Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakuri aduk inda kake na sanin halin ka baka da hakuri duk wanda yayi maka sai kayi masa gai Zayyanu baya ƙasar nan ace har yanzun mutum be dawo gida ba gurin iyalin sa fisabillahi.


Ajiyar zuciya yayi yace " ni fa ina tunani akwai matsala gaskiya saboda ni mai kai tun ranar da mukayi waya da Daddy har yanzun ko na kira shi sai yace mani wai nayi hakuri aiki yayi masa yawa wata rana sai dai naji abokin sa wato Alhaji bature ya ɗauka yace mani mudai cigaba da addu'a akan mahaifin mu" Ayanah kuwa tunda taji ya ambaci sunan Bature sai da gaban ta ya faɗi maimai mata sunan take yi a cikin zuciyar ta lumshe idanuwan ta tayi Hajiya Kakus tace "Allah ya dawo munda shi gida lafiya" tashi tsaya Ayanah tayi tace "Hajiya zan wuce gida yanzun insha Allah" kallon ta Hajiya Kakus tayi tace "kai tun yanzun bazaki bar ku ci abinci ba"!? Girgiza mata kai tayi tace Aa wallahi Alhamdulillah Ummy na ke jira na yanzun shiyasa" ok babu damuwa Aryan kaji ka sauke ta gida haɗa ido sukayi da shi da sauri yace"sai na gama shan lemo sannan " Aa wallahi Hajiya tare nake da bala driver ne cewar Ayanah tana kallon su.......



⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉





_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________29&30__________*


Watsa mani harara yayi ni kuma na murguɗa masa baki na masa gwalo Hajiya Kakus tace "to tashi kaji ka rake ta mana" turo baki yayi cikin shagwaɓa yace " kai Hajiya Kakus bari dai naji wuce muje" lafiya muke kamar abun arziƙi tafiya muke har mun fito daga cikin falon dai dai baki kofar falon nayi tsaye ina haɗa hannuna saman kirjina nace " to malam sai ka komai inda ka fito ko"!? wata dariya da yayi sai fararen hakonsa suka bayana yace " ina laifin miji ya raki matar sa ai ba laifi bane ko"!? Haɗe rai nayi nace "to wace ce matar taka din kasan na fi ƙarfin ka ko" ina kika fi ƙarfina yarinya ai ni wallahi da sauri muka haɗa ido kashe mani ido yayi yace "ina my son yanzun dai ya kusan zama nawa ko"!? Kau da kaina gefe nayi ina kallon gurin motoci.


Dariya ya saki yace "Afuwa madam ni ne ko to Sorry ba zan kara ba yauwa ɗan aromani wayar ki zan tura wani abu" bazan ba ƴar da wayar ba dan Allah kada ka sanya mani hawan jini pls" Au hawan jini ma zan san yaki to shike nan ki gaida su Mommy da my son" ko kallon sa banyi ba na wuce gurin motocin bala driver ne tsaye tunda da ya hango ni ya buɗe motar karasowa nayi na shiga cikin motar rufewa nayi sannan shima ya rufa ya tuƙa motar ya fito daga cikin gidan tafiya muke a cikin motar ahankalina yana gurin tunani Alhaji bature to meyasa naji gaba na yana faɗuwa meyasa haka" huuuu ajiyar zuciya nayi ina kallon waje motocin na wuce lumshe idanuwana nayi har muka shigo cikin gida ban san ba sai da bala driver yace "Hajiya ƙarama mun iso gida fa" buɗe idanuwana nayi sannan na fito daga cikin motar cikin gida na shiga buɗe kofar falon nayi baki na ɗauke da sallama can na hango junior duk ya lallata gurin da ledodin chocolate da rubar Ice-Cream dafe kai na nayi nace" junior! Junior!! da gudu ya taso yazo inda nake yana kallona yace "Mum Uncle ya siya mun chocolate da Ice-Cream Ummy ce ta fito daga cikin kitchen hannunta ɗauke da plate murmushi tayi tace "har kin dawo"!? Zubewa saman kujera nayi ina murmushi nace "wallahi kuwa Ummy na gaji sosai "ƙarasowa tayi cikin falon tace "kin gaji sai kace wanda tayi wani uban aiki himm Allah ya shirya ki Ayanah har yanzun halin ki na nan ko"!? Turo baki nayi cikin shagwaɓa nace "Allah Ummy na gaji sosai kuma su Hajiya suna gaishe da ku" mun amsawa ya mai jiki"!? Alhamdulillah da sauki wallahi wani irin ciwon take abun mamaki kamar asiri" ajiyar zuciya Ummy tayi tana kallona tace " ikon Allah kamar ya "!? Labari na bata tunda farko har ƙarshe girgiza kai tayi cikin tausaye tace "Allah sarki wallahi tabani tausaye sosai to meyasa basu neme maganin Hausa ba ko shi mai gidan ta baya so maganin Hausa"!? Ajiyar zuciya nayi nace "Aa sam ba haka bane shi baya ƙasar nan fa Amman insha Allahu kafin mu tafi zan taimaka masu kiran sallah la'asar ne ya katse muna magana .


