Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sa a ga alkhairi" Daga haka ta juya ta koma dakinta. Karfe biyu da rabi na ranan Nihal ta shigo dakin Umma, Umma na zaune kan darduma rike da carbi, tun da ta idar da sallahn azahar wajen karfe daya da wani abu take zaune saman darduman take ta jan carbi, da taji hawaye ya zubo idonta sai tayi sauri ta goge, Nihal ta zauna gefen gadonta, Umma na kallonta ganin yanda ta rame tace "Anya baza kije asibiti a maki thorough Checkup ba Nihal? Kin ga yanda kika koma kuwa?" A hankali Nihal tace "Toh ba final exams bane da muka yi Umma" Umma tace "Toh naga ramar tayi yawa ne, and u look pale" Nihal tace "Umma zan je gidan Coursemate dita dake rijiyar zaki, ita zata duba mana result din ni bazan iya ba" Umma tace "Har an saki?" Nihal ta gyada kai a hankali tace "Eh" Umma tace "Toh Allah ya baku sa'a, ya baku nasara ya rabaku da spill over" Nihal tace "Ameen" Umma ta jawo jakarta ta ciro dubu daya daga cikin dubu sha biyar din da Farooq ya bata kafin ya koma aiki, tace "Ki rike wannan a hannu, ai driver ne zai kai ki ko?" Nihal ta gyada mata kai ta amshi kudin sannan ta mata godiya ta mike ta fita daga dakinta sai da ta fara zuwa bangaren Mumy ta sanar mata zata fita sannan ta bar gidan, Raliya Coursemate dinta ce kuma zata girmeta da kusan 4 years amma ko sau daya bata taɓa zuwa gidansu ba sai dai Raliyan ta zo wajenta, duk da dai sai a level 4 ne ma suka saba da ita har ta zo gidansu, bata da wata kawa da take zuwa wajenta a kaf garin kano, yawanci ko yan islamiyyarsu sai dai su zo gida wajenta amma ita kam bata xuwa, Suna isa kofar gidansu Raliya ta kirata a waya tace "Ina kofar gida" Raliya tace "Anya kin gane address din da na tura maki kuwa Nihal?" Nihal tace "Toh ai driver ne ya kawo ni" Raliya tace "Toh gani nan fitowa, Allah ya sa ba wani wajen daban ku ka je ba" Sai ga Raliya ta bude gate din gidansu, Nihal ta sauka daga motar tana kallon drivern tace "Kawai ka tafi idan na gama zan kiraka baba" yace "Toh Hajiya" Daga haka ya ja motar ya bar layin, Raliya ta rungume Nihal cike da farin cikin ganinta tace "Ya naga sai kara ramewa ma kika yi maimakon ki ciko da kika koma gida" Nihal ta mata murmushi kawai, Raliya ta kama hannunta suka shiga cikin gidan nasu, babban gida ne sosai, sai da Raliya ta fara kai ta ta gaida Mum dinta da Stepmom sannan ta tafi dakinta da ita, Nihal ta zauna gefen gadonta, Raliya tace "Kinji result nan da sati biyu za a saki?" A hankali Nihal tace "Allah ya kai mu" Mai aikinsu Raliya ta kawo mata ruwa da small chops, Raliya tace "Naji dadin ganinki wallahi, dama baki taɓa zuwa gidanmu ba sai dai ni in je naku, to yau dai ga ki a gidanmu and i really appreciate it" Nihal tayi murmushi amma bata ce komai ba, Raliya tace "Na gan ki wani iri, ko baki da lafiya ne dai Nihal?" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Nihal, Raliya ta koma gefenta ta zauna da mamaki tace "What's wrong dear?" Bayan few seconds Nihal tayi karfin halin cewa "Ni bani da kawa, and i have no one to confide with, kawai naji na yarda dake Raliya, For two months now.... ban ga period dina ba Raliya" Raliya was shocked ta koma baya ta dinga kallon Nihal tsoro fal idonta, a kaf department dinsu babu mutum da kana ganinsa zaka masa kallon holy somebody kamar Nihal, ita ko magana da maza ma bata yi sai taga dama, sannan bata shigar banza ko da bazata sa hijab ba bazaka taɓa ganinta da karamin