Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata driving direction din a Google map a wayarsa ya ajiye mata, sai daga baya Nihad ta fahimci dalilin kasa tukin nasa, don kuwa har suka iso gida kallonta yake, even for a second bai daina kallonta ba as if his life depends on that, Ita dai tayi concentrating kan driving da take kawai, ganin bai sauka ya bude gate din ba duk da sun iso gida ta juya ta kallesa, wani murmushi me narka zuciya ya sakar mata, ta kasa daina kallonsa, ya kamo hannunta a hankali, sai kuma ya saketa ya sauka daga motar ya bude gate din gidan ta shiga ciki da motar tayi parking a parking lot, Bata jirasa ba ta nufi kofar shiga gidan da sauri, sai dai dole ta tsaya ya zo ya bude kofar, yana budewa kuwa ta shige ciki ya bi bayanta da sauri ya rikota, bata san sanda ta fashe masa da kuka ba, ya rungumeta jikinsa sosai, yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa, murya can kasa yace "I am so sorry Nihad, i am very sorry, i am sorry i hurt you much...." Kuka take tana tuna irin azaban da yayi mata, bata ankara ba taji ya dauketa ya wuce sama da ita, ta kankamesa saboda tsoro, bai direta ko ina ba sai saman makeken gadonsa dake master Bedroom ya hau aikin lallashin da bai samu yayi mata all through that day ba, da ya ga ta hakura da kukan ya shiga bandaki ya hada mata ruwa a bathtub dinsa, ya dawo ya dauketa zuwa bandakin, he did everything for her, ita dai ta kasa hada ido da shi..... Daren ranan Khalil bai wani rintsa ba all his thought was with Mami, kukan da yaga tana yi ya tsaya masa a rai, tun kafin su kwanta ya so kiranta amma bai ma san me zai ce mata ba, infact ba ma shi da courage din kiran nata, kawai ya hakura da kiran, all through the night Nihad na jikinsa bai saketa ba, and she slept soundly. Karfe takwas na safe Khalil ya kira Ya farooq bayan kiran da Janar yayi masa na cewa su shirya shi da Nihad before 9:30 za a zo a daukesu, wayar na fara ringing Farooq ya daga, bayan sun gaisa farooq ya tambayesa ya Nihad, Khalil yace "She is fine Alhmdlh, ya Kaduna?" Farooq yace "Ina kano ai" Khalil ya fara tunanin ta ina ma zai fara sanar masa, can dai yace "Erm... dama Dad dina ne za su je kano wajen Abba yau su gaisa, so i don't know how it's going to be...." Farooq yace "Ohk, ba damuwa zan sanar masa in sha Allah, Allah ya kawo su lafiya" A hankali Khalil yace "Ameen" Don har ya fara jin kunyan Abban Nihad da Mum dinta, Farooq yace "Kamar karfe nawa kenan?" Khalil yace "Zuwa sha daya in sha Allah" Farooq yace "Allah ya kai mu" Daga haka suka yi sallama Khalil ya ajiye wayarsa ya jinginar da kansa da kujera, yau kam bai ma san da idon da zai kalli Abban Nihad ba, he wish Abbansa zai yarda yaje gidan without convoy, but that will never be possible, can kuma ya ji dama Abban ya bar sa shi kadai yaje gidan ba sai anje da shi da Nihad din ba, ya sauke wani ajiyar xuciya ya mike daga karshe ya nufi sama ya shiga dakinsa, har sannan Nihad bacci take, kana kallonta kasan it's a peaceful one, ya zauna gefen gadon a hankali yana kallonta ko kiftawa babu, abubuwa da yawa ne suka hau dawo masa tun farkon da ya fara zuwa gidansu, and he couldn't help it but smile and he wish she will go back to her former Nihad me tsiwa, wauta, fada, masifa, amma banda walakanta d'an Adam da bin kawayen banza. Aunty Maryam na zaune gefen gado a dakin Mami ta jingina jikin gadon tayi shiru bata cewa komai, can ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Aa Mami kar ki ce baza