Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kina jina ko" ɗaga mata kai nayi nace "Uhmm Insha Allah zan rungume kaddara ta da Allah ya aiko mani da ita" cikin jin dadin maganar ta Mommy tace "masha Allah nima zan tayi addu'a insha Allah Allah ya sanya Alkhairi.


Tashi tayi ta ɗauko wani abun har da galam din wani abun kamar ruwan zuma ta miƙe mani tace "kin ga wannan kullum ki sha sau ukku wannan kuma kada ki ƙara tsalki da wasu ruwa sai wannan zan taimaka maki gurin gyara jikin ki wannan kuma maganin Nononwa da hips suka inason kafin ki shiga cikin gidan ki kin sha gyara ki daina zama aƙasa saboda sanyi kada yayi maki ilah sannan wannan ruwa sai kin dafa su kina jina tsaka nina da ke babu kunya babu ɓoye komai" Murmushi nayi nace "insha Allah Mommy "yauwa ƴar Albarka nasan ki da shan zaƙi sosai Amman ki rage sha sannan akwai wasu abubuwan da zan nuna maki su kinji ko"!? Eh na fahimta.


Amrha ce tashigo cikin ɗakin da sallama kallon Mommy tayi tace "Mom zo nan ki zauna ke ma ga naki nasan halin ku wlh idan baku sha ba babu ruwa na saboda mazajin ku ba masu ɗaga kafa bane, cikin jin kunya ta karaso ta zauna kusa da Ayanah sai mun haɗa ido na watsa mata harara dariya take kasa kasa tace "eye Aryan zai sha dadi nasan bazai ƙwaliki ba hhhh" turo baki nayi nace Uhmm Uhmm Uhmm Mommy kinajin ta ko"!?.



Hararar ta tayi tace "Allah zaki fita ɗakin nan idan baki bari janta ba tau, da sauri tace, Am sorry my lollipop sister ban ƙara ba"ni dai Murmushi nayi ina kallon ta ban ce komai ba junior ne ya shigo da gudu yana cewar "Mum! Mum! Ana kiran ki awaya, amsar wayar nayi na duba sai ga na Aina'u da ɗan uwa sune nagani bayan kwana biyu Ummy ta sanar da su Hajiya kakus zamu dawo dan da wata biyu sannan na kira dan uwa na faɗa masa sannan na kira Aina'u na sanar da ita ranar da zamu dawo Nigeria..



BAYAN WATA BIYU


Yau kam gaba ɗaya mun shirya baƙin sari na saka Amrha jan sari ta saka su makam suma sari suka saka zaune muke cikin motocin yau sai Nigeria surutu junior yake zubawa kamar me dukk wanda ya sani ya kalle ni yasan Ina cikin damuwa dan har rama nayi koda muka iso Airport parking akayi sannanu muka fito daga cikin motar sai afara kiran sunan mu atare muka shiga ciki jirge muka zauna bayamunzauna aka fara sanarwa jirge zai tashi gyarawa mukayi sannan jirgen ya ɗaga sama lot.


A sauka lfy Ayanah.......

Afuwa babu edition



*Hassy Soja*

07063617906

⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_Love and romantic story_



_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉



🌹 *ELEGANT ONLINE* 🌹




*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Call me or Whatsapp me 08066268951
Or 09022823910




_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________51&52__________*

Wani matashin saurayi ne ya shigo cikin ɗaki
Ya fara bincike sosai har wadiro sai da ya buɗe dukk kayan da ciki sai na fito da su Amman bega komai ba gurin bed yazo ya cire zanin bed din bega komai ba wargi yake da matashin kai har ƙasan bed ne duba bega abun da yake nema ba wani irin ihu yayi yace "wlh bazai yuyuba sam kwalama wasu kira yayi yace "Amira boy kuna ina ne"!? Da gudu suka shiga cikin ɗakin suna kallon sa yarinyar tace "Ya dai ko baka komai bane"!? Ɗago idanuwansa yayi yace "ina fa ban ga komai ba wlh har inda take ajiya na duba sosai " dafe kansa boy yayi yace "gaskiya dai bazamu ƴarda ba har muna tunanin zamu kuɗi ace wai babu komai".


