Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abun shi da Allah "
Idanun shi jawur yace
"A'a k'anwata baza ayi haka ba sun zalunce ki da yawa bazan kyale su ba don suna tunk'aho su masu kud'i ko suna tunanin zan ji tsoron su to wallahi a'a sai na ja dasu kuma sai nayi nasara "

Hannun shi Suhaima ta k'ank'ame tana kuka tace
"Na had'a ka da girman Allah Yaya kayi hak'uri ka kyale su idan har kana son ganin farinciki na mu bar wanda ya aikata da Allah da sannu Allah zai saka min "

Tsayawa yayi kallon ta na wasu 'yan mintuna kafin yace
"Tabbas ina son ganin ki cikin farinciki k'anwata zan kyale su saboda ke kawai"..

Rungume shi tayi tana cewa
"Yawwa Yaya na nagode "

Shafa kanta yayi sannan yace
"Allah yayi miki albarka k'anwata, yanzu bari na kai miki ruwa kiyi wanka da sallah kici abinci"

"Amin Yaya na "
Har ta mik'e ya sake rik'e hannun ta sannan yace
"K'anwata kiyi min alkawarin kin rabu da Sabeer har abada "

Shiru Suhaima tayi tana mai sunkuyar da kanta ta rasa abin da zata ce ma, ta d'an jima ahaka sannan ta d'ago kanta ta kalli Yaya Aliyu wanda yake kallonta yana jiran me zatace, har ta bud'e bakinta zata yi magana da sauri Aunty Aliyah ta tari numfashin ta tare da cewa
"Yaya abar wannan maganar don Allah taje tayi wanka tukunna "

Aunty ta fad'i hakan ne don batason Suhaima tayiwa Aliyu alkawari don tasan irin soyayyar da Suhaima da Sabeer suke yiwa junan su rabasu abu mai wahala ne tasan kuma idan ya huce sai ya dawo inda Suhaima take, tasan mak'iya ne basa son ganin su tare musamman 'yan uwan Sabeer da tasan irin k'iyayyar da suke yiwa Suhaima saboda kawai don ta kasance talaka 'yar kauye, tana son Suhaima da Sabeer amman sai ya gane kuskuren shi na yanke hukunci kafin bincike.


Sakin hannun ta Aliyu yayi sannan yace
"Je ki kiyi wankan "
Cikin sanyin jiki ta wuce yayi da Yah Aliyu ya bita da kallon tausayi yarinya k'arama an mayar da ita bazawara auren da ko shekara bai rufa ba, da ace ana dawo da abin da ya wuce da ya dawo rayuwar su baya ko dan ya goge Sabeer daga rayuwar Suhaima, amman ina kaddara ta riga fata Allah ya rubuta sai hakan ya faru dasu zasu rungumi kaddara su koma zasu cigaba da godewa Allah a duk halin da suka tsinci kansu aciki, wasu hawaye ne suka zubo mishi da ya tuna mahaifiyar su da irin bak'incikin da ta fuskanta awajen d'a namiji kafin ta mutu.

Baisan ma hawayen na zuba ba sai da yaji hannun Aunty Aliyah suna goge mishi hawayen, cikin sanyin murya tace
"Kayi hak'uri Yaya komai tsanani yana tare da sauk'i rayuwar Suhaima zata inganta agaba insha Allah "

"Amin mata ta! Na gode da kulawar ki agare ni "

Tashi yayi yana kok'arin had'awa Suhaima ruwan wanka nan Aunty Aliyah ta kar6a ta had'a mata sannan ta kai mata toilet.

Shiga d'akin ta tayi ta tarar da Suhaima a zaune ko kayan jikin ta bata cire ba nan tayi zaman rarrashin ta kafin ta cire kayan ta d'aura zani ta fita wanka inda Aunty Aliyah take fad'a mata bayan tayi wankan ta zauna cikin ruwan d'umi sosai.

