Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗan ƙaramin ɗaki tace "ganin Yaya na lafiya kake mani wannan kiran"!? Dariya yayi cikin farin ciki yace "albisirn ki Halima" da sauri tace"goro kuma fari" dariya yayi yace "yau wallahi nayi farin gani kin san wana ganin"!? Girgiza masa kai tayi tace "Aa sai ka faɗa Yaya na" "Bani kujera na zauna", cewar Ya jafar da sauri ta ɗauko masa ƙaramar kujera ta miƙa masa da sauri ya amsa ya zauna yace "Himm wato addu'ar da muke kullum da safe da dare ko to yau Allah ya amshi addu'a mu wallahi naga Ayanah cikin wata shegeyar haɗaɗar mota ce take cikin ta kinga wani irin shegen kyau da tayi"!? Zaro ido tayi har da bugun kirji tace "kace Allah wayyo Allah dadi ina zan sanya kai na to ya kukayi da ita"!? Himm yace "har da wannan jaririn da tazo da shi to yanzun ya girma wallahi har da ball nagani a hannun sa Amman" sai yayi shiru kallon sa tayi tace "Amman me ya kayi shiru kana bani labari kuma kayi shiru"!? Ajiyar zuciya yayi yace "munayi ido huɗu da ita kuma san mintuna 30 da sauri ya rufe glass din motar ta kuma har na bi bayanta Amman kashii motar su ta ɓace mani" wasu hawaye ne suka zubo masa cikin tausayawa tace "Ayyah babu komai insha Allah zata dawo gare ku yanzun dai kaje ka watsa ruwa sannan.


Kaji gida gurin Ummy sai kabata labarin kaga Ayanah insha Allah zataji daɗi kuma zatayi maka maganar cikin lallashi ta kwantar masa da hankali har ya saki jikinsa tayi yayi ya zuba ruwa ga bukiti ya shiga toilet girgiza kanta tayi tace "Allah yasa Ummy ta yafe maka Yaya na......



Wata hadaɗar unguwa ce muka shiga dai dai wani shegen gida ne wanda ya amsa sunan sa gida horn mai gadi ne ya buɗe get din sulalawa da motar yayi cikin gidan kallon tsarin gidan nayi sai ya burge ni green and yellow wow nace "kai gaskiya kun iya zaɓin gida mai kyau bala driver" dai dai gurin da motocin suke nayi yayi parking fitowa mukayi cikin motar cikin gida muka shiga komai yayi kyau har da tsarin gidan ba ƙarya part din na na wuce toilet nashiga na watsa ruwa sannan na fito daga cikin toilet wadiruf na buɗe kaya sanyawa ne kala kala baƙar abaya nazaro daga cikin har da mayafin ta sai takalmina masu shegen tsini baƙi sanya abayar nayi na ɗaura mayafi akafaɗa ta junior ne ya shigo da gudu nace "zo na cire maka wannan kayan na jikinka" da sauri ya karaso yana murna cire masa kayan jikin sa nayi na ɗauko masa riga da wandon su Amman gajire sanya masa nayi sannan na fesa masa turarin masu shegen kamshi sannan nace "to muje unguwa ko "!? Kallona yayi yace "mum inda mukaje ɗazu ko "!? Girgiza masa kai nayi nace "Aa wani guri zamuje" rike masa hannu nayi muka fito daga cikin gida dai dai gurin motocin mukayi tsaye bala driver ne yazo da sauri yace "Hajiya ƙarama wace kalar mota zamu ɗauka "kallon motocin nayi nace "wan can brown din ita zaka, ɗauko muna ".


Karasowa gurin yayi ya buɗe motar ya shiga tare da junior muka shiga cikin motar yaja ta muka fita daga cikin gida gaba ɗaya tafiya muke a cikin mota yace "ina zamuje Hajiya ƙarama"kallon sa nayi nace "muje gurin shopping sannan sai mu wuce gudu yake shararawa saman titi sosai dai dai gurin wani shegen shagon ne yayi parking ATM din na , na bashi nace pin din Aryan kayan abinci da lalashe lalashe zaka siyo dan Allah kada kaɗe" amsa yayi ya fita daga cikin motar cikin shagon ya shiga ni kuma nayi jingine ajikin kujerar motar kusan minti biyar sai gashi yadawo tare wasu masu kawo kaya buɗe but din motar yayi cikin aka sanya kayan sannan yadawo cikin motar ya miƙa mani ATM din amsa nayi ya cigaba da tuƙin sa ni kuwa gabana sai faɗuwa yake sosai addu'a nake har cikin raina hanya nake ta nuna masa har muka shigo cikin unguwar mu ajiyar zuciya nayi mai ƙafin gaske lumshe idanuwana nayi nace "dai dai kofar gida mai bishiyar ɓedi zakayi parking kaji ko"!?.