Ciro waya yayi ya kara ga kunnen sa sai ta kusan tsinkewa sannan aka ɗauka yaji an ce Hello ya dai" Ni fa ban ga komai ba wlh anyi kana tunanin bata ɗauke takardun dukiyar ta ba"!? To ko ina kun duba har toilet "!? Kallon yarinyar yayi yace "shiga cikin toilet ki duba sosai"turo kofar toilet din tayi ta shiga ta cigaba da bincike sosai Amman babu komai jiki a sanyaye tadawo ɗakin tace "ni ma dai wlh ban ga komai ba" ihu yayi yace "kaji dai ko anya kana tunanin kanwar ka bata ɗauke su ba"!? Kashe wayar akayi ina huci fuce ya fita daga cikin ɗakin suma suka biyo bayan sa..



Hajiya kakus ce zaune cikin falon tana kallon sunnah TV tana sauraron sheka jafar adam kamshin turaren taji yana mata sallama ɗago idanuwanta tayi tana kallon sa sanye yake da kanana kayan sunyi matukar haɗuwa shigo cikin falon yayi yace "Mata sa ana hutawa kenan to antashi lfy" Murmushi tayi tace "lfy klau mijina wanga wanka fa har na fara kishi fa"! Murmushi Aryan yayi yace "ai kece uwar gida daga ke babu wata " hararar wasa tayi masa tace "Uhmm ranar da kayi Aure shike nan bazan ƙara ganinka sosai ba" dariya yayi har sai da fararan haƙuran sa suka bayana yace "Uhmm mata sa dai to ni dai zan wuce America " riƙe haba tayi tace "gurin me kuma Aryan "!? Ajiyar zuciya yayi yace "gurin ball ma kisan na kwana biyu ban fita ba to shine jiya renardo ya turo mani sa messing ana son ganin mu"! Kallon sa tayi tace "yanzun sai yaushe zaka dawo"!? Sai ranar da muka gama sannan " Aa gaskiya Aryan bikin ka fa saura kwana nawa fisabillahi kace wai sai ranar da kuka gama gashi har sun dawo Nigeria fa ni dai gaskiya sati ɗaya na baka Allah cewar Hajiya kakus.


Dafe kansa yayi cikin damuwa dama son yayi ya gudu ba zai dawo ba har sai angama komai to gashi Hajiya kakus ta hana shi ya jima" kallon sa tayi tace "idan satin be maka ba sai kayi zaman ka agida shike nan idan angama biki sai tafi tare da matar ka, turo baki yayi cikin shagwaɓa yace "kai Hajiya ni dai gaskiya sai nadawo haka kawai ta takura mani" kallon sa take da mamaki tace "kamar ya ta takura maka saboda kanajin kunyar fita da ita ko yaya"!? Haka kawai mutane su raina ni fisabillahi ace bana iya hakuri dole sai nazo da ita" cikin faɗa tace "wlh baka isa ba wato da ka Aure ƴar mutane sai ka har muna ita ko to su masu yawo da karuwa fa sai ace me to wlh Aryan ka kiyaye ni tau bana son maganar banza fa" Ajiyar zuciya yayi yace "Allah ya baki hakuri insha Allah sati ɗaya zanyi tare da Fauzal zan dawo" Murmushi tayi tace "haba ko kai fa yanzun naji magana" sallama yayi mata ya fuce daga cikin falon gareji yaje yayi ma driver hannun da gudu yazo yace "muje Airport, to ranka yadade, da sauri ya buɗe motar ya shiga shima ya shiga cikin motar suka fita daga cikin gidan....


Suna isa akan kiran sa sallama yayi masa sannan ya fito daga cikin motar cikin airport ya shiga be jima da shigewa jirge ba ya tashi sama.


Aryan a sauka lfy.


Ayanah ce zaune cikin falon tana waya da ɗan uwa sai dariya take sosai tace"yanzun fa mundawo ƙasar ku yaushe zaka zo"!? Cikin murna yace"haba dai ƴan kanwata to insha Allah zuwa nan da kwana biyu zan shigo sai ki turo address dinku Ummy ce ta fito daga ciki kitchan Amrha tana biye da ita tashi tsaye nayi nace "Uhmm Ummy shine kika hanani shiga kitchan to amman gashi nan Amrha ta biyo ki" girgiza kanta tayi tace "Ayanah sarkin rigima to yanzun ba gashi har angama komai ba uhm zama tayi saman kujera sai suka zauna Maa ce da Mommy suka shigo da sallama amsa masu Ummy tayi tace "har kun fito "!? Wlh kuwa gashi nan mun fito tashi nayi nazo na faɗa saman jikin Maa ina shagwaɓa nace "Uhmm Uhmm Uhmm Uhmm " shafa gashi na take tana Murmushi tace"Aa waye ya taɓa mani shalelena uhm"!? Su Uhmm Ummy ne wai ban sha kitchan ba ina turo baki Ummy dai Murmushi tayi Amman bata ce komai ba kallon mu take Maa tace "gaskiya dai aba'a kyautawa shalelena ba yanzun shike nan sai ahanaki yin aiki" Mommy tace "Ni nace kada wanda ta koma shiga kitchan saboda sati biyu masu zuwa aza'a fara masu gyaran jiki" Maa tace "ai na kira Aunty Zaliha Gusau mai gyaran jiki na faɗa mata ranar da zata zo, to shike nan Allah ya kaimu lfy"Amin suka ce.