Tashi nayi na wuce cikin ɗakina jakata na ajiye sannan shiga cikin toilet fitsari nayi sai naga period yazo wanke jikina nayi sai na fito daga cikin toilet din ciro waya ta nayi na kwanta saman gado ina hutawa magangan Aryan ne suka dawo mani wani abu ya bani dariya wani abu ya bani haushi ɗauko waya ta nayi na buɗe data cikin WhatsApp na shiga ina duba saƙo sai ga na Aina'u tayi voice tace "Aslm Alkm my ƙawata kwana biyu naji ki shiru Allah ya sa lafiya su Mama kullum sai sun tambaya ke" Ajiyar zuciya nayi sannan nayi mata voice nace " Amin wslm ƙawata lafiya klau Alhamdulillah wallahi abubuwa ne sukayi mani yawa shiyasa Amman insha Allahu zuwa gobe zan shigo yaushe ne bikin"!?.


Aina'u tace "kai my ƙawata har kin manta to gobe za'a ɗaure Aure gashi baki zo ba balle ayi maki kunshi".


Ajiyar zuciya nayi inason lalle sosai nace " yauwa kinga na gaji sosai Amman bari na turo maki bala driver sai ki haɗa shi da mai lallen ko"!?.


Aina'u tace " ok turo mani shi sai muzo tare da ita dama ban san inda kike ba"

🙄 kai sister ban son ƙarya fa yasin sai dai ki ce kin manta dai".


Aina'u tace" 😜 eh din yanzun dai turo mani shi gamun tare wallahi na gaji da aiki".


Nace" Kin gaji da aiki sai kace mai zuwa wani guri nisah"!?.


Aina'u tace "himm sai yazo zan sauka nayi wani abu kafin yazo".


Ok bye bye kashe datar nayi na kira bala driver na fada masa sannan na kashe wayar gyara kwan ce ta nayi na lumshe idanuwana har bacci ya ɗauke ni.




⚡⚡⚡⚡ ⚡⚡⚡⚡ ⚡⚡⚡⚡
ARYAN


Aryan kuwa girgiza kansa yayi yace "lallai yarinyar nan ke atunanin ki zan so ki ne Aa zan dai Aure ki saboda ciwon Ummi na nasan zaki iya taimaka mata da wasu abubuwa Amman maganar soyayya babu ta dama nace sai na wulaƙan ta ki to yanzun aka fara wasar sannan ya shiga cikin gida.


Bayan wasu awani sai gasu Taufeek da Hisham da Mustap da mommy da mom da Aunty Amarya da Alhaji Ahmda da Alhaji musa da sallama kallon su Hajiya Kakus tayi ɗaya bayan ɗaya gaida Hajiya Kakus sukayi Taufeek kuwa sai wani haɗe rai yake kamar an ce su duba sai sukaga Aryan ya ɗaura ƙafa ɗaya saman dining table yana girgiza kafafuwan sa ya haɗe rai kamar bashine yake dariya ba yace "kai uban wa yace kuzo gidan nan"!?.........

*Hassy Soja*

07063617906


⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________31&32__________*


Alhaji Ahmad ne yace "Haba Aryan kanen ka ne fa" Hisham yace "Sorry my brother insha Allahu baza'a ƙara ba yanzun kuma zuwa mukayi muga jikin Ummi ne, taɓe baki yayi yace"to ai taji sauki zaku iya tafiya bana son damuwa.


