Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Taupeek ya faɗa masa komai da komai hankalin sa duk tashe yake idanuwan sa sunyi jajaye jijiyoyin sa duk suntashi saboda tsabar tashin hankalin yace "why? Why? meya sa zaku ɓoye mani My love sister ta ɓata innalillahi wa inna ilaihir raji un to menene sanadin ɓan ta subahanahi wani irin iska mai zafi ne ya fito da shi cikin bakin sa ajiyar zuciya yake sosai lumshe idanuwan sa yayi .


Wani dattijo ne zaune saman kujera kallon su kawai yake idanuwan sa sunyi jajaye sosai yace "yanzun kun nufin ku ce mani har yanzun babu labari ƴata kenan ko to wallahi ba zai yuyuba sam buga table yayi da karfin gaskiya cikin masifa yace "to bari kuji yanzun haka Aryan yana saman hanya tunda wannan abun ya faru wani ya kira sa ya fada masa komai da komai.


Cikin tashin hankali kowa ya ruɗi saboda jin abun da wannan mutum ne ya faɗa, Wata dattijiwa mata ce tace"innalillahi, wane munafuki ne ya kira sa ya fada masa ne"!?.


Murmushi wani dattijo yayi yace "oh wa kika sani Hisham mana shine munafukin da ya kira ya faɗa masa mana da sauri Hisham ya ɗago idanuwan sa da sunyi jajaye sosai yace"Wallahi tallahi ban san komai ba game da faɗar wannan maganar ni ko kiran sa banyi kuma ku duba waya na ku ganin.


Wata matar ce bazaka ce mata tsohowa ba koma bazai kace mata yarinya ba kuka take sosai kamar raina zai fita tace "innalillahi wa inna ilaihir raji un wannan wane irin bala'i ne wayyo Allah na nashiga ukku amanar tawa ita ce ta ɓata kowa sai da ya tausaya mata saboda tashin hankalin da ake ciki Taufeek ne ya shigo cikin falon yana fito yana waƙe waƙe sa na guy phone ga kunnen sa kowa ya zuba masu ido kallon sa kawai suke Hajiya Kakus ce tace"ke taufaa kake ko wa ma dan uban ka zo nan muna cikin tashi kai kuma hankalin ka kwan ce eye..


Da sauri Mustap ya taɓo sa yana nuna masa su Hajiya Kakus cire phone din yayi yace "Aa su Hajiya Kakus lafiya kuka kallona cewar Taufeek "!?.


Uban ka muke kallon shegen yaro muna cikin tashin hankali kai kuma hankalin ka yana kwan ce wuhhuuu shike nan ƙila ma da hannunka acikin wannan mugun abun"!.


Dariya yayi yana kallon su yace"to menene nawa a cikin wani abun be rufe baki ba kawai yaji tarasss tarasss tarass mari ukku akayi masa gaba ɗaya kowa kallon wanda yayi marin yake fuskar murtuƙi babu rahama idanunwan sa jajaye sosai yace "wato yanzun iskan naka ya wuce ka lallata yaran mutane har sai ka sace yaran mutane ko to ka fito mani da my love sister dina na ganin da idanuwana kai ne kayi sanadin ɓanta nace ka fito mani da my love sister naaaaa cikin tsawa yake magana.


Kuka Mommyn sa ta fashe da shi sosai tace "yanzun shairin da zakayi wa yaro nan kenan yanzun mai Taufeek yayi maku da zaku kula masa shairi wayyo Allah na wannan ne irin tashin hankalin"!?.

Kallon su yayi yace "kamar yarda ya sace mani kanwata to hukumar yan sanda zasu kasu sutafi da su a station su ukku da Hisham da Taufeek da Mutsap har sai an gama bin cike .


Cikin tashin hankali Hisham yace " my brother wallahi ban san komai ba ka yarda da ni".


Taɓe baki yayi yace "ni bazan yarda da kowa ba har sai an ta yana gama faɗar haka ya wuce part din sa, kallon su Hajiya Kakus tayi tace "to kun gani ko abun da nake faɗa maku kenan ni dai babu ruwa wannan maganar tau wuce tayi ɗakinta.


Yan sanda ne suka shigo suka tafi da su Taufeek station mutsapah da Hishim hankalin su atashi Amman bada Taufeek murmushi kawai yake be damuba....

****** ******* ******
jirgen mu ya sauka airport lafiya kowa sai fita yake cikin jirgen ni kuma kallon su kawai nake Maa na kalla sai tayi mani murmushi tace "to tashi mu fita daga cikin jirgen ko mun iso.


