Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana daukan Suhaima lokacin da take dariya, ita kanta Jiddah pic d'in yayi matuk'ar birgeta ba kad'an ba.

D'an waro ido waje tayi kafin tace
"Haba Jiddah kada ki tura mishi please "
Ta fad'i tana langa6e kai cike da shagwa6a, dariya Jiddah tayi kan tace
"Toh naji dake da mijin ki bansan wanda yafi wani shagwa6a ba gidan ku da kallo kuwa duk an tara shagwa6a66u"

"Yanzu dai tafiya zanyi don my dear yana hanya shi da driven da ya kawo ni, yace ya gaji da yi mishi mitar da nake yak'i zuwa su gaisa da Bestyna shine yau yace zai zo "

Murmishi Suhaima tayi kan tace
"Allah ya kawo su lafiya"

"Amin "
Fita Jiddah tayi bata dad'e ba sai gata da Aunty Aliya wadda ta saki baki tana kallon yanda Suhaima ta koma tamkar ba ita ba.

Hannu tasa tana shafa hannun Suhaima tace
"Wannan da fita kika yi da ita Jiddah da nace wankan inji kika yi mata "
Dariya suka yi dukkanin su jin abin da Aunty Aliya ta fad'i.

"Aunty kema kiyi don Allah "
Cewar Jiddah, rik'e baki tayi tana cewa
"A haba wannan ai na irin kune "

"Kaiii Aunty aikuwa ya kamata kiyi "
Cewar Suhaima.

"Suhaima ki had'a mata tayi itama kafin Yah Aliyu ya dawo yaga yanda zata canja idan na dawo zan kar6i tukwicin kyauta ta "

Suna nan zaune suna hira har mijin Jiddah yazo, shigowa har gidan yayi suka gaisa da Aunty Aliya da Suhaima bayan an ta6a hira ne suka yi musu sallama suka tafi har k'ofar gida Suhaima ta rako su sannan ta dawo gida bayan sun tafi.


Bayan Suhaima ta dawo gida ne ta had'a wa Aunty Aliya itama tayi kamar yanda Jiddah tayi mata, sosai tayi kyau ba laifi bayan angama ne Suhaima tayi wa Aunty Aliya simple make-up tayi kyau kamar ba ita ba sai da Suhaima ta d'auke ta a pic's.

Suna zaune tsakar gida suna hira sai ga Yah Aliyu ya dawo nan sauran sallamar mak'alewa tayi a fatar bakin shi ganin yanda matar shi ta koma kamar ba ita ba, kallon ta kawai yake yi don ya mance da wata Suhaima dake zuba mishi sannu da zuwa, duk kunya ta d'an kama Aliyah ganin kallon da yake mata.

Yayin da Suhaima ta tattara ta arce d'akin ta don kada taga abin da yafi k'arfin idon ta, dariya k'asa k'asa take don kuwa Yah Aliyu ya bata dariya, phone nata ta d'auko data ta kunna sai gashi Jiddah ta turo mata pic's d'in da ta d'auke ta d'azu, zubawa pics d'in ido tayi ita kanta tasan tayi kyau.



*_11:30pm_*


Sabeer ne kwance kan bed yana zuba murmishi gama yin wayar shi kenan da Suhaima, duba wajen pic's nashi yayi sam bashi da pic's d'in Babyn shi yana shirin kiranta ne yaji alamar shigowar sak'o a WhatsApp d'in shi don haka ya duba sai yaga Jiddah ce ta turo mishi da wasu pic's guda 5 daga k'asa ta sanya "Yah Sabeer kada ka nunawa Besty na turo maka pic's d'in nan don inason kaga yanda Babyn ka ta zama kuma ka bani tukwici idan ba haka ba na daina turo maka " ta k'arasa da sanya d'an aljanin murgud'a baki, sannan ta kuma cewa
"Asha kallo lafiya angon Besty " ta sanya aljanin dariya da gwalo.

