Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu.?.

Haɓa ta rike zatai magana Adnan ya zabura yana gur'nani.

Deedee ta taɓa hannu tace "Alhamdulillah! Da da bakina nace wani abu saiku karyata to kungani da mazajen idanun ku.
Som Som Aljannun Basuson matsawa daga ko ina, Sunfison zaman nan din dai kamar kabari .
Ina mai tabbatar maku da cewa kuka kaishi cen saiya ida haukacemaku baki daya Ƙarshe ma ya gudu.
Abarshi nan inta kula dashi ainima d'ana yake balle ni daban taɓa haihuwaba sai najisu kamar sun Ketani sun kutso ta Jiki Na.

Aymah ta danyi murmushi lallai ta yarda duk wanda yaja da Deedee ruwa yake tsullugudum,Yau da Babu ita da Batason ya zatayi.ba ..

Addu'a suka hau jeramai ogan nasu yace yanzu dai zamu tafi zamu iya barmaki masu kula dashi ko mutum biyar haka,irin wannan ciwon wahala garai dole saida majiya ƙarfi.

Hawaye ta share tace" Kai ina! Ka ganni nan Arayuwata ina tausayin yaran da basa gaban iyayensu da iyalin su Saboda nayi Maraici banji Daɗin saba ..
Ga matasanan bakin get dake nan kusa damu sune muke neman Alfarma suna kulamana dashi gakuma ita matar tashi Da take Maharramasa..
Indai taimakon zakumana kwara ku dinga sallamar su kun'rageman nawie ,su kuma wayan nan abarsu
Su koma ga iyalan su Lami Lafiya..

Dukkan su am'sawa sukai Cikin gamsuwa.
Dayawa daga cikin su kuma sunkara sonta dan kowa ya farajin faduwar gaban barin shi da za'ayi jinyar mai laluri irin ta Adnan.

Nan fa zaratan maza suka buɗe bakin Aljihu suka fara fiddo kudi sunawa Deedee Alkhairi tana kauda kai da fadin kai duk ku kwashe abunku ni kulawarma da kukai da jikana kawai ta wadatar.

Hakuri suka shiga bata kamin su mike ogan su yace Mama zamu dauki Nawin ku na tsawon lokacin da zai warke in sha Allah.
Duk wata zamu baki 250k ina ganin zata isheki kiyi manege.
Yanzu ga motar kayan Abinci nan zansa akawomaki Allah yaba shi lfy sukuma masu kulawar dahi Ace dasu zamu basu 50k duk wata Allah yabiyaku da Aljannah.

Ameen ta amsa tana murmushi da samasu Albarka.

Harya fara tafiya ya dawo ga Aymah ya kara kallonta kallo na tsanaki kamin yace "banji ɗuriyar yaran nashi ba?


Dam gaban Deedee ya faɗi dana aymah da sauri Kuma DeeDee tace'' Deedee tace ai kason su biyune ita waccen ta nemi saki tin zuwan farko da tayi yaran kuma sunyi hankali suna wajen dangin Uwar tasu sun ruke kayan su.

Cikin gamsuwa da kalamanta ya daga kafaɗa tare da fadin" Taiwa kanta kukuma Allah yabaku ladar jinya.

Ameen Deedee tace tana masu Rakiya suka shishiga suka dauki hanya tana rakasu da Addu'a.
***
Jameel kau da Asuba ya tashi lfy klau jikin ya sauka amma fuskar shi babu walwala.
Kamar yanda yasaba shiri yayi yama iyayen:sa bankwana ya fito da kudin da jiya baiba su Aymah ba.

Ya dauki hanyar Gidan su kenan aka mai waya motar ya cika dole ya tafi ya dauki hanya zuciya ba dadi.

Deedee kam tana shiga ciki ta Ɗanɗara guda tace Adnanu kagani ko?.
Kai kayi nufin Alkhairi wa zuciyar ka kaga in komi bai warwarema ba Dan Butar ubanka.
Yanzu gashi gabanka Alkhairin Allah ya saukar muna shashasha mahaukaci, Allah kadai yason abinda ka shuka shiyasa ya nannaɗeka Haka Kamar fanke waje guda,Ka tuba kaga in Haske bai Ratsa Rayuwar kaba.
Abincin ta turamai gaban shi tana harar shi kamin tace da Aymah tisamun kudin Nan.
Ta kalli Dr tace wai nikam Ina Jamilu ne Tinjiya ko Bankwana?

