Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amina ta mike suka nufi kofa Mami ta bi su da kallo har suka fita, Mami ta sauke ajiyar xuciya ta zauna. Daga karshe ta mike ta fita daga parlon nata, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da kayan Mimi, ta shiga dakinta ta ajiye gefen gado tana kallon Nihad tace "Shiga bandaki kiyi wanka yanzu" Khalil dai na zaune yana kallon Mami, Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta fito parlor, biyota yayi ya zauna kujeran kusa da ita yayi kasa da murya yace "Don Allah ki saurareni Mami" Mami tace "Sauraran me xan maka Khalil" Yayi gathering courage xai yi magana aka bude kofa duk suka juya, Farhana ta shigo parlon tana kallon Khalil tace "Yayanmu wai kaje Abuu yana kiranka" Yayi shiru yana kallonta, Mami ta hadiye abu da kyar tana kallon Farhana tace "Ki je yana zuwa" Juyawa tayi ta bar wajen, Mami ta kallesa da damuwa tace "Ka je kaji kiran da yake maka" Khalil bai iya yace komai ba, can ya mike ya fita, slowly yake tafiya har ya isa bangaren Abba, yayi sallama sai da aka amsa masa sannan ya shiga, Abba na tsaye ya shirya alamar zai fita, Khalil yayi ma Aunty Hassana kallo daya ya zauna kasa, a hankali yace "I am here sir" Abba yana nuna masa Aunty Hassana yace "Who is she to me?" Khalil bai iya yace komai ba, Calmly Abba yace "Tambayarka nake" Khalil ya kallesa yace "Ur sister" Abba yace "Good, kasan da haka ka dawo gidan nan baka je ka gaida ita da Hajiya Amina ba" Khalil yayi shiru, Aunty Hassana tace "Aa yaya, uwar ce ta sa shi hakan ba kowa ba, ita ce xata hanasa ya shigo ya gaida mu saboda ba mu isa ba, sannan still mun tashi mun je har can bangaren nata don ganinsa amma kememe yaron nan ya ki fitowa ta wani fito tana karesa, ita Amina da abu kadan ke sa ta kuka muna fitowa ta kama kuka wai ai wannan cin mutunci ne, ni kuma kasan halina bana daukar nonsense shine yasa ma na zo na sameka yanzu, yaron da a haife na haifesa? Sau nawa nake saka ka a gaba ina cewa kayi hakuri ka bar sa ya dawo gidan nan, shine zai dawo ya saka min da haka?" Abba dai yayi shiru yana safa da marwa a babban parlon nasa, Khalil ya jefa mata wani kallo ta gefen ido, Can Abba ya juyo yana kallonsa da kyau yace "Bata hakuri, sannan duk ka bi su bangarensu ka gaishesu kace masu ka dawo" Khalil ya kalleta a takaice yace "Yi hakuri" Daga haka ya mike ya fice daga parlon, Da ido Abba ya bi sa, Anty Hassana ta saki baki ita ma ta bi sa da kallo, Can ta kalli yayan nata xata yi magana yace "Tashi ki je Hassana, xan nemesa anjima idan na dawo" Aunty Hassana ta dinga kallonsa da mamaki, sai ma taga ya nufi wajen takalmansa ya zauna yana kokarin sa wa, tashi tayi daga karshe ta fice daga parlon kamar xata tashi sama, Khalil na fita ya koma bangaren Maminsa, Mami na tsaye tana kallon Nihad dake sa mayafin Mimi da ta amso mata, Mami ta fesa mata turaren hannunta tana kallonta tace "Baki taho da dankunne ba?" Nihad ta girgiza mata kai kawai, Gaba daya in ka kalleta sai ta baka tausayi, duk ta fita hayyacinta, Khalil dake tsaye bakin kofa kallon Mami kawai yake ya ma rasa abinda xai ce mata, lokaci daya jikinsa yayi sanyi don bai san what she is up to ba, Mami ta dauko ma Nihad wani dankunnen gwal mara nauyi ta mika mata tace "Sa wannan" Nihad ta kai hannu a hankali ta amsa tace "Nagode" sannan ta saka dankunnen, Mami ta dau nata mayafin ta yafa a shoulder tana kallon Nihad tace "Mu je" Nihad ta nufi kofar ta bi gefen Khalil ta fita, Mami na isa bakin kofar ya matsa a hankali ya bata hanya, makullin motarta ta mika masa tace "Mu je" Yayi