Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da sauri nace"Mijina kuma Hajiya to ai banyi Aure ba " dariya tayi tace "yanzun dai gashi ki fada masa sunan unguwar, miƙa masa wayar tayi tace "Amsa zata yi maka bayanin unguwar "cikin jin haushi Hajiya Kakus ta haɗa shi da ƴar kauye tsaki yaji saboda tsabar haushi kallon sa tayi tace "kai lfy kakeyi wa mutane tsaki"!? Girgiza mata kai yayi yace "oh Hajiya babu komai fa ina tunanin inda zani je ne taɓe baki tayi tana kallon sa tace "to Allah ya kyauta yanzun Amsa, amsar wayar yayi ya kara a kunnen sa bace komai ba kuma tuƙin motar yake, tunda taji anyi shiru tasan shine ita bace komai ajiye wayar tayi tana hararar ta dukk abun take Ya jafar yana kallon ta da mamaki sannan ta ma yarda tana murguɗa baki murmushin gefen baki yayi yace "ke wai baki iya gaisuwa bane haka zamuyi Aure baki iya gaida miji ba" gaban ta yace rasss rasss cikin jin haushi tace "Allah ya sauwaka ni zan Aure ka wlh sai dai na mutu banyi Aure ba" hhhh lallai kam yarinya Aure kamar anyi sa ne ki zubo ido ki gani,.


Tabe baki nayi nace "kai dai kasani idan na bari maka ƙasa fa ai shike nan ko, murmushi yayi yace "ke kika ganin haka komai ai dole ki dawo ƙasar ba, da sauri na faɗa masa sunan unguwar da gidan na kashe wayar ina jin zuciya ta tana bugawa da sauri sauri dafe ta nayi ina karata addu'oi dukk wanda tazo.


Ya jafar ne ya dawo kusa ni ya zauna yana mani magana kasa kasa yace "Aa ban san ƴar Auta tana da faɗa ba sai yau da ke da waye"!? Turo baki nayi sai hawaye sannan na bashi labari komai murmushi yayi yana kallona goge mani hawaye yayi yace "ki ƴarda mana kin ga mahaifiyar sa cikin wani hali to Allah ya tsare idan ya Aure wace bada da mutumci ta wulaƙanta mahaifiyar sa kuma lokacin kinje ganin to ya zakiyi"!?.


Bata san lokacin da ta miƙa tsaye ba ta ta rufe ido ta fara masifa tana cewar "tabb ai wlh da ranar anyi kisan kai dan wlh wuƙa zan ɗauko na suka mata himm ai ba zan iya bari wani ya wulaƙanta ba bale a gaba na"ai kuwa tana buɗe Ido suka ido huɗu da Ummy da Halima sai tajiyo da sauri zata zauna shi kuwa Ya jafar kyalkkyalwa da dariya yayi sosai sannan yace"uhm cigaba mana"turo baki tayi Cikin shagwaɓa alamar taji kunya"Kallon ta kawai yake yasan kishine yake damun ƴar kanwar sa.



Murmshi yayi yace "to tunda kina sonta ko ki amince kawai kinga wata rana dole ki so shi" turo baki nayi nace "to ai shima ba sona yake ba bale"sai da tashi sakin dariya sai yace "zaku so junan ku insha Allah dukk abun da suke Ummy na kallon ƴan ta tana jin dadi har cikin zuciyar ta kwanciya tayi saman jikinsa tana murmushi yace "kin amince ko ƴar Auta"!? Tace"Ya jafar ni fa ban tashi Aure ba yanzun Amman ko saboda mahaifiyar sa ai zanyi" dariya yake sosai yace "Aa waye ya faɗa maki baki isa Aure ba"!? Har ta buɗe baki zatayi magana sai sukaji Sallama Hajiya Kakus tana kallon su Ummy tace" Aa maraba kun da zuwa ko karaso ciki mana.