gyale ba sai dai babba da zai rufe jikinta, sannan she is one of the loveliest soul da ta taba haduwa da warce bata san walakanci ba, abunta bai rufe mata ido ba sannan ga ta da tausayi, Raliya ta sauka daga kan gadon tana kallon Nihal still shocked tace "Ban gane ba Nihal? What are you trying to say now?" Kuka sosai Nihal take kamar ranta zai fita tace "Kin dai san halina duk da bamu wani dade tare ba Raliya, even male frnds i don't keep, wallahi wallahi wallahi ni ban taɓa zina ba...." Sai kuma ta kasa ci gaba ta hade kai da gadon Raliya tana kuka sosai, cikin rawar murya tace "I wish Allah zai dau rayuwata yanzu, Allah ne shaidata ni ban taɓa zina ba, i was betrayed Raliya, yaudarata aka yi...." Raliya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma don baki ga period ba ai u don't have to conclude u are pregnant wani lokacin period na haka, ko nima last 3 months sai da nayi kusan wata biyu banyi period ba daga baya sai gashi ya zo, do not conclude Nihal" Nihal ta girgiza kai tace "Ni ban taɓa yin haka ba" Raliya ta ma rasa abinda zata ce mata don gaba daya kanta ya kulle, can tace "Abinda zai faru, ki tashi yanzu mu je mu siyo Pt test strip a chemist kiyi amfani da shi don mu tabbatar" Nihal ta goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan murya tace "Toh" Raliya ta dau hijab dinta bayan ta je ta gaya ma Mum dinta za su je siyo abu su dawo ta fita tare da Nihal, ba a chemist din unguwansu ta siya ba sanin halin jama'a, sai da suka bar anguwan kwata kwata sannan suka samu wani chemist suka siya, Raliya ta tare masu ɗan adaidaita ya maida su gida, ba Nihal me test din ba, ita kanta Raliya gabanta faduwa yake sosai, ta dinga addu'a a zuciyarta Allah ya sa negative za su gani, ai ko Nihal na gama dubawa suka ga positive, Raliya was so shock ta zauna gefen gadonta ta kasa cewa komai, kuma bata hana Nihal kukan da take ba kamar zata shide, Raliya ta dinga tunanin wani taimakon zata iya ba Nihal wanda asirinta bazai tonu ba, gashi dai ita kanta ba wai idonta a bude yake ba, tana dai cin life amma gaskiya bata shashanci, wata kawarta warce tasan duniya, duniya ya santa ce ta fado mata, ta kalli Nihal cikin sanyin murya tace "I have this friend Zaliha nasan zata hada mu da Dr da zai cire cikin...." Ko rufe baki Raliya bata yi ba, Nihal ta dago da sauri ta girgiza kai hawaye na sauka idonta cikin rawar murya tace "Bazan cire ba, laifi biyu a lokaci daya Raliya?" Raliya tace "But kin ce yaudaranki aka yi Nihal, koma laifin ne astagfirullah sai dai daya na cire ciki amma ba na zina ba since yaudaranki aka yi" Kuka Nihal sosai take kamar ranta zai fita tace "Baxan cire ba, i can't" Raliya ta zaro ido da mamaki tace "How did u want to face ur parents with this Nihal?? So kike ki sa masu heart attack? Ya kike son mahaifiyarki tayi? Ta yaya zaki fuskanci mahaifinki idan aka gano wannan cikin? Ohh no think about this plss" Kuka kawai Nihal take ta ma rasa abinda zata ce ma Raliya amma ita dai tasan bazata taɓa cire cikin nan ba Allah yayi fushi da ita, cire cikin will be the last thing she will do on earth, Raliya tayi tagumi duk ranta babu dadi, this is so sad, bayan few seconds tace "Since ni dai baza ki dauki shawarata ba, don't you have any other person that u can confide in, ko namiji ko na mace wanda u are close with kiji shawaran da zata baki ko zai baki??" Nihal tayi shiru tana goge idonta tana nazarin who will that person be.....




