Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsugunna tadau rigar amma saitai baya zata fadi sabida yanda cikin yamata wani irin azababben zafi da sauri yataro ta tafado jikinshi yamata iso a fadadden kirjinshi, ihu takeyi amma baya fita tsabagen uban ihun datayi yau muryanta ya taushe tana kokarin kwace kanta amma takasa daidai lokacin akai knocking kofar. "Sir is Dr Ibrahim ur assistant permission to come inside sir" da kyar ya iya bude bakinshi dayamai nauyi yace "she's not ready Ibrahim go, will call u later" okay yafadi yajuya batare daya bude kofar ba, kokarin cirota yake daga jikinshi amma taki sakinshi saima sake rukunkume shi datayi dan wlh bazai gane mata jikiba, dan gajeren tsaki yay awahale kafin yajata ahaka tana jikinshi ya daurata akan gado, still taki rabuwa dashi saima uban kukan datake yi mara sauti, hannun shi yakai bayanshi ya bambare hanunta data kulla abayan shi ya fisge kanshi yana tsaki yana hararan ta, da sauri ta dauki rigarta dake kan gadon ta rufe kirjinta dashi tana kuka, tsaki yasake yi ya tsugunna yadau rigar ya gyara mata ta yanda zata sa sanan ya saka mata akai ya barshi anan wuyan ta, ganin yadan tarufe kirjinta da kaya ya koma baya yana kallonta yanda take sauke ajiyar zuciyar kuka tana share hawayen da sunki dena zuba yace "ke saka rigar nan da kyau an kicire wanan abun na jikinki" yanuna farin pant din dake jikinta, ko kallonshi batayi ba saima kara jajjan rigar take tana rufe cinyarta dashi daidai lokacin akai knocking juyawa yayi kaman ance dole yay maganan yace "who" daga waje akace "nurse Sameera" tsaki yasake yi yakoma kan kujeran dake wurin desk din dake dauke da computer a theater din ya zauna sanan yace "come in" shigowa nurse din tayi tana kallon Bilkisu tace "laa bakisa sakaba har yanzu, ki cire pant din mana" ko kallonta batayi ba, ganin haka yasa ta saukar mata da labulen daya zagaye gadon ta lallabata tacire ta dubata taga tai shaving dan dole idan za'ayi operation ayi shaving sanan ta taimaka mata tasaka rigar sanan ta kwantar da ita akan gadon duk tana kuka ta tattare labulen sama, sanan ta tattare kayan data cire ta linke taje ta ijiye a wardrobe sanan ta dauko roban fitsari tazo gaban desk din dayake tace "Dr nasaka mata robar fitsarin ne incase of fitsari" shiru yadanyi kafin agadaran ce yace "no intanajin fitsari a kaita tayi" komawa tayi ta ijiye tana mamakin shi wanan itace first patient din dayake hana kar asamata kome yahana oho. Bayan ta ijiye ya kalleta yace "go and call Dr Ibrahim lets start, and the anesthesiologist"
Fita tayi daga dakin shikuma ya mike yaje wardrobe ya ciro rigar operation ya saka ya kulle igayan ta baya yadan juyo ya kalleta yaga tana kwance ta lankwashe kafa tana hawaye, dan tabe baki yayi yaje gaban washhand basin ya wanke hanunshi har zuwa elbow yadawo jikin gadon ya kukkuna wasu mashina yanadan satan kallon fuskar ta idanunta alumshe ya kunna wani wuta dake saman gadon aiko ya haskota bau da sauri ta bude ido tana kakkare fuskarta tana hawaye, hada ido sukayi da sauri yawani dauke kai yakoma yasake wanke hannu sabida abubuwan daya taba sanan yazo ya saka hand glove yadauko dan kwanon dake dauke da different surgical blades daga sterilizing machine yadawo gaban gado ya ijiyesu akan table din dake kusa da kanta da karfi kwanon yay kara hakan yasa tasake bude idon data lumshe tayi ahankali dan bacci bacci tafara ji ta mugun gajiya, wasu Sharpe surgical blades ya dauko kusan guda uku ya nunamata ya daure fuska tamau yace "kingan su, kinga wayan nan wukaken" ya ijiyesu ya sake dauko wasu ya nuna mata yana wani shafa wukan da hand glove din hanunshi amma blunt side din yake shafawa yace "kinsan yanda ake fede akuya?" yay maganan yana kallon fuskar ta yanda ta zaro ido tana kallon wukaken ya kara daure fuska yana kallonta yace "haka zan fideki kaman yanda ake fede akuya yau" wani irin nishi take kaman kirjinta zai fashe, kafeta yay da ido yanda take breathing heavily tana zazzaro ido tana kallonshi, ahankali yasake ijiyesu ya dauko biggest surgical blade din cikinsu ya nuna mata yace "kinga wannan dashi zan fede duka fatocin ki uku na ciki, ur 3 layers duka zan barke" wani irin nishi takeyi hawaye na bulbulowa daga idonta ganin kaman zata sume yasa yace "fedeki zanyi namiki operation da wayan nan wukaken duka" azabure ta mike ta diro daga kan gado kaman mahaukaciya tama manta da ciwon datake fadawa jikinshi tayi ta kankame shi sosai da sauri ya ijiye wukar karya je ya yanka su, wani irin kuka tafashe dashi sosai kafin ta dago kanta dayake akirjinshi danya fita tsawo sosai, kanta ta daura hannayenta takama rigar theater dake jikinshi asaitin kirjinshi ta kalleshi da idanunta dasuka kumburu suna tsiyayar da hawaye tace "mene maka daka tsaneni haka eh?" fashewa tai da kuka sosai ta tace "kome menama ka, dan Allah kayakuri kayafemin, dan Allah karka sakamin wayanan wukaken ajikina, dan girman Allah, dan Allah kayakuri Ya Ayaan" tai maganan tana wani irin kuka tana kallon kwayar idonshi gashi dukta rukunkume shi yanda kirjinta ke bugawa kaman zai fashe tsabagen tsoratatar dayayi, ta maida kanta kan kirjinshi tana wani irin kuka mai tsuma rai tana furta "kayakuri kayakuri" agalabaice, ahankali yadan lumshe ido tareda sakin gajeruwan ajiyar zuciya.
[7/20, 12:30 PM] +234 803 238 4602: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦




