Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuka nace"dan girman Allah kuyi mata hakuri ku duba halin da take ciki ku tausaya mata dan Allah, ban rufe baki aka watsa mani wani irin mari har sai da na saki fitsari saboda azaba.


Hhhhhh hhhhh yarinya kin kawo kanki inda za'a kashe ki mu bamu san wani Allah ba bale muyi masa hhhh ita kuwa Baiwar Allah kan jariri ya fito nisa sosai take tana kira sunan Allah.


Dai dai jaririn ya fito daga cikin jikin matar yana kuka inyarr inyarr Murmushi tayi tana cewar Alhamdulillah cikin jin dadi nataso da sauri na rungume jaririn har na manta da bala'in da muke ciki ai kuwa dai dai naji halbe tasss tass....


Kuka jariri yake inyarrrr inyarrrr inyarrrr ni kuma hankali na yana gurin da akayi harbin koda na duba ita an halbe ta a gefen cikin ta wani irin ihu na fashe da shi jikina sai kirma yake sosai kamar mazari rungume su nayi ina kuka ina ce dan Allah ki tashi kada ki bar ni cikin wannan tashin hankalin wayyo Allah wayyo rayuwa ina zan sanya kaina girgiza ta kawai nake dariyar mugunta suka fashe da ita ɗaya daga cikin yan ta'adar ya kira waya sai naji yana cewar "mun aika ta ƙiyama hhhh...



Nisawa nayi sai hawaye masu zafi suka zubo mani, na cigaba da cewar" to lokacine nadawo gida sai na haɗa da Ya jafar yana ganin junior yace sato sa nayi na nuna masa kai har gurin da akayi abun na nuna masa Amman ina ko saurare na biye ba".


Haka muka zo gurin Ummy ita dai bata ƴarda ba sai na fita daga cikin gida to lokacin da na isa bakin titi wasu shagona ne na hango sai na shiga na siyo masa kayan abinci to bayan na fito daga cikin shagon sai na rasa ina zani sai na tuna da key din da ta bani sai nadawo bakin titi to na naga motar wanda aka rubuta ma ARYAN &Fannah Zaunawa nayi ina tunani to yanzun ina zani ne"!? Babu wanda zai bani amsa ina cikin tunani sai wata mata wato Maa tace " yarinya lafiya kike kuka kuwa"!?.


Ɗago jajan idanuwana nayi ido huɗu kara fashe da kuka nayi nace "nima kai na ban san kowa ba bani da kowa sai wannan jariri sai wannan motar da abun da ke cikin ta na manta komai jikina rawa yake sosai cikin tausayawa sai da tayi hawaye ta tace "Allah sarki dama yarona ɗaya kuma yana nos Korean gurin uncle din sa dama bani ƴa mace yanzun gashi Allah ya bani har da jikana to ya sunan ƴatawa da shi mijina "!?.


Share hawayena, nayi nace"Ayanah shi kuma Aryan junior.


Masha Allah tashi idan akwai abubuwan da kike bukata ki buɗe motar ki ɗauka saboda zan ba wani ya wuce da ita gida na acikin gari nan, tashi nayi na buɗe motar na ɗauko laptop da wayoyo guda ukku sai wata babban jaka buɗe jakar nayi na ga kuɗadi sosai har da takardun dukiya kuɗin gida biyu na raba su sannan nace "Maa ga kuɗadi na yazanyi da su to murmushi tayi tace "ok bani kuɗadin na za'a jowa maki su har da gida za'a siya maki da su koda kinzo ziyara.


Murmushi nayi nace "to nagode sosai Allah ya saka da alkhairi miƙa mata jakar nayi ina murmushi buɗe motar tayi tace "shiga cikin motar muje airport yanzun jirgen mu zai tashi zuwa India , shiga cikin motar nayi sannan na sauko da junior bacci kawai yake sosai lumshe idanuwana nayi bacci yayi gaba da ni mafarkin fannah nayi tana mani murmush .......


Haka muka cigaba da rayuwa da ni da junior har ya girma yanzun hakan ma ni ina karatun waƙokin india da yaren india shi kuma junior yana zuwa makaranta inda yadawo gida anyi masa lesson haka muke rayuwa wani lokacin idan na tuna da irin yarda na barku sai nayi kuka wata ranan har da ciwo yake kamani saboda hankalina ba akwan ci ba......