Bayan ta gama wankan ne ta sai kayan Aunty Aliyah ta sanya saboda kayanta sunyi datti gashi tafiya bata kwanciyar hankali ba bata taho da wasu ba, abinci ma kasa ci tayi sai fura Aunty Aliyah ta dama ta Yah Aliyu da kanshi yake bata a baki, bayan ya gama bata ne sai tasha paracetamol saboda yanda kanta yake ciwo sosai ta kwanta kan 3siter d'in d'akin Aunty ta lumshe eyes nata hannunta d'aya dafe da kanta, tunanin kawai maganganun da Sabeer yayi mata take da yanda yace ta fice mishi daga gidan shi ya tsane ta, hawaye masu zafi ne suke zubo wa daga eyes nata.

Yah Aliyu da Aunty Aliyah ne suka zage wajen gyara mata d'akin Suhaima na da gyara shi sukayi tas, suka share har zasu fito daga d'akin Yah Aliyu ya tsaya kallon d'akin na 'yan mintuna kafin ya sauke ajiyar numfashi yace

"Aliyah ya kamata na gyarawa Suhaima d'akin ta yayi kyau sosai duk wani jin dad'i ma zan tanadar mata koda duk abin da na mallaka zai k'are, don haka cikin satin nan zan nemi mai siyan d'ayan gonata na siyar sai na bar d'ayar kawai ta ishemu zaman duniya dai "

Gid'a kai Aunty Aliyah tayi kafin tace
"Gaskiya kam ka kyauta Allah ya k'ara had'e kanku Allah kuma ya k'ara bud'i "
Yana murmishi yace
"Amin mata ta "
Har zasu fito daga d'akin Aunty Aliyah tace
"Ni kuwa ina maganar cigaba da karatun ka da kayi min maganar kwanaki naga baka k'ara cewa komai ba? "
"Tana nan maganar don har na samu gurbin karatu na k'arasa secondary yanzu zan zana jarabawar wec da neco"
Murmishi Aliyah ta saki tare da cewa
"Masha Allah abu yayi kyau Allah ya taimaka ya bada sa'a "
"Amin Amin "
Daga haka suka fito daga d'akin zuwa d'akin Aliyah tarar da Suhaima tana kuka ne ya sanya su tsayawa suna rarrashin ta dakyar tayi shiru sannan suka rakota d'akin ta nan ma sun jima sannan suka yi mata sai da safe suka tafi.

Cikin wannan daren ya zamewa Suhaima wani irin dare na bak'inciki musamman idan ta tuna jiya kamar yanzu suna tare da Sabeer suna nunawa junan su zazzafar soyayya, tayi kuka Suhaima awannan daren har sai da taji kamar kanta da idanun ta zasu zazzago da ciwon da zafin da suke mata.



************

Cikin nutsuwa yake motsawa tare da kok'arin bud'e eyes nashi dakyar ya samu ya bud'e su saboda hasken da yake dallare mishi ido, kallon d'akin yake cikin mamakin me ya kawo shi, duk ya rame bakin shi ya bushe kallo d'aya zaka yi mishi kasan cewa bashi da cikakkiyar lafiya.

"Alhamdullilah Son ka farka? "
Cewar Mumy da shigowar ta room d'in kenan, cikin farinciki ta k'arasa inda yake ta zauna tare da rik'o hannun shi tana goge hawayen idonta da d'ayan hannun, don sosai lalurar Sabeer ta firgitata sosai don yau kwanan shi 3 a kwance sai drip kawai da ake sanya mishi tunda yayi doguwar suman nan.

Bai kulata ba duk yanda taso da yayi magana kawai sai ya kwanta tare da juya mata baya, runtse eyes nashi yayi yana tunano musabbabin abin da ya sanya shi cikin wannan halin, tar komai ya dawo mishi cikin brain nashi a hankali wasu hawaye masu zafi suka fara sauko mishi idan ya tuna yanda Suhaima ta cuce shi bai ta6a zaton Suhaima zata aikata hakan ba agare shi.