Runtse idanuwana nayi kamar mai bacci karasowa Hajiya Kakus tayi tace "yauwa dafatan nasameku lfy dai ko"!? Lafiya klau Alhamdulillah kujera da ke kallon mu ce ta zauna tace "Aa ina jikan yar tawa ban ganta ba kallona Ummy tayi tace "Ayanah! Ayanah!! Uhm ki tashi ga bakuwa nan tazo, A hankali na buɗe idanuwana sai naga ita ɗaya ce tasowa nayi nazo inda take nace"Sannu da zuwa Hajiya, murmushi Hajiya kakus tayi tace " yauwa ya gidan" lafiya klau tashi nayi na wuce kitchen nayi na ɗauko mata lemon da ruwa masu sanya na ajiye mata saman dining table nace "Hajiya gashi nan ki sha dan Allah".


Murmushi tayi cikin jin dadi tace "to ki tashi kije yana waje be shigo ba" junior ya fito daga cikin ɗakina da gudu Mum! Mum!! Mum!! Natashi daga bacci saman jikina ya faɗu yana cewar "uhmm uhmm Mum baki mani abun ba" ɗaukar sa nayi nace "junior kaci ka rigima fa to baka gaida Hajiya ba" da sauri yazo gurin ta yace "sannu da zuwa aljiya kinzo klau" dariya kowa yasaki saboda hausar sa tace"lafiya klau Alhamdulillah ya karatu"!? Yau kwana ɗaya biyu ukku ban je ba sai muje garin mu" baki kowa ya saki yana kallon sa da mamaki dariya tayi tace "Masha Allah yanzun dai gobe zaku komai ko"!? Ɗaga mata kai yace "yes Ajiya" gyara murya Ya jafar yayi yace "my son ji waje kace uncle ya shigo ciki, tooo da gudu ya fito daga cikin falon waje ya fita yana dube duba can ya hango sa tsaye yana latsan waya da gudu yaje gurin sa yana cewar uncle! Uncle Aryan yaji muryar da be mantawa da ita da sauri ya ɗago idanuwan sa yana kallon junior shima junior shi yake kallon ihu yayi yace "lah uncle gidan mu yeeeee yeeee mai yarda wayar sa yayi cikin aljihu sai ya buɗe masa hannu junior da gudu ya faɗa saman kirjin sa yana murna yace "Uncle nayi kewar ka fa" dariya Aryan yayi har sai da faran haƙuran sa suka bayana yace "nima haka my son dafatan kana lfy Mum dai bata dukkan ka ko"!? Lamewa yayi saman jikinsa yace "klau Aa Mum na bata dukkana Uncle kuyum da kuyum sai ta siyo mani kayan dadi har da chacocolate da komai da komai, Aryan yace "kai My son da gaske"!?.


Junior yace "wallahi kuwa Uncle yauwa an ce wai kashigo cikin gida" to muje ko haka suka shigo cikin falon da sallama da sauri na ɗago idanuwana ina kallon sa ajiye junior yayi yazo har gaban Ummy ya duƙa cikin ladabi yace "ina yini Ummy ya gida"!? Murmushi Ummy tayi cikin jin dadi har zuciya take jin son Aryan tace "lfy klau yaron kirki ya Ummana ka da jiki"!? Alhamdulillah taji sauki Umma kunyar Ummy yake ji.


Ido huɗu mukayi da shi murguɗa masa baki nayi shi kuma harara ya watsa mani wani irin murmushi yayi yace "Aa babban Yaya kuna lfy"!? dariya Ya jafar yayi hannu ya miƙa masa sukayi musabiha sannan yace"lfy klau Abokina ya gida ya mai jiki"!? Alhamdulillah sannan ya gaishe da Halima itama ta amsa tana murmushi tashi yayi ya koma kusa da Hajiya kakus ya zauna kallona Ummy tayi tace"Ayanah baki gaishe da Yayan nanki ba fa" Turo baki nayi nace"ni fa Ummy ba zan iya gaida wannan abun ba to" Baki ta saki tana kallona Ya jafar kuwa dariya yake kasa kasa murmushi Aryan yayi yace"Umma rabu da ita kawai dama haka take mani rashin kunya" Ummy tace"Ayanah baki ji bane" Cikin shagwaɓa nace"kai Ummy ni fa Yayar sa ce ni wlh shiyasa nake son komai india gurin Maa.