Ajiyar zuciya nayi nace "To kunji labari na" kowa kuka yake saboda irin abun da ya faru da ni da sauri Ummy da Ya jafar suka rungume ni cikin kuka yace "Allah sarki ashe kanwata tashiga cikin wani hali dan Allah ki yafe muna " murmushi nayi nace"ai na yafe muka ban rike ku da komai ba wallahi to kai Yaya jafar kabani labarin kai mana".


Gyara zaman sa yayi sannan ya share hawaye sa da suka zubo masa yace" lokacin da mukaje...............





⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡



_love and romantic story_


_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉



*Dan Allah ku kara mani "afuwa har yanzun dai sai ahankali idan nadawo normal zan kara yawan typing nagode sosai* 😁😁




_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 23&24 __________*

Gyara zaman sa yayi sannan ya share hawaye sa da suka zubo masa yace" lokacin da mukaje gurin da akayi abun tabbas naga alamar anyi haihuwar Amman sai ban nuna maki ba naja wo hannunki mukazo gida sai Ummy tayi fada sannan muka fita daga cikin gidan fitar da nayi nace "ko amafarki kika zo gida na sai na kashe ki sannan na wuce gida koda na isa gida cikin ɗakina na shiga nayi sallah sannan sai ga Hamra tashigo cikin ɗakin kallona take tace "my husband lafiya kayi zaune cikin ɗaki baka fita ba gashi har yanzun Ayanah bata fito tayi muna girki ba"!?.


Kallon ta nayi nace "Hamra ki daina mani maganar Ayanah dan Allah " da sauri tace "my husband kamar ya fa na daina maka maganar Ayanah kuma kanwarka tabba lallai ma" cikin masifa nace"to Ayanah bata nan to ta sace jaririn mutane" wata irin zabura da tayi tace "innalillahi wa inna ilaihir raji un Haba dai lallai kam albasa batayi halin ruwa ba wallahi haba shiyasa kullum tana cikin da damuwa Ashe tunani da take kenan to Allah ya kyau".


Kallon ta nake sosai Amman ban ce komai ba haka muka cigaba da rayuwa sai abun da yake damuna shine ko nazo gida gurin Ummy bata Amsa gaisuwa ta bale ta kalle ni abun yana damuna sosai wata ranar da dare ina cikin ɗaki ina gyarawa kamar an ce na fito sai naga Hamra durkusa ƙasa tana kuka ga bindiga an kara mata wato ƴan fashe ne suka zo muna cikin gida jikina ya ɗauke rawa fito nayi daga cikin ɗaki jikina sai rawa yake na durkusa ƙasa nace "dan girman Allah kuyi hakuri" ɗaya daga cikin su yace" kaso muyi hakuri ko to kabamu dukiyar ka idan har kaso muyi hakuri ba sai mun kashe ka ba.


Nace "kuyi hakuri yanzun ni bani da dukiya ban rufe baki ba sai nayi wani irin mugun mari har sai da na fadi kasa jikina rawa yake sosai abun da ya bani mamaki shine Hamra tace ita ta san inda suke kace ta ɗauko da gudu ta shiga cikin ɗakina sai gata tadawo da takardun dukiya ta ta miƙa masu Amsa sukayi sannan suka fita daga cikin gida gaba ɗaya ni kuma mutuwar zaune nayi ina kallon ta Ajiyar zuciya tayi tace "my husband kaganin yanzun hankalin mu ya kwana ko"!?.


Cikin tashin hankali nace"ke Hamra yanzun abun da kikayi dai dai ne ko"!? Kallon sa tayi tace "to menayi kai yanzun baka son rayuwar mu kenan ko"!? Kasa magana, nayi saboda baƙin ciki da takaici " bayan kwana biyu komai ya lallace ko abinci bamu da Hamra kuwa kullum cikin tashin hankali da bala'i bazan manta wata rana ba da dare na fita daga cikin gida koda na dawo ina ta sallama shiru kamar an ce na shiga cikin ɗakin wani irin tashin hankali na gani Ajiyar zuciya yayi yace "Hamra ce da wani suna fasiƙan ci innalillahi wa inna ilaihir raji un kuka na da shi jin sautin kuka na yadawo da su da sauri tajayo bargo cikin rawar murya tace "Jafar dan Allah ai bata rufe baki ba na watsa mata wani irin shegen mari har sai da taga wuta daga ita har shi dukan su nake kamar me sannan na kira police kafin suzo sai da nayi mata saki ukku nace"dama ashe abun da kike aikatawa kenan sai ga police suka tafi dasu.