ki ba tunda har Janar din da kansa yace ki shirya...." Mami ta dakatar da ita a fusace tace "Akwai wanda zai tilasta ni in je ne idan nace baxan je ba? To nace baxan je ba, kuma baxan je din ba" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Ni health dinki nake jiye maki Mami, don Allah ki kwantar da hankalinki abi komai a sannu, tun jiya nake gaya maki haka amma kin ki fahimtata" Mami ta kalleta tace "Wallahi ban ga amfanin zuwanki ba Maryam, na zata da kika zo za ki tayani a san ta inda za a billo ma lamarin nan, amma sai dai ki zauna ki kura ma mutane idanu baki cewa komai...." Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Ni so nake abi komai ne a sannu Mami, ni kaina i am shock, i am really shock don yarinyar bata taɓa ce min ae da aure tsakaninsu ba kuma ta bude min cikinta sosai during her stay a gidana, amma dae na fi tunanin shi ne ya hanata fadi ita kuma babu yanda zata yi, ni sai nake ganin tunda auren yayi ba shashanci ba ae da sauki da dai ace neman mata yake Mami..." Mami ta dinga kallonta ta ma rasa abinda zata ce mata don takaici, Aunty Maryam tace "That is just it Mami, wannan ne ma yasa na sa ma kaina nutsuwa ban daga hankali ba, duk da lamarin akwai shock, but one have to try and reason, though i am not in support of what khalil did da har zai yi aure babu knowledge dinku, amma ai sai abi komai a sannu" Mami bata tanka ta ba ta dalilin wayarta dake ring, ta dau wayar nata, ganin Hajiya Safeenah ce ta dinga kallon screen din wayar, can dai ta daga ta sa handsfree kawai, nan suka gaisa faram faram, Mami tace "Kina ta kirana jiya da daddare ban samu dagawa ba Hajiya, wallahi maganin bacci na sha, bana ɗan jin dadi" Hajiya Safeenah tace "Subhanallah, ya jikin yanzu?" Mami tace "Aa Alhamdulillah naji dama dama" Hajiya Safeenah tace "Toh zuwa karfe sha daya zan shigo in sha Allah" Mami ta ɗan yi shiru sai kuma da sauri tace "Koh??? kuma gashi za mu je kano tare da Janar amma yau din za mu dawo" Hajiya Safeenah tace "Ahh to shikenan, sae dai kun dawo kenan, ita Nadeeyan sae ta tafi ita kadai kawai, dama tace min zata gun Noor anjima maganar anko" Mami tace "Allah sarki, to in sha Allahu muna dawowa zan kira ki" Nan dai suka yi sallama Mami ta ajiye wayar a hankali, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Aunty Maryam dake ta kallon Mami tace "Kin ga gwara da kika ce mata haka kar ta zo ta ganki a wannan yanayin da kike ciki" Mami dae bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Ga kuma Nadeeyah tace zata zo wajen Noor, kar kuma ta zo ta ga kina nan, ba gwara kawai ki shirya a tafi kanon ba, na tabbatar idan kika je kanon zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, sai kuma a san next step da za a dauka" Aunty Maryam na fadin haka ta mike ta shiga bandaki.... Farooq yayi sallama kofar parlon Abba ya shiga ciki, ya zauna kasa ba tare da yayi interrupting din Inna dake ma Abba magana ba, Umma ma na zaune parlon ta rafka uban tagumi sai kallon innar take, Inna na kallon Abba a ɗan fusace tace "Ya kake kallona haka Ibrahim, ni fa ba kai nace ka dauko masa yan sandan ba, to wa ma zai sa ka ka lalata mana al'amarin, ni da kaina zanje gidan yan sandan in gana da ogansu daga nan ya sa a cika min mota daya da kurtaye mu je har gidan nasa su nakada masa shegen duka shi ma, kafin mu tafi da shi.... Ai ni da kaina zanje ko ɗan rakiya bana so, don ma dai kaf zuri'a bamu da soja ai da shi zan aika ya ci min ubansa kafin a kai sa gidan yan sanda" Farooq