Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyabe baki tace "Plan din naku yayi aiki...." Mami ta kalleta sai kuma kawai ta tafi part din Khalil, bata gansa a dakinsa ba, ta fito kenan sai ga Mimi ta biyota, Mimi tace "Mami yana part din Abba, he is very sick" Mami tace "Me yake yi a can?" Bata jira abinda Mimi xata ce ba ta nufi bangaren Janar, bude kofar parlon tayi, taga Aliyu a tsaye Janar dake zaga Parlon yana ma Aliyun magana, don shi bai iya tsayuwa waje daya, Ta dinga bin parlon da kallo bata ga Khalil ba, Aliyu yayi kasa da kai yace "Ina yini" Mami tace "Where is Khalil" Wani kallo Janar yayi mata ya ci gaba da gaya ma Aliyu abinda yake gaya masa na zuwa Germany da zai yi akan wani business, Aliyu ya nuna mata inda Khalil yake, ta karasa ta bude kofar da sauri, kwance ta gansa saman gado yana bacci, ga allurai da drugs a kan bedside drawer, sai kuma drip da aka sa masa, har sannan kuma hannunsa daya akwai handcuff, ya bude ido a hankali jin an bude kofar dakin don baccin nasa sama sama ne, ganin Mami sai da gabansa ya fadi, ya mike zaune da sauri kusan a firgice, Mami ta dinga kallonsa kafin ta karasa cikin dakin ta tura kofar tana girgiza kai cike da takaici tace "Wato ni zaka raina ma hankali Khalil? Ni ka maida yar iska tsohuwar banza, ni zaka raina ma wayo kamar kai ka haifeni, ka ban mamaki wallahi, ka ban mamaki, dama kuma tun farko ni ce ban tsaya nayi nazari ba, amma da na tsaya nayi nazari da na gano cewar babu iyayen arziki da za su hada 'yar su da namiji wai ya kai ta karatu, a da ina alfahari da tarbiyan da na maka amma banda yanzu, i can't count on you now, ban taɓa tunanin akwai ranan da zaka saɓa ma Allah ta hanyar zina ba" Khalil ya katseta da sauri yana girgiza kai, zuciyarsa na bugawa yace "Keep on counting on me Mami, i am not a fornicator, ban taɓa ba, kuma baxan fara ba, i am sorry ban san ta yanda zan billo ma lamarin bane, amma Nihad matata ce ta sunna... Da aurenmu na kawota gidan nan, kamar yanda kika fada da ba don aure ba babu abinda zai sa iyayenta su bari in taho masu da yar su daga ni sai ita...." Mami kallonsa take babu ko kiftawa with new shock, lokaci daya ta fashe da matsanancin kukan takaici tana girgiza kai ranta na mata zafi tace "Sai dai in bayan raina zaka zauna da ita a matsayin matarka... amma matukar da raina a doron kasa to wllh babu aure tsakaninka da yarinyar nan, wallahi baza ka zauna da ita ba...." Tura kofar dakin aka yi Mami ta juya da sauri tana share Idonta, Janar na kallon Khalil with the expression of soldiers yace "Wacece matar taka???" Mami ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai tace "Ban taɓa dana sanin haifanka ba sai yau Khalil, kuma ina me tabbatar maka sai dai ka zaɓi ko ni ko yarinyar, baxan taɓa hada zuri'a da ita ba wallahi tallahi, this time around duk abinda ubanka zai maka yayi maka sannan nima ka jiraye nawa hukuncin, sai na nuna maka ni na haifeka ba kai ka haifeni ba" Daga haka ta fice daga dakin, zufa ya dinga keto masa yaji kansa yayi masa mugun nauyi, lokaci daya zazzabinsa ya dawo masa sabo, Janar dake ta kallonsa yace "Wace yarinya kenan take magana a kai??" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Khalil idan Mami tayi masa haka waye kuma zai tsaya masa, yana kallon Abbansa ya kasa cewa komai saboda shock, Abba ya masa tsawa yace "I am talking to somebody" Khalil ya rike kansa with shaky voice yace "A gidan da na zauna a kano suka bani aurenta, ni kuma na amsa saboda sun amsheni a lokacin da aka nuna ba a bukatata a gidanmu, i can't tell them no" Janar na ta kallonsa yace "So now, where is the girl?" Khalil ya kasa dagowa yace "Tana gidana" Janar ya hau safa da marwa a dakin kamar me pareti, can yace "Sai suka ce kuma ka boye mana ko?" Khalil ya dago a hankali yana kallon Abbansa with tears in his eyes, Janar na gyada kai yace "Zaka kai ni har kanon gidan iyayen yarinyar to make confirmation, and if i should find out u are lying sai na karya maka kafa i promise, idan kuma din da gaske matarka ce that's fine...." Daga haka ya juya ya nufi kofa Khalil ya bi sa da kallo zuciyarsa na bugawa.......






Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah




Ur evidence via 07087865788


https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖 NIHAAD 💖


57




*This page is dedicated to my one and Only Deejah me lamurje, she is a sister from another Mother, ina kuma sonta har cikin raina, Allah ya bar xumuncinmu har aljanna*🥰😍
Hajiya Zahrah Me gari naji labarin Najar Jikamshi ya siya maki sabon kasuwar cikin garin dutse, to su kuma yan dutse su yi yaya? Ko da yake ga dai kasuwar Hakimi. 🤔






Khalil na zaune gefenta ya jinginar da kansa jikin gado yana kallonta ko kiftawan kirki bai yi, gaba daya a sanyaye yake kamar ba shi ba, bai taɓa jin haushin kansa irin yau ba, he know she will ever trust him again because he never fulfilled the promise he made to her, he can't tell what came over him that way, he didn't take it easy on her, and all this is making him feel so bad, duk motsin da Nihad zata yi idonsa na kanta, even in sleep she doesn't look alright, baccin karfin hali kawai take, duk tayi laushi saboda wahala, wani mugun tausayinta yake ji har ransa, a karo na farko kuma yaji yana son sanin ta yanda video dinta ya fita, yaji yana son yasan who is behind the leakage of that video of her, da kuma a inda aka yi sa, this he is going to find out by all means.... Bacci take amma restlessly, kana ganinta kasan she is in severe pain, he wish he can help her more than the way he did, but babu wani abinda xai iya mata bayan wanda yayi mata don ko kwayar magani babu a gidan, ji yake dama zai iya mayar da pain din nata zuwa jikinsa, duk ya kagu gari ya waye ya bata full care din da take bukata, ya kamo hannunta a hankali ganin ta kasa kwanciya guri daya sai juye juye take, he is been sitting there for almost an hour now, and bai damu ya zauna a hakan har gari ya waye ba just to keep an eye on her, hannunsa ya kai goshinta yaji temperature dinta is gradually getting so high, hakan da yayi yasa ta bude idonta da suka kumbura a firgice tana kokarin tashi zaune ya kwantar da ita, cikin sanyin murya me cike da damuwa yace "I am only feeling ur temperature" Taki bari su hada ido ta juya kanta tana sauke numfashi a hankali ta kulle idonta, ya duka dai dai kunnenta cikin sanyin murya that is full of remorse yace "I am sorry Nihad, i never meant to hurt you this way.... Don Allah kiyi hakuri.... I was just..." Sai kuma ya kasa ci gaba, he felt so bad because he is making her pass through much pain, ya kife kansa saman gadon ya kasa cewa komai, Ita dai bata bude idonta ba duk da hawayen dake zuba ta gefen idon nata a hakan, bayan few minutes ya dago kansa a hankali yana kallonta da idanuwansa da suka kada, ya ga alamar ta koma baccin, ya kalli agogo da yayi strucking karfe biyu da minti sha biyar, ya sake kallonta yaga baccin take yi, a hankali ya kai hannu ya goge hawayen dake fuskarta sannan ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa, karfin hali kawai yake don ji yake kamar zazzabi na neman rufesa, har ya fita ya dawo ya dau Hijab dinta ya ajiye saman bedsheet din sannan ya juya ya fita daga dakin ya kulle kofar a hankali, nasa dakin ya koma, ya shiga bandaki ya tara ruwan dumi yayi wanka sannan ya fito, a daddafe ya goge jikinsa ya saka Jallabiyarsa sannan ya kwanta ya rufa da duvet feeling feverish, ga wani sanyi da yake ji, yana son tashi ya koma dakin nata to check on her amma ya kasa tashi, lokaci daya zazzabi ya rufesa, yana ta kwance cikin duvet yaji kamar tsayuwar motoci a waje, ya bude fuskarsa wanting to be sure of what he heard, Bai san sanda ya yunkura ya mike ya nufi windown dakin da sauri ya bude curtain din, sosai gabansa ya fadi jin ana taɓa gate din gidan, da hanzari ya shiga parlornsa ya bude kofar balcony dake wajen don ta nan ne kadai zai iya hango kofar gidan da kyau, still yayi yana kallon motocin wa enda yake hangowa a kofar gidan, lokaci daya hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fito ya koma bedroom dinsa ya dau wayarsa zuciyarsa na bugawa, nan ya ga missed calls din Mami ya kusa sha biyar, Ga kuma na Aunty Maryam duk few minutes ago, he was just confused at this stage, gaba daya ya rude, ya koma dakin da Nihad take da sauri, rasa yanda zai yi yayi, ya jingina da bango zuciyarsa na bugawa sosai, da shi kadai ne gidan sai dai su shigo su dau hotonsa da za su gani manne a parlor amma ba dai shi ba, definitely sai ya sami hanyar fita cikin lokaci kankani, he will surely find a way out for himself, but yanzu bazai yi hakan ba ga Nihad, yaji kafafuwansa sun kasa daukansa ya karasa da kyar ya zauna gefen gadon ya rike kansa da yayi masa nauyi sosai, duk wani tunaninsa ya kwance a lokacin, bai kuma sannua zai yi ba, his father really caught him unaware, yana jin suna ta kokarin bude gate din gidan babu kakkautawa, can yayi karfin halin tashi ya tafi dakinsa ya dauko duvet ya fito ya dawo dakin da Nihad take, lulluba mata duvet din yayi a jiki a hankali, don riga ce iya gwiwa da ya sa mata daxu a jikinta, ta bude jajayen idonta da sauri tana kallonsa, yayi kissing goshinta yaji jikinta yayi mugun zafi, ya lumshe idonsa yayi kissing lips dinta a hankali yace "I don't want you to be cold.... I am sorry i made u sick Nihad" Ta rufe idonta don muryarta ma a dashe yake, bata taɓa sanin akwai irin wannan wahalan ba a duniya sai dazu, ya mike a hankali ya fita daga dakin, ya zura wayarsa a aljihu sannan ya sauka downstairs duk da yanda kansa ke juya masa, ya nufi kofar parlor ya bude ya fita, direct gate din ya nufa, ya ɗan tsaya for few seconds, can ya runtse ido lokaci daya ya bude gate din yana kallonsu, Sojoji ne sun kai su goma a bakin gate din, daya daga cikinsu yayi gripping din hannunsa yana kallonsa, Khalil ya hade rai yace "Easy Mr Man, kai ka kamani ko ni na kawo kaina??" Tuni wani ya miko handcuff, shi dai kallonsu kawai yake kirjinsa na sama da kasa, ganin yanda sojan ke kiciniyar saka masa handcuff din kamar wanda yayi sata, Khalil yaki bari ya saka, yana huci yace "Ce maku aka yi nayi sata ku zo ku daureni?" Duk cikinsu babu wanda ya kalli fuskarsa balle su ce masa komai a wajen, har sai da suka makala masa suka yi hanyar mota da shi, wani sojan ya tafi ya kulle gidan Khalil na kallonsa, anyi masa ire iren haka ya fi a kirga don haka ba sabon abu bane wannan a wajensa, kuma yanda Janar ya basu umarni su yi haka suke yi, shi sa duk bakaken maganar da Khalil zai gasa masu basa daga kai su kallesa balle su ce masa komai, don ko dungurinsa Najar bai basu umarni su yi ba, iyaka su saka masa handcuff su kawo masa shi har gida.... (au Janar xan ce wai Najar
😂)
wajejen karfe hudu na asuba suka isa gida da shi, direct Guard room dake cikin compound din suka kai sa suka turasa ciki sannan suka rufe wajen da kwado, leaving him all alone, Khalil ya rike kansa dake sara masa, why didn't he think twice kafin ya shiga gidan, he just forgot who his father is, babban damuwa da tashin hankalinsa yanzu bai wuce Nihad ba, she needs to be taking care of, she needs him by her side, yasan baxata iya yin komai ba, wannan tunanin yasa yaji zazzabinsa ya dawo da karfinsa, har aka yi kiran sallah na biyu ko gyangyadi khalil bai yi ba, ga sauro sai abinda suka manta ne basu masa ba a jikinsa, ko kwanciya mutum bashi da damar yi a guard room din, wajen ne ɗan tsut da shi, ana tada sallan asuba sojoji uku suka zo suka bude karfen Guard room din, fitowa yayi da kyar yana jin kansa na juya masa, ya dafa bango da sauri, ɗan cell ne wajen kafin ainahin guard room din, shi cell din ba laifi yana ɗan da sarari duk da shi din ma dai ba babba bane, a cell din kuma har da bandaki a ciki, yasan dalilin budesa da suka yi bai wuce ya fito yayi alwala a cikin bandakin dake cell din ba yayi sallah, yayi namijin kokari wajen shiga bandakin, ko kafin ya fito ya ga darduma an