Jikina rawa yake sosai haka muka fita daga cikin jirgen dai dai matatakala mukayi tsaya ina kallon gari sosai gashi dare yayi saboda akwai hasken nepa sai ya karama gari kyau sosai wasu shegen motocin ne guda huɗu ɓaka da fara har da ja wasu security da D. S. S. sun zo baki na saki ina kallon ikon Allah taɓani Maa tayi alamar muje mu shiga cikin motar saukowa kasa mukayi dai dai gurin motar mukayi tsaye sai cewar "suke welcome back madam, dan masu kai tayi da sauri aka buɗe wata irin hadaɗar motar baka shiga tayi sannan nima na shiga cikin motar da gudu suka wuce gida lumshe idanuwana nayi kamar a mafarki wai nice ƙasar India ikon Allah huuuu ajiyar zuciya nayi buɗe idanuwana nayi ina kallon titi wata unguwar masu kuɗi aka shiga wani shegen gida ne wanda ya amsa sunan sa gida horn akayi da sauri aka buɗe get sulalawa yayi cikin gidan kuma aka ƙara buɗe wani shegen get sulalawa sukayi cikin gidan nan ma aka ƙara buɗe wani shegen get sulalawa yayi cikin gida dai dai gurin ajiye motocin akayi parking wani dattijo ne na hango tsaye alamar muyake jira buɗe kofar motar akayi sannan muka fita daga cikin motar kallon gidan kawai nake gidan kowa hasken nepa murmushi ya saƙar muna cikin jin dadi yace"welcome back madam and angel baby and my boy friend " da sauri taji ta rungume sa da hannu ɗaya, ɗayan kuma tana ɗauke da junior tace "Thanks my husband dafatan kowa yana lafiya"!?.


Ni dai tsaye nake ina kallon ikon Allah wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mani nace ina ma ace ni da su Ummy na ne kallona yayi yana girgiza mani kai yace "Aa my dougta zo nan, ya buɗe mani hannun sa da sauri na faɗa saman kirjin sa na saki wani irin marayan kuka sosai kamar wace aka ce mani Ummy ta mutu rungume ni yayi sosai yana cewar "sorry dougta na kinji zamu sanya ki cikin farin ciki sosai kinji ko"!?.


Cikin shashekar kuka nace "nagode sosai daddy Allah ya kara buɗe na alkhairi.


Cikin gida muka shiga wow ashe wajen bako mai ba cikin gida shine abun kallo wani irin hadaɗin falo ne subahanahu Allah tsalki ya tabba ga Allah wanda ya halice komai da komai Zazzaunawa saman kujeru masu ɗaukar hankali ajiyar zuciya nayi zaune nake kusa da daddy yace "to my dougta yanzun kin dawo ƙasar nan da zama sai kuma yanzun maganar karatun ki sannan kuma duk abun da kike so akwai shi agidan nan komai nene kuwa sannan kuma idan junior ya girma kawai makarantar da za'a sanya shi kuma cikin gidan akwai kayan wasan yara har da na manya kuɗi kuma akwai su acikin bedroom din ke kuma kayan ku duk akwai shi kinji ko"!?.


Wani irin ihu saboda farin ciki nace "wow gaskiya ban masa ta ina zan fara maku godiya ba wallahi kuma naji dadin sosai insha Allah zanyi maku biyaya inda har be saɓama ubangijina ba maganar karatun na kuma Alhamdulillah sai inaso nayi waƙoƙin India da na hausa kallon sa nayi nace "sai dai kuma daddy kamani da wani mutum wanda nasani fa...


Dariya farin ciki kowa yayi yace "wallahi ke ma kina mani kama da wani ɗan uwa na fa Amman babu komai yanzun dai ke madam tashi ki nuna mata komai da komai acikin gidan sannan ya tashi ya wuce part dina..........




*T SOJA ce*😜 07063617906


⚡ *ARYAN&AYANAH*⚡


_Love story_




_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉








_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 7&8 __________*

*A cikn gidan Ummy kuwa*


Bayan tafiyar Ayanah wani irin kuka Ummy ta fashe da shi mai ban tausaye da sauri ta leƙa kofar gida ko zata ga Ayanah Amman bata ga kowa ba dawowa cikin gida tayi tace "kai cuni Hajaru to yanzun ko ina ƴata zata je kenan gashi bata son kowa ba innalillahi wa inna ilaihir raji un da gudu taja mayafi ta fita daga cikin gidan har bayan gida ta leƙa Amman bata ga alamar ta ba jiki asanyaye tadawo gida kwana tayi tana addu'a .


Ya jafar kuwa ko yazo gida ya gaishe da Ummy taba amsawa ko kallon sa batayi saboda shine yayi sanadin tafiyar Ayanah dinta yayi bata hakuri Amman ko kallon sa batayi ba kawai sai tace kada ya kara zuwa mata gida inda ba Ayanah yadawo da ita ba....


A can ƙasan India kuwa bayan kwana biyu an saka Ayanah school da gurin waƙokin india cikin wata ukku har ta fara jin india ce a can ɓangaren ɗaya kuma kullum cikin tunani Ummy take ko yaushe zata yafe mata Junior kuwa bulbul yayi tubarkallah kamar ɗan Shekara ɗaya.


*Bayan Shekara ukku*

Wata hadaɗar budurwa ce ta fito daga cikin kitchen plat ne ta,ɗauko ahannunta waya take naji tana cewar "Da gaske Baeyaha zakadawo jibi ko"!?.


Wani hadaɗin saurayi ne zaune saman kujera yana murmushi alamar waya yake yace"ke Ayanah wallahi kin cika rigima fa.


Turo baki nayi cikin shagwaɓa nace "Allah Aa ni bani da rigima, yanzun dai yaushe dawo ƙasar nan "!? Dariya yake sosai sannan yace "wai ke me zaki bani ne kike tambaya na yaushe zandawo insha Allah watan nan mai shigo zan dawo na kamala abun da nake yi a can yanzun dame dame kike son nazo maki da shi har da junior "!? Murmushi nayi nace "kayo mani shopping sosai da ni da shi ina karasowa cikin falon can na hango junior ƙasa yana wasa da motar sa da jirgen sa na ƙasa na wasa gasu duk ya lallata jikin sa da gurin da yake zaune ga ledojin chocolate da robar Ice-okashe wayar nayi nace "wayyo Allah Maa! Maa!! uhm uhm uhm ni dai wallahi na gaji da wannan wahalar, fitowa tayi daga cikin ɗakin ta da sauri tace "wai lafiya dai kike kira na ha Angel"!?.


Turo baki nayi cikin shagwaɓa nace "dan Allah kalle Junior duk ya lallata gurin da jikin sa fa hawaye ne suka zubo mani cikin jin haushi, rike baki tayi tace "to ina ruwan ki da shi ne wai kin sanya wa mijina ido fa tau Allah ki kiyaye ni, buga buga kafafuwar na nayi cikin shagwaɓa nace "Allah ni kullum sai na sanya masa kaya sau huɗu fa a rana ni dai gidan uncle zan komai da zama.


Junior kai junior zo nan cewar Maa, zaune yake da sauri yaso da gudu saman jikin ta ya faɗi yana dariya yana cewar "Maaa na maaa na chu, dariya tayi tana kallona ni dai turo baki nayi cikin shagwaɓa nace" Allah maa inaso zuwa nos Korean gidan uncle fa.

Kallona tayi sosai tace "nima fa tunani nake yi ke nan wallahi, Aa maganar me ake ta taunawa ne cewar daddy da yake sakowa sama bene da gudu junior yayi gurin yana dariya da sauri daddy ya ɗauke sa sama yana dariya yace "kai ɗan Angel kana lafiya ko"!?.


Girgiza masa kai yayi yace "eh klau ina zakaje ko gurin zaki zaka ne"!?.

Dariya yace "Aa yau ina gidan nan babu inda zani je ɗan Angel karasowa gurin yayi kusa da Maa ya zauna yace "Amm Angel kina waya da uncle din ku kuwa"!?.

Girgiza masa kai nayi nace "inaso zuwa gurin su uncle wallahi nayi missing din su sosai gashi bamuyi magana Amman ina magana da Amrha sosai a laptop kullum da safe da dare video call muke ina tunanin cikin wannan watan zanje, kai Junior ɗauko laptop dina zanyi waya, da gudu ya sauka saman jikin daddy part din mu ya shiga sai gashi yadawo da laptop din yace "mum gashi gashi", Amsa nayi shiga cikin kiran Amrha nayi wata irin hadaɗin budurwa ce ta bayana murmushi tayi tace "my lollipops sister ya kuke"!?.


Dariya nayi nace "o ni Allah wai ke yaushe zakiyi hankali ne ina su uncle ne kwana biyu shiru bana jin sa ga Daddy, Amsa Daddy yayi yace "my baby kina lafiya"!?.

Lafiya klau Daddy nayi missing din ku sosai ina Maa, gani nan my dougta tasamu ne"? Dariya tayi tace "wayyo Allah wallahi kina bani dariya Maa wai ina junior, wai,? Gashi nan my dougta junior zo ka amsa da sauri yazo yana kallon ta yace"Aunty na ina kike ne"!?.

Dariya tayi sosai tace"ina gida ya karatu kana ƙokari kuwa"!?.


eh sosai kullum sai maa da mum suna koya mani karatun kuma uncle yana zo gurin mani lesson kuma ina cin chocolate da robar Ice_cream firji din mu cike yake da kayan dadi sai da ya ba kowa dariya tace"gaskiya suna ji dakai my son baiwa mum dinka wayar mike mani laptop din yayi amsa nayi nace"Amma my love sister zan shigo cikin wannn satin insha Allah.


Wani irin ihu tayi cikin farin ciki tace"wayyo dadi gaskiya zanyi farin ciki sosai wallahi.

Hira mukayi ta duniya sosai sannan mukayi sallama.

Bayan kwana biyu da faruwa wannan Alhamdulillah komai yana tafiya dai dai Baeyaha yadawo gida yanzun muna cikin farin ciki ko wane lokacin Daddy ne zaune saman kujera ni kuma ina ƙasa zaune ina yanke farce daddy yace "Angel inda zakuje nos korean dole sai kun neme kayan sanyi saboda garin kankara ne ɗago idanuwana nayi nace "insha Allah ai nayi buke din kayan da zamuje da su kuma Amrha ta siya muna kayan sanyi .


Murmshi yayi yace "ok babu damuwa Allah ya kaimu ki tashi kije ki kwanta tunda junior yana gurin madam gashi da wur zaku fita, tashi nayi sannan nayi masa sai da safe.


Washe gari jirgen mu ya tashi zuwa ƙasa nos Korean garin ƙanƙara kenan
****** ****** ****** ****** ******

Abby yace "to yanzun mekake son anyi ne Aryan "!?.


Kallon su yayi yace "yanzun shekara ukku da ɓatan Fannah zan sanya adawo da su Amman ba yana nufin an gama bincike bane insha Allah za'a cigaba da addu'a.


Zaunewa saman kujeru sunkayi kowa tunani waye ya sace ta"!?.



A bangaren dan gidan Mijin Fannah kuwa tunda sukaji labarin an sace ta wasu har hawaye sukayi mata wasu kuma Allah ya kara sukayi mata mijinta kuwa yayi kuka har ya gaji har da ciwo ya kama shi sai da aka kashi asibityn saboda ko magana ba yayi sai dai yata subatu yana cewar " Fannah ta ina kika shiga ne ki dawo ki haifan mani da yan biyu masu kamar ki wasu yan uwan sa sai da sukayi masa kuka duk ya fita hayyacin sa saboda ɓatan Fannah din sa.


*Washe gari*


Fitowa yayi daga cikin ɗakin sa falo ya fito yana sanye da ƙanan kaya riga da wando kayan sun fito da kyauwan sa Hajiya Kakus ce zaune saman kujera tana karatun jarida da sallama ya karaso gurin yace"barka da hutawa Hajiya ni dai zan wuce nos Korean insha Allah na sanya Sojoji da yan sanda bin cike wanda ya sace mani Kanwata.

Aje jaridar tayi tana kallon sa cikin tausayawa tace"sannu mijina insha Allah za'a ganta kaji ko kaje Allah ya tsare ya bada sa'a ball.

Aryan yace"Amin ya Allah nagode sosai sannan ya fita daga cikin gidan sai airport sai nos Korean.


fitowa yayi daga cikin jirgen har driver yazo ɗaukar sa zuwa gidan sa wanda yake da komai a cikin koda ya shigo cikin falon ya iske abokin sa wato Fauzinl zaune saman kujera yana kallon tv da sallama ya karaso gurin kallon sa yayi yace "ya dai abokina anji labarin ta ne"!?.


Zaunawa saman kujera yayi yana girgiza masa kai lumshe idanuwan sa yayi yace"har yanzun dai babu wani labari.


Nisawa yayi yace "to baka zargin wani ɗan uwan ka ko wani maƙocinka"!?.


