Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganinka" Ya shafa kansa yace "Gani na zo ai, ina fadil?" Yace "Yana wajen Mumynmu bata da lafiya" Khalil yace "Toh kai ni in gaisheta" Har part din Mumy Sudais ya kai sa, yayi sallama bakin kofar parlon, Wata frnd din Mumy ta amsa, shiga parlon yayi kansa a kasa ya nemi saman carpet ya xauna ya gaishesu, duk suka amsa, Mumy dake xaune parlon an cire mata last drip dai kallonsa kawai take, Bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace "Ya jikin Mumy?" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah Ibrahim, ya gida?" Ya sauke kansa yace "Lafiya lau, Allah Ubangiji ya kara Lafiya" Tace "Ameen Nagode" Bai kuma cewa komai ba, Hajiya Zara ta mike ta fita daga parlon, bayan few minutes Mumy tace "Kayi hakuri Ibrahim, an cuceka an hadaka aure da warce bata cacanceka ba, nasan baka da yanda xaka yi ne kuma baxa ka iya k'in amsan tayinta da mahaifinta yayi maka ba...." Da sauri yace "Aa Mumy, Allah ne ya tsara haka, kuma muna fatan Allahn yasa hakan shine mafi alkhairi" Hawaye na sauka idon Mumy tace "Ni kam bani da abinda xan ce maka sai dai in baka hakuri akan abinda Alhaji ya maka, sannan ni baxan ce kayi hakuri da Nihad ba, idan kaga baxa ka iya ba ko xaka cutu ina me goya maka bayan ka saketa kawai ta dawo gida...." Cike da karfin hali Khalil yace "In sha Allah baxa ayi haka ba Mumy" Mumy ta share idonta bata kuma cewa komai ba, Wani duniyar tunani khalil ya fada gaba daya jikinsa yayi sanyi, he couldn't even think straight, kiran sallahn magrib da ake ne yasa ya dago kai ya kalli Mumy ya ga kallonsa take, a hankali yace "Xan je masallaci Mumy, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Ibrahim nagode" Tashi yayi a hankali ya fita daga parlon, Umma ya tarar a main parlor ta masa wani kallo sai kuma ta ja tsaki tayi hanyar kitchen, ya bi ta da ido kawai. Bayan an idar da sallan magrib tare suka shigo gidan da Abba har xuwa parlonsa, Khalil ya xauna ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa yace "Ya gidan?" Yace "Alhamdulillah" Abba yace "Ya kamata xuwa gobe ku shirya ka tafi da ita can garinku ta gaida iyayenka, bayan kwana biyu sai ku dawo" Khalil ya ɗan yi jim, sai kuma ya dago ya kalli Abba yace "Toh in sha Allah Alhaji, Allah ya kai mu goben" Abba yace "Ameen, farooq ya zo min da wani batu jiya amma sai kun dawo dai" Khalil yace "Toh Alhaji, nagode" Abba ya ciro dubu dari ya mika masa yace "Ka yi full tank, sannan kayi ma iyayenka tsaraba da sauran" Khalil ya sa hannu biyu ya amsa yace "Toh Allah ya saka da alkhairi Alhaji" Abba yace "Ameen, Allah ya maka albarka" Khalil ya amsa da "Ameen" a tare suka fito main parlor da Abba, Umma ta fito daga kitchen kenan ganinsa da Abba tace "Aa Ibrahim har xa ka tafi, bari to ga abinci ka kai ma Nihad tunda an gama" Ya kalleta yace "Toh" Komawa kitchen tayi da sauri, Abba dai ya zauna parlon har sannan kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa, dake xuciyarsa kawai yake yana ma Nihad wasu abubuwan as form of punishment amma shi yasan sonta a jininsa yake, but he can't help it, tayi disappointing dinsa sannan ta xubar masa da mutunci a idon duniya, Umma ta cika warmer da abinci, sannan ga wani warmer din daban na kaza ta fito parlor, sai da ta bubbude warmer din tana kallon khalil cike da damuwa tace "Don Allah