Kallon sa suke sai mom ta kalle su Aunty Amarya da Mommy tana masu sigel tace"Hajiya kakus ya mai jikin"!? Kallon su kawai take bata ce komai tace" lafiya klau tunda kungama abun da kuke zakuyi tafiya kun san marar lafiya baya sun surutu ko"? Alhaji Ahmda yace "haka ne inna dama zuwa mukayi dakata ban son jinkomai zakuyi tafiya komai nene zan nemeku da kaina " Cikin tsananin jin haushi duka suka fita daga Cikin gidan afusace sai da suka fita ta kalle Aryan tace" wallahi zuwan su ba alkhairi bane tunda suka shigo cikin gidan nan nake kallon su ɗaya ba ɗaya.



Ajiyar zuciya yayi yace"ni dai yanzun zanyi Aure saboda Ummi tasamu mai kulawa da ita wlh gashi ban san wanda zan Aura ba" dafe kansa yayi Cikin tsananin damuwa, murmushi Hajiya kakus tayi tace" Alhmdulillah yanzun dai tunda kasan yarinyar nan sai ka Aure ta mana zata kula maka da Umminka sosai wlh tunda naganta nake son ta, wani irin murmushin mugunta yayi yace "yauwa dan Allah asanya biki da wuri na kosa nayi Aure".


Ummi kuwa bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita saman kujera Aryan ne ya jiyo yaga har ta fara bacci Cikin tsananin tausayawa ya taso ya gyara mata kwanciya sannan ya wuce part dinsa.



Ummy ce zaune saman kujera tana kallon wa'azin Shekai daurawa da Sallama Aina'u tashigo Cikin falon tare da wata yar budurwa jiyuwa tayi tana kallon su murmushi ta sakar masu amsa masu sallamar tayi tace" ikon Allah Aina'u yau ke ce agidan namu? "!!


Cikin ladabi ta karaso har ƙasa suka duƙa suna gaishe da ita tace" Ummy ayi muna afuwa wlh abubuwa ne sukayi mani yawa, murmushi Ummy tayi tace" Ai babu komai wlh ya su Mama naki suke dafatan suna lfy ko"!? Lafiya klau Alhmdulillah suna gaishe da su Junior ne ya shigo da gudu yace"Ummyyy mu muunnn jayo da sallama Yaya jafar ya shigo cikin falon yace "Ummy barka da hutawa mundawo".


Aina'u tace" my son babu gaisuwa ko jiyawa tayi tace "ina yini Yaya jafar" dago idanuwan sa yana kallon ta da gudu ya faɗa saman kirjinta yana murna yace"Aunty yauche kika zou? Shafa gashin sa tayi tace" yanzun nan tashi muge gurin Mum da sauri ya rike hannunta suka wuce sama mai lalle kuwa baki ta saki tana kallon tsarin gidan, tana nan zaune sai da Ummy tace "ke bakije bane tashi tayi tabi bayan su, dai dai kofar dakin su Aina'u sukayi tsaye turo kofar yayi da yake ba rufe take ba shi Cikin dakin sukayi da sallama can ta hangon Ayana tana bacci hankali ta kwance da sauri junior ya faɗa sama jikinta yana kukan shagwaɓa uhm uhm uhm mum ki tashi mum ki tashi a hankali na fara buɗe idanuwana ina kallon sa nace"innalillahi wai kai junior meyasa bason kaga ina bacci ne iyee mtsss ni wlh bana son haka ai dai ban da gobe zamu koma India na huta "da sauri gurin uncle zakoma yeeeee yeeee Miss you my uncle, dariya Aina'u bushe da ita tace" sannu sarkin bacci daga magana sai bacci humm.


Ware ido na nayi naga tabbas ita ce wani irin ihu nayi Cikin tsananin jin dadi nace"my kawata yaushe kika shigo ban sani ba"!? Zaunawa tayi saman gadon sai ga mai lalle ta shigo cikin dakin da sallama kallon ta nayi nace"karaso mana Aina'u tace" Aa tashi muje falo da tagama maki sai mu wuce gida.


Tashi tsaye nayi muka fito daga Cikin daki Cikin falon muka karaso ko ɗan kwali bana ni asaman kai na kallon mu Ummy tayi tace" Auta ta meye haka ina ɗan kwalin naki"!? Zaro ido nayi ina kallon ta turo baki nayi Cikin shagwaɓa nace"uhm Ummy yana saman bed na bari" Yaya jafar yayi dariya yace"Umma kinsan ta riga ta saba da halayin India yawa fa.



Maa kuwa kullum cikin tunanin yaushe Ayanah zata dawo India daddy ne ya shigo cikin falon zaune ya hangonta saman dining table ta ajiye abinci agaban ta girgiza kai yayi yasan tana cikin damuwa sosai karasowa yayi ya dafa kafaɗar ta yace"haba dai kiyi hakuri mana nasan abun ke cikin zuciyar ki my life sweety" dago idanuwanta tayi tana kallon sa tace" bari na kira ta kasan akwai karantu junior kada lallace fa.