Daddy ne da Uncle ne zaune cikin part ɗinsa Daddy yace" Alhamdulillah gaskiya nayi farin ciki sosai yanzun to menene abun yi dangane da wannan bikin da za'a"!? Eh to ni dai zan ba kowa ce zan bata rabin miliyan sai tayi hakuri da shi" jin jina kai Daddy yayi yace "Masha Allah ni dai zan siya masu kayan daki da na kitchan da moto insha Allah zuwa jibi za'a kawo koma har nayi, order kayan.


Bhaiyah ne da Amrha ne cikin ɗakin zaune suke gurin ɗaya ɗago idanuwanta tayi tana kallon sa tace "Bhaiyah kasan na kusa daina zama da fa" da sauri ya kalle ta yace "saboda me Baby ko yanzun tunda an saka muna rana zaki guje ni"!? Girgiza masa kai tayi tace "Aa ko ɗaya Mum ce tace kada ta kara ganin mu a tare, dafe kirjin sa yayi yace "kin san ba zan iya jure wa ba gaskiya kin san yarda nake cikin bukatar ki wlh" shiru tayi Ayanah ce tashigo cikin ɗakin da sallama tsaye tayi tana kallon su tace "to lailah da majanon" da sauri suka ɗago suna kallon ta taɓe baki tayi tace "to ai sai ki taso muje an ce nazo ƙafata ƙafarki yarinya" Bhaiyah yace "yanzun Ayanah baki da tausayi baki ga har na rame ba"!? Ni dai ban ga komai ba sai dai ƙibar da kike ɗirkawa.


Zaro ido yayi yace "ni dai ko"!? Ey din tashi muje zubaida, miƙewa tsaye tayi tace "to sai anjima fuce suka daga cikin ɗakin.


AGIDAN SU ARYAN KUWA


Su Hajiya kakus ne da Aunty Amarya da Mom da momyn Hisham Taufeek da Hisham da musty da Alhaji Zayyanu da Alhaji Ahmad sai Uncle musa zaune suke cikin falon sai wata mata mai kama da Ummi Hajiya kakus tace "Kai Masha Allah gaskiya lefen nan yayi kyau sosai faɗima kin iya haɗa kayan Aure, Murmushi matar tayi tace "Wlh kuwa ai gara aɗauko mata masu kyau wanda mahassadin ta suji haushin sosai, da sauri Momyn Hisham tace "jar uba ke faɗima waye yake masu hassada kin san dai mun fi karfin muyi masu hassada ke ni ban ga abun hassada a nan ba Mum ce ta amshi zan cen tace "kwari ma kuwa ƴar matsiya da ita har za'ayi mata hassada mtsss, faɗima tace "gashi ma kuwa kun nuna da azahiri to Allah shi kyauta a dai gyara rayuwa saboda mutuwa, tsawa Daddy ya daka masu yace"wai ku meya ke damun ku ne fisabillah"!? Hajiya kakus tace "wlh ranar idan baku nan ai dukan zasuyi yanzun dan Allah menene abun faɗa anan eh saboda kaya dai ko to shike nan kai Taufeek da ku da Hisham ku saka akwatayin a cikin mota yanzun za'a tafi da su Taufeek yace "To "tashi suka suka kwashe kayan kusan akwati arbain 40 sannan Hajiya kakus tace "Faɗima da ke da su Zayyanu zaku tafi, cikin girma mawa tace "to Hajiya, gaba suka tashi suka fita daga cikin falon mota kusan ukku suka fita da ita...