Haka na cigaba da rayuwa ta ni ka ɗaye bayan wasu shekara biyu Wata rana na shigo unguwar su Ummy sai Allah ya haɗani da Halima ƴar gida liman nayi mata magana tace naji gurin Baba liman haka ko ankayi naji nasame sa na faɗa masa yace ai ya bani ai tunda sukayi zama da mahaifina sai yace tunda bani da sana'a ya bani babur nayi sana'a har Allah ya nuna mani Auren mu da Halimatu Sadiya "hawaye ne suka zubo mani cikin farin ciki nace"Allah sarki Ya jafar ashe kaga rayuwa ashe Sannu lallai Hamra ni fa tunda kabani labarin nake zargin ta Amman babu komai yanzun komai yazo karshe sallamar bala driver ya katse mani magana shigo yayi har ƙasa ya gaishe da su Ummy da Ya jafar bayan sun gama gaisawa sannan yace "Hajiya ƙarama nazo da ita" nace "to Masha Allah Amman Ummy Ya jafar Aunty Halima ku tashi muje gida wannan gidan kuma a baiwa ƴan gudun hijira su zauna".


Kallona Ummy tayi tace "too har da kayan mu"!? Girgiza mata kai nayi nace Aa Ummy ki bar su muje mayafi ta ta ɗauko ni dama kayana suna da mayafin su gaba ɗaya muka fita daga cikin gida mota muka shiga muka fita daga cikin unguwar gudu yake shararawa saman titi sosai har muka shigo cikin unguwar su Ummy sai kallon gidajin masu kudi suke dai dai gidan yayi horn baki kowa ya saki yana kallon tsarin gidan nai part biyu kowa ne yayi kyau gurin gareji yayi parking fitowa mukayi cikin motar nace "Ya jafar kaga wannan can part din ko"!?.


Ɗaga mani kai yayi yace "eh kuma yayi kyau sosai wallahi" murmushi nayi nace to Masha Allah to na kagane halat malat" da sauri ya kalle ni yace "nagode nagode" girgiza masa kai nayi nace Aa dan Allah ka wuce haka agurina kai fa Yaya na ne fa kiran mai gadi nayi sai gashi yazo da gudu yace"gani Hajiya ƙarama kallon sa nayi nace "key din wannan part zaka baiwa Yaya jafar sannan muka wuce cikin gida da sauri yaje sai gashi yadawo ya miƙa masa key din amsa yayi suka wuce part din su cikin murna Halima tace "Allah sarki ashe nima zan zama matar mai kuɗi"...



Koda munka shiga cikin falon baki Ummy ta saki tana kallon su tace"Ayanah kina jin dadin ki wallahi ban taɓa ganin irin sa ba sai yau" ni dai dariya nake sosai sannan muka zauna saman kujera ajiyar zuciya nayi nace "to Alhamdulillah Ummy ga ki ga Autar ki insha Allahu sati mai zuwa zamu komai can india ban ƙara ba sai naji waya ta na rigging ɗauko wayar nayi daga cikin jaka koda na duba sai naga baƙuwa number kallon ta nake har ta kusan tsinkewa sannan na ɗauko da sallama nace "Aslm Alkm waye" Wata murya ce naji Amman ban gane ba sai naji ana cewar"Amin wslm ƴar nan kin gane ni kuwa"!?.


Murmushi nayi nace "Eh na gane Hajiya antashi lafiya ya jikin Mama"!? Dariya Hajiya Kakus tayi tace "lafiya klau Alhamdulillah dama nakira ki ne naji kuna lafiya"! Ajiyar zuciya nayi nace " Alhamdulillah Hajiya ", Hajiya Kakus tace "Masha Allah Jiki da sauki dan Allah inason ganin ƴar nan"!.



Nace "insha Allah zan shigo Hajiya idan nashigo mota zan kira ki" a bangaren Hajiya Kakus kuwa wani irin farin ciki ta shiga yi tace "too Allah ya kawo ki lafiya" murmushi nayi nace "Amin ya Allah " sannan na kashe wayar kallon Ummy nayi nace " Ummy wallahi wata dattijuwar matar ce na haɗu da su asibity wallahi ɗaya matar iya karta ke abun tausaye sosai idan kika ganta sai ta baki tausaye wallahi"!.


