Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wata shegiyar miyar kuka wanda warinsa kadai ma ya isa yasa mutum yayi throw up, Nihad ta jinginar da kanta jikin gadon karan wasu hawayen na taruwa idonta, ita kam yau taga ta kanta, miyar kuka da ake yi me dadi da yaji naman kaza ma ba ci take a gida ba balle wannan me offensive smell, ga wani mugun yunwa da take ji, ko furan bata sha ba balle tuwon dawa, khalil kam babu shi babu alamarsa, har kusan Isha'i bata gansa ba wanda wannan ne ya kara daga mata hankali, ko ba komai ta ma dinga ganinsa kawai kilan hankalinta xai kwanta, hakurinta na rashin ganinsa ya kare, tana ganin giftawar tsohuwar ta mike da sauri ta tsaya bakin bukkar cikin sanyin murya tace "Mama ya fita ne? Naga bai dawo ba" Ko rufe baki Nihad bata yi ba sai gashi ya shigo gidan, dattijuwar tace "Toh gashi ma ya dawo" Khalil yace "Sannu Gwaggwo" Gwaggo tace "Yanxu matarka ke Tambayarka" Ya ɗan kalli cikin dakin, Nihad ta hade rai ta koma ta zauna, ya karasa ya shiga ciki ya fito da karamar wayarsa ya haska tuwon dake gabanta yace "Har kin ci tuwon" Cikin rawan murya tace "Ta yaya xan iya cin wannan abun fisabilillah?" Yace "Ta yanda kike cin abinci a gidanku mana, kawai wanke hannu xa ki yi ki fara kai loma" Ta fashe da kuka tace "Wallahi baxan ta6a iya cin wannan abun ba" yace "Ohk, ashe ba yunwa kike ji ba" Ya haska furan nan ma yaga bata sha ba, gyada kai yayi ya juya xai fita, da sauri tace "Don girman Allah ka daina barina ni kadai" Hankalinta a tashe tayi maganar, yace "Me xan maki in na zauna? Yau kuma nine baki son in bar ki ke kadai?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta, ficewarsa yayi daga dakin ta bi sa da kallo hawaye cike idonta, har kusan karfe goma Nihad na xaune inda take sauro duk ya gama yagalgala ta, wata mata ta shigo bukkar da gidan sauro da wani yakunannen zanin gado tace "Can cikin dare xa ku ji sanyi sosai, sai ki rufa da wannan, bari a daura maki gidan sauro don akwai sauro" a hankali Nihad tace "Toh" can gefe matar ta matsar da tuwo da miya da kwaryan fura dake a kulle, ta gama daura net din a saman gadon karan ta fita, Har Nihad ta fara bacci a zaunen da take ba tare da ta damu da sauro ba Khalil ya shigo bukkar, kulle karamin kofar bukkar da yayi ne ya farkar da ita, ya haska ta da torchlight sannan ya haska saman gadon karan yace "Baxa ki shiga ki kwanta ba malama" Cikin rawan murya tace "Wallahi yunwa nake ji" Ya karasa ya dauko kwaryan fura da nonon da ya dama daxu ya ajiye mata, bata da wani option don mugun yunwa take ji, haka ta dau ludayin tana deban furan a hankali tana kaiwa baki, da kyar take hadiyewa saboda kyankyami, tana yin ludayi uku ta matsar daga gabanta ta rufe tana yamutse fuska, shi dai kallonta kawai yake, yace "Shiga net Hajiya" Ta daga kai ta kallesa ta marairaice tace "Kai a ina xaka kwanta?" Ya hade rai yace "Ina ruwanki?" Bata kuma cewa komai ba ta mike ta shiga net din, abinda bata ta6a shiga ba tunda aka haifeta, ji tayi kamar a saman siminti ta kwanta, ta kai hannu ta tattaba wajen, danne dariyarsa kawai yake, can dai ta hakura ta koma ta kwanta a hankali amma sai taji kamar she is going to suffocate inside the mosquito net, xaunawa yayi saman tabarma yana jin babban wayarsa dake aljihunsa na vibrate amma bai ciro ba, wajajen karfe sha biyu ya mike yana haska fuskarta yaga tayi baccin wahala, ya fi minti biyu tsaye kamar me contemplating, can