Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi gida ko Jamila?" Nihad ta daga kai ta kalli Mumy da sauri sanin da ita take, Aunty Jamila tace "Gaskiya kam, tunda anyi sati hudu har da kwana biyu yau, kuma nasan saboda ita ne ma bai bar garin nan ba har yanzu, kar rashin hankalin namu yayi yawa" Nihad ta marairaice tace "Mumy ba sai anyi 40 days ba?" Mumy ta ɗan kalleta tace "Me za kiyi har 40 days a nan din?" Aunty Jamila tace "A duk inda kike kika ma Abbanki addu'a zai samesa ba sai lallai gidan nan ba Nihad, kinga Allah ya baki miji wanda ba ko wace mace ke samun irinsa ba a rayuwar nan, uwa uba ga danginsa mutanen kirki mutanen arziki, duk da matsayinsu amma kowa nasu ne babu girman kai ba komai, to kada mu zama kananun mutane mu yi ta ajiyeki a nan, gashi yau har sati hudu, don haka ki shirya gobe ya daukeki ku koma..." Nihad ta dinga kallonsu har hawaye ya cika idonta, tsoronta kar ta koma Abuja damuwar rasuwan Abbanta ya dawo mata sabo, don idan tana ganin Mumy da yan uwanta tana jin relieve sosai, Ta goge hawayen idonta cikin sanyin murya tace "Then can i go together with Nihal?" Aunty Jamila tace "Sai abinda mijinki yace" Nihal ta buda ido tana kallonta, a hankali tace "I will come but not now" Nihad bata sake cewa komai ba, haka Aunty Jamila ta sata gaba ta fara hada kayanta a akwati, Usman yayi sallama kofar dakin, Mumy da Aunty Jamila suka amsa masa ya shiga, bayan ya gaishesu yace "Mumy dama na shigo in gaya maki Abban Khalil ya samar min aiki a Nnpc na garin kaduna" Mumy da Aunty Jamila suka hada baki wajen cewa "Alhamdulillah" sosai suka taya sa murna, Mumy tayi masa addu'a sosai tayi masa fatan alkhairi, Yace "Nagode Mumy, Allah ya kara girma" Mumy tace "Yaushe zaka yi resuming aikin kenan?" Yace "Gobe lahadi za mu tafi kadunan tare da Farooq don shi ma zai koma aiki, on monday in sha Allah zan fara aikin" Mumy tace "Toh Allah ya bada sa'a, Allah ya tsare" yace "Ameen" Daga haka ya mike ya fita daga dakin, Aunty Jamila tace "Allah sarki, na taya sa murna sosai, Allah ya saka ma General da alkhairi" Tun da aka tura ma Usman offer din yaje ya nuna ma Umma a dakinta, ko gani bata yi ba bayan ta masa addu'a ta tasa ya je ya nuna ma Mumy a bangarenta. Aunty Jamila da Nihal na zaune parlon Mumy suna kallon wani movie Khalil ya kirata, ta daga wayar bayan ya gaisheta yace "Aunty dama zan zo da wani bako ne yanzu zai ma Mumy gaisuwa" Aunty Jamila tace "Toh sai kun zo" Nihad na can daki tare da Mumy da tun yanzu har ta fara mata nasiha ta yi hkuri ta zauna lafiya da mijinta kar ta basu kunya, gaba daya sun sa ta hada kayanta duk da dai basu ce ma khalil din gobe ya dauketa su tafi ba, tana son gaya ma Mumy auren da zai yi amma ta kasa don that's her only nightmare ynzu, Aunty Jamila ta shigo dakin tace "Yaya ki fito za a maki gaisuwa" Mumy tace "Toh" daga haka ta mike ta nufi kofa, Nihad ta bi ta da kallo, lokaci daya hawaye ya cika Idonta, Mumy na shigowa parlon ta zauna tana kallon balaraben dake zaune, ya gaisheta da turanci ta amsa da fara'a, nan yayi mata gaisuwa, ya kuma yi ma Abba addu'a sosai, cikin sanyin murya tace "Ameen, thank you very much" Khalil ya gaida Mumy don duk ranan bai shigo gidan ba, Aunty Jamila ta tafi main parlor dauko ma baƙon ruwa don in dai Nihal ce ba tashi zata yi ba in ka bibiya ma hankalinta baya tare da ita, don a ko da yaushe zaka sameta absentminded barin idan ana kallo, Baƙon ya daga kai yana kallonta yace "Hi Nihad, i am so sorry for ur lost, may Allah SWT grant him aljannatul firdauss" Khalil ya ɗan yi murmushi ya kallesa da turanci yace masa ba Nihad bace sister dinta ce, Mumy ta tabo Nihal da bata ma san ana mata magana ba, Da sauri ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, Khalil yace "Yana maki gaisuwa...." Ta kallesa duk da bata san abinda yace ba tace "Ameen nagode" Nihad ta fito daki don sarai ta dau muryarsa, ya daga kai yana kallonta bayan ta fito, tana Murmushi tace "Hi Ayman" Da Fara'a ya amsa mata, ta karaso ta zauna a parlon, nan suka gaisa yayi mata gaisuwa ta amsa ta masa godiya, yana nuna mata Nihal da mamaki yace "The resemblance is obvious, just complexion difference" Tana Murmushi tace "Yeah, she is my blood, her name is Nihal" Ya sake kallon Nihal yace "Nihal" Nihal ta kirkiri murmushi bata ce komai ba Yace "It's nyc meeting with you Nihal" Ta gyada masa kai kawai, don bata son magana yanzu, Ayman bai wani dade a parlon ba, bayan ya sha ruwan da Aunty Jamila ta ajiye masa, yayi ma Mumy sallama ya ajiye mata dollar dari biyar, Mumy da Aunty Jamila suka yi masa godiya sosai, ya fita parlon tare da Khalil, Mumy na kallon Nihad da mamaki ganin yawan kudin da ya ajiye mata tace "Who is he?" Nihad tayi murmurshi tace "Sister din Mami namesake dinki ce ta hadani da shi farkon zuwana Abuja" Aunty Jamila ta buda baki tace "Lokacin basu san da aurenki da khalil ba?" Dariya kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Jamila tace "Ikon Allah, to dama yasan khalil din ne?" Ta girgiza kai tace "Kilan sai daga baya, nasan Aunty Maryam ce zata gaya masa Abbana ya rasu shine zai ce zai zo gaisuwa, dama dai yana shigowa Nigeria but a Uk yake zama" Mumy tace "Allah sarki, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya bashi lada" Khalil bai dawo gidan ba sai dare, nan Aunty Jamila ta sanar masa gobe ya dau Nihad su tafi gida, ya dai yi shiru bai ce komai ba, komawa daki tayi wajen er uwarta, Khalil ya kalli Nihal dake juya abincin gabanta a parlon, yace "Ina wayarki Nihal?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tace "Yana dakina" Yace "A kunne yake?" Ta girgiza masa kai don for more than a month now bata kunna wayarta ba, Yace "Ki kunna za a kiraki....." Ta dai yi shiru tana kallonsa, yace "Kin ji?" Ta gyada masa kai kawai, Nihad ta shigo parlon rike da abinci ta kawo masa, ta ajiye gabansa ta zauna tana facing dinsa sannan ta dau plate tana debar masa abincin, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, Nihal ta mike ta dau abincinta ta shiga dakin Mumy, a hankali Nihad tace "Should i add more?" Yayi kasa da murya yace "I want to feed on u, not rice and stew"








Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah






Ur evidence via 07087865788










Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp 09084473900💖 NIHAAD 💖


76




Nihad tayi murmurshi kawai ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba ta kara masa nama akan abincin da ta zuba, shi dai kallonta kawai yake kasa kasa, can yayi kasa da murya yace "Baki ce komai ba...." Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa tana mika masa abincin tace "Fara cin wannan" Dariya ta basa, a hankali yace "Are you serious?" Ta gyada masa kai, ya amshi abincin ya fara ci, ta koma ta jingina da kujeran ta kusa da inda yake zaune tana kallon tv dake aiki a parlon, lokaci lokaci take satan kallonsa ta gefen ido sai taga shi ma kallonta yake, taji yayi kasa da murya yace "When are we leaving tomorrow?" A hankali tace "Sanda kace" Yace "Da safe?" Tace "Allah ya kai mu" Bai wani ci abincin da yawa ba ya ajiye ya dau ruwa, ta daga kai tana kallonsa ganin ɗan abinda ya ci tace "Bai maka dadi bane?" Cikin whisper yace "When it's not you...." Hararansa tayi ta gefen ido, yayi murmushi ya sha ruwan da zai sha ya ajiye sauran yace "Let me not over stay my welcome, bari in tafi sai da safe" Tace "Toh Allah ya kai mu..." Tashi yayi yace "Kice ma su Mumy na tafi sai da safe" Nihad ta mike ta dau gyalen Nihal ta yafa a jikinta, shi dai yana tsaye yana kallonta, ganin kallon da yake mata irin na mamakin nan ta ɗan buda ido a hankali tace "Ko baka son rakiyan ne?" Ya wara ido yace "Idan baki rakani ba ma ai bazan tafi ba sai dai in kwana parlon nan" Ta ɗan yi murmurshi ta dau wayarsa dake saman kujeran, ya nufi kofa ta bi bayansa, sai bayan da suka fito daga main parlor ya kama hannunta suka nufi gate walking slowly ko wanne da tunanin da yake a ransa, Aminu na zaune bakin gate din har sannan shi fa bai gama dawowa dai dai ba kai kace shine Farooq ko Usman, Nihad ta zame hannunta a hankali daga na Khalil ganin Aminu, ta nufi gate ta fita, khalil ya tsaya wajen Aminu, ba a dau lokaci ba Khalil ya fito kofar gidan ya ganta jingine jikin motarsa, ya karasa har kusa da ita ya tsaya yana facing dinta yayi kasa da murya yace "Till tomorrow?" A hankali tace "Allah ya kai mu lafiya" Yana kallon eye balls dinta yace "Ko mu tafi in dawo dake gobe da safe?" Ta zaro ido tace "Aa ni dai bazan iya ba" Yayi murmushi yana bin layin da kallo, wanda babu kowa cause it's few minutes to 10pm, murya can kasa yace "Can i kiss you love?" Ta sunkuyar da kanta kawai tayi murmurshi, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa da lumsassun idonsa, sai kuma yaga ta ɗan bi layin da kallo, ganin babu kowa ta gyada masa kai a hankali, ya hade goshinsa murya can kasa yace "With stew in my mouth" Daga haka ya fara kissing dinta, and he did that for almost a minute, underneath his breathe yana lumshe ido yace "I love you so much" Lumshe ido tayi, kawai yaga ta shige jikinsa a hankali tace "Same" Yace "Same what?" Da sauri ta ajiye masa wayarsa kan motar ta juya ta nufi gate, dariya ta basa sosai, ya bi ta da kallo har ta shige gidan ta kulle gate. Washegari Nihad na tashi wajen karfe tara bayan tayi breakfast ta fara harhada duk kayanta dake dakin Mumy, Aunty Jamila dai sai bin ta da kallon mamaki take don bata ce masu komai ba kawai ta hau hada kaya kamar warce ake jira a kofar gida, Ita kanta Mumy bin ta kawai take yi da kallo, tana kokarin rufe trolly dinta kamar ance ta daga kai taga duk kallonta suke a dakin har Nihal dake dakin, kunya taji ya lullubeta ta rufe fuskarta da trolly din da sauri tana turo baki, Aunty Jamila tayi dariya tace "Duk wannan azarbabin tafiya ne haka kamar muna koranki Nihad?" Ita dai bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba but she is so ashamed, Aunty Jamila na murmushi tace "Karfe nawa za ku tafi?" Ba tare da ta dago ba a hankali tace "Aa ni bai ce min yaushe ba, kawai dai naga kayan are scattered ne shi yasa nake gyarawa fa Aunty" Aunty Jamila nata murmurshi tace "Eh naga alama, kayan kam are scattered" Fasa zuge zip din Nihad tayi daga karshe ta mike kawai ta fita daga dakin ta koma dakin Nihal ta shiga bandaki tayi wanka ta shirya cikin kayan da ta cire a akwati, riga