Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai hakuran ba kenan?" Da wani expression yace "Shine nace kun min wani abu ne da ya bata min rai har xa ki zo bani hakuri tukunna?" Ta langwabar da kai tace "By the way, sunana Asma'u, amma kawayena na kirana da Husnah...." Ko rufe baki bata yi ba ya kulle gate din almost on her face ya juya ya koma cikin gida. Yana shiga daki ya dau wayarsa dake ring ganin Nadeeyah ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren tace "I saw ur calls" Ya d'an yi shiru, da mamaki yace "My calls?" Tace "Yea, minutes ago" Yace "Ohh, sorry mistake ne" Tace "Ohk, sai anjima kenan?" Yace "Sure" Katse wayar tayi, ya hau duba call logs dinsa da sauri, Nadeeyah kawai ya ga ta kira, ya kalli kofar dakin ko kiftawa baya yi. Da yamma Khalil ya shirya xai tafi can gida saboda kiransa da Abba yayi, Nihad dai na daki abun duniya duk ya bi ya isheta, da ta gaji da wannan bangaren gadon ta koma daya bangaren, ko kuma ta sauka kasa ta zauna, ita bata saba xama waje daya kamar jaririya ba, all through the week ko bata da lectures sai ta shiga school, daga school kuma su tafi yawonsu da su Husnah, tun goma na safe idan ta fita gida dama sai magariba take dawowa, sai gashi yanxu wai ita ce daga daki sai bandaki, sannan babu waya ba komai, ita da 24/7 wayarta na hannunta, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tana jin kamar ta samu wanda xai harbe mata khalil ta huta, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a duniyar, why is this happening to her, kuka ta dinga rerawa tana bubbuga kafa. Khalil na isa gida a waje yayi parking Aminu na hangosa ya taso da sauri yana daddaga hannu sama yana washe hakora yace "Sai kayi oga...." Khalil ya kashe motar ya sauko, Aminu ya kyalkyale da dariya yace "Shekaranjiya Saminu ya jiyo mana wannan lamari me ban mamaki daga bakin Hafsah me aiki, yanzu haka aka yi dama?" Khalil yace "Wani lamari kenan?" Aminu ya washe baki yace "Ahh haba ni ne fa Aminu, meye kuma xaka boye min banda abun ka" murmushi khalil yayi yace "Ba abinda xa a boye maka" Aminu ya ja sa har xuwa kan bencinsa yace "Shi kansa bencin nan yasan ba ka a gidan nan mutumina" Khalil ya shafa kai yace "Toh ya ake ciki?" Aminu yace "Ana nan dai yanda ka tafi ka bari in gaya maka, har yanzu kasan Alhaji bai fara fita aiki ba, yanxu haka yana da baki yan zuwa jaje a parlonsa, Ita kuwa uwar Nihad din na can kwance ba lafiya har da karin ruwa don har gida likitan ke xuwa dubata, kanwarta me shegen kama da ita din nan ce ke wajenta yanxu haka, Umma kuma jiya da sassafe ta fita a mota bata dubi halin da abokiyar xamanta ke ciki ba sai ga ta ta dawo mota duk ya lotse wai tayi dan karamin hatsari a hanya amma babu abinda ya sameta, ko kwarzane bata yi ba, xancen da nake maka har yanxu Alhaji bai sani ba, ko mu tace kar mu yi magana, baka ga inda taje tayi parking motar ba don kar ya gani" Khalil dai bai ce komai ba, amma Mumy da aka ce bata da lafiya ce ta tsaya masa a rai, Aminu ya tuntsire da dariya yace "Yanxu don Allah yaya zaman naku da yarinyar nan, ni fa na dauka xa ace ta kashe kanta da taga Alhaji ya aura maka ita, kiyayya ce fa ta gaske take maka" Khalil yace "Ni ban kashe kaina ba sai ita xata kashe kanta?" Dariya sosai Aminu yake yace "Gaskiya kam kai aka cuta, anyi mugun kwararka mutumina, yanxu fa har yara da jikoki sai sun ga wannan videon nata da yayi yawo a yanar gizo, tabo ne da baxai ta6a goguwa ba har karshen rayuwarta, kai don ma dai iyayenka ba yan boko bane basa hawa yanar