Tun kafin ya bud'e yake murmishin abin da Jiddah ta rubuta, sakin baki, hanci da ido Sabeer yayi yana ganin pic's d'in sai da ya sake murza eye's nashi kafin ya dad'a zubawa pics d'in ido, wannan anya Baby nace?, ya fad'i haka cikin zuciyar shi kafin maganar ta samu matsugunun tunani a brain nashi tuni ya gama hashasho Babyn shi ce.

"Wow! Gaskiya Baby nah kin had'u ashe zan more woo"
Ya fad'i hakan yana cigaba da kallon ta tuni ya tafi mafarkin ido biyu, baisan adadin lokacin da ya dauka yana kallon pics d'in ba, sai da yaji Jiddah ta turo mishi da text d'in taji shiru bata ga tukwicin ta ba.

Cikin rawar jiki ya fara typing da cewa
"Me kike so k'anwata ta kaina? "
"Yah Sabeer komai ma "
"Car or Money wanne kike so fad'i?"

"Yah Sabeer Mota nake sooo"
"Angama sister gobe za'a kawo miki key "

Wani ihun murna Jiddah ta saki har phone nata na fad'uwa k'asa don tasan kyautar Sabeer baya k'arama, nan tayi mishi godiya tare da addu'ar Allah ya bashi Suhaima, na takaice muku Sabeer ranar har dasu mafarkin Suhaima suna tare don da asuba sai da Sabeer yayi wanka sannan ya iya yin sallah..... lol.



*_Washe gari_*


Sabeer ne ya fito daga bedroom d'in shi yana taka staircase anutse ya kusan k'arasa wa palour ne ya hango Mummy da Daddy zaune ga kayan bag's na akwatinan lefe nan barbaje a palourn tun daga kan akwatunan mutum zaisan basu da wani tsada ko kalar kyau basu dashi gashi guda 6 ne gaba d'aya kayan ciki kuwa ko arzik'in kyau basu dashi.

K'arasa wa yayi cikin palourn yana kallon kayan a wulak'anci yace
"Daddy Mumy kayan wane ne wannan?"

"Nima jira nake ta sanar dashi bansan na wane ne ba nafi kyautata zaton ko gate man ne zaiyi aure ta bashi kyautar su "

Cewar Daddy kenan, duk sun zubawa Mumy ido suna sauraren abin da zata ce dasu.........



*_Ya kuka ji wannan page d'in Fans dafatan ya k'ayatar ku, inason ganin comment's, yau nayi abin kirki koh?_*😜



Aishat A Muh'd ✍🏻
[3/25, 8:09 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*



Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz





*PAGE 75-76*





Ganin Mumy tayi shiru tak'i magana yasa Sabeer yin magana cikin k'aguwa yace
"Mumy ke fah muke jira ki fad'a mana ki zo ki bani abinci yunwa nake ji "

Hankalin Mumy kwance ta bud'e baki tace
"Lefen da Daddy yace na had'a ne sune na gama had'a wa "

Cikin son sanin na waye Sabeer yace
"Na wane kodai gaskiyar Daddy ne gateman ne zai yi aure?"

Yayin da Daddy kuma ya saki baki yana kallon Mumy zuwa yanzu ya tabbatar lefen Sabeer ne da yace ta had'a shine ta had'a mishi wulak'antaccen kayan nan da ko wani talakan mai zuciyar nema idan ya sanya kanshi sai ya had'a wanda yafi shi had'uwa, ranshi ne ya soma 6aci yama kasa magana sai kallon mamaki da yake bin ta dashi,yana jiran yaji me Sabeer zaice kafin shima ya d'ora hukuncin da zaiyi don sosai wannan karon Mumy ta 6ata mishi rai, yana cikin wannan tunanin ne yaji muryar ta tana cewa Sabeer.
"Lefen auren ka ne da wannan talakar yarinyar 'yar k'auye don nasan sun fi dacewa da ita kuma zata kar6a su cikin murna don basu saba ganin irin su ba"

