Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha nono ni ya sakar ma, amma naga baki da warce kika raina sama da ni, yanzu ace wannan yarinyar da ta zo gidan nan tun jiya har ta kwana zuwa yau ya dace ace baki turata ta gaidani ta gaida Amina a gidan nan ba? Idan ita Amina bata isa ba nima din ban isa ba kenan? Kawai yarinya ta shigo gidan mutane tsabar ba a nuna mata matsayin wa enda ta samu a gidan ba sai ta wuce ka wuce bata gaida ka ba, ko daga kai baxata yi ta kalleka ba, to akan wani dalili?" Mami ta kalli Mimi tace "Mimi je ki kai ta ta gaishesu" a fusace Aunty Hassana tace "Aa bama bukata, taje ta gaida wa? kawai dai ina kara baki shawaran ki daina abinda kike, in raini kike ji a gidan nan to karki matso da shi inda nake, don ni ba abokiyar yin ki bace Fatima" tana kai wa nan ta fice daga dakin kamar iska, Mimi ta kalli Mami tace "Why is she always creating issues out of nothing? From this to that, is she normal?" Mami tace "Jeki ki kaita nace ta gaishesu ban iya wahala da safen nan Mimi, da nasan abinda ya kawota kenan ma ni cewa xanyi kice mata ina bacci" Mami na kai wa nan ta juya ta koma dakinta. Khalil na zaune parlon Abbansa, ya jira har ya gama wayar da yake na kusan minti goma, Abba na kallonsa bayan ya gama a takaice yace "May i help you?" Khalil ya gyara zama yace "My Curriculum vitae, the key to my houses and their written document, my land title, my car.... Ina bukatarsu gaba daya, and I also want my business account unfrozen" Kallonsa kawai Abba yake, can ya mike yana kallonsa da kyau yace "Till u pay ur debt of 800m, idan ba haka ba duk assets din nan da ka lissafo ina me tabbatar maka siyar da su zan yi, kuma basu kai biyan bashin ba ma, shi kuma Cv din in kona, after all i sponsored you...." Khalil ya dinga kallon mahaifin nasa, Abba yace "So Now get out before i shoot ur leg" mikewa Khalil yayi ya nufi kofa kamar xai tashi sama ya bude, sai kuma ya juyo yace "But dad, I can't pay for what I know nothing about...." Yana fadin haka ya fice daga parlon, direct bangaren Mami ya tafi, Mami na ganinsa ta mike tace "Lafiya" Yana huci yace "Mami me yasa har yanzu Abba ke danganta 800m dinsa da ni?? Ina zan kai har 800m" A hankali Mami tace "Saboda kai ya ba, a hannunka yasan kudinsa" A fusace Khalil yace "Toh ni ban san komai kan kudin nan ba, why is he not believing me?" Mami tace "Yanzu me ya kawo maganar kudin?" Yace "Naje na samesa xan amshi abubuwa na da ya amshe min" Mami tace "Amma ai na hanaka ko? What are you lacking now without them?" Khalil na girgiza kai yace "Baxan iya ci gaba da zama bana aiki ba Mami, ya sa anyi sacking dina a inda nake aiki, to ya bani Cv dina in nemi aikin a wani waje mana?" Mami tace "Idan da ka saurareni da baka je masa da maganar wani Cv ba Khalil, me kake bukata da baka samu a yanzu haka? Baka fi wani me aikin samu ba duk da haka? Every month ina tura maka 300k banda wanda kannena ke baka, so me xaka yi da Cv yanzu" a fusace Khalil yace "Ni neman auren Nadeeyar ma bana son yaje min, xan samu kawu kawai su je" yana fadin haka ya nufi kofa a fusace, Mami ta buda baki, sai kuma tace "Toh ai mun yi magana da shi jiya yace next week xai tura representative nasa su je neman auren, kar ka fara xuwa wajen kowa idan ba ɓacin ransa kake son gani ba" Tuni khalil ya fice daga parlon. Hajiya Amina ta shigo bangaren Aunty Hassana tace "Aunty Hassana kin ji abinda Oga yake ce min daxu kuwa?" Aunty Hassana tace "Me yace?" Hajiya Amina tace "Wai satin da xa a shiga xai tura a