gizo, ai da wallahi baxa su amince ka auri yarinyar nan ba, ko kai baka kare ma videon kallo bane? Saminu fa har jawo mana shi yayi kusa kusa yanda xa mu gani da kyau, ita wannan ba ma wani amfani ta sake yawo da kaya a jikinta bayan duk duniya sun san surarta" Lkci daya mood din khalil ya sauya, Aminu ya girgiza kai yace "Tirr, amma a gaskiya hada zuri'a da wannan yarinyar ma bala'i ne, banda kana jin nauyin ubanta me xai kai ka? Kai da kake da mutunci haka, Sauran titi ce fa, duk ta yasar da darajan nata ta rarrabar a titi, nan nan nan ranan ni da kai muka ganta da asuba ta dawo daga sheka ayarta tana ta rabe rabe bakin gate, kuma ta sha yin hakan tun ma baka xo gidan nan ba ya fi a kirga, labarinta ma ai sai a bakin Habibu, nasan bai san da wannan hadin ba da ya zuga ka yace kar ka yarda komin me ubanta xai ce maka, shi ma dai Alhajin ya so kansa da yawa, bai kuma yi maka adalci ba, ya rasa warce xai aura mata sai Nihad bayan ga salihar er uwarta Nihal, lalatacciya ce fa babu wanda bai sani ba, ni wallahi da kudi ma baxan amince in aureta ba balle kyauta...." Mikewa Khalil yyi ya nufi cikin gidan, Aminu yace "Auu har mun gama hirar? Ko xaka shiga ka fito?" Khalil na isa balcony ya kira Abba ya sanar masa yana gidan, Abba yace ya basa few minutes yana da baki, Khalil ya amsa masa da to sannan ya xauna saman kujeran dake wajen, har wani sarawa yaji kansa ke yi da maganganun Aminu, yana ta xaune balcony din sai ga Aunty Jamila ta fito xata kwaso kayan shanya da tayi a baya, mikewa yayi , ganinsa tace "Aa kai ne a nan..." Gaisheta yayi, ta amsa tace "Ya gida?" Yace "Alhamdulillah" Tace "Toh ka shiga ciki mana" kawai murmushi yayi bai ce komai ba, tace "Ka karasa Sudais ya kai ka ka duba Mumy kasan bata ji dadi ba" yace "Subhanallah, amma da sauki ko?" Tace "Alhmdlh" yace "Toh Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" tana barin wajen ya shiga parlon kansa a kasa, Sudais na ganinsa ya taho da gudu ya rungumesa yace "Uncle mun daina ganinka" Ya shafa kansa yace "Gani na zo ai, ina fadil?" Yace "Yana wajen Mumynmu bata da lafiya" Khalil yace "Toh kai ni in gaisheta" Har part din Mumy Sudais ya kai sa, yayi sallama bakin kofar parlon, Wata frnd din Mumy ta amsa, shiga parlon yayi kansa a kasa ya nemi saman carpet ya xauna ya gaishesu, duk suka amsa, Mumy dake xaune parlon an cire mata last drip dai kallonsa kawai take, Bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace "Ya jikin Mumy?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah Ibrahim, ya gida?" Ya sauke kansa yace "Lafiya lau, Allah Ubangiji ya kara Lafiya" Tace "Ameen Nagode" Bai kuma cewa komai ba, Hajiya Zara ta mike ta fita daga parlon, bayan few minutes Mumy tace "Kayi hakuri Ibrahim, an cuceka an hadaka aure da warce bata cacanceka ba, nasan baka da yanda xaka yi ne kuma baxa ka iya k'in amsan tayinta da mahaifinta yayi maka ba...." Da sauri yace "Aa Mumy, Allah ne ya tsara haka, kuma muna fatan Allahn yasa hakan shine mafi alkhairi" Hawaye na sauka idon Mumy tace "Ni kam bani da abinda xan ce maka sai dai in baka hakuri akan abinda Alhaji ya maka, sannan ni baxan ce kayi hakuri da Nihad ba, idan kaga baxa ka iya ba ko xaka cutu ina me goya maka bayan ka saketa kawai ta dawo gida...." Cike da karfin hali Khalil yace "In sha Allah baxa ayi haka ba Mumy" Mumy ta share idonta bata kuma cewa komai ba, Wani duniyar tunani khalil ya fada gaba daya jikinsa yayi sanyi, he couldn't even think straight, kiran sallahn magrib da ake ne yasa ya dago kai ya