Yace tindazu nike kiranshi baya ɗauka Allah yasa dai lfy.

Deedee tace tom Ameen dai.

Zai tashi ya tafi ta tsaidashi da faɗin ya raba kudin ya ɗauka..

Dariya yayi ya A'a Deedee in banbaki ba bana karɓa ba baccin kokorin Naki ne.
Wannan Hakkin kine wallahi daɗi sukaji suka baki babu kudin kowa anan .

Dariya tayi tace hakane likita wai kai ya sunan ka ne.

Murmushi yayi yace tsawon wata hudu sai yau ake tambaya to Dr Abba sunana.

Dariya tayi tace'' To Abba mungode da dawainiya Allah ya sakamaka da Alkhairi ya biya dukkan bukata na Alkhairi.
Allah kasanya kagama tsire mazaunan kowa lfy, Allah kasa kar hannun ka ya karkace ka caki wani inda cutar shan inna zata kamshi.

Dariya sosai ya hauyi AYMAH na tayashi daidai lokacin da Jameel ya turo kofar da sallama yashigo .

Ƙasa tsayawa sukai da dariya yayin da kallo daya yamasu ya ɗauke kai ya zauna kusa da Deedee ya gaidata.

Amsawa tayi tana fadin" lfy kakecin magani muna cikin hali na farin Ciki.

Ɗan yake yayi yace ba komi dama nadawone nace bari inkawomaki kudin cefane xan koma.

Aymha ce ta dakata da dariya tana binshi da ido kamin tace'' Ya aiki.

Kamar ya kyaleta kuma ya juya yace Alhamdulillah tare da mikewa yaba Dr hannu yace zai wuce.

Sosai taji ba daɗi tason kuma abinda tamai ne yasa shi kasa sakin jiki dasu yau Allah dai yasa ba wani abu ya zarga game da itaba.

Shikam Dr Abbah mikewa yayi yakama hannun Jameel din suka fito Abakin Get sukaga Su Sadam Yaran da suke kula da Adnan.
Nan ya faɗamasu bukatar zaman da akeso suyi da shi dan bazasu sake maidasu Kauye ba.
amma su maido shi Dakin Baki .

Godiya da murna suka shigayi Kamin suce zasuje su dawo.

Abincin da ka kawo masu yace su fara shiga dashi ciki kamin su wuce.

To sukace suka fara Jilarshi shikuma suka ƙarasa bakin motar Jameel din suka tsaya ya dan kama kyauran motar Jameel din kamin ya shiga zayyano mai abinda ya faru da faɗin. kai bakama lura dashiba naga Yamafara bacci..

Murmshi Jameel din yayi yace Som idona baigan shiba.
Lamarin Didi sai Addu'a .Allah dai yasakamaka kaima da mafificin Alkhairi muna godiya.

Ameen yace tare da sake rike hannun Jameel din yace.
Ya maganar soyayyar ka da Aymah kana sonta ko ka janye danni banga wani abu ba?.

Ɗan murmushi Jameel din yayi da yafi kuka ciwo yace" Tom mundai barwa Allah zaɓi kawai.
Amma ina ganin kamar nike haukan banza na ita som batani take ba hasalima daukar yaronta takeman ka kauga ba'a aure haka kwara in kyaleta .

Murmushin Dr yayi yace lallai kai sabon shigane a soyayya.
Ba'aima soyayya gadara, ba'amata fushi, komi sai sa sai da ake binsa saikaga an'cimma nasara.
Karka manta isa da gadara da banzatarwa yakai Aymah da mijinta wannan matsayin da suke Jameel.

Kaikuma yanzu kobakace AYMAH i love you ba akwai hanyoyi da dama da zaka isar da sakon ka, kana dole ka iya kawar da ido akan duk kan abinda zakagani..
Na maganar nata bakomi saika magantaba karkasanya tayimana jimla akan duk haka muke dan Allah kabi komi a sannu kaji.
In kana nan aka kirata so goma ka kawar da idonga Jameel in dai Allah yasa rabonkace to ba makawa Sai tazama taka.
Kana yanzu kai ai abinda zaka rufama kankan Asiri ya dace ka samu ni wannan jigilar motar ma fa Banason ta.
Kabari asamarmaka aikin sumogal kaga yanda cikin lokaci Abubuwa zasu zama tarihi ,Kayi saurin Gina kanka Ka kwashe matar ka.