Ummy tace"Auta ta yaushe kika iya rashin kunya yanzun wannan shine kanen ki yau naga ikon Allah " Dariya Hajiya tayi tace "rabu da su muyi abun da ya kawo mu Hajiya" murmushin 'karfin hali Ummy tayi tace "to kallon mu take, gyara murya Hajiya kakus tayi tace "dama zuwa nayi muyi maganar Auren wannan yaran "daga ni har shi sai gaban mu ya faɗi" da sauri har na tashi zan wuce Hajiya tace dawo ki zauna" jikina babu kwari haka nadawo na zauna da mun haɗa ido da shi sai ya watsa mani harara yana magana kasa kasa yana cewar dukk ke ce kika jimani ina zaman zama na, murguɗa masa baki nayi nace"ko kunya bayaji ya kwaso kafafuwa gurin neman Aure na mugu kawai mtsss , dukk abun da muke Ya jafar yana kallon mu ta cigaba da cewar"yanzun kin ga shi ba ma zauni bane kullum yana gurin ball sannan Ummin sa bata da lfy kin ga ni tsohowa ce yanzun ya kamata ace nazauna na samu hutu sai da rashin lfy ta ne yasanin kullum ina gurin ita da zama ko ƴar aiki na ɗauko wulaƙanta ta suke da sauri nace "wulaƙan ta ta kuma to shi wannan ba zai ya zama gida bane to wai meyasa mutane Nigeria, basu da imani ne" Himm yace "ke dai yanzun zaki komai da zama gurin ta ba kin kuwa muhuta da ɗauko wata ƴar aiki Ku rufe muna baki ba da ku ai magana ba cewar Ya jafar ta cigaba cewar to shine ranar da taji gida sai suka haɗa suka fahimci juna shine nazo da kai na na nema masa izzini zuwa gurin ta" Wani irin farin ciki ne ya mamaye wa Ummy Zuciya tace " to yanzun ba zan ce maku komai ba saboda Ayanah ba'a gurin na take zaune ba a ƙasar India ne ni kuma nayi maku alƙawari zan shige maku gaba agurin maganar Auren su ni dai mahaifiyar ta ce kuma na bashi ita halak malak...........



*HASSY SOJA*🌹✍🏻:


07063617906


⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡



_love and romantic story_


_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________37&38__________*


Dariya farin ciki Hajiya Kakus take har da hawaye sai ta daga hannunta sama tana cewar Alhamdulillah Allah nagode maka Ashe zan ga Auren Aryan kullum abun nake kwana da shi nake tashi sai ta mai da duban ta ga Ummy tace "to yanzun menene abun yi za'ayi da dangin ta"!? Ajiyar zuciya tayi tace "yanzun dai kina da number Ayanah na ko to kada ki samu damuwa Ayanah tashi ce ko bayan mutu ta ne" da sauri mukace "dan Allah Ummy ki daina maganar mutu plss.


To shike nan Allah ya tabbar muna da Alkhairi mu zam wuce sai dai ko zuwa anjima ko gobe yadawo gurin fira su kara fahimar juna cewar Hajiya Kakus tana murmushi ita ma Ummy murmushi take tace "to sai ya iske mu can India tunda nasan ba zai rasa zuwa ba kallo ɗaya tayi mani ta fahimci ina cikin damuwa sosai sai dai bata nuna mani komai tace "Ayanah ki bashi address din gidan sai ya iske mu can sai ayi komai agama.