Wayar sa ya miƙa mata amsa tayi tashiga cikin Call number Ayanah na kira lokacin har na fara lalle Aina'u taji wayar Ayanah tana ringing da sauri tace" daddy yana kiran ki" wani irin fari ciki ne naji da sauri na dauka nace "Aslm Alkm Miss you daddy " dariya sukayi tare da Maa yace"my baby girl ykk ygd kwana biyu babu call me ko"!?.


Nace"lah wlh ba haka bane abubuwa ne sukayi yawa Amman dai ina Maa da sauri maa tace"nayi fushi tunda bazaki neme mu ba" Cikin marairai cewa nace"am sorry my life sweet heart Maa albishirin ki to" murmshi tayi tace" goro" sai nayi dariya nace"insha Allah ban da gobe zamu dawo har da su junior da Ummy da Yaya jafar" kai kai masha Allah gaskiya nayi farin ciki sosai Allah ya kai lafiya cewar Maa.


Nace "Amin ga Ummy da junior" kallon Ummy nayi nace "gashi ku gaisa da Maa junior ya waya nan kuyi magana da su daddy.


Amsa Ummy tayi sunka gaisa har da fira da dariya bayan tayi mata sallama sannan Junior ya masa ya cigaba da surutu da su har suka gaji sannan na amshi wayar nace"Maa ga Aina'u ku gaisa amsa Aina'u tayi Cikin ladabi suka gaisa sannan nayi sallam da su.


Ajiyar zuciya Maa tayi tace" har hankali na ya kwana wlh murmushi daddy yayi mata yace" to Alhmdulillah shike nan tunda zasu dawo jibi Allah ya kaimu lafiya "Amin ya Allah.


Bayan nagama wayar sannan aka cigaba da lallen har aka gama bayan wasu minita har ya bushe najena wanke nadawo falon lallen ba karamin kyau yayi ba abu na fara mace ga ja ga baƙi tashi nayi na watsa ruwa doguwar riga red and black ce na sanya takalmai red na jakata fashion red da wayayo yi na da laptop dina na saka cikin Jakarb powde ce na shafa sai jambaki red yan kunne red gyale red turaruka masu shegen kamshe na fess jikana da su fitowa nayi daga Cikin dakin kamshin turarena ya fara yi masu sallama zuba mani ido sukayi suna kallona turo baki nayi nace"wannan kallon fa na meye "!?.


Aina'u tace "my kawata kin gaki kuwa kamar bake ba"yatsine fuska nayi nace"Yaya jafar banyi kyauba ko"!?.


Dariya yayi sosai kin haɗu yan mata Allah ya sa ki samu mijin Aure mu huta ai kuwa da sauri nace uhm uhm uhm uhm Ummy kajin sa ko dama ashe Yaya jafar ya gaji da ni" murmushi tasarka mata tace" rabu da shi shalelena Aina'u ku tashi kuje Allah ya tsare, Amin my Ummy na shiyasa nake karaso sonki sosai wlh kallon junior nayi nace" muje my son tashi yayi yana jin dadi dashi zani fita sallama mukayi wa su Ummy muka fita daga Cikin falon bala driver nayi da sauri yazo yace "Hajiya karama fita za'ayi ne" nace "muje ka sauke mu gidan biki shiga Cikin motar mukayi da ni da junior da Aina'u da mai lalle yaja motar muka fita daga Cikin gidan har mu kashigo Cikin unguwar junior sai zuba akwai yake kamar raidiyo dai dai kofar gidan yayi parking.........

⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________33&34__________*

Fitowa mukayi daga cikin motar ai kuwa yaran gidan su Aina'u sukazo da gudu suna cewar "oyoyo ga Aunty ga Aunty ga Aunty murmshin nake cikin jin dadin yaran sun burge ni sosai Aina'u ce dauke da junior suna labari



Jakata na bude yan dari dari naciro na mike masu nace"gashi nan su sai alawa kunji da gudu suka amsa sannan suka wuce gurin wasa bala driver ne ya ja motar ya bar unguwar shiga cikin gidan mukayi da sallamah wasu mata ne zaune saman tabarma suna cin tuwo sallamar da mukayi ne yasa hankalin su yadawo inda muke Aina'u ce tayi sauri tace"my kawata ki kara sa mana ".