dai sai kallon Inna yake, Inna tace "Sai kace er banza ya samu ya doka da za a yi shiru a kyalesa, to ni ba gantalaliya bace, wallahi sai an bi ma jikata hakkinta" Farooq yace "Duk wannan abun fa bangarenta kawai aka ji ba aji nasa bangaren ba Inna, ku daina saurin zartar da hukunci daga jin bangaren mutum daya" Inna ta wani jefa masa shegen kallo tace "Allah ya tsine masa shi da bangaren nasa, ya nakada mata shegen duka ya hadata da saki daya kace mu jira mu ji bangarensa?? Anya farooq? to wai ko dai kai ka sa shi yayi mata wannan abun ne bamu da labari farooq??" Shi dai Abba bai ce komai ba a parlon, Umma ma ta kasa cewa komai abun duniya ya isheta, Inna tace "Toh kuwa bai doki Kamila a banza ba sai inda karfina ya kare a wannan kes din wallahi, ga duka ga saki??" Farooq ya dauke kai yana kallon Abba yace "Abba dama Khalil ne ya kirani yanzu wai mahaifinsa zai zo gaisheka yau, zuwa karfe sha daya" Inna tace "Waye kuma Khalil?" Umma ta daga kai daga tagumin da tayi tana kallon Farooq, Farooq na kallon Inna yace "Mijin Nihad" Sake baki Inna tayi kamar warce ta ji mugun abu, can tace "Lallai duniya ta tara marasu lissafi, yanzu su yan kauyen zai zauna jira baxai fita aikinsa ba? Yau ga dai fitina kiri kiri" Abba na kallon Farooq yace "Allah ya kawo su lafiya" Mikewa Farooq yayi ya fita daga parlon, Inna ta kalli Abba tace "Kai kuma zaunawa zaka yi ka jira kauyawan?" Shi dai Abba bai ce mata komai ba, Umma ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanxu inna ya kika ce za ayi?" Inna tace "Kamilar ta zura Hijabi muje har gidan yan sandan su ga abinda matsiyacin yayi mata, daga nan su bani mota daya muje su ci ubansa, sannan mu tafi kotu..." Umma tace "Toh ai bata iya ko tashi Inna" Inna tace "Sai a min hotonta in kai masu su gani"


Wani soja ne ya bude ma Nihad kofar motar dake parke kofar gida, ta juya ta kalli Khalil dake kulle gidan, yayi mata alamar da ta shiga, a hankali ta shiga cikin lafiyayyen motar, Khalil ya karaso ya shiga motar shi ma, suka bar anguwan, direct airport motar ya nufa da su, kusan kuma a tare suka isa airport din da Convoy din Janar, Nihad dai sai kallon ikon Allah take, Lounge na manyan kasar aka yi Conveying dinsu kafin tashin jirgi.








Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah




Ur evidence via 07087865788💖 NIHAAD 💖


61




Farooq na fitowa parlon Abba ya tafi bangaren Mumy, Mumy ta fito daga dakinta jin sallamarsa yace "Bacci kike ne?" Tace "Aa ba bacci nake ba farooq, ya gajiyan hanya, jiya sai baka shigo ba har nayi bacci" Yace "Wallahi na gaji ne, i had issues with my car" Mumy tace "Haka kace, Allah Ubangiji ya tsare" Yace "Ameen" Mumy tace "Ka samu mijin Kamilar a waya?" Farooq yace "Eh na samesa amma bai daga ba kuma bai biyoni ba" Mumy ta ɗan yi shiru, can tace "Toh Allah ya kyauta, amma da ka je gida ka samesa ko?" Ya girgiza kai yace "Aa bazan je ba, duk yawancin abinda take masa dama ai ni yake kira, kuma sai dai in basa hakuri, so this time around ban san me tayi masa ba, tunda gashi har ya ga kirana bai biyo ni ba" Mumy tace "Kai abun ba dadi wallahi, Allah Ubangiji ya daidaita su" Farooq yace "Mumy dama Khalil ne ya kirani yace yau Mahaifinsa zai zo su gaisa da Abba...." Mumy tace "Yau din nan?" Farooq yace "Ehh, shine na shigo in gaya maki ko za ayi masu ko da snacks ne, tunda lokaci ya kure balle ace za ayi girki, yace min zuwa 11 za su zo and this is past 9" Mumy tace "Toh shikenan, dama Jamila na garin amma yau tace min