Junior jeki ɗakina ka dauko mani karamar jakata to da gudu ya wuce part dina sai gashi yadawo yace "Mum gashi"Amsa nayi nace ticket na bashi nace "je ka baiwa uncle shi" da sauri ya je ya haye saman kafafuwan sa yace "Uncle gashi kuma zan bika kaji Uncle.



Murmshi yayi kada kadamu zan zo naje da kai unguwa kaji ko"!? To chike nan Uncle.


Tashi Hajiya Kakus tayi tace "to muka zam wuce sai Allah ya kara haɗa mu " tashi Aryan gyara rigar sa sannan yaja hannu junior yace "Umma sai anjima" murmushi tayi tace "to ɗana sai iske mu can ko"!? Sosa kan sa yayi da key rakiyar Hajiya Kakus Ummy tayi waje sannan karaso gurin Ya jafar sukayi musabiha dai dai kafar Ayanah ya take ihu ta saki tana cewar "wayyo Allah kafana wayyo ya take mani kafana hawaye ne suka zubo mani sannan yace "ke yaushe na take ki"!? Turo baki nayi nace "yanzun nan wlh sai na rama ko ba yau" junior yazo gurina da sauri yace "Mum wane ne ya dakike na rama maki"!? Dariya Aryan yace"ikon Allah yanzun ni zakiyiwa shairi innalillahi".


Girgiza kai Ya jafar yayi yana kallon su shi soyayyar su har dariya take bashi kallon su kawai yake Aryan yace"na tafi"har ya kusan kai kofar fita sai ya jiyo yana kallona wani irin murmushi yayi yace "innalillahi Ya babba kana ganin zan fita Amman bata taso ta rake ni ba" murmushi yayi yace "to my kanwata tashi ki raka mijinki" turo baki tayi cikin shagwaɓa tace "babu inda zani ai bani nace yazo ba" haɗe rai yayi yace "oyah tashi kije bana son masu fa" tashi tsaye nayi ina bubugu kafafuwa na haka na bi bayan sa sai da muka fito waje sannan nace"malam kada ka ƙara zuwa inda nake tau" taɓe baki yayi yace " ai tunda abani sadakar ki ai shikenan zaro ido nayi nace "wa ce ce abada sadakar ta ni wlh kasan nafi karfin ayi sadaka da ni malam ka ɗan gyara maganar ka ai kai ne kana ce dole sai ka Aure ni kuma kada ka ƙara zuwa inda nake "taɓe baki yayi yace "wannan ke ta shafa ƴar kauye da ke mezanyi da ƴar kauye" cikin jin haushi nace"naji ni ƴar kauye ce kai kuma fa wa yasan daga inda aka fito kuma ai ƙauye abun son dukk wanda baya da shi to ɓeda asali" ransa yayi mugun ɓace maganar da ta faɗa masa ɗaure fuskar sa yayi kamar ba shine yake dariya ba cikin tsawa yace"ke ƴarinya bari kiji ni babu abun da zanyi da ke dube ki ɗan Allah kuma abun da ya faru tsakanina da ke bawai na manta ba ne Aa ina sane da ke kuma ki sani ni ARYAN sai na nuna mani ni waye kuwa a fusace ya bari gurin saboda idanuwan sa sun rufe yana iya mata dukkn tsiya" taɓe baki nayi nace "can da su gada ba joyawa nayi nakoma cikin gida dukk abun da suke su Hajiya na kallon su Amman sun ɗauka fira ce suke sai murmushi akawai suke sosai sannan sukayi sallama suka komai gida.



