Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai anyi test kafin in sanar maki but duk wani symptoms na ciki na gani a jikinta, ur in-law is pregnant" Mami ta dinga kallonta ko kiftawa babu, can ta sauke idonta a hankali tace "Toh Alhamdulillah" Dr Rukayya tace "Yanzu zan dauko Pt test strip a motata, don dake tabbatar da hakan" Mami tace "Toh" Daga haka ta nufi kofa ta fita, ba a wani dau lokaci ba sai ga ta da Urine specimen container da pt test stip, ta shiga dakin Mami ta gaya ma Nihad yanda zata yi amfani da shi sannan ta kama hannunta zuwa bandakin don ta kasa tsayawa sbda jiri, Dr Rukayya na ta jiranta a dakin bayan minti shidda ta bi ta zuwa cikin bandakin, murmushi tayi ganin test din was positive, bayan sun fito ta fita tayi discarding strip din da container, ta dawo parlor ta sake congratulating Mami da ke zaune looking speechless. Bayan fitar Dr Rukayya ta siyo drugs da alluran da zata ma Nihad, Mami dai na ta zaune parlor ta kasa ma shiga ciki ta duba Nihad din, can dai ta mike daga karshe ta shiga cikin dakin.... After Zuhur Khalil ya sake dawowa bangaren Mami, zuwa lokacin Dr Rukayya tayi ma Nihad duk abinda ya kamata ta wuce, Babu kowa cikin parlon amma ya kasa karasawa cikin bedroom din don bai san ko Mami na ciki ba, ya tsaya for almost 2 minutes contemplating kafin ya karasa ya tura kofar a hankali, Nihad ce kawai kwance dakin tana bacci restlessly, ya sauke wani ajiyar zuciya ganin Mami bata ciki ya karasa da sauri, ya zauna gefen gadon ya kai hannu forehead dinta yana kare mata kallo keenly, he sat there looking at her for almost 2 minutes, sai kuma yayi wani murmushi dai dai nan ta bude ido a hankali don baccin yin sa kawai take don dole, All her body is just weak, gashi ko tunanin abinci tayi sai taji zuciyarta na tashi amai na taho mata, Daure fuska tayi ganinsa, yayi kasa da murya yace "How are you feeling?" Ta kara hade rai zata juya masa baya ya dagota zaune, yayi kasa da murya cike da damuwa yace "To me na maki kike ignoring magana da ni for two weeks now?" A fusace tace "Ni ka kyaleni don Allah" Yace "Ki gaya min laifin me nayi?" Tace "Toh ai ba dole sai da ni kawai zaka yi waya ba tunda kana da warce ita ma zaka iya waya da ita" Kallonta yake yi da mamaki, ta fizge hannunta zata juya masa baya ya jawota ya rungumeta jikinsa yace "But ai ke kadai ce matata, ko da wacece zanyi waya ai ba matata bace tunda ba aure tsakaninmu" A hankali ta sakar masa kuka ya lumshe ido thinking of what to say to her don sarai ya gama gano ta, dai dai nan aka bude kofar dakin kafin yayi saurin saketa har Mami ta shigo, Nihad taji kamar kasa ya bude ta shige kawai ta huta, Ya mike da sauri ya kasa dago kai balle su hada ido da Mami, sai kuma ya nufi kofa, Mami ta bi sa da wani kalloz a takaice tace "Go back and take her to ur room" Tana fada masa haka ta juya ta bar dakin, sai a sannan ya dago kansa yana sosa keya, can kuma ya koma wajen Nihad yace "Tashi mu tafi" Wani kallo tayi masa tace "Wallahi baxan je ba ai ni ba fitsararriya bace" Ya wara ido yace "Ni ne fitsararre?" Komawa tayi ta kwanta ta juya masa baya, yayi murmushi ya juya ya fita daga dakin. Sanin Mami is watching his move ya sa ya shirya bayan la'asar ya tafi gidansu Nadeeyah... Yana ta zaune compound din gidan sai ga ta ta fito, shi dai ya ma rasa gane kanta for almost 3 weeks now, ta zauna saman kujera without looking at him tace "Ina wuni" yayi shiru yana kallonta, ta daga kai ta kallesa jin bai amsa gaisuwarta ba, yayi kasa da murya yace "Now tell