Girgiza kai tayi cikin tausayawa tace"Allah sarki Amman yanzun can zakije ko ki duba ta" Ajiyar zuciya nayi nace "tunani nakeyi kenan Ummy wallahi"Ummy ta kalle ni tace"gaskiya ya kamata acan kinji ganinta Ayanah kinsan zuwa ganin marar lafiya akwai ladah" eh haka ne Ummy insha Allah bari na watsa ruwa sannan na fito........


⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________25&26__________*

Ruwa na watsa sannan na fito daga cikin toilet ɗaure da towel wadiruf na buɗe na ciro baƙar Abaya sannan na ciro bra da pant na sanya bra da pant sannan nasanya Abaya na ɗura mayafi saman kafaɗata turarin masu shegen kamshi na fisa takalmina masu shegen tsini kafin na fito kamshin turarena ya game falon sannan na fito daga cikin ɗakin cikin falo na shigo na iske su Ya jafar zaune saman kujera suna kallon tv da sallama na ƙaraso gurin kallona yayi yana dariya yace "ƴar kanwata wannan wanka haka ko suriki na zai zo"!? turo baki nayi cikin shagwaɓa nace"Uhm Uhm Uhm Allah ni Aa ba wani suriki ni fita zanyi ko Ummy "!?.



Murmushi tayi tace "eh fita zatayi Amman tare da junior zaki ko"!? Turo baki nayi cikin shagwaɓa nace" Allah ni bada shi zani ba gaskiya ni kullum sai na fita da shi ya zauna gida ga Ya jafar nan" girgiza kai Ummy tana kallona tace" Allah ya shirya ki dariya nayi nace 'Amin Ummy na" taku nake guda guda har na kai bakin kofar falon sai najiyo nace " yauwa Ya jafar kaje gurin motocin ka ɗauke ɗaya"sai nadawo Ummy "adawo lafiya Allah ya tsare "Allah yasa ki haɗu dan shugaban ƙasa yace yana son da Aure" Zaro ido nayi nace "Ya jafar baka son nazauna da ku ko Himm sai nadawo fita nayi daga cikin falon tafiya nake guda guda har na ƙaraso gurin bala driver nace "tashi muje unguwa kallon junior nayi da gudu ya zo yace "Mum ina zakije"!? Gurin allura zanaje kaje gurin Uncle zakuje shan Ice- cream kaji ko" da gudu ya wuce cikin gida ni kuma nace "wan can mota bleak ita zamuje da ita " bala driver ya tuƙa motar ya fito da ita sai na kara sa na shiga cikin motar muka fita daga cikin gida gaba ɗaya tafiya muke a cikin mota waya ce na ciro daga cikin jaka kiran Hajiya nayi rigging ɗaya tayi sai ta ɗauka tace " Aslm Alkm ƴar nan kun taso ne"!?.


"Eh Hajiya ga bala driver sai kiyi masa bayani" miƙa wa bala driver wayar nayi ina kallon sa Amsa yayi yace "Hello Hajiya"_ a can ɓan garen Hajiya Kakus tayi masa bayanin inda za'a kai mu sannan ya kashe wayar ya cigaba da tuƙin motar ni dai ina kallon titi sai dai naga ya shiga cikin wata unguwa mai shegen kyau sosai wani irin hadaɗin gida yayi horn da sauri nace "kai bala driver wannan gidan ne kuwa kar mushiga wanda bashi ne ba fa"!? Murmushi yayi yace "Hajiya ƙarama shi wanda akayi mani bayani" shiru nayi ban ce komai ba haka ya shiga cikin gidan dai dai gurin motocin yayi parking wata irin faɗuwar gaba nake ji da sauri na dafe kirjina ina karatu addu'oi zuciya sai buguwa take lumshe idanuwana nayi nace "wai me yake shin faruwa da ni ne"!?.