To Hajiya ƙarama cewar bala driver cigaba da tuƙin sa yayi dai dai kofar gidan yayi parking sannan yace "mun iso Hajiya ƙarama" buɗe idanuwana nayi jikina na rawa na ɗauko laptop dina da wayoyo na , na sanya su cikin jakata ball na hannun junior buɗe motar nayi muka fito daga cikin motar rike hannun junior nayi ina kallon gidan addu'a nake sosai jikina rawa yake sosai haka na shiga cikin gida tunda cikin zaure har cikin gida nake kallo cikin gida na shiga bakina ɗauke da sallama Ummy ce na hango rike da tsinsiya tana shara sallamar da tajiya wada bazata taɓa mantawa da sauri ta ɗago idanuwan ta tana kallona ido cikin ido miƙewa tsaye tayi baƙinta na rawa tace"Ayanahhhhhh Ayanahhhhhh kece ko mafarki nake"!?.


Hawaye ne suka zubo mani cikin farin ciki ina kallon Ummy na buɗe mani hannu tayi sakin hannun junior nayi da gudu ta faɗa saman kirjin ta ina kuka sosai nace "Ummy dan Allah ki yafe mani ko zan samu farin ciki da natsuwa ta nake maganar cikin kuka " rungume ni tayi tace "wallahi bakiyi mani komai Ayanah har ranar da nakore ki nayi kuka har da leƙawa nayi waje ko Allah zai sa naganki Amman kashi babu ke babu labarin ki haka nadawo gida........






⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 17&18 __________*


Share mani hawaye tayi taja hannuna cikin farin ciki nace"Ummy ki bar na ƙarasa maki sharar dan Allah" girgiza mani kai tayi tace "ki bari ki huta mana" dariya nayi sosai nace "to ai da dai kin bari na share ko "!? Junior kuwa hankalin sa ga ball, ball din sa yake hankalin sa kwan ce.


Kallon sa Ummy tayi tace "Ayanah wannan shine jariri da kika zo da shi"!? Ɗaga mata kai nayi nace "Ey shine wannan sunan sa Aryan junior Amman muna kiran sa da junior.


Ummy tace "Allah sarki kai miji marar ƙabo zo nan" tana kallon sa kallon ta yayi yana dariya nace "zo mana ku gaisa da Ummy na" ai kuwa da gudu yazo ya faɗa mata saman kafafuwan ta yana dariya yace "Ummy ko"!?.


Dariya Ummy tayi tace "ke Ayanah haka yake da son jiki"!? Murmushi nayi nace "uhm Ummy dan dai baki ga su Maa ba yarda yake wasa saman kafafuwan su wallahi" kallona Ummy tayi tace "wace ce kuma Maa"!?.


Ya jafar ne yazo da babur dinsa ya hango wata hadaɗar mota ja kofar gidan Ummy dai dai gurin motar yayi parking saukowa yayi ya karaso gurin kallon motar yayi yace "ko waye acikin wannan shegen motar oh wuce wa yayi cikin gidan da sallama bala driver kuwa kallon sa kawai yake yana shan waƙoƙin Hausa.



Zanyi magana kenan sai mukaji sallama Ya jafar murmushi Ummy tayi tana kallon sa shigowa yayi gefen kitchen ya durkusa ƙasa yace "Ummy ina yini" Murmushi tayi tace "Alhamdulillah jafar ai na yafe maka" cikin sauri yace "Masha Allah wai Ummy wata hadaɗar mota ce na ganin ƙofar gidan nan ko baƙuwa mukayi ne" Kallon sa nake nace "Ummy Ya jafar ne ya koma haka"!? Da sauri yace "Ayanah ke ce da sauri ya karaso gurin yana dariya cikin farin ciki kusa da ni ya zauna nace "Ya jafar ina motar ne ya naga duk karame"!? Ajiyar zuciya yayi yace "labari ne Amman bari sai kin huta bari naji gida nazo da Halima, da sauri yafita daga cikin gida .