Sosai yayi murmushi yanajin nawin zuciyar sa na sauke wa yace.
wallahi sai yanzu naji natsuwa amma da wani kunci ke kawoma zuciyata ziyara.
inajin nazama wani kaskantacce wallahi ngd matuka da shawararvka gareni kuma kamar yanda kace zangoyamata baya akan duk abinda tasa gaba daga yau Insha Allah,Nason wannan ma kadai zaisa Tabani matsayi Babba A zuciyar Ta. .

Hannu Dr ya bashi suka kashe tare da daukar motocinsu ko wane ya doshi aikin gaban shi.

Deedee kau da aka kilga kudin data samu 600k ne cif da cif.

Harda yar rawarta ta taka tana sake godema Allah da Ni'ima dayamata.

Anan ta kalli Adnan daya tashi tace'' zan dungama sadaka shinkafa saboda abinda nasamu ta sanadinka kagama cin gari kaji ko,Zansa adinga kaima cen dakin da zasu mai daka...

Shuru yamata yanabinta da kallo kasa kasa

Mikewa tayi tace" Aymah gyaraman ayar nan ina zuwa bani awa daya Inje in dawo suma su Sadam din yanzu zasu zo su debe maki shi.

Tom tace tana dariya da tashi tashiga aikinta itakuma Deedee ta fita.

Kai tsaye Kasuwa ta nufa ta sai Frizer lg guda ɗaya mai kyau na 2700k.
Da katon inji mai kyau dayakai Dubu 130k aka samata a mota tayo gida.

Ana shigomata dasu Aymah ta rike baki da rangada guda tana faɗin.
kaji tsohuwar mai ran karfe, bata dogara ga kowaba Allah Ya kamamiki Dede nah .

Deedee ta buda hannu tace "Ameen,fada ki sake faɗa ummu nah yar aljannah allah ya kara kawo haske a rayuwar ki kinji.

Ameen AYMAH ta amsa kamin ta shiga Buɗa Kwalin Fridge ɗin..

Wayan da suka kawomata kau Duk saida suka hadamata komi kana suka tafi.

Deedee kam sake fita tayi wajen wannan mai Markadan suka gaisa ta bada markade.

Matar nata kumburi Deedee tabata 500 tace ke karba yau abinda zanbaki kenan kudin markade .
Ihu matar tayi na murna kamin suka shiga fira da kanta ta dinga tisama Deedee har saida taga yayi kamar na jiya kana ta bata.

Deedee tace Almajirai nikeso majiya karfi ba yan yaraba kana masu tsafta ba kazamaiba inaso mudinga kasuwa dasu...

Da sauri tace.
Takwana gidan sauki tana kwalama almajirin dake ta jidomata ruwa kira tace ina.
Ibrahim da Sani da naseer dake neman aiki kace gasu ya samu maza.

Aguje ya aje jarka sai gashi kau cikin lokaci da matasan yara yan 17 aguje suka zube suna gaida su.

Dede ta bisu da ido ba laifi fess suka ba alamar kazanta jikin su.

Tace tom yanzu dai ku dauka muje in samaku dokoki Akan kasuwata.

Da sauri suka dauka Tayi sallama da mai Markadan tayi gida...

❤️ *MATAR OGA NA*❤️

*UMMY AYSHA CE*
*PAGE 16*

*Koda suka isa gidan su
Sadam na nan bakin get sunsa Benci sunata fita abunsu Da wasu abokan nasu da Alama majalissa zasu maida wurin .
Sannu da zuwa suka mata ta amsa da masu sannu da aiki.

Yawwa Kaka sukace ta shige ciki Almajiran na biye da ita.

A baranda tace su tsaya kana ta samu kujera ta zauna tace tom". Da farko dai Sannuku da zuwa gidan Sanyin Haj Deedee mai Haɗa Alkhairi da warware Sharri.
zanje kasuwar in Siyomaku kaya banaso naga ko kafar wando ta kece balle A kaiga tsagewar Hantsar wando Al'aura ta samu damar shan iska.
Abu na biyu .
Wanka!.
Dole kuyi wanka kamin kuzo da safe, hakama kamin ku ɗauki tallana dan banshirya biyan kuɗin Asibitin wanda kwalara ta kama ta dalilin kayana da Mutum yasha ba.

Sannan dole kuna dawowa ku aje boket din ku anan kufara wanka ga bayi nan wajen get akwai ruwa kamin ku shigoman muyi issafi .
in dai Kukaiman Haka to zakuga Alkhairin da zanmaku kuma zan rikeku amana Har In mutu in sha Allah.