karfin halin cewa "Where Mami?" Mami tace "Amshi makullin a hannuna ko?" A hankali ya kai hannu ya amsa, Mami ta fita Nihad na biye da ita. Har suka fito compound din gidan babu wanda suka hadu da a hanya kamar dai babu kowa gidan, Nihad ta dinga bin compound din da kallo, it's soo beautiful and big, Khalil ya nufi Ride din Maminsa yana tafiya a hankali, gaba daya ya rasa tunanin da xai yi, Mami ta dinga amsan gaisuwan da securities din cikin gidan ke mata, Nihad dai sai binta take tana satan kallonsu, back seat Mami ta bude tana kallon Nihad tace "Shiga" Nihad ta shiga motar a hankali, Mami ma ta shiga sannan ta kulle motar, bayan few minutes Khalil ya ja motar ya fita compound din bayan an bude masa wagegen gate din gidan, slowly khalil ke driving din har suka fita anguwan, sai a sannan yana kallon Maminsa ta madubi cikin sanyin murya yace "Where are we going Mami?" Mami tace "Take me to Maryam's house" Ya d'an sauke boyayyen ajiyar zuciya sannan ya nufi gidan Aunt dinsa, Nihad sai kallon anguwanni masu kyau take, amma kana mata kallo daya zaka san she is worried, suna shiga estate din su Aunty Maryam basu dade suna tafiya ba suka isa gidan, Khalil yayi horn bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Mami ta sauka tana kallon Nihad tace "Sauko" Nihad ta sauko, ta bi bayan Mami zuwa gidan, Aunty Maryam ta rungume Khalil tana welcoming dinsa cike da farin ciki tace "Idon son dina kenan nake gani haka?? Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah" Murmushi kawai yayi ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa daga sama har kasa, Lokaci daya er fara'ar fuskarta ya bace tace "Welcome son, Allah Ubangiji ya saka maka abinda aka maka" Murmushi kawai shi dai yake, Aunty Maryam na rike da hannunsa ta nufi parlor tana gaida Mami da ladabi, murmushi dauke fuskarta tace "Har kinyi Kumari yar uwa, Allah Ubangiji ya raba mu da mugun ji da mugun ganin" Murmushi kawai Mami tayi, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take don ita ma kana kallonta kasan halfcast ce, fara ce kal kamar Mamin khalil, sannan ita ma ga gashinta da tayi packing har kusan gadon baya, Aunty Maryam ta kalli Nihad don sai sannan ta lura da ita tace "Sannu da zuwa yan mata, shigo ki zauna" Nihad ta sauke kanta ta zauna kasa a hankali ta gaisheta, Aunty Maryam ta amsa tana Zaunawa gefen yayarta, tuni mai aikin Aunty Maryam ta cika gabansu da ruwa da lemo da kayan maqulashe, Aunty Maryam ta kasa daina kallon Khalil tana murmushi, she is so happy seeing him, can dai ta kalli Mami tace "Ya gida Aunty?" Mami tace "Alhamdulillah, kira mai aikinki ta shiga da bakuwar nan ciki ta bata breakfast naga bata wani yi a can gida ba" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Ayya, to bari in kirata ta zo" Aunty Maryam ta kira mai aikinta a waya sai gata ta taho tace "Gani Hajiya" Aunty Maryam tace "Ki shiga da bakuwar nan guess room ki hada mata breakfast yanzu" Yarinyar tace "Toh Hajiya" Aunty Maryam ta kalli Nihad tace "Tashi ku je yan mata" Nihad ta mike a hankali ta bi bayan mai aikin da tayi wani bangaren daban da ita. Mami na kallon Khalil tace "Ko da za ayi sati admission letter din bai fito ba xata zauna nan har ta karba sannan ta koma gidansu" Khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Who is she Aunty?" Mami tace "Tare ya zo da ita" Aunty Maryam ta kallesa tace "Wacece ita din" yayi kasa da murya yace "Yarinyar mai gidan da na zauna a kano" Aunty Maryam tace "Allah sarki, Admission take nema nan din?" Ya gyada kai kawai, Aunty Maryam tace "Lallai