Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake na tsoro, yana kok'arin had'a bakin shi anata yaji alamar shigowar message a wayan shi d'an tsaki yayi kad'an sai lokacin ya tuna da bai kashe ta ba.

Janyo wayar yayi da niyyar yayi switch off d'in ta sai yaga message d'in Jiddah ce ta turo don haka sai ya bud'e shi
" _Yah Sabeer ka canja bedroom zuwa d'ayan na Suhaima nasan idan ka shiga sai ya birge ka, asha amarci lafiya, kayi k'awata a hankali please_".

Abin da Jiddah ta rubuta kenan d'an murmishi ya saki cikin zuciyar shi yana cewa lallai Jiddah ta raina shi idan ya kamata zata yi bayani har da wani ce mishi yayi hankali, batasan ya fita son Suhaima ba bazai yi abin da zai cutar da ita ba.

Tashi yayi ya janyo hannun Suhaima suka shiga toilet brush suka yi, kafin Suhaima ta ankara ya d'auke ta cak suka fita daga bedroom d'in zuwa d'ayan na kusa dashi.

Suna shiga wani sanyayen k'amshin turare ne ya fara yi musu sallama d'akin ya had'u komai kalar maroon and black ne gashi babu haske sosai sai wani hasken k'ananan bulbs kawai, d'akin yayi d'an duhu kad'an k'arasa wa Sabeer yayi kusa da bed yaga an jera wasu flowers na furanni jajaye anyi zanen heart an rubuta Suhaima and Sabeer ajiki, sosai d'akin ya birge Sabeer kuma ya k'ayatar dashi, cikin ranshi ya jinjinawa kok'arin Jiddah.

Kwantar da Suhaima yayi saman bed d'in wadda itama bedroom d'in ya birgeta sosai duk da yanda take a tsorace sai da ta gane hakan, jin Sabeer ya kwantar da ita shima ya kwanta a gefen ta ya sanya ta dawo da hankalin ta kanshi, had'a ido suka yi nan suka shagala da kallon junan su, hannun shi ya sanya yana shafa saman gashin kanta cikin wani irin yanayi yace
"Baby kin gaji ne, kina jin bacci? "
D'aga mishi kanta yayi, a hankali ya janyo ta jikin shi ya rungume ta k'am yana wani shinshina gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren ta........



_Sorry Fan's jiya nayi muku alkawarin page kuma banyi ba sakamakon ciwon kan da na yini dashi_.



Aishat A Muh'd ✍🏻
[4/3, 9:38 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺ S̺A̺N̺A̺D̺I̺N̺ S̺O̺N̺ K̺I̺*



Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aıʂɧąɬ A Mųɧɖ

Dɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ Sąɖɛɛყ Sąŋąʑ





*PAGE 81-82*






Ahankali ya janyo ta jikin shi ya rungume k'am yana wani shinshina gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren ta, cikin nutsuwa Sabeer yake yawo da hannun shi cikin jikinta, yayin da Suhaima jikinta ya hau rawa gabanta na mugun fad'uwa amman bata yi yunkurin hanashi ba, saboda tasan hakk'in shine an fad'a musu a islamia sannan Aunty Aliya da Malama Aunty Jiddah sun sanar da ita hakan, amman fah a tsorace take don tasha karanata wa a novels taji yanda amarya take shan wahala a daren ta na farko.

"Baby ki kwantar da hankalin ki bazan cutar da ke ba, wannan rawar jikin yayi yawa kin ji"

Suhaima bata yi magana ba sai wasu hawayen da suke zubo mata sakamakon wani bak'on al'amari da yake kok'arin tunkaro ta yanzu, had'e bakin su yayi waje d'aya yana wani kissing d'in ta gaba d'aya jikin shi rawa yake tamkar yanda Suhaima nata yake rawa dukkanin su sabon shiga ne a wannan yanayin, tun da ya fara kissing nata bai sakin bakin ta ba sai da yaji numfashin ta na kok'arin fita, saboda tsayin lokacin da ya d'auka nason yaga wannan bakin cikin nashi shi yasa bai yi mishi da wasa da ya cafke shi.