nema ma Khalil auren yarinyar nan dai, ita fatimar ta masa maganan hakan..." Aunty Hassana ta gwalo ido tace "Da gaske?" Hajiya Amina tace "Wallahi, kafin ya fita yake sanar min" Aunty Hassana tace "Ai ko bai gaya min ba kuma na shiga gaishesa daxu" Hajiya Amina tace "Toh dai shine nace bari in zo in sameki" Aunty Hassana tace "Toh bari inyi wanka zan fito yanzu" Hajiya Amina tace "Toh sai kin fito" Daga haka ta juya ta fita, Aunty Hassana ta mike da sauri ta dau wayarta ta shiga daki tayi dialing number aminiyarta, tana dagawa tace "Ke kuma haka ake Chamo daga cewa kina zuwa sai in ji shiru" Daga daya bangaren aminiyar tata ta kece da dariya tace "Ke dai bari na shiga rububi ne, ai da ma sai dai ki gan ni yau to kuma sai tafiya Kaduna ya kamani, ya gida ya su Sajida" Aunty Hassana tace "Lafiya lau, ni baki gaya min yanda ku yi da mutumin nan kan maganar da muka yi dake ranan ba har yanzu" Chamo tace "Wallahi yace daga dubu dari tara da hamsin ko biyar baxai sake ragewa ba, kuma ke ma dai kin shaida aikinsa, ba fa kowa yake ma aiki ba don shi aiki ma yawa yake masa" Aunty Hassana tace "Shikenan, don wallahi yanzu Amina ta shigo take gaya min satin da xa a shiga ma xa aje neman auren yarinyar" Chamo tayi wani dariya irin ta bosawa tace "Wuyarta ba a tura masa kudi an fara aiki ba, ke dai turo kudi kawai aminiya" Aunty Hassana tace "Toh Sadiya, yanzu kuwa zan saka maki, so nake da kansa zai birkice masu yace ya fasa bai sonta, kuma dab da xa a kai kudin" Chamo tace "An gama, sako kudi yanzu" Aunty Hassana ta katse wayar ta tura mata kudin.




ki biya ki karanta cikin salama hankali kwance.


Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788....
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


43




*This pages is dedicated to Safiyya Usuman uwar Sultan, sauran kuma duk su ci kansu kandas ba mai ba yaji* 🤓






Umma tace "Ayya inna ai suna can garinsu da ita" a tsorace Inna tace "Garinsu? Ina ne garin nasu? Buzu ne fa, ba shi da wani gari da ya wuce Nijar, Nijar din ya kinkimi jikata ya kai kuna gani baku hanasa ba? ta ina zata fara da zafin saharar su, ga shi ance mana ana ta juye juyen mulki a can yau kwana da kwanaki, ni da Abubakar muna ta jimami" Umma tace "Aa Inna, garin zaria ya tafi da ita" Inna ta saki baki, can tace "Kan uba, ku ka bar sa ya tafi da ita wannan garin, ai duk ɗan kano yafi karfin zama a can, Sannan da xai kai ta can din wani shegen ya bi su a cikinku??" Umma tace "Haba Inna, ai sun je sun dawo ya fi a kirga, Nihad fa ta sake fiye da yanda kike tunani Inna" Inna tace "Kai nima dai wallahi da na tsaya nake biye maki kamar wata er wiwi, maganina ma kenan, matsa ki ban waje wajen Ibrahim na zo ba wajenki ba, kai kuma Ibrahim wajenka na zo ba wajen Sumayya ba" Abba yace "Toh ya kike son ince Hajiya? Dama ana zuwa cigiyar wanda kulawarsa da komai nasa ya fita daga hannun iyayensa? Ai ni tuni na mikata garesa, alaqarsa da ita ya fi namu yanzu, don haka duk inda ma ya kai ta dai dai ne, ba ruwana, ba ruwanki, ba ruwan kowa" Inna da ta saki baki tana kallonsa tace "Yau ba lafiya, kace ba ruwanka Ibrahim?" Yace "Toh hanasa tafiya da ita xan yi?" Umma na murmushi tace "Banda abunki Inna mata da mijinta ki zo cigiyarta a gidansu, ita da gidan nan kuma ai sai dai ta kawo mana ziyara, idan aka ganta gidan nan yanzu ai ba lafiya kenan, kuma wallahi ko sati ba ayi ba sun zo gidan nan da shi sun mana sallama kafin su tafi Zarian wai garin mamarsa ce, kawai dai ba ku da rabon ganawa ne, amma yace ba