*Manage this pls, bana jin dadi ina mura*




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah




Ur evidence via 07087865788💖 NIHAAD 💖


70




Tun daga nesa Khalil ke kallonta har ta karaso ta ajiye masa tray din hannunta me dauke da drink da glass cup sannan ta zauna tana danna wayarta, bayan few seconds yace "Nadeeyah" Ta daga ido ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Do u have anything in mind that u are hiding away from me?" Tace "Iike?" Yace "You act strange this days, i don't understand u anymore" Tace "Really?" Yayi shiru yana kallonta, ta karyar da kai tace "I am not acting strange, kawai dai ina baku enough space da ku ke bukata ne da kai da matarka" a hankali yace "But ai kema matata ce to be...." dariya kawai tayi bata ce masa komai ba, sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, yace "Nadeeyah" Ta daga kai ta kallesa, yace "Seriously bana jin dadin abinda kike min, you are making me feel kamar i am wronging u without me knowing" Ita dai kallonsa kawai take, can tayi murmushi tace "Ohk sai yanzu ka gane hakan?" Yayi kasa da murya yace "But how? Ta yaya nake wronging din ki?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta bata dai ce masa komai ba, yace "Don Allah kiyi min magana" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta tace "You should have told me to move on Kjay, da baka ci gaba da ɓata min lokaci ba kana ce min in jira ka, you wasted my time for 4 years, i neva double dated because of u, da kayi aurenka da tun sannan ka gaya min in ci gaba da rayuwata...." Ya dakatar da ita yace "Haba Nadeeyah, why are u saying all this pls, how many times do i have to explain things to you, wallahi wallahi ban je gidansu da niyyar aurenta ba, hasalima ni bn santa in person ba naje gidansu, hadin mahaifinta ne aurenmu and i can't say no to him, kawai Allah ya kaddara aurena da ita ne, i neva bargained for it" Cikin kuka tace "Yanzu ai da son ranka kake zaune da ita, kuma kana sonta fiye da yanda kai kanka kake tunani yanzu, saboda son nata da gudun bacin ranta yasa kayi kamar baka gan ni ba a airport ai" Ya buda baki yana kallonta da mamaki, can ya kwantar da murya yace "Amma fa kinsan ke na fara so Nadeeyah, kuma har a yanzu ina sonki fiye da tunanin ki, babu abinda ya ragu a son da nake maki, don Allah ki cire Nihad a ranki Nadeeyah, you are my first love and u will remain my first love, and kowa yana da matsayinsa a zuciya ta" Ita dai kuka kawai take, ya dafe kansa don shi baya son wannan kukan nata, can ya dago yana kallonta yace "If Nihad is just ur problem now shikenan ke zaki zauna a nan Abuja ita kuma ta zauna either in kaduna or Kano, kinga babu ta inda za ku fara ganin juna, is that okay by u?" Ta goge idonta tana kallonsa, yace "No say something, idan da yanda kike son ayi sai ki gaya min" A hankali tace "I am not to tell u what to do Kjay, and i will neva do that, kawai dai ni nasan i have no bad intention against her, and i am trying my best to be friends with her amma she is taking me for a foe, tun asali dama bata so na, even before i know she is ur wife" Ya girgiza kai da sauri yace "Aa it's not that bata sonki Nadeeyah, kawai dai she is a kind of person da bata sakin jiki lokaci daya da mutum, tana dadewa bata saba da mutum ba, that is just it" Ɗan murmushi Nadeeyah tayi tace "No, ba haka bane, tana min kallon kishiyarta, ni kuma bana mata wannan kallon har cikin raina, duk da we were together before u met her, amma ni ban ji haushinta don ta aureka ba, i have nothing against her" Yace "I will talk to her about that i promise, gradually nasan zata saki jiki da ke in sha Allah" Murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba, yace "Ni nasan baki da matsala Nadeeyah, u are a good girl kamar yanda na san ki a ko da yaushe...." Wayarsa dake ajiye ne ya fara ring, ya dauka yana duba me kiran nasa, ganin Nihal ce ya daga ya kai kunne, ya amsa sallaman da tayi masa jin yanayinta yace "Are you okay?" Daga daya bangaren tace "Alhamdulillah, ya Nihad?" Ya ɗan yi shiru jin kamar her voice is shaking yace "Hope everything is fine Nihal?" Tace "Lafiya lau, ina son zan maka magana ne...." Yace "Oh ok, zan kira ki zuwa dare don bana gida yanzu" jin tayi shiru yace "Hello" Sai kuma tace "Allah ya kai mu, Nagode" Daga haka ta katse wayar, Nadeeyah dai sai kallonsa take, Yace "Hope everything is settled now dear?" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "Can we go out for shopping?"