Cikin nutsuwa Sabeer yake aikawa da Suhaima zafaffan soyayyar shi mai ratsa kwakwalwa da tsayawa a rai, har zuwa lokacin da ya mayar da Babyn shi cikakkiyar matar shi ya zama ita ta zama shi, gaba d'aya Sabeer ya gama rud'e wa da kid'imewa awannan lokacin in banda hawayen farinciki babu abin da yake fitar wa yana rungume da Babyn shi tamkar zai mayar da ita cikin jikin shi wani dad'i ne yake ratsa jikin brain nashi da zuciyar shi na yanda ya riski Suhaima.

Kuka sosai Suhaima ke yi idanun nan sun kumbura sosai saboda kuka na azaba don ta wahala hannun Sabeer ba kad'an ba sai da ya saukar mata da duk wani tanadi da ya dad'e yana shiryawa zuwan wannan ranar.

"Baby nah Allah yayi miki albarka, Allah ya bamu 'ya'ya masu albarka, Allah ya barmin ke har k'arshe rayuwa ta hak'ik'a kin bani farincikin da bazan ta6a manta wa dashi a iyakacin rayuwa ta, zan ajiye wannan daren da yafi kowanne dare cikin tsayin rayuwata, Baby na mallaka miki kaina zuciya ta gaba d'aya sun zama naki sai yanda kika yi dasu i luv you Baby i luv U with all my heart sweet mata ta"

Ya k'arasa fad'i yana wani sake hugging d'in ta cikin jikin shi tamkar za'a kwace mishi ita, duk da Suhaima bata cikin nutsuwar ta kalaman Sabeer sunyi matuk'ar yi mata dad'i sosai har sai da wasu hawaye suka zubo mata.

"Sweet Baby sannu kiyi hak'uri nayi miki da zafi koh gaba d'aya bana cikin hayyaci nane am sorry "
Ya k'arasa maganar kamar yayi mata kuka, ganin haka ya sanya ta aro jarumta ta girgiza mishi kanta alamar babu komai but still eye's nata na zubar da tears amman sai da ta k'ak'alo smiling na dole, kallon ta yake tamkar ya had'iye haka yake ji yasan tayi juriya sosai kuma yaji dad'in hakan, but baya son ganin wannan hawayen sai yana jin zafin fitar su cikin zuciyar shi sai yaga kamar bai kyauta mata ba.


Sai da ya 6ata lokaci yana rarrashin sosai har ya samu ta bar kukan sai ajiyar zuciya da take saukewa, sannan ya tashi ya shiga toilet wanka yayi sannan ya had'a mata ruwan d'umi acikin bathtub sannan ya fita zuwa bedroom d'in yanda ya barta akwance haka yazo ya same ta, blanket d'in da ta rufe jikinta dashi ya sanya hannun shi zai cire da sauri ta rik'e hannun shi tare da marairaice face nata, cikin rarrashi yace
"Baby nah wanka zaki yi nasan zaki ji dad'in jikin ki "
Ya fad'a yana wani bin ta da mayen kallo ji yake kamar ya maimaita abin da yayi yanzu, ko had'a ido Suhaima tak'i yi dashi saboda kunyar shi da take ji sosai, bata ankara ba taji ya d'auke ta gaba d'ayan ta har da blanket d'in da take ciki yayi bathroom da ita, saboda tsorata sai da Suhaima tayi 'yar k'ara
"Kaiii Baby kin cika tsoro da yawa "
Ya fad'i hakan yana kok'arin cire abin blanket da ta kudundune acikin shi, dakyar ya iya warware shi ya sanya ta cikin ruwan d'umin, 'yar k'ara kad'an ta sake saki kafin kuma ta sauke ajiyar zuciya saboda yanda ruwan yake ratsata.