idan ka je ka lallabata ta ci abincin nan, duk ta rame ta lalace wallahi, Shekaranjiya da naje ma da ya na samu ta ci abincin, yanxu kam ban san halin da take ciki ba baiwar Allah, wa yasani ma ko bata cin komai" Shi dai Abba bai ce komai ba, khalil kuwa banda kallonta babu abinda yake, Abba ya mike yace "Ka jirani Ibrahim" Khalil yace "Toh Abba" Ba a dau lkci ba sai ga shi ya dawo da dubu talatin ya mika ma Khalil yace "Ka siya mata carton din maltina da na madaran gwangwani" Ta gefen ido Umma ke ta kallon Abba, Khalil ya amsa yace "Toh In sha Allah Abba" Abba yace "Sai da safe, Allah ya tsare" Juyawa Umma tayi ta shige kitchen ta tsaya jikin cabinet kamar me nazari. Khalil na isa gida sai da yayi isha a masallacin dake layin sannan ya shiga gida da motar yayi parking, bayan ya kulle gate din ya dawo ya fiddo abincin daga cikin mota ya kai parlor ya sake fitowa ya kai maltina da madara parlon ya ajiye sannan ya kulle gidan, xaunawa yayi saman kujera ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, da yasan haka abubuwa xa su kasance masa da bai yarda ya fara shigowa garin kano ba, where will he even start this amendment from?? Babu warce ta tsaya masa a rai sai Mahaifiyarsa, this seriously isn't going to be easy, Mikewa yayi daga karshe ya nufi dakinsa yana tafiya a hankali, har ya bude kofar sai kuma ya fasa shiga, ya dawo ya bude dakinta, zaune ya ganta a kasa idonta yayi bulu bulu alamar tayi kukan gaske yau, ya tabe baki ya kulle kofar ya koma parlor kawai yayi xamansa, tashi Nihad tayi ta bi bayansa, ta tsaya bayan kujera tana shesshekar kuka..., ya ɗan daga kai ya kalleta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Da bashi ne?" Wani bakin ciki ya rufeta a fusace tace "Ban sani ba, ka zata kai ka isa ka dinga punishing dina? Waya biyu aka kawo min gidan nan ka salwantar min da su, toh wallahi zaka sha mamakin abinda xai faru idan baka bani wayata ba" Mikewa yayi ya bar mata parlon ya shige dakinsa ya kulle, kuka kawai take kamar ranta xai fita, babban tashin hankalinta shine Aliyu da xai yi ta kiranta ya ji a kashe, yanxu babu ta inda xata yi ta iya kiransa, da ma baya kulle gate ne ko makota ita sai ta shiga don ta kira Aliyu, amma ko daxu da xai fita kulleta yayi ta ciki, ko bin ta kan warmers din abincin dake parlon bata yi ba ta koma daki ta dinga kuka kamar ranta zai fita, har kusan karfe biyun dare Nihad bata yi bacci ba, abun duniya ya taru yayi mata yawa, last week fa warhaka tana baccinta peacefully a saman gadonta, tashi tayi a hankali ta goge idonta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar dakin nata ta fito, taga ya kashe duk wutan gidan, ko ina yayi duhu, tana lalubawa ta tafi hanyar dakinsa ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude ta shiga dakin, nan ma dai ya kashe fitilar, sai da ta fara tattaba socket din dakin cikin duhun ko xata ga karamar wayarsa a jiki taga babu, cikin sanda ta nufi gadon dakin ta durkusa, hannu ta kai xata laluba kan gadon taji hannunta saman broad haired chest dinsa, zaro ido tayi a mugun tsorace xata mike ta gudu ya fixgota ta fado saman gadon daga gefensa, yayi kneeling dai dai inda take har tana jiyo respiration dinsa, yana kallonta cikin duhun kafin yace komai jikinta na rawa tace "Wayyo na shiga uku, wallahi torchlight nake nema xan je in sha ruwa a kitchen...."








