Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡

_Love Story _




_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉

*Happy sallah Allah ya mai maita muna Allah ya karbe ibadun mu Allah ya jikan iyaye na yayi masu rahama*😭😭

_*Godiya ina mik'a d'inbin godiyata ga Allah subahanahu wata'ala daya bani damar fara wannan sabon book din lafiya"yadda nafara lafiya Allah yasa nagama lafiya Amin ya Allah*_



_*Gargad'i.l, banyarda wani ko wata yajuyamin da labari ba ...idan akayi haka to gaskiya sai mun samu matsala da ko wane ne kuwa insha Allah kuma zan d'auki mataki"*_


_*Wannan labarin tunda daga farko har karshin sa na sadaukarwa mutum ukku shi wato Nafseet Maman haidar &dan malam koko &my matar faisal ina alfahar da ku sosai*_



_Bismillahir Rahamani Rahim_




*Page one__________ 1&2___________*

Wasu ƴan mata ne guda biyu sai wani matashin saurayi ne atare da su tsalle tsalle suke da zagaye zagaye a cikin wani haɗadin falon mace da namijin kamar su ɗaya ita kuma ɗaya daban take da su dariya suke sosai wata zazzaƙar Murya ce mai shegen dadi tana cewar "Ya Jafar ka tsaya kaji wallahi wasa nake shiko saurayin kallon su kawai yake sosai yace "Allah sai ku fada gaskiya har da ke ko hamra"!?.


Dariya tayi tace" to ai laifin Ayanah ne Allah.


Da sauri ta zaro idanuwanta kyakykywa tana kallon su dariya sukeyi mata turo baki tayi cikin shagwaɓa tace "A'a fa Ya jafar bari na zauna sannan, gaba ɗaya suka zauna saman kujeru suna nishi shiru kowa yayi can sai Ayanah tace "Ya jafar wallahi jinake kamar wannan ce ranar farin cikina da dariya ta na karshe kamar wani abu zai faru da ni.


Kallon ta yayi sai yace "ke ban son hauka fa babu abunda zai faru da ke yar kanwata.


Ajiyar zuciya tayi tace" yanzun idan wata mumuna kaddara ta same ni zaka cigaba da kulawa da ni kuwa ya jafar"!?.


Wani irin dariya yayi yace "ke fa babu wata kaddarar da zata same ki yarinya ki ma daina wannan shirmen nake.


Kallon sa nayi nace "Amman ya jafar ina ji ajikina fa.


Ke Kanwata Ayanah tashi ki wuce kije ki gyara muje gida Ummy yau watan mu ɗaya bamu jeba nagaji da wannan bakin surutun.


Jikina asanyaye na wuce dakina har yanzun ya jafar be fahimci komai ba aciki raina ajiyar zuciya nayi nace "o Allah kaganin halin da nake cikin ka kawo mani ɗauke acikin rayuwa ta, mayafi na nadauko sannan na fito daga cikin ɗakin atsaye na same su, suna jirana nace"muje na gyara, to koke fa yar kanwar mu kuma Autar mu cewar Ya jafar ni dai turo baki nayi sannan muka fita daga cikin falon gurin motar sa suka tsaya buɗe munayayi sai muka shiga ciki yaja motar muka fita daga cikin gidan fuskata na kallon baki titi ya jafar da hamra labari suke suna dariya amman ban da ni gaba na kawai yake faɗuwa hankali na har yanzun be kwanata ba shiru nayi sai ajiyar zuciya nake lumshe idanuwana nayi ina jin iska na kaɗawa sosai har muka isa kofar gida ban sani ba Ayanah ke Ayanah sai da ta dake ni afirgeget na buɗe idanuwana ina kallon ta nace "har mun iso ne"!? .


Ɓala mata harara tayi tace"ban sani ba ya za'ayi kin san mun iso hankalin ki na gurin tunanin banza sai ki tashi muje cikin gida ko".

Ban ce komai ba haka na buɗe motar na fito na shiga cikin gidan da sallama wannan dan mai dai dain cin gida ne mai ɗauke da ɗaki biyu da kitchen da toilet sai ɗan filin tsakar gida gidan babu laifi yayi kyau wata dattijiwa mata ce zaune saman tabarma tana sauraron radio sallama su Ayanah taji da sauri ta ɗago idanuwan ta tana kallon mu ta rike haɓa tace "Amin wslm ku ƴaran nan dama kuna ƙasar nan "!?.

