Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kibarta tai baccin ta tunda fita zamuyi" hijabi Baaba ta dauka suka fita da Mami tare suna hira a down stairs suka hadu da Abba da big Mum da itama ta shirya duk suka shiga mota Alhaji yajasu suka fita daga gidan. Gidan yarage daga ita sai yan aiki.

Wani ubansu gida Abba yakai Baaba, sakin baki kawai tayi tana kallo dan gani tayi gidan ma yafi gidan su Abban kyau, horn Abba yayi gateman yazo yabude suka shiga, babban compound ne da aka bi bangon da flowers, sai runfan parking motoci sukai parking suka fito, bayan gidan suka fara zuwa wani ubansu garden ne daga gefe daya kuma wani hadadden swimming pool ne, ta kofar kitchen dake garden din sukabi suka shiga kitchen Baaba dai kasa rufe baki tayi yanzu Bilkisu tane zata zauna awanan gida irin gidan shugaban kasa lallai Bilkisu akwai goshi, fita daga kitchen din sukayi sukai parlor komi white and sky blue harda kujeru, center carpet da labulayen, ga gefe kuma wani babban fish bowl ne kifaye sai wasa suke aciki yanda Baaba ta dinga yi yasa suka dinga mata dariya sukai upstairs inda wani parlor ne awurin sai dakuna uku na farkon suka shiga komi off white ne, sai kuma dayan dakin da akai brown and milk dayan kuma akai brown zalla, kafin su kara komawa wanda akai brown and milk akwatunan ciki guda 24 Mami da Big Mummy sukahau bude mata shikuma Abba yakoma kasa danyi waya, sai kallon akwatinan Bilkisu take tana mamaki, Mami tace "dazaran yadawo daga Abujan zasu tare in sha Allah" nan fa Baaba ta bingile da ciro kaya tana dubawa tasami na bada labari a zaria.