Tashi ya yunkura yayi dakyar sai dai ko taku biyu bai yi ba sai yayi luuu kamar zai fad'i da sauri Mumy ta taro shi ya fad'o jikinta a kid'ime tace
"Son ya zaka tashi cikin wannan yanayin kasan jikin ka babu kwari? "
Cikin fusata yake cewa
"Mumy ki barni na kai Suhaima k'ara akan abin da tayi min bazan kyale ta ba sai na d'auki fansa akanta na yanda take zubar min da yara na "
Wani dad'i ne ya kwaranya cikin heart d'in Mumy amman sai ta marairaice tare da cewa
"Haba Son ka kyale mata Allah sai ya saka maka yanzu samun lafiyar ka shine kwanciyar hankali na "

Nan Sabeer ya birkice mata sai yaje ya sanya an kama Suhaima sai sumbatu yake daga kasan ba'a ciki hankalin shi yake ba, gani haka ya sanya Mumy yi mishi allurar bacci babu dad'e wa bacci yayi awon gaba dashi ta gyara mishi kwanciyar zuciyar ta fal farinciki....



********


Cikin tsananin 6acin rai Yaj Aliyu yake cewa
"Ki fita daga gidan nan Jiddah bana son ganin ki daga ke har 'yan uwan ki macuta "

Cikin rikicewar kuka Jiddah take rik'e k'ofar shiga gidan saboda kok'arin rufeta da Yah Aliyu yake yi
"Yaya Aliyu don Allah kayi hak'uri ba laifi na bane inason ku wallahi baza'a ta6a had'a baki dani a cuce ku ba ka tsaya nayi maka bayani"

"Tun kafin naji miki ciwo Jiddah ki fita daga gidan nan nace zan iya illata ki idan baki tafi ba "

"Allah Yaya Aliyu sai dai ka kashe ni bazan tafi ba, Suhaima Aunty Aliyah kuce mishi ya tsaya ya saurare ni Suhaima ki fad'a mishi babu hannuna wajen aikata miki haka "

Jiddah ta fad'i tana kallon su Suhaima da Aunty Aliyah da suke gefe suna kuka ganin yanda Yah Aliyu yake korar Jiddah.

Wani irin k'ara Jiddah ta saki da k'arfi saboda yanda Yah Aliyu ya rufe k'ofar da k'arfi har yana mutstsukewa da hannun ta, a rikice Suhaima ta k'arasa wajen tare da bud'e k'ofar Jiddah ta zame hannun ta har sunyi ja sosai tana kok'arin k'arasa wa wajen Jiddah Yah Aliyu ya damk'ota tare da rufe k'ofar gidan 6am har da sanya sakata, Suhaima naji kukan Jiddah tana bubbuga k'ofar sai dai bata da ikon bud'e wa wani kuka ta fashe dashi tare da shiga d'akinta da gudu...........



Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
[4/13, 12:39 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*




Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ


ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ


♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*



*PAGE 97-98*






Jiddah ta dad'e tana kuka anan sosai Babaa Lantana ce da Baba Adamu suke rarrashin ta don Yah Aliyu yak'i tsayawa ya saurare shi ranshi a 6aci yake sosai da abin da akayi wa k'anwar shi.

"Babaa Lantana Baba Adamu ku taimaka min ku fahimtar da Yaya Aliyu wallahi ba had'in hannuna cikin abin da akayi wa Suhaima ni kaina yanzu binciken da nake yi kenan don gane gaskiya amman bai kamata Yaya Aliyu yayi min haka ba? "
Ta k'arasa maganar tana goge hawaye.

"Yanzu dai yanda Aliyu ya d'auki zafin nan ki bari har zuwa lokacin da ya huce don yanzu bazai tsaya sauraren komai ba ranshi ba k'aramin 6ace yake ba "
Cewar Baba Adamu kenan.