Karfe shidda na ranan Nihal na kwance dakin Nihad don Umma ta hanata zuwa dakinta yanzu, zazzaɓi ne me karfi ya rufeta, tun dawowarta daga waje Raliya bayan la'asar take kwance dakin nata, da Umma ta shigo ta tambayeta result din makaranta sai ce mata tayi ai ba a saki nasu ba, duk da tana jin zazzabin tun a lokacin amma bata nuna ma Umma ba, kawai ce mata tayi bacci zata yi, Umma ta fita ta bar mata dakin shine take ta kwance, Mumy ce ta shigo dakin ganin tun dazu bata ga ta fito parlor ba, ta cire duvet din da ta kulle jikinta tace "Nihal jikin ne..." Shiru Mumy tayi jin yanda jikinta yayi zafi qau, gashi sae rawan sanyi take, Mumy tace "Ke dae baki jin magana Nihal, tun yaushe ake bin ki aje asibiti kin ki?" Nihal dae bata ce komai ba, Mumy ta dauko mata Hijab dinta tace "Sa mu tafi asibitin yanzu" Lokaci daya hawaye ya kawo Idonta tace "Ban son zuwa asibitin Mumy" Umma ce ta shigo dakin ita ma jin shiru shiru Nihal bata fito ba, Ganin Mumy tsaye kanta ta karasa da sauri tace "Menene, zazzabin ne ya dawo?" Mumy tace "Ehh shi ne nace ta tashi mu je asibiti" Umma ta kwace hijab din Nihal a hannunta ta saka mata ta kamo hannunta tace "Sauko in kai ki asibiti" Mumy dae ta koma gefe tana kallonsu, hawaye kawai Nihal take Umma ta dagata daga kan gadon, da kyar tace "Umma amai nake ji" Umma tace "Kin san yanda Malaria ke maki kika bar sauro suka cije ki a makaranta Nihal" Nihal ta nufi banɗaki da sauri tana ganin jiri, nan ta dinga yunkurin aman amma yaki tahowa don babu abinda ta ci, juyawa Mumy tayi ta fita ta koma bangarenta. Umma ta saka ta gaba suka fita compound, ta kwalo ma Iliya dreba kira ya taho ya bude masu motar bayan sun shiga, yayi hanyar asibiti da su, a hanya Umma ta ciro wayarta a jaka tayi dialing number Abba, yana fara ring taji gabanta ya fadi don tun bayan da ya saketa sai yau tayi dialing number sa, Ba a dau lokaci ba ya daga yace "Ina jin ki" Zuciyarta na bugawa, murya can kasa tace "Dama Nihal ce bata da lafiya mun tafi asibiti yanzu, saboda yanayin jikin nata ban san ko za su ce za a kwantar da ita ba shiyasa nace in kira in gaya maka" Yace "Tun yaushe take rashin lafiyar?" Umma ta gyara zama cikin sanyin murya tace "Tana tayi a tsattsaye wllh, sai yau ne yayi tsanani, tun dai da ta dawo makaranta bata jin dadi gaskiya" Abba yace "Allah ya sauwake, idan kun je asibitin duk abinda ake ciki a gaya min" Umma tace "Toh in sha Allah, nagode" Katse wayar yayi, taji hankalinta ya ɗan kwanta tun bayan da ya saketa, idan ko haka ne ai zata dinga son irin cases din nan su dinga faruwa yanda za su dinga ko da magana ce ta waya da shi, kilan ta hakan sai Allah ya daidaita su ya hakura har ya maida ta.... Har suka isa asibitin Nihal kuka take, tun Umma na tunanin zafin ciwo ne har dai da taga irin kukan da take tace "Ke kukan lafiya kike yi haka kuwa? Meye haka??" Nihal dai bata iya tace komai ba bata kuma fasa kukan da take ba, she wish kafin su shiga asibitin Allah zai dauki ranta kawai, a haka har Umma ta sa ta sauko daga motar tana rike da hannunta suka shiga cikin asibitin, da yake asibitin da suka saba zuwa ne kati kawai Umma ta bada suka biya kudin ganin likita, suna zaune reception wata nurse ta sanar masu turn dinsu ne na