafa fuskarta tace "maisa kike kuka haka daughter harkika fita, kodan bakiga kowa bane, salla mukeyi saisa zomuje gida" hanunta Mum takamo tafito da ita, daura hanunta daya tayi akan cikinta sosai take wani irin kuka sukai cikin gida da ita, da kyar Mum tasata tayo wanka Ummy tafito mata dawani simple riga tasaka duk sun damu, abinci ma Mum da kanta tabata sanan suka sata tai salla kafin abata maganin dare tana sha ba dadewa bacci yay gaba da ita sai uban ajiyar zuciya take saukewa, Mum ta kalli Ummy dake zaune gefenta tace "ki zauna da ita karta kara tashi taga bakowa" gyada mata kai Ummy tayi hakan yasa ta juya tafita daga dakin abakin kofar dakin taga Aaman ya tsaya ya jingina da bango yay shiru kaman mai tunani murmushi tamai tace "don't worry tai bacci, oya muje kaban labari how did d blood test go" dakinta ta shiga yabi bayanta, bowl din slice fruits dayagani akan bed din Mum ya dauka ya rike fork yadebo yakai baki saida ya shanye sanan ya kalli Mum yadan yatsine fuska yace "Mum I can't marry her, am even waiting for Dad yadawo sabida yakira parents dinta, we both are AS, AS, gaskiya I can't marry her is way too risky, banison na haifo yara sickla suzo duniya suyita wahala kullum muna hanyar hospital, thank God sef bawani sabawa mukayi da itaba, itama she's very cool with our decision mun janye zanxen auren dama tanada wanda takeso" gyada kai Mum tayi saikuma tace "kaifa?" dan lumshe ido yayi yadaura kanshi akan kafadarta, hanun tasa ta shafa sajen shi, ahankali yace "Allah zai bani wata mesona tagari Mum in sha Allah, aure lokaci ne dazaran lokacin yayi ko bacci nake saikun mini" kumatun shi Mum taja hakan yasa yay dan kara zaiyi magana sukaji wani irin ihun Bilkisu har cikin jinin jikinshi saida yaji ihun nan kafin ma Mum ta tashi shiya rigata yafita daga dakin ya bude dakin Ummi ya shiga, tana zaune kan gado sai uban kuka take rusawa hanunta akan cikinta, Ummy namata magana amma ko kallon ta batayi, ahankali yakaraso ta wajen gadon ya tsaya Mum na biye dashi hanunshi zube acikin ajihu ya kafeta da ido, dago kai tayi cikin kuka tana ganin shi takara fashewa dawani kukan tana nunashi da yatsa cikin kuka tace "ina...in..y...ina yake?" takara she magana tana kuka sosai, sassauta murya yayi ya girgiza mata kai yace "okay stop crying in kinaso nakira miki shi, zakiyi magana dashi?" da sauri ta dagamai kai tana goge kwalla tana lumlumshe ido tsabagen baccin dake fizgarta ta jinginar dakai jikin gado tana kallonshi, wayar shi yaciro daga aljihu dan shima yadamu da yanda take kukan nan, number Ayaan yaciro yay dailing harya gama ringing ba'a dagaba, sake dailing yayi har yagama ringing nanma ba'a dagaba, Mum ta kalleshi alamun andauka girgiza mata kai yayi yakara dailing akaro na uku nanma ba amsa, dan kallon fuskarta yayi ganin tai bacci yasa yadan sauke ajiyar zuciya yakalli Mum da shi take kallo, ahankali yace "Mum am feeling somehow I hope he's fine, bari naje namai addu'a Allah ya kubutar da iyayen shi" Ameen Mum tace, fita yay daga dakin Mum kuma ta zauna abakin gadon tana tofa mata addu'a tana kallon yanda ta sanya hanunta daya akan cikinta ta danne tana yatsine fuska cikin bacci.