Ummy ta koma cikin gida saboda shirye shiryen tafi suke ni dama nagama haɗa kayan mu kwan ce nake na ɗauko waya na kira su Maa bayan mun gaisa nace"Maa gobe insha Allah zamu dawo sannan kuma ki cewa Bhaiyah ko na kira sa bata zuwa " da sauri tace"da gaske my Angel" dariya nayi nace"Allah kuwa maa ina daddy"!? Ya fita tunda zu to shike nan Allah ya kaimu lfy idan zaku taso ki kirani sai na turo maku driver ko" ok babu damuwa insha Allah sai na kira" kashe wayar nayi sannan na kira Aina'u na sanar da ita sannan na kashe wayar gaba ɗaya gyara kwan ciya nayi ina tunanin abun da Ummy tace wai ta bashi ni ban san lokacin da kuka yazo mani ba.


Har bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita bata falka sa sai kusan 6 saura da sauri ta sauko daga saman gadon toilet ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito daga cikin toilet tana tsane ruwan jikinta karasowa gurin junior tayi ta ɗauke sa ta shiga cikin toilet ta watsa masa ruwa Sannan ta fito da shi dama ta haɗa masu kayan su gurin ɗaya Sannan ta buɗe jakar ta ciro masu kayan da zasu sanyawa ko da ta dubi junior har ya koma bacci kayan ta, ta saka Sannan tagabar da sallah bayan ta gama ne ta ɗauko wayar ta kuna kiran Bala driver, tayi sanar da shi zuwan su India sannan ta kashe wayar fitowa tayi daga cikin ɗakin,, ɗakin Ummy ta shiga da sallama lokacin Ummy na zaune saman sallahy shafe addu'ar tayi sannan tace "Auta har kun tashi"?.


Murmushi nayi nace"ina kwana Ummy wlh kuwa dama zuwa nayi na sanar da ke har mun gama Shiryawa ku ne kawai muke jira saboda ko da zamu isa dare yayi sosai har ta buɗe baki zatayi magana sai ga Ya jafar ya shigo cikin ɗakin ya gaishe da Ummy Sannan Ayanah ta gaishe da shi yace"Mu dai har mun gyara Ummy dariya tayi tace "to sai ku ce ni ce kawai kuke jira " murmushi mukayi Sannan nace"Su Aina'u zasu shigo yanzun bari na tashe da junior dama nayi masa wanka fita nayi daga cikin ɗakin na wuce part dina.





A GIDAN SU ARYAN


Washe gari kwan ce yake saman gado maganar da su sukayi itace take dawo masa a kunne ajiyar zuciya yayi sosai tashi zaune yayi ya sauko daga saman gadon toilet ya shiga ya watsa ruwa sai da ya kusan awa ɗaya Sannan ya fito daga cikin toilet din tsane ruwan jikan sa yake da towel gurin madubi yayi tsaye yana kallon fuskar sa ajiyar zuciya yayi Sannan yaje ya buɗe wadiruf jallabiyar ce ya ciro ruwan zuma ya saka Sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu shegen kamshe Sannan ya fita daga cikin ɗakin.



Aryan ne zaune saman kujera yana hutawa ringing din wayar sa ya dawo dashi bakuwar number ya gani batare da yayi tunanin ba ya dauka ya kara ga kunne shiru yayi yana sauraro mai magana.


A can gefen kuma zazzaune suke saman lafiyayen kujero wani kyakkyawan balarabe ne zaune gefe sai wani kyakkyawan mutum Alhaji Zayyanu mai motoci kenan ,


Alhaji Zayyanu mai motoci yace"My son kadaina kira na ko fuskarsa dauke da murmshi, Aryan kuwa cikin shagwaɓa yace"uhm Am sorry daddy kasan halin da nake ciki yanzun ma Hajiya kakus tadawo gurin Ummi da zama dan Allah daddy kadawo gida haka nan Ummi fa na bukatar ka please daddy" Wata irin zufa ce ta zubo masa muryar sa na rawa yace "why why my son meyasa baka fada mani halin da take ciki ba"!? Ina Fannah dai yanzun dafatan ta haihu lfy ko"!?.