ya yarda da kai tunda har ya bar ka da yar sa har ku ka taho tare, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi" Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace "Ameen" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "Yaushe tafiyar naku, naji shiru baki ce komai ba" Tace "Ohh wllh yace sai yayi settling a can kafin mu bi sa, may be nan da sati biyu in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai mu" Aunty Maryam tace "Ameen" Khalil yayi kasa da murya cike da karfin yace "Mami about that video.... yan dakinsu ne a makaranta suka mata bata sani ba, sannan suka saki a social media... the Case is silently in court now, mahaifin nata yayi sueing dinsu gaba daya, so that's why zai canza mata makaranta yanzu, since the incident yake processing admission dinta a nan garin so coincidentally xan taho sai yace mu taho tare da ita" shiru yayi cause he him self knows he sounds so stupid, there is nothing making sense in what he is saying, Mami tace "Toh ni ka ji nace wani abu Khalil? Allah dai ya tsare mana zuri'a gaba daya, kawai ta zauna nan har sanda xa ta amshi abinda ta zo amsa sai ta koma gida, ae shikenan ko...." Aunty Maryam dake ta kallonsu tace "Wai me ke faruwa?" Mami ta sauke ajiyar zuciya briefly tayi mata bayanin abinda ya faru daxu da safe da yara suka shigo, Aunty Maryam ta saki baki da mamaki looking speechless, can ta kalli Khalil tayi kasa da murya tace "Wai kana nufin wancan ita ce yarinyar da video dinta yayi trending weeks ago?" Khalil bai iya yace komai ba, Aunty Maryam ta girgiza kai hankali tashe tace "Amma ta bata wayonta, tayi tarnishing image dinta a idon duniya, ta kuma yi ma kanta ta6on da goguwansa sae wani ikon Allah, duk yanda aka yi bata ji, banda bata ji meye zaki zauna daga ke sai skimpy inner wears a daki har maki video kina dariya, kai ai abun nan bai min dadi ba wallahi, Allah Ubangiji ya tsare mana zuri'a, amma wannan ta6on ai baxai gogu ba har tsawon rayuwarta sai ma ta tashi aure zata gane hakan barin idan tana da mahassada" Kallonta kawai Khalil yake baya cewa komai, Aunty Maryam ta rike ha6a cike da jimami tace "Kaii, sai kawai naji bata burgeni ba don bana son yaro mara kamun kai, don da tana da kamun kai da babu yanda xa ayi tayi abinda tayi, babu yanda xa ayi hakan ya faru da ita, wallahi ranan da naga videon ta sai da nayi tashin dare nayi addu'a Allah ya kare mana xuri'a da al'ummar Musulmi baki daya, abun sam babu dadi, gashi babu inda wannan videon bai je ba, kuma kun ga wllh ban ganeta ba ni banda kun yi magana, to ma banda abun uban nata ai aurar da ita kawai ya kamata yayi a yanzu ba wai ya sake biya mata makaranta a wani wajen ba, tana kanon ma a gabansu tana shakiyanci ina ga ta hadu da yan matan garin nan ai kuma sai abinda hali yayi, gata wata sumu sumu kamar bata magana... To kai garin yaya kasan mahaifin nata?" Khalil ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa take, Aunty Maryam tace "Kayi shiru" Ya dago ya kalleta a hankali yace "A sanda na sauka a kano bani da kowa bawan Allahn ya rike ni tamkar dan sa, yayi accomodating dina, yayi feeding dina without knowing who i am, mahaifiyarta mace ce mai kirki warce saboda ita nayi dadewar da nayi a tare da su, ina jin ta kamar ke da Mamina a gidan, yayyinta maza kuwa zaman mutunci da girmama juna muka yi da su, basu ta6a nuna min ni ba dan gidan bane, haka sauran yan uwanta mata dake gidan, abinda nake so ku gane, ba wai na je masu da real identity dina bane, i went der as a nobody, babu wanda yasan wanene ni har yanzu da nake maku magana