kalli Mumy ya ga kallonsa take, a hankali yace "Xan je masallaci Mumy, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Ibrahim nagode" Tashi yayi a hankali ya fita daga parlon, Umma ya tarar a main parlor ta masa wani kallo sai kuma ta ja tsaki tayi hanyar kitchen, ya bi ta da ido kawai. Bayan an idar da sallan magrib tare suka shigo gidan da Abba har xuwa parlonsa, Khalil ya xauna ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa yace "Ya gidan?" Yace "Alhamdulillah" Abba yace "Ya kamata xuwa gobe ku shirya ka tafi da ita can garinku ta gaida iyayenka, bayan kwana biyu sai ku dawo" Khalil ya ษ—an yi jim, sai kuma ya dago ya kalli Abba yace "Toh in sha Allah Alhaji, Allah ya kai mu goben" Abba yace "Ameen, farooq ya zo min da wani batu jiya amma sai kun dawo dai" Khalil yace "Toh Alhaji, nagode" Abba ya ciro dubu dari ya mika masa yace "Ka yi full tank, sannan kayi ma iyayenka tsaraba da sauran" Khalil ya sa hannu biyu ya amsa yace "Toh Allah ya saka da alkhairi Alhaji" Abba yace "Ameen, Allah ya maka albarka" Khalil ya amsa da "Ameen" a tare suka fito main parlor da Abba, Umma ta fito daga kitchen kenan ganinsa da Abba tace "Aa Ibrahim har xa ka tafi, bari to ga abinci ka kai ma Nihad tunda an gama" Ya kalleta yace "Toh" Komawa kitchen tayi da sauri, Abba dai ya zauna parlon har sannan kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa, dake xuciyarsa kawai yake yana ma Nihad wasu abubuwan as form of punishment amma shi yasan sonta a jininsa yake, but he can't help it, tayi disappointing dinsa sannan ta xubar masa da mutunci a idon duniya, Umma ta cika warmer da abinci, sannan ga wani warmer din daban na kaza ta fito parlor, sai da ta bubbude warmer din tana kallon khalil cike da damuwa tace "Don Allah idan ka je ka lallabata ta ci abincin nan, duk ta rame ta lalace wallahi, Shekaranjiya da naje ma da ya na samu ta ci abincin, yanxu kam ban san halin da take ciki ba baiwar Allah, wa yasani ma ko bata cin komai" Shi dai Abba bai ce komai ba, khalil kuwa banda kallonta babu abinda yake, Abba ya mike yace "Ka jirani Ibrahim" Khalil yace "Toh Abba" Ba a dau lkci ba sai ga shi ya dawo da dubu talatin ya mika ma Khalil yace "Ka siya mata carton din maltina da na madaran gwangwani" Ta gefen ido Umma ke ta kallon Abba, Khalil ya amsa yace "Toh In sha Allah Abba" Abba yace "Sai da safe, Allah ya tsare" Juyawa Umma tayi ta shige kitchen ta tsaya jikin cabinet kamar me nazari. Khalil na isa gida sai da yayi isha a masallacin dake layin sannan ya shiga gida da motar yayi parking, bayan ya kulle gate din ya dawo ya fiddo abincin daga cikin mota ya kai parlor ya sake fitowa ya kai maltina da madara parlon ya ajiye sannan ya kulle gidan, xaunawa yayi saman kujera ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, da yasan haka abubuwa xa su kasance masa da bai yarda ya fara shigowa garin kano ba, where will he even start this amendment from?? Babu warce ta tsaya masa a rai sai Mahaifiyarsa, this seriously isn't going to be easy, Mikewa yayi daga karshe ya nufi dakinsa yana tafiya a hankali, har ya bude kofar sai kuma ya fasa shiga, ya dawo ya bude dakinta, zaune ya ganta a kasa idonta yayi bulu bulu alamar tayi kukan gaske yau, ya tabe baki ya kulle kofar ya koma parlor kawai yayi xamansa, tashi Nihad tayi ta bi bayansa, ta tsaya bayan kujera tana shesshekar kuka..., ya ษ—an daga kai ya kalleta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Da bashi ne?" Wani bakin ciki ya rufeta a fusace tace "Ban sani ba, ka zata