*Littafin Nihad dari biyar ne, ki fita hakkina kafin ki karanta min littafi hankalinki kwance*


3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence via👇🏻




07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


29




A hankali Nihad ta bude idonta ta dalilin sanyin da take ji, at first sai da tayi imagining cewar ai fa kauyen nan take, a firgice ta tashi xaune tana tattaba daya side din gadon don wutan dakin a kashe yake, amma taji ba kowa wajen, jin laushin duvet yasa ta tuna ashe a hotel suke, wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, ta sauka daga kan gadon tunda hotel din ba bakonta bane ta san inda switch yake, tana tafiya a hankali ta xagoya xata kunna wutan taci tuntube da mutum ta fada kansa duk da a zaune yake, da farko tayi mugun tsorata amma tana jin kamshin turarensa ta gane shi ne, tashi tayi ta dafa bango ta kunna wutan, zaune ta gansa saman darduma alamar sallah yake, ta zaga daya side din ta kalli agogon dakin ta ga karfe biyu da minti goma, komawa tayi gefen gado ta zauna tayi tagumi, sai kuma ta tuna bata yi isha'i ba ta tashi da sauri ta shiga bandaki. Har ta idar da isha'i sallah yake shima, ta ɗan yi jim kamar xata tashi ta koma ta kwanta can dai kuma kawai ta mike ta hau sallan nafila, har ta mance rabon da tayi qiyamul lail, sai dai in mistakenly ta kwana dakin Nihal shine Mumy ke tashinsu su yi sallan dare, don dare daddaye ne Mumy bata sallan dare, a wannan daren kuma tayi addu'a sosai a kan Allah ya toni asirin duk wanda yayi ruining happiness dinta cikin gaggawa, abinda bata ta6a yi ba tun da abun ya faru, daga karshe tayi addu'ar Allah ya sa khalil ya rabu da ita na har abada don ita ba class dinsa bace, sannan baxata ta6a zama da shi a matsayin mijinta ba, ta kuma yi addu'an bayan Khalil ya rabu da ita Allah ya mallaka mata Aliyu, wajajen karfe Uku da rabi ta fara jin bacci, ta ɗan saci kallon side dinsa, yana zaune saman darduma shi ma da alamar ya idar, amma kana kallonsa xaka san yayi nisa tunanin da yake, and he look so distressing, dauke idonta tayi daga kansa tayi kwanciyarta saman inda tayi sallan, har dai bacci ya dauke wajen karfe hudu bata ga alamar Khalil xai kwanta ba. Da asuba loudspeaker din masallacin dake hotel ne ya tasheta, bata gansa a dakin ba alamar ya tafi masallaci, bayan ta idar tana zaune saman darduma tana azkar ya shigo dakin, ba tare da ya kalleta ba ya shiga bandaki, tana ta zaune kan darduma taji ring din wayarsa kallon gaban madubin tayi da sauri don bata san wayar na nan ba, kuma bata ta6a jin wayarsa na ring ba sai da vibrate, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi gaban madubin, Mami ta gani gaban screen din karamar wayar, ta dauka kenan kawai ya bude bandakin ya fito da sauri ya nufota yace "Keee" Ba karamin rikicewa tayi ba ta juyo wayar na hannunta, zaro ido tayi ta saki wata er kara ganinsa daure da towel ta durkushe kasa ta rufe fuskarta da gwiwanta a tsorace, yana isa inda ta durkusa ya warce wayarsa a hannunta ya koma bandakin, duk da taji rufewar kofar bandakin taki dago kanta, bayan kusan minti daya ta dago a hankali tana kallon kumfan da ya sa mata a hannu wajen warce wayarsa, turo baki tayi ta mike jiki a sanyaye ta koma can daya side din gadon ta kwanta tare da juya ma kofar bandakin baya. Tana ji ya fito daga bandaki bayan kusan minti sha biyar sai kuma ta ji ya fita daga dakin gaba daya. Wajen karfe takwas ta gaji da kwanciya ta tashi ta zaga ta shiga bandakin, wanka tayi ta fito bayan ta goge jikinta ta maida kayan da ta cire, tana zaune gefen gado ta jinginar da kanta da gadon tana kallon Tv duk da hankalinta baya kan kallon ya bude kofa ya shigo dakin, tunda ta kallesa sau daya bata yarda ta sake kallonsa ba, ta dai ga ya canxa kaya, shi kam bai kalli inda take ba ya dau towel din da ta yasar saman gado ya shigar da shi bandaki ya fito, ya dauko magungunan da ya siyo mata jiya dake yashe kasan dakin ya jefa mata gefenta ya hade rai yace "Wato dama lafiyarki qlau kika sa naje chemist nayi asaran kudina ko?