ganin Dr, Umma ta mike tana rike da hannun Nihal tace "Kiyi ta yin abu kamar ba mace ba Nihal, ni dai ki kama jiki mu shiga office din" ko rufe baki bata yi ba taga yarinya ta sulale kafin ta kai kasa tayi saurin kamota tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nurses din suka taso da sauri, nan aka yi emergency ward da ita aka tafi kiran likita, Hankalin Umma yayi mugun tashi ta dinga salati tana zaga reception din, Patient din wajen sai cewa suke ta kwantar da hankalinta Allah zai bata lafiya, jakarta da ta bari kan kujera wata mata ta dauka ta kai mata tace "Ana ta kiranki a waya Hajiya" Umma ta amsa da sauri, ta bude jakar ta ciro wayar taga Abba ne ke kiranta, daga kiran tayi ta fashe da kuka tace "Yallabai muna shigowa reception din asibitin ta suma yanzu haka an shiga da ita emergency ward" Abba yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, bari in taho yanzu dama ina hanya" Daga haka ya katse wayar, Umma ta mayar cikin jakan ta zauna tana share hawayen idonta.... Bayan kusan minti arba'in wani likita ya fito yana kallon Umma yace "Hajiya mu je office" Umma ta mike da sauri ta bi bayansa zuwa office dinsa, Zaunawa tayi kujeran dake gaban table dinsa tana kallonsa, ya gama kauda files din table din sannan ya kalleta, hankali tashi tace "Ya jikin nata Dr?" Yace "Alhamdulillah, ina mijinta?" Umma tayi kasake tana kallonsa sai kuma tace "Miji kuma?? Budurwa ce fa Dr, bata yi aure ba, Ni mahaifiyarta ce kuma ni na kawota" Likitan ya dinga kallon Umma, can yace "Kuma er cikinki?" Umma tace "Kwarai kuwa, second to the last born dita ce, ta gama final exams dinta a Ahmadu Bello University ta dawo gida shine take ta zazzabi sama sama, to dama idan sauro ya cije ta gaskiya tana wahala haka, nafi tunanin fita karatun daren da take ne yasa ta kwaso malarian" Likitan ya girgiza kai yace "I am sorry to say Madam, mun gano tana dauke da ciki wata biyu da sati biyu" Still Umma tayi tana kallon bakin likitan kamar yare yake mata ba Hausa ba, Likitan ya girgiza kai ya ajiye mata takardan test din yace "She is 2months 2 weeks pregnant" zumbur Umma ta mike jin pregnant, tana kallonsa bakinta na rawa tana zaro ido kamar zasu tuttulo waje tace "Meye kuma pregnant likita nace maka budurwa ce, ko dai result din wata ka kawo min, meye haka kake gaya min don Allah, bata taba aure ba fa, ta yaya zaka gaya min haka kamar kana shaye shaye?" Ya dau takardan da ya ajiye mata ya mika mata yana kallonta yace "Ga test result din Hajiya" lokaci daya Umma taji wani azababben jiri ya ziyarceta, kan kace me taga office din ya fara juya mata, sai taga ko ina ya koma bakikirin, kafin likitan ya taso ya yo kanta ji kake timmm a kasa ta kara buga goshi dai dai inda bai gama warkewa ba a tiles din office din sai ga jini kamar an buda pampo, Likitan ya fita ya kira nurse biyu... Wani dakin daban aka kwantar da Umma da har bayan minti ashirin bata farfado ba, sai tsarkewa numfashinta yake kamar zai dauke har sai da aka saka mata oxygen, ga wani bandage da aka tula mata a goshi inda ya kara fashewa, likitocin suka ji tausayinta sosai bayan likitan da ya sanar mata Nihal na dauke da ciki ya gaya masu duk yanda aka yi a office dinsa, duk suka dinga Allah wadaran