Ahankali tayaye bargon data lullube dashi dan takasa baccin, suna fita taji gidan yamata wani iri duk ba dadi, mikewa tai tsaye tana sanye da soft jersey drape skirt black sai pink crop top daya dan saukan mata kasa amma bai rufe cibi ba sabida ma ance tadinga barin wurin dinkin nashan iska ne yasa Mami ta siyo mata irin kayan yakin, skirt din yabi jikinta sosai ya fito da shape dinta dudda bai wani kamata ba, rigar kuma tamata chachas ajiki tareda kara bayyana kyan surarta, dan black hulane akanta wanda yadan zame baya gashinta da aka tsefe aka gyara mata ya bayyana duk ya kwanta yana shining, wayarta tadauka tasaka bathroom slippers white daya bayyana fararen dogayen yatsun kafarta tafito tana tafiya ahankali harta sauko down stairs babu kowa afalon gashi bata iya kunna makeken tv bangon suba, dan tsaki tayi tai hanyar fita daga dakin tafito tsakar gida sai kalle kalle take ganin babu kowa sai uban motocin dasuke apake, ahankali take tafiya tana dan yatsine fuska dan rabon ta da tsakar gidan tun randa aka sallamota daga asibiti, ahankali take ta tafiya tana zagaye gidan harta ganta a garden, bin wurin tai da kallo yanda flower din wurin sukai kore yirr ga watering can akasa, cigaba da tafiya tayi tana shafa flowers din tana murmushin dake lobar mata da dimple, karan katca dataji yasa tadan daga kai ta kalli saitin inda taji karan wani worker gidan ne dake sanye da uniform yana bama wani dan biri haka dake sanye da kaya ajikinshi jeans da riga ayaba, an daure burin ajikin bishiyan mango da chain, ware ido tayi cike da mamaki harda dan saurin ta takara so wajen ta kalli mutumin dayake ta kallonta sanan ta kalli birin dake kallonta shima yanacin banana, ta nunashi da hannu tace "laaa monkey dama da monkey agidan nan, monkey wayene?" murmushi mutumin yayi yana barema birin wani ayaban yace "na oga ne wlh, bakiga yanda yakeson monkey nanba, shima monkey haka yake sonshi kome yace yayi saiyayi" murmushi tayi batare data matso ba dan tsoron biri take tunda aka taba labari a school wai biri nason mata yanxu ma dan taga akulle yake da kacah ne saisa tazo tana kallonshi, ganin yanda aka samai kaya masu kyau harda sarka awuya sai abin yabata dariya ma, mai aikin yacigaba da kallonta yana bama birin ayaba yace "amma ke ba yar gidan nan bace ko, bakuwa ce dan bantaba ganin kiba wlh" gyadamai kai tayi batare data janye idonta daga kan birin daketa dambe da ayaba ba, shikuma mai aikin sai binta yake da kallo daga sama zuwa kasa yana wanan kyakkyawan fa haka aranshi. "kai!" atsorace daga shi har ita suka juyo sakamakon wani irin tsawa daya dakama mai aikin, yana sanye da white singlet daya kama jikinshi sai neon Beach floral 3 quarter, fuskar nan babu alamun wasa, da hannu yamai alamu yazo, da sauri jikinshi har rawa yake ya karaso gabanshi kanshi akasa yace "good morning si..." wani wawan mari Ayaan ya dauke shi dashi azuciye kafin yanunamai hanyar barin garden din yace "u are fired, out" ganin babu alamun rahama afuskar shi yasa guy din yabar garden din da sauri, arude sumi sumi jikinta har rawa yake tazo zata wuce ta gefenshi ya damko hanunta ya maida shi tabaya ya lankwasa ihu tayi "wash Allah na wai mena maka ne nikuma?" juyo da ita yay takusa fadawa jikinshi da idanunshi dasukai jajir yace "are you trying to seduce my workers" kallonshi tayi da idanunta dasuka cicciko da kwalla tama kasa magana ya daka mata tsawa. "am talking to you" hannu tasa ta taushe kunenta sabida yanda dodon kunenta ya amsa tafashe da kuka sosai fizgan hanunta yy takusa faduwa yajata har side dinshi wanda shine ke tare da garden din kofar ya bude ya jata ciki wani kamshi da sanyi sukai mata sallama wurgar da ita yay akasa tafashe da kuka ya maida kofar ya rufe, arude ta mike tsaye tana waige waige, ganin ya dumfarota da idanunshi da suka chanxa kaman banashi ba yasa ta shige bedroom da gudu kafin ya iso ta kulle kofar, key data gani ajiki tasaka ta kulle tacire key tana komawa da baya tana kuka sosai, buga kofar yayi azuciye yace "ke kibude kofar nan tunda ba gidan ubanki bane, kibude nace" komawa baya tadinga yi harta jingina da jikin wardrobe ta sulale kasa ta kama kafafuwan ta tana kuka tana kuma addu'a Allah dawo dasu Mami.

