Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar wajen, Nihad na isa tashan bayan ta ba mai adaidaita sahu kudin ta shiga ciki, ai ko ta samu mota da xai kama hanyar kano a lokacin, nan ta tambayi nawa ne kudin mota aka ce mata dubu takwas, tayi kuri da ido ta kasa ce masu komai don dubu uku kadai ne a hannunta, can ta koma gefe ta tsaya kamar munafuka, dreban motar yace "Hajiya nawa xaki bada?" Tayi shiru sai kuma tace "Ni bani da kudi amma idan na baka wannan xaka karba?" Tana magana tana kokarin ciro dankunnen kunnenta, duk da akwai haske a wajen sai da mutumin ya kunna fitilar wayarsa yana haska ɗan kunnen da kyau, can ya kira wani abokin aikinsa shi ma ya duba, Mutumin na kallonta yace "Ai kawai ki fadi nawa zaki siyar ba cuta ba cutarwa sai a baki kudinki ki cire kudin mota" Nihad tace "Ai ban san nawa zaka siya ba" Yace "Kin siyar dubu talatin?" Nihad dai tayi shiru sai kuma tace "Toh" Mutumin yace "Toh ina zuwa" Can sai gashi da cash din dubu talatin ya mika mata, Nihad ta amsa ta kirga dubu takwas ta basa, sannan ta shiga motar wanda duk maza ne a ciki, suka bar mata jikin window ta zauna.... Mami ce tsaye parlor tare da Mum din Nadeeyah suna kallon Khalil dake zaune saman kujera ya ki ce masu komai, kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, Mimi sai hawaye take, Noor dai na zaune saman kujera don tare da Mami suka zo gidan, Nadeeyah kuma na tsaye can kusa da dinning area, Mami tace "Magana fa nake maka ka min shiru Khalil, ina kake tunanin yarinyar mutane zata tafi da daddaren nan? Lokaci fa na wucewa" Mikewa yayi without looking at them yace "Nima ban sani ba" Daga haka ya nufi kofa, Nadeeyah ta bi sa da kallo har ya fice daga parlon, Mumy ta saki salati tace "Wallahi duka duka ko minti goma fa basu yi da shigowa gidan ba, har nake tambayarsa tana ina da naga ita bata shigo parlon ba yace tana waje tana waya da yayanta, ina yar mutane ta shiga ni Safeenah" Mami dai ta kasa cewa komai don hankalinta ya tashi ita ma, where are they going to start from, kasa ci gaba da tsayuwa tayi ta nemi kujera ta zauna tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta.... Ko barin Abuja Nihad basu yi ba bacci ya dauketa a motar, Khalil bai jin ya taɓa shiga tashin hankalin da ya shiga a wannan lokacin, ko abinda Abbansa yayi masa bai daga masa hankali irin wannan ba, ganin abun yake kamar a mafarki fa, ya ma rasa wani tunanin zai yi, sai da yaga karfe goma yayi tashin hankalinsa ya fara fitowa sarari, tun takwas su Mami suka koma gida don barinsu ma yayi a gidan yayi wucewarsa, amma saboda yanda hankalin Mum din Nadeeyah ya tashi haka ta sake bin su gidan tare da Nadeeyah, Duk suna zaune parlorn Mami wajen karfe goma da yan mintuna khalil ya shigo parlon ta dalilin kiran da Mami tayi masa, Mami tayi karfin halin cewa "Nace ka kira gidansu ka ki, nace ka kira yayanta ka ki, to wai ya zan yi da kai, in ma baxa ka kira ba ni ka bani numbersu mana, wannan wani irin tashin hankali ne" Khalil that was trying all possible means to be calm yace "In kirasu ince masu me Mami? I should call and tell them I can't find their daughter cikin daren nan? In kirasu ince masu an kasa rike yar su a gidanmu saboda kanwar Abbana tace baxata zauna ba kuma Mamina bata da abinda xata iya yi game da hakan? Mami ni na zata akan yarinyar nan sai inda karfinki ya kare, i thought zaki yi repaying good deeds din da iyayenta suka min ta hanyar riketa just like su Mimi, ina ce you will always be there for her, if not for her family i would have been depressed by now, right in front of u Abbana sent me away from his house and u couldn't do anything about it, kina gani na bar gidan nan baki iya yin komai a kai ba, naje inda suka rikeni ba tare da sun san ni ba har suka damka min amanar dukiyarsu amma ta haka za muyi repaying dinsu mu kasa rike masu tasu er?" Mami dai kallonsa kawai take ta rasa abinda xata ce amma duk jikinta yayi sanyi, juyawa yayi ya fice daga parlon Nadeeyah ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Hajiya Safeenah ta nemi kujera ta zauna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wajen karfe biyu da rabi na dare Nihad suka shigo garin Kano, tayi bacci har ta gode Allah a hanya, mamaki ya cikata ganin adaidaita har sannan a tasha, tana kallon wanda ke tambayarta inda xata tayi shiru, tana tunanin ko dai kawai taje hotel ta kwana tunda tana da kudi kuma tasan prices din hotels na Kano, nan ta gaya masa hotel dai dai kudinta ya tafi da ita kuwa, tana sauka ta basa kudinsa ta shiga ciki, ta biya kudin daki aka bata makulli ta wuce zuwa dakin, wanka ta fara yi a bandaki sannan ta dauro alwala tayi magrib da isha ta kwanta, amma ta kasa bacci sai juye juye kawai take, babu wanda ke ranta kuma a lokacin sai Nadeeyah, she just hate her with passion, bata son ganinta kwata kwata, da tasan gidansu zasu je da tun daga gidansu Khalil ta gudu don ko haduwa da ita bata so har cikin ranta.... Karfe takwas saura na safe Nihad ta tashi daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, ta fita waje zuwa supermarket dake kusa da hotel din ta siyo brush da maclean ta koma ciki, kafin karfe tara har ta gama shiryawa ta fito ta tare adaidaita yana tambayarta inda xata tayi shiru, don sai a sannan gabanta ya fara faduwa don bata san me xata je ta tarar a gida ba, kilan ma Abba ya koreta idan taje, amma a haka ta dake ta gaya masa inda xata sannan ta shiga adaidaitan a sanyaye, ya kama hanyar gidansu, tunda suka dau hanya gabanta bai daina faduwa ba, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso gidan, at first kasa sauka tayi daga cikin adaidaitan ganin ya juya yana kallonta, tayi karfin halin sauka ta basa kudinsa ta nufi gate tana tafiya a hankali, she is so afraid, daurewa kawai take, bude gate din tayi taga Aminu zaune bakin gate da er radio a hannunsa, yana ganinta ya zare ido ya mike da sauri yace "Hajiya" Ta ɗan yi murmushi tace "Aminu" Bakin Aminu har kunne ya dinga mata sannu da zuwa, sai kuma ya nufi waje da gudu duk zatonsa tare take da Khalil, Nihad dai ta ci gaba da tafiya gabanta na faduwa ganin motar Abbanta a parking space, taga motar ya Usman ma alamar yana gidan, har ta isa balcony dinsu ta kasa daga kafarta da kyau, tsoro ne fal zuciyarta, ta kusa minti daya a tsaye kafin ta murda kofar a hankali ta shiga ciki tana kallon parlon, Umma ta fito kitchen kenan rike da breakfast din da ta hada ma Nihal tayi sororo bakin kofa tana zaro ido tace "Wa zan gani kamar 'ya ta Nihad?" tun da Nihad ta mata kallo daya ta dauke kai ta nufi bangaren Mumy tana tafiya a hankali, Umma ta buda baki with shock ganin abinda tayi mata ta bi ta da kallon mamaki, tuni Nihad ta bude kofar Parlon Mumy a hankali ta shiga, Mumy ta fito dakinta kenan tayi ido hudu da Nihad, still tayi bakin kofar dakin tana kallonta with surprise, Nihad ta tafi da gudu ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy dai ta kasa motsi, can tayi karfin halin dago kanta tace "Daga ina?" Nihad na Murmushi tace "Gida Mumy" Mumy tace "Ke da wa??" Nihad tace "Ajiyeni yayi yaje ya dawo" Bude kofar Parlon aka yi duk suka daga kai, Umma ta shigo, Nihad na ganinta ta shige dakin Mumy ta kulle kofar, Umma tayi kasake a inda take tsaye, Can tayi karfin halin cewa "Ko ba Nihad bace?" Mumy ta kirkiri murmushi tace "Ehh wallahi, yanzun nan ta shigo na ganta nima" Umma tace "Allah sarki, to sannunta da zuwa, ina jin ta gaji ne" Daga haka ta juya ta fita daga parlon, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri tana kallon Nihad tace "Me yasa kika yi mata haka ta zo ganinki Nihad? Why did u leave the parlor" Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mumy tace "Why didn't u greet her?" A hankali Nihad tace "I need rest, and beside ke na zo gani" Mumy dai ta kasa cewa komai ta dinga kallonta, Nihad tace "Mumy ina jin yunwa" A hankali Mumy ta juya ta fita daga dakin don kawo mata breakfast, Mumy na fita ko minti uku ba ayi ba Nihal ta shigo dakin....








Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah






Ur evidence via 07087865788
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖 NIHAAD 💖


51




Nihad ta ki yarda su hada ido da shi, ya dinga kallonta don duk a tsorace take, ya kamo hannunta zai yi magana aka bude kofa Mami tayi ta fito daga dakinta, Khalil yayi saurin tashi daga kusa da ita ya nufi kujera, Mami ta kallesa ta kalleta, ita dai Nihad kanta na kasa, Mami tace "Ya ciwon kan? Kin sha magani?" Nihad still bata dago kanta ba tace "Na sha" Mami tace "Toh Allah ya sauwake, je kiyi kwanciyarki kawai...." Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, Mami na kallon Khalil fuska daure tace "Ban gane ma'anar shisshige ma yarinyar nan da kake ba Khalil?" Ya zaro ido da sauri, sai kuma ya xauna yace "Mami shisshige mata kuma? I just saw she is sick and...." Mami ta katse sa rai bace tace "If she is sick ni baxan iya mata abinda ya kamata ba sai kai? Sannan who did she tell she is sick? i see no reason da xai sa kana shiga dakin da take at the first place ita ba muharramarka ba, meye ma'anar hakan? to gaskiya bana so, don't ever try it again, idan wani abu ya dameta ta zo ta gaya min bana son wannan shige matan da kake we are not pagans" Khalil ya mike yace "Mami ai baki taɓa gani na...." Dakatar da shi tayi tace "Bana son jin komai, na dai gaya maka abinda xan gaya maka, khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, ta juya tayi komawarta cikin dakinta, a hankali ya koma ya zauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, kansa bai taɓa kullewa yanda ya kulle ba yanzu, ya ga alama it's not going to be easy, it doesn't look Mami will take things easy kafin aje ga Abbansa, sai a sannan ya fara tunanin he wished bai boye ma Aunty Maryam komai ba tun farkon dawowarsu, may be she will have understood him, yasan yanzu its too late ita kanta baxata fahimcesa ba yanxu, it's just too late, bayan wani lokaci Mami ta fito daga dakinta ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofa zata fita, ya jima bai ga ta hade masa rai haka ba, wannan yasa jikinsa yayi sanyi, he don't think she will ever support him in any way, Mami xata bude kofar parlon aka bude before her, hakan yasa ta daga kai suka yi ido hudu da shi, da fara'a tace "Aa, Aliyu yaushe ka dawo?" Yace "Not too long Mami" Khalil ya wani murtuke fuska yana danna wayarsa, Mami ta koma ta zauna tana kallon Aliyu tace "Sannu da zuwa, ai ban san ka dawo ba wallahi" Ya zauna saman kujera yace "Ina yini Mami" Tace "Alhamdulillah, ka dawo lafiya?" yace "Lafiya lau Alhamdulillah" Mami tace "To maa sha Allah, gaskiya ka dade sosai wannan karan" ya ɗan yi murmushi da iyakarsa baki yace "Na shigo ne in gaisheki dama...." Tace "Toh Nagode Aliyu, i will be coming downstairs later, you are welcome dear" Yace "Alright" Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Mami ta kalli Khalil da damuwa tace "Why didn't u speak to him Khalil?" Khalil kamar jira yake yace "Why will i speak to him Mami?" Mami ta girgiza kai tace "No.... gaskiya bana son haka, tunda ya shigo har nan ya gaisheni menene a ciki don ka gaisa da shi? Me yake yi som" Khalil yace "Am i his mate da xan fara gaishesa Mami? or da can ya saba shigowa gaisheki a nan idan ba hypocrisy ba, look