Dariya ya jafar yayi yace "afuwa Ummyn mu wallahi laifi na ne tafiye tafiye ne ya same ni shiyasa Amman yanzun nadawo gashi nan munzo goge laifin mu ko Autar Ummy ni dai nayi shiru har yanzun ban ce komai ba, Ummy kuwa kallo ɗaya tayi mani ta fahimci akwai abun da yake damuna kira na tayi tace "Ayanah ta zo nan".


Jikina a sanyaye nazo inda take na zauna sai na sunkuyar da kaina ƙasa riƙe mani hannu tayi tace "meya ke damun ki ne naga anan ta magana Amman kinyi shiru ko baki da lafiya"!?.


Girgiza mata kai nayi nace "ko ɗaya Ummy kawai dai hankalina tashe yake gaba na sai faɗuwa yake kamar akwai wata mumunan ƙaddarar da zata same ni cikin lokacin nan rike mata hannuwanayi nace "Dan Allah Ummy duk abun da ya faru da ni ki yafe ma ƴarki pls ina ji ajikina har ƙasar na zan bari wasu zaffan hawaye ne suka zubo mani, Ajiyar zuciya tayi tace "Ayanah yanzun ke shirmen ki yakai haka ikon Allah har da kuka kuma subahanah Allah ya kyauta to yanzun dai ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai faru da ke sai alkhairin Allah ....


Haka dai muka tashi muka wuce gida saboda har dare yayi saboda Amman har yanzun dai gaba na faɗuwa yake cikin falo na tsaya na ce sai da asuba ya jafar wuce cikin ɗakina nayi na buɗe dirowa kallon kayana nayi sosai cikin ƙasan kayan na ɗaga na ɗauko kudaɗe na da nake ajewa zasu kai dubu hamsin cikin aljihu nasanya su sannan na kwanta har bacci yayi gaba dani .


Misalin Karfe ukku na dare gari yayi duhu sosai ga iskan hadari yana kaɗawa, gari yayi tsint bakajin motsin komai sai na tsuntsaye Ayanah ce Kwan ce take tana bacci cikin bacci taji ihu a waje afargiget ta tashi zaune amman ihun adai dai window yake fitowa tashi tayi tazo dai dai window leƙawa nayi banga kowa ba, kuma ihun karuwa yake da sauri fito daga cikin ɗakina part din Yayana na shiga sai dai na sai mesh suna bacci jiyowa nayi nafita daga cikin ɗakin fito wa nayi tsakar gida ahankali ahankali na buɗe kofar gidan leƙawa nayi naga ko lafiya ina ta dube duba can na hango wata mata da tsohon ciki, dafe take da cikin agajiye ta gaji sosai, salati na fara da gudu naje gurin taimakon ta har na rike hannunta kawai sai naji halben bindiga,


Hankalin na ya tashi sosai rike nake da ita har zamu shiga cikin gida kawai sai dai na bi bayan gidan gudu muke bana wasa ba sai da mukayi nisa sannan na tsaya ina nisa nace"Baiwar Allah daga ina kuma meya ke faruwa da ke?ban rufe baki ba kawai sai naga ta dursune kasa tana nisa sosai nakuda ce ta taso mata zangu zangu cije baki take tana yarfe da hannu ita kuwa hawaye ne suka zubo mani cikin tausayawa nace"sannu Baiwar Allah haihuwa ce zakiyi ko gashi ni yarinya ce ban san ya zan taimake ki ba,


Murmshi tayi mata mana girgirza mani kai sannan ta cigaba da nisa .


Wasu manya manyan yan fashi ne suka zagaje mu wata irin dariya suka fashe da ita zaro ido nayi jikina ya fara rawa sai na fashe da kuka nace"dan girman Allah kuyi mata hakuri ku duba halin da take ciki ku tausaya mata dan Allah, ban rufe baki aka watsa mani wani irin mari har sai da na saki fitsari saboda azaba.


Hhhhhh hhhhh yarinya kin kawo kanki inda za'a kashe ki mu bamu san wani Allah ba bale muyi masa hhhh ita kuwa Baiwar Allah kan jariri ya fito nisa sosai take tana kira sunan Allah.