banda ita yarinyar yanzu, amma suka min karamci a irin wannan zamanin da muke ciki, i know i can never repay them their good deeds, kuma yace in taho tare da yarinyarsa ta amshi admission letter saboda wani mistake nata sai in ki?" Aunty Maryam ta sauke ajiyar xuciya tace "Baxa ka ki ba kam, amma surutun yan gidan nan naku ake gudu" Mami ta kalli Aunty Maryam tace "That is it dear, abinda na guda kenan na kawota nan gidan har ta gama abinda ya kawota ta koma, banda mu da muka san wannan labarin da ka fada a kan gidansu yarinyar waye ya sani? Nobody, kai ko sun ji cewa xa su yi karya kake, don haka duk abun magana gudunsa nake nan da ka gan ni, daxun ma da suka shigo ba saboda Allah bane, gulma ce ta kawosu, yarinyar kawai suka zo gani, ita kuma wannan yarinya ta bata wayonta don waje daddaya ne xata je aki ganeta, Allah dai ya kiyaye ya tsare mana zuri'a, ya bata mijin da xai aureta yayi overlooking mistakes dinta ya rufa mata asiri duniya da lahira, da da mijin ma da auren kawai yayi mata ta ci gaba da karatun nata a dakin mijinta don hakan zai fi mutunci, Allah dai ya takaita mata gori a duk inda xata kasance" Khalil dai kallonsu kawai yake, Aunty Maryam tace "Ameen, da ganin wannan lamari kasan influence na bad friends ne hade da rawan kai irin na yaran yau, saboda haka ne ya kamata mu kara sa ma yaranmu ido sosai" Wayar Mami ya fara ring ta daga ta kai kunne, bayan sun gaisa tace "Lahh ai gani a gidan Maryam, kin fito ne?" Mami tace "Yauwa to, kawai ki taho nan din idan kin fito, shima yana nan ai" Daga haka ta katse wayar, Aunty Maryam na kallonta tace "Wacece?" Mami tace "Hajiya Safeenah ce" Aunty Maryam tace "Allah sarki, taji sauki kenan" Mami tace "Aa da sauki sosai, 3 days ago ma ai taje can gida wajena" Aunty Maryam ta mike tace "Bari inje in sanar ma mai aikin can tayi mata wani abun kafin ta iso" Daga haka ta bar parlon, Mami na kallon Khalil tace "Wai fasa tafiyar kayi yau Khalil?" khalil na danna wayarsa yace "Sai na shirya Mami" Aunty Maryam ta ɗan tsaya kitchen din tayi assisting mai aikinta bayan da ta gama hada komai ta bar mata ta fito parlor, duk bata tarar da su a parlon ba, har zata wuce sama sai kuma tayi bangaren guess ta kara ganin Nihad, don kawai abun ya tsaya mata a rai tun daxu, bude kofar dakin tayi ta shiga ta ganta zaune kasa ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam na kallon abincin dake ajiye tace "Baki yi breakfast din ba?" A hankali Nihad tace "Na koshi" Aunty Maryam tace "Toh fito parlor kiyi kallo, yara sun jogane kayan kallon nan din sai an gyara" Nihad dai bata ce komai ba ganin Aunty Maryam ta juya ta mike a hankali ta bi bayanta, har suka fito parlor tare, nan din ma a kasa ta zauna, Aunty Maryam ta tafi ta kulle kofa sannan ta wuce sama wajen Mami, Khalil na kwance saman kujera Mami na basa labarin abubuwan da suka faru baya nan, Aunty Maryam ta zauna kenan aka kira Mami, Mami ta daga tace "Kin iso ne?" Sai kuma Mami tace "To bari a bude" Katse wayar tayi tace "Kin kulle kofar parlon ne Maryam?" Aunty Maryam ta kalli Khalil da sauri tace "Dr ka bude mata kofa, yanzu kuma na kulle kafin in hauro" Ya mike ya fita daga parlon ya sauka downstairs, Nihad na zaune ta k'ura ma Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi a ciki take ba, kallo daya yayi mata ya nufi kofar parlon ya bude, Da ladabi ya gaisheta yayi mata sannu da zuwa, da fara'a tace "Maa sha Allah, ka dawo lafiya Khalil?" Yace "Alhmdlh mum" Tace "Toh Alhamdulillah, sannu, Allah Ubangiji yayi maka albarka" Yana murmushi yace "Ameen" Sannan ya koma