ajiye masa nan cell din, ya dauka ya shimfida, suna ta tsaye bakin kofa har sai da ya idar da sallah, suka sake maida sa cikin guard room din suka kulle sannan suka kulle cell din ma daga waje, Khalil ya hade kansa da karfen Guard room din, duk da yanayin da yake ciki Nihad ce kawai a ransa, he is so worried because of her, banda ita he don't mind being in the guard room for weeks tunda dai ya saba zama ciki, kuma yanda Abba yasa aka ajiyesa a nan zai iya tafiyarsa ya mance da batunsa har sai randa Allah ya dawo da shi, iyaka a dinga kawo masa abinci da ruwa, for the sake of Nihad yaji zai iya mayar masa duk abinda yayi seizing, duk da zafin da guardroom din shi sanyi yake ji.... Yana nan a haka har wajen karfe takwas ya ji ana bude kofar cell din, ya daga kansa, sojan na gama bude cell din Mami ta shigo ciki tana kallon ɗan guardroom din, Sojan ya karaso ya bude karfen guardroom din... Khalil ya kasa fitowa saboda zazzabin da ya ci karfinsa, Mami ta karasa tana kallonsa, cike da karfin hali ya fito, Mami na ganin yanayinsa taji hankalinta ya tashi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yanzu meye amfanin haka khalil, kaga abinda nake ta gudar maka ka kasa ganewa...." Sai kawai ta fashe da kuka, Da sauri taga ya shiga bandakin cikin cell din wanting to throw up, ta bi bayansa hankalinta a mugun tashe, tana rike da hannunsa suka fito daga bandakin don ya kasa aman, ya zauna nan kasan cell din ya jinginar da kansa jikin bango ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, Mami dai sai hawaye take barin yanda taji jikinsa yayi zafi, it's rare aga yana rashin lafiya shi yasa ma hankalinta ya tashi yanzu, to kiran Abban nasa zata yi tace bashi da lafiya yanzu kenan, tana yin hakan kuma zai ce ita ke supporting dinsa yayi duk abinda yake yi, gaba daya she is confused, ta durkusa gabansa tace "Abinda nake ta gudu kenan, kasan waye Abbanka Khalil, kasan abinda zai iya aikatawa, ban san me yasa zaka shiga gonarsa ba..." Sai kuma ta fashe da kuka, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "I am sorry Mami...." Tace "Ka fada min wani maganin za aje a siyo maka idan kayi breakfast yanzu sai ka sha" Ya girgiza mata kai kawai, tace "You don't look okay, so kake ciwon ya kwantar da kai a nan? Ka gaya min maganin da za a siyo maka in je yanzu a siyo" Yayi kasa da murya yace "I am not sick, i am just worried, i am disturbed, not because ina cikin guard room" Mami na kallonsa tace "What is making you worried then?" Ya kasa hada ido da ita, sai ma sunkuyar da kansa da yayi, da damuwa tace "Talk to me son, meye damuwarka? Ni mahaifiyarka ce kar ka boye min" Lokaci daya idanuwansa suka kada ya dago kai cike da karfin hali yace "Na maku laifi during my stay in kano" Mami ta dinga kallonsa tace "Laifi? Laifin me son?" Ya kamo hannunta gathering all sort of courage, muryarsa na rawa yace "I got married while in kano" da wani expression Mami ta dinga kallonsa kamar me son fahimtar abinda yace, can tace "Ban fahimta ba, menene married?" Ya kasa kallonta with shaky voice yace "I am sorry Mami, Allah ne ya kaddara min haka, but i never bargained for it" Mami ta janye hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tana kallonsa with a weird expression tace "Zazzabin ne yasa kake wannan sumbatun Khalil? Kasan me kake cewa kuwa" Hawaye ta gani idonsa, cike da karfin hali yace "Mami i am in my right senses, i am telling u the fact, kuma tana can gidana yanzu haka" Mami na zare ido tace "Ita wa?" A hankali yace "Matar, kuma sojojin sun kulle gidan, she is inside the house" Mami ta fi minti daya tana kallonsa with shock, shi dai ya kasa hada ido da ita, burinsa kawai aje wajen Nihad a bata kulawar da ya kamata a bata, A hankali Mami ta juya ta nufi kofar cell din, kana ganinta kasan jikinta yayi mugun sanyi and she is speechless, ya bi ta da kallo zuciyarsa na bugawa har ta fita......