Ko minti biyar ba'ayi ba sai gashi yadawo tare da Halima ni dai kallon su kawai nake cikin farin ciki Halima tace "Ayanah ashe da gaske Yaya na yake ya ganinki cikin mota gaskiya Allah shine abun godiya tana kallona murmushi nayi nace " haka ne Halima yanzun ku biyu ne kenan yanzun dai bar ku gaisa da Maa sannan sai muyi magana" Zaunawa sukayi saman tabarma suna kallona cikin murna ..



Jakata na buɗe laptop din na, naɗauko na cire mata password kiran Maa ne nace "Ummy bari ku ganinta yanzun " rigging take ɗauka tayi wata hadaɗir mata ce Zaune saman kujera ka hango wani kusa da ita dariya nayi sosai nace "Uhm Maa miss you, kallona take fuskar ta ɗauke da murmushi tace "my Angel kin manta da mu "!? Girgiza mata kai nayi nace "Aa fa Maa wallahi yanzun na samu zama ".



Dariya tayi sosai tace"to yanzun ina mijinah yake wani matar fa"!? Murmushi nayi nace "ga Ummy na da Ya jafar dina ga kuma matar sa" Zaro ido tayi tace "kai Masha Allah bata mu gaisa" miƙa wa Ummy nayi Amsa tayi tace "ina yini Hajiya" Maa tace "lafiya klau ya gidan ashe kun gane Ayanah ko to Masha Allah Amman yaushe zaku zo ƙasar mu"!? Dariya Ummy tayi tace "to ni ina nasan ƙasar ku" da sauri nace "Ummy ƙasar india muke fa" Maa tace "wallahi kuwa can muke" Ummy tace "ina Godiya sosai da kulawa gaskiya naji dadi ganin tarbayar ƴata lafiya klau Alhamdulillah Allah ya saka maku da alkhairi...



Dariya Maa tayi tana kallon su tace "Aa babu komai wallahi yanzun dai yaushe zaku zo ƙasar mu ne"!? Da sauri nace "Maa zuwa sati mai zuwa insha Allah" jin jina kai tayi tana kallon mu tace "to Allah ya kawo ku lafiya kuma Amrha tana so zuwa inda kike saboda akwai wani abun da zakuyi" ajiyar zuciya nayi nace "insha Allah zan dawo Amman jibi ake bikin da nazo yi ki gaishe mani da su daddy sai na kira sa" murmushi tayi tace "zasuji insha Allah " kashe wayar nayi ina murmushi nace Alhamdulillah Ummy kun ga su Maa ko"!? ...........


Kallona Ya jafar yake sosai sannan yace "ƙanwata yanzun kina nufin a ƙasar india kikaje har kikayi rainon wannan yaro"!?.


Nace "ey mana ku bari sai gobe insha Allah zan baku labarin tafiya na can ƙasar india a nan zan kwana gobe sai mu koma can gida na gaba ɗaya kowa da kowa sannan kai bari dai sai gobe sai ka bamu labari " Halima tace "Ayanah yanzun kina nufin har da gida gare ki ikon Allah".


Ummy kuwa murmushi kawai take cikin farin ciki kallon mu take da sauri junior yace "Mum baki ɗauko mani chocolate dina ba na baiwa Ummy caya ba"!? Sai da kowa yayi dariya nace"eh Amman zo kaje gurin bala driver kace ya shigo da kayan ko zo tare da sauri miƙe gudu ya fita gurin bala driver, bala driver yana ganin junior sai ya buɗe motar yana dariya junior yace "Uncle wai Mum tace ka shigo da kayan cikin gida " yana dariya bala driver ya fito daga cikin motar ya zagaya but ya ɗauko kayan abinci da su chocolate da etc rufe but din yayi sannan ya shiga cikin gidan da sallama gaida su yayi sannan ya fara ajiye kayan ledar chocolate junior ya ɗauko sai nishi yake sosai har da zufa dai dai gurin Ummy ya ajiye su yace" Ummy na ga caya ba nan nakowa maki yana dariya.