"Kiyi hak'uri Jiddah ki koma gida duk lokacin da ya huci zan sanya Aliyah ta kirawo ki awaya sai kizo "

Gid'a kanta Jiddah ta iyayi kawai daga nan ta shiga mota driver ya jata, wani tsanar familyn su ya d'arsu cikin zuciyar ta yanzu da ba don sun aikata haka ba da tuni Suhaima tana tare da masoyin ta Yah Sabeer, dole zanyi iya yi na do ganin an kama wanda ya aikata haka bazan iya jure rashin Suhaima kusa da ni ba ina sonta, lallai Yah Sabeer ba k'aramin ganganci yayi ba na korar Suhaima don koda zata dawo gidan shi sai yasha wahala ba k'arama.



Tun daga lokacin abubuwa suka fara canjawa don Sabeer sai da yayi wajen sati biyu a hospital kan a sallame shi, yayi wani irin ramewa sosai ko abinci baya iya ci sosai sai an matsa mishi ga wata k'asumba da ya tara yak'i yarda yaje aski agyara mishi ita sannan Mumy ma tayi kok'arin cire mishi ita da kanta amman yak'i yarda, gaba d'aya Sabeer ya canja ya koma wani iri kamar bashi ba yana zuwa aiki office amman daya dawo fah idan ya k'unshe kanshi a d'aki baya sake fitowa sai dai idan sallah zai tafi masallaci.


Ya fara zama mafad'aci abu kad'an zai fara fad'a baya shiga harkar family d'in shi kamar da, har wani lokacin ita kanta Mumy tsoron kulashi take tana mai mamakin me ya canja mata d'anta lokaci d'aya haka, idan ya sake da wani suna hira har da murmishin shi to Daddy ne kawai don ko Dr Ahmad d'an fillo baya sake musu kamar da, sosai abin yake damun su a ransu Jiddah ma baya kulata sosai kamar da sai gaisuwa ce kadai ke tsakanin su idan ma har sun had'u, ita kanta Jiddah duk yanda take da son Sabeer tana jin haushin shi.


Duk yanda yaso da ya fitar da Suhaima daga zuciyar ya kasa ji yake kamar ma k'ara mishi sonta yake, baya iya bacci kullum sai yaga pic's d'in ta, yayi kukan sosai wani lokacin ji yake daman zai iya cire zuciyar shi ya fito da ita ya goge son Suhaima aciki ko ya huta da abin da yake ji cikin zuciyar shi.


Ta 6angaren Suhaima itama kusan haka al'amarin suke sai dai ita ta cigaba da zuwa makarantar islamia kullum da yamma duk da tayi saukar alqur'an but tana sake fad'ad'a karantun ta da sauran litattafai, gashi bata yi rama kamar yanda Sabeer yayi ba don ita sosai tana kok'arin yakice shi cikin ranta ga kuma yanda Yah Aliyu suke tsananin bata kulawa duk da har yanzu son Sabeer na mak'ale cikin zuciyar ta, kullum idan tayi sallah tana addu'ar Allah ya toni asirin wanda yayi mata wannan sharrin, har a makaranta tana fad'a wa Malamai su sanya ana mata addu'a Allah ya yaye mata abin da yake damunta, sai dai kuma tana shan zund'e akauyen shi don tasha surutai don ma Yah Aliyu yayi musu kyakkyawa warning duk wanda ya k'ara nuna k'anwar shi da hannu yana aibatata sai ya sanya an d'aure shi da wannan warning da yayi musu suka samun sauk'in abun don Yah Aliyu yana da arzik'i duk ta sanadiyyar noma da kiwon da ya rik'e hannu bibbiyu.


Ko zancen Sabeer ba'a k'ara tayar dashi ba agidan ba kowa yabar abun cikin zuciyar shi, duk wani kyautata wa Yah Aliyu yana kok'arin yiwa Suhaima duk abin jin dad'i yana kok'arin bata shi.