Cikin sauri suka amsa da yimata godiya tayi murmushi tace kujira inzo.

Ciki ta shiga inda ta iske Aymah ta gama maya duka zobon ta kullemata ta jera sai faman latsa wayar Adnan take da alama abu mai mahimmanci take.

Ganin hakan yasa Deedee sallama da faɗin. Aymah na dawo.

Da sauri ta dago kanta kamin tace" Sannu da zuwa Deedee nah ya gajiyan markaɗe?.

Murmushi tayi tace haba mu agayamana gwagwarmayar rayuwa Aymah ba wata gajiya.
nayi Almajirai gasunan su zasuma dinga kaiman markaɗan da Talla.
Yanzu zan tace kunun inje in'dawo.

Aymah ta tayata murna tare da tashi ta karɓa ta tacemata ta hadamata kamar yanda taga tayi .

Deedee kam yara taja suka sake komawa kasuwa layin yan gwanjo ta samar masu masu kyau da sauki kala biyar biyar kana suka biya wajen masu injin markaɗe nan ta sai guda aka doramata a napep sukayo gidan Su jameel.

Sosai Inna su taita murna da ganin Deedee dan ba karya tayi missing nata ,Tanason zuwa ta ganta amma wani dalili na hanata.

Dede tace Baraka gafa aiki na hadaki Dashi banaso yanzu ahlina su sake zaman banza dan naga illar sa.
Kinga mijinki na ƙoƙarin nemomaku na abinci kema tinda ba inda zaki ga inji nan na sawomaki na markaɗe ki aika makwafta ki sanar dasu kinga dai yanda muke wahalar abun markade a wannan Unguwar.
Ga azumi dama yana kusantowa ba karamin Alkhairi zaki samuba in dai kin tattala,Shima Jameel yanzu abarshi ya tara nashi yayiwa kanshi Amfani..
To gashinan dai nidai kam na saimaki halak malak dan Keɗin diyata ce.

Har kuka saida Inna tayi dan tana da burin ace yau ga binda zatana Ɗan sarrafawa wanda zai kawomata kudi ko dan ragema mijinta dawainiyar wani abun gashi Allah ya kawomata sirika mai kaunarta ta siyamata.
Sosai tama Deedee gdy kana Deedee ta tashi tafiya ta bata 5k akan ta rike ta fita shima malam habun tabashi sukamata gdy kana taja yan Almajiranta sukayi gida sunata murna da kayan da tabasu.

Wanke kayan tasa sukayi suka shanya kamin cikin Nasu suka ɗakko masu sabunta sukazo aka shiryamasu tallah suka tafi .

Jameel kau cikin nishaɗi ya dawo ya biya ya karɓin sabon dinki daya bada amasa na wani maroum ɗin Yadi mai kyau da saukin kuɗi..
Bayan ya dawo gida kamar yanda suka saba ya zuba uban wanka cikin wannan yadin dayamasa masifar kyau kamin ya dakko turare ya fess ya gyara sumar shi ya fito yamasu sallama yatafi .

Sai da yabiya Bakin layi ya masu kunshin Tsire mai zafi babba kamin ya wuce gidan .
A waje suka gaisa dasu sadam kamin yayi ciki yana tako dai-dai .

Kwance take tana fuskanta kofa
Wasu fitinannun kananun kaya ne jikinta da suka mata mugun kyau.
Wani Black Wando ne jikin ta bai kai kasa ba yafi kuma karfin 3quater.
Sai white din shirt data ɓalle maɓallin saman guda biyu kana Hango bakar brah ɗinta.
Daga kasa kuma Ta ɗan ɗaure rigar sai yabada wani tsari mai kyau.
gashinta zube agadan baya sai kyalli yake batasa hulaba sai Black bandana da tasanya ko bant bata saba

Tana ta latsa wayar Adnan Yayin da Deedee ke gefenta tana kilga kuɗin da aka kawomata ta ware ribar ta ta aje ,ta warema Almajiran nata masu hazaka nasu ta aje , sauran kuma na sayayya gobe ne dan da alama Allah yasama abin Albarka ko daya basu maido ba ga gida anata nema ga majalissa dasu sadam suka fara haɗawa sai shigowa ake saye dole gobe ta ƙara mudu in sha Allah.