Maman Abd Shakur

39 - 40

Ahankali yadaura hannayen shi akanta yana shafa manyan da kananun kitson dake kanta batare daya bude idanun daya lumshe ba, knocking kofar da akayi yasa yadan bude ido ahankali yace "common in" yay maganar yana saukar da hannayen shi daga kanta tareda gyara bayan rigarta. Dr Ibrahim, Nurse Sameera da Anesthesiologist mai suna Moses ne suka shigo dukansu atare, da ido yama Moses alamu ya shirya alluran, hannu yasa zai cirota daga jikinshi amma taki sakinshi sai kuka take kasa kasa, daukar ta yay batare data sakeshin ba ya kwantar da ita akan gadon zai tashi takara rirrikeshi tanamai kukan dabaya fita sosai tana kallon fuskar shi, jin yanda kirjinta ke bugawa yasa yadan hadiye haushin kanshin dayake ji namata wani laushi ahankali yace "relax nafasa miki to, calm down" sake kama rigarshi tai gam gam kaman mai rada tace "dagaske" yana kallon yanda lips dinta sukai jajir tsakiyar ya gyada mata kai yakai hanunshi bayan rigar yadan bude daidai inda za'ayi allurar da Moses yagama hadawa batare data masan yayiba dan duk hankalin ta atashe yake da wukaken dayace zai fedeta, da ido yamai alamu yayi, sanan yadan kalli fuskarta yanda take kallonshi da idanunta dasuka kankance tsabagen kuka ga dogayen gashin idon duk sun jike sun mammanne da juna kaman tasa gum, iskan bakinshi ya hura mata akan idon hakan yasa ta lumshe idon da sauri, wani irin azaba dataji tabayan ta yasa ta bude ido tareda kara damke shi da karfi tana kuka sosai saikuma luuu ta komar da kanta kan gadon wani irin bacci yay gaba da ita batare data sakeshi ba, dan murmushin gefen baki yayi sanan yasa hanunshi yacire hannayenta dake kan rigarshi ya maidasu kan gadon ya ijiye tareda sake gyara mata kwanciya ya dauko wani zani yarufe tundaga kafarta har cikinta sanan ya bude daidai wajen ciwon yadau abun rufe hanci da baki yasaka tareda kunna wutar operation, samira data rike kwanon surgical blades din da tagama kirgasu tace "Sir daga gani wanan patient din is very special sai kappa kappa kake da it..." wani irin kallo daya mata yasa tai shiru bata karasa ba, wani abu kaman marker Dr Ibrahim ya mikamai nan yay layin daidai saitin inda zasu yi aikin, sanan yakara mika hannu aka sakamai wani surgical blade akai, ahankali yadan kalli fuskarta kafin yasaukar dawani labule daya raba tsakanin su, sanan yama Moses magana yakara sakko da wutar kasa sosai yanda zasuga cikin da kyau, wukar ya dauka ya yanka fatar wajen Dr Ibrahim na share jinin dake zuba.... Nan dai operation ya kankama.