gefe ta shigo parlon, ya juya ya nufi inda remote yake ya dauka don rage volume din Tvn, a hankali Nihad ta gaisheta ta amsa da fara'a, Khalil Yace "Suna sama Mumy" Upstairs ta nufa, Kamar ance ya juya ya ganta ta jingina da kofar parlon tana kallonsa tana murmushinta me kyau, wara ido yayi kafin yace komai ta taho da sauri ta rungumesa ta lumshe ido a hankali tace "I have missed you so much" Daga kai Nihad tayi ta kalleta, shi kam yayi stiff a wajen da yake duk ya daburce cause she took him unaware, Lokaci daya ta lura da Nihad dake wajen da sauri ta sakesa ta koma baya tana mata murmushi tace "Sannu, sorry i just badged in, Assalamu alaikum" Nihad dake kallonta daga sama har kasa ta dauke kai kawai, Khalil ya bude palm dinsa with surprise yace "But you didn't say u are coming with Mum" Ta langwabar da kai smiling at him tace "Surprise" Kallonta kawai yake, a hankali hawaye na taruwa idonta tace "I missed u so much..." Ya mata wani kallo yace "Come off it dear" Lokaci daya Nihad ta mike ta fice daga parlon zuwa guess room da take ciki daxu, Nadeeyah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kallesa tace "Dear Wacece ita? Ko dai taji haushin yanda na shigo ko? Wallahi i was just overwhelmed" Khalil ya daga kafada yace "No, kece dai kika ga haka...." Tace "Ohk, tayi hakuri in ma taji haushina ne, where is Mami?" Ya nuna mata sama tace "Let me go and greet her" yace "Ohk dear" Tana barin wajen ya bi ta da kallo har ta haura sama.....






Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah




Ur evidence via 07087865788




Assalamu alaikum manyan mata!!


For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰




Join my WhatsApp group for beautiful samples.


Contact https://wa.me/c/2349090591769
[8/15, 8:24 AM] Maman Al'ameen VIP: 💖💖 NIHAAD 💖💖


40




Aunty Maryam ta kai hannunta saman shoulder din Nihad ta dafata a hankali tana kallonta don har sannan tunane tunane take with shock written all over her, da sauri Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tana girgiza kai tace "Ni ba wanda ya taba gaya min abubuwan nan, ni ban sani ba, you are just telling me now" Aunty Maryam tace "And hope you've realized what i am saying?" Nihad ta gyada kai hawaye na sauka idonta, sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Aunty Maryam tace "Ni ban san bata so na ba Aunty, Lokacin wani saurayina yace iyayensa xa su xo gidanmu shine na gaya mata sai tace min kar in gaya ma kowa har Mumyna, ita da kanta xata je ta gaya ma Abba, na gaya mata da few days aka saki Video dina a internet shine yayi blocking dina" Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonta and she was speechless, Nihad na kuka sosai don sai sannan abubuwan ke dawo mata, sai yanzu ƙwaƙwalwarta ya fahimci abubuwa da dama, Tana kuka sosai tace "Da Abbana ma ya koreni bata ce komai ba" Aunty Maryam ta dafata da sauri tana kallonta da mamaki tace "Ya koreki daga ina?" Cikin raunin murya Nihad tace "Gidanmu, yace baya son ya sake ganina har abada, she was standing at the door bata ce masa komai ba, and she saw me leaving the house" Sai ta kara fashe da kuka sosai, she is so pained, bata ta6a kallon Umma from this perspective ba, ga dai komai vividly a bayyane amma bata ta6a ganewa ba, Aunty Maryam tayi karfin halin cewa "Kina nufin he sent you away from his house?" Nihad ta gyada mata kai tana kuka, Aunty Maryam ta kasa rufe baki, can ta kalleta da kyau tace "Dalilin kawo ki garin nan da Khalil yayi kenan dama?" Sai a sannan Nihad tayi realizing she just said what she's not suppose