Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata yi alfahari da abun nan da ka min Yaya?" Ko rufe baki bata yi ba ya sauke mata tagwayen mari wanda sai da taga stars, ya kuma umarci Sojojin da su zane su idan za su kawo masu taurin kai, Ita dai Hajiya Amina ba abinda tace amma ranta fari kal ta tona ma Hassana asiri, don shekara kusan 17 kenan Hassana ke amfani da ita a gidan, don dai ita ma tana da wayo da sai dai ta tashi a tutar babu, Aunty Hassana ta juya da sauri tana kallon Janar kafin a fita da ita daga parlon tace "Kuma wallahi wallahi Hanan ba er ka bace, bata da gadonka, boka ne yayi mata cikinta don juya ce ita bata haihuwaa...." Sojan ta kwada mata mari ta turata suka fita daga parlon..... Kamar yanda Janar bai yi bacci ba daren ranan nan haka Mami warce ta ma fi sa girgiza da wannan abu da ya faru, da ya tuna abinda Hassana ta fada na karshe sai hankalinsa ya tashi, wai Hanan ba er sa bace, then there is need for a DNA test.... Mami na idar da sallah da asuba Aunty Maryam ta fara kira don bata mance furucinta a jiya da yamma kafin ta tafi airport ba, sai gashi hakan har ya faru, amma bata sameta a waya ba, can ta mike a hankali ta fita daga bangarenta, dakin Aliyu ta fara zuwa don duba kafarsa, amma taga dakin wayam kuma bata ma ga alamar ya kwana a dakin ba, juyawa tayi ta fita ta karasa bangaren Janar, ta samesa zaune saman kujera still pondering, bata taba ganinsa a yanayin nan da yake ciki ba sai many years ago, kana ganinsa kasan abun ya tsaya masa a rai, ta gaishesa cikin sanyin murya, ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ta kwantar da murya tace "Plss kar ka sama kanka damuwa Yallabai, this isn't proper for ur health, sannan ina rokon ka ka dubi albarkacin zumunci ka kyale Hassana, sai kaga Allah ya maka sakayya ta inda baka zato...." Janar ya kalleta da sauri kuma a fusace yace "Amma ina ga baki da hankali ko Fatima??" Mami dai tayi shiru, yace "Then if u have nothing good to say ki bar min parlona kada ki kara bata min rai don Allah" Mami ta sauke ajiyar zuciya bata dai sake cewa komai ba, Khalil ne ya shigo parlon da sallama, shi fa duk abinda ya faru jiya a gidan bai sani ba don yana barin bangaren Aunty Hassana dama gidansu Nadeeyah ya tafi kuma bai dawo ba sai kusan karfe goma saura, Ya zauna saman kujera ya gaida Janar, Janar ya amsa without looking at him, he felt guilty duk abubuwan da ya ma ɗan nasa a baya, Khalil ya gaida Mami ita ma ta amsa, bayan few seconds Janar yace "When are you leaving?" khalil ya daga kai ya kallesa yace "Later in the day in sha Allah" Janar yace "Da matar taka zaka tafi can din?" Khalil ya ɗan yi shiru, he felt unhappy da bazai iya tafiya da ita ba, ya so ace da ita zai yi tafiyar but it's not going to be possible in ba dai daga tafiyar zai yi ba, a hankali yace "Ai bata da passport" Janar yace "Ohk, sai ayi kokari tayi, it's important...." Khalil yace "Is the trip urgent sir?" Janar yace "It is, tun 5 days ago ya kamata" Khalil yace "Ohk" Daga haka ya mike ya basu waje ya fita daga parlon. Karfe takwas Janar ya shirya da escort dinsa suka tafi barikin da aka kai Aunty Hassana da Hajiya Amina, ai ko ya tarar sojojin sun ci ubansu dai dai gwargwado, tun karfe hudun asuba suke tsaye har zuwa yanzu da Janar ya zo, ga tsallen kwadon da suka yi daren jiya na kusan awa biyu, banda azaba babu abinda cinyoyinsu ke masu, ga sauro da zafi a inda aka ajiyesu, duk sun yi duhu kamar basu taɓa shan Ac ba, Janar na kallon Hajiya Amina bayan ya shiga har inda suke ya ajiye mata farin takarda a gabanta, Hajiya Amina taki daukan takardan, yace "Na sake ki, saki daya, biyu, har uku, Hanan kuma zan kai ta ayi DNA test, if i should find out that she isn't my daughter, you are to go with her" Yana gama fadin haka ya juya ya fita ya shigo tare da sojoji murdaddu har biyar yana kallonsu ya nuna masu Aunty Hassana yace "Ku bi duk hanyar da za ku bi sai ta furta maku inda takardun gidajen da take siya da motoci suke" Suka ce "Yes Sir...." Juyawa yayi ya fice daga babban guardroom din.