Akan kujera dake hanyar wurin theater din duk suka zauna Mami, big Mummy da Baaba dasuke ta bata baki dan kuka take ganin yanzu kusan awa uku kenan ba'a gamaba balle a fito, Abba da Baba Sulaiman suna tsaye suma addu'an samun lpy ta suke.
Anyi anyi Baaba tazo atafi gida taki tafiya wai ita sai taga anfito da Bilkisu tukunna zata tafi.

Sai wuraren 12:50 nadare suka gama operation din tatas, sai kallon appendix din daya cire mata suka saka awani kwalba yake yanda yay girma sosai dan gab yake daya fashe, inda kuma yafashe da mutuwa zatayi wlh. Da kanshi ya gungurota daga gadon dan kaita dakin hutu yana fitowa kam yaga su Abba dasu Baaba sun tatashi suna kallonta, Baaba ta fashe da kuka tana tattaba fuskarta ganin bata motsi, dan murmushi yay yace "lpy ta lau bacci take zata farka, operation din was successful" Alhamdulillah duk suka ce, yace "bari nakaita dakin hutu" wani daki ya bude kofa ya shiga da ita dakin mutum dayane ga gado ga tv harda fridge sanan akwai bayi aciki, ahankali ya dauketa sabida dinkin ya daurata akan gado yadan sake kallon fuskarta kafin yajuya yafita dan zuwa dauko wani rigan asibiti danna jikinta duk yabaci da jini, tsayawa chak yayi yay folding hanunshi akirji jin yanda Abban shi ke tonamai asiri a hospital.
Dariya Nurse Sameera da Dr Ibrahim harma da Moses sukayi, Nurse Sameera tace "habawa no wonder naga Dr was extra careful sai lallabata yake kaman Kwai shida baya wani lallaba patients, ashe matar shi ce" Abba yawani kara washe baki yace "biki ma har yana neman wata biyu" Dr Ibrahim yace "lallai nema shine koya fadama" daure fuska yay yazo zai wuce wajen ya shiga theater Abba ya fizgo shi, kaman zaiyi kuka yace "Pops kaga kadena badani a wajen aiki, ni kuma zo kutafi please" ya karashe maganan kaman zai mutu sabida haushi, Big Mummy tace "dont mind them boy kuzo mutafi" ta kalli Abba tace "mu barshi yay aikin shi da kyau gaskiya Alhaji". Kaman zaiyi kuka ahankali yace "stop calling me Boy in front of them big Mum" rufe baki big Mummy tai da sauri tanaso tai dariya aiko duka wajen aka kwashe da dariya, shigewa yay theater abinshi Abba ya kalli Baaba da Mami dake zaune suna yar dariya suma yace "mutafi gida ki huta ga mijin tanan ai xai kwana da ita" hakanan suka tashi sukaje driver yajasu sai gida