zata koma, bari in kirata ko zata bari da yamma" Farooq yace "Ohk to, sai a karo drinks da ruwa" Mumy tace "Toh shkkn" Yace "Zan siyo drinks din da ruwa" Daga haka ya fita daga parlon Mumy ta dau wayarta ta shiga kiran Aunty Jamila, babu ɓata lokaci kuwa Aunty Jamila ta iso gidan suka shiga kitchen da Mumy, Hafsah na taya su, Umma ta fito ɓangarenta jin yanda kamshin soye soye ya cika gidan ta tsaya kofar kitchen tana kallon Mumy tace "Wai!! Sannunku da aiki, toh dai Allah ya sa su iya ci, yan kauye suka san wani Samosa da spring rolls banda abun ki Maryam, dama dai tuwo miyar kuka kika masu da wannan wahalan ai" Ko kallonta Aunty Jamila bata yi ba tana ci gaba da aikin da take, Mumy tace "Toh gashi nan dai muna yi, ya jikin Kamila?" Umma tace "Da sauki...." Daga haka ta juya ta bar kitchen din, sai a sannan ta tabe baki ta koma bangarenta. Nihad ta kasa hada ido da Aunty Maryam da Mami dake zaune Lounge din, sai Aunty Hassana da bata yi shawara da kowa ba ta dau gyalenta ta shige daya daga motocin Convoy, kuma daga Mami har Aunty Maryam babu wanda yace mata komai, Ita kuwa Hajiya Amina dama sai yanda Aunty Hassana tace mata to bata ce mata ta taho ba balle ta biyosu, Wani waje sak parlor Nihad ta hango Janar zaune da wani mutumi sanye da kayan soja suna magana, Nihad bata iya ta dago kanta ba, ta gaishe da su Mami a hankali, Mami ta amsa ba tare da ta kalleta ba, Aunty Maryam dae sae kallonta take bayan ta amsa gaisuwan, can ta nuna mata kujeran dake side dinta ganin gefe ta koma ta tsaya, a hankali Nihad ta karasa ta zauna kan kujeran, Aunty Hassana ta dinga kallon Nihad tana nazarin abinda Aliyu ya gaya mata, Khalil dama kin shiga Lounge din yayi, ya zauna a Departure Lounge din kowa da kowa... first class passengers suka fara boarding din plane din, wanda iyaka ahalin Janar ne a first class din, sai da Aunty Maryam ta nuna ma Nihad inda zata zauna cikin jirgin sannan ta zauna, kamar yanda Khalil ke ta avoiding eye contact da Mami ita ma haka ta dinga avoiding, wani kunyarta take ji, Khalil ne karshen shigowa ya zauna, Aunty Maryam ta taɓe baki ganin yanda yake wani sinne kai, ita kam ta gama tsorata da lamarinsa bata jin zata sake yarda da ko wani maganarsa, duk yanda take da shi amma ya boye mata wannan lamarin..... Karfe sha daya da kusan rabi jirgin ya sauka a Aminu Kano international airport, sai da suka fara sauka daga jirgin before the rest class, Nihad ta dinga kallon jerin motocin dake jiransu har da na sojoji da suka yi bake bake a airport din, tuni wani soja ya bude ma Janar da babban sojan dake tare da shi motar da za su shiga, Khalil dai sai nesa nesa yake da su kamar baya son a san tare suke, kai kace karere ne shi a wajen, Aunty Hassana kuwa sai daga kafada ake ana taku dai dai uwa ita ce matar Janar din, Nihad ta daga kai a karo na farko ta kalli Khalil tun barin su Abuja, taga ko kusa kusa da family din nasa bai son matsowa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, wasu abubuwan da tayi masa a baya ne suka hau dawo mata vividly, irin humiliating dinsa da tayi a gidansu, and even for once bai taɓa attempting nuna mata ya fi ta komai na rayuwa ba, yawanci duk abinda take masa sai dai yayi kamar bai san tana yi ba, bata san sanda hawaye ya kawo idonta, and because of him today she is among this elite, standing in the midst of them, kamar ya san kallonsa take shi ma ya kalli direction din da take, suna hada ido tayi saurin kauda kanta, Aunty Maryam ta bude daya daga