Ajiyar zuciya yayi yace "ina tunani su Taufeek ne saboda na iske shi yana dariya yana cewar to shi ina ruwan sa acikin wannan maganar".




Subhanallahi gaskiya wannan da ruɗani acikin sa yanzun shekara ukku fa cewar Fauzinl yana kallon sa...


Zan ajiye wannan maganar saboda babu wata shedar wanda ya sace ta zamu cigaba da addu'a Allah ya baya na muna ita idan tana raye cewar Aryan yana shafar marar sa.



Ajiyar zuciya Fauzinl yayi yace "to Allah ya baya na ta Amman wai meye damun ka ne ko har yanzun baka yanke shawarar Auren ba"!?.


Taɓe baki yayi yace "kai ni fa har yanzun ba a haifi yarinyar da tayi mani bane fa".


Dariya Fauzinl yayi yace"Amman kai ɗan iska ne yanzun kana nufin babu mace a garin nan"!?.


Cikin gadara da ƙasaita yace "eh kwarai babu ta duk maza ne ai inaso mace wada ta iya shagwaɓa da iya girki da murya mai shegen dadi mai kananan kaya ai".


Dariya yake sosai sannan yace "uhm kada dai a wuce guri ni dai ɗan kallo ne yaushe zamu fita dafe goshin sa yayi sai yanzun ya tuna ashe beda wasu kayan ci yace "Zamuje Shopping anjima har da lemo ya kusan ƙare wa.



Mun iso cikin koshin lafiya fito nayi daga cikin jirgen dai dai bene nayi tsaye alamar ƙanƙara ke saukowa daga sama wani irin sanyi ne nake ji sosai ɗaukar junior nayi na rungume sa saboda sanyi jikina har rawa yake saboda sanyi saukowa ƙasa nayi cikin farin ciki su Amrha ne suka hango ni da junior da sauri ta karaso gurin tana dariya tace "welcome back my lollipop sister.


Dariya nayi nace "kai sister Allah garinan akwai sanyi sosai da sauri junior ya jiyo yace "Aunty na mishi you" dariya mukayi nace "kai har kagane ta sarkin surutu,.


Wucewa mukayi muna tafiya dai dai motar suka tsaya buɗe kofar motar tayi sannan muka shiga ciki rufewa tayi ta tuƙa motar muka wuce gida.


Bayan mun isa gida parking tayi sannan muka fito daga motar cikin falo mu kashiga da sallama wata mata ce zaune saman wata hadaɗar kujera sallamar mu tajiya da sauri ta ɗago idanuwan ta tana kallon mu fuskar ta ɗauke da murmushi tace"lala lah yau manya baƙine agidan na mu ikon Allah har da mai gidan nawa,"!?.


Dariya mukayi har da Amrha nace "Afuwa mommy nasan nayi laifi sosai sorry, da gudu junior ya karasa gurin mommy yace "oyoyo mommy.

Buɗe masa hannu tayi da sauri ya faɗi saman jikin ta yana dariya tace"eh ai dole kayi dariya saboda yau nice mai ɗaki ba Ayshat ba ko"!?.


Ɗaga mata kai yayi yana kallon tv ajiyar zuciya nayi nace "ina uncle be dawo bane"!? Mommy tace "eh sai da dare zai dawo insha Allah yanzun kuzo kuyi wanka ku ci abinci sai muyi fira ko"!? Ok miƙewa tsaye mukayi sannan muka wuce cikin ɗaki wanka nayi sannan nayiwa junior bayan nagyara masa sannan muka fita daga cikin ɗaki falo muka zauna kallona Mommy tayi tace "himm mai hali baya fasa halin sa ko yanzun bazaki ci abincin ba ne"!? Girgiza mata kai nayi nace "Aa bana jin yunwa Amman yanzun inaso muje shopping ne Mommy.


Amrha tace "ina zuwa da sauri ta shige cikin ɗaki sai gata tadawo da jaka tace muje kai, atare muka fita daga cikin falo hannu na rike da hannun junior muna tafiya dai dai gurin mota muka tsaya buɗe kofar motar tayi sannan muka shiga cikin motar tuƙawa tayi muka fita daga cikin gida gudu take shararawa saman titi.


Aryan ne zaune cikin mota ya jingina kansa saman kujera Fauzinl ne sai driver gudu yake sosai can ya hango wata mota gaban su murmushi yayi yace "wannan motar daga ganinta mace ce ke tuƙin ta insha Allah, taɓe baki yayi yace "wai kai ina ruwan ka ne mtss ɗan iska kawai.