kai ka isa ka dinga punishing dina? Waya biyu aka kawo min gidan nan ka salwantar min da su, toh wallahi zaka sha mamakin abinda xai faru idan baka bani wayata ba" Mikewa yayi ya bar mata parlon ya shige dakinsa ya kulle, kuka kawai take kamar ranta xai fita, babban tashin hankalinta shine Aliyu da xai yi ta kiranta ya ji a kashe, yanxu babu ta inda xata yi ta iya kiransa, da ma baya kulle gate ne ko makota ita sai ta shiga don ta kira Aliyu, amma ko daxu da xai fita kulleta yayi ta ciki, ko bin ta kan warmers din abincin dake parlon bata yi ba ta koma daki ta dinga kuka kamar ranta zai fita, har kusan karfe biyun dare Nihad bata yi bacci ba, abun duniya ya taru yayi mata yawa, last week fa warhaka tana baccinta peacefully a saman gadonta, tashi tayi a hankali ta goge idonta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar dakin nata ta fito, taga ya kashe duk wutan gidan, ko ina yayi duhu, tana lalubawa ta tafi hanyar dakinsa ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude ta shiga dakin, nan ma dai ya kashe fitilar, sai da ta fara tattaba socket din dakin cikin duhun ko xata ga karamar wayarsa a jiki taga babu, cikin sanda ta nufi gadon dakin ta durkusa, hannu ta kai xata laluba kan gadon taji hannunta saman broad haired chest dinsa, zaro ido tayi a mugun tsorace xata mike ta gudu ya fixgota ta fado saman gadon daga gefensa, yayi kneeling dai dai inda take har tana jiyo respiration dinsa, yana kallonta cikin duhun kafin yace komai jikinta na rawa tace "Wayyo na shiga uku, wallahi torchlight nake nema xan je in sha ruwa a kitchen...."








*Littafin Nihad dari biyar ne, ki fita hakkina kafin ki karanta min littafi hankalinki kwance*


3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence via๐Ÿ‘‡๐Ÿป




07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: ๐Ÿ’–๐Ÿ’– NIHAAD ๐Ÿ’–๐Ÿ’–


24


Farooq ya daga kai ya kallesa har sannan kuma wayar na hannunsa yana jujjuyawa, karasowa parlon Khalil yayi ya ajiye ruwa da glass din hannunsa, ya ki yarda su hada ido da Farooq yace "Oh kamar fa na makotanmu ne da suka shigo daxu, babu tantama wayar daya daga cikinsu ne, ban ma kula ba sai yanxu...." Farooq dake ta kallonsa ko kiftawa babu kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Now tell me who you are Khalil!!!" Khalil ya ษ—an yi jim, can yace "Ban fahimce ka ba" duk wannan abun ya ki yarda su hada ido da Farooq, mikewa Farooq yayi ya dafa sa yace "Tell me what ur mission is, what is ur intention of coming to stay with us? ka gaya min kai wanene, menene manufar xuwanka gidanmu" Sai a sannan khalil ya daga kai ya kallesa amma bai ce komai ba, Farooq yace "From day one, i know u are not who u claim u are, u lied about ur personality to us, you have a mission definitely, be it revenge, spy, Dss.... And what have u!" Khalil ya girgiza kai a hankali yace "I have no mission Farooq, and my intentions of staying with u people is pure, aiki kawai ya kai ni gidanku, baya ga shi kuma babu wani abinda ya kai ni gidanku...." Farooq na kallonsa keenly yace "I will like to know u more" Khalil ya koma ya zauna, kamar baxai ce komai ba sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "Duk abinda na gaya maka a kaina a baya hakan yake, i am a nobody like i said earlier, i was just opportune to go to school, i was opportune to be a literate, nayi diploma a fce nan kano wanda har yau ban samu aiki ba, bayan wannan komai game da ni na gaya maka a baya, u can even call Habib and confirm" Farooq yace "But meyasa kace iyakarka secondary?" Khalil yace "Ina tsoron kar a ki bani aiki a gidan ne" Farooq dai kallonsa kawai yake as if forcing himself to believe him, Can yace "Wani course din kayi?" Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace "Business Admin" Farooq ya koma ya zauna kamar me naxari, ta gefen ido Khalil ke kallonsa hoping he is fully convinced, Farooq na daga kai Khalil yayi saurin dauke idonsa daga kansa, Farooq ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ohk then, in sha Allah xa mu yi magana da Abba, nasan xai yi iya kokarin ganin ya samar maka aiki dai dai da qualifications dinka" Khalil yace "Toh nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Farooq yace "Ameen" Bayan few minutes Farooq yace "Ina Nihad din?" A hankali Khalil yace "Ban san inda ta tafi ba" Da wani expression Farooq yace "Ban gane baka san inda ta tafi ba, isn't she under ur control now?" Khalil yace "Nayi kokarin hanata fita amma ta ki" Farooq yace "What? Sai kai kuma ka saka mata ido har ta fita?" Khalil dai yayi shiru. Nihad ce ta sauka bakin gate ita da Husnah da tayi ma kawayensu karyan xata je park ta amso sako, nan kuma ta gaya ma Nihad inda xata jira ta su hadu sannan su taho gidan gaba daya, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin motar ya Farooq a waje, Husnah ta zaro ido tace "Toh yanxu ya xa mu yi kenan?" Nihad ta hade rai tace "Toh ba daga makaranta nake ba, shiga kawai za mu yi, ai ba yawo na tafi ba" Husnah tace "Aa, kinsan yayan nan naki ba saiti garesa ba haka kawai inje ya ritsa da ni" Nihad tace "To me xai min? Kawai mu shiga idan ya so sai ki zaga bayan gidan ki nemi waje ki zauna, idan ya tafi xan fito in gaya maki sai ki shigo" Husnah tace "Toh gwara haka dai" A tare suka shiga gidan Nihad ta kulle gate, duk da yanda gabanta ke faduwa hakan bai hanata dakewa ba ta nufi cikin gidan kamar wata boss, Husnah ma dai duk a tsorace take, tayi sauri ta zaga bayan gidan ta nemi waje ta zauna, a hankali Nihad ta murda kofar parlon ta shiga ciki da sallama, ta kara kicin kicin da fuska ta karasa cikin parlon tana kallon yaya Farooq da ya bi ta da ido, ta ษ—an durkusa tace "Yaya ina yini" Mikewa yayi, yayi ball da ita cikin xafin nama, yace "Daga gidan uban wa kike?" Ta fashe da kuka ta mike xata gudu ya fincikota, jikinta na rawa tace "Yaya wallahi makaranta na tafi ba ko ina ba, ka kira makarantar ma ka tambaya" Duk a gigice take don a wajen duka xa a iya ba Farooq A1, Ya kai mata wani wawan mari yace "Uban wa ya baki izinin tafiya makaranta?" Ta rushe da kuka jiki na rawa tace "Wallahi na gaya ma Umma kafin in fita, ita tace in tafi, ka kirata ka tambayeta" Hauri ya kai mata yace "Ke da Umma ce a gidan nan? Ko Umma ke da iko dake yanxu?" hankali tashe tace "Don Allah kayi hakuri yaya baxan kara ba wallahi, kaji har na rantse maka" Shi dai khalil na xaune bai ce komai ba sai kallonsu yake, Har baya Husnah ke jiyo muryar Nihad tana ihun neman agaji, ba shiri ta mike ta nufi gate da gudu tun kan Nihad tace tare su ke, da hannu farooq ya dinga makan Nihad, mari kuwa yayi mata har sau uku, kuka take iya karfinta tana basa hakuri tana cewa baxata kara fita ba, daga karshe yayi ball da ita ta mike tsaye da gudu ta shige dakinta ta sa makulli tana rusa kuka, Farooq yace "Gobe ko nan da gate ki fita in samu labari ki ga yanda xan faffasa maki jiki da belt, munafuka kawai" Ko minti uku bai kara a gidan ba yayi ma Khalil sallama, khalil ya rakasa har mota, farooq na kallonsa da kyau yace "Kar ka kuskura ka raga mata