Inna ce tsaye tsakar parlon tayi mitsi mitsi da ido tana bin duk masu kallon akwatunan kayan Nihad da kallo kada ko tag a nema a rasa cikin kayan, akwatuna 12 ne tsadaddu, 6 iri daya sauran shiddan ma irinsu daya, kayan ciki kuwa sai son barka, Aunty Jamila da kawarta da wata kawar Mumy basu siya mata kayan banza ba, kaya ne na gani na fada masu tsada, matan yayan Abba ne da yan uwa da abokan arziki cike a parlon ana ganin kaya kowa sai sa albarka yake, Umma dai na zaune one sitter sai bin kowa da ido take bata cewa komai, gaba daya tayi bakikirin kamar ba ita ba, ita fa har yanzu gani take zata farka taga duk wannan abun mafarki take, da ko anyi mummunan mafarki in haka ne, amma dae shiru shiru bata ga ta farka ba, gashi duk dare da kyar take rintsawa saboda sai taji kamar an soka mata mashi a zuciyarta, ta dingi juye juye kenan tana numfashi da kyar, Kamila ma na tsaye bayan kujera duk ta rame saboda damuwa, sai bin akwatunan take da kallo, wanda ko rabin kayan ciki ita bata samu ba, Inna na daga hannu tace "Toh a gaskiya idan ba ganin haramun ku ke son yi ma kayan nan ba kuma ae ya isa haka, ganin kaya kusan minti ashirin yanzu kamar wa enda aka ajiye ma kwari, ai yawansu bazae sa ma a gama ganinsu ba don ma ku ji, kai wllh baza ma a sake bude kayan ba koma wa zai zo, iyaka ya ga akwati mu ce masa kayan miliyan goma da dubu goma ne a ciki ya juya yayi tafiyarsa, idan ana yawan bude akwatin ma ai sai su samu matsala mu shiga uku su ce sakwan muka siyo...." Aunty jamila dake kan kujera tace "Gaskiya kam Inna" Inna tace "Toh kun gani, ae ba ayi ma lefe kallon haramun haka, idan anyi saisa saisa sae a tashi kuma" Wata er uwar Mumy dake zaune parlon tace "Toh yanzu yaushe za a kai kayan Hajiya?" Inna tace "Aa wannan sai sanda Ibrahim ya sa mana lokaci, muna isa Habujan dama sai ayi waya da Halilun ya sanar a gida ga fa mu nan zuwa da kaya niki niki, kun ga ai kafin mu karasa sun mana girki irin tasu ko? tunda ance Abujan ma tana da girma" Matar tace "Toh mutane nawa ne za su je kai kayan idan lokacin yayi?" Inna ta kalleta daga sama har kasa, ta sake kallonta da kyau, can dai tace "Sirara ma za a tafi da saboda matsi a cikin mota, dama daga ni sai Jamila da wannan da aurenta ya mutu wato Kamila za mu je, kinga ai duk bamu da jiki, Ita Sumayya an barta ta ji da jinyar goshinta da hannu kar a fama mata a hanya, amma dama ai ba gayya za ayi ba" Matar bata sake cewa komai ba, bude kofar parlon aka yi Nihal ta shigo da trolley dinta, Inna tace "Oyoyo yan makaranta"