Key dataji yasaka a kofar yana murdawa yasa ta mike tsaye da sauri kirjinta na bugawa bude kofar yayi yawani bugo da gudu ta kwasa zatai bayi taku daya yay ya damkota yajawota jikinshi tana kokarin fizgewa amma saida ya hadata da kirjinshi ya matse, yanda take nishi kaman zata mutu ne yasa yace "ke" abakin gado ya zauna har lokacin kanta na kirjinshi tana kuka, cirota yay daga jikinshi yana wani irin hararan ta, kin kallonshi tayi saima bayan hannu datasa tana share kwallan daya zubo mata, yanuna ta da yatsa da kakkausar murya yace "wlh duk randa kika kara fitowa tsakar gida ahaka saina zaneki da belt mara hankali kawai" murya chan ciki tace "niba mara hankali bace saidai kai" bakinta dayaga yay motsi yasa ya kama hanunta atsorace ta kallai yace "me kikace?" dauke kai tayi ta turo baki tareda zame hulanta daga kai tana goge hawayen daya bata fuskarta tace "ni bance komiba" dogon jelar gashin ta yabi da kallo kafin ya maida kallonshi kan fuskar ta ganin kokarin fizge hanunta take batare data kallai ba, murya chan kasa yace "hau gado na duba ciwon ki" ko kallonshi batayi ba tace "ai ya warke baya zafi" dan murmushi yayi ya kalli cikin inda akai aikin kafin yamike tsaye daukar ta yay hakan yasa ta fasa uban ihu kaman zata tsaga gidan, buge bakinta yay da sauri tai shiru ya kwantar da ita akan lumtsetsen gadonshi shi da sauri tai yunkura zata tashi ya dakamata tsawa. "ki natsu" ba karamin tsoron yanayin fuskarshi tajiba hakan yasa ta kulle idonta kam kirjinta na bugawa, fuskar yadan kalla kafin ahankali yakai hanunshi gun ciwon yadan taba kadan sanan yacire hannu, flat cikin nata yabi ya kallo kafin ya sauke idanunshi akan kirjinta dake cikin rigar ya kafesu da ido, jin baya taba cikin yasa tabude ido ahankali karaf suka hada ido da sauri ta janye nata ganin yanda ya cika mata ido ta tashi zaune ta sauka daga kan gadon duk yana kallonta, hanyar kofa tai da sauri zata bude tafita, da kakkausar murya yace "ubanwa yabaki izinin fita" da sauri ta juyo idanunta sun cicciko da kwalla, mai matsalar mutumin nan da itane wai, da yatsa ya nunamata gadon yace "dawo inda kike" ahankali tafara tafiya tadawo kan gadon ta zauna nesa dashi tana goge kwalla, mikewa tsaye yayi yaje gaban fridge din dakin ya bude yaciro farm fresh yogurt ya cika glasscup sanan ya mayar cikin fridge yadau laptop dinshi dake kan kujeran dakin yadawo bakin gadon ya kalleta yanda taketa share kwalla, wani irin mugun kallo yamata yace "matsa ciki ke" a tsorace ta matsa cikin gadon ta jingina da bangon gadon azaune tana share kwalla kirjinta sai bugawa yake, ajiye glasscup da yogurt din ke ciki yayi akan bedside drawer ya kwanciyar zama yasa pilo akan kafarshi yadaura laptop akai tareda gyara zaman kanshi a filo biyu daya hada yana daddana laptop din batare daya kalleta ba yadauko yogurt din yana sipping kadan kadan yana danna laptop da hannu daya, sosai take share kwalla duk hankalin ta yatashi takara makewa ajikin gadon gashi sanyi takeji sabida yanda ya kara Ac sosai. Yakai kusan 10mins yana abinda yakeyi kafin yajuyo dakai ya kalleta har lokacin share hawaye take da bayan hannu ya daure fuska yace "ke" kaman bata jishiba haka tai hakan yasa ya dakamata tsawa. "ke" arude ta kallai, glasscup din yogurt din da har yanzu ko rabi bai shaba ya mika mata alamun tazo ta karba girgiza mai kai tayi wasu hawayen na zubowa, yanda ya kafeta da ido babu alamun wasa yasa taji gabanta yafadi ahankali ta rarrafo zuwa inda yake ta karba tana kuka mara sauti zata koma inda take yace "ke anan zakisha" gyada mai kai tayi duk ta rude dan bata saba ganin namiji a singlet ba, kaiwa bakinta tayi tafara sha duk yana kallonta da gangan yakara daka mata tsawa ganin zata shanye. "ke nace ki shanye duka ne" da sauri tacire cup din daga baki tana girgiza mai kai ta mikamai cup din, karba yayi yana kallon yanda yogurt din yama sama lebenta layi kaman gashin baki, zata koma inda take ya harareta yace "karki sake ki tashi" zama tayi dukta rasa inda zatasa kanta sai goge kwalla take da bayan hannu, glass cup din yakai bakinshi shima yanashan Yougurt din data rage yana kallon fuskar ta ya tura hanunshi a aljihu yaciro handky ya mikamata yace "clean ur mouth" karba tayi ta share bakinta batare data share inda Yougurt din yabata ba ta mikamai handky din tana kokarin boye hawayen dake shirin zubo mata, karba yayi tareda ijiye cup din akan bedside drawer ya kalleta da lazy eyes dinshi murya chan ciki yace "baifita ba zo na share miki" yay maganar yana daura hanunshi abayan ta, arude ta kallai tareda sakin kukan dayake cinta, hannayen shi biyu ya daura a bayanta ya jawota zuuuiiii tazo jikinshi janye hanunshi yay daga bayanta lazy eyes dinshi akan lips dinta inda Yougurt yabata, hada goshin shi yay da nata da sauri tasake kallonshi suka hada ido azabure tafara kokarin mikewa amma baibata damar ba, hannunshi daya yakai ta bayanta ya janyota ya hadata da jikinshi da kyau shikuma yay relaxing bayan shi ajikin bangon gado, yasa dayar hannun yakamo habarta yana kallon yanda ta runtse ido gam tana kuka jinkinta har barbar yake, matso da kanshi yay sosai saitin fuskar ta dan sunajin numafashin junan su kafin ya fito da harshen shi ahankali ya daura akan saman upper lips dinta yafara lashe yogurt din.