Kukan shagwa6a ta sanya mishi sai ya fita daga toilet d'in, ba don yaso ba ya fita saboda yana son taimaka mata, gyaran kan bed sannan ya fita zuwa d'ayan bedroom d'in Suhaima ya d'auko fresh milk da cup ya fito ya dawo d'akin.


Bayan ta gama gyara jikinta ne sai ta d'ora towel tana kok'arin fitowa daga bathroom Sabeer ya turo k'ofar ya shigo saboda jin ta shiru da yayi, d'aukan ta yayi ya had'e ta da jikin shi akan bed ya sauke ta, sannan ya zauna kusa da ita yana murmishi yau jin shi yake cikin nishad'i kamar yafi kowa farinciki ayau d'in nan.


Ita kuma sai nok'ewa take tana sunkuyar da kanta tare da jan towel d'in jikinta wanda yake iyakar cinyar ta yanda take janshi tamkar zai k'ara tsawo akan tsayin shi, hannun shi ya sanya saman kan cinyar ta yana shafawa a hankali sannan yace
"Baby nah ya jikin naki "
Cikin sanyin murya tace
"Ni.... Ni lafiya ta qlau "
Mak'ale kafad'a yayi sannan yace
"A'a Baby ban yarda ba, fad'a min gaskiya idan wani wajen nayi miki ciwo"
Kamar zata fashe da kuka tace
"da gaske nake ni kawai bacci nake ji sai jikina da kaina da suke ciwo "
"wayyo sannu Baby nah nasan its all my fault, am so sorry "
Yana maganar ne yana mammatsa mata jikinta fuskar shi duk tayi kalar tausayi.

Fresh milk ya zuba a cup ya bata tasha da pain relief, kok'arin tashi take ya rik'ota tare da cewa
"Baby ina xaki? "
"zan sanya kaya ne "
Rungumo ta yayi jikin shi had'e da cewa
"Muyi baccin mu kawai Baby "
D'an d'aga ido tayi ta kalli agogo sai taga har 4:35 na dare kafin ta mayar da eyes nata ta lumshe su, shafa ta yake tare da yi mata tausa a hankali wani bacci mai nauyi ya d'auke ta, yayin da Sabeer kuma ya zuba mata eyes yana kallon ta wani sonta na sake ratsa mishi zuciya da haka shima baccin ya d'auke shi yana rungume da ita cikin jikin shi.


*_8:30ąɱ_*

Ahankali take bud'e idanun ta sakamakon shafa mata fuska da ake, had'a ido da Sabeer tayi yana zaune kusa da kanta fuskarshi d'auke da murmishi har yayi wanka yana sanye cikin wata white t-shirt and trouser black kayan sun kar6e shi gashin kannan nashi yasha gyara sai shek'i take.

"Baby gari ya waye fah"
D'an lumshe eyes nata tayi sannan ta bud'e su, kafin ta fara kok'arin tashi zama tayi sannan tayi mik'a kallon Sabeer tayi sai taga ya k'ura mata ido sai wani mayataccen kallo da yake bin jikinta da kallo ganin haka ya sanyata bin inda yake kallo da eyes nata sai taga ashe towel d'in ne ya cire wanda batasan lokacin da ya fita ba, wani 'yar k'ara ta saki da sauri tare da k'udundune kanta da blanket tana mai tsananin jin kunyar shi, dariya abin ya bawa Sabeer sai ya shiga cikin blanket d'in yana dariya yace
"baby mene kuma abin 6oyewa kuma bayan naga..... "
Da sauri ta sanya hannun ta tare da rufe bakin shi k'am, d'an cizon hannun yayi kad'an da sauri ta janye shi tana yarfewa bayan 'yar k'arar shagwa6ar da ta saki.

"Ayyah Baby nah mu gani da zafi ne?"
D'aga kanta tayi alamar eh, kama hannun yayi yana busa mata shi daga k'arshe ya shagala da wani abin daban, dakyar ta kwace kanta ta shige toilet a daddafe, Sabeer kuwa kwanciya yayi saman bed jikin shi sam babu k'arfi idanun shi akan bathroom d'in.