Koda suka iso gidan su Ayanah suna ɗakin ban sanda zuwan su ba haka aka gama komai har suka fita bayan sun fita su Maa da Mommy da Halima aka buɗe kayan kowa cewa yake masha Allah guɗar Mommy ce sukaji da sauri suka fito suga lfy akwatuna ne nagani na faɗa kallon juna sukayi alamar tambaya su Ummy da Maa da Mommy da Halima an zaune suna kallon kayan Amrha tace"Mommy lfy mukaji kina guɗa"!? Jiyowa tayi tana kallon mu tace"wlh abun farin ciki ne Ayanah zo ku gani, karasowa mukayi mu dai kallon ikon Allah kawai muke ni da Amrha zaunawa saman kujera mukayi Maa tace"Akwati 36 aka kawo ma My Angel din ta" da sauri na kalle ta sai da gabana ya faɗi cikin raina nace"shikenan ta faru ta ƙare wayyo Allah na burin sa ya cika a fili kuwa da gudu na wuce dariya suka saki gaskiya kayan sun haɗu Mommy tace "Akwati sha biyu dukk kanana kaya ne "wayyo Allah dadi kice Sister na ana cikin daulah yeeee yeee dole nayi rawar india wlh.


Su Ya jafar ne suka ahigo cikin falon da sallama kayan da suka ganin yasa suka saki baki suna kallon su Ummy tace "ku karaso mana ga kayan ƙanwar ku an kawo, karasowa gurin sukayi sannan suka zauna saman kujera Bhaiyah yace "wow gaskiya akwatun nan babu karya fa Ya jafar ne ya amshi zan ce yana cewar "gaskiya ƴar kanwar mu tayi goshi Allah ya sanya Alkhairi Amin ya Allah suka ce.


*Washe gari da rana*

Aryan ne yadawo tare da Fauzal suna zaune cikin ɗaki wanka ya shiga kusan minti tallatin ya fito daga cikin toilet din dai dai madubi ya tsaya yana gyara jikinsa kallon sa Fauzal yayi yace "ni fa gaskiya na ƙosa naga Amaryar mu" wani ban zan kallo Aryan ya watsa masa ya cigaba da shafe shafen sa wadiro buɗe ya ciro jallabiya ruwan zuma saka jallabiyar yayi sannan ya feshe jikin sa da turakun masu shegen kamshi sannan ya buɗe wata ƴar roba ya haanun sa ya ciro sweet ya saka abakin sa jiyowa yayi har zai fita yaji muryar Fauzal yana cewar "wannan ai iskan ci ne ana jiran ka zaka wani sa kai kace fita zakayi".


Dawowa yayi yace"ba iskan ci zaka tsaya mani ba mtsss sannan ya fita daga cikin ɗakin, da kallo ya bisa saboda ya sanin halin Aryan.


A GIDAN SU AYANAH KUWA.

Yau tunda safe nayi wanka na tafi ɗakin Ummy na zaune na same ta tana gyaran kayan sakawa da sallama nashigo cikin ɗakin kallona tayi ta amsa mani tace"lfy na ganinki tunda da safe"!? Turo baki nayi nace"lfy klau dama baƙo ne zanyi zuwa anjima" da mamaki take kallona tace "Ayanah ban gane wani zai zo gurin"!? Ajiyar zuciya nayi nace "eh baƙo dai zanyi wani ne muka haɗu dashi afacebook shine, zai zo" himmm! ni dai babu ruwa na wlh kin san dai bikin ku ya matso ko to yanzun idan Aryan yazo ya iske ko fa kinsan dai Namiji kishi ne da shi ko"!? Shiru nayi ina jin haushin maganar Aryan nace"to kiyi haƙuri tunda baki so" Ummy tace "to shike nan amman kada ki dade wlh idan Aryan yazo ke da shi ne ehe! Dariya nayi cikin jin dadi nace"nagode sosai, Allah ya kara girma da gudu na fita daga cikin ɗakin.


Tunda yamma Ayanah take gyara gyare Amrha tace "wai wannan girkin da kike na waye ko angon zai zo"!? Share ta tayi ta cigaba da girkin ta bayan ta kamala ne ta zuba shi a cikin kula mai kyau sannan tace "Safuwan ne zai zo"! Zaro ido tayi cike da mamaki tace "wane Safuwan bada wannan yaron ba "!? Harara ta watsa mata tace "shi Safuwan ɗin ne yaro baki da hankali" Amrha tace "to yanzun idan Aryan yazo ya iske ki kina fira da wani fa"!? Taɓe baki nayi nace"wannan kuma matsalar shi ce ba tawa ba kinga ki daina mani maganar sa wlh" cikin jin haushi tace "wlh baki iska kuma indai Aryan zaki gani da idanuwan ki fuuu tayi ta fita daga cikin kitchan din taɓa baki nayi nace "oh dai keki sani mtsss aikin banza maka malam...