me ur problem pls Nadeeyah, is it Nihad? In dai ita ce u need not to bother plss ba gida daya zaku zauna ba, sai ma ku yi wata da watanni baku ga juna ba i am assuring you, pls ina son ki kwantar da hankali ki daina duk wani kokwanto a ranki, kuma ki sa a ranki i owe u a lot saboda halaccin da kika min" Nadeeyah tace "And this is the fifth time u are saying this to my ears, komai kace saboda halaccin da na maka ba, ko kuma kace baza ka karya alkawarin auren da ka min ba... so what i want u to make me understand now is that saboda abun da kake ganin na maka ne kake so ka aureni so that it wont be like baka min adalci ba, ko kuma saboda alkawarin da kake ikirarin ka min na aure shine zai sa ka aureni don ka zamo me cika alkawari or whatt?" Khalil yayi shiru yana kallonta babu ko kiftawa, tayi wani murmushi tce "No talk to me" Yace "Why are you complicating issues Nadeeyah? Me yasa zaki yi wannan tunanin?" Ta girgiza kai tace "You are the one complicating issues Kjay, bana mantawa kwanakin baya na tambayeka me ya kai ka gidansu Nihad driving, a ina kasan su har kaje gidansu, but u told me that should be a story for another day, kaga sai yanzu na fahimci cewar saboda ita kaje gidansu ka nemi driving don ka zauna a gidan har ka aureta" Khalil ya zaro ido yana kallonta yace "Billah ban taɓa ganinta ba sae da naje gidan, kin ji na rantse, kuma Nadeeyah na gaya maki times without number mahaifinta ne ya hada aurena da ita, wllh at first bata san ni aka aura mata ba mw" Nadeeyah ta mike tace "My frnds are waiting for me inside kuma wucewa suke son za su yi" yayi shiru yana kallonta, can yace "Ohk sae mun yi waya, ki gaida Mumy" Daga haka ya mike ya nufi motarsa ita kuma tayi wucewarta cikin gidan.


Inna ce zaune saman kujera a dakin Umma, ga Umman kwance saman gado ana kara mata ruwa sai nishi take Kamila da Nihal na zaune gefenta, Zaune a dakin Mumy ce da matan yayan Abba duk sun zo duba Umma, Hajiya Turai ma na zaune daga bakin kofar dakin, Inna tace "Toh ni dai bamu san kan ciwon Sumayya ba gaskiya, abu kamar wasa karamar magana ya zama babba, daga fasa goshi da targade a hannu, anya ba aljanu suka shafeta ba kuwa" Babu me cewa komai dai a dakin, sallama aka yi can parlor Inna tace "Kuma masu shigowa dubiyan nan ma ya kamata a hanasu haka don ba a san zuciyar wani ba, banda haka ciwo yaki ci yaki cinyewa, ta ina zamu kama hanyar kai akwati hankali ba a kwance ba, kila ma har sun gaji da jira a can Habujan kada ma suyi tunanin cinye kudin aka yi" Husnah ce ta makale jikin kofar dakin ganin mutane da yawa zaune ciki sai wuwwurga ido take, lokaci daya kuma tana sosa gabanta daga cikin Hijabin jikinta, gaba daya tayi wani zuru zuru da ita kamar ba Husnah ba, Hajiya Turai ta yamutsa fuska jin wani axababben doyi da ya bugi hancinta, Inna ta toshe hanci da gyalenta a gigice tace "Wacece wannan kuma? Ba haya tayi a wando ko me?" Husnah ta ɗan durkusa tana in ina tace "Aa wajen Umma na zo dama... Umma nake nema" Umma dake fama da kanta ta ɗan bude ido daya tana kallon Husnah, Inna na kara toshe hancinta a gigice tace "Wacece Umma, me zata maki?" Husnah ta fashe da kuka tace "Ni dai dama inda zan samu Nihad nake nema, ko ta waya ne don Allah" Inna ta mike da sauri ta koma can kofar bandaki tace "Wai wannan doyin meye haka yake gigita ni...." Mumy na kallon Husnah jin abinda tace, tace "Me Nihad din zata maki kike nemanta?" Umma ta mike zaune da sauri ba tare da ta shirya ba tace "Ke ya zaki fado ma mutane daki haka kai tsaye?? Daga ina haka?"








Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788








Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰💖 NIHAAD 💖


68




Inna bata ba Husnah chance din magana ba ta daka mata wani tsawa tana kara toshe hanci tace "Don Allah ki fita ki bamu waje, wacece kuma Nihad, Nihad da ke gidan mijinta ɗan Janar Jikamshi, meye hadinki da ita" Umma da zuciyarta ke bugawa sosai tace "Turai don Allah ki fitar mana da ita zuciyata tashi take...." Husnah ta marairaice tace "Ko number...." Hajiya Turai ta mike da sauri cikin daga murya tace "Fita ki bamu waje, fita" Juyawa Husnah tayi da sauri ta bar bakin kofar ganin Turai ta yo kanta gata jibgegegiyar gaske, Nihal ta bi Husnah da kallon mamaki, Umma ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ta koma da kyar ta kwanta har sannan gabanta na faduwa, Inna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Da kyar idan ba wani cutar bane ya kamata, amma wannan doyin gaskiya ba na lafiya bane, a bude mana window a kara Ac...." Mumy ta ji kamar ta bi bayan Husnah taji neman me take ma Nihad, tana ta nazarin maganan nata amma ta kasa tashi sai kallon kofar dakin take. Ana idar da magrib Mami ta shiga dakinta, tun yamma take da baƙi a gidan basu tafi ba sai dab da magariba, tana kallon Nihad dake kwance saman darduma tace "Me yasa kika kwanta a kasa?" Cike da karfin hali tace "Sallah nayi" Mami tace "Toh koma saman gadon" Nihad ta mike ta kwanta kan gadon, tun dazu zazzabin ya dawo mata sosai amma a haka ta daure ta tashi tayi sallah, Mami ta dauke darduman ta ajiye inda yake sannan tace "Me kike son za ki ci yanzu?" Nihad ta girgiza mata kai kawai, Mami ta kashe Ac din dakin ganin kamar sanyi take ji, sannan tace "A kawo maki Custard za ki sha?" Nan ma Nihad ta girgiza mata kai kawai, Mami ta juya ta bar dakin, Bilkisu ta kira ta sa ta dama Custard din, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta shigo da shi a cup Mami ta amsa ta kai cikin dakinta tana kallon Nihad ta ajiye Cup din a kasa tace "Bari ya ɗan huce sai ki tashi ki sha" Daga haka ta tafi ta gyara curtains din dakin sannan ta rage hasken wutan ta fita.... Bayan minti goma Mami ta sake komawa dakin, ganinta still a kwance tace "Ai ya huce haka, tashi ki dauka ki sha" Nihad ta mike zaune, Mami ta dau cup din custard din ta mika mata, amsa tayi amma tana kallon cikin cup din taji zuciyarta ya fara tashi, ta kauda kai tace "Bazan iya sha ba" Mami tace "Toh me za ki ci?" Shiru tayi bata ce komai ba, Mami tace "A kawo shayi?" Nan ma dai girgiza kai tayi, Mami tace "Kin dai san baza ki kwanta da yunwa ba ko? Think of anything you want to take ayi a kawo maki yanzu" Hawaye ne ya cika idonta, Mami ta karasa kusa da ita cikin kwantar da murya tace "Shayin ma baki so?" Ta gyada mata kai, Mami tace "Toh a siyo maki abu a waje zaki ci?" Nihad ta gyada mata kai, Mami ta juya ta fita daga dakin, wayarta dake parlor ta dauka tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga tace "Eatry zaka je yanzu ka siyo abinci ka kawo min" Yace "Abinci? Wani irin abinci?" Mami tace "Idan an samu pounded yam ko Semovita with vegetable soup" Yace "Ohk" Katse wayar tayi ta zauna saman kujera. Ba a dau lokaci ba Khalil ya dawo rike da ledan takeaway din abincin, ya ajiye parlon Mami yana kallonta, tace "Na manta ban ce ka hado da fruits ba" Yace "Yanzu komawa za ayi a siyo fruits din?" Mami tace "Ehh" Juyawa yayi a hankali ya fita daga parlon, ta dau abincin ta shiga dakinta da shi, ta kira Bilkisu ta kawo mata plate, tana gama zuba pounded yam din a plate ta kalli Nihad tace "Sauko kasa ki ci" Nihad ta mike zaune ta sauko kasa ta zauna kan rug da ta shimfida mata tana kallon pounded yam din, it looks so enticing kuma bata ji zuciyarta na tashi ba, Ta kalli ruwan wanke hannu da aka ajiye mata ta wanke hannunta sannan ta fara cin pounded yam din, Mami tace "Do not rush it, idan kin ci kadan ki rufe anjima sai ki ci sauran" Nihad ta gyada mata, Mami ta dauko mata magungunanta ta ajiye gabanta sannan ta juya ta fita, Nihad bata wani ci da yawa ba kamar yanda Mami tace mata, ta dau maganinta ta sha sannan ta rufe abincin ta tafi bandaki ta wanke hannunta, ta dauro alwala ta fito tana idar da sallah ta kwanta bacci ya dauke ta. Wajen karfe sha biyu saura Mami ta shigo dakin ganin idonta biyu tace "Za ki sha kankana a kawo maki?" Nihad ta girgiza mata kai Mami ta dau abinda zata dauka ta fita daga dakin.... Da kyar Nihad ta bude ido ta sauko daga saman gadon Mami ta durkusa saboda daure mata da mararta yayi, Mami dake zaune saman darduma ta kunna wutan dakin tana kallonta tace "Ya aka yi?" Tana yarfe hannu cike da karfin hali tace "Cikina ke min ciwo" Mami ta mike da sauri tace "Ciki kuma?" Kallon agogo tayi taga karfe uku saura na dare, ta zagayo side din da take tace "Sannu, tashi zauna gefen gadon" Mami ta dagota zata zaunar da ita gefen gadon taga stain din jini a rigar jikinta, cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nihad ta koma ta durkusa saboda murda mata da maran ke yi sosai, Waya Mami ta dauko da sauri tayi dialing number Khalil, sai da ya kusa katsewa ya daga, Tace "Ka taho part dina yanzu yanzu" Daga haka ta katse wayar, ta kara dago Nihad tana mata sannu, duk ta rikice ta rasa abinda zata yi... Khalil na shigowa dakin ya nufosu da sauri ganinta rike da Nihad yace "Me ya faru Mami?" Mami tace "Wai cikinta ke ciwo and she is bleeding ko za mu tafi asibiti ne?" Ai bai san sanda ya amshi Nihad daga hannunta ba hankali tashe yana kallonta yace "When did u start bleeding?" Ta kasa ce masa komai sai sai hawaye ke sauka idonta, tuni Mami ta dauko makullin motarta, ganin yanda ya tsaya shi ma ya rasa abun yi duk ya rude, ta masa tsawa tace "Dallah ni ka fito min da ita mu wuce asibiti" Daga haka ta fice daga dakin da sauri zata kai ma drivernta makullin mota kafin ya fito da ita, Asibitin da ya fi ko wanne tsada a Abuja Mami ta sa suka tafi, kuma har suka isa asibitin bata daina bleeding din ba, duk iya dauriyarta sai da ta fashe da kuka sosai, likitocin suka shiga da ita emergency, tsabar rudewar da Khalil yayi har mancewa yayi ashe shima fa likita ne, ya jinginar da kansa jikin bangon asibitin with throbbing heart, he just cant say why he is bleeding that way, Mami ma ta kasa zaune ta kasa tsaye a