Bayan ta gama wanka ne da d'aura alwala ta fito daga toilet d'in, tana d'an d'ingishi kad'an bata ga Sabeer ba tana tunanin ko ya fita, don haka wajen dressing mirror ta nufa cream ta shafa sannan ta nufi closet ta janyo wata atampha white da touch na pink ajiki d'inkin riga da siket ne, bayan ta sanya underwears sai ta sanya kayan sunyi mata kyau tare da zauna mata ajikinta, hijab ta d'auko ta sanya tare da shimfid'a praying mat tayi sallah tare da yin addu'a.

Zama tayi kan stool bayan ta jona hand dryer ta fara busar da gashin kanta, duk wad'annan abubuwan ta iya su ne wajen Jiddah, bayan ta gama ta shafa mishi mai tare da taje shi ta d'aure shi da ribbon, simple makeup tayi a face nata daga powder da ta sanya sai tayi gira tayi blending d'inta ta kwanta sosai gashi ta fitar da shape, sai jambaki pink da ta sanya kad'an a lips d'inta.

D'aura d'ankwalin ta tayi style mai kyau tayi mishi then sai perfumes da tayi using dasu different color's wanda daga kan body sprays, humurah and perfumes na kaya, kallon kanta tayi jikin mirror ta tabbatar da tayi kyau yanda take so, sannan ta k'arasa kan bed tana gyarawa bayan ta gyara shi yanda take so sai ta share d'akin fes duk da kuwa dauriya take don duk jikinta babu dad'i amman bazata iya kallon d'akin a hargitse ba, tana gama wa ta sanya turaren wuta a burner sannan ta fesa air freshener tuni d'akin ya d'auke k'amshi, kan sofa ta kwanta tana mayar da numfashi tare da bin d'akin da kallo yayi mata kyau.

Sabeer ne ya shigo bedroom d'in kallon d'akin yayi sosai yaji dad'i cikin zuciyar shi da ta gyarashi wani son ta ya sake shiga cikin heart nashi, k'arasawa yayi inda take kwance saman sofa har ta fara lumshe ido zata yi bacci ta ganshi ya kafeta da eyes.

Cike da kunyar shi ta sauko daga kan sofa tsugunnawa tayi cikin sanyin murya tace
"Ina kwana? "
Zama yayi fuskar shi k'unshe da murmishi ya janyo ta jikin shi kan k'afafun shi yayi mata masauki kan yace
"Lafiya k'alau Baby nah, ya kika tashi? "
"Alhamdullilah "
"Masha Allah naji dad'in ganin ki a haka Baby "
Ya k'arasa maganar yana yi mata peck a cheek nata.
"Kinyi kyau sosai Baby"
Tana wasa da warwaron hannun ta tace
"Nagode "

Sakin layi ya farayi yana mata wasu abubuwa ita gaba d'aya a tsorace take da abin shi ya sanya jikin ta ya fara rawa, cikin 'yar rawar murya tace
"Me zan dafa maka kayi breakfast "
D'an murmishin yak'e yayi abin da ya kamata ace Mumyn shi zata yi ta aiko musu ko na kwanaki 3 ne, amman hakan yasan bazai yiwu ba.
"Baby zo mu je kitchen d'in mu ga abin da za'a dafa but ni fah ko kunna gas ban iya ba sauran kiyi min dariya "

Aikuwa ya bata dariyar musamman yanda ya wani d'an had'e face yana yamutsa fuska, don haka ta sanya dariyar ta amman ta sigar jan hankali a nutse tayi ta.