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Kudin babana dai" kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace "Gaskiya ne, kudin babanki ne, sai ki taso mu koma can garin kiyi kumallo a can gidanmu, kinga can ai kudin babana ne ba na baban wani ba" Kallonsa tayi da sauri, ganin hada abubuwansa dake dakin kawai yake, tayi karfin halin cewa "Wani garin xan je in yi kumallo?" Ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace "Ina jiranki a waje" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni wallahi baxa ka maida ni wannan garin ba, wai kai baka tsoron Allah ne?" Juyowa yayi ya rungume hannu ya jingina da kofa yace "Sai ke" Cikin kuka tace "Allah baxan je ba, kaji har na rantse, dama ba kwana biyu kawai xa mu yi ba? To wllh baka isa ka maida ni ba" Yace "Ohk, xan nuna maki kuwa na isa, sannan in mun koma sai mun yi wata daya kafin mu bar garin, kinga baxa ki kara min gorin kudin babanki nake ci ba" Cikin tashin hankali tace "Kaga don girman Allah kayi hakuri ka daina ce min haka, wallahi in ka sake maida ni kauyen nan xan iya mutuwa kawai" Khalil yace "Toh mu je a ga adadin kwanakin da xaki iya a can din kafin ki mutu" Cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri" Shiru yayi na few seconds, sai kuma yace "Ohk, baxan maida ki garin ba amma da sharadi" Tana goge idonta tace "Ina ji" Ya fi second talatin yana kallonta kafin yace "Nasan komin daren dadewa xa mu rabu... Don haka idan Allah ya kai mu lokacin ina son ko me xai faru baxa ki fasa nuna ma iyayenki cewar ke kika bukaci mu rabu ba ni ba....." Nihad dake ta kallonsa da mamaki tace "Toh me yasa yanxun baxa mu rabu ba kawai, kuma wallahi babu wanda xan gaya ma, kaga babu wanda xai sani sae mu biyu" Yana kallonta yace "Ohk ta yaya kike tunanin xa mu rabun yanxu?" Ta gyara xama tace "Kawai kace ka sakeni, babu me sani sai ni da kai" Yace "Toh idan aka yi hakan sai me xai faru?" Ta daga kafada tace "Ba komai, kawai kayi rayuwarka inyi ta wa, ni xan ma iya bar maka gidan gaba daya kawai sai dai in dinga xuwa diban kayana, idan kana so ma sai ka saka yan haya ka dinga karban kudin kana xubawa a aljihu" Khalil ya ɗan yi murmushi ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, sai ki ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya kenan ko?" Tayi masa wani kallo tace "Me kake nufi? Ni nake yin iskanci? Kana nufin ni yar iska ce?" Yayi wani murmushin takaici yace "Toh baxan yi abinda kike so yanxu ba, kawai dai ki sa a ranki lokacin hakan na zuwa, nan ba da dadewa ba" Ta kyabe baki tace "Ni fa lokacin da kake nufi da yanxu duk daya ne ni a wajena" Ya daga kafada yace "Gwara dai a jira lokacin" Ita dai bata kuma cewa komai ba amma a ranta tunani take ashe ma ba wani babban sharadi bane, dama ita ai babban burinta su rabu na har abada, Ta kallesa tace "Ka dai yi alkawarin rabuwa da ni??" Yace "In sha Allah" Wani farin ciki taji ya rufeta tace "Toh nima in sha Allah ko ma me xai faru xan ce nice nace mu rabu babu ruwanka" Yace "Toh" Tace "Toh nima ina da deal dina in har kana son inyi abinda kace nima sae kayi abinda nake so" Yace "Ina sauraronki" tana gyara zama tace "Na farko ina son ka bar ni in ci gaba da xuwa