Idanuwan sa suka rikeɗi sukayi jajaye sosai yace"Daddy sai dai kadawo gida akwai magana" shiru daddy yayi yana jin zuciyar sa na matsanin cin bugawa sosai da sauri Alhaji bature yace "lafiya Aminina meya ke faruwa ne"!?


Bai kashe wayar ba yace"Akwai matsala a gida fa tabbas wani mummun abu yake faruwa a cikin iyalina, A gaskiya dole a gobe nadawo Nigeria.

Runtse idanuwan sa yayi wani irin farin ciki ne ya mamaye masa Zuciya Alhmdulillah Akwai yake mamaye tawa.

Yasan tabbas da Abbyn sa yadawo zai baiwa Ummin sa kulawa ta musan man gyara murya Abby yayi yace"my son kana jini kuwa"!? Aryan yace"uhm Abby" kayi hakuri insha Allah zandawo gida dan naga iyalina halin da suke ciki nima lokacin naso nadawo Nigeria abubuwa ne sukayi mani yawa Amman insha Allah zan dawo aikina zan baiwa Alhaji bature ya kula mani da shi kaji ko ɗan saurayi na"!?.


Murmshi Aryan yayi mai sauti yace "ok babu damuwa Allah ya dawo muna da kai gida lfy my Abbyna"Ajiyar zuciya yake yana tunani wani ciwo ne ya kame Ummi batare da yasa ni ba sai yaji kamar wani lokaci Hajiya kakus ta sanar da shi Ajiyar zuciya Alhaji Zayyanu mai motoci yake maimaita innalillahir wa inna ilaihir raji un huuu iskan bakin sa mai zafi yake hurowa kashe wayar yayi Aryan kuwa da sauri ya tashi ya shiga cikin gida yana kwalah ma Hajiya kakus kira, Hajiya kakus ce ta fito daga cikin daki da sauri tana cewar "lafiya mai gida wannan kira fa "da gudu ya rungume Hajiya kakus yana juyawa da ita cikin falon cikin shagwaɓa yace "uhmm Abby ne ya kira ni yace na fada maki gobe sai dawo ƙasa Nigeria fa" wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya hannunta ta ɗaga sama tana cewar "kai Alhmdulillah yaro na zaidawo gida kai masha Allah Allah kaine abun godiya sosai duban Aryan tayi taga yana cikin farin ciki sosai wasu hawaye ne suka zubo mata da sauri ta goge kada Aryan yaganta, Aryan kuwa lokacin da hawaye suka zubo ma Hajiya kakus yana gani sakin ta yayi yana kallon ta A hankali yace "ban san meyasa duk lokacin na nake cikin farin ciki ba lokaci ɗaya baƙin ciki yake mamaye mani zuciya kullum ina tunani wace irin rayuwa zanyi a nan gaba meyasa lokaci ɗaya farin ciki na yake ɗaukewa ban sani ba dukk lokacin da na kalle Mahaifiya ta tana cikin matsala ban meyasa lokaci ɗaya ciwo ya kame Ummi na ba huuuu wata irin Ajiyar zuciya yayi sannan ya jawo hannu Hajiya kakus suka zauna saman kujera yana kallon ta yace"Hajiya wlh bazan ɓoye maki ba har yanzun ina mamaki ciwon Ummi na ni yanzun abun da yake kara damuna shine wace yarinya ce zan kawo ta ringa kula da Ummi na da sauri Hajiya kakus ta katse sa tace"Aa ai yanzun Ummin ka ta samu mai kulawa da ita sosai kuma ai yanzun Aure zakayi ba ƴar aiki zaka ɗauko mata ba ba'an baka Ayanah ba"!?.



Shi har ga Allah ya manta da wata wai ita Ayanah aduniya sai yawaske yace "kuma fa haka fa to yanzun yaushe zamuje naga my son dina"!?