"Auuu kika yi min dariya Baby nima sai na rama "
Yayi maganar yana wani shagwa6e face har da bubbuga k'afa a k'asa ta shagwa6a, tunawa tayi da vidoen da Jiddah ta ta6a turo mata ya sanyata sake tuntsirewa da dariyar, kallon ta yake cikin sha'awa sosai dariyar tayi mata kyau d'an matse ta yayi ajikin shi har sai da tace
"Wash!".
Tana yamutsa fuska ta fad'i hakan.
"Raguwa kawai don na d'an rik'e ki har da wani wash!, nima yanzu zan rama dariyar da kika yi min don haka ki shirya"

Yana gama maganar ya sanya hannun shi zai zuge zipe, nan Suhaima ido ya raina fata ta fara rarraba ido na tsoro, dariya ya sanya kan ya gyara mata rigar yace
"Kin cika tsoro Babe tashi mu tafi "



Yana rik'e da hannun ta suka fito parlour direct kitchen suka nufa, sosai tsarin kitchen d'in da yanda aka shirya shi yayi matuk'ar birgeta sosai.

Jingina bayan shi yayi jikin bango yana rik'e da hands nata yace
"Baby gashi nan na kawo ki kitchen me zaki dafa mana naci girkin 'yar amarya ta "

Murmishi kawai tayi kafin tace
"Me zan had'a maka? "
"Komai ma Baby zanci tunda ke zaki dafa min"

Tana kok'arin kunna gas ne suka ji an danna door bell, kallon ta yayi sannan ya yamutsa fuska yana cewa
"Yanzu haka Jiddah ce zata zo ta dame mu muna cikin hutawar mu ko lokacin da tayi nata auren wane ya tak'ura mata da zata dame mu"
Dariya ta kusan kubcewa Suhaima amman sai ta danne don taga fuskarshi d'auke da damuwa, amman gaskiya har cikin zuciyar ta taji dad'i zuwan Jiddah har idan itace d'in.

"Har kasan Jiddah ce ta zo? "
"Of course don nasan itace zata yi zuwan wannan wurin "
Tunawa da Suhaima tayi ko lokacin da zasu fito a d'aki da 11 na safe yayi shine zuwan wuri, Sabeer yasan ba mai zuwa cikin family d'in shi sai Jiddah shi yasa ya kawo ta cikin ranshi itace.

Fita yayi tare da bud'e door d'in aikuwa tunanin shi ya zama gaskiya Jiddah ce da sauran friends na Suhaima wad'anda anjima kad'an zasu koma gidan su, shine suka zo yiwa Suhaima sallama.

Wata harara da Sabeer ya watsawa Jiddah sai da dariya taso kubce mata amman ta danne ta tare da turo baki tace
"Wai... wai kai Yah Sabeer indai muka had'u sai kayi ta harara ta ni me nayi maka? "

Share Jiddah yayi yana amsa gaisuwar friends d'in Suhaima da suke mishi yana gama amsa wa ya basu hanya zasu wuce, aikuwa ya sanya hannun shi ya rankwashi kan Jiddah har sai da ta saki k'ara ta rik'e kanta nata wanda sauran kad'an ta zubar da basket d'in hannun ta.

Jin k'arar Jiddah ya sanya Suhaima fitowa daga kitchen duk saurin da taso yi amman ta kasa sai a hankali ta taho, Jiddah na hango ta da sauri ta k'arasa wurinta had'e da rungume ta.

"Lafiya naji kina k'ara? "
Tana turo baki tare da kau da kanta daga kallon Sabeer tace
"Ba mijin ki bane ya rankwashe ni akaina ba, duk abin da nayi mishi bai gani ba"

Had'a ido tayi da Sabeer taga yana shafa bayan kanshi, d'an murmishi tayi tare da girgiza kai kawai wannan abu tsakanin su ne ita me zata iya yi akai, hannun Jiddah Sabeer ya kamo yana cewa
"Sorry sweet sister ke kika ban haushi ina cikin hutawa zaki zo ki katse min hutu, yanzu me kika kawo mana? "

Duk a hankali yake mata maganar, yayin da Suhaima ta k'arasar da friends nata cikin parlour suka zauna.