da skirt ne da babban mayafi wanda Aunty Maryam tayi mata a Abuja, bata taɓa sa shi ba dama sai yau, tana gama shiryawa ta kwanta gefen gado kawai... Karfe sha daya Nihal ta shigo dakin, tana kallonta tace "Ur husband is around" Nihad ta daga kai ta kalleta sai kuma ta mike zaune, Nihal tace "Bari in daura maki dankwalin" Daga haka ta dau dankwalin ta tafi gaban madubi ta jawo stool tana kallon Nihad tace "Dawo nan" Nihad ta mike ta tafi gaban mirror din ta zauna, eye pencil kawai ta saka a idonta sai lip balm da ta saka a lebbenta amma zaka yi tunanin har powder ta shafa, she looks so beautiful, ga shi ta ɗan marmaro daga raman da tayi, Nihal tayi mata dauri me kyau ba kuma me hayaniya ba, ya zauna dass a kanta, sosai kyanta ya kara fitowa, Nihad na kallonta a hankali tace "Thank you" Nihal na Murmushi tace "You look beautiful sweet sis, nasan bazai gane ki ba" Nihad dai murmushin kawai ta mayar mata, Nihal ta dauko mata gyalenta ta mika mata ta amsa sannan suka fita daga dakin tare, tun da suka shigo parlon Mumy Khalil ke kallon Nihad babu ko kiftawa don at first bai gane ita bace duk da na kwalliya tayi ba a fuska amma bai taɓa ganinta da daurin dankwali ba, ta zaune tana kallonsa a hankali tace "Ina kwana" Ya lumshe ido ya bude a hankali yace "You look beautiful dear, how was ur night?" Tana wasa da fingers dinta tace "Alhamdulillah" Ita dai Nihal na zaune a parlon ta maida hankalinta kan tv, Khalil yace "Ur box?" Nihal na jin haka ta mike ta tafi dakin Mumy don dauko akwatin Nihad ta fita main parlor da shi, Aunty Jamila ta shigo parlon tana kallonsu tace "Toh ku yi ma yan gidan sallama dai kafin ku fita" Khalil yace "In sha Allah" Aunty Jamila tace "Kafin in koma Jigawa in sha Allah za mu taho da lefen nata Abujan, inna ta kai su can gidan ta ajiye a dakinta" Khalil yace "Allah ya kai mu Aunty" Aunty Jamila tace "Ameen, a gaida mana su Hajiya da General, mun gode kwarai Allah ya bar zumunci" Khalil yace "In sha Allah" Nihad ta mike ta tafi dakin Mumy, ta sameta zaune saman darduma, ta duka gefenta murya can kasa tace "Mumy za mu tafi" Mumy na kallonta tace "Toh Nihad, Allah ya tsare, Allah ya baku zaman lafiya, ki dau iyayensa tamkar naki sai ki zauna lafiya a rayuwa kin ji, Allah ya baku zuri'a dayyaba" Ita dai Nihad kanta na kasa, Mumy tayi shiru bata dake cewa komai ba, don bata son hawayen dake taruwa idonta ya zuba, she knows she is so much going to miss her daughter most especially in this trying time, banda Aunty Jamila na nan da bata san kuma ya zata yi ba, Nihad ta goge hawayen da ya kawo idonta a hankali tace "Allah ya ji ƙan Abba ya basa aljanna...." Sai kuma ta fashe da kuka, Mumy da hawaye ya fara sauka idonta tace "Ameen, ta shi ki je" Cikin rawan murya tace "Idan su Sudais sun dawo ace masu na tafi" Kai kawai Mumy ta iya gyada mata saboda bata son tayi breaking, Nihad ta mike ta nufi kofa Mumy ta bi ta da kallo tana share hawayen dake sauka idonta, Aunty Jamila ta bi Nihad da kallo bayan ta fito daga dakin, can ta mike ta tafi wajen Mumy, ba a dau lokaci ba ta fito tare da Mumy da ta tsaya jikin kofar dakin nata tayi ma Khalil sallama cikin sanyin murya, ya kasa kallonta yace "Ameen Mumy, Allah ya kara hakura" Ta amsa masa da Ameen, sannan ta juya ta koma daki, Tare da Aunty Jamila suka fita main parlor, Nihal na zaune main parlor din tana jiran fitowar su, ba don ran Nihad ya so ba suka nufi bangaren Umma da khalil, shi ma kawai don