Da sallama ya turo kofar yashigo kanshi tsaye dan yason dukkan su suna cikin kyakyawan yanayi sai dai kash an samu akasi dan Zuciyar AYMAH baitaɓa bata zuwanshi ba duba da Yanda yamata da safe .

Cak ya tsaya wuri guda kamar an dasa shi yayin da kanshi yayi kasa zuciyarsa na bala'in tsalle,Baitaɓa ganinta a wannan yanayin ba sai so ɗaya kuma shima bai ƙure ganinta ba saɓanin yau da ita ke fuskantar kofar tana kwance akan carpet ranar kau duke take ƙasan kujera tana kuka.

Deedee ce ta dago da sauri tana binshi da kallo tace" Sannu da zuwa Jamalun Deedee lfy ka tokare nan ko ka haɗu da sharrin Baseee mai tsiro ne?

Karamin bakin shi ya turo still bai dagoba sai wasa daya kama da hannu shi yana Taune lips da kyal ya iya cewa " ina wuni .

Aymah kau data kalle shi murmushi Tayi kamin ta tsareshi da ido sai kuma tayi karama dariya tana tashi zaune ta gyara zaman rigarta kullin datama ta kwance ta gyara wuyan daya bude batare da saninta ba kana tace " Bissimillah.


Duk tunanin shi Hijjob ta sanya shiyasa tace mai haka da sauri kau ya dago idon shi yana watsamata harara kuma cak ya tsaya da ganin shi akan baiwar ƙirar zatin da Allah yamata.
Duk iya son Ya kawar da kanshi akanta kasawa yayi saima wani masifaffan yanayi daya tsinci kanshi aciki...
A'Hankali ya hau matsawa inda suke idonshi still akanta baya ko kyaftawa..

Wannan kallo ya tadamata hankali dan batai tinanin hakaba. cikin lokaci ta kasa natsuwa da sukuni da suri ta mike dan haurawa ta canza kaya.

Saidai kash saurinta da kuma gushewar Hankalin da yayi yasa bata an'kareba sukayi mugun Karo gabaki daya ta faɗa jikin shi.
Yayin da shikuma ya mata wani mugun cafka ya riketa gam zuciyar sa na daka tsalle Yanajin inama inama😜 .

Deedee kam ido ta shiga kyaftawa kamin da rarrafe ta shafasu ta shige kiching tana fadin.
" Yan banza wannan ai sai kuka tunoman da Malamina Allah sarki kamar banci Uwar sabadaba ni Saude,Dafa tsabar gayu haka nike zamana gaban malam dagani sai ɗan Kanfai da vest in baza murjanai da jigida ina yawo ɗan tsakar gidan mu in maida idon bawan Allah nan kamar Danjar besfa yayita bina da kallo Yana mazurai.
Hahaha ta sheke da dariya da faɗin Allah ya jikan ka Malam nayi kewar ka.
Da Allah yama tsawon kwana da Har yanzu ina nan ina bazama gayu da kasheka da Kallo na mai tada hankalin Lafiyayyen Dattijo .
Sai kuma ta saki fari kamin ta shiga buga kwano kasa tana fadin.
" kwara kuji ƙara ku dawo hayyacinku kar Allah ya kamani munafukan banza duk kun gama ɓoye ɓoyen an faɗamaku dama so Mahaukaci ne.

Buga kwanan Deedee kam yayi tatsiri dan gabaki daya sun shagala da duniyar da suke da saurin su suka mike Jameel kau jin jiri zai kada shi cikin wani mugun yanayi ya cafko hannun Aymah data nemi haurawa sama kana ya rungumeta tsam a jikinshi yana sauke numfashi zuciyar shi na bada sautin fat fat fat da karfi.

Ayyah sorry! tace tana shafa kwantaccen gashin kanshi kamin ta shiga neman kwace kanta amma yaro yamata rikon manya.

Cikin wata murya mai sanyi sosai na mai neman taimako yace.
" Kibani dama dan Allah,kibani chance na shiga rayuwar ki,Ki budeman kofofin yarda da Aminci ,Kibama zuciya da gangar jiki damar cika muradinsu,Karki duba rashin Cancanta ko Yarinta a'a tausayi da taimako zakiwa aiki ,Ina so....

Mugun tsalle zuciyarta ta dingayi mussamman da ya datse kalman shi ta karshe taso jin furuncin sa kodan samun sauƙin abinda ke dawainiya da ita .