kawai ya dage net din ya shiga ya kwanta ya juya mata baya sannan ya sake net din. Yana jin ta wajajen karfe daya da rabi tana juye juye, don bai yi bacci ba, can ta mike xaune tana lalubasa, hade rai yayi sae dai bai ce mata komai ba, bayan ta tabbatar shi din ne, ta hau tashinsa tace "Don Allah ni ban san inda xan je in yi fitsari ba" A takaice yace "Sai ki fita ki duba ai" Ya dage net din ya sauka don ya bata waje ta fita, ta sauko kasa tana kallonsa cikin duhun tace "Wayyo wallahi ya matseni" Ya kunna fitilar karamar wayarsa ya mike ya bude kofar bukkar ya fita ta bi bayansa da sauri ta dau butar da tagani tsakar gida, yana nuna mata bandakin dake xagaye da kara ta gwalo ido tana lekan ciki tace "A nan din xan yi fitsari?" Banxa yayi mata ya koma gefe ya tsaya, babu yanda ta iya haka ta shige ciki tana toshe hanci, tana fitowa ya koma bukka ta bi bayansa da sauri, ta xauna kasan tabarman dakin hawaye har ya cika idonta tace "Wallahi yunwa nake ji baxan iya bacci hka ba" ledan da ya shigo da shi daxu ya dauka ya ciro bread ya mika mata, ta dinga kallon bread din sai kuma ta amsa ta bude ta jinginar da kanta jikin gadon karan ta fara cin bread din a hankali, bata wani ci da yawa ba haka ta dau ruwan da take kyankyami ta sha kadan, shi dai yana zaune bai ko kallon direction dinta, a sanyaye ta mike ta shiga cikin net din ta koma can karshe ta kwanta, bayan wasu mintuna da shigarta shi ma ya shiga ya saki net din, nan da nan bacci ya kara dauketa, sae kusan karfe biyu da rabi yayi bacci shi ma, kusa da asuba garin yayi sanyi sosai, kamshin da ya ishesa ya sa ya bude ido a hankali, dab da shi ya ganta ta takure waje daya alamar tana jin sanyi, ya kalli gashinta wanda shi ne ya damesa da kamshi, hade rai yayi a hankali ya juya mata baya, ganin tana matsowa ya ɗan juya ya kalleta, bayan few minutes ya daga net din a hankali fuska daure ya sauka kasa, zanin gadon da mata ta kawo mata ya shimfida saman tabarma ya kwanta, bai sake komawa bacci ba har asuba tayi. Zaro ido Nihad da ta farka da safe tayi ganin gari yayi shar, ta kalli gefenta taga baya nan, da sauri ta sauka ta fita tsakar gida, bayan ta dauro alwala ta shigo bukkar ta dau hijab dinta tayi sallah, bayan ta idar ta mike ta koma gefen gadon karan ta zauna abun duniya duk ya dameta, ta kalli uban kayanta bayan ta tuna abinda ya ce mata wai sai ta gama sa su sannan xa su bar kauyen nan, da daddaya da daddaya aka dinga shigowa gaisheta, mata ta farko da ta fara shigowa gaisheta haka ta bude akwati ta bata atamfa riga da skirt, a haka ta dinga rarrabar da kayan nata, ai ko har da makota a shigowa gaisheta, har kayan kwalliya da shafe shafenta bata bari ba, daga karshe ta ba dattijuwar akwati daya, mata biyun dake gidan su ma duk ta basu kyautar akwatuna daddaya, da atamfa kala daya da Hijab ta tsira sai turare shi ma daya da handbag dinta da takalmi sauran duk ta yi sadakansu, ai ko ta sha godiya sannan albarka ta sha shi kwando kwando, wani kunu me ruwa ruwa aka dire mata as breakfast da dumamen tuwon da bata ci jiya ba, Nihad tayi tagumi tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta ya xubo ba, wajen karfe takwas aka kai mata ruwa tayi wanka bayan ta dawo bukkar ta shirya sai ga khalil ya shigo gidan tun daga bakin kofa Dattijuwar ke basa labarin alkhairin da Nihad tayi masu da makota, har da fito da akwatin da Nihad ta bata ta nuna masa, yana shiga bukkar da Nihad take yaga babu kaya ko daya ya kalleta, ita dai kanta na kasa, can yace "Ina kayanki suke?" A takaice tace "Na rabar, ko kai baka ga kayan da suke sa wa bane" Yace "Ohk, ashe xaki yi ta maimaita kaya kenan...