Ya sanya anyi gyaran gidan sosai ya kashe kud'i sosai agyaran, ginin zamani na dai dai talaka mai rufin asiri ya sanya akayi mishi, sai gidan Baba Adamu suka koma akayi gyaran, inda Suhaima ta samu yalwataccen d'aki babba guda d'aya har da toilet aciki ya sanya akayi mata, sai kuma palo babba da akayi da 2 bedrooms wanda ya kasance na Aunty Aliyah da nashi sai kitchen da toilet a waje, amman filin tsakar gidan ya ragu sosai gashi ko'ina yasha sumunti dak'unan tiles ya sanya aciki, hatta furnitures sababbin ya sanya na dai dai mai rufin asiri ban da kayan kallon da ya had'a musu duk wannan abin Yah Aliyu yayi shine don kawai faranta ran Suhaima saboda yana ganin tayi rayuwa ta cikin kud'i tsayin wasu watanni ta fara sabawa da jin dad'i shine dalilin da ya sanya yayi haka duk da ya san bai kai rabin rabin kyan da gidanta na da yake dashi.


Suhaima taji dad'in abin da Yayan nata yayi mata kawai don ganin farincikin ta, nuna mishi farincikin ta da yayi ne a lokacin ya sanya shi cikin jin dad'i da walwala wanda rabon da ya kasance cikin haka tun kafin Suhaima ta dawo gida, acikin wannan lokacin ne yaje ya zana wec and neco a wata secondary ta gaba da kauyen su don makarantar ma ta shiga cikin gari sosai, Suhaima ba k'aramin jin dad'i tayi ba na komawar da Yayanta makaranta da zai yi, shima yace mata ta kwantar da hankalin ta zai nema mata wata university d'in ta d'ora karatun ta sai ya cikawa mahaifiyar su burinta insha Allah na ganin sun samu ilimi sosai, saboda jin dad'in wannan maganar Yah Aliyu sai da Suhaima tayi kuka ashe daman zata cikawa kanta buri na ganin tayi karatu mai zurfi.

Bayan exam d'in su Yah Aliyu ta fito ne dakyar da sod'in goshi ya samu gurbin karatu a jami'ar Buk da taimakon wani Alhaji da yake kai mishi kwai da kaji duk karshen wata gidan shi a birni, duk da kyan da takardun Yah Aliyu sukayi inda zai yi karatun Mass com inda Allah ya taimake shi ma yana da machine d'in hawa sai dai cacar kud'in mai da haka ya fara karatun shi cikin nasara da kwanciyar hankali.


***********

_*AFTER 7 MONTHS*_


Sabeer ne na hango yana fitowa daga side d'in shi duk yayi wani tamkar ba Sabeer d'an gayu d'an kwalisa ba yana sanye cikin wani jallabiya milk mai yankakken hannu, tafiya yake kamar zai fad'i saboda yanda jikin babu kwari, bedroom d'in Mumy ya nufa yana son fad'a mata yana son shan coffee a dafa mishi.



Har ya d'ora hannun shi kan handle d'in bud'e k'ofar zai murd'a yaji muryar Mumy tana cewa
"Ga wannan kud'in na sallame ki daga yau ki koma kauyen ku yanzu yanzun nan don na fahimci sosai Daddyn Sabeer ke zargin ki kuma naga yana sanya miki ido a duk wani motsin ki nasan idan ya cigaba da hakan asirin mu ne yake daf da tonuwa, tunda kinyi nasarar raba wannan shegiyar matsiyaciyar da d'ana aikin ki ya gama, idan kuwa kika yi kok'arin tona min asiri kinsan zan iya sanya wa a kulle ki har karshen rayuwar ki ko a 6atar min da ke "

Cikin rawar jiki mai aikin tace
"Wallahi Hajia bazan ta6a tona miki asiri ba baza ki k'ara ganina ba ma har abada "

Wani murmishi Dr Faridah ta saki kafin tace
"Good da ya fiye miki alkhairi kuwa tashi maza ki had'a kayan ki ina son yau kibar gidan nan "
"Toh toh Hajia yanzu ma kuwa "

Ta kwashe kud'in mai yawa da Dr Faridah ta bata ta fito zata fita daga d'akin. Jikin Sabeer wanda ke rawa kamar mai yin rawar sanyi yayi hanzarin barin bakin k'ofar ya 6uya a wani corridor yana kallon ta ta wuce can part d'in su na masu aiki.