Baki kowa ya saki yana kallon sa ni dai murmushi nayi nace "to Ummy ki ɗauka mana tunda yazo maki da su" amsa tayi tana kallon sa cikin sha'awa tace "Allah yayi maka albarka ya jikin da sauri nace "Amin Ummy ai ba sai kin ai ƴaba" kallona sukayi ni kuma na ɗaga masu kai, kiran sallah magrb ne yasan Ya jafar ya tashi yana kallon Halima yace " to tashi muje gida madam " cikin jin kunya ta tashi suka yi muna sallama suka fita bala driver ne yashigo yace "Hajiya ƙarama ba yanzun zamu wuce gida bane, nace "eh ka tafi gida sai gobe insha Allah Amman inda zaka zo ka ɗauko farar mota kazo da ita dan Allah " cikin girmamawa yace "to Hajiya ƙarama insha Allah" sannan ya fita daga cikin gidan......

***** ***** ***** ******


Hajiya Kakus ce Zaune saman kujera tana kallon su fuskar ta babu annuri su Alhaji Ahmda Mommy da Hisham da mom da Taufeek da Aunty Amarya da mustapah suna zaune kowa yana kallon ta gyara zaman ta tayi tace "to ku sani kowa babu wanda ban san halin sa to zanyi baƙuwa kwanan nan wallahi duk wanda ya nuna mata halinsa to sai da ya bar wannan gidan idan kuma kai Ahmda ne ko musa to sai dai ku zaɓi uwa Amman ba dai ni ba taƙarshe maganar tana harara su" Hankalin kowa sai da ya tashi sosai jikin su Alhaji Ahmda ya kama rawa gaba ɗaya suka ce insha Allahu babu abun da zai faru Hajiya Kakus.


Oho dai ko ku gyara ko ma kardai Allah ya sa ku gyara na fada maku tau ku tashi ku wuce ku ban guri cewar Hajiya Kakus tana harara su da sauri kowa ya kama gaban sa mai da hankalin ta tayi gurin kallon sunnah tv...



*A GIDAN UMMI KUWA*


Zaune take saman kujera ta gaji har tasaki kashi saman kujera sai kallon tv kawai take wata ƴar aikin ta ce tashigo da sallama tana mere baki tsaye tayi tana harara ta tace "ke uwar banza ni fa wallahi na gaji da baƙin wannan aikin wallahi haba fisabillahi ke kullum baki da aiki sai baƙin kashi da fitsari a zaune to ba zan iya ba fita tayi daga cikin falon kusan awa ukku tana nan zaune har falon ya lallace da wari sai ga Hajiya kakus tazo da sallama warin da jiya ne da sauri ta rufe hanci tana kallon Ummi tace" ya Rasu lillahi manzon Allah (S. A. W) me zan ganin haka ke mero! Mero!! Tsaye tayi tana kallon kofar falon sai ga mero ta shigo cikin falon da sauri Hajiya Kakus ce ta ganin da sauri ta durkusa ƙasa jikin ta rawa kawai yake kallon ta Hajiya Kakus tayi tace "ke mero yanzun aikin da nasa aka ɗauke kenan to shike nan yanzun maza maza ki tatara naki inaki ki bar mani gida wallahi tallahi ko minti biyar kikayi ko Himm " kuka ta fashe da shi sosai tace "dan Allah Hajiya" da sauri Hajiya Kakus tace" Hajiyar uwar ki ko to bari ki ganin" wayar ta ta ɗauko daga cikin jaka zata kira wani da gudu mero ta fita daga cikin falon..........


. ⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_Love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉



*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Call me or Whatsapp me 08066268951
Or 09022823910




_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 19&20 __________*

Tura keken Ummi tayi tashiga da ita cikin toilet wanke mata jikinta tayi sosai sannan ta fito da ita daga cikin toilet din falo tadawo da ita ta zaunar da ita saman kujera sannan ta ɗauko turarin ɗaki ta sanya falon ya kamsashi dawowa tayi ta zauna tana ajiyar Zuciya.


Ummi kuwa sai kallon Hajiya Kakus take tana murmushi alamar taji daɗi sosai Hajiya Kakus tace "Insha Allah zaki warke Sameera"


*A GIDAN ARYAN*


Aryan ne zaune saman lafiyayan gado yana kallon sama tunanin mafita yake cikin ransa yana cewar "kai ya kamata ace naji Nigeria saboda naga halin da gidan mu yake" ajiyar zuciya yayi a fili yace"AYANAH hhhh AYANAH him ban manta da ke ba kina cikin raina bawai na ƙale ki bani Aa" sai yayi murmushin mugunta da sauri ya tashi ya haɗo kayan ya ɗauke key din gidan ya fita daga cikin gida sai airport jirgen Nigeria ya shiga sai ƙasa Nigeria.