Wata 'yar dariyar ban yarda ba Sabeer yayi kan yace
" are you serious Mumy maganar ki nasan da wasa ne ai? "

"Sabeer kadaina sanya wasa cikin maganar nan da gaske nake duk abin da nace "

Wata dariyar Sabeer yayi wadda tafi kuka ciwo yace
"Yayi kyau Mumy "

Ya fad'i hakan yana barin parlourn cikin 6acin rai da taiaicin abin da Mumy tayi na niyyar wulak'anta shi yake hawa staircase d'in da sassarfa, bedroom nashi ya nufa yana shiga ciki ya bud'e tafkeken wardrobe nashi ya fara watso kayan ciki yana barbaza su a ko'ina, shi Mumy take neman wulak'antawa saboda kawai yana son d'iyar talakawa wadda ta rayu a k'auye.

"Why Mumy why shi talakan ba mutum bane, ba Allah ne yayi shi ba yaso ganin shi haka a rayuwa ba, Mumy kada k'ureni muzo muna yin abin da kowa zai yi nadama "

Wani 'yar k'arar takaici ya saki yana sanya hannun shi cikin sumar kanshi wadda tasha gyara yana hargitsawa, can kuma kamar wanda aka mintsina ya mik'e zumbur ya fara cire kayan jikin shi ya canja da wasu jeans black da T-shirt maroon colour mai k'aramin hannu ya d'auko phone da car key's ya fito daga d'akin.


Yana saukowa daga upstairs yaji muryar Daddy yana yiwa Mumy fad'a sosai akan abin da ta aikata, suna ganin sai kuma suka dawo da hankalin su nan, cikin damuwa Mumy ta fara cewa

"Son ina zuwa baka ce min yunwa kake ji ba, ga breakfast fah na had'a maka favourite foods naka? "
"Bana buk'atar su "

Sabeer ya fadi hakan ba tare da ya kalli inda take ba ya k'arasa wajen Daddy yana cewa
"Daddy zan fita "
Rik'o hannun shi Daddy yayi tare da cewa
"Ina zaka Son? "
"Daddy zan je na nemi mai had'a min lefe wanda nasan baza su so na kunyata a rayuwata ba "

"Da kyau Son but da ka nemi Jiddah da Yusrah (Yayar Jiddah wadda take bi itama dai bata da tsaurarawa sosai akan abu wanda ya danganci talaka tana da aure har da yara 2), nasan zasu fitar da kai kunya baza su so kansu ba da yawa, kamar wasu mutanen da basu d'auki talaka a mutum mai mahimmanci ba, wanda kuma agaba zai iyayi mishi wani abin alkhairi mutum ya dawo yana jin kunyar aikata abin da yayi"

Mumy ta cika tayi fam sai huci take don tasan da ita yake don tuni ta tsargu.

Sai lokacin hankalin Sabeer ya d'an kwanta don dama shi baisan wurin da zai je ba kawai ya fito da niyyar barin gidan ko yaji sanyi cikin ranshi.

"Yanzu Daddy wanne k'asa zasu je? "
"Ina tunanin su je dubai su had'a acan idan ma bai wadatar ba sai a dad'a neman wata k'asan, yanzu zan kirawo mazajen su na rok'i wannan alfamar a wajen su, ka kwantar da hankalin ka Son "

Rungume shi Sabeer yayi cikin jin dad'i yace
"Nagode Daddy nah hak'ik'a kai uba ne na gari wanda yake faranta ran d'an shi koda yaushe Allah ya barmin kai "

"Amin Son nima ina alfahari da kai "

Yana gama fad'in haka yaja hannun Sabeer suka fita daga side d'in, suka bar Mumy da baki a sake tana mai bin su da kallo cikin mamakin gasa mata maganar da suka yi sannan suka fitar mata da waje ko sallama babu gashi ba wanda yayi breakfast a cikin su, kuma saboda su ta shiga kitchen ta tsara girki shine suka watsa mata k'asa a ido, zubewa tayi kan kujera tana faman kallon kayan da ta sanya house girl d'inta ta had'a su, da yake er aikin dattijuwa ce kuma er k'auye ce sosai sai tace ta had'a mata lefe kamar yanda suke had'awa a k'auyen su, amman irin wanda mai kud'in k'auye zai iya had'awa amman sai tace mata akwatina 6 zata siya shine fah ta had'o kayan, ko lokacin da ta gansu sai da taci dariya ta more saboda abubuwan da aka zuba aciki.


D'an ta6e baki tayi kan tace
"Ni ban ga wulak'anci anan ba nasan da gudu zasu kar6a suna murna tun da basu saba ganin kayan lefe masu yawa irin wannan ba"

Ta k'arasa fad'i tana kwanciya kan kujera wata tsanar Suhaima na k'ara shiga cikin zuciyar ta,tun kafin taga yarinya take jin tsanar ta kuma tabbas sai tayi nadamar auren d'anta don bazata barta tayi rayuwa cikin jin dad'i ba, (kun ji tunanin Mumy fah sai kace itace mai tsarawa mutum rayuwar shi).



Tun da Sabeer da Daddy suka bar gidan basu dawo ba sai wurin 11 na dare suka shigo part d'in, tun after sallahr ishsha suke cikin gidan ba tare da Mumy ta sani ba don ko dinner a Muh'd part d'in Hajjah suka yi, Mumy kuwa batasan sun dawo gidan ba don haka ta k'ule iyakar k'uluwa akan abin da Sabeer da Daddy suka yi mata don ko abincin dare da kanta ta shiga kitchen ta 6ata lokaci sosai wajen shirya musu abinci, tun tana zuba idanun ganin su har ta hak'ura ta kwanta kan kujera 3 siter tana sak'a da warwara ina mijin ta da d'anta suka yi.

Tana cikin wannan tunanin ne taji shigowar su palon don haka ta mik'e tana kallon su cikin mamaki yanda suke ta zuba fara'a abin su Daddy ya rik'o kafad'ar Sabeer tamkar wani abokin shi.

Kanta ne ya k'ara d'aurewa ganin zasu shige upstairs basu kulata ba, yanda ma suka nuna ko alamun sun san da ita a palon basu yi ba, kasa jurewa tayi don haka tace

"Hala baku kula da ni ba, ina kuka zauna har wajen 11pm baku dawo gida ba? "

Tsayawa suka yi tare da juyowa suka had'a ido lokaci d'aya suka had'e fuska sannan Daddy yace

"Ina ruwan ki da inda muka je wannan ba matsalar ki bace? "

Gaban Mumy ne ya fad'i kaddai ace adalilin Suhaima mijinta da d'anta su juya mata baya, ganin har sun fara taka staircase ya sanya ta katse tunanin ta da sauri tace

"Ga abinci nan fah na girka muku "

"Mun koshi Mumy wata k'awar Daddy ta bamu abinci mai dad'i mun ci don haka ki bawa masu aiki su ci "
Cewar Sabeer kenan wanda sauran kad'an dariya ta kubce musu shi da Daddy don haka da sauri suka fad'a bedroom na Sabeer suka rufe suna kyalkyala dariya, har da rufe baki da hannun su saboda kada Mumy ta jiyo sautin dariyar tasu.

"Son ka razana Mumyn ka da yawa fah kada wani abu ya samu mata ta ina jin tsoro "

"Haba Daddy daga wannan maganar sai wani abu ya faru da ita? "
"Eh mana Sabeer kasan yanda Mumyn ka take da kishi kuwa ni bama zan jure ganin ta cikin damuwa ba bari naje na rarrashi abata "

Daddy ya k'arasa fad'a yana kokarin fita a d'akin, da sauri Sabeer ya rik'o hannun shi tare da cewa
"Nooo Daddy kyale Mumyn nan, nima kaina bana son ganin ta cikin damuwa but Mum batason ganin farincikina i swear"

"Kada kace haka Son nasan nan gaba zata so Suhaima "

"Anya kuwa Daddy, na fahimci Mum ta gama tsanar Suhaima "

"Kada kace haka Son addu'a zaka cigaba da ni "

Gid'a kai Sabeer yayi kafin kuma su zauna suna hira akan tafiyar da su Jiddah da Yusrah zasu yi nan da gobe da yamma jirgin su zai tashi zuwa dubai, kafin daga bisani Daddy ya wuce side d'in shi don dare ya d'an yi.