*kuyi manage yau ruwa aka yi tayi in gaya maku a kano* 😯




*Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*




Ur evidence via 07087865788




https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114💖 NIHAAD 💖


59




Mami na fitowa bangaren Janar Aunty Hassana ta bi ta da kallo ganin yanda take kuka, can ta kalli Aliyu da shi ma ya bi ta da kallo yana tsaye parlon, Aunty Hassana ta bude hannu murya kasa kasa tace "Lafiya na ganta haka?" Aliyu ya daga kafada yace "I don't know...." Aunty Hassana tayi shiru, can ta mike ta nufi bangaren yayan nata da sauri, A parlonsa ta samesa yana dube duben wasu takardu, ta nemi waje ta zauna da damuwa tace "Yaya lafiya naga Aunty fatima ta fito tana kuka?" Janar ya daga kai ya kalleta yace "Toh me ya hanaki bin ta ki tambayeta? Ko ita ta turo ki ki tambayeni?" Aunty Hassana ta ɗan yi yaƙe tace "Haba ai bata ma tsaya ta saurareni ba, kawai dai i was just worried ganinta da nayi cikin wannan yanayin shi yasa na fara shigowa nan, amma bari in je in sameta" Tana fadin haka ta mike har ta nufi kofa sai kuma ta dawo tace "Ya jikin Khalil din Yaya?" maimakon ya amsa mata sai ya daga wayarsa dake ring wanda wani babban sojan ne ke kiransa, kofa ta nufa ta fita daga parlon duk kanta a daure, to lafiya ta fito tana irin wannan kukan kamar warce uwarta ta mutu, ko dai sakinta yayi? Tunanin hakan ba karamin dadi yayi ma Aunty Hassana ba, da ace bata yaɓa mata magana bane dazu da ta shigo parlon da sai ta bi ta bangaren nata, amma yanzu da kunya ai ta bi ta, kyaɓe baki tayi a ranta tace "In ta yi wari ma ji dai" Daga haka ta tafi bangarenta don Aliyu ma ya bar parlon. Mimi na zaune gefen Mami duk hankalinta a tashe ganin yanda Mamin ke kuka, tace "Ko ma menene don Allah ki daina kukan nan Mami for the sake of ur health" Mami dai ta kasa daina kukan da take, she still can't believe abubuwan da Khalil ya gaya mata, ita in particular zai yi fooling haka? Ita zai yaudara haka ya kawo yarinya for almost 2 months tana gidan sai yau ne zai bude baki yace wai matarsa ce, ta ina hakan zai yiwu? Ai bazai taɓa yiwuwa bane tunda ba film ake acting ba, zata nuna masa ita ta haifesa ba shi ya haifeta ba, Ta jawo wayarta for the 4th time ta kira Aunty Maryam amma bai shiga ba, har ta tashi zata dau mayafi zuwa gidan Hajiya Safeenah sai kuma ta tuna to idan ma taje can din kukan me zata ce mata tana yi? Me zata ce mata ya faru? Ai bata jin zata iya sanar mata da wannan mugun abu da Khalil ya