Ɗaya daga cikin su tace"lah bikisu duba kuga ƴar India da sauri duka suka tashi tsaye suna kallon mu ni dai har na tsargu Mama ce ta fito daga cikin daki zata wuce kitchen kenan sai taji muryar junior da sauri ta kalle kofar gidan baki ta saki tana kallon mu a hankali tace"lalla lallah ƴata yau ke ce agidan namu to sannu da zuwa karaso mana ashe zaku shigo"!? Murmshi nayi nace"ey wlh Mama ya jikin da sauki sosai ko"!? Matar gidan ce ta fito daga cikin daki tanajin an ce junior da sauri tace "oyoyo yar gidan Mama ta ya gida"!? .



Murmshi na sakar mata nace "ey Alhmdulillah ina Ya zaki ne "!? tabarma aka shinfiɗa mani na zauna ina kallon gidan nace "my kawata ina Ya zaki ne ko hidimar ta ɓoye sa"!? Waya Aina'u ta ciro ta kira sa ko minti biyar beyi ba sai gashi ya shigo cikin gidan da sallama yace"ina kanwata take ne dariya ya bani nace "har an faɗa maka zo ko Allah my Sister ce ta sanar maka da zuwan mu, gaba sai da sukayi dariya saboda hausa ta sai ahankali zaunawa yayi saman kujera yace"eh mana gashi ko nazo da sauri na" murmshi nayi nace "ey hakane ya hidima gobe ne ko"!?.


*RUGAR FULAHANI*

*TALLAH TALLAH*



Insha Allah gashi nan har na gaji da surutun mutane wlh cewar Ya zaki yana murmshi "nace to Allah ya kara sa alkhairi jibi dai zamu koma insha Allah"

Sai da mutanen gidan sukayi mani dariya ko ni sai da na baiwa kaina dariya nace "na baku dariya ne ko"!? Ya zaki yace "Aa ai kanwa ta ta iya hausa sosai.

Murmshi nayi Ina kallon su Aina'u tace ku tashi muje gidan da muke taro.


Haka acigaba da shirye shirye har dare yayi sosai Aina'u ce rungume da junior yana bacci duk kwan ci muke nace "gaskiya garin nan zaffi yayi yawa ga sauro" yan matan dake cikin ɗakin duk sunyi bacci waya ta ce na ciro daga cikin jaka Kiran Ummy nayi na sanar da ita bazamu da yau ba sai gobe sannan mukayi sallama har na buɗe data sai na tuno da maganar da mukayi da .



Hajiya kakus ajiyar zuciya nayi nace "ni fa gaskiya ban tashi Aure yanzun ba koda Aure zanyi ai ba zan iya Auren wannan mugun mutum nen ba fa shiru nayi ina tunanin sannan na tura mata number Ummy sannan na kashe wayar addu'a nayi a hankali a hankali har bacci ɓarawo yayi awun gabani.


Washe gari tunda safe mukatshi aka gyare gyaren gida wani gida muka shiga itace aka dauko aka fara sakawa ga murhu ni dai yanzun ban iya irin wannan girkin ba agidan biki kuwa ya cika da yan biki misalin ƙarfi 2:30 pm aka daura Auren Aliyu da sadiya akan sadaki dubu hamsin , ango ya sha farar shada mai aiki blue gaskiya ba kariman kyauwa yayi ba sai washe baki yake kamar mai gurin, Aina'u ce sanye da Atamfa orange ta fito daga cikin daki .


Ni kam zaune nake saman tabarma kallona tayi tace"my kawata ke baki sanya kayan ba fa"!? Kallon ta nayi ina murmshi nace "eh sari zan saka ne shiyasa waya tace ta fara ringing daukowa nayi na duba sunah Ummy yake yawa ga screen din wayar dauka nayi nace "Aslm Ummy barka da rana, Ummy tace "yauwa lfy klau Ayanah har yanzun baki dawo ba ko za'a kawo maki kayan ku ne"?



Nace "yauwa Ummy sari zan saka Amma tumace zaki haɗu mani" ajiyar Zuciya tayi tace "OK bari na aiko maki bala ya kawo maki sari wane iri to"!? Amma pink zaki dauko mani sai Takamli pink sannan dukk dai kayana da na jounir zaki haɗu mani su guri ɗaya yau da dare zan dawo goda sai mu fara shirye Shiryen tafiya ko? .