"Yaya breakfast na had'awa Besty na da kai, ko an kawo muku daga gida? "
Girgiza kanshi yayi cikin takaici ya furzar da numfashi, hannun shi ta kamo cikin jin tausayin shi tace
"Yaya kayi hak'uri komai zai wuce insha Allah "
"Nagode 'yar uwata "

Dinning table suka k'arasa zama yayi sannan Jiddah ta fara jera kayan breakfast d'in kan table sai da ta gama sannan ta shiga kitchen ta d'auko su plate, cups, spoons and sauran abubuwan buk'ata na kayan tea, sai da tayi serving Sabeer tea ne sai pepper chicken and chip's da egg's, sannan ta had'awa Suhaima ta kallo inda take zaune acikin parlour ta d'an d'aga murya tace
"Babyn Yah Sabeer kizo kiyi breakfast "
Murmishi Suhaima tayi kan ta tashi ta taho zama tayi ta d'an fara shan tea d'in, da yake su Jiddah sunyi breakfast a gida sai kawai ta d'auko musu ruwa da drinks ta zauna a parlour cikin k'awayen Suhaima suna hira tare da kallo.

Ganin yanda take cin abincin ne yasa shi cewa
"Baby lafiya kuwa? "
"Me yafaru? "
Ta fad'a tana kai cup na tea bakin ta.
"Bakya cin abincin sosai "
Kamar zata yi kuka tace
"Ni bana jin dad'in baki na ne "
Tausayin ta ne ya kamashi cikin kulawa ya rik'o hannun ta sannan yace
"Sannu Baby amman ki daure kici abincin zaki ji dad'in jikin ki"

Fork d'in ya kar6a daga hannun ta bata yake abaki a hankali take kar6a har tace mishi ta koshi sannan ya rabu da ita, tashi suka yi daga dinning table d'in parlour ta dawo yayin da shi kuma ya shige upstairs.

Cikin 30 minute's ya fito ya canja kaya zuwa wani black boyel takalmi ma black da watch d'in shi but bai sanya hula ba sai ya gyara gashin kanshi, sosai yayi kyau Suhaima ma binshi da kallo tayi kan ta d'auke kanta kuma tana yiwa Allah godiya da ya bata Sabeer a matsayin miji.

Saukar numfashin shi taji kan face nata, d'ago eyes nata tayi suka had'a ido kafin ta janye nata, d'an murmishi yayi yana daf da k'arasa cire wannan kunyar.

"Baby zan tafi gida wajen su Daddy mu gaisa "
"Okay, ka gaida su Allah ya dawo da kai lafiya "
Sai da ya lumshe idon shi yaji dad'in abin da ta fad'a, kafin yace
"Amin Baby nah "
Yayi kissing nata a kumatu sannan ya fita.

Hira suka yi sosai har zuwa lokacin da 'yan uwa Suhaima suka zo, gara suka kawo kamar yanda al'adance ake yiwa amarya sai su dublan, alkaki da su cincin, wani abin dad'in a wajen Suhaima har da Baba Lantana da Aunty Aliyah aka zo.

Don Aunty Aliyah kasa jurewa tayi sai da ta biyo su aikuwa Suhaima rungume ta tayi k'am tana kuka, dakyar dai aka rarrashe ta tayi shiru sannan Suhaima ta canja kayanta zuwa wani lace milk and touch pink ajikin shi sai mayafi pink da shoes nan Jiddah ta fesa mata perfumes masu sauk'in kamshi suka tafi gidan su Sabeer don damk'a amanar Suhaima a hannun su.


Sakin baki da hanci suka yi suna kallon had'uwar gidan, inda Allah ya taimake su basu da yawa suka zo su 5 ne sai Suhaima, Jiddah da friends nata.

Jiddah ce tayi musu jagora har zuwa part d'in Alhj Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa suka tarar a parlour tana zaune ta wani hamshak'e kan kujera eyes nata d'auke da medical glass tana kallon tashar Arewa 24 suna yin film na india mai translation in hausa.

