Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bude baki tace "Shi farooq din?" Cikin kuka tace "Ehh Umma" Umma tace "Yi shiru xan yi maganinsa don ubansa" Nihad na shessheka tace "Toh Umma yace kada in sake fita makarantar kuma" Umma tace "Ai ba shi ya haifeki ba da xai hanaki xuwa makaranta, kanki tsaye gobe ma ki shirya kiyi tafiyarki duk inda xa ki ba ma makaranta kadai ba, ki kyaleni da shi kawai xan yi maganinsa" Nihad tace "Toh" Umma tace "Kar ki sake asaran hawayenki a banza, kinji abinda nace maki" A hankali Nihad tace "Na ji" Umma tace "To sai da safe" Daga haka ta katse wayar, mikewa tayi direct ta tafi dakin farooq, luckily ta samesa xai fita Masallaci, strictly tace "Farooq daga yau sai yau in har ba baki kake son in maka ba bana son in sake kara ganin ƙafafuwanka a hanyar gidan Nihad, kuma babu ruwanka da harkarta da abinda take yi, in dai ba so kake in ce maka je ka ka gani, kai ko a waya na haneka da kiranta" Da mamaki Farooq ke kallonta, tace "Ni dai na gaya maka, kana kiranta ko da a waya ne Allah ya isa, balle har ya kai ka taka har gidanta, daga yau bana son magana ya sake hadaka da ita ko a ina kuwa" Tana gama fadin haka ta juya fuuu ta fice ya bi ta da kallo, a parlor ta tadda Amina xata fita, tace "Ke kuma ina xa ki?" Amina tace "Umma kati xan amso" Umma tace "Ban hanaki fesa turare haka ba idan xa ki fita? Kuma ba nace maki wannan hijabin bana son kina sa shi ba? Meye amfanin hijabi da xai dinga nuna surarka? Maza koma ki dau wani hijabin" Amina ta juya tace "Dama kyautar da hijab din xan yi Umma, kawai bana son daukan gogagge ne shi sa na sa shi yanxu" Umma tace "Maxa ki bayar idan ba haka ba in kona, bana son sake ganin ɗan iskan hijabin nan a gidan nan" Amina ta juya ta koma daki, Umma ta wuce ɓangarenta. Karfe tara da wani abu Nihad ta gama shirinta xata kwanta, har sannan taki daina kukan maganganun da Khalil ya gaya mata, wai er titi, sannan har da cewa tayinta Abba ya basa, takaici kamar ta hadiye xuciya, can ta mike ta fita daga dakin nata, a parlor ta gansa xaune yana kallo, tana harararsa tana huci tace "Ba dole ka sa tv a gaba ba tunda babu a house" Shi dai bai ko kalleta ba, tace "Kuma da kake cewa Abbana tayina yayi maka, in ka cika ɗan halas ka sakeni yanxu yanxu mana..." Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta maka masa wani harara tace "Idan kuma baka da takarda da biro ni ina da su" Bayan few seconds yace "Ohk ashe dai kinsan da aurena a kanki?" Ta wani kyabe baki tace "Oho dai" Ya gyada kai yace "Kar ki damu akwai lokaci, kawai mu jira lokacin, ina son sai sanda kika fahimci ni ba sa'an aurenki bane sannan xan sake ki...." Tace "Aikin banza kenan, yanxu ya kamata ai, don tun yanxu nasan ni ba class dinka bace, kuma baxan ta6a xama class dinka ba" Khalil bai sake tanka ta ba, ta juya fuuu ta koma ciki, wayarta ta dauka a karkashin pillow tayi dialing number Aliyu, amma ta kasa samunsa sbda ba shi da number, Naf ta kira tace "Naf don Allah ki kira Aliyu kiyi mashi sending wannan number nawa yayi saving i want to talk to him" Naf tace "Ohk" Daga haka ta katse wayar, bayan wani lkci Naf ta sake kiran Nihad tace "Nihad na tura masa number taki yace xai kiraki" Nihad tace "Toh nagode sosai" Nihad na kwance tayi lamo kan pillow tana ta jiran kiran Aliyu, sai ga kiran nasa, farin ciki ne ya cikata ta mike xaune da sauri ta daga kiran, a hankali tayi masa sallama, ya amsa yace "How are you?" cikin sanyin murya tace "Alhmdlh" Yace "Are okay?