Anyi biki lfy angama lfy kowa yayi gida Ayanah ma sun koma gida agajiye.



Hajiya kakus zaune saman bid tana kallon Ummi da alamar baccin yayi mata dadi ne tashi ta fito daga cikin daki kara messg taji a wayar ta dauko ta tayi saman dining table bata duba Ayanah ce ta faɗu mata acikin rai saman kujera ta zauna ko minti biyar batayi da zama ba sai ga Aryan ya fito daga cikin daki kamshin turaren sa ya game falon da sallama ya karaso .


Hajiya kakus kallon sa take alamar tambaya Ajiyar zuciya yayi sannan yace "ba nisa zani ba fa" Dama inaso ka sauki ni gidan su ƴarinyar nan ko zaka akai ni"!? .



Kallon ta Aryan yace"kai Hajiya yanzun dai dole sai muje gidan su wannan ƴar kauye"! Da mamaki take kallon sa tace "kamar ya fa mijina ban gane ba"!? Da sauri yace"tooo tashi muje babu koma fa" .



Himm akwai tace tashi tayi ta shiga cikin daki ta dauko mayafi gyara mayafin tayi sannan ya shiga gaba ita kuma tana biye da shi baya waje suka fito buɗe kofar motar yayi ta shiga sannan ya zagayo ya buɗe ya shiga ya tuƙa motar suka fita daga cikin gidan.



Ayanah ce ta shigo cikin falon hannunta rike da hannu junior da sallama suka shigo Ummy ce ta fito daga cikin kitchen amsa sallamar tayi tana kallon su tace "wai har kundawo"!?.......

*Hassy Soja*

07063617906


⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________35&36__________*


Ajiyar zuciya nayi nace "wlh kuwa mun gaji sosai Ummy zaunawa saman kujera mukayi kallon mu take tace "ki tashi kuje ku watsa ruwa mana" jikina babu kwari haka na wuce cikin daki toilet na shiga na gyara jikina sannan na fito daga cikin toilet junior ne kwan ce saman gado har ya fara bacci kallon sa nayi nace "ko yayi bacci ne bari da na koma falo gurin Ummy idan ya tashi sai na watsa masa ruwan da sallama na shigo cikin falon Halima ce da Ya jafar ne zaune saman kujera kallon su nayi nace "ku kuma yaushe kuka shigo.



Dariya Ya jafar yayi yace "Aa my kanwata har kun dawo kenan yanzun muka shigo cikin falon Ummy dai kallon mu take tana murmushi tace "Ayanah kin ci abinci kuwa"!? Girgiza mata kai nayi nace "sai dai anjima zan ci saboda nasha lemon juice ne da biskin baki suka saki suna kallona da mamaki Ummy tace "Ayanah yanzun wannan abun zakin shine zai kosar da ke"!? Dariya nayi nace "kai Ummy mamaki kuke bari sai muje ko gani da idanuwan ku, shiru sukayi saboda tsabar mamaki bace komai ba ajiyar zuciya Ummy tayi tace "to Allah ya kyauta dai" Amin ya Allah mukace, kallon Halima nayi nace "Amma Aunty ban karasa maganar ba waya na ta fada rigging ɗaukota nayi gefena Sunan Hajiya yake yawo ga screen din waya na da sauri najiyo ina kallon su nace "Ummy Hajiya ce ke kira yanzun wlh har na manta da ita, dauka nayi na kara ga kunne nace "Aslm Alkm Hajiya" Hajiya Kakus kuwa tana cikin mota tana kallon Aryan tana murmushi tace "Amin wslm ƴar nan har kin manta da kakar ki ko"!?.


Murmushi nayi cikin shagwaɓa nace "uhmm uhm Am so sorry Hajiya wlh sai yanzun na samu zama gida ne gashi munta shirye shirye koma wa India ne" zubo mani ido sukayi suna kallona, Hajiya Kakus tace "Allah sarki ƴar nan to yaushe zaku gidan mu"!?.



Shiru nayi ina tunanin ajiyar zuciya nayi nace "sai dai mun dawo gaskiya abun inason a fara yiwa Mama maganin Hausa ko Allah zai sa adace" wani irin farin ciki ne ya mamaye mata zuciya tace "yanzun dai bari na haɗaki da mijin ki sai ki faɗa masa sunan unguwar ku saboda muna cikin mota zamu zo inda kuke"wani irin faɗuwa gaba nakeji yana yi

Please Login or Register in order to submit comment