Jameel kau Jajayen idonshi ya ɗago yana cije lips kamin ya saketa ya tallabo haɓarta ya jefa kwayoyin idonsa cikin nata yace"..

Kiyimin yafiya akan abinda y@ faru ,Bazan sakeba na miki Alkawari,Kar wannan yasakimun fassara ba ɗabi'ana bane takura kowa balle ke da kika zama tamkar Amanata.
Ummu ina bayanki akan duk abinda kika sama gaba in dai bai Saɓama Shari'a ba,Duk abinda kikason mafita ne a rayuwarki ki tunkare shi kai tsaye, in kuma kina neman agaji kimun magana zan tsayamiki da karfina in sha Allah.
Abu na karshe kibani dama dan Allah kamar yanda nace miki na shiga Rayuwar ki kai tsaye ma'ana Inaso Babbar akala mai girma tashiga tsakanin mu.

"Kunya sosai ta kamata sai taji ta duk wani iri tabbas Ba karya ta girmi Jameel nesa ba kusaba amma kuma a sigar jiki wani zai iyacewa shine Babba mussamman Yanzu da girman keta sake masa kutse ya fita tsawo sosai gashi da faffaɗan Jiki dan baya cikin layin Ramammun maza
Dan ita kanta ta sheda haka dan wani masifaffan daɗi taji lokacin daya sakata jikinshi ya Rungume wannan kaɗai ya nunamata in'garman namiji ne Babu inda bazai leka ba.

Ido ya zubamata ganin tashiga duniyar tinani.

A'Hankali ya huramata iskar bakinshi mai kamshin Tomtom Yana langwaɓe kai kalar tausayi Yace "Ya dai Ummu nah.

Ɗan farr tayi da ido kamin Cikin sauri tace" mene ma kacemun?.

Ido ya ɗan juya yana shafa kanshi kamin ya zubamata ido yace.

*Kina sona*

Wow...

Wani mugun dirar mikiya maganar tashi tamata dan ko a mafalki batayi tinanin Jin wannan tsadaddar kalma a bakin shi ba dan yanzu.
Dan alayin maza masu mugun zurfin ciki tasa Jameel mussamman akan abinda suke so tanaganin kamar bazai taɓa iya furtawa da wuri haka ba.

Ya tsunshi yasa ya d'an murzasu akan fuskar ta kamin Yace" kinji!.kodai na miki yaro ne..kafaɗa ya ɗaga yana taɓe baki yana wani lumshe ido cikin gaskiya da Gaskiya yace" Aymah nifa ba yaro bane wallahi kinji na rantse miki.


Ido ta zaro kunya sosai ta kamata aguje tayi sama yabita da kallo yana sakin dariya da shafa kai yace" kinbani kam,Nafara gajiya da ɓoyemiki dole nayi saurin ɗaukeki dan in'dinga ganinki cikin wannan shigar mai kwantar min da Hankali.


Deedee ce ta kwalamai kwano aka tace" munafuki ashe dama kana magana haka shine ni in zamuyi magana kaitacin magani kana budeman Hanci.

Cikin nishaɗi yace" to ke auranki zanyi da zan buɗe baki naitai miki kalami,Dan Allah Deedee nah kitayani yaki akan soyayyarta wallahi yanzu ina sonta , In dai ta shirya zama dani a haka Zanyi iya bakin kokarina naga na tsayama rayuwarta bance saina mata komiba amma nayi alkawarin bazatayi kuka ba, Dan Allah Deedee nah kicemata ta soni kinji

Murmushi tayi tace "karka damu ka barwa Allah, a halin da muke ciki yanzu bazan turasasa Aymah son kaba Jameel.
in naimata haka kamar ban kyautatamata ba,Saidai kai namiji ne dole kabi dukkan hanyar da kason zata fisheka ta kawo kanta da kanta,Ai bazai yiyu daga cewa kana sonta ba ta amsa kabari tayi shawara,Balle ma ni inaji ajikina tana sonka, yo wazaiki jinin Deedee ai sai wanda bai samu ba,Kadai ganni da tsufana amma yau dattijon da zai haɗaman injin markaɗe sauran kaɗan ya faɗamai ga kafa yo ai mune kyau wlh.

Dariya yayi kamin ya rungumeta yace "ina sonki yar kyakyawar Kakata gagara ba dau an'buga dake an barki..

Faɗa ka sake faɗa Jameelun Deedee tace tana bashi hannu suka kashe dukkan su cikin farin ciki.

