Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah na innalillah wa inna lillahi raji un waya ya ciro ya kira Ya jafar ya faɗa masa abun da yake faruwa sannan ya kira Fauzali ya sanar da shi har yamma tayi babu labarin ta .


Bayan sati ɗaya da sace Ayanah hankali family biyu tashe kowa cikin damuwa an cikin haka Aryan ne da Ummi da Hajiya kakus da Aunty fadima da Alhaji Zayyanu, da Alhaji Ahmad da Uncle musa sai su Daddy da Uncle da Alhaji bature da Ummy da Mommy da Maa da Ya jafar da Halima Amrha da byaiha sautin kukan Aryan kawai ke tashi cikin falon sai lallashin sa ake Hajiya kakus tace "haba dai Aryan kai fa Namiji kayi haƙuri mana yanzun Addu'oi kala kala za'ay mata".



Cikin kuka yace "yau fa sati ɗaya fa daga naje nadawo ace an sace Ayanah sai kace leda gashi mai gadi yana asibiti be da lfy sun buge sa taya hankali na zan kwanata Hajiya? Ana cikin haka sai sukaji anyi sallama gaba ɗaya suka zubo mani kofa ido wata mata ce da wani saurayi ne suka shigo cikin parlour Sai wata irin haɗaɗin ƴar budurwar da sauri Aryan da Hajiya kakus da Ummi da su Alhaji Zayyanu suka miƙe tsaye Aryan yace "Fannahhhhh"!!!! Da gudu tazo rungume Aryan ta saki kuka mai ban tausaya tana shafar fuskar sa tace"Yaya Aryan dina "Shima rungume ta yayi sosai yace "ina kika shiga ne suka waɗan shekarun"!? Zauna na baku labarin abunda ya faru " gaba ɗaya suka zauna saman kujera sannan tace "lokacin da ina daki kwan ce gashi mararta ciwo take ina rufe idon na kawai sai naji muryar Ya Hisham yana waya da mijina sai na ƙara kashe kunna naji yana cewar yanzun lokacin da ya kamata ace Fannah ta mutu ne saboda dukiyar ta ko" yace "tabbas nima abun da nake so kenan ni dama ba son ta nake ba kudin ta nake so hankalina yayi mugun tashi haka suka gama waya sannan ya kwanta kusa da ni yana tunanin ta ina zai fara wa har bacci ya ɗauke sa ni kuma wani irin tashin hankali da fargaba ya shige ni ban san lokacin da na tashi zaune ba na sauko daga saman bed wadirof na buɗe na kwaso dukiya ta da wayoyina da komai nawa na saka cikin jakata kwana zaune nayi tunda da nagama sallah Asuba nace masa zanje asibiti be ce komai sai yace kada naji ma to da sauri na gyara na fita bayan na fita ne fa aka biyo ni gudu nake har na fita cikin gari naje kaduna har dai Allah ya haɗa da wata yarinyar ita ce muka sha wahala tare ajiyar Zuciya tayi tace, Doctor basu labarin abunda ya faru.



Gyara zaman sa yayi yace' to lokacin da nazo wuce sai naga wannan baiwar Allah shine ni kuma na taimake saboda naga akwai alamar rai atare da ita kuma naje da ita ƙasa London akayi mata magani kuma ta bani labarin abun da ya faru da ita har da jaririn da ta haifa" Allah sarki Allah ya saka maku da Alkhairi ashe har yanzun akwai mutane na ƙwari"!?wlh kuwa sannan Hajiya kakus ta sanar da su abun da yake faru" Fannah tace "wlh wannan abun ba kowa bane face Ya Hishima tare da Mommyn sa" Da sauri Aryan ya tabbas nima wallahi yanzun nayi tunanin haka lallai sai ya gane be dawayo..


Jijiyoyin jikina gaba ɗaya ji nayi sun daina mani aiki ko ina ya tsaya cak hatta kwakwalwa ta ta tsaya da aikin jikina yayi bala'in saki ko kwakwkwan motso na kasa saki saboda tashin hankalin da nake ciki har ta abun da idona suke ganin mani wato su Mommy da Hisham sune sukayi kid napping dina abun da nakejin labarin su wato ƴan kid napping yau nice aka ɗauke gani da ciki ƙarami innalillahi wa inna ilaihir raji un kuka na fashe da shi sosai ina kallon su.


Dariya suka fashe da ita sosai durkusawa ƙasa kusa da fuska ta yayi yana dariya yana kallona yace "wow matar brother Aryan hhhhh" jikina har yanzun ɓeyi kwakwkwan motsi ba saboda mamaki da tashin hankali wayar sa ya ɗauko ya kira su Aryan lokacin suna tare da ƴan sanda yace"Hhhh mune waɗan da sukayi kid napping Matar ka idan har kana sonta to ka kawo muna miliyan 200 kacl idan kuma gawarta kuke so shike nan hhhhh ya kashe kira dukk abun da yace D. P. O yana jin sa kuma haka yayi location din number sa ya tura wa wani sai gashi ƴan sanda suka shiga neman inda suke tare da Aryan suka je gurin wani ɗan karin gida ne suka gani kuma anan ne abun yake nuna masu Number @360 Suka shigo gurin aka kashe wasu aka kama wasu sannan suka kama su Momyn Hisham da Hisham din aka wuce da su Ayanah kuwa somewa tayi gurin da sauri Aryan ya ɗauke Ayanah ya tafi da ita asibita Doctor yayi binkice ya gano ta ɗauke da ciki na wata biyu kuma babu wata matsala da ta faru da ita sai dai tashin hankali ne ya somar da ita farin ciki ba'a magana Aryan har da sujada yayi ta godiya ga Allah da ya azurtasu da samun ƙaruwa bayan ta fararɗo ne taga su Ummi da Hajiya kakus da Aunty fadima da Maa da Mommy da Amrha azagaye da ita kowa yana cikin farin ciki da sauri ta tashi zaune tana kallon su tace "Ummi Maa Mommy Amrha rungume ta sukayi suna farin ciki sosai Ummi tace "MashaAllah ina taya muna farin ciki da ƴata tadawo gida lfy tare da ƙaruwa" kowa sai cewa yake Alhamdulillah Cikin raɗa Amrha tace "ƴan uwa ina tayi ki farin ciki da samun ciki da sauri tace" gaske ni ke da ciki"!? Tabbas "cewar Mommy da sauri ta rufe fuskar ta cikin jin kunya ......... .


*TALLAHAMMDULILLAH*
*Allah na gode maka daka nuna min ƙarshen wannan littafin nawa ARYAN DA AYANAH lfy*.

_Ya Allah ka gafarta min kurakurai na ka jikan iyayen na kayi masu gafara tare daku nin wanda suka rigamu gidan gaskiya kasa su cikin aljannahar ka mai girma_🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

```Da wanda na sani da wanda ban sani ba mace ko Namiji babba ko yaro in har nayi maku laifi ku yafemank dan Allah``` 😢😢🥺🥺🥺🥺🥺🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


_Sai mu haɗu a sabon littafina mai zuwa RUGAR FULANI insha Allah_
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

_Ina matuƙar godiya da hakuri da kuka yi kuna bibiyan wannan littafin ina matuƙar kaunar ku masoyana_😘😘😘😘😘

*HASSY SOJA ce*

T SOJA
07063617906
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment