Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana addu'ar ba fah Baby? "

"Kamar yah fah"
"Ki gane mana kamar kice Allah ya barmu tare Allah ya bamu yara masu kamar ku "
Murmishi kawai tayi ta kasa magana daga k'arshe dai tattarawa suka yi suka nufi gida don dare ya fara yi, haka suka rabu cikin tsananin begen junan su.

Washe gari wajen 10 na safe Sabeer yayi sallama da kowa ya fito Yah Aliyu ya d'auke shi a machine don fitar dashi titi, gaba d'aya kayan da yazo dasu ya bawa Ashiru su iyakar jakar laptop d'in shi sai phone nashi d'ayar kawai.

Sun d'an jima a tsaye a titi kafin dakyar su samu taxi wanda zata kai Sabeer gida, shiga cikin motar yayi yayin da Yah Aliyu yaja driven taxi d'in gefe ya bashi kud'in motar Sabeer shi kadai zai dauka har gida ba tare da Sabeer ya sani ba, sai da Aliyu yaga tafiyar Sabeer tukunna ya koma gida zuciyar shi fal kewar Sabeer don su saba da junan su.......



_Na gaishe ku masoya na ina jin dad'in yanda kuke bibbiyar labarin nan nawa_❣

_bazan mance karamcin ki ba my Momma nah (Aunty maijiddah musa), Ni Aishat ina matuk'ar kaunar ki kirkin na daban ne wallahi, Allah ya bar mu tare ya raya zuri'a, Amin ya rabbi_. ❤


Aishat A Muh'd ✍🏻
[3/8, 9:09 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*


Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz




*PAGE 67-68*




Wata sassanyar ajiyar zuciya Sabeer ya sauke a lokacin da driven taxi yayi parking a k'ofar get d'in D'AN FILLO FAMILY kallon gidan yake tamkar yau ya fara sanin shi, fitowa yayi daga cikin motar tare da rataya jakar laptop d'in shi a kafad'a sannan ya kalli d'an taxi yace
"Malam nawa ne kud'in ka? "
D'an taxi murmishi yayi kafin yace
"Yalla6ai ai wanda ya rako ka d'in nan ya biya ni kud'ina "
D'an zaro ido kad'an Sabeer yayi tare da cewa
"Da gaske ne maganar ka"
"Kwarai kuwa ya bani"
Cikim tabbatar wa driven taxi d'in ya fad'a, gid'a kai Sabeer yayi cikin zuciyar shi kuwa wani son Suhaima da Yayan ta ne ya Kara ji sun shiga zuciyar shi gaskiya Aliyu yana karamci, amman duk da haka sai da Sabeer ya k'arasa d'an taxi d'in kud'i.

Nan yayi ta godiya tamkar bakin shi ya tsinke saboda godiya yasan yau koda gida ya koma zai samu abin ciyar da iyalan shi na kwana biyu daga k'arshe yaja motar yayi gaba.

Knocking d'in k'ofar gate yayi nan gateman ya bud'e, duk da ramar da bak'in da Sabeer yayi hakan bai hana shi gane d'an lelen family d'in D'an fillo ba ne ya dawo, washe baki yayi tare da bud'e k'ofar yana yiwa Sabeer sannu da zuwa, da D'an murmishi akan face nashi ya amsa mishi kafin ya wuce zuwa part d'in su.

Yana shiga part d'in ya tarar Mumy bata nan haka ma Daddy don haka kawai ya wuce bedroom nashi, bude shi yayi ya tarar da ko'ina tsaf sai kamshin air freshener yake tamkar yana gidan, sai duhun da d'akin ya d'an yi sannan yayi zafi don haka k'arasa wa yayi ya kunna ac da fanka tare da kunna light d'in d'akin, ajiye jakar yayi saman sofa sannan ya hau cire kayan jikin shi.