Asauka lafiya Aryan......



Aryan ne ya sauko da cikin jirgen kiran waya yayi sai gashi cikin minti biyar sai ga driver yazo ɗaukar sa ƙarasowa yayi gurin ya buɗe motar ya shiga driver yaja motar suka bar gurin rufe idanuwan sa yayi sai ga fuskar Ayanah lokacin da ta watsa masa mari da sauri ya dafe kuncin sa yana shafawa cikin masifa yace "wallahi sai na wulaƙan ta ki ni ko ba ƴar gwanan ba ko ƴar shugaban ƙasa kike wallahi sai na wulaƙanta ki sai kinyi da nasani zuwan ki nos Korean wallahi" driver kuwa sai da yaji tsoro saboda yasan halin ogan su akwai masifa wata rana.



A tsora ce yace"wani gida zamu sauka ko gidan Ummi zamuje" ƙalesa yayi kamar beji abun da yake cewa ba sai da ya kusan minti biyar sai yace "gidan Ummi zamuje" sai yayi shiru gudu yake shararawa saman titi har ya shigo cikin unguwar su horn yayi sai mai gadi ya buɗe kofar sulalawa yayi cikin gidan sannan ya fito daga cikin motar cikin gida ya shiga ko da ya shiga cikin gida da sallama Hajiya Kakus kusa da Ummi zaune ajiyar zuciya yayi yace " Hajiya Kakus yaushe kika zo "!? Da sauri ta ɗago idanuwan ta tana kallon sa tace "Aa mijina yaushe kadawo kuma"!?.



Karasowa yayi gurin durkusawa ƙasa yayi yana kallon Ummi hannun sa a fuskar ta yace "Hajiya Kakus hankalina yadawo gurin Ummi na ina ji a jikina kamar tana cikin damuwa cikin bacci nake ganinta Hajiya Kakus ko ƴan aikin ta ban ƴarda da su ba wallahi ni yanzun ma abun da nake tunani ina zan samo mata ƴar aiki mai kula da ita "!? Nisawa tayi tace "ni dai yanzun abun da nake so da kai shine kayi Aure matar ka ita ce zata kula da kai da ita Ajiyar zuciya yayi yana kallon Hajiya Kakus yace "to ina zan samu matar Hajiya Kakus ni fa har yanzun ban ga yarinyar da tayi mani bane.


Rike haɓa tayi tace "o naga shashan ci to shike nan zan zaɓa maka kwana nan zata zo zan kira ka sai kazo ku gaisa daga nan sai ayi maganar Auren ku daga baya ko" taɓe baki yayi yace "oho dai ni dai yanzun wuƙa da nama na hannunki Hajiyar mu" tashi yayi ya zauna kusa da Ummi ita kuma sai kallon sa take tana murmushi yace "Ummi na insha Allahu kun kusan samun lafiya kamar kowa da ƴardar Allah.




*A GIDAN SU AYANAH KUWA*


Washe gari da safe kwan ce nake saman gado Amman ba bacci nake ba junior ne zaune tsakiyar ɗakin yana kallon waje da sauri yataso ya faɗo mani saman jiki cikin shagwaɓa yace" uhm uhm uhm Mum ki tashi haka nan ina jinsa Amman ban ce komai ba kuka ya fashe da shi dafe goshina nayi nace "ya sallam wai me kake so ne kaje gurin Ummy mana ka taya ta aiki" tashi yayi ya fita da sauri ajiyar zuciya nayi sannan na sauko daga saman gadon gyarawa nayi sannan na fito daga cikin ɗakin ko da na fito har Ummy tagama girki kallon ta nayi nace "Ummy ina kwana" murmushi tayi tace "lafiya klau kun tashi lafiya ya baƙunta"!? Dariya nayi nace "Alhamdulillah Ummy gashi ko ya zo tamaki aiki" Uhm lallai kam gashi nan yazo yana damuna da surutu ba " dariya nayi sannan nace "lallai kam" tsintsiya na ɗauka na fara sharara gida sallama su Ya jafar naji da sauri na ma yarda da kallona gurin su dariya abun ya bani yarda suka shigo kamar wanda zasuji wani gari tashi tsaye nayi ina murmushi nace "Good morning Ya jafar Good morning Aunty Sadiya" cikin jin daɗi yace "lafiya klau ƴar kanwata dafatan kun tashi lafiya kallon junior yayi yace "my son zo mu gaisa da gudu yazo ya faɗa saman jikin sa yace " Good morning Uncle my Aunty" sama ya ɗaga shi yana jiyowa da shi yace "morning howa are you my son" am fine and you Uncle.