corridor din emergency ward din, she looks so disturbed, lokaci daya Khalil jikinsa yayi mugun sanyi, he just can't imagine Nihad loosing the pregnancy, ya kasa ci gaba da tsayuwa ya zauna kan kujeran dake wajen ya rike kansa zuciyarsa na bugawa, bayan kusan minti arba'in wani baturen likita ya fito, Mami na ganinsa ta nufesa da sauri, gabanta na faduwa da turanci take tambayarsa ya ake ciki, yace ta samesa a office, sosai taji gabanta ya fadi, Khalil ya daga kai yana kallon likitan har ya bar wajen, can ya kalli Emergency ward din, wani bahaushe ne ya fito, Mami ta kara bin sa, cike da karfin hali tace "Likita ya ake ciki don Allah??" Ya tsaya yana kallonta yace "Ki kwantar da hankalinki Hajiya, she will be fine da izinin Allah, mu je office" Bin bayansa tayi zuwa office dinsa, suna shiga ta zauna saman kujera ya kunna Ac din babban office din nasa ya zauna yana kallonta kamar yanda ita ma take kallonsa, yace "Ki kwantar da hankalinki, bleeding din ya tsaya amma there is high chances of her miscarrying the pregnancy gaskiya" Mami ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, sosai taji hankalinta ya tashi, tayi karfin halin cewa "Cant anything be done about it pls Dr?? Babu abinda za a iya yi?" Likitan ya girgiza kai yace "Kawai dai yanzu zan baku shawarwari ne ta yanda za a tafiyar da cikin nata har Allah ya sa ta wuce stage din nan, she is just 4 weeks pregnant now, and she is having a cervical insufficiency kinga idan ba abi a hankali ba sannan kuma ba wani iko na Allah ba she is going to loose the pregnancy at anytime, bazai zauna ba..." Mami tayi shiru tana kallonsa ta ma rasa abinda zata ce masa, he could see how worried she is, yace "Nan da sati biyu ya kamata ku yi mata pre natal Ultrasound saboda its likely yan biyu take dauke da...." Mami ta bude ido sosai tana kallonsa, ya gyada kai yace 'Yeah mun ga alamar hakan but it's not as if we are 100% sure don at this stage ba a gani, Allah ya bamu ikon gano hakan ne base on experience and how good we are" Yana murmushi ya kare maganar, Mami dai ta kasa ce masa komai, Cikin kwantar da murya yace "In sha Allah everything will be fine Hajiya, kar ki wani daga hankalinki, but nan dai da sati biyu ayi Ultrasound din don tabbatarwa, by then she is 6 weeks pregnant" a hankali Mami tace "Amma babu abinda ya samu cikin yanzu ko Dr?" Yace "Cikinta na nan har yanzu, kawai dai yanzu zan baki measures da za a bi don gudun miscarrying cikin, sannan we will keep her here for some days, Da farko well balanced meal, kuma duk wani abu da zai dameta ya daga mata hankali da fargaba a gujesa gaskiya, sannan she should be on bedrest, shi yasa nace za mu yi admitting dinta a nan na yan kwanaki..." Sosai Mami ta basa attention dinta tana sauraronsa har ya kai karshe, Bayan ya gama Mami tace "Idan aka bi duk abubuwan nan da ka fada ai shikenan babu wani abu da zai samu cikin kuma ko Dr?