ƙarar buɗe kofar motar naji da sauri na buɗe idanuwana ina kallon bala driver yana cewar "Hajiya ƙarama mun iso fa" ok fitowa nayi daga cikin motar gyara zaman a bayata nayi na cigaba da tafiya cikin gidan na shiga na su Hajiya kakus da Aryan Ummi na zaune kusa da shi kallon Hajiya kakus yayi yace"Amma bari na shiga ciki na watsa ruwa sai na fito ɗaga masa kai tace "mijina dan Allah kada kaje kayi zaman ka ga baƙuta ta kusan iso kaji ko"!? taɓe baki yayi yace"bsƙuwar da take muna rowar ganin ta gaskiya baƙaramin so kike mata ba sannan ya fuce daga gurin bayan tafiya sai Hajiya kakus ta girgiza kan can sai taji, K'was K'was K'was k'arar takalmin na ya karad'e cikin falon baki ta saki tana kallon kofar falon kamshin turare na ya fara game falon bakina ɗauke da sallama tunda na shigo Hajiya Kakus take kallona fuskar ta ɗauke da murmushi tace"oyoyo ƴar nan sannu da zuwa" murmushi nayi nace " yauwa Hajiya na sa me ku lafiya" tasowa tayi tazo ta rike hannuna taja sai gurin kujera ta zaunar da ni tace "lafiya klau ya su Umma nake suna lafiya ko"!? Lafiya klau suke ita ma tace a gaishe ku".


Koda najiyo Ummi tana kallona tana mani murmushi nace "lah Mama Sannu da jiki" Hajiya Kakus tace " ai batajin mekike faɗa sai kin rubuta mata a takarda" da sauri najiyo ina kallon Hajiya Kakus tace "kwarai ma kuwa ƴar nan" wasu hawaye ne suke zubo mani cikin tausayawa nace "Hajiya wannan wane irin ciwo yake damun Mama"!? Ajiyar zuciya tace "lafiya klau muka kwanta da ita koda mukatashi da safe wannan ciwon ya same ta" shiru nayi ina tunani nace"to anyi mata maganin Hausa kuwa"!? Girgiza kai tayi tace "Aa gashi yanzun shekaru da yawa muna amfanin da na asibity".


Girgiza mata kai nayi cikin tausayawa nace"Allah sarki to yanzun me take son taci"!?.....


Beru da takarda Hajiya Kakus ta miƙa mani amsa nayi na rubuta mata kamar"Mama mekike son ci yanzun" aza mata takardar nayi murmushi tayi sai ta rubuta kamar " duk abun da kika dafa zan ci" miƙa mani tayi sai amsa na karata sai nayi murmushi nace "Hajiya tana cin Jallop kuwa" dariya tayi sosai tace "kamar kin sani tashi muje na nuna maki kitchen sai kiyi girki, tashi mukayi tare muka shiga cikin kitchen........




⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page _________27&28 __________*

Baki na buɗe ina kallon haɗuwar kitchen din green ne da fari yayi kyau sosai kitchen din cike yake da kayan aiki Hajiya Kakus tace" yauwa ƴar nan kinga komai akwai cikin kitchen dinan sannan akwai naman kaji acikin farjin kinga gurin magi nan ko wane iri sannan idan baki gane wani abu ba ki tambaya ni zan fada maki" to Hajiya insha Allah ficewa tayi daga cikin kitchen din, ni kuma na ɗauko tukunyar girki na wanke ta sannan na kunna gas din sai na ɗura tukunyar saman gas ruwa na zuba ciki na rufe ajiyar zuciya nayi ina kallon kitchen kallon gefena nayi sai naga buhun shimkafa karasowa gurin nayi.


Shimkafa na zuba a cikin ruba sannan na durkusa ƙasa na buɗe kofar dirowar sai naga su tarrugu da tattasai gefe ɗaya su Ali-no-moto da curry chicken da onga da Ami etc a gurin kowane sai da na ɗauka sannan nayi markaɗai kayan miya sannan ajiye sa gefe kusan minti sha biyar ko ina ya ɗauke kamshin girki Aryan ne zaune saman kujera yana kallon madubi kamshin girki ya dake hancin sa sai yaji cikin sa na juyawa dafe cikin sa yayi sannan ya fito daga cikin ɗakin yana kalle kalle hango Hajiya Kakus ce Zaune saman kujera tana kallon tv karasowa gurin yayi yace "uhm Hajiya kamshin girki nake ji wallahi ko girki kinkayi"!? Kallon sa tayi tana murmushi tace " Aa wallahi yarinyar da nake faɗa maka to ita ce take ma Ummar ka girki" Zaro ido da sauri ya jiya ya tafi kitchen Ayanah kuwa tana tsaye sai tayi zuciyar ta tana bugawa da sauri sauri kula ta ɗauko zata fita waje sai ga Aryan ya shigo cikin kitchen din karo yayi da ita tunda ƙasan ta har saman kirjin ta yake kallo itama kallon kirjin sa take jikinta sai ya ɗauke rawa.