Yana gama cirewa toilet ya fad'a ya jima yana wanke jikin shi sosai a bathroom sannan ya d'aura alwala ya fito, lotion ya shafa tare da sanya white 3quater and T-shirt red colour mara hannu yayi kyau don kayan sun amshe shi, perfumes ya fesa different colours bayan ya taje kwantaccen gashin kanshi ya shafe shi da mayukan gyaran gashi tamkar wata mace.

Bayan ya kammala gyara jikin shi tukunna ya shimfid'a abin sallah, nan ya gabatar da sallahr la'asar bayan ya idar ne yayi en addu'o'in shi sannan ya fito zuwa parlor.

Tun daga kan steps d'in stairs ya hango Mumy zaune a saman dining table tana cin abinci, d'an girgiza kai yayi don ganin yanda Mumyn shi ta d'an rame alamar akwai abin da yake damunta cikin zuciyar ta, cikin tafiyar sand'a ya zagaya ta bayan ta ya sanya hannun shi dukka biyun ya rufe mata idonta yana murmishi.

Mumy na cikin cin abinci taji an rufe mata ido da farko ta tsorata amman da taji wani kamshin turaren tilon d'anta sai ta d'an nutsu don fuskantar wane, don tasan dai Sabeer baya gidan sai dai ko Daddyn shine yake son zolayar ta sai ta sanya hannun ta saman hannun wanda ya rufe mata idon tana kok'arin zame hannun shi, amman ta kasa zame hannun sai kok'arin cirewa take but Sabeer yak'i bud'e idonta yana yin wata dariya k'asa k'asa.

Cikin mak'e murya Sabeer yace "canki ko wane sai na bud'e miki ido "

Jin muryar Sabeer tayi ta rikid'e mata kamar muryar Daddy don haka tace
"My dear bud'e min ido please na ganka daman yau throughout ban ganka ba "

A hankali Sabeer ya zame hannun shi a eye's nata ya jingina bayan shi da jikin bango yana sakin murmishi, juyawa Mumy tayi da nufin ganin Daddy sai eye's nata suka hango mata tilon d'anta, tsabar mamaki ne ya hanata gasgata abin da ta gani sai da ta mutsutstsuke idonta sannan tace
"Sabeer! "
Da mamaki da kuma rud'ewa da ganin shi ta sake ambatar sunan shi kafin wasu hawaye su fara zubowa daga idanun ta kallon shi take tamkar yau ta fara ganin shi.

Shima wasu hawayen tausayin Mumyn tashi ne suka zubo mishi cikin sassarfa ya k'arasa ya tsugunna agabanta ya dire gwiwar shi a k'asa sannan ya d'ora kanshi saman cinyar ta, hannun ta take saman lallausan gashin kanshi tana shafawa ta kasa magana ma gaba d'aya.

Muryar shi na rawa hawaye na zuba yace
"Mumy baki yi murnar ganina ba koh, saboda ba'a son ranki na tafi ba, kina fushi da ni ne?"
Girgiza kai take yi lokacin da yake magana, cikin sanyin murya tace
"Bazan iya fushi da kai ba Son"
"To gashi kin sanya damuwa a ranki kin rame ba"
D'an murmishi tayi kafin tace "tunanin halin da d'ana yake ciki ne ya sanya ni ramewa da shiga tashin hankali,amman yanzu tun da nagan shi a gabana zan kwantar da hankali na "

"Mumy kenan, nayi kewar ku ke da Daddy wai yana ina ne? "

"I missed U too Son, Daddyn ka yana office bai dawo ba, yaushe ka dawo, zo kaci abinci "

Duk ta rud'e da ganin tilon d'an nata sai faman tambaya take watsa mishi akan lafiyar shi don ta d'an razana da ramar shi da ta gani da duhun da D'an yi, hannun ta ya kamo yana kallon ta kafin yace
"Mumy ki nutsu ni ina cikin lafiya sosai "
"Okay zo kaci abinci, me zan zuba maka? "

D'an shiru yayi kafin yace "ki ban duk abin da kika ci"
Cikin farinciki tace "okay Son taso ka zauna "
Haka ta kamo hannun shi ta zaunar dashi kusa da ita, kafin ta mik'e tsaye ta fara zuba mishi abincin, da kanta take bashi tana faman kallon shi tamkar wata sabon halitta a gabanta, ita kanta tasan tayi kewar d'an nata da yawa duk saboda matsiyar yarinyar nan d'anta yayi mata nisa.

