Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fiddo mata shi ma a masa auren tunda abun en aure aure ne" Aunty Hassana tace "Ke dai ki zuba ido mana, gwara shi auren zai yi, can kuwa kashe kudin xa ayi a banza babu zancen auren" Sallama aka yi bakin kofar duk suka yi shiru. Umma ce zaune dakinta tana magana da Nihal, Umma tace "Ke in zaki bude baki ki min magana ki bude, meye kuma ana maki magana kiyi ta amsawa mutane ciki ciki, ko baki da lafiya ne dai?" Nihal tace "Ce maki nayi ya turo min daxu" Umma tace "Nawa ya tura maki?" Nihal tace "Dubu hamsin" Umma ta tabe baki tace "Me dubu hamsin xai maki, ko dai baki ce masa kayan abinci xa ki siya ba?" A hankali Nihal tace "Na gaya masa" Shiru Umma tayi, don da Nihad ce ai dubu dari zai saka mata ko fiye da haka, shi sa fa ita bata jin ko dar akan abinda ta aikata, don akan Nihad sun ga abubuwa iri iri a wajen Abba a gidan nan ita da yaranta, haka ya kwashi kudi ya kai ta Maryam Abatcha dab da bikin Kamila bayan ga kayan gadon da kamila ta zaba ya ki siya mata wai yayi kudi, wanda a lokacin ko dubu dari takwas kayan gadon basu yi ba, tana ji tana gani kuma ya tura mata Nihal dinta Zaria, kuma ko nunawa a fuska Umman bata yi ba balle a gane taji haushi, Umma tace "Toh ai Shikenan, kawai ki kira farooq ko Usman su kara maki, ita er son ma ko biyar ta daina samu ai yanzu, wa ma yasan isilinta" Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ke in fa baki da lafiya ne nasanki da zurfin ciki ki dawo gida a maki treatment kar kije ki jaza min jaraba, lafiyarki kuwa?" Nihal tace "Lafiya ta kalau ni" Umma tace "Toh ai shikenan, Kina da labarin Nihad?" Nihal ta girgiza kai tace "Aa" Umma tace "Allah sarki, kamar ba ayi ta ba, ko ana wani kauyen yanzu kuma, yanzu kenan wayar dreban baya shiga?" Nihal tace "Ehh" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, ya wannan saurayin naki ɗan senator, in ji dai kin ci gaba da kulasa banda walakanci ko?" Nihal tace "Eh" Umma tace "Yana zuwa wajen naki?" Nihal tace "Eh" Umma tace "To madallah, ki dai kula banda cewa xaki bi sa ko ina komin takuraki da zai yi, kuma ban amince da tadi a mota ba, sannan iyakan ku cikin makaranta, ko wajen makaranta ban yarda ki bi sa ba, banda dai mata sun zama abinda suka zama da sai ince ko hira xaki fita in ya zo ki dinga fita da roommate dinki wannan da kika raka garinsu, to yan matan ne sai su maka snatching" Ita dai Nihal bata ce komai ba, Umma tace "Ki dai kula don Allah kin ji Nihal?" Nihal tace "Toh" Umma tace "Naga kamar bacci kike ji sai da safe" a hankali Nihal tace "Allah ya tashe mu lafiya" Umma tace "Ameen auta" Daga haka ta katse wayarta, ta shiga neman number Husnah, ita kam tana son taji wani hali Nihad take a kauyen da dreba ya kai ta, yana fara ring Husnah ta daga, Bayan sun gaisa Umma tace "Kwana biyu ko leko mu kun daina" Husnah tace "Wallahi kuwa, nima ai banji dadi ba kwanaki, na ma kwana biyu a asibiti da kamar xa a min aiki a ido sai kuma Allah ya takaita, wallahi ban dade da fara fita ba yanzu haka, don idan na fita cikin rana idon kamar ya cire don azaba" Umma tace "Subhanallahi, to Allah ya tsare, Allah ya kara lafiya, gashi bamu da labari ai da ko dubaki ne sai in zo inyi" Husnah tace "Ameen Umma, ya mutanen gidan?" Umma tace "Lafiya lau wallahi, nace dai yau bari in kiraki in ji ko kina ji