Sai Dr Faridah da take gefen ta suna d'an ta6a hira jifa jifa a tsakanin su, a wani kyamace suka amsa sallamar tasu ko wajen zama ba'a basu, sai da Jiddah tayi magana cikin bak'inciki tace
"Babaa Lantana Aunty Aliyah ku zauna "
Nan suka zauna jikin su a sanyaye da irin tar6ar da aka yi musu, Jiddah fita tayi ta kirawo Umman ta da sauran matan gidan duk suka taho part d'in Hajjah Hauwaa sannan taje kitchen d'in Hajjah Hauwaa ta d'ebo musu soft drinks and snack's sai ruwa ta ajiye musu.

Suna yamutsa fuska suka amsa gaisuwar su, sannan Babaa Lantana ta damk'a musu amanar Suhaima babu dai wanda yace komai saboda takaici Jiddah barin parlourn tayi, tana kyamar halin family d'in su.

Ko drink's d'in da Jiddah ta kawo basu sha ba suka taso suka fito gaba d'aya gwiwoyi a sanyaye, sosai Jiddah ta basu hak'uri a hanyar dawowar su ta gidan Suhaima.

Abinci ma sai takeaway Sabeer ya sanya akayi musu saboda lokaci ya k'ure zasu tafi, bayan sun gama ci suka yiwa Suhaima nasiha sosai Aunty Aliyah ta d'ora da bata shawarwari masu kyau.

Suna yin sallahr la'asar suka ci abinci suka tafi, driver Sabeer ya aiko ya mayar dasu gida tare da kyautar kud'i da ya basu mai yawa, Suhaima tasha kukan rabuwa dasu sosai, har jikin ta ya fara d'umi alamar zazza6i ne zai rufe ta kwanciya tayi tana kuka musamman idan ta tuna family d'in Sabeer basa sonta sai Jiddah da Daddyn Sabeer kawai, rarrashin ta Jiddah tayi sannan ta gyara mata gidan tsaf, sai da tayi wanka Jiddah tayi mata kwalliya ta shirya cikin wata gown tayi kamata sosai duk wani sura na jikin ta ya fito da yake irin roba d'in nan ce, ita ma Jiddah shawarwari ta bata sosai sannan tayi mata sallama ta tafi.

Kwanciya tayi kan kujera ga jikinta babu dad'i, ga abin da 'yan uwan Sabeer suka yi musu ga kewar gida da kad'aicin ita kad'ai agida sai kawai ta fashe da kuka aikuwa nan da nan zazza6i da ciwon kai suka tarar mata lokaci d'aya........



Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
[4/5, 9:47 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*




Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ


ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ






*PAGE 82-83*





Tana nan kwance ta kudundune cikin bargo tana rawar zazza6i ga hawayen da suke zuba a idanunta, kanta ciwo yake mata kamar ya cire duk eye's nata sunyi ja sun kumbura, tana cikin wannan halin Sabeer ya shigo bedroom d'in nata.

"Baby baccin yamma kike me yasa Jiddah bata zauna da ke ba har na dawo? "
Yana maganar yana hawa kan bed d'in, yaye blanket d'in yayi tare da sanya hannun shi zai d'ago ta jikin shi, sai yaji zafi sosai jikinta da ya ta6a jikinta, a rikice da kallo ta sai yaga hawayen da take nan da nan hankalin shi yayi mugun tashi har ya rasa me zaice yana tsoron kada ya kasance ya illata 'yar mutane, jiki na rawa ya d'auke ta ya shimfid'e ta saman k'afafun shi cikin tashin hankali yace

"Baby nah me ya same ki, ina ne yake miki ciwo, me yasa baki kirawo ni kin fad'a min na kirawo doctor ya duba ki ba, tun yaushe wannan zazza6in ya rufe ki haka? "

Muryar shi da d'an rawa yake maganar, kasa magana Suhaima tayi sai hawayen da suke zuba kawai ita abin da yake sake firgitata da tsorata ta

Please Login or Register in order to submit comment