Dai dai jaririn ya fito daga cikin jikin matar yana kuka inyarr inyarr Murmushi tayi tana cewar Alhamdulillah cikin jin dadi nataso da sauri na rungume jaririn har na manta da bala'in da muke ciki ai kuwa dai dai naji halbe tasss tass....


Kuka jariri yake inyarrrr inyarrrr inyarrrr ni kuma hankali na yana gurin da akayi harbin koda na duba ashe ita ce aka halbe ta a gefen cikin ta wani irin ihu na fashe da shi jikina sai kirma yake sosai kamar mazari rungume su nayi ina kuka ina ce dan Allah ki tashi kada ki bar ni cikin wannan tashin hankalin wayyo Allah wayyo rayuwa ina zan sanya kaina girgiza ta kawai nake dariyar mugunta suka fashe da ita ɗaya daga cikin yan ta'adar ya kira waya sai naji yana cewar "mun aika ta ƙiyama hhhh...........

****** ****** ****** ****** *******
Aryan! Aryan!! Aryan!!! Aryan!!!! Mutane ne zaune cikin statedioum suna kallon ball wani hadaɗin saurayi ne sanye yake da kayan ball shine number ta shida guda yake sosai sai kirari ake masa sai da ya yaja da baya sosai sannan ya halba ball din ta shige cikin raga, ihu mutane ko ina suna cewar "eyy goooo gooo wannan hadaɗin saurayi ya durkusa kasa yayi sujadar gode Allah yar uwan sa da al, umma suna cikin farin ciki sosai da gudu wasu ƴan uwan sa suka rungume shi suna murna sosai.



Agurguje suka koma gida cikin farin ciki a cikin wannan hadaɗin falo suka zube saman kujeru suna ajiyar zuciya shi kuma gogan tashi yayi yana tafiyar gadara har ya shiga cikin part din sa nima na bayan sa na shiga cikin part dinsa gashin kansa yayi luf, lufu har walƙiya yake da sheƙi saboda kyawun sa gefen kumatun sa dai dai gurin kunnuwan sa ɗauke take da saje mai kyau wanda yara tsa saman leɓin sa na sama ƙasan leɓin sa ga gemun sa da ya kara masa kyau sosai subahanahu Allah tsallaki ya tabba ga Allah subahanahu wata'ala da ya halici wannan bawan iya haɗuwa ya haɗu fitowa yayi daga cikin toilet ya watsa ruwa ya daura towel ajikin sa dai dai madubin dakin yayi tsaya yana tsane ruwan jikinsa zaunawa bakin gado yayi yana kallon photon wasu manya manya mutane da ke tsaye tare da wata yar budurwa tana dauke da murmushi ajiyar zuciya yayi yace "oh Allah na manta ban kira my love sister na ba.......



*T SOJA ce* 07063617906

*Comment and share*



⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_Love Story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉



_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 3&4__________*

Ɗan fashim ya kira waya sai naji yana cewar "mun aika ta ƙiyama hhhh..


Da sauri na ɗago jajayin idanuwana ina kallon su shi kuma ya kalle sauran yace " ku wuce muje..


Kuka nake sosai kamar raina zai fita durkusawa kasa nayi ina kallon su har suka fita daga cikin dajin kuka nake sannan hankaki na yadawo gurin matar riƙe mani hannuwa tayi numfashin ta nayi sama da ƙasa bakin ta jini yake zubowa duk da dare ne akwai hasken hadari murmushi ta saka mani hannun ta ɗaya ta sanya cikin rigar ta sai ga wasu abubuwa ta fito da su tana kallona muryar ta na rawa tace"ki rike wannan zasu taimaka maki har da jaririn ki na baki shi halak malak yar uwa ajiyar zuciya take ni kuma kallon ta kawai nake sannan ta cigaba da cewar "wannan shine key din mota ta da nazo da shi akwai wasu abubuwa sosai wanda dole sai kin neme su acikin laptop dina da Wayoyina password din sa shine Aryan ko ina zaki shiga cikin dole sai kinya sanya Aryan wato yaya nah ne sunan na Fannah........