"Mumy tunanin me kike ne ba gashi na dawo ba"
Da murmushi kan face nata tace
"Son kawai ina tunanin irin wacce wahalar kayi a k'auyen da ko wutar nepa babu "

"Haba Mum aikuwa suna da wuta sai dai ba'a fiye samu sosai ba"
D'an ta6e bakin ta tayi sannan tace "kuma kana iyacin abincin su naga duk ka rame kayi bak'i "
"Mum kibar wad'annan tambayoyin please "
"Shikenan Son na bari "

Tana gama bashi abincin suka koma parlor tana rik'e da hannun shi gane take tamkar zai sake guduwa ya barta, basu dad'e da zama ba Daddy ya dawo agajiye sosai yake, amman had'a ido da Sabeer yasa shi neman gajiyar tashi ya rasa nan suka yi hugging d'in junan su cikin tsananin k'aunar junan su.

Nan babu dad'e wa Family d'in D'an fillo dashi kanshi Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka samu labarin dawowar Sabeer, nan suka dunga shigowa ganin Sabeer kusan dukkanin su sunyi farincikin ganin shi, musammam Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah don rungume shi sukayi tamkar zasu mayar dashi cikin jikin su saboda tsabar son da suke mishi.

Jiddah wadda agidan ta wuni ta d'ago kanta suka had'a ido da Sabeer wanda yake ta zuba musu shagwa6a su kuma sun shashance da lalla6a shi, dariya take son fashewa da ita amman ganin hararar ta da yake yi ne ya sanya ta kunshe dariyar ta, daga k'arshe sai ta faki idon shi tana mishi video don ta nunawa Suhaima ta shirya zama da shagwa6a66en miji.....



Aishat A Muh'd ✍🏻
[3/14, 5:17 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*


Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz





*PAGE 69-70*





Tun bayan tafiyar Sabeer gida Suhaima ta shiga tsananin kewar shi ranar cikin kewar shi take duk ta sanyawa kanta damuwa ko abincin kirki ta kasa ci sai tunanin Sabeer, sam ta mance bata kunna wayar da ya bata ba duk a tunanin ta a kunne take.

Sabeer kuwa duk ya shiga tashin hankali da ya kirawo ta yaji wayar a kashe yana son sanar da ita ya sauka lafiya sannan ya fad'a mata yanda yayi kewarta na tsawon yini guda, daga k'arshe dai sai kiran Yayah Aliyu yayi bayan sun gaisa yake fad'a mishi ya sanarwa da Suhaima ta kunna phone nata zai kirata tukunna suka yi sallama.


Tana kwance still har yanzu har bacci ya fara fisgarta sai taji sallamar Yah Aliyu ya shigo d'akin, kallon ta yayi cikin kulawa kafin yace
"K'anwata me yake damun ki duk kinyi wani iri yau kodai duk tafiyar Sabeer d'in ne ya sanya ki zama haka"
Ya k'arasa maganar cikin zolaya, da sauri Suhaima ta rufe fuskar ta da hannayen tana 'yar dariyar jin kunya tace
"Kaiiii Yaya! "
"Eh mana gaskiya ce ina kula da ke fah ko abincin kirki baki ci ba sannan baki zo munyi hira ba "

Kasa magana tayi don batasan da me zata kare kanta ba don kuwa maganar shi haka take, ganin haka yasa shi mik'e wa tsaye yana murmishi yace

"Sabeer yace ki kunna wayar ki zai kirawo ki sai da safe "
Yana gama fad'in haka ya fita, d'an waro ido tayi kad'an tare da cewa
"Daman wayar a kashe take oops! "
Bata tsaya 6ata lokaci ba ta janyo wayar ta kunna ta sannan ta zuba mata ido tana sauraren kiran Sabeer.