Mami i am begging you to stop forcing me do what isn't necessary, babu abinda ya hadani da su" Mami tace "No Khalil, me yasa kake daukan komai da zafi a rayuwarka ne? ko kaki ko ka so ɗan uwanka ne fa" Khalil ya mike yace "Ba ɗan uwana bane ban hada komai da shi ba..." Mami ta daure fuska tace "Kace min ba ɗan uwanka bane" Yace "I want to excuse my self plss" Kallonsa Mami ta dinga yi, yace "I said i want to excuse my self Mami" Mami ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ohk" Juyawa yayi ya fice daga parlon a fusace, Mami ta girgiza kai irin zuciyar Khalil na damunta, he is the one always causing problem for himself, sai yace baya tsoron kowa, hatta mahaifinsa tasan yanda duk suke shakkarsa shi baya yi, shi yasa yana ce masa ya bar masa gida ko minti goma bai kara ba a gidan yayi gaba, bayan few minutes ta girgiza kai ta mike ta fita daga parlorn ta nufi dakin da Nihad take don ce mata ta hada kayanta, Khalil yayi stiff a bakin kofar dakin don zai fito kenan sai ga Mami, Kallonsa Mami take babu ko kiftawa ta ma kasa ce masa komai, confidently yace "I left my phone in here, so i came to pick it up" Daga haka ya bar ta tsaye bakin kofar without waiting for her reply, ta bi sa da kallo, Can ta shiga cikin dakin, Nihad na kwance ta rufe ido kamar me bacci, Mami ta dinga kallonta for some seconds, sai kuma ta karasa kusa da gadon, Nihad ta bude ido da sauri, ganin Mamin ta mike ta zauna tana murza idonta, Mami tace "Are you feeling better now?" Nihad tace "Alhamdulillah" Mami stood for almost a minute looking at her, Sai kuma ta juya ta fita daga dakin. Khalil na komawa bedroom dinsa yaga miss calls din Farooq, zaunawa yayi gefen gado yayi dialing number, yana fara ring Farooq ya daga, suka gaisa sannan farooq yace "I think Nihal will be going to kano for the weekend don dazu Umma ta kirani tace in tura mata Tp ta ce mata ta taho Kano, after exams ai xata iya zuwa Abujan ko?" Da sauri khalil yace "Sure ba damuwa, i think that will even be better" Farooq yace "Toh maa sha Allah" Daga haka suka yi sallama khalil ya katse wayar. Mimi na dawowa makaranta Mami ta shigo dakinta, Mimi dakw goge jikinta da towel tace "Mami good afternoon" Mami tace "Afternoon dear, kina ji na" Mimi ta kalli Mami tace "Ina ji Mami" Mami tace "Za ku je gidansu Nadeeyah ke da Nihad ku yi 2 days a can" Da mamaki Mimi tace "Why Mami? Me ake yi a gidan?" Mami tace "Ba komai, but you have to do as i say" Mimi tace "Ohk" Mami tace "Idan kin huta kin ci abinci anjima sai kice mata ta shirya kayanta, kema ki shirya naki" Mimi tace "Toh" Juyawa Mami tayi ta fita daga dakin. Nihad na kallon Mimi dake zaune gefenta a kan gado tace "Ina za mu je?" Mimi ta wara ido tace "Somewhere, gidan sister din Mami" Nihad felt a bit relieve jin haka, don dama har cikin ranta ta gaji da gidan nan, and har zuciyarta taji bata son tana ganin Khalil don wani tsoronsa take ji, da ta tuna abinda yayi mata sae taji hawaye ya zubo mata, ita duk tunaninta ae ya santa fa, a hankali Mimi tace "But pls tell me Neehad, why are u always unhappy, ur eyes are often swollen, u are always silent, ko baki son gidanmu ne?" Nihad ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Mimi tace "Or are you not comfortable here? Am i not nice to you? Kinga ai bakya