Wani irin ihu nayi ina girgiza ta Amman shiru kuka nake gashi ban san yazanyi da cibiyar su ba wani tunanin ya faɗu mani da sauri na cire ke ɗan kunne na na, yake masa cibiya sannan na cire ke ɗan kwalina na sanya masa jikina sai rawa yake kamar mazari haka natashi nabe hanya jikina duk jini ne agashi an fara kiran asallatu har ina iso bakin get sai yanzun hankalina ya kara tashi sosai to ta ina zan fara masa baya ni ni kuwa babu yadda zanayi haka na shiga cikin gidan dai dai lokacin ya jafar ya fito daga cikin gida zayaje masallaci hango ni yayi tare da wani abu sosai yayi mamakin ganina wannan lokaci ina ganinsa wani irin dumm dumm naji gaba yana yi addu'a nake ko wace irin ce karasowa nayi jikina na rawa nace "Ya jafar kafin naƙara sa sai yaji kukan jariri inyarrr inyarrr zaro ido yayi yana salati yace "ke Ayanah ina ki sato jariri nan"!?


Jikina yana rawa nace "Wallahi tallahi da gaske nake Yaya ba sace wannan jariri nayi ba mahaifiyar sa ce ta bani shi lokacin da anka kashe ta.


Wata irin dariya yayi yace "lallai kam Ayanah ah ni zaki raina wa hankali wai yaushe aka haife ki da har zakiyi mani karya mtss kin ga ki fada mani gaskiya ko wallahi yanzun muje gida gurin su Ummy.


Da sauri dago idanuwana jajaye ina kallon sa wai Yaya na abun sona shine be yarda ni ba innalillahi wa Inna ilaihir raji un wannan wace irin kadara ce wayyo Allah na nace"yanzun inda mukaje da kai gurin zaka yarda da ni"!?.


Kallona yake sosai yace "tashi muje din Amman kisan duk na duba naga karya kike ko to wallahi ke da gida na har abada wuce muje jikina na rawa haka muka fita daga cikin gida tafiya muke sosai sai da mukayi nisa sannan nace "Ya jafar ga gurin can muje kagani kallona yake Amman be ce komai ba haka ƙarasa gurin abun mamaki shine babu wanda matar hankalina yayi dubun tashi nace "to ina tashiga ne innalillahi"!?.


Wani irin kallo yake be da tashi afusace ya yaja hannu na giriri kamar kayan wanki ina cewar "Ya jafar wallahi daga gaske nake baƙarya nake ba ko kallon inda ke beyi ba gashi har gari ya waye mutane ya fitowa a ƙafa mukaji gida cikin gida muka shiga ko sallama ba lokacin Ummy na share share shigowar mu ne ya sanya ta miƙe tsaya tana kallon mu tace "ku kuma lafiya zaku shigo mani cikin gida ko sallama babu eye"!?.


Cikin fushi Ya jafar yace"Ummy kalle hannuwan Ayanah kigani fa"


Kallona tayi sosai har idanuwanta suka sauka gurin jaririn dake hannuna kuma jikina duk jini ne tace "menene a hannun ki Ayanah ki faɗa man.

Kuka na fashe da shi sosai muryar ta na rawa nace "Ummy ban karasa ba yace"to jariri ne ahannu ta Ummy ashe cikin shege tayi bamu sani ba, da sauri na kalle sa nace "Ya jafar cikin shege kuma wai ni kake cewar cikin shege nayi innalillahi wa inna ilaihir raji un wallahi tallahi ko hannuna babu saurayin da ya taɓa rike hannuna sai kai ɗan uwa na wallahi Ummy ku yarda da ni mana dan Allah".