Ko mintuna goma cikakku batayi da kunna phone d'in ba taji ta d'auki ringing, d'auka tayi ba tare da duba screen d'in ba saboda sauri da zak'uwan son jin voice d'in Sabeer.


"Hello Baby nah ".
Lumshe idonta tayi saboda jin saukar daddad'ar muryar Sabeer cikin kunnen ta har ta shagala ma sai da ta sake jin muryar shi yana mata magana sannan ta sauke ajiyar zuciya ta amsa mishi tare da gaida shi.

Bayan ya amsa ne suka d'an ta6a hira ta tsayin wajen mintuna 30 sannan suka yi sallama da junan su don ganin dare ya fara yi, kowannen su cikin kewar d'an uwanshi suke.


Bayan dawowar Sabeer da kwanaki uku ne ya buk'aci da iyayen shi su je neman mishi auren Suhaima, nan take Daddy ya aminta da hakan don haka ya had'a kan 'yan uwan shi maza suka had'u zuwa part din mahaifin su suka sanar mishi don ya tsayar musu da ranar tafiya neman auren Suhaima.

Sam Alhj Ahmad d'an fillo ba'a son ranshi yayi magana ba don kana kallon fuskar shi zaka karanci hakan, don farincikin Sabeer kawai ya aminta da auren nan amman sam baya so Suhaima, nan ya yanke lokaci zuwa nan da sati biyu su Daddy zasu je, aikuwa Sabeer najin haka ya tubure bazai yadda ba don sati biyu sunyi mishi nesa shi fah da ason ranshi ne aranar a d'aura auren Babyn shi ta tare a gidan shi, ganin yanda ya tada rigima ne ya sanya shi tambayar shi yaushe yake son aje.

Bud'ar bakin Sabeer yace shi gobe yake son aje kuma a tsayar da lokacin biki nan da sati uku, don fah shi har ga Allah satin ukun ya fad'a ne kawai amman sunyi mishi nisa, yanda ya buk'ata haka Alhj Ahmad d'an fillo ya amince ba don yaso ba sai don baya k'aunar 6acin ran d'an lelen shi, don haka ya kirawo 'ya'yanshi ya shaida musu gobe kowa ya tashi cikin shirin tafiya don zuwa neman wa Sabeer aure nan take suka amince da hakan.


Sabeer ba k'aramin farinciki yayi ba da jin sun amince da abin da yake so, da dare Daddy yake sanarwa da Mummy yanda suka tsara shi da 'yan uwan shi ko uffan Mumy bata ce ba k'arshe sai juya mishi baya tayi ranta a k'untace batason Suhaima bazata ta6a son yarinyar da ta fito daga k'auye ba kuma 'yar talakawa ta had'a zuri'a da ita dole ta sami mafita ta tarwatsa auren kafin lokaci ya k'ure mata.


*** *** ***


Duk wasu shirye shirye sun kammala shi na saukar bak'in su, anyi musu lafiyayyen girki sannan Yah Aliyu ya siyo musu drinks na kwali da faro, d'akin da Sabeer ya zauna nan suka tsaftace shi aka sanya mishi turaren wuta aka shimfid'a tabarmi don nan zasu sauki bak'in su.

Bayan Suhaima ta k'arasa gyaran gidan taje tayi wanka ta shirya cikin wani maroon less d'inkin riga da skirt sunyi mata kyau sannan ta zuba hijab agurguje ta fice daga gidan don tana kunyar su zo su sameta, ban da wani irin nishad'i da take ji a cikin zuciyar na daban a yau d'in nan gashi tana son ganin kyakkyawar fuskar Sabeer.