jimawa xa su yi ba za su dawo, suna dawowa kuma da kaina xan je can gidan in dauke ki in kaiki gidan nasu" Inna tace "Toh wai ni shikenan nuna masa ku ka yi bani da matsayi ne da tun da aka aura masa ita daga shi har itan babu wanda ya taka yaje inda nake yace min ci kanki? duk da dai naje Bauchi kwanan nan na dawo" Umma tace "Au ashe dai kinyi tafiyar dai, to ki dai yi hakuri Inna, sun je ne baki nan, ki tambayi yan gidan kilan basu gaya maki bane da kika dawo" Inna tace "Kai Ibrahim fito za mu yi magana" Daga haka ta juya ta nufi kofa tace "Don ban ga xan iya magana gaban kwaɓeɓiyar nan ba" Abba ya mike ya bi bayanta suka fita, Umma ta bi ta da harara, can ta ja tsaki tace "A haka dai"
Ranan alhamis Aunty Maryam suka fara shirye shiryen barin Nigeria tare da mai aikinta da yaranta mata biyu da ke wani boarding school a nan Abuja, duk sai jikin Nihad yayi sanyi, the present of Aunty Maryam use to make her feel strong, it's making her move on with life, tana kara samun kwarin gwiwa har ta mance duk wata damuwar da take ciki and now she is leaving her, Aunty Maryam na lura da sanyin da Nihad tayi, and she felt really sorry for her, she wish she could do something about it, she wish xata iya tafiya da ita inda xa ta, daren Thursday Aunty Maryam ta idar da sallahn da take a sama ta sauko kasa ta karasa sauran kintse kintsen da bata yi ba a gidan don ranan Asabar za su tafi, har xata koma sama sai kuma ta tafi ta bude dakin Nihad duk da taga jiya bata yi tashin daren ba da ta leka ta, zaune ta ganta kan darduma ta hade kai da gwiwa, ta dago kai jin an bude kofar dakin, Aunty Maryam ta shigo dakin ganin idonta tace "Kukan me kuma kike Nihad?" Wasu sabbin hawayen suka ciko idonta ta kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Talk to me, why are you crying?" cikin rawar murya Nihad tace "Aunty you are leaving me... idan kika tafi kika bar ni i don't have anybody here" tana fadin haka ta fashe da kuka, Lokaci daya jikin Aunty Maryam yayi sanyi ta dagota ta zaunar da ita gefen gado tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ke da zaki fara makaranta Nihad, sannan wajen yayata fa za ki zauna, she is also nice, you will like her so much, and Khalil is also there for you always" kuka kawai Nihad take don tasan idan Aunty Maryam ta tafi shikenan she might go back to her former self, there will be no one to encourage her anymore, har ranta bata son gidansu Khalil, she don't think she can cope staying there, ganin yanda take kuka Aunty Maryam ta jawota jikinta cike da tausayinta tace "Kiyi hakuri Nihad, bana son kina wannan kukan, ni ma ina son mu zauna dake kawai bani da yanda xan yi ne, but even with my absence baxa kiyi lacking komai ba" Kai kawai Nihad ta daga mata hawaye na sauka idonta, Aunty Maryam tace "Je ki wanke fuskarki ki zo ki kwanta" Tashi tayi a hankali ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta hau saman gadon amma wasu hawayen ne ke zuba idonta, mikewa Aunty Maryam tayi jikinta a sanyaye ta fita daga dakin, ita kanta tasan in dai ba khalil na gidan ba zaman gidan ba lallai yayi ma Nihad sauki ba, duk excuses da Mami ta kawo a kan dalilin da baxata riketa ba gaskiya ne, amma saboda babu wani option yasa Aunty Maryam duk tayi shunning excuses din. Washegari friday tana dakinta tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga bayan sun gaisa tace "Baxa ka dawo weekend ba?" Yace "Ina airport yanzu haka, in sha Allah yau xan dawo" Aunty Maryam tace "Toh kana sauka ka daure ka fara biyowa ta nan gidana" Yace "Ohk, hope all is well?