Wani irin kuka Ummy ta fashe da shi sosai tace "yanzun tarbiyar da naki kenan Ayanah yanzun abun da zaki shaka mani da shi kenan innalillahi wa inna ilaihir raji un hasbinallahu wan'imalwakil ina Godiya sosai da zuba mani da mutumci da kikayi kai kuma irin amanar da na baka kenan ko shike nan nagode Amman ka sani wallahi da sauri nace "Ummy kada ki tsine mani naji zan bar maki gidan ki insha Allah wata rana zaki gane gaske kuma zaki yarda da ni da sauri na fita daga gida ina kuka kofar gidan nayi tsaya ina kallon sosai sai ga Ya jafar ya fito daga cikin gida ko kallona beyi ba ya sanya ka ya wuce sai kuma ya dawo yace"kuma kada ki kurkura da sunan zakije mani gida wallahi sai na kashe ki mtsss sannan ya wuce ya bar ni kaɗa ajiyar zuciya nake har kai na ya fara ciwo kukar jariri ne ya dawo da ni daga cikin tunani tashi tsaye nayi ina girgiza shi nace "to yanzun ina zanije ko na fara zuwa asibityn yara ko kuma can sai maganar Fannah ta faɗu mani arai nace "Ya Allah ka raya mani Aryan junior ya Allah ka da ka barshi da aikata zina da sauran laifufukan ka Allah, kallon sa nayi har sai daga gaba ya faɗi goya sa nayi sannan natashi na cigaba da tafiya ta kamar wace kwai ya fashe mata acikin ciki har na shigo unguwar su Ya jafar na kallon kofar gidan hawaye na zubo mani gogewa nayi sannan na wuce ina tafiya har junior yayi bacci har sai da na kawo bakin titi wata katuwar motar da aka fada mani ita ce na hango sai kuma wani farin ciki ya kamani kamar bani ce ke kuka ba gefe na na kalle shagogon da ke gurin sai naga nasiha medicine da sauri ta tashi na shiga cikin shigon da sallam mutane ne gurin sosai wani ya ganina yace"me za'a baki yarinya, shiru nayi ina tunani sai can nace dan Allah malam madarar jariri zaka bani kuma nawa take"!?.


A. B. C ce duk guda ɗaya naira dubu take akwai kuma babbar ta wanda yake sa shi jiki sosai nace "to ina kuma nawa take ne malam, yace "gaskiyar ta dubu ukku take Hajiya, ok bani guda huɗu da kuma pampa dan Allah Akwai Feda ...

Eh akwai ta Hajiya nace ok ka sanya mata ita dan Allah ok Hajiya...


****** ****** ****** ****** ******

Aryan ne ya ya ciro wayar kira cikin phone number ya shiga my love sister yayi call Amman akashe wayar take shiru yayi yace "wai meya faru ne ina kiran ta bata shiga da sauri kira wata number.


Wasu manya manya mutane zaune saman kujeru kowa yayi shiru wata dattijiwa mata ce tace"Me kuke nufi ne wai kuna nufin wai Fannah din ce ta ɓata sai kace leda to wallahi kun san halin mijina da yaji wannan labari kun shige su ni da wallahi sai bata kara sa sai taga rigging din waya ta tace "dan halak gashi ya kira sai da ta kusan tsunkewa sannan ta ɗaga tace "mijina ya kake"!? .


Ajiyar zuciya yayi yace "lafiya klau mai ɗakina wai ni ko ina Fannah ta shiga ne ko cikin ya hanata shaƙatawa ne"!?.

Hansfree ta sanya tana kallon su tace "meka ce ban jiya ba"!?.


O ni Aryan nace wai ina Fannah ta shiga ne wai"!?.


Shiru kowa yayi yana tunanin ta ina zai fara gyara tayi sosai tace "ayyah ai ta fita wai zataje Asibity ne".


Ajiyar zuciya yayi yace "ok babu damuwa zan kira anjima idan tadawo asibity sai ya kashe wayar.


Kallon su tayi tace "Ahmda musa ku tashi kuje duk inda tashiga ku nemota wallahi kunji na rantse ko to girgiza kafafuwanta take tana hararar su.


Wani ɗan saurayi yana jin duk abun da yake faru dariya ya fashe da shi sosai sannan ya ciro wayar ya kara ga kunnen sa yace" yanzun za'a fara wasar ni Taufeek ai ba'a wasa da ni hhhhhhhh.


Wata balarabiyar mata ce tashiga cikin wata hadaɗin mota sai wani driver yake tuƙin motar matar tana baya beni beni ta kalle agogon hannunta tace "wai har yanzun ba mukai shago hamza ba ne mtss na fa gaji wallahi kasan jirgen mu ya kusan tashi ko"!?


Driver yace "dan Allah kiyi hakuri Hajiya mun kusa isowa gurin, sannan ya cigaba gaba da tuƙin har sai da ya shigo cikin unguwar dai dai inda motar Ayanah take anan yayi parking da sauri ya fito ya buɗe mata kofar motar fitowa tayi daga cikin motar tana gyara glass pink tafiya take har ta shiga cikin wannan shigon kayan kitchen da yara..