haduwa da cousins dina da step sister dita Hanan, basa shigowa part din nan so it's rear ku hadu, and idan kika saki jiki da Noor xa ki ga she is also nice, u misunderstood her ne kawai from the beginning" Nihad dai ta kasa ce mata komai she wish she can tell her abinda khalil yyi mata ko zata samu saukin abinda ke damunta a zuciya, Ganin haka Mimi ta sauke ajiyar zuciya tace "So now kawai ki hada kayanki, nasan you won't get boring gidan da za muje cause they are not strict, we will be having enough freedom there to go anywhere unlike here, and i will be taking u out to many places in Abuja" A hankali Nihad tace "Okay thank you" daga haka ta sauka daga saman gadon ta tafi wajen kayanta, Mimi ta bi ta da kallo, seeing how she is walking tace "Are you injured?" Da sauri Nihad ta kalleta tace "I am getting better now" Mimi tace "Ohk"


Umma na jera kayanta da Isiya me wanki da guga ya kawo mata dazu a Press aka bude kofar dakinta, daga kai tayi tana kallon kofar ganin Amina tace "Wai baki tafi islamiyyar ba?" Amina tace "Umma, Aunty Nihal ta dawo" Umma ta ajiye kayanta da sauri tace "Kai haba, oyoyo oyoyo" Daga haka ta fice daga dakin da sauri ta tafi can bangaren Mumy ta shiga dakin Nihal, Kwance ta ganta Mumy na zaune gefenta, cike da farin ciki Umma tace "Oyoyo autana, sannu da zuwa, sannu da zuwa" Sai kuma ta karasa bakin gadon tace "Aa baki da lafiya ne?" Nihal ta girgiza kai tace "Aa lafiyata qlau" Mumy tace "Nima tambayar da nayi mata kenan, ina jin gajiyar hanya ce kawai" Umma tace "To taso mu je, ga favourite dinki can na maki" Nihal tace "Umma bana jin yunwa sai anjima" Umma tace "Ni dallah taso, dubi yanda kika rame kamar baki cin abinci a makarantar, ni wallahi wannan jarabbaben makarantar ya isheni Allah ya so shekaran karshe kike ki huta mu ma mu huta" Mumy tace "Tashi kije Nihal" Nihal ta sauka daga kan gadon ta bi bayan Umma suka fita daga dakin, Mumy dai ta bi su da kallo, at times ganin Nihal na sa ta mance duk wani damuwarta, yana rage mata kewar Nihad da take, tana jin Nihal kamar Nihad a zuciyarta, sannan tun bayan da Farooq ya kirata ya sanar mata yaje har inda Nihad take a Abuja, Mumy ta samu rest of mind, duk da yace sauran bayanan sai ya shigo Kano zai mata amma ta kwantar da hankalinta Nihad is fine and comfortable where she is. Umma ta cika ma Nihal abinci a gabanta, ita dai Nihal ta daura chin dinta a saman gwiwarta tana kallon abincin, Umma ta dawo ta zauna tace "Toh deba ki ci mana" A hankali Nihal ta jawo plate ta fara zuba abincin, Umma dai sai kallonta take don ta rame sosai ba kadan, sannan ba lively Nihal dinta take gani a nan ba, Umma tace "Nihal" Da sauri Nihal ta dago ta kalleta, da damuwa Umma tace "Did you have any problem?" Nihal ta girgiza kai da sauri tace "Aa Umma, i am okay" Umma tace "Na ganki a sanyaye kamar kina da damuwa daughter" Nihal ta girgiza mata kai kawai tace "Ba komai Umma" daga haka ta ci gaba da dibar abincin da take, Umma na ta kallonta tace "Ko dai Nihad kike tunani har yanzu Auta?" Lokaci daya taga hawaye ya kawo idon Nihal, nan da nan hankalin Umma ya tashi, ta mike don a duniya babban tashin hankalinta kukan Nihal ko kuma damuwar Nihal, Umma tace "Yanzu meye abun kuka? Wallahi in dai Nihad ce ni sai in sa duk inda take a samota in hakan ne xai