*inhar kasan baka biyaba ka karanta ban yafeba, dan novel din kudine*

In kanason littafin nan chat me up tanan 07012181461
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦


Maman Abd Shakur

43...

Kokarin juyar dakai tafara jin wani irin zirr zirr da jikinta keyi har kunnuwanta, yasaka hannayen shi biyu yay cupping fuskarta kafin yakara fito da harshen yafara lasan yogurt din ahankali ahankali kaman yana tickling dinta har yagama lashewa yakara resting fuskarshi akan nata yana kallon idonta yanda ta runtse su ta kankame su gamgam hawaye na bubbuluwa ta gefe, kirjinta na mugun bugawa, dogon hancinshi ya daura akan nata dogon hancin yadan jujjuyar da kanshi hakan yasa hancin suka bugi juna, tsayawa yay batare daya raba fuskokin suba ya kafe lips dinta da ido, ahankali ya gangaro da bakinshi ya daura akan lips dinta da sauri ta mayad dasu ciki ta daure bakinta gamgam tana nishi kaman mai asma, murmushi yay ya saukar da hannunshi daya yakai gefen cikinta dakeda lpy yamata chakulkule da sauri tasaki bakin zatai ihu ya kamasu, wani irin kiss ya shiga mata tana mutsu mutsu iya karfin ta ta kwace bakinta amma takasa kara janta jikinshi yay sosai ya saka hannun ya tunbuke ribon din data kama gashin kanta dashi ya hargitsa mata gashin gabaki daya, sosai take kuka kaman zata mutu saidai ba kara sabida bakinta daya kama, mirginowa yay yana kokarin juyawa dauke da ita ajikinshi sukaji karan laptop bam yafadi akasa, karan yasa ta daddage ta fige bakinta dayake neman katsawa da kyar tana mugun kuka shikuma ya juya da kyar ya kalli laptop dinshi dake kan jikinshi daya fadi warwas akasa, dan sakinta yay batare daya cireta daga jikinshi ba ya mika hannu daya kasa yana kokarin daukan laptop din yaduba dan akwai a whole lot of patient records aciki, fizge jikinta tai wup da gudu tafita daga dakin tana haki ganin hularta ga gashin ta duk abarbaje tai waje ahaka yasa ya mike tsaye da kyar yabita, tsaye yaganta tana falo tana faman murda handle tana kokarin bude kofar yaki buduwa yana gab da isota tasamu tabude tafice kafin tafita daga balcony din ya cimmata ihu tabude baki zatayi ya daura hannunshi akan bakinta yana hararan ta tareda jawota jikinshi, tafashe da kuka duk jikinta na rawa ya kafeta da ido, daidai lokacin Mami da tundazu suka dawo sai nemanta suke basu ganta ba ta tambayi yan aiki sunce basu ganta ba hakan yasa hankalin ta yatashi tafara zagaye gidan, kaman ance ta daga kai ta hangosu tsaye Ayaan na kokarin sakamata hula, da sauri ta juya Ayaan daya dago kai ya ganta yace "gud afternoon Mami na" arude tafara kokarin fita daga jikinshi jin yana gaida Mami, sakinta yay ta fizge hularta kanta akasa sabida kunya, dan juyowa Mami tai ta kallesu sau daya kafin tacigaba da tafiya abinta tace "saukar yaushe, daughter kizo kiyi sallama da Baaba" ta wuce abinta da sauri tabi bayan Mami tana saka hular duk arude, bin yanda take tafiya yay da kallo kafin yay dan murmushin gefen baki ahankali yace "she has special lips, soft skin, soft hand" dan tabe baki yayi kafin ya koma ciki ya dauko black shirt yakasa yafito yay garden dan dubo monkey shi.