Cikin zafin nama Sabeer ya bita a baya da sauri aikuwa yayi nasarar ritsata zata shiga d'akin, kallon Sabeer take tuni cikinta ya d'auki k'ara yana hautsinawa ganin yanda ya rikid'a kamar wani zaki.

Bata ankara ba ya dalla mata mari har guda biyu zata yi ihu yayi saurin sanya hannun shi d'aya a baki alamar tayi shiru yana zare mata ido wad'anda suka yi ja jikin shi yana rawa sosai, ba shiri ta mayar da bakin nata ta rufe shi k'am har da d'ora hannu ta damk'e bakin nata.

Kafin ta ankara wani fitsari mai zafi ya kubce mata yana tsiyaya sai faman matse kafa take da sauri Sabeer yaja baya kafin yana yarfe hannu tare da duba jikin shi ko ta 6ata shi, belt d'in jikin shi ya cire ya fara zuba mata, sai rawar disco take gashi ba damar yin ihu, gani yayi belt d'in kamar bata shigarta sai kawai ya yar da ita ya nufe ta ya shak'e mata kamar zai kashe ta tuni idanun ta sun firfito kamar zasu zazzago ga dakyar take sauke numfashin ta, Allah ne ya kawo Daddy hanyar wajen zai tafi garden yaji kakari awajen ya nufo wajen, ganin abin da d'an nashi yake kok'arin aikatawa da sauri ya nufi wajen dakyar ya 6am6are ta daga hannun shi sai wani huci yake fuskar nan tashi tayi ja.

Yana sakin ta ta zube tana jan numfashi cikin rud'ewa Daddy yake girgiza Sabeer yana cewa
"Son me kake shirin aikatawa ne me tayi maka iyeeeee? ""

Cikin rawar murya Sabeer yake nuna ta da hannu yana cewa
"Dad.... Daddy kace ta tayi magana ita... itace ta... take zubar wa da Suhaima ciki "

"What! "
Cewar Daddy da sauri.

"Keee fad'a mana uban da ya sanya ki aikata hakan? "
Cewar Daddy a fusace, cikin rawar murya tace
"Don Allah kuyi hak'uri wallahi sanya ni akayi "

"Wane ya sanya ki? "

Murya na rawa da jiki na 6ari ta kasa magana sai da Sabeer ya daka mata wata razananniyar tsawa sannan ta bud'e baki dakyar tace
"Wallahi Hajiya ce ta sanya ni ba laifi na bane "
"Wacce Hajia? "
Cewar Daddy cikin zak'uwa.
"Hajiya Faridah ce wallahi take sanya ni zubawa Suhaima maganai a abu tasha sai cikin ya zube "

"What!? "
Cewar Daddy da Sabeer a lokaci d'aya suka furta hakan cikin matuk'ar razana tare da firgita da jin abin da tace, sulalewa Sabeer yayi a k'asa tare da d'ora hannun akai shikenan Mumy ta cuce shi ta gama dashi wayyo Allah nah Suhaima daman ba laifin ki bane yanzu ta ina zan iya dawo da Suhaima a rayuwa ta.

Wata zabura da yayi sai da ya firgita Daddy cikin tsananin fusata ya nufi cikin palo yana kwallawa Mumy kira, yayin da Daddy ya tura Larai cikin d'aki ya sanya key ya 6ame k'ofar don baza'a barta ta gudu a banza ba sai ta fuskanci hukunci dai dai da abin da ta aikata, kafin ya bu bayan Sabeer don yau za'a yi tashin hankali..............





Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
[4/14, 9:08 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*




Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ


ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ


♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*



*PAGE 99-100*








Mumy har ta fara gyangyad'in bacci acikin bedroom d'in ta bacci ne take son yi ko hospital bata lek'a ba sai da yamma, kamar cikin mafarki taji Sabeer na kwalla mata kira a firgice ta fito saboda tasan wannan kiran bana lafiya bane.