makaranta na, na biyu baxa ka hana duk wanda xai zo wajena xuwa ba, like kawayena infact everybody, na uku xaka bani spare key na gida nima, sannan na karshe ina son ka bar ni da wayata..." Kallonta kawai khalil yake, ta langwabar da kai ta wara ido tace "Ehh, ni gwara nawa minor request ne, babu abinda xai ragu a jikinka idan kayi accepting, naka request din kuwa kilan har tsine min xa a iya yi a gida amma kuma ban damu da hakan ba na amince xanyi yanda kace" Khalil yace "Abu biyu kadai xan iya maki a abubuwan da kika ce, idan kuma kinga hakan bai maki ba kawai a bari, mu ci gaba da zaman mu yanda muke, kuma dole a titi ace maki matar drivern gidanku" Ta marairaice sai kuma tace "Toh ina ji, ka gaya min abu biyun" Yace "Babu xancen xuwa makaranta sannan baxa ki rike waya ba!!!" Shiru Nihad tayi tana nazari, wato kawayenta xa su iya xuwa gidan sannan xai bata makullin gida, daga kai tayi ta kallesa taga kallonta yake yana jiran jin me xata ce, tace "Toh ai shikenan, na amince" Yace "Sannan abu na karshe wanda muhimmancinsa kusan daya da sharadin farko...." Tace "Ina jin sa" Yace "Babu ke babu kallon inda wayata take balle ki ta6a, a takaice babu ruwanki da wayana har xuwa lokacin da xa mu rabu" Nihad ta kyabe baki tace "Toh dama ni meye ruwana da torchlight phone dinka bawan Allah??" Ya gyada kai yace "Toh" Juyawa yayi ya fita daga dakin, ta mike ta dau ledan magungunanta ta saka Hijab sannan ta bi bayansa. A reception ta tarar da shi ya bada makullin dakin ya fita compound din hotel din ta bi bayansa, wani ma'aikacin hotel din ne irin masu share share ya ganta yace "Ahh Hajiya kwana biyu kin buya, ya kawayenki" Nihad ta juya ta kallesa, murmushi tayi tace "Lafiya lau ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, yau baku zo da kawayen naki ba kenan? Naga kullum tare ku ke" Sai kuma ya kalli Khalil dake tafiya yace "Au ashe da oga ku ke...." Katse sa Nihad tayi da sauri tace "Aa, drivern gidanmu ne, ya kawo ni in amshi sako wajen wani" Murmushi kawai Khalil dake tafiya xuwa inda ya ajiye mota yayi ba tare da ya juyo ya kallesu ba, Ma'aikacin ya fasa gaida Khalil da yayi niyyar gaidawa, sai kuma yace "Allah sarki ni na zata oga ne ae nagansa kalarki, to na gaisheki Hajiya" Bude jakarta tayi taga dari biyar ta zaro ta mika masa, ya amsa da ladabi yana mata godiya, tuni Khalil har ya kai gun mota ya bude driver seat ya shiga, Nihad ta karasa ta bude back seat ta shiga ta kulle, har suka isa gida bai ce mata ba bata ce masa ba, bayan yayi parking ya sauka ya tafi ya kulle gate, sannan ya nufi entrance din gidan ya bude kofar main parlor, Nihad dake ta tsaye tana jiran ya xo ya bude ta kyabe baki ta bi bayansa suka shiga parlon, wani ajiyar xuciya ta sauke direct ta nufi dakinta. Bacci sosai Nihad tayi bayan ta shiga dakinta, wajen karfe sha daya da rabi ta farka ta dalilin yunwan da take ji, a hankali ta mike ta shiga banɗaki tayi wanka ta wanke baki sannan ta fito, bata gansa a parlor ba har ta nufi dakinsa sai kuma ta fasa bude kofar ta dawo parlor ta zauna tana jiran ganin fitowarsa bude kofar parlor aka yi ta juya da sauri, taga ya shigo parlon rike da leda kallo daya yayi mata ya dauke kai ya karaso cikin parlon, a takaice tace "Makulli xaka bani xan fita in siyo kayan miya, sannan anjima xan je kasuwa siyo atamfofi don na kyautar da duk kayana a can garinku" Ya girgiza kai yace "Baya daga cikin sharadinmu, duk me kike bukata xa a siyo a ajiye maki" Ta kyabe baki tace "Toh a fita a siyo min kayan miya" Cike da isa tayi maganan, yace "Sai sanda nayi niyya" Yana gama fadin haka ya ajiye ledan hannunsa ya nufi kitchen don