Saida ta tsaya ta gyra hularta tamaida gashin ta da kyau ciki kafin ta shiga bangaren kanta akasa sabida wani irin kunya datake ji, babu kowa afalo hakan yasa tai stairs tafara hawa daidai lokacin big Mummy itama tafito daga dakin Baaba rike da bowl din fruits da fork tanaci "sannu da zuwa Mummy" wani irin faduwa gabanta yayi harsaida bowl din fruits din hanunta ya bare da sauri Bilkisu ta tsugunna tana kokarin tattare fruits din tace "subhanallah" bayanta big Mummy tabi da kallo ta rasa mesa duk idan taji muryar Bilkisu kokuma ta kalli fuskarta sai gabanta yafadi, dan murmushi tayi ta dagota tace "ki barshi keda bakida lpy, wuce kitafi wurin Baabar ki gatachan ta shirya" badan tasoba tatafi.
[7/20, 11:39 AM] +234 803 238 4602: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

44 - 45

Ahankali ta turo kofar, Baaba ce kadai tanata faman daddanna touching screen wayar da Abba yasai mata tana ganinta ta ijiye tace "zonan tawaje na" harda dan gudun ta tafada kan Baaba sai kuka, cikin kuka tace "Baaba dan Allah karki tafi ki barni, dan Allah mukoma gida tare banason mutumin nan" girgiza mata kai Baaba tayi fuskarta ba alamun wasa tace "da auren akan ki, ai auren kenan, kifara zama dashi kafin ki tantance ko bakison shi yaron me halaye na gari haka, hakanan zaki daure kindaiga iyayen mijinki yanda suke sonki saiki bisu sau da kafa, kima mijinki biyayya inya kiraki kije karna karajin kince bakison shi" nan ta shiga yimata wa'azi mai shiga da ratsa jiki. Mami ce tashigo dakin da sallama tana murmushi ganin yanda Bilkisu ke kuka ta kankame Baaba tace "wanan kuka haka daughter kiyakuri kinji bagamu nanba" tashi Baaba tayi tana tureta tace "kinga sakeni nafara latti banison nai dare fa ahanya" tafita da sauri dan batason tai kukan da takeji, tashi tayi Mami tarike mata hannu tafashe da wani kuka sosai, hannu Mami tasa ta share mata hawayen tana murmushi tace "daughter nafa jaruma ce, dena kukan zomuje mumata rakiya" hijabi ta dauka tasaka suka fita sai uban kuka take mara sauti har waje, tsaye yake kusada Baaba sai magana suke wanda bata iyaji amma fuskarshi dauke da lallausar murmushi, budema Baaba kofar bayan mota yayi da gudu taje ta kankame Baaba tana wani irin kuka cirota Baaba tayi daga jikinta tana lallashi tanuna Ayyan dayay kaman bai gantaba tace "baga mijinki nanba kikema mutane kuka, ke dalla rabu dani karna makeki" Mami da Big Mum duk suka mata fatan alheri ancika boot da kayan atsaraba takaima yan zaria, ta kalli Bilkisu data kasa daina kuka ta shafa kumatun ta tace "Allah bada zaman lpy ki rike abinda nafada miki kinji" ta shiga motar da sauri tana boye kwallan daya zubo mata Ayaan yarufe motar yanama driver alama yatafi, tanaji tana gani Baaba ta tafi abinta tabarta. Batare daya sake kallonta ba yay wucewar shi wurin big Mum yace "big Mum yunwa nakeji" murmushi tai cike dajin dadi tace "muje nabaka abinci my boy" sukai wucewar su sukabar Mami daketa lallashin ta saida tai shiru sanan suka wuce part dinta.