Nihal. Tun shigowar Abba asibitin yake kiran wayar Umma bata dagawa, hakan yasa ya kashe motarsa kawai ya shiga cikin asibitin, bayan sun gaisa da nurses din yace "An kawo wata mara lafiya yanzu, tare da Baabarta suka zo...." Wata nurse da ta ganesa don in dai Nihad bata da lafiya shekarun baya yawanci shi ke kai ta asibiti, kuma duk tunaninta ma Nihad ce aka kawo yanzu, Nurse din sai duk jikinta yayi sanyi tace "Ina zuwa sir" Wajen likitan da yayi attending ma Umma ta tafi ta sanar masa ga mai gidan Umma ya zo, yace tayi masa iso zuwa office dinsa, Nurse din ta kai Abba har office din likitan, Abba ya zauna yana kallon likitan bayan sun gaisa yace "Jikin nata yayi critical ne haka? I need to see her first pls" Likitan yace "It's okay sir, daughter dinka ce ko?" Abba yace "Sure, she is my daughter" Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "I am sorry to say sir, mun gano er ka na dauke da cikin wata biyu da sati biyu" Abba ya dinga kallonsa babu ko kiftawa as if trying to apprehend what he just said, Likitan ya ajiye masa result din yana kallonsa, Abba ya sauke idonsa kasa, the Dr can see tension and shock written all over him, Likitan ya sauke ajiyar zuciya yace "Kar ka daga hankalinka Alhaji, it shall be well in sha Allah, daga hankali da mahaifiyarta tayi ya janyo tayi pass out dazu, yanzu haka ita ma tana kwance ba a kuma jima da cire mata oxygen ba, kuma jininta ya hau, don haka kayi hakuri ka dauki dangana, ka kuma kula da matarka har Allah ya bata lafiyarta, yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba, sae dae a bi su da addu'ar shiriya kawai" Duk wannan abinda yake fada Abba bai ma san me yake cewa ba, Likitan ya mika masa bill din yace "This is the bill sir, in kuma tare kake da dreba yayi kokari ya maida ka gida Alhaji, you need to relax and accept this with good faith" Abba ya mike yace "It's okay, it's okay" Kudi masu yawa ya ciro aljihunsa ya ajiye kan table din likitan ya juya, Maimakon yayi hanyar kofar fita, sai yayi hanyar bandakin likitan, Likitan yace "Ga kofar can Alhaji, don Allah ka kwantar da hankalinka saboda shekarun ka" Da sauri Abba ya nufi kofar fita bai dai ce ma likitan komai ba har ya fita ko rufe office din bai yi ba, likitan ya ga ya bi right maimakon left, Likitan ya girgiza kai with pity, suna samun ire iren cases din nan sosai, but ya za ayi? Sai dai kawai Allah ya kyauta ya shirya yan baya. Wata nurse ce tsaye kan Umma tana duba ko jininta ya dawo dai dai amma taga har yanzu 180 ne, Umma ta bude Idonta da yayi mata nauyi da kyar tana kallon nurse din ta cafko hannunta tana harhade magana tace "Nurse a ina ake cire ciki a garin nan? Ko kuna cirewa a nan??" Nurse din ta girgiza kai tace "Ba a cire ciki a asibitin nan Hajiya" Umma tayi karfin halin mikewa zaune cikin rawan murya tace "Don Allah gaya min inda kika san ana cire ciki, don Allah ba don ni ba, ki rufa min asiri ki gaya min er nan" Nurse din tace "Hajiya ban san asibitin da ake cire ciki ba gaskiya, nima sabuwa ce a nan" Umma ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace, komai ya tabarbare min ni Sumayya, wayyo Allah na" Nurse din dai sai kallonta take, Umma

Please Login or Register in order to submit comment