Dariya yake sosai sannan yace "naji dai ko mai zaka ce ai wallahi maza bayin mata ne, Shiru yayi ɓe ce komai ba sai dai lumshe idanuwan sa da yayi hango motar ɗazu yayi tayi parking gurin shagon shopping da sauri shima yayi parking dai dai inda motar su Ayanah take har yanzun basu fito cikin motar ba dariya yace "ai kuwa sai naga wannan ko wace irin budurwa ce.


Fitowa nayi ni da junior daga cikin motar itama Amrha ta fito daga cikin motar Cikin shagon Shopping muka shiga atare ni da su Amrha da Junior gefen chocolate da robar Ice- cream muka je gurin atare da su Amrha da junior Amrha kuwa komai taga junior yana so sai ta ɗauka, a bangaren su Aryan kuwa, shigowa cikin shagon shopping din sukayi Junior ne ya hango su da gudu yace "uncle! Uncle!! Aryan ne yaji ana cewar uncle da sauri ya jiyo yaga mai kira wani hadaɗin yaro ne ya ganin mai kama da kanwar sa Fannah yace "Fauzinl duba kaganin da sauri shima ya kalle wannan yaron yace ikon Allah wallahi kamar su ɗaya da Fannah, da sauri ya karaso gurin yana dariya yace "uncle tare nake da mum dina fa makazo siya ne"!?.


Wani irin farin ciki ne ya mamaye masa zuciya be san sanda yayi murmushi yace"my son kaya zan siya.


Junior yayi dariya yace "lah Uncle babba da kai zaka siya kai"!?.


Dariya su Aryan da Fauzin sukayi sai Aryan yace "my son what is your name"!?.


Jinjina kai yayi yace "Aryan junior Amman su mum dina da su daddy suna ce mani junior.

Wow nice name.


Kallon sa junior yayi yace "to kai Uncle yayi sunan ka "!?.

ARYAN ne suna na cewar Aryan yana kallon sa cikin sha'awa.


Murmshi junior yayi yace " lah Uncle irin sunan mu ɗaya da kai ashe to kana da mata ne"!?.



Dariya sukayi masa sannan yace " Aa bani da mata ko zaka bini zuwa gidana ne.



Ɗaga masa kai yayi yace "eh zan bika uncle zaka siya mun chocolate ne"!?.



Eh zan siya maka chocolate Amman sai kabini gidana be rufe baki ba sukaji muryar mai shegen dadi tana cewar "babu inda zaya bika saboda kana ɓaron yara ko? to ko kana sace yaran wasu to bazaka iya sace nawa yaron ba....


Kallona yayi da mamaki nace "kwarai ma kuwa ɓaron yara kawai mtsss a fusace ya watsa mani mari har guda ukku.....



⚡ *ARYAN&AYANAH* ⚡


_Love and romantic story_

_*HASSY SOJA*_🌹✍🏻:

*T SOJA* 😉





_Bismillahi Rahamanin Rahim_



*Page __________ 9&10__________*


Dafe kunci na nayi ina kallon sa saboda tsabar mamaki kamar amafarki afusace na watsa masa Mari ina kallon sa cikin ido nace "kai waye da har zaka mari ne yaro na kuma bazan baka ba ni Ayanah nace ba zaka dauke mani yaro ba da sauri najiyo ina kallon su nace "ke Amrha wuce muje junior zo muje gida rike hannun sa nayi muka fita daga cikin gurin yana cewar uncle ina zuwa gurin ka please Mum zan be shi watsa masa harara nayi nace o yah wuce muje gida shashashan yaro mtsss wallahi nayi da nasanin zuwan wannan shopping din gobe zan komai inda na fito.


Mutuwar tsaye yayi yana kallona har suka fita daga cikin gurin runtsine idanuwan sa yayi yana kallon lokacin da ta watsa masa mari yace"ni zaki mara yarinya waye uban ki agarin nan kai masa'ud kaji kane mo mani waye uban ta agarin nan"? Afusace ya buga rigar sa ya fita daga cikin gurin cikin fushi.



Tuƙin Amrha take ni kuma da junior muna gaban motar kuka nake sosai kamar raina zai fita lallashi na Amrha take Amman ko sauraron ta banyi ba har muka shigo cikin gida ko parking bata iyarba na fito da sauri cikin gidan na shiga da gudu wani dattijo ne da mommy zaune suna

Please Login or Register in order to submit comment