Apalor suka zauna kanta akasa Mami ta kunna kallo tasa mata zee world tana janta da hira sai asanan tadan saki jikinta ganin haka yasa Mami tai sama dan akwai kiran datake so tayi.
Kallonta take dudda rabin tunanin ta na gida, dan bawani gane kan film din takeba, yadade tsaye abakin kofa kafin ya shigo dakin fuskarshi adaure yana tafiya cike da izza, kamshin dataji yasa ta daga kai da sauri tana ganinshi ta mike tsaye da sauri zatai stairs da hannu ya nunamata kujeran data tashi gabanta na faduwa takoma ta zauna, Apple yadauka dake kan hadadden bowl asaman dining table sanan yadawo cikin falon shima akan kujeran ya zauna yadau remote din da Mami ta ijiye mata akusa da ita ya chanza channel zuwa na wrestling kafin ya kwanto ya daura kanshi kan cinyarta yana gutsuran apple din dake hanunshi yanaci, dudda yanajin yanda jikinta ke rawa hakan bai hanashi gyara kwanciya da kyau ba yanacin apple dinshi batare daya kalli fuskarta ba, stairs ta kalla dan ko kadan bataso Mami tazo ta gansu ahaka sanan ta kalli fuskarshi ta fashe da kuka tana share kwalla ko kallonta baiyiba, ahankali Mami ke saukowa daga stairs bayan tagama wayar datake yi da Ummu Haneef tsayawa tai chak hango Ayaan yanda ya daura kanshi akan cinyar Balkisu yana kallo abinshi girgiza kai tayi tajuya da sauri rashin kunyan Ayaan ya girmi tunanin ta wlh, bari baban shi yadawo yauyau dinan zata bashi matar shi sutai gidansu.
Kallon agogon dakin tayi ganin karfe uku kuma tun kafin azahar take dakinshi bataga yay sallaba yasa ahankali tace "anyi sallan azahar fa" sai a lokacin yadan birkito da kanshi ya kalleta ya daure fuska tamau yace "ke nakema sallan dama?" girgiza kai tayi atsorace yace "gud, to banga damar yiba nd u shut d f*ck up kona natsar dake" "daughter" daga sama Mami ta kwalamata kira ahankali tace "na'am" sanan ta kalleshi ganin baida niyar dagata yasa ta daura hannuwan ta akanshi ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa ta tsorata ta janye hannuwan dan tazaci dukanta zaiyi, jin Mami takara kiranta nabiyu yasa yadagata tareda lumshe ido da sauri tamike tai sama da gudu yabita da kallo yana murmushin gefen baki, dakin Mami ta shiga da sallama kanta akasa, cup Mami ta mika mata tace "shanye wanan ina zuwa" karba tayi Mami ta tashi tafita daga dakin ahankali ta kafa cup din abaki ta shanye ta zauna akasa tana jiran shigowan Mami, ba'a jimaba tadawo da dan babban bowl dauke da farfesun kaza dayaji magani ajiye mata tayi tace "zoki cinye kafin ya huce" murmushi tayi dan wlh tanason kaza kafin akunyace tazauna akan gadon data ijiye mata tafara ci ahankali Mami kuma nawaya har taci iya cinta taji tai dam, Mami batare data yanke wayarba ta kalleta tace "idan ya isheki toki shanye roman tass" gyadakai tayi ta shanye roman kafin ta mike tsaye tafita daga dan kai plate din kitchen hada ido sukayi da sauri ta dauke kai ganin har lokacin wrestling yake kallo kenan la'asar ma baiyiba wanan wani irin dan iskan mutum ne, astagafurullah tace ta shiga kitchen ta ijiye kafin takoma sama dakinta ta shiga kasancewar bata salla yau tai zaman ta tana wasa da wayarta.