Jin jina kai yayi yace "masha Allah" shimfiɗa masu tabarma nayi sannan kowa yazo ya zauna abinci Ummy kawo muna murmushi nayi nace "Ummy ai ba yanzun muke breakfast ba sai zuwa anjima" sukam su Ya jafar ko tayi ba'a masa ba ya sanya hannu yana ci har kusan cinyewa sai da Ummy tace "Haba jafar yanzun kai ko kunya bazakaji ka cinye abinci ba da ƴata ba kuma gata da ciki eye"!? Sosa kansa yayi da key din babur din sa yace"to Ummy ba komai take ci ba fa"hararar sa Ummy tayi tace "wai haka ne ƴata"!? .



Cikin jin kunya tace "Eh Ummy kunu da kosai nasha yanzun sannan muka fito" murmushi tayi tace "Alhamdulillah kace ci kanka" gyara zama nayi nace "to yanzun zan baku labarin tafiya ta ƙasar india............



⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_Love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉


*ALLAH SARKI MAMAN SUHAILA ALLAH YA JIKANKI DA RAHAMA TARE DA IYAYENA DA DUKKAN MUSULLMI BAKI DAYA YA GAFAR TA MAKU YASAN ALJANNAH CE MAKOMAR KU* 😭😭😭😭😭😭😭😭


*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Call me or Whatsapp me 08066268951
Or 09022823910


_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 21&22 __________*

kowa sai yayi shiru yana kallona gyara zama nayi nace "lokacin da muka koma gida ni da su Ya jafar da hamra dama gaba na yana faɗuwa Amman sai ban sanadar da Ya jafar ba saboda ko na fada masa bazai yarda ba haka na wuce cikin ɗakina gurin dirowa na tsaya ina kallon ko ina daga cikin ɗakin ajiyar zuciya nayi sannan na buɗe kofar dirowa ƙasan kayana na ɗauko kuɗadi na zasu kai dubu hamshin na sanya su cikin aljihu sannan na kwanta.


Misalin Karfe ukku na dare gari yayi duhu sosai ga iskan hadari yana kaɗawa, gari yayi tsint bakajin motsin komai sai na tsuntsaye Ayanah ce Kwan ce take tana bacci cikin bacci taji ihu a waje afargiget ta tashi zaune amman ihun adai dai window yake fitowa tashi tayi tazo dai dai window leƙawa nayi banga kowa ba, kuma ihun karuwa yake da sauri fito daga cikin ɗakina part din Yayana na shiga sai dai na sai mesh suna bacci jiyowa nayi nafita daga cikin ɗakin fito wa nayi tsakar gida ahankali ahankali na buɗe kofar gidan leƙawa nayi naga ko lafiya ina ta dube duba can na hango wata mata da tsohon ciki, dafe take da cikin agajiye ta gaji sosai, salati na fara da gudu naje gurin taimakon ta har na rike hannunta kawai sai naji halben bindiga,


Hankalin na ya tashi sosai rike nake da ita har zamu shiga cikin gida kawai sai dai na bi bayan gidan gudu muke bana wasa ba sai da mukayi nisa sannan na tsaya ina nisa nace"Baiwar Allah daga ina kuma meya ke faruwa da ke?ban rufe baki ba kawai sai naga ta dursune kasa tana nisa sosai nakuda ce ta taso mata zangu zangu cije baki take tana yarfe da hannu ita kuwa hawaye ne suka zubo mani cikin tausayawa nace"sannu Baiwar Allah haihuwa ce zakiyi ko gashi ni yarinya ce ban san ya zan taimake ki ba,


Murmshi tayi mata mana girgirza mani kai sannan ta cigaba da nisa .


Wasu manya manyan yan ta'ada ne suka zagaje mu wata irin dariya suka fashe da ita zaro ido nayi jikina ya fara rawa sai na fashe

Please Login or Register in order to submit comment