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "Toh meye don na masu sadakan kaya, idan haka ne mu koma gida in kwaso wasu kayan sannan mu dawo mana" Yace "Koh?" Tace "Ehh mana" yace "Okay, xamu koma ki debo duk kayan naki sai mu dawo" tana share idonta tace "Na yarda, daga nan ma sai mu taho da ruwan gora da biscuits" Yace "Toh" Daga haka ya fita daga bukkar. Har rana ya fara yi Nihad na ta baza ido bata ga Khalil ba balle su bar garin, da rana aka kawo mata ordinary wake da aka dafa aka xuba masa man gyada ita da bata cin wake, ga shi wani axababben yunwa take ji, haka ta bar masu tsiyarsu, wasa wasa har kusan la'asar ba khalil ba labarinsa, da taga yunwa xai mata illa haka ta daure ta dinga danna fura da nonon da aka dama mata, shiru shiru har magrib, bayan ta idar da sllh ta ci kukanta ta gode Allah, har aka yi isha bata ga Khalil ba har ta daina tambayar dattijuwar dake assuring dinta yanxu xai shigo, bayan tayi sallan isha kawai ta dage net ta shige tana shesshekar kuka ba tare da ta bi ta kan tuwon dawar su ba, can wajajen karfe goma sha daya saura ta dinga jin kamshin turarensa, sai kuma ta ji suna gaisawa da mutanen dake tsakar gida kafin ta shigo, xa a kawo masa abinci yace masu ya koshi, bayan like 10 mins ya dage net ya hau saman gadon ya haskata da karamar wayarsa, duk da tana jin sa bata yarda ta bude idonta ba, kashe fitilan yayi ya kwanta, ta bude ido ta dawo kusa da shi ta fashe da kuka tana shessheka tace "Kai fa kace idan na gama sanye kayan da na kawo za mu tafi gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan canza gobe bani da shi" Yace "Sae ki maimaita na yau" kuka take sosai, ya juya mata baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take. Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi....


*Ki biya dari biyar ki karanta hankalinki kwance er uwa*


NIHAAD is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via👇🏻




07087865788....
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


26


Khalil na ganin number dake saman screen dinsa ya kalleta da sauri, bai san lkcn da ya saketa ba ya shiga call logs dinsa hurriedly to check if tayi sending kiran, Nihad tayi using opportunity din saketan da yayi ta fice daga dakin a guje ta shige nata ta kulle, jingina tayi da kofar tana maida numfashi with surprise written all over her face, why did Aliyu's number appeared on his phone daga fara dialing, how will that be? lokaci daya tayi assuring kanta cewa ai jiya ne ya kwashe number a wayarta bayan ya dauke mata wayar, karasawa tayi ta zauna gefen gado da tunani iri iri a ranta, does it mean bayan ya jefa wayar cikin ruwan cirowa yayi ya busar kenan ya shiga call logs dinta ya dau number Aliyun? Dama kuma da Aliyu da Umma sai su Husnah kadai tayi magana da a sabon wayar, numbobinsu kadai ne a wayar, tsaki ta ja ta mike ta tafi kusa da window ta tsaya, why will she even be stressing her self, takaicinta guda yanxu da bata tsoma wayar tasa cikin ruwa ta fito da sauri ba, yunwan da ya addabeta wajen karfe sha biyu ya sa ta bude kofar dakinta a hankali ta fito parlor, bata gansa a parlon ba ta saci kallon kofar dakinsa sai kuma ta shige kitchen da sauri, ta bayan windown kitchen