Ayanah ce zaune cikin harabar gida ta sanya atamfa pink mai ratsin black riga da sike sai mayafin ta pink da takalmin ta suma pink zaune take saman kujera sai wani dan saurayi zaune kusa da ita suna fira yana bata labari dariya take sosai kamar me Aryan ne tare da abokinsa Fauzal cikin mota shigowa suka cikin gidan dai dai gareji yayi parking kamar an ce ya dube gefen sa hango Ayanah yayi tana dariya har da dafe ciki rain sa yayi mugun ɓace idanuwan sa suka rikiɗa sukayi ja sosai afusace ya fito daga cikin motar, Ayanah tace "kai gaskiya abun ku yana burge ni sosai yace "kin ga ƴarda take fushi tana cewar wlh dukk ranar aka Aureni baka ba kallon ƴan matan waje, tuntsurewa tayi da dariya shi kuma ogagan yana karasowa gurin ɗago idanuwanta tayi tana kallon sa tunda ga saman sa har zuwa kasan sa halbe yayi da tirin lemon da ruwa tace "wai ke lfy malam lfy klau kake kuwa "!? beyi wata wata kawai ya watsa mata wani irin mari har da ta zube kasa some sannan ya shaƙi wuyan ɗan saurayin har sai da idanuwan sa suka fito waje hankali Fauzal yayi mugun tashi da gudu ya ƙaraso gurin yana cewar "Subhanalillah Aryan kana da hankali kuwa kada kashe ɗan mutane fa, cikin fushi yace "Sai na kashe shi kowa ya fita wato shi ƙwarto ko ni zan nuna maki waye ARYAN kuwa daƙir Fauzal ya kwaci ɗan saurayi ahannun Aryan da gudu ya fita daga cikin gidan sannan hankalin sa yadawo gurin Ayanah Ɗaukar ta yayi kamar wata jaririya ya shiga da ita cikin gidan........


*Hassy Soja*

07063617906



⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡

_Love and romantic story_




_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉



🌹 *ELEGANT ONLINE* 🌹







_Bismillah Rahamani Rahim_


*Page __________53&54__________*


Koda ya shigo cikin falon Amrha ce da Maa zaune cikin falon shigowar sa ne ya sa hankalin su dukk ya tashi cikin tashin hankali Maa tace"Aryan lfy me yake faruwa da My Angel"!? Ajiye ta yayi saman kujera cikin fushi yace"fira take da wani ɗan iska da kuɗin Aurena akanta ni kuma naji haushi shine na mare ta, da gudu Amrha ta ɗauko ruwa masu sanyi aka zuba mata ajiyar Zuciya tayi sai ta fashe da kuka, Su Ummy ne suka shigo cikin falon kallon su tayi tace "lfy "!? Cikin ladabi Aryan ya duƙa ya gaishe da su sannan ya faɗa masu abun da yake faruwa , Murmushin manya Ummy tayi karasowa gurin tayi tana kallon su tace "Ayi haƙuri dai da ƴar kanwar ka Aryan ko babu Aure atsakanin ku ai kanwarka ce da kanta tazo ta same ni ta sanar da ni baƙonta zai zo, nayi tambayoyi sosai tace" mani wlh babu komai atsakin su sai zaman mutumci shine nace taje Amman kayi hakuri bazata koma fita ba kaji ko"!? Cikin kuka nace"Wlh ni ba Yaya na bane wannan mugun wata rana ai kashe ni zai ne" sai ta basu dariya sosai sannan Mommy tace " tashi ki wuce cikin ɗakin ku ban son rashin kunya haka zakuyi Auren kuna faɗa kamar kaji"!? Cikin jin kunya yace "ayi hakuri wlh raina ne yaɓace shiyasa Amman komai ya wuce " jin jina kai sukayi sannan yace "ina my son Ummy"!? Wlh yana part din Halima saboda ya dame mu da surutun shirme shiyasa na tura sa can ko akira sa ne"!? Sosa kansa yayi da key cikin jin kunya, shidai fauzali kallon ikon Allah kawai yake cikin da mamaki da tambayoyi iri iri wanda zaiyi wa Aryan.