*************************

Sosai Pops ke kuka, dago kanshi yayi asandaren ya daura akafadar shi ya kankameshi sosai yafashe dawani irin kuka mai tabarai, cikin kuka yace "tun inada shekaru ashirin aduniyar nan nai aure amma ban sami haihuwa ba, babu wani irin asibiti daban leka aduniyar nan ba, da wanda zanje nikadai da wanda zanje nida matayena amma duk maganun da likitoci zasu fadamin daya ce bana haihuwa" Bude idanunshi dake zubar da hawaye yayi ya kalli sama, cike da mugun rauni dawani irin muryan ban tausayi yace "har na cire rai na fidda tsammani, na hakura nacigaba da rayuwa kaman kowa, inada shekaru arba'in da biyar a duniyar nan Allah kamin kyautan wanan Yaron, kanuna min ba kudina zaibani haihuwa ba, kaine keda wanan ikon kuma aduk lokacin dakaga dama, ka sharemin hawaye na, kanuna mini duk wanda ya mika lamarin shi gareka tabbas ka isar masa, kamini kyautar Ayaan, kabani Ayaan" hawayen dasuka zubomai ya share tareda dago Ayaan daga kafadar shi ya kwantar dashi akan cinyar shi, yahade hannayen shi biyu yayi alamun roko yana kallon sama yace "Ya Allah, bazan tabaja da ikon kaba kai ubangiji nane duk hukuncin daka yanke min daidai ne agareni, duk duniyar nan kaikadai zan gayama bukatuna kabiya min su, Ya Allah ina mai tawasilli da sunayen ka kyawawa, Ya Allah kaine Al ahadus samadu lazi lamyalid walamyulad walam yakullahu kufwan ahad, Ya Allah kaine Al Hayyu Al Qayyum, Ya Allah kaine AL mutasarifu maijujjuya al'amura, Ya Allah na, badanni ba badan halinaba Ya Allah ina mai tawasilli da dukannin ayuyyukan alhairi danai aduniyar nan sabida kai Ya Allah, Ya Allah karkasa Ayaan yamutu yanzu, Ya Allah karka rabani da kyautar nan dakamin yanzu, Ya Allah ka tashi kafadar shi, Ya Allah, Ya Allah, Ya Ubangiji na..." Sai kuka kuma ya sake daga Ayaan daga cinyar shi ya sanya shi a jikinshi, jikinshi yay sanyi sosai ya rungume shi tsam tsam yana wani irin kuka mai sosai rai, polisawan ma sunkasa cewa komai dan suma jikinsu yay sanyi sosai idanunsu tab da kwalla, ahankali Abba yaji saukar numfashin Ayaan a wuyanshi dan kadan kuma a mugun hankali, wani irin ihu Abba yayi yaciro shi daga jikinshi yace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah na godema, Allah banda abin godiya saikai, Ya Allah thank you Ya Allah, my boy is alive, yarona is alive, mutafi asibiti" da sauri likitan dake cikin polisawan ya dubashi ya kalli CP dake kallon su yace "yes he's alive muje asibiti baya numfashi da kyau" karban shi akai daga hanun Abba, polisawan na murna suna "ashe doguwar suma ce" aka fita dashi shima Abba da bakin shi yakasa shiru sai "Alhamdulillah, Alhamdulillah yake" aka kinkime shi akai waje dashi, Mami ma haka, sanan kuma Big Mum mayya mai taurin rai harbi biyu gareta a hannu, biyu akafa, daya a kafadar haggun, dagata wasu polisawan sukayi suka sakata a motar su itada su Bala da Ayaan ya raunatar sukai asibitin polisawa da ita.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

90 - 91

*Momma!! You're Special!! I love the you in you!! I admire your courage!! Remember Allah is with you, u are not alone in dis journey, so let's keep fighting and pushing, you u will definitely reach dat spot dat I picture you to be. All it takes is patient u will overcome this phase of life my Momma*.





Bayan 2 weeks.