Mumy kuwa tun lokacin da maganar Sabeer tayi mata dirar mikiya cikin kunnen ta, ta gama firgicewa kusan suman tsaye tayi tsabar kad'uwa da jin abin da Sabeer ya fad'a mata, wato dalilin da ya sanya su yin dare a waje kenan, aikuwa ba 'yar iskar da zata shigo gidan nan matsayin matar Hussein wallahi duk wadda tayi gigin shigowa kuwa sai tayi dana sani kuwa.

Tana gama fad'in haka haka ta wuce side d'in ta tana shiga bedroom saboda tsabar takaici ta rushe da kuka kamar wata k'aramar yarinya, Allah yayi ta mace mai tsananin kishin sosai ji take har numfashin ta yana kokarin d'aukewa tsabar tashin hankali.

Anutse Daddy ya shigo bedroom d'in jin kukanta ba k'aramin d'aga mishi da hankali yayi ba don shi yaushe rabon yaga kukan matar shi kamar haka har ya mance.


Cikin sanyin jiki ya k'arasa inda take ya zauna kafin ya dafa kafad'ar ta yace
"Yake matata kukan me kike haka? "

D'ago kanta tayi ta kalle shi idanunta suna zubar da hawaye ta fad'a jikin shi ta k'ank'ame shi tare da cewa
"Ina tsananin son ka Hussein ina kishin ka bana son wata mace ta ra6ar min kai but why da zaka yi min haka kaje wajen wata kai da Son har kuci abincin ta? "

Murmishi Daddy yayi kafin yace
"Haba Faridah kinsan bazan iya kallon wata d'iya mace da sunan ina sonta ba, banyi hakan tun k'uruciya ta ba sai yanzu da na girma kinsan ke kadaice cikin zuciyata daga ke babu dad'i, duk wannan maganar tsokanar ki Sabeer keyi"

Kallon idanun shi take don son tabbatar da gaskiyar maganar shi, gid'a mata kai yayi tare da lumshe eye's nashi alamun haka maganar take.

"Toh ina kuka je da Son har kukayi dare? ".

Fuskar shi d'auke da murmishi yace
"Muna part d'in Hajjah ana hira "

Rungume Daddy tayi tana sauke ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji ta a nutse nan kuma suka 6ige da nunawa juna kauna.


Washe gari da yammacin ranar Jiddah da Yusrah suka d'aga zuwa dubai don siyayyar kayan lefe, sosai Daddy da Sabeer suka saki kud'i don a had'o kaya masu kyau da tsada.


**** **** ****


Satin su Jiddah 2 suka dawo Nigeria da tarin had'add'un kayan lefen da suka had'a, kaya sunyi ta ko'ina sosai kayan Daddy da Sabeer suka yaba za6en su ko Mumy sai da ta jinjina irin dukiyar da aka narka anan ko ita kayan sun birgeta duk hassadar mutum yaga kayan sai sun birgeshi, har da tukwici Daddy yayiwa Jiddah da Yusrah don sun mishi yanda yake so.

Har zuwa lokacin Sabeer tsakanin shi da Mumy gaisuwa sam yak'i sake mata kamar da, don ba k'aramin 6ata mishi rai tayi ba akan lefen da ta had'a wai za'a kaiwa Babyn shi idan ya tuna hakan har ranshi 6aci yake.


Duk wannan kayan da aka had'o sai da Jiddah ta kar6i kud'i na musamman hannun Sabeer ta siyawa Suhaima kayan da zata yi amfani dasu wajen biki komai sai da ta had'o yanda ya kamata.