Tana shiga gidan Babaa Lantana da sallama a bakin ta suna had'a ido da Babaa Lantana ta sanya dariya tare da cewa
"Oh amarya Suhaima ai na d'auka bazaki bar gidan ma zama zaki yi da na ji ki shiru "

Akunyace tayi 'yar dariya tare da zama a gefen ta tana cewa
"Haba Babaa kinsan bazan iya zama ina jin kunya ne "

"Ai na d'auka ku 'yan zamani babu wannan kunyar a wajen ku ashe da akwai masu ita "

"Uhmmm"
Kawai Suhaima tace kafin ta d'ora da cewa
"Ni daga zuwa kin isheni da surutu ko ruwa baki ban balle ki kawo min abin dad'in da Baba ya kawo miki "

"Lallai gidan bakon ki ne ko yau kika ta6a zuwa ai kinsan hanyar wajen ajiye ruwan"

"Tabbb d'an tsohon nan naki yana kok'ari nasan shima idan ya dawo gida ko ruwan sha bakya kawo mishi "

'Yar hararar wasa Babaa Lantana tayi wa Suhaima kafim tace
"Ku yanzu mai kuka iyama a yiwa miji hidima, wata ma miji ya dawo daga aiki ko sannu da zuwa babu balle aje batun kawo mishi ruwa mai sanyi ya jik'a mak'ogaran shi, wata ma ko kallon inda yake baza tayi ba balle yasa ran ayi mishi magana duk wata kulawar miji da hidimar shi ba'a fiye sauke mishi ba sai afkin kwalliya kamar ta aljanu da kyalakyalen da basu zu amfane su ba, wata ma ba don mijin nata zata yi kwalliya ba sai don zata fita anguwa gasu nan da yawa muna gani kuma muna jin labari, idan kika ga wata awaje ma fes da ita idan kika je gidan watak'il ko ruwan gidan baza ki iya sha ba sannan....."

"Kaiii Babaa Lantana daga tsokana zaki d'auko dogon sharhi haka kamar wata ma'aikaciyar gidan redio sai zuba kike "
Cewar Suhaima kenan bayan ta katse Babaa Lantana daga maganar da take.

D'an hararar ta tayi kafin tace
"Yo ai gaskiya nake fad'a da kin barni na cigaba sai ki d'auki abubuwa masu amfani ke da zaki tafi birni ga mijin ki kyakkyawa kamar balarabe don nasan baza ya rasa mata masu rububin son shi ba, don yanzu mun zo wani irin zamani da sam wasu matan basu da alkunya sai kaga mace har mace amman ta zubar da k'imar ta tana furta wa namiji so babu kunya wannan abin yana ban takaici "

"Allah ya kyauta "
Abin da Suhaima tace kenan tana jin wani abu yana mata tuk'uk'i cikin zuciyar ta da taji Babaa Lantana tace yanzu haka da akwai wasu matan da suke son Sabeer wad'anda suka fita kyau, wayewa da ilimi na boko tunda ita iyakar ta secondary kawai.


"Yanzu me kika shirya mishi wanda zai ci idan yazo? "
D'an yatsina fuska Suhaima tayi tare da cewa
"Tabbb ni ban wani shirya mishi komai ba sai abubuwan da aka tanadarwa bak'in"

Kama baki Babaa Lantana tayi sannan tace
"Allah ya shirye ki Suhaima yanzu baki d'an yi mishi abu na musamman ba shi d'aya haka ake tar6ar saurayin"

Cikin yanayin shagwa6a tace
"Toh ni me zanyi mishi kawai yaci wannan na gaji tun safe nake aiki wallahi "

"Ke tafi can tsaya sanyin jiki na kwace miki shi "
Dariya Suhaima tayi kawai nan Babaa Lantana ta tashi ta fara kiciniyar aiki.