Babban dakine acikin asibitin, yana kwance akan gado sanye da white singlet da aka nannade sama kadan sabida bandejin dake cikin shi daidai inda aka ciro bullet din, saikuma dogon wandon jeans, Abba ne zaune kusa dashi da sandar dayake dogarawa yay tafiya dan tunda aka ciremai bullet din baya iya tafiya saida taimakon Sanda, saikuma Malam wanda yazo duba Ayaan yauda safe shida Raiyana dan kuka tadinga yi zata bishi ta dubo Bilkisu zuwan suma saisuka tarar da sabon labari, saikuma Baba Suleman dake zaune akan doguwar kujeran dakin, gabaki dayan su barin ma Abba yafi ramewa sosai sabida rashin lafiyan Ayaan, bugawa zuciyan shi yayi abinda ma yahana shi tashi har yanzu kenan dan sosai zuciyar shi tabugu sabida tashin hankalin daya shiga, inda akamai aiki kuwa harya soma warkewa wanda yauko gobe ma za'a cire bandejin gabaki daya.

Hankalin Abba sosai yake atashe dan basuga Bilkisu ba kuma duk wani gidajen su saida yasa aka duba koya boyeta awurinne amma babu ita, saisa addu'a kawai sukeyi Allah ya tashi kafadar shi yafada musu inda Bilkisu take.

Big Mum kuwa bayan ancire mata bullets din datasha, hanunta da Ayaan yataka yamata wasu irin karairaya ne da aka kasa gyarawa saidai aka guntule hanun gabaki daya, bayan kwana biyu aka shigar da case din kotu bayan all d evidence da lawyer dake kare Abba ya gabatar a kotu nan Alkali yay sentencing life in prison na yunkurin kinsan kai, kidnapping dakuma sauran crime dinta, taci kuka kaman idanunta su fito da guntulallen hanunta, lawyer Abba ya mikamata takardan sakin da Abba yabashi ya bata saki uku takara rushewa dawani kukan, suma su Bala duk prison din aka kaisu sai tsine ma Big Mum suke Wai ita tasasu awanan wahalan shiko pilot kuka wiwi, yanada aikin shi gashi alhaji na kyautata mai yabiye ma big mum gashinan abinda tajamai, kuka kam ya Shahi haka aka tattara su akai gidan yari dasu.

***********************



A Abuja kuwa Bilkisu ta tasasu agaba kuka badare ba rana d only maganan da take yi shine ina yake ina yake, Aaman kaman zai haukace yanda kukan ta ke tadamai da hankali tun yana kiran number Ayaan ya shiga har yazo yadena shiga gabaki daya, hankalin shi dukya tashi maiya sami Ayaan? So yake yaje Abujan amma yakasa dan inhar bashi yazo ya lallabata yace mata gashinan zuwa yana hanya ba batacin abinci, yaudai ya yanke shawara zai tafi Kanon yaje yadubo meke faruwa sati biyu bawasa ba gashi wani irin mugun zazzabi ta tashi dashi yau, da kyar Mum ta lallabota tai wanka tafito tana rawan sanyi, kaya tabata tasaka, tabata tea mai zafi tana karban tea ta ijiye tana girgiza kai tana yatsine fuska, ahankali Mum ta rungumota jikinta tace "yakuri kisha kinji daughter yauwa yar albarka sha nabaki magani" Mum tai maganan tana kai tea din bakinta yatsine fuska tayi ta kurbi kadan, ture tea tayi da sauri tana kokarin yin amai da sauri Mum ta ijiye tea tanason ta dagata amma harta kwaro aman anan kan gado. "subhannallah sannu yar nan" dagata Mum tayi da taimakon ta tai bayi da ita ta wanke mata fuska da wuyan data bata sai uban kuka take, jikinta yay mugun zafi hanunta Mum tarike tafito ta ita tai dakinta da ita kasancewar tariga tabata gadon, abakin kofar dakin sukaci karo da Aaman duk yay wani irin yana kallon fuskar Bilkisu dake kuka awahale, kallo daya Mum tamai ta shige da ita dakinta kwantar da ita tayi akan gadonta ta lulllubeta ganin sanyi takeji ta kashe AC tadawo kusa da ita tana share mata hawaye tana bubbuga bayan ta tana girgiza mata kai tace "stop crying yar albarka sleep" haka tadinga mata har wani wahalallen bacci

Please Login or Register in order to submit comment