motocin dake jere tana kallon Nihad tace "Shiga" Nihad ta shiga mota sannan ita ma ta shiga, Mami ta shiga wani motar daban, Aunty Hassana ta shiga motar da Mami ta shiga don me shegen tsada ne, nan suka bar airport din, Khalil da zai yi directing dinsu zuwa gidan ya hau motar dake gaba, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka iso Nasarawa GRA.... Nihad na ganin sun shigo layinsu gabanta ya dinga faduwa, Tuni Aminu ya taso da sauri yana leko gate jin jiniya kamar tashin duniya, ganin jerin motocin sannan ga na sojoji a gaba ya gwale ido yana jiran yaga sun yi gaba sannan ya ga gidan wa za su amma sai ya ga sun jeru dai dai kofar gidan, kan kace me sojojin sun sauka sun zagaye layin, a hankali Aminu ya tura gate din ya rufe ya saka lock yana zaro ido, to meye kuma suka tsaya masu a kofar gida, ko dai ɓatan hanya suka yi, A mugun tsorace Aminu ya kalli gate din jin ana bubbugawa, haba kan kace me sai ga Aminu har cikin parlon gidan ba tare da yasan ya iso ba, Inna da dawowarta kenan daga police station tana bada labarin yanda aka je har gidan Kamila ba a tadda tsinannen mijin ba, ta saki baki tana kallon Aminu tace "Me zan gani haka? waye wannan kuma??" Jiki na rawa Aminu yace "Hajiya wallahi sojoji ne sun fi hamsin a kofar gidan nan, yanzu haka su ke bubbuga gate din, ban san wa suke nema ba" Farooq ya mike yana kallon Aminu, Inna tace "Sojoji? Meye su din?" Umma dake zaune parlon ita ma tana kallon Aminu tace "Sojoji fa kace Aminu" Zufa na keto ma Aminu yace "Wallahi su Hajiya, da manyan bindigu na gansu sun sauka kofar gidan nan" Inna tace "Aa to ko dai bariki za su suka yi ɓatan hanya suka shigo ma mutane anguwa, da ba sai ka leka kace masu ba hanya ba" Abba ya fito daga parlonsa jin bubbuga gate din da ake ta yi ba kakkautawa, shi dai Farooq na ta tsaye yana kallon Aminu ya kuma kasa fita waje, ganin Aminu a parlon Abba yace "Lafiya" Aminu ya durkusa ya makale jikin kujera yace "Wallahi Alhaji sojoji ne sun kusa dari ban san wa suke nema ba, ni dai shine na kulle gate din na taho, ga su can suna ta buga gate din" Ai ko rufe baki bai yi ba Farooq ya nufi kofa da sauri, a tsorace Inna ta mike tace "Ina za ka farooq??" Umma ma ta daka masa tsawa amma tuni ya fice daga parlon, da gudu Inna ta bi sa tana kiransa a gigice, yana tafiya ya fiddo wayarsa dake ring a aljihu yaga Khalil ne ke kiransa, dagawa yayi khalil ya sanar masa suna waje, Farooq ya karasa bakin gate din ya bude, Khalil ne tsaye bakin gate din sai sojojin dake kewaye wajen ko wanne da bindiga a hannu, sai a sannan Janar ya sauko motar tare da abokinsa, Inna ta gwale ido uwa munafuka ganin Khalil ga sojoji sun zagayesa, sai kuma ta fashe da kuka ta saki salati tace "Dama sai da na fada, sai da nace ɗan kinnafa ne su Ibrahim suka gwaleni suka maida ni wawa....." Sai kuma ta kalli Janar da sojojin dake wajen suna kallonta tace "wallahi ranka shi dade bamu taɓa saninsa ba, ce maku yayi ya san mu? Ɗan Nijar ne fa" Sai kuma ta juya da gudu taje ta gaya ma Abba ya buya, gaba daya ta rikice ta gigice, Farooq sai kallon Janar yake wondering if Lieutenant General Abubakar I Jikamshin da ya sani ne wannan yake gani a gabansa or just kamanni ne, shi dai Janar was patiently standing, su Mami kuma basu kai ga sauka daga motar ba, Khalil yayi kasa da murya yana kallon Farooq bayan ya shiga compound din da sauri yace "He is my Father" Muryan sojan dake tare da Janar suka ji yace "Is this how u treat ur guess?" Yana kallon Farooq yayi