Kamar an ce su haɗa ido ɗago idanuwan ta tayi sai sukayi ido huɗu da shi sosai wata razana tayi Zaro ido yayi jikin sa na rawa ya ɗago hannun sa yana nuna ta da yatsan sa haɗa baki sukayi gurin ɗaya suka ce"ke" kai wa ya kawo ka anan gidan"!? Dariyar rainin hankali yayi yace "waya kawo ni wannan gidan to ke gidan ku ne"!? Ni ba gidan mu bane Amman ai gurin matar gidan nazo ko"!? Eh lallai kam to ni ɗan gida ne ko kina da magana ne" murguda masa baki tayi tace "bani da magana kuma ai ba gurin kanazo ba balle" rashin kunya zakiyi mani kenan karo na biyu ko"!? Oho wannan matsalar ka ce ba tauba" ke a tunanin ki na manta da marin da kikayi mani ne"!? Dariya tayi sosai sannan tace" to kai fa ai ban manta ba lokacin da katashi sace mani yaro ba" zai mare ta da gudu ta fita daga cikin kitchen din sai kusan kaiwa gurin su Hajiya Kakus sai ta gyara tafiyar ta ƙasowa cikin falon tayi.



Bakin ta ɗauko da sallama da sauri Hajiya Kakus ta miƙe tsaye tana kallon ta tace "ke ƴar nan har kin gama girkin ikon Allah gaskiya yarinya duk wanda ya Aure ki ya jidaɗi wallahi ina ma ace zaki Auri jikana dana fi kowa jin dadi " murmushi tayi tace "Aa ki bar shi na ajiye maku saman dining table ta ajiye kular abincin Zaunawa saman kujera kusa da Ummi tayi sunkuyar da kanta ƙasa tayi jikin ta sai rawa yake Aryan kuwa murmushin mugunta yayi ya buɗe farjin lemon juice ya ɗauko sannan ya fito daga cikin kitchen falo ya shigo ɗago idanuwan ta tayi sai sukayi ido huɗu da shi da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun ta karasowa gurin yayi yace"uhm gaskiya baƙuwar ku akwai kunya" wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya tace "wallahi kuwa akwai shi sosai ko har kunyi maganar ne"!? Uhm eh har ma ta amin ce da maganar mu da sauri Hajiya Kakus tace "kai Aryan ta Amince da maganar Auren ku kai Alhamdulillah" da sauri ta ɗago idanuwan ta sukayi ido huɗu da shi kashe mata ido yayi yana murmushin mugunta har ta buɗe baki zatayi magana ya katse ta yace "babu komai ai nasan kunyar su kike ji ki kwantar da hankalin kinji my love" Zaro ido tayi ta kalle Hajiya Kakus ta kalle Aryan Hajiya Kakus tace "Masha Allah ke ƴan nan ki bani number Umman ki zamuyi magana " wani irin faɗuwa gaba Ayanah take ji cikin damuwa tace "zan turo maki ita yanzun zanje gida saboda akwai wata hidimar da zanyi" kallon ta Hajiya Kakus tayi tace "hidima kuma ƴar nan" eh Hajiya wata ƙawata ce to Yayan ta za'a daura ma Aure gobe jibi zamu komai india insha Allahu" cikin mugunta yace " kai har india zakuje to yanzun ya maganar Auren mu gashi ban son ajima.


Gaskiya Hajiya Kakus Uhm Uhm Uhm dariya Hajiya Kakus tayi tace "kaji jairin yaro yanzun dan baka da kunya agaban mu kake wannan maganar"!? Cikin shagwaɓa yace uhm Allah da gaske nake Hajiya Kakus din mu Allah sarki my life sister da tana kusa da yanzun ta sanya bakin ta hawaye ne suka zubo masa ga kumatun sa da sauri Hajiya Kakus ta goge masa hawayen tace " kayi hakuri komai yana da lokaci idan tana raye Allah ya baya na muna ita idan kuma ta rasu Allah ya jikan ta Ayanah kuwa tana jin su Amman bata ce komai ba a cikin zuciyar ta mamaki tana tambayar kanta wace ce "my sister din sa kuma me ya sameta"ɗago idanuwan ta tayi tana kallon su rungume sa taga Hajiya Kakus tayi tana lallashi sa tana cewar Aryan kazamo mai

Please Login or Register in order to submit comment