Nihal na zaune ne bazata iya ce masa a'a ba da yace mata za su shiga wajen Umma, banda haka da bazata ba wllh, Kamila na zaune parlon Umma, ta gaida Khalil ya amsa mata da murmushi, ita dai Nihad wasa kawai take da gefen mayafinta, Amina kuma ta shiga dakin Umma, sai ga Umma ta fito ta zauna nan bakin kofar dakinta rike da carbi, Khalil ya gaisheta ta amsa cikin sanyin murya, yace "Za mu koma ne yanzu in sha Allah Umma" A hankali Umma tace "Toh Allah Ubangiji ya tsare hanya, Allah ya kai ku lafiya, ya kuma baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya rabaku da sharrin masu sharri" Kansa a kasa yace "Ameen" Ita dai Nihad bata kalli Umma ba, Umma ta ɗan kalleta, sae kuma cikin sanyin murya tace "Toh Nihad, Allah ya kai ku lafiya.... Allah ya ji ƙan mahaifinku ya gafarta masa...." Ba tare da Nihad ta kalleta ba don har hawaye ya cika idonta tace "Ameen" Khalil ya mike yace "Toh Allah ya ƙara hakuri Umma" Umma tace "Toh Khalil, a yayyafe... Allah kuma yasa muna da rabon ganawa, Allah ya kaddara saduwan mu" Yace "In sha Allah, Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Nihad ta mike ta nufi kofa ta fita, Khalil ya bi bayanta, Umma ta kalli Kamila tace "Toh ki raka su ko" Mikewa Kamila tayi ta bi bayansu har zuwa main parlor, Khalil na kallonta yace "What did u study in school?" Tace "Microbiology" Yace "Ohk maa sha Allah, kuma duk Cv's dinki na nan ai" Tace "Eh suna nan" yace "Toh bari mu shiga muyi ma Inna sallama kafin mu fito ki dauko min" Tace "Toh" Suna shiga dakin Inna suka sameta ita kadai tayi backing kofar dakin tana ta faman aikin kirgan uban kudaden da aka bata, har ta jawo zani zata boye ganin Khalil ne da Nihad ta bar su a sarari, ta marairaice fuska tana kallon Khalil tace "Sannu Halilu" Ya zauna kasan Carpet yace "Ina kwana inna?" A hankali tace "Lafiya lau Halilu, ya gajiya" Yace "Alhamdulillah Inna" Nihad ta durkusa gefen gado tace "Ina kwana" Inna ta kalli Khalil tace "Daga ita har Nihal sai sun ga dama suke shigowa su gaisheni su ce min ya hakuri kuma sun san ina gidan nan, kai kace ni na kashe Ibrahim din" Khalil ya ɗan buda ido yace "Aa gaskiya basu kyauta ba" Inna tace "Atohh bayan wanda ya hada ma Allah ya daukesa ya bar duniyar da kalubalen dake cikinta kadai ta ishi bawa, ai nasan in sha Allahu yana kyakkyawan masauki tunda shi din ba mutumin banza bane, don haka tsakanina da su kawai kowa ya kama kansa, dama babu abinda na hada dasu har ga Allah...." Khalil ya ɗan yi murmushi yace "Kiyi hakuri Inna" Nihad dai bata kalli inda Inna take ba, Khalil yace "Dama za mu koma Abuja ne yau, shine muka shigo mu yi maki sallama" Inna tace "Kai, kaga da anyi arba'in ai sai in bi ku inje na musamman in ma Janar da mahaifiyarka godiya don ba ko wasu surkai ne za su yi abinda suka yi ba, mutanen kirki wllh, sannan kuma duk abi da ni gidan abokansa da suka zo har nan in masu ban gajiya, babu wanda bai ban dubu dari ba a cikinsu, kaga yanzu nake ta hada kan kudaden ko rijiya ce in sa aje kauye a haka ma bayin Allah, duk wanda ya sha ruwan Allah ya kai ladan gun Ibrahim dina" Khalil yace "Gaskiya ne inna, hakan abu ne me kyau kuwa" Inna tace "Wallahi abinda nake so in yi kenan, shi yasa na fito da kudaden yau nake kirgawa, sannan filayena biyu a siyar a gina dankareren masallaci a bakin titi da sunansa, in sha Allahu abinda zan yi kenan, idan Allah ya kara hore min har gidan marayu sai na gina da sunansa wllh, to idan ban masa ba wa zai masa?? Sai dai ko yayansa Abubakar, balle ma Abubakar din ya dauke nauyin karatun kananun yaran da ya bari wato Sudais da Fadil, ita Amina naji ance ta gama sakandarin amma fa yace bazata jami'a ba, ni dai nace ko wa aka samu kawai ayi mata aure ta bar gidan nan don babu ruwana kuma wllh, mai gadi ma kaga Abubakar ne zai dinga biyansa albashi daga yanzu, da nace a kori ko me gyaran fulawan da sharan tsakar gida a bar me wanki da guga kada kudin yayi ma Abubakar din yawa sannan fa ga albashin dreba me kai kananun mazan nan boko da islamiyya amma yace duk zai iya ba sai an kori kowa ba, cefanen gidan kuma Farooq da Usman sai su dage, duk da buhunhunan shinkafa sun kusa goma yanzu haka a store wanda abokan Marigayi da yan wajen aikinsa da yan anguwa suka harhada aka kawo, ga jarkan mangyada manya manya har biyar, indomie ma da na kirga katan 11 ce wllh, ga taliya, kuskus, macaroni, kai har fa da gero da masa ko wa zai ci?? Sannan ga buhunhunan sugar, flawa, kai mu je ma in nuna maka store din ka gane ma idonka kawai, wllh ko kwakkwaran spes babu a store din ya cika makil da kayan abinci" Khalil yace "Duk na gani ai Inna, ina nan duk aka kawo" Inna tace "Toh banda shi mutumin kirki ne waye zai ma iyalinsa haka? Ko nan da shekara biyu bana tunanin kayan abincin nan za su kare, kawai fatana kada su yi espaya kawai" Khalil yace "Baza su yi ba in sha Allah" Inna tace "Allah ya sa, sannan lefen matar nan in sha Allahu idan zan taho godiya da bangajiya da su zan zo" Khalil na Murmushi yace "Toh Allah ya kai mu inna, bari mu je kada jirgin ya tashi babu mu" Da sauri Inna tace "Maza ku je, Allah ya tsare" Dubu hamsin ya ajiye mata, tayi ta godiya tana sa masa albarka ta rakosu har main parlor, Kamila na tsaye tana ta jiransa da takardun nata, ya nufeta ya amsa tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi" Yace "In sha Allah, zan kai ma Abbana" Tace "Toh Allah ya kai ku lafiya" Gaba daya yan gidan suka rakosu gun mota banda Mumy da Aunty Jamila sai Umma, Inna ta dinga cewa "Allah ya kai ku lafiya, Allah ya kiyaye hanya...." Khalil ya bude motar yace "Ameen Inna, Allah ya saka da Alkhairi" Aminu ya gwalo ido ganin wanda ke tahowa a mashin dinsa, shi kansa khalil tsayawa yayi yana kallonsa, Inna tace "Waye wannan kuma da mashin duk ya cika anguwa da ƙara" Yana isa dai inda suke ya kashe mashin din ya sauka ya fashe da kuka sosai, Aminu ma ya rushe da kuka kamar jira yake, Inna ma sai ta fashe da kuka tace "Habibu?? In gaya maka Habibu Allah yayi ma Ibrahim rasuwa" Habibu ya nemi dakali ya zauna yana rusa kuka Aminu ya zauna gefensa yana tayasu, Kamila tace "Don Allah meye haka, ku da za ku dinga bin sa da addu'a" Habibu yace "Haka ne, Allah Ubangiji ya gafarta ma Alhaji, wallahi na shiga Nijar saro ma yayana kaya sai jiya na dawo labarin nan ya riskeni, Allah sarki Alhaji har yau gashi ina ta cin moriyar shagon da ya bude min har na gina gidana a birni" Inna tace "Toh in kai me hankali ne sai ka duba marayun da ya bari kanana idan ko ba haka ba Allah sai ya tsine maka wllh" Habibu ya dinga cewa "Haka ne inna, gaskiya ne Inna" Kamila ta daga ma Nihad hannu ta juya kawai ta shiga ciki, Amina ma tace "Allah ya kiyaye Aunty Nihad" Daga haka ita ma ta shiga ciki, Nihal ta mata side Hug cikin sanyin murya tace "I will miss u sweet sis" Daga haka ita ma ta koma cikin gida, Habibu ya taso yana kallon Nihad da ladabi

Please Login or Register in order to submit comment