Murmushi su Maa sunkayi sannan ya miƙe tsaya yayi masu sallama ya fita daga cikin falon bayan ya sun fita ne su Mommy sukayi dariya sosai Maa tace"kishi ne fa ya rufe masa ido shiyasa ya mare ta" dariya Ummy tayi tace "ai shiyasa na bashi haƙuri kun san halin Ayanah bata jin magana sai da na faɗa mata kada tajima fa, Amrha tace "ni fa har faɗa mukayi da ita saboda shi tace mani ina ruwanta da shi ai kowa yayi rayuwar sa kuji fa" Allah dai ya shirya muna ita kawai.


BAYAN SATI ƊAYA A YAU NE ZA'A FARA GYARAN JIKIN AMARE

Zazzaune suke cikin ɗakin Ayanah da Aina'u zaune suke gurin ɗaya sai Amrha da take kwance tana kallon sama Aina'u tace "my ƙawata yau fa ne za'a fara maku gyaran jiki fa" taɓe baki nayi nace "oh ni fa ban damu ba ki ɗai na ma wannan maganar " dariya Amrha tayi sosai tace "Allah sarki wata ranar nake kallo irin yanda da za'a ta muna rawar jiki" mtsss aikin banza kawai iskan cin ne ya motsa ko ai be ko sa cewar Ayanah, dariya ta bushe da ita tace"ke dai my ƴar uwa wata baiwar Allah ce jikinta na rawa tayi ma saurayin ta girki sai ga wanda zata Aure kin san abun da yafaru"!? Girgiza mata kai Aina'u tayi tace "Aa sai kin faɗa menene " jefe ta nayi da mayafin Aina'u nace"ke dai kinji haushi wai ace har yanzun baki manta ai wlh kullum na tuno da marin nan sai nayi kuka dan yanzun dai tsoron sa nake kamar me" au wai dama ke ce ake magana hhhh lallai kam kice kinji maza"!?.


Himm ke dai bari sister ai wannan baƙin Aryan ɗin mugun ne na bugawa ga jarida dariya sukeyi gaba ɗaya Mommy ce ta shigo cikin ɗakin da sallama tace "to ga Aunty Zaliha nan mai gyara jiki sai ku gyara da sallama ta shigo cikin ɗakin da kayan gyaran jiki da Ayanah aka fara jiyowa Mommy tayi tafi daga cikin ɗakin.



AGIDAN SU ARYAN KUWA


Gidan su Aryan ya fara cika da mutane sosai Hajiya kakus takira kowa da kowa bayan sun zauna tana kallon su tace "Nafseet da ke da Maryam da Maimuna ku tashi ko koma gidan ku sai kuyi hidimar bikin saboda kun wannan baiwar Allah bata son hayaniya sosai kuna jina ko"!? Momyn Hisham tace "haba Hajiya fisabillah sai aware mu saboda ba'a son mu acikin hidimar bikin nan ai ko babu komai anan bari har agama biki sannan " Aunty Amarya tace "wallahi kuwa wannan maganar gaskiya ce Hajiya adaiyi hakuri kawai.


Lallaɓa ta sukayi sannan tace"to naji Amman wlh kuka ja mani magana a cikin gadan bikin nan to ni da ko ne zaku iya tafi" godiya muke Hajiya tashi tsaye sukayi sannan suka fita daga cikin falon, binsu da kallon take har suka fita, tace "Allah ya shirya ku wlh halin ku sai ku dai.



Alhaji Zayyanu ne zaune cikin part dina alamar waya yake naji yace "haba dai yau kai Alhaji bature kana Airport kenancan ɓangaren maganar sa yace "Eh gamu nan atsaya, ok babu damuwa bari na turo maka Hisham kashe wayar yayi sannan ya fito daga cikin ɗakin da sallama ya shigo cikin falon su Hisham ne suka fito zata su kiran Hisham yayi da sauri yadawo baya yace "gani Daddy, amm kaje Airport yanzun abokina yana jin ranka, to sannan ya fita daga cikin gidan.


Alhaji bature kuwa tunda suka shigo cikin Nigeria gaba ɗaya jinsa yake wani irin gaban sa sai faɗuwa yake har Hisham ya iso gurin yace "barka da zuwa Uncle muje" sai da ƴar sa ta taɓa shi sannan ya amsa buɗe ƙofar motar yayi sannan suka shiga ya rufe motar ya ja motar suka bar gurin, tafiya suka sosai, shi kuma kallon titi yake can ya hango wata Unguwa kansa ne yayi mugun sarawa dafe kai sa yayi yana cewar "innalillah wa inna lillahi raji un runtse idanuwan sa yayi matar sa da ƴarsa suka ce

Please Login or Register in order to submit comment