daga wajen kawarki, kamar anyi ruwa an dauke yau wata daya kenan ni Sumayya" Husnah tace "Wallahi jiya jiya su Naf suka gama wannan zancen, Umma kinsan wani abun mamaki kuwa??" Umma tace "Aa me ya faru?" Husnah tace "In gaya maki kafin su bar garin nan ina kwance asibiti sun je dubani, turanci a bakin dreban nan kamar bature" Umma tayi shiru, can tace "Turanci kuma?" Husnah tace "Wallahi" Umma tace "Aa to ai dama yace yayi sakandari, dama dole xai iya turanci ai in dai ba dakiki bane, amma tabbas iyakarsa dai sakandari" Husnah dai tayi shiru, can tace "Yanzu ko Abba baxa kice ya tuntubi...." Da sauri Umma tace "Aa ko xancen su bai so gaskiya, yanzun nan hawan jininsa sai kiga ya tashi, shi yasa na daina gaba daya, dama wai inji inda suke ne" Husnah tace "Shekaranjiya saurayin Nihad din ɗan janar jikamshi ya kira Naf asking for her whereabout, muka ce ai mu ma bamu sani ba gaskiya..." Umma tayi shiru, can tace "Shikenan dai, shi banda abunsa ko da ba a mata aure ba ta ina iyayensa xa su amince da auren wata Nihad, ai da ko Aminata ce sai ya nema tunda ita Nihal na da wani saurayi, ko ɗan minister ne ko sanata ni dai na manta yanda tace min, kuma yana sonta sosai sai kinga kudin da yake kashe mata, don da bata ma kulasa ni ke ta tursasata ta dinga kulasa bata san waye mijinta ba, kwanaki har mota yace xai bata taki, nima kuma ban goyi bayan hakan ba" Husnah tace "Gaskiya kam" Umma tace "Shikenan, sai dai yanda ta yiwu" Husnah tace "Muna nan dai muna binciken inda xa mu samota in sha Allah" Umma tace "Toh don Allah ku kokarta" Nan suka yi sallama Umma ta katse wayarta. Da safe Mimi ta gama shiryawa zata tafi makaranta wajen karfe goma, bayan ta sallami Mami ta kalli Khalil dake parlon yana danna wayarsa tace "Yayanmu sai na dawo" ya kalleta yace "Isn't ur frnd going to lectures?" Tace "I met her lying down tace baxata ba, i don't think she is even okay" Bai ce komai ba har ta fita daga parlon, Bata jima da fita ba Noor ma ta shigo parlon ta je ta sallami Mami sannan ta fito, tana kallonsa tace "Yayanmu amma dai yau zaka je wajen Nadeeyah ko? You know u didn't try yesterday, she made all u requested but u ended up not coming, you just spoilt her mind" Yace "Zan je" Tace "Better, cause she is so sad" Shi dai bai kara ce mata komai ba har ta fita daga parlon, wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Nihal ce, tun jiya da daddare ya kirata to check on her ya ji ta on another call kuma bata kirasa ba sai yanzu, Bayan sun gaisa jin she sounds dull yace "Are you okay Nihal? You sound stressed out" Nihal tace "I am fine, i just woke up, ya Nihad?" Yace "Alhamdulillah, yaushe za ku fara exam?" A hankali tace "There is still time, CA muka gama yanzu" Yace "Are you sure baxa ki je gida ko weekend ba so that u can get enough rest? Naga kamar wannan semester din da zafi" Nihal tace "Toh xan je" Yace "Or will you like to come over to ur sister?" Nihal ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "I will love that" Yace "Ohk then, i will talk to farooq about it later, idan ya amince sai in zo Zarian gobe in daukeki" a hankali tace "Okay, i am grateful" Yace "Take care dear" Tace "Sure" Daga haka ya katse wayar, Mami ta fito, Khalil na kallonta yace "Mami are you going out?" Tace "Ehh xa mu fita da su Amina, xa mu je wani gaisuwa ne..." Yace "Ohk, are you staying long" Tace "Not at all, but i might branch Hajiya Safeenah's place" Yace "Ohk Allah ya tsare" Tace "Ameen, ina da magana da kai idan na dawo" Yana kallonta yace "Maganar me Mami?" Tace "Sai dai na dawo" Ya bi ta da kallo har ta fita daga parlon, yana jin fitarsu daga gidan with escort bayan kusan minti sha biyar, mikewa yayi ya fita daga part din Mami. Dakinsa ya koma ya kwanta, deep in his thought, kiran Nadeeyah ne ya shigo wayarsa, ya dinga kallon wayar har ya katse, can ya dauka ya kirata, kamar me bacci yace "I will call u later Nadeeyah, i am still on bed..." Jin bata ce komai ba yace "Hello" Tace "Ohk" Katse wayar yayi ya mike zaune, bayan kusan minti biyar ya kalli agogon dakin dake nuna karfe goma da rabi, tashi yayi ya dau wayar Nihad dake gaban mirror dinsa ya fita, daren jiya Ayman ya kirata yayi sau biyar, yau da safe ma still sai da ya kira duk Khalil na kallon kiran, direct ya nufi dakin da Nihad take ya bude kofar ya shiga, kwance ya sameta ta rufe har kanta da duvet, ya karasa ya cire duvet din ya jefa mata wayar a gefenta, fuska daure yace "Kirasa yanzun nan kice kada ya sake kiranki, do that immediately...." Ko bude ido Nihad bata yi ba balle ta kulasa, ya wani hade rai yace "Ba dake nake ba?" Tashi tayi ta sauka daga kan gadon zata nufi bandaki ya fizgota, ta fashe da kuka tana turasa da dashashiyar muryarta tace "Ni ka kyaleni wallahi, kai me bakinka yake yi da baxa ka gaya masa da kanka ba sai ni??" Yana mata wani kallo yace "Ni kike gaya ma haka?" Cikin tsawa tace "Na fada maka din, tell him ur self and stop bothering me, ko kuma ka kira Aunty Maryam ka gaya mata ita ta gaya masa" Sai kuma ta fashe da kuka ta durkushe wajen, tayi me isanta duk yana kallonta sannan ta mike ta figi Hijab dinta zata fita ya fixgota, ta buge hannunsa cikin rawan murya tace "Ni ka kyaleni, baxan sake kwana a gidanku ba, gwara in tafi wajen grandma dita nasan she will accept me, it's not as if I don't have anywhere to go...." Yana mata wani kallo yace "Da izinin wa zaki je wajen nata??" Cikin kuka tace "Wallahi idan baka barni na tafi ba sai na gaya ma kowa a gidan an mana aure da kai, kaji har na rantse" Da mamaki yake kallonta baki bude, xata kwace kanta ya riketa gam yace "Ohk, kinsan an mana auren kike kula wani farin katon banza a waya har kike ce masa you love him too?" Ta hadiye kukan da take ta kallesa tace "Kai kuma da kake kula wata farar katuwar banza fa? Sai ni ce baxan kula wani ba...." Duk da dariyar da ta basa ya kara murtuke fuska yace "Ohh kika ce sai kin kulasa?" Tace "Kuma baka isa ka hanani ba, don bansan da auren kowa a kaina ba, i neva accepted ur marriage even for one second, nasan kuma da shi ne he is too gently and calm to raise his hand on my face, and dole ka sakeni in auresa because i am beginning to love him...." Kuka take sosai tana son kwace kanta amma yaki saketa yana kallonta babu ko kiftawa, ta fara kai masa duka a kirji ganin ya ki saketa, lokaci daya ya dauketa cak ya nufi saman gado da ita ya jefata kai, ta hadiye kukan da take tana kallonsa tana komawa baya ganin yanda ya daure fuska yace "I will show you ni mijinki ne yau, and you have nothing to do about it" Kawai taga ya juya ya yaje ya sama kofar dakin key, ta yi wani tsalle xata shiga bandaki, yayi hanzarin fizgota kafin ta shiga.....






Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah






Ur evidence via 07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


48




Washegari wajen karfe tara na safe kiran Farooq ya shigo wayar khalil dake bacci, bude ido yayi a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, ganin Farooq ne ya daga ya kai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Pls kwanakin baya kace min kuna gaisawa da Nihal, when last ku ka yi magana da ita on phone?" Khalil ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Not too long mun yi magana da ita, ta turo min waec result, birth certificate, i mean all those stuffs saboda makarantar da nake nema ma er uwarta...." Farooq yace "When was that pls?" Khalil yace "It was just last week, Though bana iya reaching dinta a line dina so i used my other line shine na kirata muka yi magana, hope all is well?" Farooq yace "For 2 days yanzu ba a samunta a waya, i just arrived zaria but bani da contact din any of her Coursemate as i am talking to you now...." Khalil ya mike zaune yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, or did she lost the phone?" Farooq yace "Ko ma haka ne ai ya kamata tayi using ko wayar Coursemate dinta ta kira ta sanar, her problem is that she neva get close or mingle with frnds" Khalil yace "Haka ne.... I am hoping she is fine in sha Allah" Farooq yace "Shikenan, sae mun yi magana, thank you" Khalil yace "In sha Allah... Nima xan yi ta trying line dinta" daga haka suka yi sallama, khalil yayi amfani da daya wayarsa yayi dialing numberta don bata yi unblocking dinsa ba har sannan daga main line dinsa, shima yaji wayar a kashe, he felt a bit tensed, then what happened to her? Tambayar da yayi ma kansa kenan, after trying her line for like 3 times ya ajiye wayar a hankali ya sauka daga saman gadon ya shiga bandaki. Har kusan karfe sha biyu Khalil na trying line din Nihal also, he is just restless, and he prays she is okay... Yana zaune parlon Mami wajen karfe uku Mami ta fito daga dakinta ganinsa tace "Dama kana nan har yanzu?" yace "Eh" Mami tace "Wai har sun kai kudin, ai kunyi magana da ita ko?" Khalil ya daga kai da sauri yace "Ohh really, ni nama manta..." Mami tayi masa wani kallo da mamaki tace "Ka manta? I don't understand ka manta" Yace "Wallahi i am disorganized ne gaba daya yau Mami" Mami tace "Me ya faru?" Da har zai gaya ma Mami what is happening sai kuma ya fasa cause bai san ta sigar da zata dau lamarin ba, bai san daga wani perspective zata yi viewing issue din ba, kar tayi tunanin gidan ba tarbiya or something like that, Mami tace "Kayi shiru" Ya sauke ajiyar zuciya yace "I am having a terrible headache tun dazu" Da damuwa Mami tace "Subhanallah, toh Allah ya sauwake, ka sha magani?" Yace "Yanzu xan je in sha" Tace "Do so immediately pls, ko da abinda kake so a girka maka?" Yace "No, i am okay" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita other parlor din, dai dai nan Mimi da Nihad suka bude kofar parlon dawowarsu kenan daga makaranta, Hijab ne har kasa jikin Nihad with Nikab, she looks so cute in them, Mimi tace "Yayanmu ina yini" yace "Lafiya lau" Nihad ta sunkuyar da kai ba tare da ta kallesa ba slowly tace "Ina yini" ya ɗan kalleta yace "Lafiya lau" Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, suka karasa can parlon, Mimi ta zauna saman kujera looking very tired ta gaida Mami, Nihad ma ta gaisheta, Mami tace "Sannunku da zuwa" Mimi tace "Mami Noor bata dawo ba har yanzu?" Mami tace "Tana gidansu Nadeeyah, kinsan yau aka kai kudin" Mimi ta zaro ido tace "Seriously? Yaushe aka sa auren?" Mami tace "4 weeks in sha Allah" Mimi tace "Awwnn maa sha Allah, Allah Ubangiji ya nuna mana