maganar babu yaɓo babu fallasa, Da sauri Farooq ya gaishesu a daburce yana welcoming dinsu ya bude gate din sosai ya basu hanya, nan su Mami da Aunty Maryam suka sauko daga motar, Khalil dai kansa na kasa, walking fast ya fara leading din Janar da abokin nasa zuwa entrance din main parlor ganin kamar Farooq ya rikice and at anytime Janar zai iya exploding ya masu kwarkwar gaba dayansu a wajen barin yanda aka barshi a tsaye, Nihad taji kamar taje ta rungume yayan nata, she is so happy seeing him, A balcony Khalil ya hadu da Abban Nihad, a bit confuse Abba ya dinga kallon Janar dake tahowa like the soldier he is, Abba ya kalli Khalil sae kuma ya sake kallon Janar with his friend, kamar Janar Jikamshi yake gani a gabansa, ko idonsa ne ke masa gizo, lokaci daya sojojin da suka biyo bayan Janar da abokinsa suka nemi each and every angle of the compound suka tsaya, hakan dai bai sa Abba ya fasa ba Janar hannu ba yana masa sannu da zuwa, sannan ya ba daya sojan ma hannu kafin yayi leading dinsu har cikin Main parlor, Saminu da Isiya sai wuwwurga idanuwa suke daga Chalet suna jiran suga an fara kwashe kowa na gidan har su, har sannan kuma Aminu na makale a inda ya durkusa a parlon tun dazu, Hajiya Inna kuma na can kuryan dakin Mumy bata ma san sanda ta isa nan ba tsabar gigicewa sai salallami take tana cewa ya cucemu ya cucemu, dama sai da nace masu ban yarda da shi ba hankalina bai kwanta da shi ba aka maida ni wawa.... Khalil ya daga kai ya kalli Umma da ta koma bayan kujera ita ma sai zare ido take a tsorace, Mumy na tsaye kofar kitchen da Aunty Jamila, ko wanne zaka ga Fargaba karara kwance a fuskarsa, sunkuyar da kansa yayi kawai, Bayan Janar da abokinsa sun zauna ya nuna ma Abba ganin bai zauna ba yace "Bismillah Alhaji" Abba ya kirkiri murmushi ya zauna yace "Barkan ku da zuwa, amma sai dai ban san me ke tafe da ku ba, ina kuma fatan Allah ya sa lafiya" Nihad ce ta shigo parlon su Aunty Maryam na biye da ita, duk suka zauna a parlon, Mumy da Aunty Jamila suka dinga bin su da kallo, lokaci daya gaban Mumy ya fadi, what's happening??? Umma dai kamar idanuwanta za su fito tsabar yanda take gwalesu tana bin sabbin occupant din parlon da kallo, Farooq ne kawai ke ta masu sannu da zuwa a parlon da fara'arsa, ya tafi ya dinga jido pack din ruwa da lemo, Nihad ta kasa ci gaba da zama kawai ta tafi da sauri ta rungume Mumy cike da farin cikin ganinta duk da basu wani dade da ganin juna ba, but she is having a new strong love for her mum now, Mumy ta hadiye wani abu da kyar, murya can kasa kasa tace "Su waye wa ennan Nihad? Why are they here??" Yanda zaka san kowa a tsorace yake ko gaida su Mami da Aunty Maryam babu wanda yayi a parlon ana dai jiran aji abinda ke tafe da su, most especially Abba da hankalinsa ya tashi sosai, kawai dai bai nuna bane a fuska, Muryar Janar dake kallon Abba suka ji yace "Babu wani abu dake tafe da mu sae alkhairi Alhaji, kuma muna me ba kai da iyalanka hakurin yanda muka shigo maku gida kai tsaye, may be without any notice.... and most important of all, i hope kai ne Alhaji Ibrahim??" Abba ya gyada kai yace "Kwarai ni ne" Janar yace "Sunana Abubakar Ibrahim Jikamshi...." A hankali Abba yace "Lieutenant... General.... Abubakar Jikamshi" Janar yace "Haka ne" Umma ta dafa kujeran kusa da ita tana sake kallon Janar da kyau kamar idanuwanta za su fito, kwarai kuwa sai yanzu ta ganesa, Ita kanta Mumy da Aunty Jamila kallonsa suke

Please Login or Register in order to submit comment