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Yaushe ne tafiyar Aunty?" Tace "Gobe in sha Allah" Yace "Ohk, sai na dawo in sha Allah" Sallama suka yi ta katse wayar, gaba daya ta kasa sauka gun Nihad don har ranta bata son ganin kukanta. Wajen karfe biyu zeenah ta shigo wajenta a daki tace "Ummi why is ur visitor crying since morning?" Aunty Maryam ta kalleta tace "Go and mind ur business please dear" Ta zaro ido tace "No i was only trying to show concern" Aunty Maryam tace "Je ki kira min ita" juyawa tayi ta fita daga dakin, Bayan wani lokaci sai ga Nihad ta shigo parlon Aunty Maryam tana tafiya a sanyaye, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kasan Carpet, Aunty Maryam ta dinga kallon idanuwanta da suka kumbura, can ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya tace "Wajen yayata ne baki son zama Nihad?" Girgiza mata kai kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Toh ki gaya min inda kike son zama" cikin sanyin murya Nihad na wasa da gefen gyalen jikinta tace "Bani da inda zan zauna" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, irin wannan yarinya karama haka ace wai an koreta daga gida, why? to yanxu da ba don Khalil din ya taho da ita ba da ya zata yi kenan, sai da ta shiga duniya kenan tunda gashi wai dangin mamarta basa nan, what a cruel world we are in, how comfortable is this her step mum now da tasa aka kori yar teenager haka daga gida saboda selfish interest dinta, lallai duniya abun tsoro, bayan few seconds Aunty Maryam tace "Je ki zuba abinci ki ci" Tashi Nihad tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon. Karfe hudu saura Khalil ya shigo gidan ya tarar da Aunty Maryam dake parlonta a zaune, tayi welcoming dinsa ya zauna sannan ya gaisheta tace "Ya hanya?" Yace "Alhamdulillah" Kallonta kawai yake yana jiran ya ji kiran da take masa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Kjay, ina tunanin halin da Nihad xata shiga idan na tafi na bar ta a kasar nan, she's been crying since 2 days ago, i feel really sorry for, she is too young to be passing through all this, tana bukatar tausayawa da soyayya irin ta uwa, ban san yanda xan yi ba...." Kallonta kawai khalil yake, can a hankali yace "Aunty ba wajen Mami za ki bar ta ba?" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Kai ma kasan mun banbanta da Mami ta ɓangarori daban-daban, yanda na jawota jiki har ta sake ta buda min cikinta Mami baxata yi haka ba, sanyinta baxai bari tayi hakan ba, ko me xa ayi mata a gidan kuma nasan iyaka Mami tace tayi hakuri, toh da wanda ya dameta zata ji ko da na yan gidanku KJay?" Khalil dake ta sauraronta yace "Toh meye shawararki Aunty?" Aunty Maryam tace "I am thinking of telling Abu Zeenah sai mu tafi tare da ita ƙasar da za mu" Khalil was speechless at first, can yayi karfin halin cewa "Aunty karatun nata fa?" Aunty Maryam tace "Sai a samar mata a can ta fara" Yayi kasa da murya yace "But i have paid all the fees, kuma kinga ai na kashe kudi da yawa, ni kuma baxan wani iya bin processes din refund ba" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonsa, ya kwantar da murya yace "Kar ki damu Aunty in sha Allah she won't be uncomfortable as you are thinking, beside Mimi na gidan, nasan baxata bari ana ci mata fuska ba, sannan nima next week zan gama abinda nake a can in dawo Nigeria gaba daya" Aunty Maryam still ta kasa cewa komai but deep down her tausayin Nihad kawai take ji kawai tana jin da