lafiya, nasan it won't exceed that... I am so happy for the love birds" Mami dai ta juya zuwa dakinta ta dalilin wayarta dake ring, Nihad dake ta kallon Mimi ta mike daga saman Carpet da ta zauna, ta dawo gefenta ta cire Nikab din fuskarta tana kallonta tace "Who is getting married?" Mimi ta wara ido tace "I thought i told u yesterday, Yayanmu is getting hitched, yau aka kai kudin aurensa with sister Nadeeyah...." Tana murmushi ta kare maganar, Kallonta Nihad take babu ko kiftawa, Mimi tace "U remember me telling you?" Nihad ta sauke idonta tace "Sure" Tashi tayi tace "Xan je inyi wanka" Mimi ma ta mike tace "I too, i need warm shower" Tuni Nihad ta rigata ficewa daga parlon ta nufi dakin da take, ta fi minti 2 tsaye bakin kofar dakin bayan ta shiga ciki, can ta karasa inside of the room ta zauna gefen gado a hankali.... Khalil na komawa dakinsa yaga miss calls din Nadeeyah har hudu a babban wayarsa, ya zaune gefen gadon ya jingina bayansa da pillow yayi dialing numberta, yana fara ringing ta daga, a hankali yace "How are you Nadeeyah?" Kamar xata yi kuka tace "Why ain't you picking ur calls, ina ta kiranka no response" Yace "Bana kusa ne" Tace "Ta yaya zaka ce min baka kusa, i called almost 2 hours ago" yayi kasa da murya yace "Kina da son korafi da yawa Nadeeyah, why?" shiru tayi, yace "Kinsan baxan ƙi daga kiranki just like that ba ai, so why not believe bana kusa and have rest of mind" Nan ma bata ce komai ba, yace "Hello, nasan kina ji na" a hankali tace "Shikenan, Allah ya baka hakuri, only called to say Hi, na ji ka shiru all through" yace "Ina parlon Mami tun daxu, i am sorry i missed your call, it wasn't intentional....." Ta gyada masa kai kawai bata ce komai ba, yayi murmushi sanin da kyar if she is not in tears already, yace "Karfe biyar xan zo in sha Allah, ki min wannan drink din da pancake me dadi da kika min the other day, immediately after Magrib kuma we will be going out for shopping" A hankali tace "Ohk" Calmly yace "I love you" Tana goge hawayen idonta tace "Love you too" Yayi murmushi kawai ya katse wayar. Khalil ya sake trying wayar Nihal for the countless time but a kashe, as at 2pm dazu ya kira farooq yaji if there is any positive news, farooq yace har yanzu ba labari, ya ma je har department dinsu wajen malaman, and an dubo few of her Coursemates sunce ai tun jiya bata yi attending lectures ba, wannan batu ya sa hankalin Khalil ya tashi. Biyar saura minti sha biyar Khalil ya shirya zai je wajen Nadeeyah kamar yanda yayi mata alkawari, yana fita ya nufi bangaren Mami xai je yayi mata sallama, a hanya ya hadu da Mimi tace "Yauwa yayanmu pls kana da paracetamol a dakinka?" Yace "Check my room, who is taking paracetamol?" Tace "Neehad ce tace min kanta na ciwo, so i want to give her to take" Yace "Where is she?" Tace "tana daki" Bai kuma ce mata komai ba ya karasa parlon Mami ya zauna, after like 15 minutes Mimi ta dawo parlon ya daga kai yana kallonta, tace "I have given her ta sha, yayanmu fita zaka yi kayi dropping dina gidansu frnd dita Aziza pls? Today is her birthday...." Yace "Aa, ki je driver ya kai ki" Tace "Ohk, tot u were going out" Ta figi jakarta don dama ta shirya tace "Bye" Yace "Wait kin gaya ma Mami?" Tace "Yeah i told her kafin su fita da Mom, i will be back in sha Allah after Magrib" Yace "Ohk, stay safe" murmushi tayi masa ta gyada kai sannan ta fita da sauri daga parlon, wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya duba ganin farooq ne ya daga da sauri, farooq yace "I just reached her minutes ago, the stupid girl wai ta raka wata roommate dinta garinsu bata da lafiya a nan Zaria, i still don't get dalilin da yasa bayan ta rakata bata dawo a ranan ba, wai kuma babu wuta and bata je da power bank ba...." Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh Alhamdulillah, but you have to take it easy pls, kasan ba halinta bane, baxata zauna haka kawai babu dalili a can ba" Farooq yace "That's so stupid of her, tasan mutane nawa ta daga ma hankali a can gida, har yanzu maganar da nake maka bamu sanar ma Abba ba, we don't even have the courage to do so, and God being so kind dama basu waya da shi kamar yanda yake da Nihad, sai in tana bukatar abu suke waya da shi" Khalil yace "Take it easy pls, it's well in sha Allah" Farooq yayi masa sallama ya katse wayar, sauke ajiyar zuciya Khalil yayi don sai yanzu yaji hankalinsa ya kwanta, Nihal have a special place in his heart cause she's one of the kindest soul he have ever met, ita ma baxai taɓa mance kindness dinta toward him ba, dialing numberta yayi ya fara ring, bayan some seconds ta daga, a hankali tace "Hello" Khalil yace "Me yasa kika yi abinda kika yi Nihal?" Ta fashe da kuka kamar jira take bata dai ce komai ba, yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta amma ta kasa cewa komai, yace "Nihal" tayi karfin halin cewa "Na'am" Yace "Don't try that again pls, idan ma zaki je wani waje ki sanar before doing so, ur parents trusted you so well shi yasa har suka bari kika yi nesa da su kike karatu, ita er uwarki me gathering bad friends ai kinga they didn't allow her move an inch from kano" Nihal dai kuka kawai take bata ce komai ba, a hankali yace "Kin ji abinda nace maki?" cikin rawan murya tace "In sha Allah" yace "Take care of ur self pls" a hankali tace "Ka gaishe min da Nihad" Yace "I will in sha Allah" Daga haka ya katse wayar ya mike ya fita daga parlon Mami, dakin da Nihad take ya nufa ya bude kofar dakin gently, kwance ya sameta ta rufe har kanta da duvet, ya karasa bakin gadon ya janye duvet din a hankali yana kallonta, she is just wearing a short gown, ta bude ido da sauri, suna hada ido ta hade rai ta juya, yace "Ni kika ma wannan kallon?" Ta fashe da kuka ta sake juyowa tace "Ni ba da kai nake ba" Yace "Tashi zaune" Ba musu ta mike zaune, zai cire duvet din daga jikinta ta rike da sauri tace "Ni ban sa kaya ba" ya daure fuska yace "Sake" A hankali ta sake ya cire ya mayar gefe, ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace "What's wrong with you?" Taki ce masa komai, sai kuma hawaye ya hau zuba idonta, Kallonta kawai yake ba ko kiftawa, ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, bai san sanda ya zauna gefenta ba ya dagota da mamaki yace "Are you okay?" Kuka kawai take ta ki cewa komai, ta sauke kafanta daga saman gadon zata sauka ya jawota ta fado jikinsa, sai ta kara sautin kukanta, ya rungumeta yana kallonta amma bai sake ce mata komai ba, ta gaji don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya tana shaƙar kamshinsa, for almost 10 minutes suna nan a haka, jin ta sakar masa jikinta gaba daya tana sauke numfashi a hankali ya sunkuya yana kallon fuskarta, bacci yaga tana yi, ya dinga kallon lips dinta for almost a minute, sai kuma ya dago a hankali ya jinginar da kansa jikin gadon ya lumshe idonsa.... Da sauri khalil ya bude ido ta dalilin wayarsa da ke ring, he realized he just slept off also, shi da baya baccin rana balle na yamma, ya kalli Nihad dake kirjinsa tana ta bacci kamar warce ta samu lafiyayyen katifa, ya ciro wayarsa da sauri jin ana sake kiransa, yaga Nadeeyah ce, kallon agogon wayar yayi yaga har shidda da minti arba'in just few minutes to magrib, he was shocked and surprise at the same time, ya sake kallon Nihad sai bai daga wayar ba har ya katse, still Nadeeyah ta sake kira, Nihad ta bude idonta da

Please Login or Register in order to submit comment