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace "No" Da damuwa yace "Me kuma ya faru?" Tana girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Baxan iya jure xama waje daya da wannan drivern din ba, Har xagina sai da yayi daxu fa" Aliyu yace "Ya zage ki?" Cikin kuka tace "Ehh, wai ni ya ce ma er titi, er tasha, har da cewa Abbana tayina ya basa" Aliyu yace "Shi Drivern?" Tace "Ehh" kasa cewa komai Aliyu yayi, can yace "Wait u mean driver ne ya gaya maki wa ennan maganganun?" Nihad tace "Wallahi" Rai bace yace "Har ya kira ki da er titi?" Cikin rawan murya tace "Haka yace" Aliyu ya fuzar da iska yace "Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki, xan dawo Nigeria soon, and everything will soon come to an end in sha Allah" Tana share idonta tace "Nagode" Yace "Kar ki sake xubar da hawayenki, sai yayi da ya sanin zagin nan da yayi maki wallahi" Nihad tace "Sannan nace ya sakeni ya ki" Aliyu yace "He just have to, cause u are not meant for him...." Ɗan murmushin jin dadi tayi, yace "Are u on WhatsApp?" Tace "Aa xan bude yanxu" Yace "Idan kin bude, ki kirani" Tace "Ohk" Daga haka ya katse wayar, sosai hankalinta ya kwanta da abubuwan da Aliyu ya gaya mata, bayan ta bude WhatsApp din Video call suka yi da Aliyu har kusan karfe dayan dare, tun bayan da Video dinta ya tafi viral sai ranan tayi bacci cikin dadin rai. Cikin dare taji kamar ana daga pillow din da ta daura kanta, ta bude ido da sauri, bata ga kowa ba banda duhu dake dakin, gabanta ya dinga faduwa don da gaske taji kamar ana daga pillow dinta, ta mike xaune tana bin ko ina da kallo duk da duhun dake dakin, hannunta ta kai xata yi switching wutan dakin taji ta daura a kan hannun mutum, wani ihu ta fasa a mugun tsorace xata sauko daga kan gadon taga an kunna wutan dakin haske ya gauraye ko ina, yana jingine jikin bango kusa da bed side drawer, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa a mugun tsorace kuma da mamaki, ya daga pillownta ya dau wayar dake ƙarƙashi, xaro ido tayi ta taho da sauri tace "Wallahi kar ka kuskura ka ta6a min...." Wani mugun kallo yake mata yace "Kar ki matso kusa da ni" Ta fashe da kuka sosai tace "Wallahi ka bani wayata, kaga ba kai ka siya min ba, ba kuma da sisin ka aka siya ba" Kofa ya nufa ta koma gefe tana kuka tana kallonsa har ya fice daga dakin, da sauri ta bi sa dakinsa tana cewa "Wallahi ka bani wayata" Bude kofar bandaki taga yayi tana kallo ya tara ruwa a bucket sannan ya cilla wayar a ciki ya fito ya sa ma bandakin makulli, saboda shock kasa ce masa komai tayi ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, bai ko kalleta ba ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa saman gado.... Har gari ya waye Nihad bata yi wani bacci ba, ta ci kuka har ta gode Allah, ta sake tabbatar da cewa bata ta6a tsanar mutum a duniya irin khalil ba, karfe takwas saura taji kamar ana welding a bakin gate, ta mike da kyar ta fito parlor ta tafi kofar fita parlorn, tsaye ta gansa a compound, ga kuma me welder da me canza lock din gate suna ta aiki a bakin gate, juyawa tayi da sauri hawaye cike idonta ta koma dakinta, ta xauna gefen gado tana shessheka, ta shi tayi ta tafi dakinsa ta bude kofar bandakin ta duba bucket din da ya jefa wayarta taga babu wayar a ciki, ta fito ta ga karamar wayarsa a gefen gado, da sauri ta dauka ta fito ta shige dakinta, Call logs ta shiga taga number anyi Saving da Nadeeyah with love Emoji, kallon Number ta dinga yi sai kuma tayi scrolling xuwa