sa ki daina damuwa, in ma kauyen xaki je ki masu kwana biyu sai kije in dai wannan ne damuwarki Nihal" Nihal dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, nan Umma ta hau lallashinta tana jin kukan nata har cikin ranta. Da yamma Umma ta dau makullin mota ta fita sai gidan Hajiya Turai, bayan sun gaisa Umma tace "Anya turai baxa ki sake rakani gidan malamin nan ba a sassauta abin nan da yayi" da mamaki Hajiya Turai tace "Saboda me?" Da damuwa Umma tace "Toh Nihal ce har yanzu na rasa gane kanta wallahi, duk ta sukurkurce, kinsan sun shaku sosai da er uwar, wallahi daxu da naga test script dinta sai da hankalina yayi mugun tashi, Nihal da bata taɓa faduwa a makaranta ba, gashi shekaran karshe take, a'a gaskiya mu je a sassauta abin nan Turai" Hajiya Turai tace "A karya asirin kenan nufin ki?" Umma tace "Aa, a karya kuma?? Cewa nayi fa a sassauta yanda dai Uban zai bar Nihad din ta shigo gidan amma babu yabo babu fallasa sannan ko sisinsa baxai shiga hannunta ba balle na dreban, kin dai gane ai, ni dai in samu hankalin 'ya ta ya kwanta, ta ci gaba da karatunta cikin aminci" Hajiya Turai tace "Amma abun da mamaki, tun da can bata daga hankali haka da abun ya faru yana zafi zafi ba sai yanxu?" Umma tace "Ke kuwa sabo, nima dai farko naga bata yi haka ba duk da ta damu gaskiya, amma wai daga zuwa makaranta shkkn abu ya lalace, Sai ma kiyi ta kiranta a waya bata son dagawa, gaba daya tayi sanyi yanda kika san an zare mata laka, wallahi abun na damuna, kuma nasan saboda er uwarta ne, gashi yanzu naga uban ma yana jan ta jiki tunda ba Nihad din, ko Shekaranjiya ce min yayi xai canxa mata laptop, to taki kwantar da hankali" Hajiya Turai tace "Toh sai mu koma gobe" Umma tace "Yauwa Hajiya turai, sannan ita ma Kamila ina son a kara aiki akan mijinta, don suna ta samun matsala kwanan nan, ita kuma Nihal wani da minister ya fito yana sonta shi ma sai ayi aiki a kai" Hajiya Turai tace "Duk Allah ya kai mu goben" Umma bata jima a gidan ba tayi mata sallama ta kama hanyar gida.
Dab da magrib Nihad ta gama shiryawa tana tsaye gaban mirror tana daura Nikab dinta sai ga Mimi ta shigo ita ma ta shirya, Mimi ta wani ɓata fuska tace "C'mon plss where r u going with this mask, ba fa school xa mu je ba" Bata jira me Nihad xata ce ba ta kwace Nikab din, Nihad ta juya tana kallonta don khalil ne yace ta sa Nikab din, da tayi niyyar baxata sa ba amma kuma kawai ta dauko daga karshe, Mimi na girgiza kai tace "Don Allah ki dau mayafi ki yafa mu fita, we are not going to school fa, beside this is evening" Nihad tace "I am more comfortable with the Nikab Mimi" Mimi tayi shiru tana kallonta, Nihad ta mata murmushi ta amshe Nikab din a hannunta ta shiga daurawa, Mimi ta daga kafada ta fita daga dakin xuwa parlon Mami, ganin Khalil zaune parlon tace "Yauwa yayanmu pls ka kai mu mana since u are around, i don't want to be escorted" Ya kalleta sai kuma yayi kasa da murya yace "Tell Mami so" Da sauri ta shiga daki wajen Mami tace "Mami since yayanmu yana nan ya kai mu can gidan mana" Mami tace "Ohk" Mimi tayi murmushi ta juya ta fita ta kulle mata kofa, Tana kallon Khalil tace "She said ohk" Daga haka ta fice daga parlon. Mimi ta sauka downstairs tare da Nihad bayan Bilkisu ta

Please Login or Register in order to submit comment