Cikin sauri take taka steps na bene saboda har yanzu Sabeer bai bar kiranta ba, cikin sauri ta k'arasa wajen shi inda yake tsaye tsakiyar parlour yana faman kiranta ga hawaye da suke zuba a eyes nashi.

"Son lafiya irin wannan kira haka? "
Kallon ta yayi hawaye na kwaranya a idon shi yace
"Mumy ashe bakya son bakya kaunata ko kad'an Mumy kin cuce ni kin cuce ni! "

Gaban Mumy ne yayi wani irin fad'uwa sosai da sauri ta dafe kirjin ta da hannu tare da zaro ido irin na shiga rud'u tace
"Son me kake nufi, me nayi maka har na cuce ka anya kanka d'aya ko wani abun kasha ne, ina matsayin mahaifiyar ka zan cuce ka ne ? "

Idanun shi jawur yace
" Mumy sam baki cika uwa mai bawa d'anta farinciki a rayuwa ba, kin rabani da 'ya'yana har biyu tun kafin su zama mutum kika zubar min dasu bayan haka kin rabani da mata ta Suhaima anya Mumy zan iya yafe miki kuwa? "

Sauran kad'an Mumy ta kife a k'asa tsabar firgita da kalaman Sabeer, amman sai ta wayance da cewa
"Haba Son wanne munafiki ne ya shirya maka wannan zancen kamar a mafarki, kada ka yarda da wannan shirmen zancen"

Kallonta Sabeer yake ba don mahaifiyar shi bace da idan ya shak'eta sai ta kusan daina numfashi, kasa magana ma yayi saboda takaici da bak'inciki sai wani irin kallo da yake mata mai tattare da nuna kin cuce ni, wannan kallon da Sabeer yake yiwa Mumy shi yafi komai d'aga mata hankali.

"Kada ki nemi ki raina mana hankali Faridah daman nasan duk wannan abun da ya faru da sanya hannun ki aciki"
Cewar Daddy a fusace wanda k'arasowar shi palourn kenan.

Kukan kissa da munafurci Mumy ta saki tare da cewa
"Na shiga uku Daddyn Sabeer ni kuke cewa na aikata hakan ta ina, na ta6a zuwa gidan Sabeer ko kuma na ta6a bata wani abun da hannuna taci cikin ya zube? "

Sam Mumy ta d'auka Larai tabar gidan kamar yanda ta umarce ta. Cikin fusata Daddy yace
"Ta dalilin 'yar aikin ki Larai mukasan komai, wadda kika turata gidan Sabeer don tana taimaka wa matar shi ayyukan gida ina fatan ba sai na k'arasa miki maganar ba kinsan komai tunda ke kika shirya hakan"


Da sauri Mumy ta dafa bango don ganin yanda take kok'arin fad'uwa kallon Sabeer da Daddy take tamkar wasu sababbin hallita agabanta yanda suka rikid'e mata kamar wasu zakuna, can kuma ta aro jarumta ita ma afusace tace

"Nayi nayi d'in! Duk abin da kuka fad'a na aikata su saboda bana son yarinyar da Sabeer i hate her bazan iya had'a zuri'a da shegiyar matsiyaciyar yariny..... "

"Stop it Mumy! Kada ki k'ara aibata min mata ta, nagodewa Allah da ban sake ta ba!"

Sabeer ya fad'a cikin hargowa, kallon shi Mumy kawai take cikin mamaki yau Sabeer ne yake mata tsawa.

"Son ni kake yiwa tsawa akan waccan 'yar iskar yarinyar "

Kuka ya fashe dashi kan yace
"Daddy! Daddy ka fad'awa Mumy ta daina danganta Suhaima da wad'annan kalaman"

Hugging nashi Daddy yayi yana bubbuga bayan

Please Login or Register in order to submit comment