Khalil bai ji dadin rashin ganin Nihad ba sanda zai tafi wajen karfe sha daya da rabi na safe, wai Mami tace su tafi su yi gyaran gashi da Mimi, he don't know how to ask Mami wani saloon din suka tafi, don yayi ta kiran layin Nihad din a kashe, Mimi kuma bata picking, sai yayi tunanin ko Mimi bata tafi da wayarta ba, Har ya isa airport mood dinsa was so dull.... Da yammacin ranan sojoji suka shigo da Hassana gidan tana dingishi da kyar, kana ganinta kasan ta ci baƙar azaba hannunsu, dama basu shigo gidan ba sai da suka Sanar ma Janar zuwansu, yana tsaye babban parlor kuma suka shigo, har bangarenta ta kai su suna biye da ita babu rahama a fuskarsu, Janar ya bi bayansu, tsabar yanda hannunta ke ciwo ta kasa daga wani babban akwatinta dake dakin, wani soja ya sauke mata akwatin ta bude lock din ta hau ciro atamfofi kusan kala talatin wanda bata dinka ba, yawancinsu super ne da holland, can kasan akwatin ta ciro wani envelope, sojan ya dauki makeken sarka da dankunnen gwal da zobe sun kusa biyar dake kasan akwatin, Tana zare ido tace "Takardu fa ku ka ce, kuma ga su" Sojan ya fizge envelope din hannunta ya mika ma Janar ya amsa ya bude ya ga takardun gida ne har hudu, Ya mayar cikin envelope din yace "Akwai saura..." Hassana ta fashe da kuka tace "Ni su kenan wllh wllh, ba wani takardan gida..." Wani naushi sojan kusa da ita ya kai mata a baki, Janar ya mika masu envelope din yace "Ku mayar ku kulle akwatin ku fitar min da shi" Suka yi yanda yace, Janar na kallon Hassana yace "Na baki awa daya ki tattara komai naki ku bar min gidana dake da yaranki gaba daya" Ta fashe da matsanancin kuka ta durkusa kasa tace "Yaya ka mance tsakanina da kai ne? Kanwarka ce fa ni, Yanzu duk inda mahaifiyarmu take zata ji dadin wannan walakanci da tijaran da ka min Yaha" Yana kallon sojojin strictly yace "Awa daya za ku jira ta hada komai nata ta bar min gidana ita da yaranta, sannan ku yi alerting sojojin anguwan she is no longer welcome in my house...." Yana gama fadin haka ya juya ya fita, babu bata lokaci Aunty Hassana ta hau hada kaya tana kuka sosai kamar ranta zai fita, ga gwala-gwalan nata ma duk suna akwatin, sai ma sun bude wani zip din za su gansu kaca kaca sun yi na miliyan 40, duka duka account din nata ko dubu dari bakwai bai kai ba, ta ina zata fara???? cikin minti arba'in ta dau iya abinda zata iya dauka a dakinta, ta sa su Sajida ma duk suka hada kayansu suna kuka, sojojin suka tasa keyarsu aka fitar da su daga anguwan gaba daya suka yasar da su bakin titi....








Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via


07087865788






Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰💖 NIHAAD 💖


67




Bayan kwana biyu da tafiyar Khalil aka fara shirye shiryen biki a gidan, kai da ganin irin IV din da aka buga kadai kasan bikin na masu kasar ne, kusan kullum Mami sai ta fita for the wedding preparation, biki ne na gani na fada ake shirin yi, a kwana a tashi dae har bikin ya rage saura sati daya, tuni Noor ta koma gidansu Nadeeyah ta tare a can su ma suna nasu shirin da sauran kawayen Nadeeyah. Yau ma kamar kullum Mimi ta gama shirin tafiya school ta juya tana kallon Nihad da ba ta da wani aiki sai kwanciya all this days a daki, a ko da yaushe kuma zaka ganta babu walwala tare da ita, she look so dull, abincin ma wani lokacin sai Mimi tayi mata da gaske take dan tsakura, all this while kuma duk kiran da Khalil zai yi ma Mimi ta bata waya, sai dai ta amshi wayar amma baxata masa magana ba don Mimi na mika mata wayar take fita daga dakin ta bata space, har ya ma gaji da kiran ya daina, wayarta kuwa dama ta kashe ta ajiye kusan sati biyu kenan, a daddafe ya iya yin kwana sha biyu a Jamus don gaba daya hankalinsa yayi gida ba kuma wajen kowa ba wajen Nihad, rashin maganan da take masa via phone call ya damesa sosai.... Mimi ta ajiye handbag dinta ta zauna gefen gado tana kallonta tace "Nihad me yasa baki maganar makarantarki ne yanzu?" Nihad ta daga kai ta kalleta amma bata ce komai ba, Mimi tace "Soon za ki ji ance exams fa, for almost 2 month now baki shiga lectures ba, kuma naga ma kamar makarantar ne baki so ko??" Nihad dai bata ce mata komai ba, Mimi ta mike ta dau jakarta tace "Sai na dawo, zan bar maki breakfast dinki a parlon Mami ba sai kin je downstairs ba" A hankali Nihad tace "Allah ya tsare" Mimi na fita ɓangaren Mami ta tafi zata sallameta, Mami na kallonta tace "Breakfast din fa?" Tace "Ehh xan yi before leaving" Mami tace "Toh ita fa?" Mimi tace "Idan ta fito zata yi, she is still lying down, zan aiko Bilkisu ta kawo mata nata nan parlon" Kafin Mimi ta tafi ta sa mai aikin Mami ta kawo breakfast din Nihad nan parlon Mami ta ajiye, wajen karfe tara Mami ta fita zuwa wajen wata kawarta warce ita ce tayi assigning lafiyayyun chefs da za su yi girki na bikin, sae kusan karfe sha biyu ta dawo gida bayan an mata calculation din nawa kudin abincin zai kama gaba daya kuma ta tura masu, don tuni Janar ya tura mata a account dinta, Babu kowa gidan yanxu sae ita da su Mimi da Nihad sannan mai aikinta, Hanan kuwa na can gun uwarta, Janar ma yau kwanansa uku da tafiya India for checkup, the house is so empty duk da dama can gidan babu hayaniya, Mami na isa ɓangarenta taga breakfast din Nihad har sannan a ajiye bata shigo ba balle ta dauka, mamaki ne ya cikata ta fita zuwa dakin Mimi, sae da ta kwankwasa kofar dakin sannan ta bude, kwance ta sameta saman gado ba kuma bacci take ba, Nihad na ganin Mami ta mike zaune a hankali, Mami tace "Me yasa baki shigo kinyi breakfast ba?" ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Mami tace "Toh tashi ki fito kiyi...." Nihad tace "Toh" Juyawa Mami tayi ta fita, ta kira Bilkisu ta sa ta fita da Breakfast din tace "Make a new one immediately" Bilkisu ta amsa da ladabi sannan ta dau abincin ta fita... Ba a dau lokaci ba Nihad ta shigo parlon Mami tana jan kafa..., Hijab ne har kasa jikinta, Mami dake zaune parlon tana kallonta tace "Bari ta kawo maki wani yanzu" Nihad tace "Toh" Zata zauna kasa Mami tace "Zauna saman kujeran" Ba musu ta zauna kan kujeran ta jinginar da kanta jiki, Mami dae sai kallonta take, can ta ci gaba da Chatting da sister dinta Hamida da zata taso jibi daga Yemen tare da mahaifiyarsu da kanninta mata biyu, tana sanar mata abinda zata taho mata da shi daga Yemen, Nihad na ta zaune har bacci ya ɗan fara daukarta Bilkisu ta shigo ta ajiye tray din hannunta a kusa da ita sannan ta fita, Mami tace "Shiga bedroom za ki ga carpet karami ki dauko sai ki zauna a kai, zuwa anjima za a kawo na parlon nan dazu aka fitar da wanda ke kasa" Nihad ta mike ta nufi bedroom din Mami, juya mata taga parlon ke yi, tayi baya zata fadi Mami dake kallonta ta mike da sauri, amma tuni har ta kai kasa, Mami ta nufeta da hanzari ta dagota zaune tana kallon ta da mamaki tace "Are you okay?" Kasa cewa komai Nihad tayi don har sanan kanta juya mata yake, Mami ta dagota tsaye tana rike da ita ta kai ta bedroom din dinta, ta taimaka mata ta zauna gefen gadonta tace "Sannu" Ita dai Nihad bata ce komai ba sai sauke numfashi take a hankali, Mami ta juya ta fito parlor, shayi me kauri ta hada mata a mug ruwan zafin ma ba da yawa ta zuba ba tayi diluting da Table water sannan ta koma dakinta, kwance ta gan Nihad gefen gadon idonta a rufe, Mami ta ajiye mug din shayin dake hannnunta ta dagota tace "Tashi ki sha shayin, it's already noon" Nihad ta mike zaune a hankali, Mami ta dau mug din ta mika mata, amsa tayi ta kai baki ta fara shan shayin. Mami ta juya ta fita daga dakin, ko rabin shayin Nihad bata sha ba ta ajiye da sauri tana toshe bakinta, bata san sanda ta zabura ta mike tsaye ba har ta nufi kofa ganin aman ya riga ya taho mata kawai ta dawo ta shige bandakin Mami, nan ta dinga kwarara amai, Mami dake parlor ta mike da sauri ta koma dakin don a bude ta bar kofar shi yasa ta juyo kakarin amanta, bandakin ta shiga ta dafata tana kallonta tace "Sannu" Nihad ta kasa cewa komai, bayan ta wanke bakinta, Mami ta cire mata Hijab din jikinta sannan ta koma dakin da ita ta zaunar da ita gefen gado tana mata sannu, Nihad ta kasa ci gaba da zama kawai ta kwanta gefen gadon, Mami ta koma bandakinta don ta gyara, ko da ta fito bacci ta tadda Nihad take yi, ta fita parlor ta dau wayarta ta kira Dr Rukayya bayan sun gaisa tace mata ta zo gida zata duba mara lafiya. Mami na ta zaune parlonta bayan minti talatin da kiran Dr Rukayya aka bude kofar parlon, ta daga kai tana kallonsa, ya karaso ciki da sallama, ya zauna saman kujera ya cire face Cap dinsa sannan ya gaisheta, Mami ta amsa tace "Ya hanya?" Yace "Alhamdulillah, ya gida" Tace "Lafiya lau" Tace "Dama tafiyar ta sati biyu ce?" Ya ɗan shafa kansa yace "Eh" Mami tace "Ohk" Yace "Naga ba kowa a gidan Mami" Mami tace "Mimi ta tafi makaranta, Noor na gidansu Nadeeyah" a hankali Khalil yace "Ok...." Mami bata sake ce masa komai ba, bayan few seconds yace "What about Hanan?" Mami tace "Washegarin ranan da ka tafi ita ma ta tafi kaduna" Yace "Ohk" Suna ta zaune parlon for almost 5 minutes, bai ce mata komai ba ita ma haka, Wayarta ne ya fara ring tana dubawa taga Dr Rukayya ce, Mami na dagawa ta sanar mata tana compound, Mami tace "Ohk, bari Bilkisu ta karaso ciki da ke" Mami ta katse wayar ta kira Bilkisu, shi dai kallon Mami kawai yake, ya rasa ta ya zai ce mata ina Nihad, don yana shigowa gidan dakin Mimi ya fara nufa amma yaga ba kowa ciki, ya koma visitor room