din ta hangosa xaune saman farin kujera yana waya, kasa kunne tayi amma babu abinda take ji saboda window din kitchen din dake a kulle, idan kuma tace xata bude xata yi drawing attention dinsa, juyawa tayi ta fice daga kitchen din ta nufi kofar fita parlor, cikin sanda ta isa har ta wajen da yake ta tsaya inda baxai hangota ba don backing wajen yayi, kawai tana son tabbatar da cewa da Nihal yake waya kafin ta san irin rashin mutuncin da xata mata sannan kuma ta hadata da Umma, ji tayi yayi kasa da murya yana cewa "Amma Baby me yasa kike tunanin ina Nigeria?? Wani yace maki ya gan ni a Naija ne?" Gwalo ido Nihad tayi ta bude baki tana kallonsa, murmushi taga yayi yace "Ranan da na dawo ai bayan wajen Mamina wajen ki xan taho har sai kince min in tafi, kinga ko abinci ma kadan xan ci na Mami.... Naki ne xan ci in koshi" Nihad dai ta kasa rufe baki sai kallonsa take da mugun mamaki, cikin cool voice dinsa yace "Nasani Nadeeyah.... In sha Allah ina dawowa babu bata lokaci kuma kamar yanda na maki alƙawari xa mu yi aure...." Sai a sannan Nihad tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Yau naga ikon Allah, babba da shirga karya" juyawa yayi da sauri yana kallonta, ta wani hade rai tace "Katon mutumi da kai baka ji kunyar irin wannan karyar da ka zauna kake laftawa ba? Wato ba a Nigeria kake ba, na shiga uku ku ji wai baya Nigeria, to a wani kasar kake? ko da yake ita ce babban mahaukaciyar da ta tsaya take sauraronka har kake fesa mata wannan mugun karya haka..." Tuni khalil ya katse wayar ya mike yana mata wani kallo yace "Kar ki sake kiranta da mahaukaciya" A fusace Nihad tace "Ance mata mahaukaciyar me xaka yi? idan waya xaka yi da ita ka fita titi kayi mana ai dai naga nan gidan Ubana ne ko? Ko Abbana ce maka yayi ka zo ka dinga masa waya da mata a gidansa?" Khalil yace "Zaki gane ke ce mahaukaciya ba ita ba" Cike da tsiwa tace "Sai dai ku ne mahaukata ba ni ba wallahi, kuma kar ka sake kiran wata banzan mace a gidan Abbana" Bai kuma ce mata komai ba ya gyada kai kawai ya bar wajen, ta bi sa da wani harara, sai kuma ta ja tsaki tace "Wai baya Nigeria, kai har kana da kudin fita nan nan Niger ma balle wata kasar?? Ai har ka mutu ko kamshin airport baxa ka ta6a ji ba don ma kaji in gaya maka" Shi dai tuni ya bar wajen don Nadeeyah na ta kiransa a waya, Bin bayansa Nihad tayi tace "Dama idan waya xaka yi ka fita can titi kaje kayi ba dai a gidan Abbana ba na gaya maka" kafin ma ta shigo parlorn har ya shiga dakinsa ya kulle da makulli, ta ja tsaki tace "Aikin banza" kitchen ta tafi ta dafa indomie, tana kitchen din taji ana kwankwasa gate, ta ɗan leka parlor sai gashi ya fito daga dakinsa ya fita compound, kashe gas din tayi da sauri ta fito daga kitchen din ta shige dakinsa, gun wayarsa dake saman gado ta nufa, sbda tsoro har wani rawa hannnunta yake ta dau wayar ta shiga call log don taga da warce yake waya har yake karyan ba a Nigeria yake ba, Nadeeyah ta gani, mamaki ne ya cika ta don ai tayi blocking number jiya, ai ko yau sai ta tona masa asiri ba dai baya Nigeria ba, xai ga aiki da cikawa yanxun nan, dialing number tayi har ya gama ring ba a daga ba, ta sake kira nan ma yana ta ringing no response... Khalil na isa gate din ya bude, Husnah ce tsaye bakin gate din tana sanye da Hijab har kasa, ta ɗan yi murmushi tana kallonsa tace "Ina yini?" Babu yabo babu fallasa yace "Daga ina kuma wa kike nema?" Tana Murmushi