kawai ya bari sun tafi da ita, shi dai kallonta kawai yake hoping she is convinced, daga karshe tace "Shikenan, Allah yayi mana me kyau, Allah ya bata ikon kwantar da hankalinta a gidan naku" a hankali Khalil yace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ba komai, ka tafi gida kawai, gobe da safe za mu hadu a airport" Yace "Allah ya kai mu" har ya tashi tace "And one last thing xan bata waya, kar kuma kace zaka amshe, kawai dai ka sa mata ido wajen ganin da su wa da su wa take communicating" Yayi shiru yana kallonta, tace "Sannan na ba Ayman layin da na sa mata a wayar da xan bar mata" Shi dai Khalil kallonta kawai yake, tace "Ka ji abinda nace?" Yace "Na ji" tace "Sai anjima" juyawa yayi ya fita daga parlon nata. Khalil na sauka downstairs ganin Zeenah a parlor yace "Ina Moon?" Tace "She is sleeping upstairs" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya?" Tace "Mun gama tun jiya" yace "Good" Ya fi minti biyar tsaye a parlon, daga karshe kawai ya fita compound, nan gidan ya bar motarsa don akwai wani abokinsa a layin da xa su je wani wajen tare yanzu. Washegari da safe Khalil ya nufi airport tare da Mami da Mimi with Noor, Aunty Maryam ta tafi da motarta da yaranta uku da mai aikinta da Nihad, don tun da taga motar khalil a gidanta ta sanar masa xata taho da motarta airport sai ya maido mata gida ya dau nasa, Noor kuma tayi driving dinsu Mami su koma gida, har suka isa Airport Nihad bata daina kukan da take ba, she felt everything is over for her, it's just like they are sending her away from home for the second time, she felt insecure without Aunty Maryam, she won't have anyone to confide in anymore, bayan Aunty Maryam ta isa airport din tayi parking, har ma ta daina ba Nihad baki ganin ba sauraronta take ba, ta dau waya ta kira khalil, ya sanar mata sun kusa isowa, tana ta jira har ya shigo airport din with escort, murmushi tayi don tasan babu abinda ya tsana kamar wannan escort din, kawai dai babu yanda xai yi don escort din na Mami ne sae in ita tace masu bata bukata, wannan kuma sai in ba waje me nisa xa ta ba, tuni aka masu providing wajen parking babu 6ata lokaci, bayan few minutes Mami da su Mimi suka sauko daga motar, Aunty Maryam ma ta sauka ta tafi ta gaida Mami, yaranta ma duk suka sauka xuwa wajen, Noor ta rungume Aunty Maryam tace "Ohh i feel like crying Aunty, xa mu yi missing dinki sosai" Mimi ma ta marairaice tace "Me too Aunty" Mami na murmushi tace "Toh ba sai ku tafi gaba daya ba" Noor tayi dariya tace "We wish" Nan mai aikin Aunty Maryam ta durkusa ta gaida Mami, Mami ta amsa tace "Murja sai Uk ko?" Murmushi tayi tace "Za mu yi kewanku Mami" Mami tace "Toh Allah ya tsare, Allah ya kai ku lafiya" Nihad bata yarda ta sauka daga motar ba ta hade kai da gwiwa tana shesshekan kuka, Aunty Maryam bata yi forcing dinta ta sauko ba cause she feel sad seeing her cry that way, Mami tace "Toh ina yarinyar?" Aunty Maryam ta ɗan yi murmushi tace "Kuka take a motar shi sa ma ban bari ta sauko ba" Mami tace "Kuka kuma? Kukan me?" Aunty Maryam tace "Sabo mana Mami" Mami tace "Allah sarki" Tuni aka sauke kayansu zuwa cikin airport din, Khalil dai na tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu, lkci lkci yake kallon motar Aunty Maryam, Sai da xa su shiga cikin airport din bayan sun yi sallamar karshe da su Mami Aunty Maryam ta koma gun motarta ta bude back seat ta dafa shoulder din Nihad a hankali tace "Be a good girl dear, Allah ya tsare ki, Allah kuma yayi maki albarka, in sha Allah xa