dake bangaren Mami nan ma yaga ba kowa ciki, har Mimin ya kira yaji inda suka je amma tace masa ai ita tana makaranta Nihad kuma na gida ta bar ta, Mami na gama waya da Bilkisu ta ajiye wayar a gefenta, Jinginar da kansa yayi jikin kujera yana ta kallonta, Mami ganin kallon da yake mata tace "Toh sai ka tashi kaje kayi wanka ka nemi abinda zaka ci ka bani waje ko??" A hankali yace "I am okay" Mami tace "Toh ka bani waje za a shigo min da bakuwa yanzu" Cike da karfin hali yace "Mami tare suka fita da Mimi ne?" Mami tace "Wa?" Sai kuma ya kasa cewa komai, Mami tace "Baka da number Mimin ne?" Yayi shiru yana kallonta, bata sake kallon inda yake ba har Bilkisu ta shigo da Dr Rukayya, Khalil ya dinga kallonta, Ta gaida Mami da ladabi, Mami tace "Sannu da zuwa Dr" Dr Rukayya ta kalli Khalil murmushi kwance fuskarta tace "Barka da rana ranka shi dade" Yace "Longest time Dr" Tace "Ai kam ka buya" Mami ta mike tace "Mu je ciki Dr" Dr Rukayya ta bi bayanta zuwa bedroom dinta, Khalil ya bi su da kallo har suka shiga, kasa daurewa yayi ya mike ya bi bayansu, Tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallon Nihad dake bacci saman gadon Mami, Dr Rukayya dake duke dab da ita tana kallonta ta kai hannunta a hankali goshinta to feel her temperature, sosai taji jikinta yayi zafi, Dr Rukayya ta mike tana kallon Mami tace "Tun yaushe ne bata da lafiyan?" Mami tace "I just noticed today, da yake ba bangaren nan take ba tana dakin Mimi ne" Dr Rukayya ta gyada kai tana kallon Nihad da ta bude ido a hankali tana kallonsu, Mami na kallonta tace "Ya jikin?" Kai kawai ta iya gyada mata, Mami tace "Toh ki dubata Dr bari in baku waje" Tana fadin haka ta juya ta bar wajen, Khalil bai bari sun hada ido da Mami ba ya juya da sauri shi ma ya bar bakin kofar dakin, ko da ta shigo parlon bata gansa ba ya koma can first parlor, Dr Rukayya ta duka tana kallon idon Nihad da kyau, ta dago hannunta tana kallon fingers dinta, calmly tace "When last did u see ur period?" Nihad tayi shiru, sai kuma ta buda hannu alamar bata sani ba, Dr Rukayya tace "Akwai abu a bakin ki ne da baki son bude bakin kiyi magana Dear" Nihad ta girgiza kai cike da karfin hali tace "Aa" Dr Rukayya tace "Good, now tell me how you r feeling?" Nihad ta jingina da gadon cikin sanyin murya tace "Ina jin jiri idan na tashi, sannan in na ci abu sai in fara jin amai, i am feeling dizzy..." Shiru tayi daga haka, Dr Rukayya tace "Tun yaushe kika fara jin hakan?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Not too long" Dr Rukayya tace "Good, koma ki kwanta" Nihad ta kwanta a hankali, Dr Rukayya ta juya ta fita daga dakin zuwa parlor, zaune ta tadda Mami ita kadai a parlon, ta zauna saman kujeran dake kusa da Mami tace "Hajiya ina mijinta kuwa?" Mami tace "Shi kika tarar dazu ai da kika shigo" Ta ɗan buda ido da mamaki tace "Wai Dr Khalil?" Mami tace "Eh" Dr Rukayya tace "Maa sha Allah, ashe surkarki ce wallahi da na ganta fara na zata ko yarinyar er uwarki ce, maa sha Allah that's nice, ashe Khalil yayi aure ba labari" Mami dai kawai ta ɗan yi murmushi, Dr Rukayya na dariya tace "Yana matsayin likita amma baxai duba matarsa ba sai an kira mata likita daga waje, ko rudewa yake... Kinsan haka wasu likitocin suke" Mami tace "Toh yanzu dai me ke damunta?" Dr Rukayya na murmushi sosai tace "Congratulations Hajiya, u are going to be a grandmum soon, duk da na so

Please Login or Register in order to submit comment