to say to her, ta dakatar da kukan da take da sauri ta hadiye abu da ya tokareta a throat, ta kalli Aunty Maryam, sai kuma ta fara kame kame "Aa Aunty kawai dama.... Dama, makaranta...." Aunty Maryam da tuni ta ganota tace "Kar ki min karya" Nihad ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Jikin Aunty Maryam yayi sanyi sosai, wato dalilin kawota Abuja da Khalil yayi kenan? But ai Mami tace mata Abba ne ya bukaci ya dawo kuma, she became so confuse at this point, Can ta kalli Nihad tace "Ya isa haka, ki daina wannan kukan, ki tafi bandaki ki wanke idonki ki kwanta kafin Asuba ya karasa" Nihad ta kasa ce mata komai, Aunty Maryam tace "Tashi" Tashi tayi da kyar tana jan kafa ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito, Aunty Maryam tace "Ki kwanta, kuma bana son ki sake wannan kukan kin ji me nace?" Nihad ta gyada mata kai ta kwanta saman gadon, Aunty Maryam ta mike ta fita daga dakin ta kullo mata kofar. Kwanciyar da Aunty Maryam bata sake yi ba kenan har gari ya waye, lamarin Nihad ya tsaya mata cak a zuciya, taji tausayinta da mahaifiyarta ainun, ta kuma ji mata takaicin wannan baƙin taɓon da aka mata da xai bibiyeta har karshen rayuwarta, this is soo painful, ta kuma tsine ma Umma ta la'anceta yafi a kirga, ta jima bata ji labarin irin wannan zaluncin da aka ma Nihad ba, ta kara tabbatar da cewa kishiya bala'i ce kuma masifa ce. ƙarfe takwas saura ta kira Khalil, yana bedroom dinsa kwance yayi nisa a tunanin da yake, he is so confused and looking for a way out a kan wannan lamarin, gaba daya kansa ya daure on what next to do, ko jiya da daddare sai da Mami ta sake masa magana yayi kokarin ganin Nihad ta amshi admission letter din nata ko gobe ne kar a shiga weekend, idan yaso idan ta amsa ko ranan sai ta bi jirgi ta koma gida, ita dai duk ta damu ace Nihad ta tafi gida, ga Abba a jiyan shi ma yayi masa maganan business din da zai yi a zanzibar, which he will be leaving Nigeria in 2 days time, that is on Sunday, kiran Aunty Maryam ya kara rikita masa lissafi ya mike zaune da sauri yana kallon wayar, Allah ya sa ba wani maganan Nihad tayi mata ba dai, sai da wayar ya kusa katsewa ya daga ya kai kunne, yayi composing kansa yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau, idan baka komai ka taho yanzu ina jiranka" Nan yaji gabansa ya fadi sosai, Ya dake yace "Hope all is well Aunty?" Tace "Nace dai ina jiranka" Yayi gathering courage yace "Toh" Daga haka ta katse wayar, duk da sanyin Ac dake dakin ji yayi zufa na keto masa ta ko ina, he just can't Imagine ace Nihad tace mata ai an daura mata aure da shi, yayi saurin kawar da tunanin don bai ma son yayi, ya sauka daga saman gadon da kyar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito, cikin few minutes ya gama shiryawa ya dau perfumes dinsa ya fesa sannan ya dau makullin motar Mami dake wajensa ya fita, ko part dinta bai tafi ba ya fita zuwa compound, har Khalil ya isa gidan Small mum dinsa ba shi da nutsuwa babu tunanin da bai zo ransa ba, tunda ya san ba wani saiti gare Nihad ba nan da nan zaka bugi cikinta ta bude maka komai, yana parking compound din Aunty Maryam ya kashe motar ya sauka sannan ya nufi parlonta, xuciyarsa na bugawa ya kwankwasa kofar parlon, mai aikin ta bude, ta gaishesa ko amsawa bai yi ba ya karasa ciki ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, sai ga kiran Aunty Maryam a wayarsa ya daga ya kai kunne tace masa ya hauro sama, ya mike yana kallon mai aikin yace "Ke ina bakuwar da take gidan nan?" Da

Please Login or Register in order to submit comment