mu dinga waya sosai duk abinda ya dameki kar ki boye min ki dinga gaya min kin ji, kuma kar ki fasa addu'a da tashin daren da kike kamar yanda kika saba in sha Allah xaki ga sakayya cikin gaggawa, sannan ki dinga daukan kiran mutumin da na ba numberki banda walakanci my dear, he is a good guy, and u will enjoy communicating with him" Nihad ta kasa ce mata komai sai kuka take, Aunty Maryam ta juya cike da karfin hali ta bar wajen duk Khalil na kallonsu, Ta mika masa makullin motarta yace "Allah ya tsare Aunty" Ta gyada masa kai ta nufi cikin airport din su Mami na daga masu hannu, Khalil ya mika ma Noor makullin motar Mami dake wajensa, Ta amsa tace "Till we meet home yayanmu" Juyawa yayi ya nufi motar Aunty Maryam ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, ya riga su Noor fita daga airport din, har sannan Nihad bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita, shi ma kuma bai ce mata komai ba, har ya isa gidan Aunty Maryam, bayan an bude masa gate ya shiga yayi parking motar a parking space, Nihad ta kasa dago kanta, ya sauka daga motar ya jingina jiki, bayan few minutes ganin ba bude motar xata yi ta sauko ba ya bude mata, da kyar ta sauko daga motar xata bar wajen tana harde kafa tana kokarin danne kukan da ya taho mata taji ya jawota kusa da shi, lkci daya ta fashe da kukan ta rufe fuskarta a jikinsa, drawing her more closer to himself yayi kasa da murya yace "Da kin bi ta ai" Ya bar ta ta ci kukanta bai hanata ba, har ta gaji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta rufe ido tana shaƙar daddadan kamshin jikinsa, tana kuma jin yanda zuciyarsa ke bugawa. They stood in that way for almost 5 minutes, lokaci daya yaji ta sakar masa duk jikinta, yayi saurin rungumeta sosai kar ta zame kasa, he could feel her breathing calmly, kamar kuma warce aka tsikara ta bude ido da sauri ta janye jikinta shi ma yayi saurin saketa, ta koma gefe tana murza ido, shi kuma yayi keeping straight face.... she is so sleepy don jiya ba wani baccin kirki da tayi, ya ciro makullin motarsa ya bude tasa motar, ya shiga yana warming dinsa tana kallonsa tace "Kayana" Ya daga kai ya kalleta, ta koma gun motar Aunty Maryam ya bude booth din da makullin, ta ciro jakunkuna biyu, daya na wasu kaya da Aunty Maryam tayi mata, daya kuma wanda ya siya mata, ta zuba kayan a booth dinsa ta kulle sannan ta shiga back seat, bayan ya gama warming motar suka bar gidan, Nihad ta ɗan shinshina Hijab din jikinta jin kamshin dake tashi a jiki, a hankali ta kwanta jikin motar ta lumshe idonta, har suka isa gidansu bata sani ba tana bacci, bayan yayi parking ya kashe motar ya sauka still Nihad bata farka ba, ya bude back seat din yana kallonta, patting din kujeran motar yayi still bata bude ido ba, sai kuma ya kai hannu jikinta yana tashinta, sae a sannan ta bude ido da sauri tana bin inda suke da kallo, ganin compound din jikinta yayi sanyi, ya zaga ya bude booth ya fiddo jakunkunanta, ta sauko daga motar tana kallon securities din bakin gate din, ya kulle motar yana rike da jakunkunan nata biyu ya fara tafiya, ta bi bayansa tana jan kafa tayi kalan tausayi da fuskartar, ta inda ya shigo da ita gidan ranan farko da suka zo ya bi da ita yanzu ma, har suka isa bangaren Mami, ya kai mata kayanta guess room dake bangaren, tana tsaye bakin kofar har ya karaso ya shiga parlon Mami sannan ta bi bayansa, Mimi ce kadai zaune parlon, Mami kuma na bedroom dinta, ya zauna saman kujera Nihad dai

Please Login or Register in order to submit comment