"Babaa me zaki yi ne haka? "
D'an hararar ta tayi kafin tace
"Tsaya ki gani yarinya kiga yanda ake tar6ar bak'o "
D'an ta6e baki Suhaima tayi tare da kwanciya tana ganin yanda Babaa Lantana take zirga zirga k'arshe ma fita tayi daga gidan, tayi mintuna goma da fita sai ga ta da kaji biyu yankakku ta cigaba da aikinta bata k'ara bi takan Suhaima ba.


Phone nata ta d'auka ta bud'e data da yake tayi downloading what's app da Instagram sai fb da yake taga yanda Jiddah take charting shi yasa batasha wahala wajen iyawa ba, message's ne suka fara shigowa duk da iya Jiddah da Sabeer ne kawai take what's app dasu sai wani group na kitchen da na novels sai na make up wanda Jiddah ta sanya ta.

Kan number d'in Jiddah ta shiga nan taga ta turo wani video tare a tsokanar ta amarya, bud'e videon tayi bayan ya gama bud'e wa sai ta fara kallo tun tana murmishi har ya sanya ta fara tuntsira dariya ganin irin shagwa6ar da Sabeer yake yiwa su Daddy sai kace wani d'an yayen yaro k'arami dariya tayi sosai har da hawaye, Babaa Lantana kuwa sakin baki tayi tana kallonta kafin kuma ta girgiza kanta tana cewa
"Allah ya shirya "
Ta wuce ta cigaba da aikinta.


Bayan ta gama dariyar ta fad'a dogon tunani daman haka Sabeer yake duk da tasan daga yanayin shi zai yi shagwa6a bata zaci shagwa6ar zata yi haka wani murmishi kawai take saki wanda ita kadai tasan ma'anar shi.


Wajen misalin karfe 2 na rana su Daddy suka k'araso tare da jagorantar Sabeer don yana son ganin Babyn shi, suna k'araso wa sun samu kyakkyawar tar6a daga wajen Yaya Aliyu, Baba Adamu da kuma wasu amintattun dattijai biyu abokanan Baba Adamu kuma mak'obtan su, su Daddy sunyi mamakin ganin irin wajen da Sabeer yaje neman aure duk da haka kuma k'auyen ya basu sha'awa gashi sun ji dad'in tar6ar karamcin da aka yi musu.

Bayan sun yi sallahr azahar ne don a hanya ta riske su, sai aka yi zaman gaisawa kafin kuma a fara cin abinci, a d'an kyamace suka fara kai abincin bakin su amman da suka ji irin dad'in d'and'anon shi tuni suka zage suka fara ci.

Ganin sun fara cin abincin ce yasa Sabeer zamewa zuwa cikin gidan suka gaisa da Aunty Aliyah sannan ta fad'a mishi a inda Suhaima take wani murmishi ya saki kafin ya fita kuma.


"Wannan 'yar tsohuwar me kike girkawa ne duk kin cika min hanci da k'amshi yawu na sai tsinke wa yake "
Cewar Suhaima tana shiga madafin Babaa Lantana wadda ke zaune akan kujera 'yar tsugunno tana faman yin aiki.

"Tafi can ki ban wuri kina kallo ina faman aiki ko kizo ki taya ni da yake ci ne ai gashi kin taho, toh ko d'and'ane bazan baki ba na megidan nawa ne "

Dariya Suhaima tayi tare da cewa
"Yanzu duk wannan kamshin da nake shak'a ace baza'a sammin ba haba 'yar tsohuwa ta kaina "

"Yarinya duk dad'in bakin ki bazan bayar ba ki bari idan yaci ya rage kyaci sauran "