Bayan kwana 2 duk 'yan uwa sun gama ganin lefen sai zuzutashi suke saboda had'uwar shi but idan suka tuna 'yar kauye za'a kaiwa wannan duk sai ransu ya 6aci su fara jan tsaki da k'ananun maganganu, babu mai goyon bayan Sabeer akan wannan bikin sai Daddy don ko Dr Ahmad d'an fillo kadaran kadahan don farincikin Sabeer ya hak'ura.

Shiyasa Sabeer da Daddy ne kawai suke kid'an su da rawar su, duk wadannan tarin kayan da aka had'a sai da Daddy ya k'ara da wata dank'areriyar sark'ar gold mai matuk'ar kyau da tsada ba kad'an ba da kuma key na mota, don Daddy tuni ya zubar da makaman yak'inshi na k'in talaka yanzu sosai yake tsayawa sauraren talakawa masu neman taimako yana taimaka musu kuma hakan ba k'aramin jin dad'i yake ba da kuwa daga iya fidda zakka shikenan.


Wannan abun da Daddy yayi wa Suhaima ba k'aramin bak'anta ran Mumy yayi ba don ita aganin ta taya zai tsaya siyawa 'yar k'auye wannan gold d'in mai tsada bayan wad'anda aka zuba mata a lefe gashi har da wani kyautar mota ko'ina 'yar k'auye da tukin mota me zatayi da ita, banzatar dasu zata yi tunda batasan darajar su ba, Daddy sai da ya toshe kunnen shi don kuwa Mumy da Hajjah sai mitar abin suke yi, shi kuwa ganin farincikin tilon d'an shi yafi mishi komai.


Ko ranar da za'a kai lefe motoci 3 Daddy yace za'a yi na mutane saboda bayason a had'a su da wahala kuma bayason ayi hatsaniya don sosai sai da ya gargad'i wad'anda zasu kai wanda suka kasance daga kanwar su Daddy sai k'annen matanshi da yaran su mata kad'an daga ciki, sai kuma motar Suhaima wanda aka zuba kayan lefen ta a ciki nan suka d'auki hanyar k'auyen su Suhaima.



Sai wurin 3 na yamma suka k'arasa kowanne ya fito daga mota sai faman yatsina fuska da ta6e baki suke suna yiwa mutane kallon d'ai d'ai, koda suka shiga gidan su Suhaima sunsha mamakin ganin yanda gidan yake don kuwa Yah Aliyu ya kashe kud'i sosai wajen gyara gidan har da sabon fenti akayi, shi yasa ko'ina yayi kyau yayi fes ga an tsabtace gidan sai k'amshin turaren wuta yake.


Anan tsakar gidan suka zazzauna saman tabarma, su Aunty Aliya da Babaa Lantana da wasu daga cikin 'yan uwan su Suhaima sun d'an zazzo kar6ar lefen, wasu kuma don ganin kwakwaf suka zo don sunji ance d'an mai kud'i Suhaima zata aura suna son tabbatar wa aikuwa da ganin irin motocin da suka zo acikin ta sun tabbatar da gaskiyar zancen.


Babu wanda yayi gigin shiga toilet sai alwala da suka yi suna tsoron kada su shiga su ga abin da zai sanya su amai, dai dai da ruwan alwala da bottle na faro suka dunga yi saboda tsantsanin ruwan suke.

Jiddah ranta ya 6aci sosai da wannan wulak'ancin da 'yan uwanta suka yi don an zuba musu ruwa a botoci suka k'i amfani dashi suka d'auko bottles na faro, kasa magana tayi don tsabar takaici, yayin da mutane suka saki baki da hanci suna kallon wannan sabon salon nasu, awurin sallahr ne kawai basu da yanda zasu yi suka yi akan tabarmar da aka shimfid'a musu bayan sun idar aka sake gaisawa sannan aka fara fito musu da abinci zuwa drink's da ruwa na bottles.