ko na second daya idan tace xata dinga kawo maka raini" Khalil ya ษ—an yi murmushi kawai, Farooq yayi masa sallama ya ja motarsa ya bar layin, juyawa khalil yayi ya koma cikin gidan, ya zauna saman kujera ya dau Iphone dinsa hade da sauke ajiyar zuciya, tashi yayi ya tafi daki ya ajiye wayar, Nihad na jin ya bude kofar dakinsa ta fito da sauri, parlor ta tafi ta tabbatar da gaske yaya farooq ya tafi, sai da ta kara duba takalmansa nan ma taga babu alamar dai ya tafi, share hawayenta tayi ta nufi dakin nasa ta bude hade da turawa da karfi, tana kallonsa cike da rashin mutunci da tsiwa tace "Toh da ka kirasa ka gaya masa sai aka yi yaya? Nace sai me da ka kirasa? Mutuwa ka ga nayi bayan muguntan da yayi min? Kuma ka zata xan fasa fita in tafi makarantana ne ko in tafi duk inda nake so? To wallahi karya kake yaro don ko gobe ma ba a haifi wanda xai hanani xuwa makaranta ba kaji in gaya maka, Kuma da kai da ka kirasa da shi da dokeni Allah ya isa ban yafe maku ba...." Wani tsaki ta ja tana hararansa cike da tsana, ya girgiza kai yace "Akwai lkcn da matsayin tsayawa bakin kofar dakina ma baxa ki samu ba balle ki gwada min halinki na rashin tarbiya... bari kiji ba bakin kofar dakina ba har bangarena ma sai ya haramta gare ki wataran wallahi...." Sai kuma ya mike ya nufeta, sosai gabanta ke faduwa ganin yanda ya daure fuska amma ta dake ta tsaya bakin kofar, ya tsaya dab da ita yace "Kinsan me yasa baxan ke kulaki ba idan kina nuna rashin tarbiyar ki? Saboda ke din ban dauke ki a bakin komai ba, ban dauke ki mace ba, ba kuma kallon mace nake maki ba, kallon yar titi kuma er bariki nake maki, na dai girmama mahaifinki na amshi tayinki da yayi min don shi din mutum ne me daraja da kima a idona, banda haka ko da duk arxikin duniya aka hadani da ke wallahi wallahi baxan aureki ba don ni ba ajinki bane ta ko ina na fi karfin ki...." Nihad ta zaro ido hade da bude baki tana kallonsa, sai kuma ta cakumo kwalarsa cike da tsiwa tace "Ni kake ce ma yar titi kuma er bariki??" Shaketa yayi ya hadeta da kofa ba shiri ta sakesa gabanta na mugun faduwa, ya dinga kallonta fiercely yace "ina me baki shawara da kakkausar murya, Kar ki sake gigin kai hannunki jikina, idan ko kika sake yin wannan kuskuren to xaki sha mamakin abinda xan maki a gidan nan" Yana gama fadin haka ya turata waje ya kulle kofarsa, kiris ya rage ta fadi, tana huci bayan tayi regaining balance dinta tace "Kai din banza zaka bani shawara da kakkausar murya, aa sai dai karyayyen murya, waye kai kuma me kake takama da shi, kuma wallahi ni ba er titi bace don ina da gatana kuma da arxikin iyayena, kai kuma fa? Naga sai kayi tuki kake samun na xubawa a aljihu?" Sai kawai ta fashe da kuka ta shige dakinta ta fada kan gado tana rera kuka, duk Abba ne ya ja mata yau wai driver din gidansu ke kiranta yar titi kuma yar bariki, kuka take kamar ranta xai fita, gaba daya ta mance da wata Husnah, sai da taji ana kiran magrib sannan ta tashi ta goge idonta ta xauna saman gadon, tana jinsa ya fita masallaci, banda muguwar tsanarsa babu abinda ya cika xuciyarta, wallahi ta tsanesa, she hate him with passion, tana jin ya fita masallaci ta mike ta dau mayafinta ta fita xuwa baya wajen Husnah, wayam ta ga wajen, ta juya ta koma ciki, wayarta ta fiddo can kasan jakarta ta hau dialing number Umma, Sai da ya kusa katsewa Umma ta daga, bayan sun gaisa ta fashe da kuka tace "Umma ya farooq ya zo har gida ya zane ni saboda na tafi makaranta wai" Umma ta

Please Login or Register in order to submit comment