Sabon kayan asibiti ya dauka ya koma dakin ya ijiye kayan akan gadon yana kallonta yanda fuskar ta yay fayau tsabagen wahala da kuka gakuma santala santalan cinyoyin ta dasuka bayyana, dan gajeren tsaki yaja yay gaban gadon yadan zauna ta baki bakin kafin yasa hannu ya dagota ahankali, dan igiyan bayan rigan ya warware yana wani ciccije lebe, sakin igiyan yayi kafin yakai hanunshi ta gaban rigar yawani ja rigar kasa da sauri ya saketa tafada gadon bam dudda cikin bacci take saida tadan yatsine, runtse idonshi yayi da karfi kafin yadan mikar da hannu yana kokarin ya maida mata rigar inyaso yafita yakira Sameera tasamata, neman rigar yake wacce ya zameta takai kan cikinta, hanunshi dayaji ya sauka akan kirjinta yasa ya matsa baya da sauri har yana bigewa da kujera yace "f*ck!" fita yay daga dakin da sauri kaman ana ingiza shi, yay hanyar office dinshi daidai lokacin Nurse Sameera tafito daga dakin wata patent daure fuska yayi yace "kije ki chanza mata riga" ahankali tace "to Ango" wani mugun kallo dayamata yasa tabar wajen da sauri tana gimtse dariya, office dinshi yakoma ya shiga ya rufe kafin ya wuce bedroom din ciki, bayi ya shiga yay wanka abinshi yafito daure da towel fridge din dakin yabude yadau Vita milk mai sanyi ya bude yakoma kan gado yana sha, agogo ya kalla yaga har daya nadare yawuce ma tsaki yayi dan bazai iya kiran Meram ba is too risky hakan yasa ya ijiye bottle din yakoma ya kwanta sai bacci ba zancen salla.

Wuraren 8:30 yatashi da kyar, ya shiga bayi yayo brush yay wanka yay alwala, yadau mai ya shafa sanan ya shirya cikin dogon black jeans da soft cotton t-shirt maroon bakaramin kyau yamai ba color, ya shafa man gashin shi dake karasa gashin kanshi kyalli sanan yadau turaren shi mai kama jiki ya fesa kafin yahau dadduma yay sallan asuban yana idarwa ya mike yana kallon agogo dan baida lokacin yin azkar, takalmi ya zira sanan yadau lab coat yafita once ya zagaye ward yaduba patients dinshi da yarinyar chan gida zai tafi ya huta tun jiya baihuta bafa.
Saida yagama duba patients sanan yawuce dakin datake tun kafin ma ya shiga yaji maganan su Abba, daure fuska yayi ya shiga dakin, Abba dake shirin fita shida Baba Sulaiman ya kalla yace "Morning Pops, morning Baffa" kanshi Abba yazo zai shafa da sauri ya doje dan bayason abinda zaisa yarinyar chan ta raina shi, Abba daya bishi da kallon mamaki saikuma yay shiru shida Baba Sulaiman suka kalli juna sukai murmushi Abba yace "muntafi office, anjima da yamma zamu dawo" daure fuska yasake yi yace "saikun dawo" murmushi Abba yay suka fita daga dakin Baba Sulaiman yace "daga zuwan matar shi yasoma girma bayason kana badashi, shiba yaro bane ba yanzu wayaga su Ayaan da iyali" dariya dukansu sukayi Abba ya gyara zaman babbar rigarshi yace "ai haka nakeso dama".