still tace "Ba lallai dama ka nuna ka gane ni ba duk da nasan ka gane ni, dama ba wani abu ya kawo ni nan ba illa in baka hakuri akan abinda muka maka shekaranjiya ni da kawayena, tun ranan wallahi ban samu nutsuwa ba sabda walakanta d'an Adam ba shi daga cikin halina, ba tarbiyar gidanmu bane, ni ban ta6a ba sai ranan, kuma mun yi hakan ne kawai don mu faranta ma kawar mu kamar yanda ta bukaci mu yi, daga baya na gane bamu kyauta ba biye mata da muka yi muka ci maka mutunci.... Nayi magana da sauran kawayena mu zo mu baka hakuri ko ba tare da sanin Nihad din ba amma sun nuna baxa su iya xuwa ba shine ni na taso da kaina in zo har nan in baka hakuri, don girman Allah kayi hakuri ka yafe mana gaba daya, ko a jiya ma da ta fito xuwa makaranta idan ka lura ai da wuri ta dawo, to mu muka sa ta gaba muna nuna mata illan kin yi ma miji biyayya ko da kuwa baka son shi, dalilin barin ta makaranta kenan da wuri ta dawo gida, yanxu haka bata san xan xo nan ba, kawai kaina tsaye na taho...." Khalil yace "A takaice dai me ya kawo ki nan Malama?" Ta sauke idonta a hankali tace "In baka hakurin abinda muka yi maka ni da kawayena, kuma mu nemi gafararka" Yace "Toh rike hakurin ki, su ma ki mayar masu da nasu, don ba ku kai ku min abinda xai bata min rai har ki xo bani hakuri ba" Ta daga kai ta kallesa tace "Baka dai hakuran ba kenan?" Da wani expression yace "Shine nace kun min wani abu ne da ya bata min rai har xa ki zo bani hakuri tukunna?" Ta langwabar da kai tace "By the way, sunana Asma'u, amma kawayena na kirana da Husnah...." Ko rufe baki bata yi ba ya kulle gate din almost on her face ya juya ya koma cikin gida. Yana shiga daki ya dau wayarsa dake ring ganin Nadeeyah ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren tace "I saw ur calls" Ya d'an yi shiru, da mamaki yace "My calls?" Tace "Yea, minutes ago" Yace "Ohh, sorry mistake ne" Tace "Ohk, sai anjima kenan?" Yace "Sure" Katse wayar tayi, ya hau duba call logs dinsa da sauri, Nadeeyah kawai ya ga ta kira, ya kalli kofar dakin ko kiftawa baya yi. Da yamma Khalil ya shirya xai tafi can gida saboda kiransa da Abba yayi, Nihad dai na daki abun duniya duk ya bi ya isheta, da ta gaji da wannan bangaren gadon ta koma daya bangaren, ko kuma ta sauka kasa ta zauna, ita bata saba xama waje daya kamar jaririya ba, all through the week ko bata da lectures sai ta shiga school, daga school kuma su tafi yawonsu da su Husnah, tun goma na safe idan ta fita gida dama sai magariba take dawowa, sai gashi yanxu wai ita ce daga daki sai bandaki, sannan babu waya ba komai, ita da 24/7 wayarta na hannunta, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tana jin kamar ta samu wanda xai harbe mata khalil ta huta, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a duniyar, why is this happening to her, kuka ta dinga rerawa tana bubbuga kafa. Khalil na isa gida a waje yayi parking Aminu na hangosa ya taso da sauri yana daddaga hannu sama yana washe hakora yace "Sai kayi oga...." Khalil ya kashe motar ya sauko, Aminu ya kyalkyale da dariya yace "Shekaranjiya Saminu ya jiyo mana wannan lamari me ban mamaki daga bakin Hafsah me aiki, yanzu haka aka yi dama?" Khalil yace "Wani lamari kenan?" Aminu ya washe baki yace "Ahh haba ni ne fa Aminu, meye kuma xaka boye min banda abun ka" murmushi khalil yayi yace "Ba abinda xa a boye maka" Aminu ya ja sa har xuwa kan bencinsa yace "Shi kansa bencin nan yasan