Koda daddare bayan Abba yadawo da Mami tasame shi da maganan abama Ayaan matar shi sutafi gida bakaramin murna da dadi yajiba, waya yadauka yakira Ayaan dake Part dinshi yazo itakuma Mami takoma ta shirya Bilkisu cikin wani hadadden lapaya maroon sanan tahada mata magunguna datace tadinga sha kullum kafin tarike ta takaita falon Abba, hadasu Abba yay yamusu wa'azi sosai sanan yakara bama Ayaan amanar ta, big Mummy ma tamusu Mami ma tamusu sanan suka rakosu har mota sai uban kuka take itadai yau tabanu Mamin datake gani taji dadi ma yanzu tafiya zatayi ta barta kuma gidan wanan mutumun, a motar shi suka sakata ya kunna motar yabar gidan yana murmushin keta. Ganin tana neman kashemai dodon kunne da kuka yasa yawani irin taka burki akan hanya arude ta dago kai da kakkausar murya yace "wlh koki natsu kona wurga ki kan titin nan na takeki na wuce" gum tayi ko tari bata karayiba harsuka kai gidan yay horn mai gadi ya bude mai ya shiga yay parking ya kalleta yace "wuce kitfita ke" adan tsorace tabude kofar ta fito tamaida mai tarufe hararan ta yayi sanan ya kunna motar yama mai gadi horn yana budemai yafita da gudu dan sauri yake club zaije su Fawaz tun dazu da Pops keta maganganun shi suke kiranshi, takai minti shabiyar a wurin kafin tai hadadden flat din da tagani ahankali ta bude kofa ta shiga tana kallon ko ina yanda yamata kyau yanzu itane agidan nan da wanan mutumin dako salla bayayi itadai rayuwa bata mata adalci ba wlh. Upstairs tayi tanata waige waige koda takai tarasa gane wananne dakinta saida taga akwatunan aure a saman wardrobe yasa tagane wanda take cikine nata. Ahankali ta zauna abakin gado tafashe da wani irin kuka zuciyar ta namata zafi maisa Isyaka zaimata wanan abin, ita yanzu bama fasa auren nata yake mata ciwo ba abinda yafi mata ciwo shine hadata da wanan mugun mutumin da akayi, dama taimako kan zama haka? Sosai take mugun jin kewan Baba su Raiyana da Layla Umma da mama, kankame filo tai tana kuka ga wani tsoro tsoro datake ji ahaka bacci yay awon gaba da ita.

Wuraren biyar ta farka sabida kiraye kirayen salla na farko dataji, bayin dakin ta shiga ta tsaya tana kallon ikon Allah gadai pampo amma bataga inda zata danna ruwa yafito ba tace "kodai sun manta ne basu sakaba" tabe baki tayi takoma wajen shower din shima haka babu inda zata danna ruwa yafito, kaman zatai kuka tafito ta zauna akan gado tana tunanin yanda zatayi, tafi 2min azaune kafin ta mike tsaye takara komawa bayin ta dudduba tap din ta lelleka jikinshi irin kodai itace take kauyanci bata iya budewa ba amma bataga abinda zata danna ko murda ruwa ya zuboba, shower ta koma tana dubawa shima bataga wani abu dazata danna yafito ba karkashin shower ta

Please Login or Register in order to submit comment