Sai alokacin ya kalli Mami da Baaba dake hirarsu, yadan saci kallonta tana zaune cikin riga da sket na material mai taushi dark blue sai dot din white ajiki, kanta rufe da white hula tazauna tana jingine da gado idanun nan sunyi jajir alamun bata dade dagama yin kuka ba, ga dan karamin cup da aka mata tea aciki tana deba da cokali tana sha dan kin yarda Mami tabata tayi, ahankali take sha bakaramin kyau taiba, dauke kai yasake yi ya kalli Baaba yace "ina kwana" kafin ta amsa ya kalli Mami da tunda tamai kallo daya bata sake kallonshi ba dan har yanzu basu shiryaba, yace "Good morning Mami" Baaba ce kawai ta amsa shi tamai ban gajiya da sannu sanan ta kalli Mami dake magana da Bilkisu kasa kasa tace "suruka nidai zomu zaga nagaji da zama wuri daya jikin tsufa kafafuna sunyi tsami" dan dariya Mami tayi ta tashi tana gyara zaman babban gyalen jikinta tabi bayan Baaban harara ta watsa mai dasuka hada ido da sauri ya dauke kai, saida ya waiga yaga sun fita sanan yawuce gaban drawer dake dakin yajawo yana kokarin ciro wani drip dake ciki ya juyo da kai ya kalleta fuska adaure ganin daga fitar su tasoma matsar hawaye yace "ke!" kin kallonshi tayi dan wlh kallonshi kadai tadamata da hankali yake barin ma dazu data tashi akace operation yamata ga wajen na bala'in mata zafi ganin su Abba ne yasa ta mugun daurewa. "ke!" yakara daka mata tsawa daidai lokacin ya matso wajen gadon, arude ta kallai hawaye na gangarowa daga idonta yawani daure fuska yace "agidan ku ba'a koya miki gaisuwa bane" da kyar ta iya bude baki heart dinta na racing tace "in ina kwana" tsaki yaja ya kalli cup din tea hanunta ganin ko rabin tea batayi ba yay tsaki yace "malama finish dis tea nasamu nabaki maganin ki inba hakaba inbar wajen dinkin yay tsami daga bayama ya rube" yakara she yana wani irin hararan ta kafin yajuya yafita daga dakin, pharmacy dinsu yaje dakan shi ya faffadi magungunan da xa'a kawomai ya ciro ATM card dinshi yabiya da POS sanan yadawo dakin, tadan sha tea dudda bata shanye ba, wani cup ya dauka yadebo ruwa a dispenser dakin na zafi ya sirka dana sanyi ya danyi dalam dalam ya mika mata yana dauke kai, ahankali hanunta har rawa yake ta karba zatakai baki tsawa yadaka mata "ke wai nace kisha ne, God she's so so dull" yay tsaki yadauko ledan ya ciro magungunan dazata sha kusan kala biyar, ya babbalo tablet da capsules din yasaka ahannu ya mika mata, ahankali ta mika hannu tana goge hawaye da bayan dayan hannunta ya saka mata, sosai take kuka wanan karan harda kara, tasa dayan hannunta tana kirga uban kwayoyin maganin daya bata tasha kaman zararra, guda goma shadaya, dago kai tayi ta kallai kafin tasake fashewa dawani irin mugun kuka mara sauti dan ko nishi mai karfi