D'an turo baki tayi cikin sigar shagwa6a tace
"Nayi ma fushi bazan ci ba "
"Da naji dad'i kuwa "
Cewar Babaa Lantana tana tattare kayayyakin zuwa cikin kitchen, nan ta shirya farfesun kaza da tayi mishi guda d'aya sai gashashshiya kaza d'aya tasha kayan had'i da mai sai shek'i da tashin k'amshi take, sannan ta dama mishi fura da ruwan randa mai sanyi ta zuba ta a dogon kofin silver, sauran kayan ma a cikin kwanan silver ta zuba sai ta d'ora saman farantin silver, bayan ta gama had'a su ne ta fito daga d'akin girkin tana cewa
"Gashi nan na gama shirya komai sauran ya zo ki kasa kawo mishi don nasan an fad'a mishi kina nan zuwa kowanne lokaci zaki iya ganin shi ".
Suhaima na dariya tace
"Toh naji 'yar tsohuwa sannun ki da aiki don nasan yau kika kwanta sai kin kasa motsi saboda gajiya "

Da harara ta bita kafin tace
"An gaya miki jikina irin naki ne koda zan yini aiki ras zaki ganni, Allah Suhaima ki rik'e yaron nan sosai saboda yana son ki wallahi na tsakani da Allah "

Tana gama fad'in haka ko rufe baki bata yi ba suka jiyo sallamar Sabeer aikuwa da gudu Suhaima ta fad'a d'akin Babaa Lantana, sosai abin ya bawa Babaa
Lantana dariya.

Kallonta Sabeer yayi had'e da cewa
"Matar ke dawa kike dariya haka? ".
Cikin dariya tace
"Ni da wannan matar da kake kok'arin jajibowa ne daga jin sallamar ka ta kwasa da gudu sai kace wadda taga wani abin firgitarwa ".

Murmishi ya saki tare da cewa
"Babyn tawa ce kunya ce da ita Babaa, amman gashi ai kin hutashshe ta sai ki min sannu da zuwa "

Washe hakora Babaa Lantana tayi tana cewa
"Eh mana rabu da ita ni na kwace ka ai tun da babu abin da ta fini "
Sosai maganar ta bawa Sabeer dariya, Suhaima na jin su a d'aki tana mirmishi ita kadai.

"Ai sai ki fita ki kai mishi tabarma kyayi murmishin da dalili ba ki k'ule d'aki kina murmusawa ba ke d'aya "

"Kaiii Babaa "
"Ni dai ki tafi maza kin bar mutum a tsaye "
Babaa Lantana ta fad'a tana mik'awa Suhaima sabuwar tabarma, kar6a tayi sannan ta fito daman Allah ya taimake ta da hijab d'in ta a jikinta.


Fitowa tayi daga d'akin tana d'aga kai suka had'a ido da Sabeer sai kawai ta zuba mishi don yayi mata kyau sosai duk d'an bak'in nan da yayi da rama ya washe tsaf dashi, yana sanye cikin wani black jeans and T-shirt black mai kwala sai kuma ya d'ora wata yellown T-shirt mai dogon hannu daga sama, takalmin shi baki haka ma belt d'in shi sai agogon hannun shi k'irar Gucci shima bak'i, gashin kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake gwanin sha'awa, shagala da kallon shi Suhaima tayi haka shima kallon ta yake don tayi mishi kyau ba kad'an ba.

"Idan kun gama kallon junan naku sai ka zauna ni na wuce d'aki zanyi bacci ".

Firgigit suka dawo hayyacin su tamkar wad'anda suka tashi daga bacci, saboda jin muryar Babaa Lantana da suka yi a kusa dasu duk kunya ce ta kama su ba irin Suhaima da take ji tamkar ta nutse a k'asa, wayance wa tayi da shimfid'a tabarmar yayi da Sabeer yake sosa kai, murmishi Babaa Lantana tayi ta wuce d'aki ta bar su.


Bayan ta gama shimfid'a tabarmar ne cikin sanyin murya tace
"Ka zauna mana "

Zama yayi yana cewa
"Baby ki k'ara kyau mene sirrin "
Kunya taji ta sake tuk'unk'une wa cikin hijab, sai kawai ta fara gaida shi amsawa yayi cikin murmishi.

Suna gama gaisawa ta tashi ta d'auko mishi abubuwan da Babaa Lantana ta had'a ta ajiye mishi tare da da ruwa

Please Login or Register in order to submit comment