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Hajiya to be sincere to u... the chances of keeping this pregnancy, and the chances of loosing it is just 50/50, that's just the plain truth" Mami ta kasa ce masa komai, can ta mike tace "Muna bukatar sallama zuwa da safe Dr" Ya daga kafada yace "Alright then, Allah ya kai mu goben" Tace "Zan iya shiga in ganta yanzu?" Yace "Sure, ai an maidata ward yanzu haka" Tace "Nagode" Daga haka ta fita daga office din, wani likita ta tambaya ya gaya mata ward din da aka kai Nihad, tana isa kusa da ward din ta tsaya ta ciro wayarta a jaka tayi dialing number Janar, hoping he is going to pickup, yana fara ring kuwa ya daga, daga bangaren yace "Why are you awake by this time??" Tace "Fatima ce bata da lafiya" Har Janar zai tambayeta wacece Fatima kawai sai ya tuna warce take nufi wato Nihad, yace "Hasbunallah what's wrong with her?" Mami tace "Na kira Dr Rukayya ta zo jiya ta dubata da na fahimci bata da lafiya, bayan ta dubata ta tabbatar min tana dauke da ciki" Janar ya ɗan yi shiru, can yace "Maa sha Allah, that's a good news, Allah ya bata lafiya, maa sha Allah" Mami tace "Toh dazu Ina sallah wajejen karfe uku ta fara bleeding, cause she is in my room" Janar yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kuna ina yanzu?" Tace "Muna asibiti, and they are telling me nonsense, that there is high chances of her loosing the pregnancy, sannan cikin ma na yan biyu ne" Janar yace "Take her away from that hospital immediately, i will make some calls now zuwa gobe za ki fita da ita America....." Mami tace "Shi yasa dama na kiraka" Janar yace "Ina khalil din?" Tace "Tare muka zo asibitin da shi, amma ni ban ga amfanin ma zuwa da shi ba, yanzu na fito office din likitan wanda nake tunanin bai san abinda yake ba gaskiya, har yana bani assurance akwai high chances of loosing the babies who does that, i dont think he is okay" Janar yace "Ku koma gida ku fara shiri kawai" Mami tace "Shikenan sai anjima" Daga haka ta katse wayar ta shiga ward din, Khalil na zaune kusa da Nihad yana rike da hannunta yana kallonta, ita kuma tana bacci, gaba daya ya zama wani iri kamar shi ne babu lafiyan, yana ganin Mami ya juya yana kallonta, he doesn't look himself at all, gaba daya a sanyaye yake, Mami ta nufi gadon tana kallonta ita ma, a hankali ya mike ya fita daga ward din zai je gun likitan don jira yake ta fito dama. Da asuba Mami ta bar masu asibitinsu tare da Nihad bayan ta biya bills din, dama sojan da ya kawota da motar soja guda daya da ya biyosu suna cikin asibitin giving dem security tun a jiyan, gari ya fara haske suka isa gida, Mami ta sauka daga motar tana kallon Nihad dake kokarin saukowa tace "Ki fa yi a hankali" A hankali ta sauko daga motar Mami na biye da ita a baya making sure ba sauri take ba suka shiga gidan, shi dai Khalil ya bi su da kallo, Mami ta ajiye mayafinta ta shiga bandakinta ta hada mata ruwan wanka a bathtub sannan ta fito dakin tace "Shiga kije kiyi wanka, and be careful as u do so" Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta koma parlonta ta tadda Khalil a zaune tace "Ka hada mata kayan sakawanta da duk abinda zata bukata a jaka za mu tafi asibiti..." Da mamaki yace "Asibiti kuma?" Wani asibitin?" Mami bata tsaya basa amsa ba ta koma ciki ta dau wayarta, kanwarta Hamidah ta kira, yana

Please Login or Register in order to submit comment