Naman daya wullar ya dakko ya bata yace Anyi kiran sallah yau na dawo da wuri zanje sallah na dawo mikika dafa?

Tace Taliyace na silala maza ka dawo kaci ka mayar da fura akai.

Fita yayi yana kallon sama ko Aymah zata sakko amma ina bata fito ba.

Saida ya biya Toilet din waje ya tsarkake kanshi da wanke dogon wandon sa kamin ya daura Alwallah yayi masallaci.

Aymah kau tinda tayi sama ta fara daka tsalle na murna tanajin wani dadi tanajin rabin matsalarta ta kau a daidai wannan lokacin.


Cikin farin ciki tace na Amince my jameel amma inajin kunyar faɗama gaskiya.

Wanka tashiga tayi ta canza kaya da pad kamin ta fito waya makale a kunnan ta.

Sosai taji tanajin kunyar Deedee gani take kamar tason komi.

Deedee kam wayan cewa tayi da faɗin Aymah ga namanki nan keda Jameel.

Murmushi tayi tace mungode zai dawo ne?

Kai kawao Deedee ta dagamata tana kabbara sallah.

Aymah kau wayar ta dauka tashiga latsawa cikin lokaci kuma ta mike ta dauki Hijjob ta fita.
Bayan sun gaisa dasu Sadam ta buɗe get ta fita dukkan su suka bita da Kallo.


Bai yarda ya fitoba saida akayi Isha kamin ya fito farin ciki kwance a kan Kyakyawar fuskar shi.

Daga nesa yake Hango kyakyawar fuskar ta dake jike da Hawaye.
A'Hankali ya fara tahowa zuciyar sa na bugawa. inda yakejin sautin maganata kasa kasa wasu takaddu rike a hannuta tana faɗin.

"Babu yafiya tsakanina dashi yamun babban tabo,Badan ina kai zuciyana nesa'ba da tabbas da kaina zan kashe shi,Badon rabbi ya bani danganaba da bazan iya haɗa makwanci dashi ba.
Amma na yarda kar akai magana Court abarshi ya girbi abinda ya shuka tin anan Duniya.

Mutumin da ke zaune akan Machine kanshi rufe da p-cap ya fara magana.

Aymana ko kinso ko kinki hujjoji sun kammala sai na makashi court.

Cikin kuka tace A'a...Nace aa dan Allah ta karasa cikin mugun kuka.

Jameel kau sosai kanshi ya ɗauki zafi tabbas yason wannan mai magana , Amma ina? kuma waye shi a wajen ta? waye zasu kai court? minene akaimata miye Aymah ke ɓoye masa ya salama ya fada yana karasawa inda suka cikim sassarfa.

Mai Machine din da ba'a ganin fuskar shi ya tada Machine yayi tafiyar sa tinda yaga kussantowar Jameel.

Aymah!.
Jameel ya fada yana kama hannuta.

Da sauri ta juyo bata tsaya komiba ta fada jikinshi ta hau uban kuka...


Kafaɗarta ya shiga bibbugawa kamin ya kama hannuta suka ɗan matsa gaba da gidan wajen dake da karancin haske.

Akan wani Ɗan Dandamali ya zaunar da ita kamin shikuma Ya ɗora gwiwoyinsa kasa.

Gabaki daya hannuwan sa ya haɗe yace dan Allah dan Annabi Kiyi Hakuri,bazan takuramiki.ba Aymah akan sai Nason mikike ɓoyemun.
Amma dai inaso kiyi tawakkali, Kana duk Rintsi kalmar kisa ta daina zama bakin ki,Babu mai cuta a wannan Rayuwar ya zauna lfy.
Kana babu abinda ke dawwama sai ikon Allah.
Kiyi hakuri dan Allah in dai bakyaso wannan yanayin naki ya kwantar dani...

Idonta dake cike da Hawaye ta dago tace Jameel minaima Adnan A Rayuwata.
Mi iyayena suka tare masa.

Jameel ko kason Adnan ne Ya tura Babba motar da ta latse iyayena?????



❤️ *MATAR OGA NA*❤️
*UMMY AYSHA*

Page 17


""Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un yace yana dafe kansa da rintse idonsa sosai Hawayen tausayi dana jimami na zubomai . .
Lokaci daya kuma wannan masifaffan zazzabin dakemai sallama ya fara hayayyaƙomasa

Please Login or Register in order to submit comment