kasa taga number Nihal wanda ko jiya ma sun yi waya, shiga tayi taga maganar minti nawa suka yi taga kusan minti goma, dialing number tayi yana fara ring Nihal ta daga, Rai bace Nihad tace "Ban san ke munafuka bace kuma algunguma sai yanxu Nihal, kuma in sha Allahu ke abinda xai sameki sai ya fi wanda ya sameni ki rubuta ki ajiye, don naga kamar farin ciki kike da condition din da nake ciki, banda kina farin ciki da abinda ya sameni wayar me xaki dinga yi da enemy din nan nawa? Me yake gaya maki, me kike gaya masa?" Nihal tace "Haba Nihad, what is this u are saying? Da kinsan wayar da nakeyi da shi da baki kirani kina gaggaya min wa ennan maganganun ba, kema kinsan baxan ta6a farin ciki da bakin cikin ki ba..." A fusace Nihad tace "Babu abinda xa ki gaya min da xai gamshe ni, kuma xan ga ta inda xaki sake waya da shi" Nihal tace "Toh shikenan, amma ki sani ko na kirasa ke nake cewa ya ba waya sai baxai baki ba" Nihad tace "Oho wannan ke da shi ya shafa" Nihal tace "Jibi xa mu yi hutu, and we need to talk idan na dawo Nihad" Nihad bata kuma sauraronta ba tayi ending call din, Yanxu tasan xamanta da kowa a duniya, Abba ne oo, Mumy, Ya farooq, Nihal, duk ashe ba sonta suke ba, kuka sosai ta saki, sai kuma tayi blocking number Nihal a wayar sannan ta bi duk calls din ta goge, Kallon Number Nadeeyah ta dinga yi ganin how special the line is with multiple 2's, can ta ja wani tsaki ta danna masa block sannan tayi deleting shi ma gaba daya a call logs, sai kuma ta tuna cewar she needs to tell Aliyu cewar ya amshe mata waya incase zai yi ta nemanta, dialing number Aliyu ta fara yi, ko digit hudu bata sa ba sai taga number ya fito barau barau amma ba tare da suna ba, still tayi tana ta kallon screen din karamar wayar baki bude da mugun mamaki, to ko dai jiya da ya dau wayarta ne ya kwashe number??? lkci daya ta juya da sauri jin taku, wani irin faduwa gabanta yayi ganinsa a bakin kofar dakin yana kallonta, cikin rikicewa ta ajiye wayar hannunta gefen gadon gabanta na faduwa, shigowa dakin taga zai yi, ta marairaice ta koma can karshen bangon dakin xuciyarta na bugawa tana kallonsa amma hakan bai hanata hade rai ba, ya kalli wayarsa sannan ya kalleta, daukar wayar taga xai yi ta nufi kofa a guje yayi saurin fixgota, kuka ta saki ta rirrike hannunsa tace "Ni wallahi ka sakeni, me kaga nayi kuma again, ba yar uwata na zo inyi magana da ba na dade ban ji muryarta ba...."










Nihaad is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via👇🏻




07087865788📚✍🏻
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD💖💖


27


Kunna wutan dakin Khalil yayi ya koma gefen gadon ya zauna fuskarsa daure yace "Ohk, dauki torchlight din ki fita" Har sannan gabanta bai daina faduwa ba, a hankali ta dawo edge din gadon tana satan kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Dauki ki fita nace" Ta sauke ƙafafuwanta kasa a hankali tana kallon karamar wayarsa da ta hango gefen pillow, Ya jefa mata wani mugun kallo yace "Ko bayan shi da wani abun da kike so ne?" Ta ɗan turo baki tace "Ga can torchlight din da xan ara" Ya kalli inda take nuna masa, sai kuma yace "Ohk" dauko wayar tasa yayi ya mika mata yana kallonta, a hankali ta kai hannu xata amsa, da karfi ya buge mata hannu da wayar, da sauri ta janye hannunta ta bude baki tana kallonsa tana yarfe hannun, ya mike ya dau shirt dinsa ya saka sannan ya nufi kofa ya bude mata da kyau, fuska daure yace "Zo ki fita" Ta fashe da kuka tace "Shine har sai ka kwala