bata yi sabida ciwon, sai ta kalleshi ta kalli magungunan tafin hanun nata tafashe da kuka dan har ga Allah bama tasan ta yanda zata hadiye duka magungunan nan abakin taba ita bama tasaba shan kwayoyin nanba jike jike Baba kemata, dan murmushin gefen baki yay saikuma ya zauna akan gadon kusa kusa da ita da sauri ta makale jikin bango, hanunshi yasaka akan hanun nata ya kwashi duka magungunan ya rike kafin ya ciro biyu ya mikamata, karba tai atsorace takai baki takai ruwa tana bata baki tasha, sake mika mata biyu yayi tasha, yasake mika mata biyu tahadiye, zai kara bata biyu tafashe da kuka tana girgiza mai kai, daure fuska yay hakan yasa ta karba ta hadiye da kyar ya mika mata ukun dasuka rage babu alamun wasa akan fuskar shi da kyar tasha kaman zata suma ya karbi cup din ruwan ya ijiye yana duba agogon hanunshi kiran Rolex, saida tai exactly 5 minutes sanan ya mike tsaye ya dauke cup din tea data rage ya ijiye akan table ya kalleta yace "ke kwanta inason na duba inda na fede" ko kallonshi batayi ba saima dauke kai datayi tana kokarin hadiye hawayen dake shirin zubowa, takowa yayi yadaura hannunshi akan kafadun ta da sauri ta kallai kirjinta na bugawa ahankali ya kwantar da ita ya daura kanta kan filo batare daya janye idonshi daga kan fuskarta ba, runtse ido tai da sauri sabida wani irin azaban dataji, hannun ya cire daga kafadar ta ya dage rigar sama, bugawan da kirjinta yayi harsaida yagani daga cikinta, wajen dinkin yabi da kallo kusan na 3mnutes kafin ya mike tsaye ya makala drip din daya dauko akan karfen makalasu yamata fixing drip din yadauko wasu allurai yay acikin ruwan 8sanan yadawo bakin gadon ya zauna yana kallon wurin aikin kafin yabi cikin gabaki daya da kallo yanda yay flat ga fatar looking fresh sai glowing yakeyi, ahankali ya mika hannunshi ya daura akan dan cibiyar ta, da sauri ta bude ido ta kallai atsorace ita shima yake kallo akasalan ce yace "wat?" shafa cibiyar yacigaba dayi ahankali kafin ya gangara da yatsar shi zuwa inda yay dinki yana zagaye wurin hanunta ta daura akan nashi tana wani irin wahalallen kuka, akaro nabiyu yakara kallonta murya kasa kasa yace "wat?" da kyar ta iya bude bakinta tace "zapi" hanunta data daura akan nashi yabi dawani irin kallo hakan yasa tai yunkurin janye hannun da sauri ya rike hanun yana kallon fuskar ta kafin ya maida dubanshi ga hannun, ahankali ya sa hanunshi ya shafa tsakiyar fatar hanun nata yana feeling yanda hanun keda wani irin taushi kaman hanun jariri, bin jajayen yatsun ta dasuka sha lalli yay da kallo kafin ahankali yakai yatsar wurin bakinshi yana kallon yanda idanunta ke fitar da hawaye.
[7/20, 12:30 PM] +234 803 238 4602: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦



Maman Abd Shakur

41 - 42

Ahankali yasa yatsar cikin bakinshi yana wani irin tsotsar yatsar kaman yasami minti, sosai takara karfin kukan ta sabida yanda takejin wani iri gashi yaki bata daman fizge hanun, knocking kofar akayi hakan yasa yacire hanun daga bakinshi ya maida ya ijiye yana kallon fuskar ta da idanunshi dasuka chanza launi yay hanyar kofar yabude wata Nurse ce Amina dan Sameera tagama night wanan tai taking over, gaidashi tayi batare daya amsaba yace "ki cema Dr Ibrahim ya dubata dan i will not be available today" yana fadin haka yasa kai yafice daga dakin office dinshi yakoma yadau car keys da wayarshi yafita daga office din bayan ya kulle, wajen parking yaje ya shiga motar shi yabar asibitin gidanshi ya wuce direct yay parking yafito ya shiga ciki, akan dogon kujera ya kwanta jin kaman ma zazzabi zazzabi na neman rufeshi, wayarshi ya lalubo daga aljihun wando yay dailing number Meram saida kiran yakusa katsewa ta dauka tai shiru, dan murmushi yay dan tunda taji labarin yay aure tadau zafi sosai, dan murmushi yay yace "ina jiran ki agidana now" zatai magana ya katse wayar tareda kara gyara kwanciya ya sanya hannayenshi abayan kanshi yana kallon POP, tashi yay zaune ya dunkule hannu ya daki iska angrily, kafin ya dafe kanshi, tashi yayi yawuce bedroom dinshi yafada kan gado ya lumshe ido. Wajen 30min Meram ta dauka kafin tazo tana sanye cikin wani open neck white top me spaghetti hand sai strap belt long skinny pant navy blue, braids ne akanta masu tsawo babu dan kwali tafito daga motar taci uban hill tai cikin gida bayan tai parking rike da yar jakarta na Louis Vuitton tana taku daidai ta shiga gidan tana tauna cingum ta mugun daure fuska, ganin baya sitting room yasa tai bedroom dinshi yana kwance idanunshi biyu saidai duk sun kankance tsayawa tai daga kofa tana kallon shi yanda maroon t-shirt din jikinshi ya mugun yimai kyau tai kewanshi bakadan ba itama tasani amma maisa zai yi aure aboye bayan yasan yanda take sonshi, dan juyo dakai yay ya kalleta sabida yanda jikinshi yabashi ana kallonshi, kafeta shima yay da ido batare dayace mata ta shigo ba, dauke kai tayi daga kallonshi cike da basarwa tace "why are u calling me? Bani ka yaudara ba kana using dina sanan kaje kai auren ka, ancemin ma yarinya kaje ka auro, very decent ba irinaba, ni kawai am just ur machine ko, u use me as u pleases, hmmm har ka gaji dacin amarcin ne ka kirani dama..." "Ke!" ya daka mata tsawan dayasa tai shiru, tashi yay ya zauna abakin gado da idanunshi dasukai jajir ya nuna mata kofa yace "out" bude ido tayi tana kallonshi cike da mamaki yasake nuna mata kofa yace "i said out kema kinsanni bana rokon abu, are u expecting me na lallaba ki dannai aure, dama chan ni saurayin kine? Okay is over Fita daga nan, i don't need u as well rubbish" yaja tsaki rai abace, fashe mishi tai da kuka ganin yanda yaci serious tafado jikinshi tana kuka ta kankame shi tana kissing face dinshi tace "am sorry Ayaan please karka rabu dani, naji na yarda i will be ur side chick, have me" ta wurgashi kan gado yanda jikinshi yay laushi ne yasa yatafi shima luu, nan ta shiga aika mishi da sakkonni kafin ya biyemata dan dama yana cikin sananin bukata.


Tunda ga ranan bai kara komawa hospital dinba kiran Abba ma yayi yace "yatafi wani conference meeting a Abuja" daganan ya kashe wayarshi dukama dan bayason damu. Dr Ibrahim ke kula da ita bayan 5 days ya sallameta aiko taji dadi dan tagaji da asibitin ga dinkin ya fara warkewa dan jikinta nada kyau sosai da kanta zataje bayi tai alwala tai wanka kawai dai bata daukan abu mai nauyi ne kwata kwata, gidan su Abba aka wuce da ita sabida takara warkewa kafin akaita gidan mijinta idan yadawo.

Yau satin ta daya agidan taji sauki sosai yanda Abba da Mami keji da ita ita abinma har kunya yake bata.
Tana kwance hadadden adakin ta lullube da bargo ta daura kanta akan cinyar Baaba daketa fama da Mami ita gaskiya zata koma yau Mami namata dariya, sallama Abba yayi ya shigo Mami tace "yauwa Alaji kajifa wai tadage tafiya zatayi yau" kaman Baaba zatai kuka tace "to Alaji taji sauki dan Allah kubari natafi nabar Muji shi kadai agida" itadai lumshe ido tayi kaman tana bacci dan batason Baaba ta tafi dan ita take gani takejin dadi, Alhaji yace "to to to shikenan ai, amma ki shirya" ya kalli Mami yace "muje mu kaita taga gidan yarta ko anjima inmun dawo sai nasa driver ya kaiki zaria" washe hakora Baaba tayi Alhaji yafita yana dariya, tashi tayi tana kallon fuskar Bilkisu data lumshe ido ta kalli Mami tace "kinga kasar nan ashe bacci tayi ana hira" dariya Mami tayi tace "yata ba kasa bace

Please Login or Register in order to submit comment