ba ka a gidan nan mutumina" Khalil ya shafa kai yace "Toh ya ake ciki?" Aminu yace "Ana nan dai yanda ka tafi ka bari in gaya maka, har yanzu kasan Alhaji bai fara fita aiki ba, yanxu haka yana da baki yan zuwa jaje a parlonsa, Ita kuwa uwar Nihad din na can kwance ba lafiya har da karin ruwa don har gida likitan ke xuwa dubata, kanwarta me shegen kama da ita din nan ce ke wajenta yanxu haka, Umma kuma jiya da sassafe ta fita a mota bata dubi halin da abokiyar xamanta ke ciki ba sai ga ta ta dawo mota duk ya lotse wai tayi dan karamin hatsari a hanya amma babu abinda ya sameta, ko kwarzane bata yi ba, xancen da nake maka har yanxu Alhaji bai sani ba, ko mu tace kar mu yi magana, baka ga inda taje tayi parking motar ba don kar ya gani" Khalil dai bai ce komai ba, amma Mumy da aka ce bata da lafiya ce ta tsaya masa a rai, Aminu ya tuntsire da dariya yace "Yanxu don Allah yaya zaman naku da yarinyar nan, ni fa na dauka xa ace ta kashe kanta da taga Alhaji ya aura maka ita, kiyayya ce fa ta gaske take maka" Khalil yace "Ni ban kashe kaina ba sai ita xata kashe kanta?" Dariya sosai Aminu yake yace "Gaskiya kam kai aka cuta, anyi mugun kwararka mutumina, yanxu fa har yara da jikoki sai sun ga wannan videon nata da yayi yawo a yanar gizo, tabo ne da baxai ta6a goguwa ba har karshen rayuwarta, kai don ma dai iyayenka ba yan boko bane basa hawa yanar gizo, ai da wallahi baxa su amince ka auri yarinyar nan ba, ko kai baka kare ma videon kallo bane? Saminu fa har jawo mana shi yayi kusa kusa yanda xa mu gani da kyau, ita wannan ba ma wani amfani ta sake yawo da kaya a jikinta bayan duk duniya sun san surarta" Lkci daya mood din khalil ya sauya, Aminu ya girgiza kai yace "Tirr, amma a gaskiya hada zuri'a da wannan yarinyar ma bala'i ne, banda kana jin nauyin ubanta me xai kai ka? Kai da kake da mutunci haka, Sauran titi ce fa, duk ta yasar da darajan nata ta rarrabar a titi, nan nan nan ranan ni da kai muka ganta da asuba ta dawo daga sheka ayarta tana ta rabe rabe bakin gate, kuma ta sha yin hakan tun ma baka xo gidan nan ba ya fi a kirga, labarinta ma ai sai a bakin Habibu, nasan bai san da wannan hadin ba da ya zuga ka yace kar ka yarda komin me ubanta xai ce maka, shi ma dai Alhajin ya so kansa da yawa, bai kuma yi maka adalci ba, ya rasa warce xai aura mata sai Nihad bayan ga salihar er uwarta Nihal, lalatacciya ce fa babu wanda bai sani ba, ni wallahi da kudi ma baxan amince in aureta ba balle kyauta...." Mikewa Khalil yyi ya nufi cikin gidan, Aminu yace "Auu har mun gama hirar? Ko xaka shiga ka fito?" Khalil na isa balcony ya kira Abba ya sanar masa yana gidan, Abba yace ya basa few minutes yana da baki, Khalil ya amsa masa da to sannan ya xauna saman kujeran dake wajen, har wani sarawa yaji kansa ke yi da maganganun Aminu, yana ta xaune balcony din sai ga Aunty Jamila ta fito xata kwaso kayan shanya da tayi a baya, mikewa yayi , ganinsa tace "Aa kai ne a nan..." Gaisheta yayi, ta amsa tace "Ya gida?" Yace "Alhamdulillah" Tace "Toh ka shiga ciki mana" kawai murmushi yayi bai ce komai ba, tace "Ka karasa Sudais ya kai ka ka duba Mumy kasan bata ji dadi ba" yace "Subhanallah, amma da sauki ko?" Tace "Alhmdlh" yace "Toh Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" tana barin wajen ya shiga parlon kansa a kasa, Sudais na ganinsa ya taho da gudu ya rungumesa yace "Uncle mun daina

Please Login or Register in order to submit comment