min waya a hannuna? Sai kace kai baka shigo min daki idan ina bacci" Cikin kakkausar murya yace "Zo ki fita nace" ganin babu alamar wasa tattare da shi ta mike ta nufi kofar hawaye cike idonta, tana fita ta juyo ta kallesa tace "Ban yafe buge min hannu da kayi da shegen wayarka ba, don ma ka samu xa a ari torchlight din shegen wayar" Yi yayi kamar xai bi ta, ta ruga ta shige dakinta ta kulle kofar da sauri tana maida numfashi. Washegari da yamma bayan Khalil ya gama shiryawa yanda xai je ya sanar ma Nihad ta shirya xa su yi tafiya ne babban aiki a wajensa, tun safe ya fice gidan don kawai ya daina ganinta, ko awa daya bai yi da dawowa ba kuma bai ji motsinta ba bai kuma duba dakin nata ba, daga karshe kawai yayi dialing number Nihal tana dagawa ta gaishesa ya amsa yace "Ya makaranta?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin dawo ne?" Tace "Aa ya farooq yace min yana hanya" Khalil yace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Tace "Ameen" Shafa kansa yayi yace "Dama so nake ki sanar ma er uwarki ta shirya kayanta kala uku xa mu je can gida, kawai haka xa ki ce mata" A hankali Nihal tace "Baxa ka iya gaya mata ba kai kenan?" A takaice yace "Ehh" Tace "Toh Shkkn, ka bata wayar" yace "Zan kai mata yanzu" Nihal tace "Ohk" mikewa yayi ya tafi dakin Nihad ya bude kofar dakin, tana tsaye jikin window abun duniya ya tarar mata, har ta gaji da kuka, tun da garin Allah ya waye ruwa kawai take ta sha don ta gaji da cin indomie gashi babu kayan miya a gidan, yunwa take ji sosai, jin ya bude mata kofa ta juya a fusace tace "Malam ka daina shigo min daki kanka tsaye kamar wata matarka, idan ma wani abun ne baxa ka kwankwasa ka jira in fito ba?? Balle ma ni bana son kana min magana a gidan nan har abada" Kallonta kawai yake, ta murguda baki ta ci gaba da kallon tsuntsayen da take kallo ta window, khalil ya sa handsfree a wayar hannunsa yana daga inda yake tsaye yace "Gashi ki gaya mata" Nihal tace "Hello Nihad" Nihad ta wani tamke fuska tace "Menene??" Nihal tace "Abba yace ki shirya kayanki xa ku je can gidan" Nihad ta buda ido sosai tace "Don Allah da gaske?" Nihal tace "Ehh" Wani farin ciki ne ya rufeta, cike da murna tace "Ai kayana a hade suke ban ciro su a akwatin ba" Khalil bai bari Nihal tace komai ba ya katse wayar ya juya ya fita, kan kace me Nihad ta gama rurrufe akwatunanta ta ja su ta kai parlor gaba daya, ji take kamar mafarki wai xata koma gida, she sooo happy, da ido Khalil ya dinga bin ta, haka ta ja akwatunan duk da nauyinsu har gun mota sannan ta koma ta dauko handbag dinta, xata fita khalil dake ta bin ta da kallo yace "Duk wa enan kayan ina xa ki kai su?" Tayi masa wani shegen kallo tace "Ohk da so kayi in bar maka wasu ka dauka kaje ka siyar ka samu na xubawa a aljihu? To baxa a bari ba" tana gama fadin haka ta fice ta tafi jikin mota tana jiransa, bayan few minutes sai ga shi ya fito, cike da gadara tace "Bude min booth Malam" Ba musu ya bude mata booth din, ta daddage ta shigar da akwatunanta booth da duk karfin da Allah ya bata, back seat ta bude ta shiga ta zauna farin ciki fal ranta, ta lumshe ido tare da sauke wani ajiyar xuciya, at last.... Ganin ya ki tada motar ta ki ce masa komai, don ita kam baxata biyesa ba tunda dai ta samu xata koma gida, bayan few minutes ya sauka motar yaje ya bude gate, lumshe ido Nihad tayi bayan ya ja motar sun bar compound din, ya sauka ya kulle gidan sannan ya dawo cikin motar, Ta madubi yake ta kallonta kai kana ganinta kasan