Dariya tayi tace "kaji jairi marar kunya wato matar ka ita ce gaban ka ko to Allah ya shirya muna kai kabari sai Abban ka yadawo ƙasar nan sannan...



Alhaji Zayyanu ne ya kasa zama ya kasa tsaye abun duniya yayi masa yawa Alhaji bature yana zaune yana kallon sa yace "sai dai Addu'a abokina saboda tunda lokacin da abun yasame ta an kira ka Amman hankali ka yana gurin wace shegeyar karuwar golloriya kullum baka da lokacin iyalin ka sai nata ni kuma ina bakin kokarina na nuna maka hanya Amman baka saurare ni ba....


Ajiyar zuciya yayi yace "to yanzun yakake son nayi da ita kaga wlh ni har tsoranta nake idan naje gidana basan meya ke damuna ba....


Alhaji bature yace "innalillahi wa inna ilaihir raji un to Allah ya sauwaka bari dai zamuyi magana ni dai bari naji gurin iyali na ko Raihana tadawo school tashi yayi sannan sukayi musabiha ya fita daga cikin office din......


*HASSY SOJA*


07063617906



⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________39&40 _________*


Ummy Ya jafar junior Halima Aina'u da ango zaki sai ni Ayanah zaune muke a cikin motar sai labarin suke ni kam waya nake da Maa a can ɓangaren Maa tace "yanzun har na turo maku driver, yazo ya ɗauke ku "dariya nayi nace"to masha yanzun muna cikin mota da zarar mun iso zaki jimu dan yanzun mun shigo cikin Airport"ok babu damuwa Allah ya kawu ku lfy " Amin ya Allah kashe wayar nayi sannan muka iso idan zamu tsaya bayan yayi parking lot.


Fitowa mukayi daga cikin motar dukk mukayi tsaye kallon su nayi nace "Mungode sosai Aina'u da Yaya zaki sai mun kara shigowa ko"!? Kwalla ne suka zubo ma Aina'u tace" to insha Allah mune da godiya sosai sister Allah ya bar zumunci" Ummy tace "Haba dai kuka be dace da ke ba ƴata zamu dawo har ma sai kungaji da juna gashi dama har Ayanah ta samu mijin da zata Aure cikin farin ciki tace "wow gaskiya naji dadin haka Allah ya tabbar da Alkhairi ".



Turo baki nayi cikin jin haushin maganar ƙasa ƙasa nace"Ba Amin wlh " afili kuwa nace "bala driver ka ma yarda da su gida dan Allah "jakata na buɗe na ciro kuɗaɗe na meka masu nace "gashi nan dan Allah kuyi hakuri da su da ƙar suka amsa Sannan na meƙa wa bala driver nace" gashi nan sai ka sama mai gadi kiran sunan mu akayi Sannan mukayi masu sallama muka shiga cikin gurin, cikin jirge muka shiga muka zauna junior da Halima ni da Ummy sai Ya jafar da ke, zaune gefe ɗaya wata baturiya ce ta shigo ta sanar da mutane jirge zai tashi kowa ya sanya balls din jirge Sannan ta koma cikin ba'ayi mintan biyar ba jirge ya tashi zuwa indai.


To Su Ayanah a sauka lfy.



A ƁANGAREN SU ARYAN KUWA



Tunda wuri Aryan ya gyara Sannan ya fito falo ya iske Hajiya kakus zaune Ummi tana kallon Sunah tv murmushi yayi ya karaso gurin yace"Hajiya barka da hutaw" kallon sa tayi tace "yauwa mai gida na har ka shirya kenan" antashi lfy ya jikan Ummi na"!? Alhamdulillah jiki da sauki tunda tana iya zama sai dai har yanzun abun ya nan.


Ajiyar zuciya yayi karasowa gurin ta yayi yana shafar gashin ta yace"insha Allah zata samu lafiya yanzun dai bari nayi sauri

Please Login or Register in order to submit comment