Sunyi mamakin na ganin irin abincin da suka gabatar musu dashi don basu yi zaton samun hakan ba, basu san wannan duk aikin Jiddah ba ne don kawa batason a 'yanuwanta su wulak'anta mata Suhaima.

Sun ci abincin bayan sun kammala aka gabatar da kayan lefen da car key sai kuma kud'in da ake d'ora wa saman kaya har 1 million, sakin baki, hanci sukayi 'yan kauye don ganin irin wannan abun da basu ta6a tsammanin zasu ganshi da ido ba nan kowa ya fara kokwanto cikin zuciyar shi anya ba siyar da Suhaima su Aliyu suka yi ba yo banda hakan ina za'a bayar da irin wannan kayan lefen haka har da mukullin mota da 1 million akai.

"Kada ku damu wannan ba wani babban abu bane a wurin mu don mun bayar da wadannan 'yan kayan don haka ku dai na mamaki, kodan nasan dole kuyi mamakin don ido bai ta6a ganin irin kayan ba "

Cewar Aunty Fadilah kanwar su Daddy tana wani yatsina fuska banda kallon raini da take bin su dashi, don 'yar gaban goshin Dr Faridah ce tana taya matat wan nata bak'in cikin wannan abu.

"Haba Aunty Fadilah don Allah ki daina irin wannan maganganun babu dad'i "
Cewar Jiddah tana turo baki wata uwar harara Aunty Fadilah ta aikawa Jiddah kafin tace
"Daman ina zaki ga rashin dacewar hakan bayan an shanye mana ke da Sabeer har da Yaya Hussein, idan ban da k'addara ina mu ina neman aure a irin wannan wurin "

Ta k'arasa maganar tana jan tsaki, cikin rashin kunya Jiddah tace
"Allah Aunty kika sake magana sai na gayawa Daddy tun da har kin mance abin da Daddy ya fad'a kafin mu taho "

Wata hararar ta sake zabga mata tamkar idanunta ya fad'o amman bata sake magana ba don tasan sarai halin Jiddah tsaf zata fad'awa Daddy kuma tasan tsaf zai ci mutuncin ta.



Sai bayan la'asar da suka yi sallah suka taho da tarin kayan snacks da drink's d'in da Jiddah ta bayar akayi, sai kuma cikin kud'in da suka kawo aka basu tukwicin dubu d'ari biyar, a wulak'anci suka kar6a kud'in babu sallamar arzik'i suka tafi.

Sai bayan tafiyar su ne aka saki jiki ana kallon lefen akwatina har 15 kowacce cike da kaya damk'an dakyar bag's ake zuge zipe saboda cikar kayan.

Duk kwakwkwafar mutum dai ya hak'ura da ganin kayan, k'arshe bayan an gama gani Aunty Aliya suka tattara su aka zuba su cikin d'akin Suhaima, daman Suhaima bata gidan tana can gidan Babaa Lantana ita da wasu kawayen ta biyu wad'anda suke shiri dasu.

Sai dare Suhaima ta dawo gida kasa kallon kayan tayi sabida kunya sai da Aunty Aliya ta dunga fito mata dasu tana gani a haka shima Yah Aliyu ya tarar dasu ya d'an kalla sama sama kafin yace
"Masha Allah kanwar tawa tayi goshi sai dai gaskiya kayan sunyi yawa sosai wallahi"

"Gaskiya kam sunyi kyau sai dai yawan su mu muke ganin haka amman su ba wani abun ne rabon ta ne"

Cewar Aunty Aliya kenan tana bud'e bag d'in da aka zuba sark'ok'i, sannan ta d'ora da cewa
"Yanzu ya zamu yi da motar ta? "

Sai lokacin Suhaima tasan har da mota haka ma Yah Aliyu.
"Tabd'ijam har mota fah kika ce Aliyah? "

"Kwarai kuwa baka ganta a waje ba? "

"Naga mota na d'auka ko lalace musu tayi "
"A'a ta Suhaima ce "
"Yanzu yanda za'a yi idan

Please Login or Register in order to submit comment