she is over happy, tun Nihad na tunanin traffic yake kaucewa ganin hanyar da suke ta bi har dai taga sun dau hanyar da baxae ta6a kai ka gidansu ba, ta dake tace "Malam mance hanyar gidan namu kayi ne ko kuma Shaye shaye ka fara? Ba ga can hanyar da xaka bi ba" Banza yayi mata, a mugun fusace tace "Tunda kai ba kurma bane nasan kana ji na, ka gaya min ta ina hanyar nan da muke bi xai kai mu gida??" Nan ma yaki tanka ta, mamaki ne ya cika Nihad ta dinga bin hanyar da kallo, to ina xai kai ta, bata kuma ce masa komai ba tana ta kallon ikon Allah, bayan tafiyar kusan minti arba'in taga sun shigo wani karamin gari da xa a iya kiransa da kauye, she was more than shock, wanda hakan yasa ta kasa ce masa komai, sae kallonsa take baki bude, a wani gida da aka xagaye da katangar kasa yayi parking bayan sun lula can cikin garin, ya kashe motar, sannan ya bude ya sauka, duk motar tayi butu butu da jan kasa, ga yara da ke ta bin motar tun shigowarsu karamin garin, har Khalil yayi parking, yaran duk suka kewaye motar suna murnan ganin mota, Haka Nihad ta dinga kallon inda suke with shock, khalil ya bude side dinta yana mata kallon cikin ido yace "Sauko" Ta fashe da wani matsanancin kuka tace "In sauko in yi me?? Wallahi baxan sauko ba" Duk da dariyar da ta basa haka ya dake ya hade rai yace "Baxa ki sauko ba??" Cikin kuka tace "Ehh, ina ne nan din da ka kawo ni da kake cewa in sauko?" A takaice yace "Garin mu!!! don ki tabbatar mu ma muna da gida, dolenki kuma ki sauko ki gaida iyayena, sannan adadin kayan da kika kwaso adadin kwanakin da xa mu yi a garin nan kenan" Ta fashe da kuka hankali tashe tace "Na shiga uku na lalace...." Ko sauraronta bai kuma yi ba ya xaga bayan booth ya hau sauke akwatunanta, ta gwale ido ganin yayi hanyar shiga cikin gidan da shi, kuka take kamar ranta xai fita tana cewa ta shiga uku ta lalace, tun da aka haifeta ita kam sai dai taga irin wajajen nan a Tv, dama da gaske akwai irin garin nan a reality?? Ba a dau lokaci ba sai gashi ya fito da wata dattijuwa tana washe baki ta taho ba ko takalmi a kafarta tana cewa "Lale lale" Sake baki Nihad tayi tana kallonta a tsorace, matar ta karaso kusa da mota tace "Sannu da xuwa, lale lale" Nihad ta hadiye wani abu da kyar tace "Ina yini?" Khalil dake tsaye gefen matan yace "Sauko" Da kyar tayi karfin halin saukowa daga motar, kana ganinta kasan a tsorace take, matar tace "Bismillah mu shiga ciki, lale" Tana jan kafa ta bi matar xuwa cikin gidan, Khalil ya bi ta da kallo yana wani side smile, sai da Nihad ta duka kafin ta iya shiga cikin gidan, nan taga hut a jere kusan hudu a karamin tsakar gidan, lkci daya tsikar jikinta ya dinga tashi taji ta fara jin sanyi kamar xaxxabi xae rufeta, Matar ta shiga wani hut din tace "Bismillah shigo ciki...." Nan ma sai da Nihad ta duka sosai kafin ta iya shiga hut din, banda karnin nono babu abinda hut din yake, sae da ta kara gwalo ido don ta tabbatar kasa ne kwance a dakin kamar waje, sai gadon kara an shimfida wani yamutsatsen zanin gado a kai, daga can gefe kuma kwarya ne sun kusa goma an jera, Matar ta dinga nuna ma Nihad gefen gadon karan wai ta xauna, cike da karfin hali Nihad ta xauna tana kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, dattijuwar ta fita daga dakin tana cewa "Bari a kawo maki ruwa" Wani hawaye ya xubo idon Nihad a hankali tace "Na shiga uku na lalace" da sauri ta goge idonta ganin wasu mata sanye da kaya irin na fulani sun tsaya bakin kofa suna gaisheta da fara'a, Da