dauko plate, bin sa tayi da kallo yana shiga tayi saurin dauke ledan abincin nasa ta shige daki da sauri ta sa makulli, shinkafa ne da miyya da yaji uban nama sannan ga coslow a wani karamin takeaway din, ga ruwan roba me sanyi da drink, tayi er dariya ta gyara zamanta ta dau cokali ta fara cin abincin. Wajajen karfe uku Nihal ta kira Khalil, bayan sun gaisa yace "Kin dawo lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha daya, yaushe xa ki zo ganin er uwar taki?" Nihal tace "Shine dama nake son in ce mata xan zo yau, ka kai mata wayar pls" Yace "Xan gaya mata, Allah ya kawo ki lafiya" Tace "Ameen" daga haka ya katse wayar, tun da Nihad ta shige masa da abinci daki bata sake fitowa ba, don bayan ta ci ta koshi ma ramuwan baccin da bata yi a kauye ba ta ci gaba da yi. Wajen karfe biyar Nihal ta iso gidan, Khalil ne ya bude mata gate bayan ta kirasa a waya ta sanar masa tana bakin gate, ta sunkuyar da kai ta gaishesa ya amsa da murmushi yace "How are you Nihal?" Ta daga kai ta kallesa tace "Alhamdulillah" Yace "Maa sha Allah" Tana biye da shi suka shiga parlon gidan, ganin ta zauna a parlon ya daga kafada yace "Tana can daki, ki shiga" Nihal tace "Ko zaka dan mata magana ta fito" Yace "Aa, just go in" Mikewa tayi ta nufi kofar dakin da ya nuna mata, a hankali ta kwankwasa kofar, Nihad ta juya tana kallon kofar, to me xai ce mata yake mata Knocking, can dai ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, ido hudu suka yi da Nihal, wara ido tayi ta rungumeta tace "Yaushe kika dawo Nihal?" Nihal na Murmushi tace "3 days ago" Sai kuma Nihad ta hade rai ta koma cikin dakin, Nihal ta bi ta da kallo sai kuma ta bi ta cikin dakin ta kulle kofar, Nihad tace "Wato ke har xa a iya hada baki dake a cuceni ko Nihal? Ni nasan babu yanda xa ayi kice baki san komai a kan abin nan da Abba yayi min ba" Innocently Nihal tace "Wallahi ban san komai ba Nihad, kiji har na rantse" Nihad tace "Toh sai aka ce maki yarda xan yi da ke? Bayan nasan har tadi ku ke yi da drivern nan a waya amma kice baki sani ba?" A hankali Nihal tace "Allah ne shaida na, amma meye ribata idan nayi maki karya?" Nihad ta tabe baki tace "We have already sort out things da shi daxu da safe, and we are okay with our plan" Nihal tace "What plan?" Nihad tace "Ba sai kin ji ba, ina umma?" Nihal ta mika mata wayarta tace "Tace in na xo ki kirata" Murmushi Nihad tayi ta amshi wayar ta tafi can karshen gado ta hau kiran Umma, Umma na dagawa tace "Auta har kin je gidan ne?" Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Nihad, wato dai wannan matsiyacin duk wayar da aka baki sai ya karbe ga shi tatattce ko?" Nihad ta tabe baki tace "Wallahi Umma" Umma tace "Toh xa mu xuba da shi kuwa, xan kawo maki waya sannan in mika masa a gabana ya damka maki wayar da hannunsa" Nihad tace "Kin ma san abinda yayi min Umma?" Umma ta zaro ido tace "Me yayi maki?" Nan Nihad ta labarta ma Umma garinsu da ya kai ta ta kusa mutuwa, Umma tace "Ikon Allah, amma shine matsiyacin nan ya samu waje yake nuna ma mutane isa daga an aura maki shi? Asha ɗan kauyen kayau ne" Nihad tace "Wllh Umma ban gama rainasa ba sai da naje garinsu, yanxu 100% na rainasa wallah, Umma ko wuta fa babu a garin, sannan rafi suke xuwa debo ruwa, kai ni baxan ma iya baki labarin garin nan da baki ba, sai da nayi rashin lafiya kamar xan mutu sannan ya dawo da ni cikin gari" Umma da ke ta sauraronta tace "Ikon Allah, dama ance talaka da matsiyaci basu iya samun waje ba, ki ga yanda ya dawo birni ya kile yake daddaga ma mutane kai alhalin ko mage me gata baxata iya

Please Login or Register in order to submit comment