Madara jariri ya ɗauko da pampa da feda cikin leda ya sanya mani sannan na ciro dubu goma shida na bashi ɗaukar ledar nayi na fito daga cikin shagon dai dai kusa da wata motar nayi zaune kamar marainiya shiru nayi ina tunani duniya hawaye ne suka zubo mani masu zafi kuka na fashe da shi gashi har da yunwa nakeji fitowa matar tayi har zata shiga, cikin motar sai ta hango ni zaune ina kuka kallon driver tayi tace "amm sanya mani kayan cikin motar ina zuwa zagayowa tayi dai dai ina nake zaune tazo tace"yarinya lafiya kike kuka kuwa"!?.


Ɗago jajan idanuwana nayi ido huɗu sai da gaban ta ya faɗi kara fashe da kuka nayi nace "nima kai na ban san kowa ba bani da kowa sai wannan jariri sai wannan motar da abun da ke cikin ta na manta komai jikina rawa yake sosai cikin tausayawa sai da tayi hawaye ta tace "Allah sarki dama yarona ɗaya kuma yana nos Korean gurin uncle din sa dama bani ƴa mace yanzun gashi Allah ya bani har da jikana to ya sunan ƴatawa da shi mijina "!?.


Share hawayena, nayi nace"Ayanah shi kuma Aryan junior.


Masha Allah tashi idan akwai abubuwan da kike bukata ki buɗe motar ki ɗauka saboda zan ba wani ya wuce da ita gida na acikin gari nan, tashi nayi na buɗe motar na ɗauko laptop da wayoyo guda ukku sai wata babban jaka buɗe jakar nayi na ga kuɗadi sosai har da takardun dukiya kuɗin gida biyu na raba su sannan nace "Maa ga kuɗadi na yazanyi da su to murmushi tayi tace "ok bani kuɗadin na za'a jowa maki su har da gida za'a siya maki da su koda kinzo ziyara.


Murmushi nayi nace "to nagode sosai Allah ya saka da alkhairi miƙa mata jakar nayi ina murmushi buɗe motar tayi tace "shiga cikin motar muje airport yanzun jirgen mu zai tashi zuwa India , shiga cikin motar nayi sannan na sauko da junior bacci kawai yake sosai lumshe idanuwana nayi bacci yayi gaba da ni mafarkin fannah nayi tana mani murmushi.......



*HASSY SOJA ce*✍🏻

_T SOJA CE_📚🔥 07063617906



⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_Love Story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 5&6__________*




Tana cewar "gaskiya ina godiya sosai da sadaukarwa rayuwa ki a gare ni insha Allah zakiyi alfahar da wannan rayuwa, da sauri na tashi zaune ina kalle kalle har mun iso airport koda na idanuwana sai naga Maa tana kallona tana mani murmushi tace"har kin tashi Angel dina kenan ko"!?.


Dariya nayi nace"eh Maa wallahi ban san mun iso airport ba fa.


To tashi muje har yanka maki ticket yanzun an fara kiran mutane, wayar ta ce, take rigging da sauri ta ɗaga tace "Na'am my husband eh yanzun ma haka tare muke da su ok dan Allah kayo masu shopping har da mijina junior hhhh wallahi kuwa sai mun iso insha Allah ok bye bye kashe wayar ta tana dariya tace "wallahi daddy kin ya bani dariya tunda na bashi labari komai na ki yace "sai mun iso.


Fitowa mukayi daga cikin motar amsar junior tayi ta ɗaura sa saman kafadar ta rike hannuna tayi kallon driver tayi tace "ga wannan ka kira Alhaji bala kace masa muyi waya da wannan saƙona ne kaji ko murmushi yayi yace "to Hajiya Allah ya kaiku lafiya insha Allah zan fada masa komai har da motar zan wuce da ita ko murmushi tayi tace "yauwa dan gari babu damuwa insha Allah zan turo maka Alts , sannan kuma wuce cikin Jirge kujera gefe muka zauna ko mintin biyar bamuyi da shiga ba aka fara sanarwa kowa ya gyara zaman sa Jirge zai tashi ballet aka nuna mani sannan na ɗaura jirgen mu ya tashi sama lumshe ido nayi gaba na sai faɗuwa yake addu'a nake har ya dai daita da tafiyar sa.... .



Aryan ne cikin jirgen yau zai dawo Nigeria

Please Login or Register in order to submit comment