aikata, haba wannan ai abun kunya ne, Mimi ta fashe da kuka tace "Mami na tambayeki me ya faru kin ki gaya min, kuma sai kuka kike, don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki koma menene" Mami ta fashe da sabon kuka tana fatan da ma ace duk wannan abun mafarki ne..... Tun bayan fitar Mami khalil ya kasa komawa ya kwanta, gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, bai ki ya ga fushin Abbansa ba, amma baya wasa da fushin Mami, he strongly detest anything that will make her angry, bai taɓa zaton haka zata dau al'amarin nan da zafi ba, he never expect that from her, he was thinking Abbansa ne idan yaji zai kusan harbesa, sai yaga Abba ma bai dau issue din personal ba, sai Mami da ya dau hope ya daura mata yana ganin ko wani bai goyi bayansa ba ita zata goyi bayansa dari bisa dari, A hankali ya zare drip din hannunsa ya sauka daga saman gadon duk da yanda yake jin jikinsa ya nufi kofa ya fita, Janar ya daga kai yana kallonsa, tunda khalil ya kallesa sau daya ya dauke kai ya nufi kofar fita daga babban parlon, Janar yace "Hey Mr Man, koma ka kwaso drips din da magunguna da ka bar min a dakin...." Khalil ya juya ya koma dakin ya kwaso duk kayan treatment din nasa ya fito, Janar ya bi sa da kallo sai kuma yace "Ita yarinyar da ake magana akai tana ina?" Tsayawa khalil yayi kamar baxai juya ba sai kuma ya juyo yace "Can gidana" Janar yace "Tana ciki aka kulle gidan?" Khalil yayi shiru, Janar ya dau wayarsa zai kira daya daga manyan sojojin dake tare da shi, Khalil yace "Daga gidan Mami take yanzu" Janar yace "Toh wa ya bata izinin zuwa? Sannan wa ya kai ta har ya bude mata gidan?" Shi dai khalil bai ce komai ba, can dai ya juya ya fita daga parlon. Hajiya Amina ce tayi sallama cikin parlon Mami, Mimi tayi saurin tashi don kofar bedroom din a bude yake ta nufi kofa ta fito tace "Ina yini Mama?" Hajiya Amina na kokarin kutsa kai ta shige dakin tace "Lafiya lau ina Hajiyar?" Mami tayi kamar bacci take, hakan bai hana Hajiya Amina karasawa cikin dakin ba, tace "Hajiya rasuwa aka min nace in zo in gaya maki" Babu yanda Mami ta iya haka ta bude idonta ta mike zaune tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wa ya rasu?" Hajiya Amina na kallonta tace "Makociyar kanwata Nana, kinsan muna mutunci da matar, yau ta rasu wajen haihuwa" Mami tace "Allah sarki, Allah ya ji kan musulmi" da mamaki Hajiya Amina tace "Lafiya na ganki haka Hajiya?" Mami tayi yake

Please Login or Register in order to submit comment