kyar tayi karfin halin gyada tana kirkiran murmushi tace "Nagode" Ai kuwa da wannan set din matan sun tafi sai wasu set din sun taho duk ana zuwa yi mata lale, sai ga dattijuwar da kwanon sha dauke da ruwa ta ajiye ma Nihad a kasa, Nihad ta dinga kallon ruwan ganin particles na ta swimming a ruwan, tun da aka haifeta bata ta6a ganin irin kwanon shan da aka xubo mata ruwan ba a ciki gashi duk yayi tsatsa, wata mata ce ta shigo rike da kwarya da nono a ciki, ta ajiye mata da wani karamin kwaryar me dauke da fura, tace "Sai ki dama hurar iya yanda kike so, idan kuma kina son suga sai a amso maki" Nihad dai ba bakin magana sai gyada kai, suka fita suka barta ita kadai da kudaje dake ta zaryarsu a dakin, a hankali ta fashe da kuka tana bin bukkar da kallo, who have she offend to deserve this in her life? Why is all this happening to her?? Khalil ya shigo ciki yana kallonta kasa kasa, cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka maida ni gida, wallahi baxan sake maka duk abinda nake yi ba...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga akwatunanta ana shigo mata da su dakin, da sauri ta share idonta tana bin yaran da suka shigo da akwatunan da kallo kamar idanuwanta xa su fito, Khalil ya jira har suka gama shigowa da su yace "Yauwa sannunku" Tana kallonsa ya tafi ya hau jera mata akwatunan step by step, ta rushe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace, me nayi maka kake min haka don Allah???" Ko tanka ta bai yi ba, ya dawo yana kallon fura da nonon yace "Ba lallai kin iya damawa ba, bari a dama maki" wata karamar tabarma da ya gani a dakin ya shimfida kasa sannan ya xauna ya tankwashe fararen kafarsa ya hau dama mata furan hade da nono a kwarya, kallonsa kawai take hawaye na sauka idonta tace "Don girman Allah kayi hakuri ka maida ni gida" Ba tare da ya kalleta ba yace "Sai kin gama sanye duk kayan dake akwatinki... Sannan nan din gidanmu ne, gidan iyayena ne dolenki ki xauna, adadin kayan akwatunanki adadin kwanakin da xa mu yi....." Hade kanta tayi da gadon karan da take zaune kai tana shessheka a hankali. Bayan ya gama dama furar ya dauka yana kallonta ya mika mata yace "Gashi" Dago kanta tayi tana kallonsa cikin rawan murya tace "Wallahi baxan iya xama a nan ba kaji na rantse maka" Yace "Xa ki iya idan kika kwana biyu, har ma xaki saba da kowa na garin" Ta fashe da sabon kuka tace "Na shiga uku wayyo Abbana" mikewa yayi ya ajiye mata furan a gefenta sannan ya fita daga bukkar, Nihad ta ci kukanta ta gode Allah, da ta ji alamar xa a shigo sae tayi maza ta goge idonta tayi feigning smile kamar ba komai, ga mutanen are so hospitable, sun ma rasa inda xa su sa ta, they are trying all they can to make her comfortable, hankalinta bai kara tashi ba sai da taga yamma yayi likis alamar dabb ake da magariba, gashi har sannan bata sake ganin Khalil ya shigo ba, Dattijuwar ta shigo tace "Fito kiyi alwala kin ji" Da kyar ta mike ta fito daga bukkar ta tafi inda aka nuna mata buta kusa da tulunaye uku, tana xuwa wajen Dattijuwar ta bi ta tace "Ko xa ki kama ruwa?" Ta girgixa kai da sauri, haka dai tayi alwala ta dawo bukkar matar ta nuna mata inda xata kalla tayi sallah, Nihad na ta xaune saman abinda tayi sallah, ita kam yau xata ga yanda ake kwana a wannan hut din, Wata budurwa ta shigo ta kunna mata wani fitila wanda da shi gwara babu, yarinyar na fita Nihad ta fara sabon kuka, wata mata ce ta shigo mata da tuwon dawa

Please Login or Register in order to submit comment